ZABIN SAMHA CHAPTER 2
Washe gari da safe samha ta tashi, Yau kam batada lectures sai zuwa karfe biyu na rana. Bayan ta shiga bayi ta wanke bakinta ta fito taje dakin anty fanneh don ta gaisheta, ta sameta tana faman shirin zuwa aiki.
“Ammi ina kwana” ta gaishe ta.
“Lafiya lau baby, kin kwana lafiya? ya ciwon kan yanzu. Hope dai ya lafa miki?” Anty fanneh ta tambayi diyarta.
Samha ta bata ansa da eh ya lafa mata.+
“Toh nasan yau bakida lecturers da wuri, zan baki dan kudi keda lami zuwa anjima kuje kasuwar kingsway ku danyi mun cefene. Kinsan munada bako yau zai zo, so inason a dan dafa mishi delicacies.”
“Kai ammi wai dan Allah dan yaron mutumin nan zai zo zaki wani ba kanki wahala kiyi girki? Sai kace wani babban bako zamuyi. Ai ko snacks da ruwa aka bashi idan yazo sun isheshi.”
” Kuji mun yarinyar, dan nashi kike ce ma yaro? Toh ashekaru dai ya girme ki nesa ba kusa ba don har shekara hudu ya baki da zaki ce mishi wani yaro. Kinga idan Allah ya yarda ma very soon shima zai zama dana. Kinga zaki samu yayah namiji da zai dinga kula da ke ballanta ma kinga makarantar ku daya. Bayan haka Kumma samha, ance bakonka annabin ka. Kema kinsan duk bakon da zamuyi a gidan nan sai mun mushi tarba mai kyau. So bana son wani surutu, ga kudin nan anjima in kin shirya kuje mun kasuwa”.
Dariya samha tayi tace ” Toh ammi yi hakuri, na tabo miki da. Bazan sake kiranshi yaro ba daga yanzu ma yayah zan dinga ce mishi”
anty fanneh tace ” wanan kuma keh kika sani,in kinga dama ki kirashi da kaninki, wanan ya rage tsakaninku. Ungo ki karba, ni kinga tafiyata ban so nayi late.” Anty fanneh ta mika mata kudin, ta karba sukayi sallama ta wuce aiki.
Samha na shiga dakinta tadda wayarta nata faman ringing akan gado. Da sauri ta karasa ta dauki wayar, sunan amjad ta ganni a rubuce a wayar ta daga.
Muryanan nashi mai dadin sauraro kuma mai kashe mata jiki taji ya doke kunnenta. ” hello samha, good morning ya kike?
Lumshe idanunta tayi kamar yana gabanta sa’anan tace mishi “lafiya lau”
“Da fatan kin tashi lafiya?” ya tambayeta.
” Lafiya lau, ya gida?” ta tambayeshi.
Nan shima ya bata ansa. Ya fara tambayarta karfe nawa zata shigo makaranta yau. Tace mishi kafin karfe biyu.
“Zan iya biyowa ta gidanku sai mu wuce school tare? Ya tambayeta.
Cike da zumudi ta bashi ansa da eh yabiyo ta gidan nasu. Yace ta turo mishi da address. Tace toh zata turo mai sukayi sallama.
Tsalle ta dinga yi tanata faman murna. Ji takeyi kamar a mafarki. Wai yau amjad ne zai zo har gida ya dauketa su tafi makaranta tare?.
Duba lokaci tayi taga har sha daya ta kusan yi. A gurguje ta fada bayi tayi wanka ta fito ta shirya, ta kira lami suka tafi kasuwa. Driver din gidan ne ya kaisu, Nan suka tsaya sukayi cefanen da anty fanneh ta aikesu. A hanyar dawowarsu ma suka dan samu go slow a hanya. Barin ka lagos da hanyoyinta bata taba rabuwa da traffic.
Ko da suka dawo gida ma lokaci har ya tafi don karfe daya har ta gota. Ta haura sama ta fara shirinta zuwa makaranta.
A gaban mudubi ta zauna bayan ta fito daga wanka ta fara caba kwaliya. Dayake bata wani saba yin make up ba, tana gamawa taga ta canza kamar ba ita ba. Doguwar sumar ta data sha gyara sai shekki takeyi ta fara tajewa. Sa’anan ta dauko Ribbon ta tufke gashin a tsakiyar kanta. Samha bata cika yin kitso ba saboda laushin gashinta, ko tayi warwarewa take. Shiyasa rai da rai zaka ga sumar kanta babu kitso.
Doguwar abaya ta ciro ta saka, ya zauna a jikinta cib cib kamar an gwadata akayi dinki. Ta dauko gyalen abayar tayi wrap round dashi. Turaruka ta debo ta fefesa gabadaya jikinta. Tana cikin haka wayarta ta fara ringing ta daga. Amjad ne ya sanar da ita yana kofar gidansu. Tace mishi gatanan yanzu zata fito. Yace toh sai ya ganta.
Bakin takalmi ta ciro ta sanya a kafanta sa’anan ta dau jakar makarantarta ta fito.
A nan kofar gida ta tadda dashi yayi parking motarsa. Bude kofar seat din gaba tayi hade da sallama ta shiga ta zauna.
Ya ansa sallamar. Binta ya dinga yi da kallo don tayi mishi kyau sosai bai san sanda ya furta “wow, samha you look beautiful. Kinyi kyau sosai.”
Kunya ce tadan rufeta ta sunkuyar da kanta tace mishi ” nagode”.
Taji dadin yabon kwaliyarta da yayi.
Murmushi ya sakar mata sa’anan ya tada motar suka dau hanyar makaranta suna tafiya suna dan taba hira yana dan zolayar ta. Ita kam sai rufe fuska take tana murmushi cike da jin kunyarsa.
A haka suka iso makaranta, wurin da students suke parking motoci yaje yayi parking, suka fito tare.
Students suka fara binsu da kallo dan yau ce rana ta farko da aka gansu tare sun shigo makaranta. Samha da amjad sukayi kamar basu aketa faman kallo ba suka shiga cikin department suka karasa aji.
Su khady ta tadda a cikin aji, taje ta same su, shi kuma amjad ya nema seat a gaba ya zauna suna jiran lecturer dinsu ya shigo. Bafi yan mintina ba dr kabir ya shigo ya fara musu lecture. Bayan ya gama lecture din ya sanar dasu ranar da zasuyi test dinshi don haka su shirya.
Wasu daluban suka nuna farin cikinsu a fili game da test din wasu kuma na fargaba don sun san bazasu kai labari ba a course din.
Ranar dai kwata kwata bata wani ji duriyar sabah ba, idan tunaninshi ma yazo mata sai tayi saurin kawar dashi don bata son abun da zai katse mata farin cikin da take ciki a yanzu. Ranar ita da amjad suna tare,don har cafeteria suka tafi dashi da ita dasu khadija suna ta faman hira tsakaninsu. Amjad kam bashida matsala don nan da nan suka saba tsakaninsu.
Da suka gama lectures su khadija suka musu sallama, suka wuce gida ya rage taga ita sai shi.
Amjad duban samha yayi yace suje ya ajiyeta a gida tace mishi toh bari ta sanar da amminta don ita ke zuwa daukanta a makaranta. Yace toh. Nan ta ciro waya ta kira anty fanneh tace mata ba sai tazo daukanta ba, friend dinta zai kawo ta gida.
Anty fanneh ta fara tambayarta akan friend din da tace zai kawo ta gida, tace mata course mate dinta ne . Ammi tace mata toh ta kulla sai tazo gida, ta katse wayar.
Inda yayi parking motarsa suka nufa suka shiga ya tada motar suka dau hanyar gida.
Cikin yan mintuna sai gasu a kofar gida, yayi parking dai dai gate din gidansu.
Juyowa yayi yana dubanta ya kira sunanta a hankali “samha…”
Yanda ya kira sunan nata taji gaba daya jikinta ya mutu ta dago kanta ta kafe shi da shanyanyun idanunta tana kallonsa.
“Gaskiya yau naji dadin kasancewa tare dake. Bazan iya misalta miki yanda nakeji a duk sanda na tsinci kaina tare dake ba cikin yan kwanakin nan” ya fada mata yana kallonta.
Ajiyar zuciya samha tayi tace ” nima naji dadin kasancewar mu tare yau amjad. Ni kaina bazan iya explaining yanda nakeji ba a duk sanda nake tare dakai ba.Thanks for making my day.”
Maganar datayi yasa yaji dadi ya Kamo lalausar hanunta cikin nashi yana sakar mata murmushi daya kara bayanar da kyaun halitar fuskarsa.
Sun dau kusan minti biyar suna kallon junansu basu sake cewa komai ba.
Samha ce ta zame hanunta daga cikin nashi ta bude jakarta ta ciro handkerchief dinshi data wanke. Ta saka mishi a hannu tana fadin ” nagode sosai da kulawar daka bani ranan. Bansan irin godiyar da zan maka ba daka kasance tare dani a wanan lokacin”.
Girgiza mata kai yayi sa’anan yace ” meye na godiya kuma samha. Ai kin cancanci fiye ga haka a wurina. Baki san halin dana shiga ba dana ganki cikin wanan yanayin. Promise me bazaki sake barin wani abu makamancin haka ya saki kuka ba, kuma handkerchief din ki rike ba sai kin dawo mun dashi ba.”
Wani irin sonsa ne ta kara ji yana fusgar zuciyarta. Godiya ta sake masa ta mishi alkawarin bazata sake bari ya ganta cikin irin wanan yanayin ba.
Nan sukayi sallam yace zai kirata a waya zuwa anjima. Tace mishi toh, ta fita daga motar ta shiga cikin gida cike da farin ciki.
Shi kuwa Amjad, Binta yayi da kallo har ta shiga cikin gida, yana ajiyan zuciya. Ya rasa gane irin feelings din dayake ji game da samha don tun ranar daya ganta tana kuka yaji gaba tausayinta ya kama shi. Ya kasa daina tunaninta. Daman shima ya jima yana sonta. Kawai tunkararta ne baiyi ba ya fada mata, don tun a aji daya yake lura da ita. Batada rawan kai irin na sauran matan department dinsu da suke kawo kansu gareshi. Ita komai nata daban yake kuma yana ganin mutuncinta sosai don haka yana ganin in har suka daidaita bazata bashi matsala ba.
Da wanan tunanin yaja motarsa ya wuce gida.
Samha na shiga gida ta tadda anty fanneh ma har ta rigata isowa gida. Tana ta faman girki ita da lami. Shiga kitchen din tayi ta gaishe su tana musu sanu da aiki. Suka ansa.
Anty fanneh tace mata oya oya ta je ta ajiye jakarta in tayi sallah ta sauko tazo ta taya su a kitchen. Samha ta ansa mata da toh ammi, ta haura sama.
Bayi ta fada tayi wanka ta dauro alwala tayi sallah, ta sa kaya sa’anan ta sauko kasa ta samesu a kitchen ta fara taya su.
Cikin dan kankanin lokaci suka kammala girkin suka jera kan dining.
Anty fanneh tace zata haura sama ta dan watsa ruwa a jikinta. Samha tace mata toh ta samu wuri ta zauna a parlour ta dauki remote ta fara duba channels tana kallo.
Can sai ga anty fanneh ta sauko har tayi wanka ta canza kaya. Tace ma samha bakon su har ya kirata a waya yana hanyar zuwa. Samha tace toh sai yazo, Allah ya kawo shi lafiya.
Bayan kusan minti talatin sukaji karan horn a kofan gida mai gadi ya bude gate, mota ta shigo. Daman anty fanneh ta fadawa mai gadi zasuyi bako, don haka idan yazo ya bude gate ya barshi ya shigo.
Bayan yan mintuna Sukaji an kada kararawar shigowa, samha tacewa wa ammi bari taje ta shigo dashi. Ammi tace mata toh. Mikewa tayi ta nufa hanyar shigowa parlour.
Tana bude kofar tayi churus ta tsaya ganin abunda bata taba tsamanin a rayuwarta ba.
Sabah ta gani tsaye a bakin kofa, kamar ko da yaushe, hannunsa duka biyu sanye cikin aljihu. Sanye yake cikin kaftan. Bata taba ganinsa cikin kaftan ba sai yau kuma Kayan sun mishi kyau sosai.
Bude baki samha tayi tana binshi da kallon mamaki daga bisani ta rufe idanunta ta sake budesu don ta tabbatar ba gizo suke mata ba.
Sabah din nan dai ta gani still yana tsaye. Shima kallon mamaki yake binta dashi.
Tsabar rudani bata san sanda ta rufe kofar ba ta barshi tsaye a waje zuciyar ta sai faman bugu takeyi. Abubuwa da dama ne suke mata yawo a kai a wanan lokacin. Toh meye sabah yazo yi a gidansu? Kar dai shine yaron mutumin da ammi take kirarin zata aura?
rufe idanunta tayi gam tana fadin inaa it’s not impossible… bazai yuu ba. Killan batan hanya yayi.
Anty fanneh data ji shiru shiru ta mike don ganin abunda yasa samha ta dau lokaci, zuwa tayi ta tadda da ita ta rufe ido ta jingina a jikin kofar.
” keh meye haka, kin wani rufe ido kina tsaye? Ina bakon da kika ce zakije ki shigo dashi?.
Samha bude ido tayi tana duban anty fanneh zuciyarta sai faman bugu takeyi tace mata yana waje. Salati anty fanneh ta sake tana fadin ” samha wani irin shashanci ne wanan zaki bar bako tsaye a waje baki bari ya shigo ba? ban hanya na wuce” ammi ta fada ranta a bace.
Girgiza kai samha tayi tana kallon anty fanneh sai faman zare ido takeyi kamar batada gaskiya.
Tsaki anty fanneh taja ta tureta daga jikin kofar ta bude. Har lokacin sabah yana tsaye a bakin kofar. Anty fanneh na ganinshi ta fara bashi hakuri akan barinshi da samha tayi a waje tace mishi ya shigo.
Yace mata babu komai, ya shigo ciki.
Nan ta sake rufe samha da fada ta inda take shiga ban nan take futa ba kamar zata rufe ta da duka. Sabah hakuri ya fara bata yace kar taga laifinta.
Samha bata ce komai ba illa wani irin kallo data dinga binshi dashi. Anty fanneh ta karaso dashi cikin fallo tana mishi sannu da zuwa nuni ta mishi da kujera daya zauna. Sabah cikin girmamawa ya samu wuri ya zauna sa’anan ya gaisheta. Cike da fara’a anty fanneh ta ansa mishi
tana tambayarsa mutanen gida. Ya bata ansa da duk suna nan lafiya. Bayan sun gama gaisawa ta mike tace tana zuwa ta shiga kitchen. Ya rage daga samha sai shi.
Harara ta galla masa sa’anan ta bude baki tana fadin ” meya kawoka gidan mu? Ko ka biyo ni har gida ne kaga ka kara musguna wa rayuwata?” Ta jefo mai tambayar.+
Shima harara ya galla mata hade da jan tsaki sa’anan yace ” keh fa kin cika daukan kanki da muhimanci dayawa. An gaya miki nasan cewa nan ne gidanku? Ai dana san zan ci karo dake a gidan nan bazan ma bata lokacina nazo ba”
“Toh ai yanzu ma bata bace ba, zaka iya tashi kayi tafiyarka tunda lokaci bai kure maka ba” Ta gaya mishi hade da daga murya.
Anty fanneh da take kitchen tana kokarin hada mai kayan lemun da zai sha ta jiyo samha tana faman daga murya. Da sauri ta baro kitchen din ta shigo fallon taga samha ta bata rai kamar zata rufeshi da duka” wai samha akwai abunda yake damunki ne yau dinan. Bakon namu ne kike yiwa tsawa haka? Meye haka?” Ta tambayeta.
Samha turo baki tayi tana galla masa harara. Shi kam murmushin mugunta ya sakar mata ta bayan anty fanneh. Ai kam nan da nan ta cika tayi fumm cike da fushi ta mike fuuuu tayi hanyar sama ta shige dakinta.
Anty fanneh ta bita da kallon mamaki, toh wai me ke faruwa ne. Don bata san dalilin dayasa samha take haka ba. kirkiro murmushi tayi tana duban sabah wanda kanshi a sunkuye yake cike da jin kunyar anty fanneh. Hakuri ta sake bashi akan abunda samha ta mishi, yace mata babu komai. Lami ta kira tace mata ta kawo mishi kayan motsa baki. Lami ta shiga kitchen ta debo lemun sanyi ta fara ajiye mishi akan table dake gabansa. Daga bisani ta koma ta debo mishi abinci ta kawo mishi. Lemun kawai sabah yasha , suka sake gaisawa da anty fanneh. Nan suka dan taba hira tana mishi tambayoyi game da karantunsa da sauransu. Anty fanneh taji sabah ya shiga mata rai farar daya, ko don kamar dataga yanayi da mahaifinsa ne. Gashi kuma tana ganin bazasu samu matsala ba don ta lura kamar yaron yanada hankali. Suna cikin maganarsu sai ga kiran mahaifin sabah nan ya shigo wayarta ta daga. Bayan sun gaisa ya fara tambayarta ko sabah ya zo tace mishi eh gashi nan ma suna tare. Yace to yayi kyau sai zuwa anjima sai sake kiranta. Sukayi sallama ta kashe wayar. Suka cigaba da maganansu. Dayake anty fanneh batada matsala nan da nan ta fara janshi a jiki kamar wani danta har ta samu ya sake jiki sunata faman hira.
Bayan kusan minti talatin sabah ya duba lokaci yace zai wuce, bai son dare ya masa. Anty fanneh tace toh ya dan jirata tana zuwa. Nan ta haura sama ta debo mishi kaya kala kala ta zuba cikin jaka ta sauko kasa ta mika mishi tace gashi ya kaiwa kakarsa hajiya bilkisu. Godiya ya mata yace zai mika sakonta.
” toh sai yaushe kenan sabah”.
“Insha Allah nan bada jimawa zaki sake ganina Anty” ya bata ansa.
Taji dadi tace “toh shikenan nagode sosai sabah sai ka sake zuwa, ka gaishe mun da mahaifinka da mutanen gida”
Yace toh zasu ji sukayi sallama yaje inda yayi parking motarsa yaja ya tafi.
Sabah yana barin gidan, anty fanneh ta haura sama cikin sauri ta nufi hanyar dakin samha ranta a bace. Tana shiga ciki ta tadda ta zaune a kan gado gabadaya tayi wani iri sai faman hucci takeyi.
Nan take Anty fanneh ta fara mata fada ta inda take shiga ba tanan take fita ba, har bata san sanda ta fashe da kuka ba don abunda samha tayi ya mata ciwo don tana ganin kamar bata son ta sake wanan auren ne shiyasa tayiwa sabah haka. Samha tana ganin ammi ta fashe da kuka hankalinta ya tashi ta matso kusa da ita ta fara bata hakuri tana rarashinta.
Cikin sheshekar kuka ammi take fadin “yanzu samha don baki son na sake wani auren shiyasa kikayi wa yaron mutuminan wulakanci dazu? Ai da kin fito filli kince mun baki san wanan auren ba sai kin fake da wulakanci ba, halin da ban sanki dashi ba. Wallahi kin bani mamaki. Yanzu idan yaje gida ya fadawa mahaifinsa da wani ido zai kalleni eh samha. Kin wulakanta ni yau wlh. Amma babu komai.”
Samha hankalinta a tashe jin kallaman anty fanneh ta fara fadin ” wlh ammi ba haka bane, wlh har ga Allah banyi niyan wanan abun ya faru dazu ba. kawai nayi mamakin ganinsa ne a gidanmu. Don na sanshi tun a makaranta kawai dai bamu shiri ne dashi. Ta fada amma bata gaya wa ammi gashi abunda ya hadasu ba.
“Ammi dana ce na baki goyon bayan auren nan dari bisa dari wallahi har ga Allah da gaske nake. Kiyi hakuri akan abunda ya faru dazu, bazan sake ba”. Ta karasa maganar tana kamo hanun ammi tana share mata hawaye.
Da kyar dai ta samu ta rarashi anty fanneh tukuna ta dan sauko. Mikewa tayi tace mata zata tafi daki sai da safe. Samha itama ta mata sai da safe. Anty fanneh na barin dakin samha ta zabga uban tagumi. Tunani kala kala ne ke mata yawo aka. Wanan wani irin damuwa ce wanan ta tambayi kanta. Tana cikin wanan tunanin kiran amjad ya shigo wayarta , tana ganin shine ke kira ta danji sanyi a ranta, ta daga.
Amjad yaji muryar ta wani iri kamar ba yanda ya saba jinta ba. Nan da nan shima ya shiga cikin damuwa ya fara tambayarta. Tace mishi babu komai kanta ne ke dan mata ciwo. Ya mata sannu yace tasha magani. Bayan sun dan taba hira, yace bari ya barta ta huta zai kirata da safe. Sukayi sallama ta kashe wayar.
A daren ranar dai da kyar samha ta runtsa.
Washe gari da safe ta shiga school kenan dai dai hanyar shiga department dinsu taga anzo anyi parking power bike a gabanta. Mashin ce irin mai shegen gudu dinan. Sabah ta gani zaune kan bike din ya cire helmet din daga kanshi ya zuba mata ido. Itama tsayawa tayi tana kallonsa. Yau sanye yake cikin bakaken kaya riga da wando baki sai leather jacket shima baki daya dora akan rigarsa. Komai nashi bakake harta power bike dinsa ma baka ce. Tana mamakin yanda akayi aka barshi ya shigo cikin makaranta da wanan katuwar mashin nin mai shegen gudu.
Dataga kallon nasa yayi yawa ta kawar da kanta gefe tana kallon wani wurin.
Bude bakinsa sabah yayi ya fara fadin ” daman nazo na gaya miki ne, babu dole zaki iya gaya wa mahaifiyarki ta janye maganar aurenta da mahaifina. Kinga daga nan kowa zai samu zaman lafiya. Ba wai kizo kina wani cicin magani in kinga mutane ba. Don haka tun wuri ku yanke shawara.
Samha ta dubeshi fuskarta a daure sa’anan tace ” farin cikin mahaifiyata yanada mahimancin a wurina fiyye da yanda kake zato, bazan iya nuna rashin amincewata da wanan auren ba saboda ina samun matsala da kai ba. Sabah ko a yau ni da kai zamu kasance muna samun sabani kullum bai isa nace zan tauyewa mahaifiyata farin cikinta ba. Nasan ba lallai bane ka fahimce hakan tunda kai farincikin dan adam ba komai bane a wajenka ba. Don haka ni ka bani hanya na wuce” tana karasa maganar tabi ta gefensa tayi tafiyarta ta barshi a wajen.
Bayan tafiyarta shiru yayi yana nazari maganganunta s’anan ya girgiza kai ya tadda mashin dinsa yayi gaba.
Samha na shiga cikin aji ta samu wuri ta zauna suka fara lectures. Su khady suna zaune a gefenta. Amjad shima yana zaune a seat din gaba. Suna gama lectures dinsu. ita da amjad suka sauko kasa tare. Departmental garden dinsu suka je suka samu wuri suka zauna. Wurin shiru sai kukan tsuntsaye ga sanyi dayake ratsa wurin saboda yawan bishiyoyi. Wurin dai abun sha’awa.
” ya ciwon kan naki yanzu, ina fatan ya lafa miki” ya tambayeta .
Murmushi ta sakar masa sa’anan tace ” karka damu amjad, ciwon kaina ya lafa. Jin muryarka kadai ya isheni na warke ai”
Wani irin dadi yaji daga jin kalamanata. ” Allah ko? Amma naji dad don jiya gabadaya hankalina a tashe yake dana ji kince kanki na ciwo kinsan banso naji ki cikin wata damuwa gabada daya sai naji na kasa samun sukuni”.
Juyowa amjad yayi yana fuskantar ta. shiru yayi yana kallon fuskarta sa’anan yace “Samha a gaskiya bazan cigaba da boye miki ba, yau zan fallasa miki sirrin dake cin ruhi na, ina son ki samha. Kuma so tsakina da Allah. Nasan zaiyi wuya ki yarda amma samha na jima ina dawainiya da sonki. Tun muna aji daya nake noticing dinki. Kuma na yaba da halinki. Kinada kirki samha kuma ga nutsuwa. Haka nake son naga ya mace. Dan Allah samha ki bani wanan damar na nuna miki irin son danake ji a tattare dake”.
Samha kamar daga sama taji kalaman nasa. Bude baki tayi tana kallonsa kamar a mafarki. Wai yau Amjad ne ya furta mata yace yana sonta? Anya kuwa kunenta sun jiyo mata daidai?
Murmushi amjad ya sake sa’anan ya cigaba da fadin. Nasan kina mamakin kalamai na, ni kaina mamaki nakeyi game da yanda nakejin ki cikin zuciyata yan kwanakin nan amma ba abun mamaki bane tunda Haka Allah ke abunsa. Kuma shine ya jarabceni da sonki.”
Shiru samha tayi ta cigaba da kallonsa, don kamar mutuwar zaune tayi ta kasa cewa komai.
“Kinyi shiru baki ce komai ba samha, kin barni inata magana”
Dagowa tayi tana dubanshi bata ce komai ba.
“Kin amince kina sona samha?” Ya tambayeta .
Ta gyada masa kanta. “A’a nafi son inji daga bakinki. Ki kira sunan kice mun kina sona samha ko zanji sanyi cikin zuciyata.”
Bude baki tayi cike da jin kunyarsa sa’anan tace ” Na amince ina sonka Amjad” ta fada tana sunkuyar da kanta.
Amjad ji yayi kamar an masa kyauta da gidan Aljana da jin kallamanata. Wani irin dadi ne yaji ya rufe shi yace ” nima ina sonki samha. Nagode sosai kuma naji dadi da kika amince dani. Yanzu as from now you’re officially my girlfriend koh? Ya tambayeta.
Gyada mishi kanta tayi. Dariya yayi sa’anan yace ” anya zan iya bacci kuwa yau dinan, gaskiya kin sani farin ciki matuka yau dinan.” Ya fada yana cigaba da dariya.
Ita kam samha duk abunda ke wakana tsakinta dashi ji takeyi kamar a mafarki. Bata taba tunanin zuwan wanan ranar ba. amjad ne ma yafi bata mamaki, musamman kalamansa, don ita kallon shuru shuru take masa. Ashe ya iya tsara kalamai haka? Ta tambayi kanta.
Cike da farin ciki suka dinga fadawa junansu kallamai masu ratsa zuciya.
A ranar dai tare suka dinga komai bayan sun gama lectures dinsu na ranar da kanshi ya kaita har gida. Koh data isa cikin gida ta gaida ammi ta haura sama dakinta wayarta ta ciro ta fara neman su khady a layi. Nan ta zayane musu komai cike da murna da farin ciki suka dinga hirar amjad, suma suka nuna jin dadinsu.
Samha ta dinga jin kanta a sama, taji duk wata damuwa ta gushe mata. Batada wani farin ciki sai na amjad. A daren ranar suka jima suna waya ita dashi, da kyar bacci ya samu nasarar dibanta.
Yau asabar ta kasance ranar da amjad da sabah zasuyi practice na basketball dinsu. Samha tayi tayi da amjad akan ya fasa zuwa buga basketball dasu sabah. Murmushi kawai yayi yace “c’mon baby, it’s just a friendly match. Kawai fa practice zamuyi dasu. Babu komai a ciki”.+
Da kyar dai ya samu ya shawo kanta tace toh taji amma tare zasu je gym din. Yace babu matsala. Ta kirasu khady a waya tace su shirya su zo gym din makaranta. Akwai match da za’ayi, Amjad da su sabah zasu buga basketball.
“Sabah da amjad kuma?” Khadie ta tambayeta.
“Kedai kawai kuzo ke da amina, idan kunzo zan baku labarin komai”.
Tace to sai sunzo ta katse wayar. Cikin dan kankanin lokaci ta gama shirita ta sauko kasa ta fadawa anty fanneh zataje school ta dawo. Anty fanneh tace mata toh sai ta dawo.
Amjad ne yazo ya dauketa a gida suka tafi makaranta tare. A hanya ma sai mishi korafi samha takeyi akan practice din da zasuyi, shi kam ya dinga bata baki har suka isa makaranta. A gaban gym yayi parking motarsa, ya fito ya kira sauran yan team dinshi suka ce mishi suna ciki, yace toh gashinan zuwa.
Su na shiga ciki suka tadda yan team nashi sanye da uniform dinsu na basketball. Amjad yaje suka gaisa shima ya shiga changing room ya saka nasa uniform din. Su khady ne suka shigo suka hango samha zaune kan kujerun dake saman benen gym din da akayi don zaman yan kallon wasan. Tare suka haura saman matakalla suka sameta.
Khadija ce ta fara tambayarta abunda ke faruwa. Nan samha ta zayane musu komai. Amina ce ta girgiza kai tana fadin “lallai sabah dinan sai a hankali, sai kace wani shaidan. Meye matsalar shi ne wai?”
Khadija ce tace ” ku barni dashi kawai, ni ce maganinsa. kwana biyun nan na zuba mishi ido ne naga iya gudun ruwansa amma zan gyara masa zama ne”. Ta karasa maganar tana hucci.
Dariya samha tayi tana fadin ” ku kyaleshi kawai. Ni bazan biye mishi ba. Zai gaji ne ya bari”.
Suna cikin maganarsu sai ga sabah da abokanansa sun shigo cikin gym din. Kowa yayi shiru aka zuba musu ido ana kallonsu. Yanayin shigarsu ma daban yake. Fuskarsu a daure tamau kamar basu taba dariya ba suka karaso cikin gym din, sabah na gaba su shinoh na biye dashi a baya. Amjad ne ya karaso fuskarsa dauke da murmushi yazo shima yan team dinshi na biye dashi a baya ya mika hanu suka gaisa dasu sabah.
Amina ta duba su samha tace ” ya naga su sabah sun shigo sai kace wani yaki za’ayi, Kalla fa yana yin su.”
Daman tunda su sabah suka shigo samha taji hankalinta ya tashi, tana tsoron abunda zai biyo baya sanadiyan buga wanan kwallon. Zufa ne ya soma karyo mata duk da AC da aka zube cikin gym din suna aiki.
Cikin yan mintuna coach din ya sanar dasu za fara wasa su shirya. Dayake gym din babban wuri ne har yawanci dalubai sun shishigo sun zazauna suna son su kalla wasan. Coach ya hura whistle alamun su fara bugawa. Nan da nan wasa ta barke kafun kace meye sabah ya kwace kwallon daga hanun amjad ya saita ta cikin raga ta shige. Nan da nan yan kallon daga department dinsu sabah suka sa ihu suna murna.
Amjad yayi curuss yabi sabah da kallon mamaki don shi a tunanin sa sabah bai iya bugawa ba shiyasa ma yazo ya sameshi daya koya masa.
Amma ya kawar da mamakinsa gefe shima ya zage jiki ya fara bugawa cikin zafin nama, su shinoh ma ba barsu a baya ba don kafun kace meye, ko minti goma ba ayi ba da fara bugawa har su sabah sunci score bakwai su amjad suna na biyu.
Hankalin samha ya tashe ta dubi amjad wanda yaketa faman zufa shida yan team dinshi suna kokarin su kwace ball din daga wajensu sabah amma hakan ya citura. Samha da khadija hankali a tashe tare da sauran daluban department dinsu suka dinga ihun kiran sunan amjad daya samu ya kwace ball din daga hanunsu sabah. Haka sukayita bashi karfin guiwa. Ba jima ba coach ya hura whistle alamun za’ayi first half kowa yaje ya huta kafun a zo a cigaba. Haka aka tsayar da wasan, suka bar fillin wasan. Amjad ya koma gefe ya bude bottle water daya ya fara sha, zufa nata karyo mishi ta ko ina a jikinsa, shima sabah komawa gefe yayi ya bude ruwa ya soma sha shima sai faman zufa yakeyi. Kwantaciyar sumar dake bisa kansa duk ta hargitse. Amjad ne ya dube shi yace ” ya naga kai da team dinka kun dage sai faman buga basketball dinan kukeyi sai kace ba friendly match ba. Kuma ai nazata baka iya bugawa sosai ba, kamar yanda kamun bayani”.
sabah ne ya juyo yana dubansa kyakwar fuskarsa dauke da murmushi sa’anan yace “ka ganni nan, idan nasa abu a raina nayi niyan yi toh sai na tabbatar nazo na daya a cikinta, babu abunda zan bari yasha gabana. Batun ko na iya buga basketball ko ban iya ba, na jima ban buga bane shiyasa nace maka ban iya ba don a tunanina na manta da yanda ake bugawa amma sai kuma naga akasin haka, yanda kake mamaki nima haka nake mamakin kaina.”
Murmushi amjad ya sake don ya fuskanci inda maganar tasa ta dosa sa’anan yace “Da kyau kam, yanada kyau duk abunda zakayi a rayuwa ka tabbatar kayisa da kyau don ka kece raini”.
Suna cikin maganarsu coach ya kara hura whistle alamun za’a cigaba da buga wasan. Haka suka koma fillin wasan, wanan karan kam amjad ya dage shida team dinsa har suka kusan kamo su sabah. Samha sai murna takeyi tanata daga mishi hannu daga sama. Sunyita bugawa na kusan mintin 30, samha ta dubi agogon hanunta taga lokaci ya kure saura minti biyu a gama wasan gabadaya gashi su amjad saura musu score daya su kamo su sabah. Mikewa tayi daga inda take zaune zuciyarta nata faman bugu cikin kirjinta. Addu’a takeyi Allah yasa na karshen nan da zasu buga amjad yaci nasara kwallon ta shiga cikin raga. Ai kam amjad na daga ball din ya wurga ta sama saitin inda ragar take, ko ina yayi shiru aka mike kowa idansa na kan ball din ana so aga inda zata sauka. Hatta sabah ya bude baki yana kallon ball din har tazo ta sauka kan ragar amma ba’aci sa’a ba tabi ta saman ragar ta fadi a kasa. Yan department dinsu sabah suka sa ihu sunata murnan sun ci. Amjad fuskarsa ta fadi gabadaya yaji wani iri babu dadi, amma still sai yaji abun bai wani dameshi ba. Samha kam kamar zatayi kuka, duk hankalinta a tashe data ga su sabah sun cinye su amjad.
Amjad yazo sukayi hannu da sabah fuskarsa dauke da murmushi yace mishi “Barka wanan karon na yarda kun cinye mu da kai da team dinka kunyi kokari, amma baka tunanin zaka iya hadewa da team dinmu mu dinga bugawa makaranta? Kai da abokananka zaku iya joining dinmu, tunda nine captain na team dinan zan iya saka ka zama team leader, koh ya ka gani?” Amjad ya tambayeshi.
Murmushi sabah yayi yace “naji zamu iya joining team naku amma da sharadi daya”.
“Me kenan?” amjad ya tambayeshi.
“Inaso so wacen ta zama team manager dinmu” ya fada yana nuna inda samha take tsaye tare da kawayenta. Yanda sabah yayi maganar yasa kowa ya juyo yana kallon inda samha take. Itama cike da mamaki ta nuna kanta, don batayi tunanin da ita yake ba.
“Wa? Samha kake nufi?” Amjad ya tambayeshi.
“Eh ita” ya bashi ansa.
Shiru amjad yayi yana nazari sa’anan yace “Toh babu matsala, daman muna bukatar sabuwar manager, wace take tare damu last session tace bazata iya ba kuma, kuma tun daga lokacin bamu samu wace zata mayar da gurbinta ba.so babu matsala zata iya zama manager din. Baby me kikace toh, aikin na dan daukar time din mutum so idan bazaki iya ba, babu wanda zai tilasta miki ki zama manager din, kinji”.
Samha bata san sanda tace mishi “karka ka damu, zan iya. Wanan ba matsala bane”.
Sabah ne ya dube ta yana murmushi fuskarsa cike da makirci sa’anan yace ” zaki iya? Toh ai shikenan, daman haka akeso.”
Dafa kafadar Amjad yayi yana fadin “Kaga Bakada matsala, daga yanzu ka samu team leader da team manager kaga komai ya zauna kenan” yana gama fadin haka ya kama hanyarsa yayi gaba ya barsu a wajen.
Murmushin muguntar da samha tagani a fuskar sabah yasa ta gano cewa daman da biyu yace a mayar da ita team manager. Nan da nan hankalinta ya tashi. Amma toh ya zatayi tunda ta rigada ta amince zata zama musu manager din? Cike da takaici da bi bayan sabah da kallo har ya bace mata daga gani.
Bangaren su sabah kuwa bayan sun koma inda suka saba shakatawa suna zaune suna hira. Zack ne ya dubi sabah yace ” yanzu wai SB da gaske kake zamuyi joining din basketball team dinsu amjad?”
” kwarai kuwa da gaske nake, ka taba ganin na amince da abunda banyi niya ba” sabah ya watsa mai tambayar.
“Toh meyasa kake so kayi joining?” Abba ya tambayeshi.
” yanzu zaka ce mun baka ji dadin bugawan da mukayi bane dazu” Sabah ya mayar mai da nasa tambayar.
“Naji dadin bugawa mana” ya bashi ansa.
“Toh kaji dadin bugawa meye kuma zaka sani a gaba da waenan tambayoyin. Idan baka so kayi joining ba dole bane karkayi joining mana”. Sabah ya bashi ansa hade da hararar sa.
Abba yayi shiru bai sake cewa komai ba. Suma su shinoh shiru sukayi suna turo baki, kowa yaja jinin jikinsa, basu sake dauko maganar ba don sun san halin sabah sarai haka suka cigaba da hirarsu.
Tun daga lokacin su sabah sukayi joining din team dinsu amjad, idan sun gama lectures kafun su tafi gida haka zasu hadu a gym suna practice. Yauma kamar sauran ranaku amjad da yan team dinsa sunje gym suna practice, su sabah suna hanya basu karaso ba. Samha as team manager dinsu tana zaune a gefe ita kadai tana kallon wasan da sukeyi. Kurawa amjad ido tayi ta kasa dauke idanunta daga kansa. Duk inda yayi idanunta na biye dashi, yanda yake buga ball din cike da kwaranta yasata cikin raga ba karamin birgeta yakeyi ba. Wani irin sonshi takeji yana fusgar zuciyarta a koda yaushe idan ta daura idanunta a kansa. Murmushi ta dinga yi ita kadai kamar wata wawiya. Tunani kala kala ne ke mata yawo a ka game dashi. Tana cikin duniyar tunaninta kamar daga sama taji an zungure mata kai. Juyawan da zatayi taci karo da sabah da su shinoh suna tsaye kusa dashi.
Dafe kanta tayi ranta a bace ta galla masa harara ” Me na maka kuma ina zaman zamana zaka zo ta talle mun kai?” Ta tambayeshi.
Girgiza kansa yayi sa’anan yace ” Aikin manager kenan kinzo kin wani zauna anan kina shashanci? Murmushin meye kikeyi ke kadai kamar wata tababiya?”
“Ina ruwanka? Kaga mallam ka wuce kayi tafiyarka ka kyaleni ka fita daga harkata”
Tsaki sabah yaja suka wuceta su ka barta a wajen. Ita kuwa ta bi bayanshi da harara tana fadin mugu kawai azalumi.Su sabah suka hadu da amjad suka fara practice dinsu. Bayan sun buga na kusan hour daya. Sabah ya nema wuri ya zauna, cike da dagin murya ya kira sunan manager. Badan taso ba haka samha tazo ta sameshi inda yake zaune, turo dan karamin bakinta tayi tana galla masa harara. “Meye kuma naji ka kirani?” Ta tambayeshi.+
“Manager aikin ki shine ki dinga kula da lamarin masu buga kwallo, duk wani bukatarsu yana rataye a kanki kuma dole ki tabbatar da sun samu. Don haka kije ki kawo mun ruwa nasha, kishi nakeji” ya fada mata.
Wani irin kallo da bishi dashi sa’anan tace ” ban gane in kawo maka ruwa kasha ba, meya samu kafafunka” Ta tambayeshi.
Ji tayi ya daga murya yana fadin “captain, wanan manager din fa bata san aikinta ba. Ya kamata mu canza ta!”
Samha najin ya ambato sunan amjad, ta zaro ido. Babu shiri ta bar wurin taje nemo masa ruwan da zai sha don bata san amjad yaga gazawarta wurin aikinta na manager.
Cikin yan mintuna kadan sai gata da bottle water ta kawo mishi. Karfa yayi daga hanunta ya bude ya fara sha. Zata juya ta tafi kenan taji ya sake fadin ” ki kawo mun towel da kuma juice”.
Cike da takaici ta sake juyawa taje ta nemo masa juice da towel ta kawo masa. Karfan towel din yayi daga hanunta sa’anan yace ta bude masa juice din. Babu yanda ta iya haka ta sa hanu ta girgiza kwalin juice din sa’anan ta bude masa ya karfa ya fara sha.
Kafun ta tafi ya dakatar da ita yace mata saura abu daya. Zuciyarta ne ya soma tafarfasa don taga rainin hankalin nasa ya soma wuce tunani, kuma gani takeyi don ya sameta ne shiyasa yake mata duk abunda yaga dama.
Cike da takaici ta juyo tana dubansa. ” me kuma zan maka” ta tambayeshi.
Gira daya ya daga mata yana dubanta. kyakyawar fuskarsa dauke da murmushin makirci wanda yasa har dimple dinsa guda biyu dake gefen fuskarsa suka bayana, bude baki yayi yace ” Abu daya ne ya rage miki kanwata, tausah nake so ki mun, gaba daya jikina ya mutu daga wasan nan da muka gama bugawa”.
” wa zai maka tausah? Ni din ce zan maka tausah?”ta fada tana nuna kanta.
Gyada mata kai yayi, ya cigaba da kallonta.
“Amma sabah rainin hankalinka yayi yawa wlh amma ba laifinka bane. Laifi nane dana baka chance kake mun duk abunda kaga dama.” Tana gama fadin haka ta ja tsaki ta tafi ta barshi a wajen.
Shikam dariya ya sake yana girgiza kai, kishingida yayi akan kujera dayake zaune akai ya lumshe idanunsa kamar mai bacci.
Samha ta samu wuri ta zauna tayi tagumi, haushi da takaicin sabah duk ya adabe ta. Tana cikin tunaninta su khadie suka karaso suka zo suka sameta.
Amina ce ta tambayeta ” samha ya na ganki haka duk a hargitse? Ina amjad din kun samu kun kebe kuwa yau dinan?”
“Ina fah, kina tunanin hakan zai yu ne idan wancan iblees din yana nan?”
Amina ta girgiza kai sa’anan tace ” samha ya kamata ki dage da aikin ki a matsayin manager na wanan team din fa”
“Ban gane ba, me kike nufi?” Samha ta tambayeta.
“Na samu labari sabah tun yana secondary school yake buga basketball ball, kuma ya kware sosai, a lokacin dai bansan meye ya hadashi da coach dinsu ba, sabah ya mishi dukan tsiya, shiyasa ma aka koreshi daga team din, har suspending dinshi daga makaranta akayi a wanan lokacin.” Amina ta sanar da ita.
” wato har dukan coach din secondary school dinsu yayi? Kunga halin nasa ba?” Samha ta fada tana girgiza kai.
“Toh ai dayake family dinsa suna da kudi sosai, shiyasa ma ba koreshi daga makarantar ba, suspending dinsa kawai akayi aka share maganar.”
“Akwai gyara a maganarki, ba haka abun ya faru ba” suka ji magana kamar daga sama. Juyawa sukayi sukaga zakari wato zack abokin sabah a bayansu. Wuri ya samu ya zauna a gefe ya kishingida sa’anan ya cigaba da fadin.
” sabah ba haka yake ba. Bari na baku wata labari, Lokacin da muke secondary school, a team dinmu na basketball akwai wani yaro a cikin mu. Dan lukuti ne don yana da jiki sosai, baya iya gudu ko kuma ya daga jikinsa kamar sauran masu buga kwallon. Haka ya dinga jawowa team din matsala. Har tsawon shekara biyu yana team dinan hanunsa bai taba kama kwallo ba idan anzo bugawa. Wata rana abun yaba coach dinmu haushi ya hayako wa yaron yana fadin ” ka cika shirme, kullum sai dawo mun da aiki baya kake, daga yanzu kawai ka zauna a gefen kana kallon yanda sauran mates dinka suke bugawa, na gaji da sluggishness dinka” yaron kam sai kuka yake faman yi yana bawa coach din hakuri amma coach yaki sauraronsa sai zaginsa yakeyi. Abun ya bawa sabah haushi yanda yaga coach din na zagin yaron yanata bada shi a gaban kowa. Kawai ganin sabah mukayi yaje yaci kwallar coach din ya kai mishi naushi a hanci ya fadi a kasa. Ya hau kan coach din ya cigaba da zazaga mai duka ta ko ina. Da kyar dai muka samu muka raba sabah da coach din. Saboda hakan daya faru, aka kore sabah daga team din gabadaya. Nasan maganar da coach yayi wa yaron babu ruwan sabah a ciki amma yanda sabah yayi reacting yana dukan coach din kya ce shine coach din ya zaga.”
Dagowa zack yayi yana duban su samha sa’an yace ” wanan dan lukutin da sabah yayi fada da coach akai ba kowa bane ila ni dinan da kuke gani a gabanku” ya karasa maganar yana murmushi.
Cike da mamaki samha da su khadija suka bishi da kallo. Zack ya zira hanunsa cikin aljihu ya ciro wani hoto ya mikawa samha ta karba, su Khadija suka matso kusa da ita suna kallon hoton da zack ya mika mata. Zack ne da Sabah a cikin hoton amma da alamun lokacin zack yanada jiki sosai don da kyar su samha suka iya ganeshi.
” bari in sanar daku wani abu, yawanci mutane suna tunanin muna tare da sabah don mahaifinshi nada kudi ko kuma don muna jin tsoronsa ne. Amma ko daya, mutuncin shi kawai muke gani, don sabah yana kare mana mutuncin sosai fiye da yanda kuke tunani shiyasa kuka ga muke biye dashi kuma muke bashi nashi respect din. Barshi dai da zafin ransa da komai, amma wlh sabah mutum ne kuma yanada kirki sosai”.
Tunda zack ya fara maganar gabadaya jikin samha yayi sanyi, maganganunsa nata mata yawo a kai.
Murmushi zack yayi ya tafi ya barsu a wajen cike da jimami.
Yau ma kamar ko wace rana bayan an gama lectures su sabah da amjad suna gym suna practice. Bayan sun gama practice sabah ya kwala wa samha kira yace tazo. Tana zuwa ya bata wani uban list yace taje ta siyo mishi abubuwan dake rubuce a ciki. Haka ta fuzge takardan da kudin daga hanunsa ta tafi taje ta jido mishi kayakin daya bukata. Hanunta a cike da ledoji da kyar ta rukosu. Sai faman haki takeyi tana zagin sabah cikin ranta. Don koh za kwana zack yana yabon halayen sabah a wurinta, bazata daina mishi kallon mugu ba don dubi irin aikin daya sata yanzu take mishi, kamar mara imani.
Samha tazo zata haura step da zai kaita gym kenan taci karo da mutum. firgita tayi kayakin data debo a hanunta suka zube. Dagowa tayi taga Aliyah tsaye a gabanta ta rungume hanunta biyu bisa kirjinta. Idanunta kyam akan samha tana kallonta cike da tsana. Wasu yan mata guda uku ne suke biye da ita suna tsaye a bayanta.
“You again? Wai me kuma kikeso yanzu?” Samha ta tambayeta ranta a bace.
Girgiza kanta Aliyah tayi fuskar babu walwala sa’anan tace “Naga har yanzu kina nan rabe da prince bayan duk kashedin dana miki a baya.”
“Prince? Waye kuma prince?” Samha ta tambayeta.
” Banza, sabah nake nufi. Wai tsaya ma tukuna bana dawo miki da letter dinki ba? Meye kuma naga kina rabuwa da prince har yanzu?” Aliya ta tambayeta.
“Letter kuma?” Samha ta tambayeta.
“Kwarai kuwa, letter da kika rubutawa captain din basketball team na department dinku. Ya ma sunanshi mujaheed ne ko meye?” Aliya ta tambayeta.
” Ai na tayaki posting din letter a notice board. Nazata hakan zai taimaka ki rabu da prince amma kuma sai naga ba haka ba”
Zaro ido samha tayi Kuma nan danan abubuwan da suka faru a ranar da taga anyi posting din letter dinta, Da dariyan da course-mates dinta suka dinga mata har da marin sabah dataje tayi duk suka dinga dawo mata.
Bugun zuciyar ta ne taji ya karu. Wato daman ba Sabah bane ya aikata kuma babu hanunsa a ciki? Duk sharin Aliyah ne? Ta tambayi kanta.
Dagowa tayi tana kallon Aliyah zuciyarta na tafarfasa sa’anan tace ” Amma fa ke muguwa ce, kuma bakida mutunci, me na miki a rayuwar nan da zaki mun haka?”
“Muguwa? Ni ce banida mutunci?” Aliya ta tambayeta. Dariya ta sake tana girgiza kai sa’anan ta sake matsowa inda samha take tsaye.
“Nasan nida ke ba wani sanin juna mukayi ba. Amma bari na dan baki tarihina . Kin gani nan? Kadan kenan daga cikin abubuwan da zan iya aikatawa indai akan prince ne. Don zan baki mamaki a makarantar nan fiye da yanda kike zato, in har bakiyi yanda na umarce ki ba. Aliyah ta karasa maganar tana murmushin mugunta. Kallon yan matan da suka rakota tayi sa’anan ta basu order da ” ku kama mun ita, yau zan fara koya mata hankali”.
Yan matan suka karaso inda samha take suka kamota., zata sa ihu suka toshe mata baki, daya daga cikinsu ta ciro igiya daga cikin jakarta suka sa suka daure mata hannu dashi.
Lighter Aliya ta ciro daga cikin aljihunta ta kunna tana murmushin mugunta tazo ta tsaya dab da samha ta cire mata dankwalin dake kanta. Dogon gashinta ya bayana. Kamo jelar gashinta aliyah tayi tana wasa dashi sa’anan tace ” yanzu idan nasawa gashin nan naki wuta me kike tunanin zai faru? Ta tamabayeta.