ZABIN SAMHA CHAPTER 3
Samha ta zaro ido tana girgiza mata kanta alamun karta mata haka. Kwalla ya ciko mata idanunta. Murmushin mugunta Aliyah ta cigaba dayi. Ta kamo karshen gashin samha zata hada da lighter din kenan kamar daga sama sukaji an watso musu ruwa.
A firgice suka juyo sukaga wani mutum rike da bokiti da mop a hanunsa. Da alamun daya daga cikin masu sharan makaranta ne.+
“Meye kuke haka?” Ya tambayesu yana kallonsu daya bayan daya.
Shiru sukayi basu ce komai. Aliyah sai faman galla masa harara takeyi. Kare musu kallo yayi sa’anan yace .
“Badai cin zali kukeyi ba. Me ta muku da zaku kamata ku daure haka?” Ya tambayesu.
Ya juyo ya dubi Aliyah sa’anan yace ” keh kuma kyakyawar yarinya kamar ki amma zuciyar ki babu kyau? Konata zakiyi?”
Daya daga cikin yan matan ne tace ” kai tsoho ina ruwanka. Bamu san surutu, ka wuce ka bamu wuri kaje ka cigaba da aikin sharanka. Ta fada mishi cike da fitsara.
“Ni kike ce ma tsoho, toh bari inje in kira daya daga cikin malaman naku suzo su ga abunda kuke aikatawa.
Aliyah ce ta juyo tana kallon samha sa’an ta fada cikin kakausar murya “kin ci sa’a yau dinan da kinga abunda zan miki. Amma next time zamu sake haduwa. Kuma haduwar tamu bazatayi kyau ba.” Tana gama fadin haka tayiwa yanmatan alamu dasu bar wajen. Haka suka tafi suka kyale samha wace hawaye ne ke ta gangaro mata bisa kunci.
Nan da nan mutumin yazo ya kwance igiyar dasu aliyah suka daure ta dashi daga hanunta. Hakuri ya soma bata yana rarashinta. Kallon mutumin samha keyi gani takeyi kamar tasan fuskar a wani wuri. Godiya ta mishi ta share hawayenta. Suna cikin haka samha ta jiyo takun mutum aka zo aka tsaya a kansu. Dagowa tayi taga sabah fuskarsa a daure.
“Abba ya haka?” Samha taji ya tambaye mutumin. Cike da mamaki samha ta kalli sabah sa’anan ta sake dawo da dubanta ga mutumin.
“Haba baby boy dina, dan na danyi tafiya na kwana biyu kuma koh oyoyo baza ayi wa daddy ba” ya tambayeshi.
Sabah ya bata rai ya kawar da kansa gefe. Samha kam kallon kallo ta fara binsu dashi. Kardai wanan mutumin shine mahaifin sabah. Wanan tunanin na fado mata, da sauri ta juyo ta kura wa mutumin ido. Nan da nan kuma taga kamanin dake tsakaninsu. Shiyasa jikinta yayita bata kamar ta sanshi a wani wajen. Ashe kamanine kawai. Mutumin kyakywa don daga ganinshi kasan yayi tashen kyau lokacin yana yaro. Komai nasu iri daya da sabah, haske ne kawai sabah ya fishi. Amma kana ganinsu tare, kasan mahaifinshi ne.
“kaine mahaifin sabah?” Samha ta tambayeshi. Gyada mata kai yayi fuskarsa dauke da murmushi.
Sabah ne ya dubeshi sa’anan yace ” Abbah dan Allah wani irin shiga ne kayi yau. Yanzu wani ya ganka basai yazata kai cleaner din makarantar nan ne ba. Duba fa harda bokiti da mop ka ruko”. Sabah ya tambayeshi cike da takaicin yanayi mahaifin nasa. Ya rasa gane meyasa yake abubuwa haka.
“Haba baby boy, meye acikin shigar danayi yau. Na jima banyi cleaning bane shiyasa nace bari na gwada yau.”
” a cikin makaranta kuma abba zaka gwada?” Sabah ya tambayeshi.
Gyada mishi kai mutumin yayi yana murmushi. Duk wanan da sukeyi samha kallonsu kawai take ta faman yi cike da mamaki, musamman mahaifin sabah din. Anya mutumin nan nada lafiya kuwa, ta tambayi kanta. Yanzu wanan ne amminta zata aura? Jibi yanda yakeyi kamar wani yaro karami.ta tambayi kanta.
Tana cikin wanan tunanin taga wani mutumi sanye cikin suit ya karaso inda suke tsaye.
Cike da girmamawa ya dubi mahaifin sabah sa’anan yace ” sir, tun dazu muke ta nemanka bamu ganka ba, har wayarka mun kira bata shiga, akwai meeting da za ayi yau a senate, don tun hazu har an taru kai kawai ake jira” mutumin ya sanar dashi.
“Au kaga fa na manta da wani meeting da za ayi yau. Toh bari na shirya muje. Ka kira jubril a waya kace yaje mota ya ciro mun daya daga cikin sababin suit dinan ya kai mun office gani nan zuwa”. Ya sanar da mutumin.
“Okay sir”, anyi an gama ya fada kansa a sunkuye. Mahaifin saba yajuyo yana fuskantarsu sabah sa’anan yace shi zai wuce. Yace wa samha ta gaishe mishi da mahaifiyarta. Tace toh zataji.
Haka ya tafi ya barsu a wajen yana tafe mutumin na binshi a baya.
Kallon takaici sabah yabi bayan mahaifin shi dashi sa’anan yayi ajiyar zuciya. Juyowa yayi ya mayar da dubansa ga samha wace ta kura mishi ido. Murmushi ta sakar masa da suka hada ido.
Harara ya galla mata sa’anan yace ” meye haka kuma, murmushin me kikeyi?” Ya tambayeta.
“Bakomai ta fada mishi” still tana kallonsa tana murmushin.
Nan kuma ta fara tuno da abubuwan da suka faru a baya, da marin data mishi akan letter din. Da kuma bakaken maganganun data dinga fada mishi. Har tana fada mishi bazai taba samun farin ciki a rayuwarsa ba. Nan take taji babu dadi, ta sunkuyar da kanta cike da jin kunyarsa. Ta soma nadamar abunda ta aikata don ita duk a tunaninta sabah ne yayi posting letter dinta, ashe duk aliyah ce ta hada mata wanan gurmin.
Dagowa tayi da kanta tana kallonsa sa’anan tace ” Sabah kayi hakuri dan Allah, I’m really sorry nasan na aikata baban kuskure gareka.” Ta fada mishi.
“Kuskuren meye kuma?” Ya tambayeta.
“A da nayi tunanin kaine kayi posting letter na, sai kuma na gano cewa ba haka bane. Kayi hakuri da bakaken maganganun dana fada maka a baya. I’m very sorry. Nasan ban cancanci yafiya daga gareka ba. Yanzu koma meye kace zaka mun bazan ga laifin ka ba Sabah, Ko rama marin dana maka kace zakayi bazan hanaka ba. Ta fada tana dubansa kwayan idanunta cike da nadama.
Sabah shiru yayi yana kallonta bai ce komai ba ya mata alamun data biyo shi.
Bangaren amjad kuwa bayan sun gama practice yaje inda ya ajiye jakarsa. Ya ciro bottle water dinsa ya bude ya fara shanruwan ciki, idanunsa ne suka sauka kan tickets din da ya siya guda biyu, daya nashi daya kuma na samha. Daman yasa rai weekend dinan zai kaita cinema suje su dan shakata, ciro tickets din yayi daga cikin jacket dinshi. Zack ya hango ya fara tambayarsa ” wai nikam ina samha taje ne tun dazu ban ganta ba. Kuma ga wayarta anan tana charging bata tafi da ita ba.”
“Ai tun dazu ta tafi siyowa yan team lemun da za’a sha har yanzu bata dawo ba.” Zack ya sanar da shi.
” toh barin in bi bayanta nasan kayan nan zasu mata nauyi bazata iya rukosu ita kadai ba” yana gama fadin haka ya kama hanya cikin sauri yayi hanyar waje.
Zack ne ya soma fadin ” sabah fa yabi bayanta tun dazu, inajin suna tare yanzu” amma ina amjad har ya fice bai ji abunda yace ba.
Bangaren su samha kuwa tafiya sukeyi ita da sabah yana zolayenta.
“Kince zan iya rama marin da kika mun, idan na daga hanu na mare ki fuskarki fa zatayi damage, zaki iya cira hakora ma” ya fada mata cikin wasa.
Ita kam ta dage tace bata damu ba zai iya ramawa, tanan ne kadai itama zata iya yafewa kanta abunda ya faru.
Tsayawa sabah yayi ya juyo yana kallonta, ya kurawa kyakyawar fuskarta ido. Fararen idanunsa masu matukar kyau da daukan ido ya dora su kyam a kanta. Itama tsayawa tayi ta juyo tana kallonsa.
“Toh naji zan rama marina” ya fada mata.
Zaro ido tayi hankalinta a tashe don batayi tunanin zai ce zai rama ba.
Muryarta na dan rawa tace ” shikenan na amince zaka iya ramawa”.
“Rufe idanunki” ya fada mata. Babu musu ta rufe idanunta.
“Kin shirya?” ya tambayeta. Gyada masa kanta tayi.
Sabah ya dago hanunsa kamar zai kai mata mari sai kuma taji ya janyo ta jikinsa ta fado bisa fafaden kirjinsa. Rungumeta yayi gam a jikinsa, Yana ajiyar numfashi.
Amjad ya sauko kasa kenan ya ci karo da Sabah rungume da samha a jikinsa. Wani irin mahaukacin bugu zuciyarsa tayi, nan take ya soma ganin dishi dishi. Samha dinsa ne rungume a jikin wani a gabansa? Me zai gani yau?”
Samha ce ta ture sabah daga jikinta “meye haka?! ta tambayeshi a tsawace.
Sabah ya sake matsowa kusa da ita ya sunkuyar da kansa sa’anan ya rada mata cikin kunne ” Ai na sha fada miki, duk abunda na sa agaba ina so nayi toh babu wani mahalukin daya isa ya hanani” ya fada muryasa kasa kasa.
” ban gane nufin ka ba, akan me zaka matse ni a jikinka haka?”
“Saboda ke tawa ce” ya fada yana kallon cikin kwayar idanunta.
Wani irin kara samha ta sake tana toshe kunnenta.
Kamar daga sama sukaji ana fadin ” meye zan gani haka? ina kai da ita yayah da kanwa ne”.
Juyowa sukayi sukaga amjad tsaye yana kallonsu cike da tashin hankali, zuciyarsa na masa wani irin zafi.
Sabah na ganinshi ko shakka babu ya sake janyo samha jikinsa sa’anan yace ” eh kanwata ce amma nan gaba nida ita dangerous siblings zamu zama” ya fada mishi yana murmushi.
Sake tureshi samha tayi tana fadi hankalinta a matukar tashe ” ka kyaleni! wani irin banzar magana kake gaya mishi haka sabah”
Ta mayar da dubanta ga amjad tana girgiza masa kai “wallahi amjad karya sabah yakeyi karka yarda da abunda yake fada maka. wlh babu komai tsakanin mu”.
” duk abunda na fada maka gaskiya ne babu karya cikinta” sabah ya fada mishi.
Samha ta galla masa harara idanunta cike da hawaye, ta karaso inda amjad yake tsaye tana girgiza masa kai tana bashi hakuri da karya saurari abunda sabah yake fadi. Shi kam sabah sai faman kara wuta yakeyi.
Murmushi karfin hali amjad yayi sa’anan yace ” babu komai, soyayya ai ra’ayi ce kuma zaka iya yinta da duk wanda kaga dama don haka kusha soyayyarku lafiya” yana gama fadin haka ya kama hanyarsa ya tafi.
Samha ta durkushe guiwowinta biyu akasa tana rapsa kuka tana kiran sunan amjad da yayi hakuri ya saurareta.
Samha tana zaune a kasa sai faman rapsa kuka takeyi. Sabah ne ya karaso inda take durkushe ya tsaya yana dubanta sa’anan yace ” yanzu kukan meye kike haka sai kace an miki mutuwa?”+
Samha ta dago tana dubansa duk fuskarta ta bace da hawaye, bude bakinta tayi tana fadin ” meyasa zaka mun haka Sabah? Meyasa ka fadawa amjad haka. Kasa yanzu yayi wa kalamanka wata fasara ta daban.”
” wa? Wai dan na fada mishi nidake zamu zama dangerous siblings? Ai gaskiya na fada mishi. Gwanda ya sani tun wuri”.
Mikewa samha tayi daga inda take zaune, hade da ta watsa mishi wani irin kallo sa’anan ta kama hanya ta tafi ta barshi tsaye zuciyarta na mata wani irin kuna. Gabadaya samha ji tayi abun duniya ya ishe ta a ranan. Tun a school take ta faman kiran layin Amjad yaki dagawa, Kiran duniya tayi mishi amma kememe yaki daga wayarta. Daga baya ma kashe wayan yayi gabadaya. Duk tabi ta sukurkuce ta rasa meke mata dadi.Ko data isa gida a ranar ma kin fitowa tayi taci abinci tace ma Anty fanneh bata jin yunwa.
A daren ranar dai ko runtsawa batayi ba. Washe gari ma data je school tasa ido ko zata ganshi amma ko alamunsa bata gani har aka gama lectures bata ji duriyansa ba. Suna gama lectures ta fara duba sauran lecture halls din department dinsu ko zata ganshi still babu alamun sa. A ranar dai babu inda bata je nemansa ba, har library inda ya saba zuwa karatu ta duba bata ganshi ba. Ko data hadu dasu khadie suma suka lura da yanayinta kamar babu lafiya suka sata a gaba suna tambayarta abunda ke damunta. Nan ta zayane musu duk abunda ya faru a jiyan. Shiru sukayi suna mamakin karfin hali irin na Sabah.
Bayan kwana uku da faruwan abun, samha tana zaune cikin aji, ko walwala babu a fuskarta, duk tabi tayi wani iri, kana ganinta kasan tana cikin damuwa. Khadija da amina suna zaune a gefenta suna kokarin janta da hira, suna cikin maganarsu sai ga Amjad ya shigo cikin ajin, sanye yake cikin yellow sweater da black jeans. Yau kwana nawa kenan samha bata daura idanunta a kansa ba, sai taga har wata yar rama yayi cikin yan kwanakin. Suna zaune suna kallonsa har ya karaso cikin ajin, Koh kallon inda samha take baiyi ba ya nema wuri a gaba ya zauna. Ciro littafi yayi daga cikin jakarsa ya fara rubutu, amma gabadaya tunaninsa a hargitse yake. Babu abunda ke masa yawo aka inbanda kallaman Sabah daya ce mishi shida samha zasu zama dangerous siblings. Wanan kalamun ba karamun tadda mishi da hankali yake ba idan ya tuno su.
Wani irin zafin kishi ne ya tunduke shi daya tuno da yanayin daya riskesu a ranar. Biro din daya rike a hanu yana rubutu dashi bai San sanda ya danata da karfi ba ta karye a hanunsa. Bayan an gama lectures, samha tanaso taje ta tunkareshi amma tana tsoron abunda zai biyo baya idan tayi hakan don tasan amjad ba karamin fishi da ita yayi ba. Haka suka shafi kusan sati basu magana da juna. Samha sai dai ta tura mishi da text tana rokon shi daya yi hakuri ya yafe mata, amjad yana gama karanta text din sai ya goge daga cikin wayarsa koh replying dinta baya yi.
Yau ta kasance ranar litinin da safe, bayan an gama lectures, su samha suna saukowa daga steps, amina ta dubi samha tace “wai samha kin daina zuwa gym ne?”
” me zanje in musu a gym kuma bayan amjad ko ganina bai son yi” ta tambayeta.
” kin manta har yanzu ke team manager dinsu ce?”.
” team manager koh baiwar sabah? Ai ya mayar dani Yar aikensa na musaman a gym dinan”
” yanzu ba wanan ba” khadie ta katse su.
” kamata yayi samha kisan yanda zaki shawo kan amjad ki bashi hakuri. Haba yau kwana nawa kenan? nasan idan kika sameshi kika mishi bayani zai fahimce ki.”
Ajiyar zuciya samha tayi sa’anan tace ” nasan yanzu amjad zai yita min kallon wace batada kamun kai. Da farko na rubuta mishi love letter yanzu kuma ya gani rungume a jikin wani.
“Ai dole yayi miki kallon wace batada kamun kai” khadie ta bata ansa.
Duban ta samha da amina sukayi cike da mamakin maganarta.
” haba khadie, ya zaki fadawa samha haka? Da wane kikeso taji?” Amina ta tambayeta.
“Ai in har bata je ta bawa amjad hakuri ta wanke kanta ba, toh ta cancanci koma waye ya mata kallon mara kamun kai” khadie ta fada tana kawar da kanta gefe.
Nan take samha ta sunkuyar da kanta tana tuno kalaman amjad na karshe gareta. Inda yake fada mata “soyayya ra’ayi ce, zaka iya yinta da duk wanda kaga dama” Jikinta ne ya kara sanyi don bata San taya zata fara tunkararsa ba.
“Share shi kawai bazan iya tunkararsa ba” samha ta fada musu.
“Kin tabbata? Amjad ne fa?” khadie ta tambayeta.
Gyada mata kai samha tayi jikinta a sanyaye.
” toh bazaki ji haushi ba Idan naje na tunkari amjad na fada mishi ina sonshi?” Khadie ta tambayeta.
Zaro ido amina da samha sukayi suna kallonta.
” ban gane ba” samha ta fada mata ta bata rai.
” yanzu dai zabi ya rage naki, koh kije ki sameshi ki bashi hakuri ku shirya ko kuma ni inje in fada mishi ina sonshi.”
Tana gama fadin haka ta tabe baki ta tafi ta barsu a wajen. Binta da kallon mamaki sukayi.
” meye kike jira samha? Taho muje mu nemo amjad” amina ta fada tana Jan hanunta.
Bangaren amjad kam ba’a cewa komai don tun daga ranar gabadaya ya rasa samun sukuni don koh a aji ma baya iya fahimtar komai, bashida wani tunani sai na samha da abunda ya faru a ranar. Koh yau da aka gama lectures, gym ya nufa shi kadai. Yana shiga cikin gym din ya tsaya yayi shiru yana nazari tunani kala kala na masa yawo aka, yayi kusan minti ashirin yana tsaye sai faman tunani yakeyi. Kamar daga sama yaji ankira sunansa. Farfadowa yayi daga duniyan tunanisa, ya juyo don yaga mai kiran nasa.
Khadija kawar samha ya gani a tsaye tana kallonsa. Fuskarta cike da damuwa, kallon bayanta yayi yaga samha da amina sun bullo suma suka shigo cikin gym din.
Samha wace gabadaya jikinta a sanyaye yake tama kasa kallonsa ta bude bakinta daga inda take tsaye muryarta na rawa ta soma fadin “Amjad kayi hakuri akan aikin manager din ban…”
“Kina iya barin aikin manager ai ba dole bane, babu wanda ya tilasta miki kiyi” Amjad ya katse ta bai bari ta karasa maganar data yi niyan yi ba ya kama hanya ya soma barin wajen.
Gaban samha ne ya fadi da jin kalamansa, khadija da amina suka kalla junansu cike da damuwa.
Khadija ce tabi bayansa cikin sauri, tana isa dab dashi ta soma fadin ” Haba amjad meyasa kakeyin haka? Samha tazo ta sameka tana kokarin ta baka hakuri amma sai wani shashareta kakeyi kana gaya mata magana? Kaima kasan irin son da samha take maka kuma kasan bazata taba aikata hakan da gangan ba. Duk sharin sabah ne, kaima ka sani”.
Juyowa amjad yayi yana duban Khadija fuskarsa a daure yace “wanan kuma matsalar kuce ba nawa ba. Yanzu kun gama bayanin naku? kuna bata min lokaci don ni banida lokacin irin wanan shirmen”.
Khadija dasu samha suka sake baki suna binshi da kallon mamaki dan basu taba tunanin waenan kalaman zasu fito daga bakin amjad ba. Juyawa yayi ya tafi ya barsu a wajen.
Amina ce ta bude baki tana fadin ” amma dai mafarki nakeyi koh? Amjad da muka sani babu ruwanshi yanada matukar kirki shine yake waenan maganganun?”
Khadija kam bata dadara ba ta sake bin bayanshi cikin sauri. Amjad yazo dab da inda yayi parking motarsa, taje ta sha gabansa. Tsayawa yayi yana kallonta.
“Amma amjad ka bani mamaki, ban taba tunanin haka daga gareka ba” ta fada mishi tana kallon cikin kwayar idanunsa.
kawar da kansa gefe yayi fuskarsa a daure bai ce mata komai ba. Itama shiru tayi tana kallonsa.
Kamar daga sama ya jiyo tana fadin “Amma amjad akwai lokacin da idan na ganka sai inji kana birgeni kuma ba karamin kyau kake mun ba”.
Amjad cikin sauri ya juyo yana kallonta cike da mamakin kalamanta. Kallonta ya cigaba dayi bai ce komai ba still fuskarsa a daure.
Nan da nan Khadija taja jinin jikinta don bata san sanda maganar ta kubuce mata daga bakinta ba. Wayancewa tayi ta soma fadin ” amma banga laifinka ba don ka fada abunda ke ranka dazu”.
Shiru yayi still yana kallonta daga bisani ya bude baki yana fadin ” abunda na fada dazun ai bama shi nayi niyan fadi ba”.
” Eh toh dukda haka amjad, inaso ka bawa kai da samha wata damar ku dawo kamar yanda kuke a da, don ba karamin wahala samha tasha don kawai taga ta samu ta jawo hankalinka gareta ba. Nasan kaima bazaka so samha ta kubuce maka haka nan ba” ta fada mishi.
Shiru yayi yana nazarin maganarta, daga bisani kawai taga ya juya cikin sauri yayi hanyar gym ya tafi ya barta a tsaye a wajen. Khadija ta tsaya ta kurawa bayan amjad ido har ya bace mata daga gani, wani irin feelings ne ke mata yawo a ka game dashi. Danne zuciyarta tayi ta juya ta soma tafiya a hankali ta bar wajen.
Bangaren samha kuwa tana tafiya ita kadai jiki babu kwari, yanayinta babu walwala kwata kwata. Sai faman tunanin kalaman da amjad yayi dazu take ta faman yi ” yanzu amjad ya tsane ni, ji irin kallon ma daya watsa mun dazu” ta fada cikin ranta. Takun mutum ta soma ji cikin sauri ana bin bayanta. Daga bisani Kamar a mafarki ta jiyo muryan amjad yana kiran sunanta.
A hankali ta juyo don ta tabbatar wa kanta abunda kunnenta suka jiyo mata. Amjad ta gani tsaye yana dubanta fuskarsa dauke da damuwa. Kwayar idanunsa cike da kewa da tarin sonta.
Karasowa yayi inda take tsaye yazo ya tsaya a gabanta yana kallon cikin kwayar idanunta. Murmushi ya dan sakar mata sa’anan ya mata nuni da kujerun dake gefen hanyar zuwa gym yace suje su zauna. Babu musu samha tabi bayansa suka je suka zauna.
Shiru sukayi na kusan minti biyar babu wanda yace kalla a tsakinsu daga bisani amjad ne ya bude baki ya fara fadin ” Samha nayi nadamar abunda suka dinga faruwa a tsakanin mu ni dake cikin yan kwanakinan”.+
“Ai ni ya kamata nayi nadama bai kai ba amjad” samha ta bashi ansa tana dubansa.
Murmushi amjad yayi ciki ciki sa’anan ya cigaba da fadin ” A rayuwar nan samha, akwai mutane da zakiga suna so sugan ka cikin damuwa, akwai kuma waenda zakiga su dinne zasu fada cikin damuwa saboda kana cikin damuwa. Ban sani ba koh kin fahimce hausa na ba”. Ya tambayeta yana dubanta.
“Burina samha bai wuce ace na zamanto nine mai kore miki duk wata damuwa dake cikin rayuwarki ba, Amma sai yau aka waye gari nine ma nake saka ki cikin damuwan”. Amjad ya karasa maganar yana sunkuyar da kansa.
Samha ce ta soma girgiza masa kanta tana fadin “Ranar amjad wlh bansan meyasa sabah ya aikata haka ba,wlh…”.
Amjad dagowa yayi bai bari ta karasa maganar ba ya katse ta da ” gobe kina free bayan an gama lectures? Akwai wani funfair da students din physics department zasu yi a Rockview, har na siya mana tickets ni da ke, idan babu matsala ina so ki shirya sai mu tafi tare”.
Cike da mamaki samha ta juyo tana dubansa.
” A ranar danazo na ganku tare ke da sabah, daman tickets din suna hanuna, nayi niyan nazo na fada miki ki shirya zamu fita tare cikin weekend. Amma sai yayan nan naki mara mutunci yazo ya bata komai. A karshe ma yasa nazo nayi wasu maganganun da basu kamata ba gareki, dazun ma haka banji dadin yanayin dana miki magana ba, shiyasa na ce miki samha ina cike da tarin nadamar abubuwan da suke faruwa tsakaninmu. Kiyi hakuri kinji” ya karasa maganar yana dubanta.
Samha ta sake girgiza masa kanta tana fadin ” Meyasa zaka bani hakuri amjad? Ni ce ya kamata na baka hakuri ai tunda ni ce mai laifi.” Ta fada mishi.
Murmushi ya sakar mata bai ce komai ba yana kallonta. Itama kallonshi takeyi ta soma Murmushi. Wani irin sonsa ne taji yana karuwa cikin zuciyarta.
” mu bar maganar kawai, komai ya wuce kinji baby? Ya fada fuskarsa dauke da murmushi .
Wani irin dadi taji ya ratsata data ji ya kirata da sunan baby. Sunan da bata taba zaton zata sake jin ya kirata da shi ba.
“Tashi muje sai na ajiye ki a gida , lokaci ya tafi kuma kinga la’asar ta kusan yi. Haka suka mike suka fara tafiya inda yayi parking motarsa cike da farin ciki. Shima amjad wani irin dadi da farin ciki ne ke ratsa duk ilahirin jikinsa daya ga samha tare dashi suna tafiya cike da walwala babu wani sauran fada a tsakaninsu.
Bangaren sabah kuma yana tare dasu shinoh a babban assembly hall na rockview dake kusa da makarantar su. Shirye shirye aketa faman yi na funfair din da zasuyi cikin weekend din. Zaune yake tare da shamsu wanda shine president na physics department. Tataunawa suke akan yanda abubuwa zasu kasance. Deeni ya dubi sabah yana kara masa godiya akan sa bakin dayayi da mutanen senate din makarantar da suka bari suyi amfani da hall din saboda sai kanada kafa sosai a makarantar za abarka kayi amfani da hall din. Amjad yace mishi babu komai, har su shinoh yayiwa magana yace su dan taya su da wasu shirye shiyen da za ayi a hall din. Deeni ya sake mishi godiya ya mike yaje ya tsaya akan aikin da akeyi cikin hall din.
Deeni na tafiya, sabah ya zauna yayi shiru yana tunani, ba abunda ke mishi yawo a ka in banda fuskar samha da irin kallon data watsa mishi kafun ta tafi ta barshi a wajen ranar. Gabadaya sai yake jin wani iri idan ya tuno da irin kukan data dinga yi a ranar. Tun lokacin har yau bai sake sanya samha a idanunsa ba, don samha duk inda tasan zata bi su hadu da sabah kauce masa takeyi. Shima duk jikinsa yayi sanyi tun faruwar abun.
Yau asabar, ta kasance ranar da samha da amjad zasu fita tare, da wuri ta tashi ta fara shiri, don funfair din zuwa karfe goma na safe za a fara. Binciken kayanta ta dinga tana neman kayan da zata saka taje funfair din dashi, haka ta hargitsa dakin ta rasa samun kayan data ga ya dace ta saka ta fita tare da amjad. Daga karshe dai wasu hadadun english wear ta ciro. Gown ce mai ratsen purple da green flowers. Ta ciro takalmanta da jakanta designer wanda aka masa daurin kyallen material green ajikin hanun jakar ta ajiye su a gefe. Bayi ta fada tayi wanka ta fito ta zauna a gaban mudubi ta fara shiri. Tana gama makeup dinta ta saka kayanta, doguwar sumanta ta taje tayi donut dashi a tsakiyar kanta sa’anan ta dauko dankwalin gown din ta saka. Tana gama shirin tazo ta tsaya a gaban mudubi tana kallon kanta. Ba karamin kyau taga tayi ba. Murmushi ta sakar ta dauko turare tabi duk ilahirin jikinta da shi. Daman sunyi da amjad zata zo ta sameshi a cikin makaranta don ta sanar da mahaifiyarta zata shiga school yau, anty fanneh tace itama zata bi ta hanyar makarantar so zata ajiyeta. Bazata iya musanta mata shiyasa tace wa amjad kawai ba sai ya biyo ta gidansu ba ya fara zuwa school zata hadu dashi a can. Tana gama shirinta ta fito ta sauko kasa zuwa parlour ta tadda anty fanneh harta gama shirinta ita kawai take jira. Anty fanneh na ganinta tace ” wow, baby wanan kwaliyar haka fa, kinyi kyau. Haka nakeso naga kina dressing ki fito tsab abunki”.
Dariya samha tayi tace ” Allah koh ammi? Shiyasa nakeson na dinga kwaliya irin naki ammi, idan kinyi kwaliya har kasa daina kallonki nakeyi, sai in dinga ganin kamar babu wace takai ammi na kyau a duniyan nan”.
Tare suka sa dariya. Anty fanneh tayi gaba samha na binta a baya sukaje inda suke parking motoccin gidan, suka shiga anty fanneh ta tadda motar taja mai gadi ya bude musu gate suka bar gidan.
Bangaren amjad kuwa har ya isa makaranta yana tsaye a wajen gate din makarantar su bai shiga ciki ba, Jingine yake a jikin motarsa yana jiran isowar samha. Yana tsaye ya hango sabah yana takowa shi kadai, suna hada ido amjad ya kawar da kansa gefe, shima sabah share shi yayi ya cigaba da tafiyarsa.
Kafun kace me? Amjad kawai ganin sabah yayi ya kwasa a guje, cike da tashin hankali amjad ya juyo yana binshi da kallo. Gani yayi sai faman gudu yakeyi bai tsaya ko ina ba sai gaban wata yar karamar kwali da aka ajiyeta kan hanya, tsugunawa yayi ya kwance wata yar karamar tantabara da aka daureta da igiya kan kwallin, yana gama kwance ta yayi wurgi da kwallin gefen hanya, kwallin sai fitar da hayaki takeyi cikin minti kadan sai ga kwalin ta kama da wuta tana ta faman ci.
Cikin sauri amjad yazo ya tadda sabah inda yake tsugune.
“Meya samu tantabarar da fatan dai bata ji ciwo ba?” Amjad ya tambayeshi.
Mikewa sabah yayi daga inda yake tsugune yace ” bata ji ciwo ba, ina jin daya daga cikin yaran nan ne da basu jin magana suka sawa kwalin wuta kuma suka daure tantabarar akai don mugunta”
“Amma ya naga hanunka yana jini, kamar fa kaji ciwo” amjad ya sanar dashi.
Sabah ne ya bashi ansa da” Na sani amma wanan ba wata damuwa bace” yana gama fadin haka ya bude tafin hanunsa sai ga tantabarar ta tashi sama tayi tafiyarta. Amjad yabi tsuntsun da kallo har ta bace sa’anan ya dawo da dubansa ga sabah. Kallonsa yake cike da mamaki da jimamin abunda ya faru.
Sabah dayaga kallon yayi yawa ya bata fuska sa’anan yace ” ya kuma na ganka a makaranta yau weekend, me kuma kazo yi ?” Ya tambayi amjad.
Shiru amjad yayi sa’anan ya bashi ansa da ” funfair din da physics department zasuyi a rockview nazo gani”.
Sabah ya dubeshi sama da kasa sa’anan yace ” Ban taba tunanin zaka so kaje funfair mai hayaniya irin na rockview ba, ni danake maka kallon shuru shuru mai kuma zakaje ka nema a wajen?”
Amjad ya dan nesa sa’anan yace ” Nima ban taba tunanin bayan abunda ka aikata ranar bazakayi nadama ba musaman abunda ka aikata game da kanwarka. Sai naga koh ajikinka”.
“Haka ka ce?, to bari kaji in gaya maka, ba kanwa take ba koma wacece ita a wurina, bazanji shakkan sake aikata abunda na aikata ba ranan ba. Kuma duk wanda ta kawo a matsayin zabinta sai na canza mata ra’ayi don bazan taba bari ta kasance tare da wani ba sai ni. Saboda ita dinan da kake gani, tawa ce ni kadai. Sabah ya fada yana kallon cikin kwayar idanun amjad koh shakka babu.
Amjad shiru yayi yana kallonsa daga bisani yayi wani murmushin yaqe yace ” Gaskiya sabah kanada karfin hali kuma kana bani mamaki idan naji waenan kalaman na fitowa daga bakinka. Amma kuma baka sani ba, ko kadan maganganun ka basu tadda mun hankali” amjad ya sanar dashi”.
Dariyar da bata kai ciki ba sabah ya sake ya kawar da kansa gefe yace ” Allah ko?”.
Amjad ya cigaba da fadin ” inajin ko dan saboda ni captain ne wajen buga basketball ball. Don nasan idan ina cikin fillin wasan kwallo ina bugawa babu abunda nake sawa a rai in banda na tabbatar da nazo na daya naci wanan wasan”.
Sabah ne ya katse mishi maganar yana fadin ” ka da ka manta, nima fa na iya buga wanan kwallon”.
Yana gama fadin haka sabah ya bar wurin cikin sauri. Wani karemin yaro yaje ya tare. Yaron yana rike da wani karamin kwali sak irin wanda sabah ya kawar daga kan hanya dazun. Kamo yaron sabah yayi ya fara mishi fada a tsawace “kai wani irin mugunta kakeyi haka? idan na sake ganinka ka daure tantabara mai rai a kan wanan kwalin kana so ka konata zaka ga abun da zan maka. Kana jina koh? Oya bace mun daga nan na gani!. Yana gama fadin haka ya kwace kwalin daga hanun yaron ya tunkuda keyarsa. Yaron ya kwasa a guje yana gudu yana waiwayan inda sabah yake tsaye.
“Au Wato har yanzu juyowa kakeyi kana kallona, sai na biyo ka na kamaka?!” Sabah ya tambayeshi. Yaron kara wuta yayi wa gudunsa bai sake waigowa ba.
Ana cikin haka sai ga samha ta karaso inda suke. Tsayawa tayi a bayan amjad tana kallon yanda sabah yake yiwa karamin yaron tsawa har yana cewa zai bishi ya kamoshi.
Sabah yana juyowa yaga samha tsaye ranta a bace, sai faman watsa masa harara takeyi, ya kawar da kansa gefe yayi kamar bai ganta ba. Ita kam ranta a bace cikin sauri ta karaso inda yake tsaye don ita a tunaninta sabah ya kama karamin yaron yana cin zalinsa ne don bata san me yaron yayi mai ba.
“Akan meye zaka kama karamin yaro kana cin zalinsa haka? Mahaifiyarka bata koya maka tarbiyar cewa ba acin zalin yara haka bane?”
” ai kinfi kowa sani na, tunda har ita mahaifiyar tawa na gagareta ta kasa iyawa dani koh tarbiya ban samu daga gareta ba” sabah ya fada mata ransa a bace.
“Ai ni ban san me zan ce maka ba, ace kana aikata abu mara kyau, kuma ka sani amma koh nadamar aikatawa baka yi. Allah ya kyauta maka da irin wanan hali naka”. ta fada mishi ranta a bace.
Amjad ne ya karaso inda suke “yana kokarin mata bayanin ba abunda take tunani bane ya faru”.
Amma ina samha ko sauraransa batayi ba don har lokacin tana cike da jin haushin sabah. Sabah tsayawa yayi yana kallon su, idanunsa ne suka sauka kan kyallen material da samha tayiwa jakar hanunta kwaliya dashi. Sa hannu yayi yaja kyallen ya kwance daga jikin jakar.
” karka kuskura ka taba ni!” Samha ta fada mishi a tsawace tana ja da baya.
Sabah bai ce komai ba ya fara tafiya, tsayawa yayi dab da inda amjad ke tsaye sa’anan yace “wanan kwaliyar da samha tayi yau ban taba ganin ta da irinta ba kuma tayi kyau sosai. Bazan boye maka ba, a yanzu haka wani irin kishi nakeji don na tabbata saboda kai tayi wanan kwaliyar. Amma wanan kyalan dakaga na cire daga jikin jakarta, na cire tane dan na rage mata marking kwaliyar datayi.”
Juyawa sabah yayi ya karewa samha kallo sama da kasa fuskarsa dauke da murmushi wanda har saida kyawawan dimples dinsa suka bayana sa’anan yace” samha gaskiya kinyi bala’in kyau yau dinan kuma kinyi mugun tafiya da imanina amma kada ki manta cewa keh fa tawa ce” yana gama fadin haka ya girgiza kansa ya kara gaba yana tafiya yana daga musu hanu rike da kyallen daya kwata daga jakarta. Binshi da kallon takaici amjad da samha sukayi har ya bace musu daga gani.
samha ce ta dubi Amjad wanda duk yanayinsa ya canza da jin kalaman sabah tace mishi “Baby ka share shi kawai, karka bari kalaman sabah suyi tasiri akanka nasan yana fadin haka ne don kawai yaga ka tanka mishi amma kawai ka share shi kaji.”+
Amjad ajiyar zuciya yayi yace ” babu komai, taho mu tafi”. Haka suka karasa inda yayi parking motarsa suka shiga. Dayake rockview babu nisa daga makaranta, nan da nan suka isa. Amjad ya nuna tickets dinsu a gaban gate aka barsu suka shiga, suna shiga ciki dalubai suka tadda a cike cikin hall din. Daman tickets din da amjad ya siya na VIP ne, so a gaba shida samha suka samu wuri suka zauna, aka fara show din. Celebrities kala kala akayi inviting suka zo suna performing a gaban stage din. Cikinsu ma har da waenda samha bata taba ganinsu ba. Dalubai sai ihu sukeyi da ganin celebrities din. Samha ma ba karamin murna tayi ba dataga daya daga cikin mawakin da take yawan sauraronsa yana performing a stage. Funfair din dai ya hadu babu laifi.
Amjad mikewa yayi yace mata bari yaje ya siyo musu abunda zasu dan motsa baki dashi a stalls din dake baya. Tace mishi Toh shikenan. Yana barin wajen, samha na zaune ita kadai tana kallon performance din da akeyi a stage, sai taji kamar ana kallonta. Juyowar da zatayi kenan sai sukayi ido biyu da sabah wanda yake zaune a can gefen stage din tare da abokanansa, fararen idanun nan nasa masu matukar kyau ya kafeta dasu sai faman binta da kallo yake yi. Suna hada ido samha taji bugun zuciyarta ya karu, Itama kasa daine kallonsa tayi data ga irin kallon dayake mata koh kyaftawa baya yi.
Samha dana zuciyarta tayi tana kokarin kawo wa kanta nutsuwa game da yanda take ji a wanan lokacin. Sabah kashe mata ido daya yayi daga inda yake zaune ya daga mata hanunsa wanda yake daure da kyallen daya kwance daga jikin jakarta. Gashi duk kyallen ta bace da jini sai faman diga takeyi amma koh nuna alamun damuwa baiyi ba. Tabe baki tayi ta kawar da kanta gefe daga inda yake zaune. Bafi minti goma ba sai ga amjad ya dawo dasu lemu da cakes ya ajiye a kan table din dake gabansu.
“Sorry baby, kinga na jima koh? Ya tambayeta
Murmushi samha tayi sa’anan tace ” koh kadan ai kuma naga kayi sauri”.
Dariya amjad yayi ya bude musu lemun da cakes din suka fara ci. Haka suka cigaba da shakatawa a funfair din har akazo aka tashi. Bayan an tashi daga funfair din suka fito daga hall din sukaje inda amjad yayi parking motarsa, suka shiga amjad ya tayar da motar suka dau hanyar gida. Suna isa kofan gidansu amjad yayi parking. Samha ce ta dube shi fuskarta dauke da murmushi tace” gaskiya yau naji dadin fitan nan da mukayi tare ni da kai, na jima banzo funfair dauke da dimbin jamma’a ba irin wanan. Nagode baby” ta fada mishi tana dubansa.
Murmushi ya dan sakar mata sai kuma taga ya bata rai yana cewa ” Nima naji dadin kasancewar mu tare a yau dinan amma akwai abunda nayi niyan na fada miki tun farko amma sai gashi sabah ya rigani” amjad ya fada mata yana dubanta.
“Me kenan?”ta tambayeshi.
” daman inaso na fada miki cewa kinyi kyau sosai yau dinan” ya fada mata.
Murmushi ta sakar mai sa’anan tace mishi “Nagode”.
Murmushi shima ya sakar mata
Sa’anan yace “bayan haka akwai abu daya danake so na fada miki, dazun da kika zo kika tadda ni da sabah, ba abunda kike tunani bane ya faru. Ba wai yana cin zalin karamin yaron bane, a’a ya kama yaron yana abunda bai dace bane shiyasa kikaga yana mishi fada. A gabana komai ya faru”. Amjad ya sanar da ita.
Nan take samha sai taji wani iri. “Dukda dai banso na fada miki ba saboda sanin halin sabah amma gani nayi ya kamata kisan Gaskiyar al’amarin.” Amjad ya sake fada mata.
Shiru samha tayi tana nazari sa’anan ta danyi murmushi ta soma fadin “babu komai kuma Naji dadi daka sanar dani asalin abunda ya faru, kuma na gode. Ta fada mishi. Hira suka danyi a tsakaninsu sa’anan sukayi Sallama ta fita daga motar ta shiga cikin gidansu.
Amjad ya tsaya yabi bayanta da kallo har ta shiga ciki.Nan take kuma sai yakejin wani iri ” Anya nayi abunda ya dace kuwa? Ya nakejin dukda na fada mata gaskiyan al’amarin kuma nake dana sanin fada matan danayi?” Ya tambayi kansa. Ajiyar zuciya yayi ya tadda motarsa ya tafi.
Bangare sabah kuwa, zack ne ya lura da hanunsa yaga sai faman digan jini yakeyi ” SB wanan ciwon dakaji anya bazaka je asibiti koh chemist a duba maka ba? Duba fa yanda hanunka keta diga da jini”.
Sabah share shi yayi ya cigaba da abunda yakeyi. Kyallen dake daure a hanunsa ya sake gyarawa ya daura hanunsa da kyau. Zack dayaga bashida niyan zuwa a duba masa hanun, sai ya kyale shi kawai don yasan halin sabah sarai da taurin kai idan baiyi niyan yin abu ba.
Bangaren samha kuwa, tana shiga cikin gida tayi sallama ta shiga fallon, gidan shiru babu alamun kowa, lami ta tafi kasuwa yin cefane. Samha ta haura sama ta fara duba dakin ammi taji shuru bataji duriyan ta ba, nan take ta fara tunanin ko har yanzu bata dawo daga unguwan data je bane. Dakinta ta shige ta soma cire kayan jikinta ta daura towel sa’anan ta fada bayi. Kuna Fanfon dake saman Bath tub din bayin tayi ruwan dumi ya fara zuba, Sai data cika tub din da ruwa tukuna ta kashe fanfon. Bude body wash dinta mai kamshin man kwakwa tayi ta zuba a cikin ruwan ya fara kumfa sa’anan ta cire towel din data daura jikinta ta shige ciki. Ajiyar zuciyar tayi data ji wani irin dadi yana ratsa duk ilahirin jikinta.Nan da nan kuma tunanin abubuwan da suka dinga faruwa da ita cikin yan kwanakin nan suka dinga dawo mata, musaman yanayin sabah, don yanayinsa ba karamin daure mata kai yakeyi ba. Mamakin kanta takeyi musamman dazu a wajen funfair da suka hada ido dashi taji bugun zuciyarta ta karu, gabanta sai faman faduwa yakeyi. Bata taba jin irin haka ba. Toh meke shirin faruwa ne? Ta tambayi kanta. Haka ta zauna kusan 30 mins cikin bath tub din sai faman tunani takeyi, bacci ne taji ya soma deban ta ta fara gyangyadi. Kamar daga sama taji wayarta na ringing daga cikin daki. Farkawa tayi daga gyangyadin da takeyi ta soma kokarin mikewa daga cikin bath tub din, towel dinta ta jawo ta daura. A dadafe ta fito daga cikin bayin zuwa dakin tana ganin dishi dishi. “Ya nake jin kaina haka koh don na jima cikin ruwan dumin ne,” ta tambayi kanta. Tana kokarin karasawa wajen gado inda ta ajiye wayarta kawai taji wani irin jiri ya debeta bata san sanda ta fadi a kasa ba sumamiya.
Bangaren anty fanneh kuwa tayi ta faman kiran wayar samha bata daga ba. Itama lami yar aikinta tayi ta faman kiran layinta bata daga ba. “Koh lami ta bar wayanta a gida ne?”Toh ita samha ina ta ajiye wayarta ne fissabilillah inata faman kiranta taki dagawa.” Anty fanneh ta tambayi kanta Hankalinta a tashe don tana son ta sanar da samha cewa bazata samu damar dawowa gida ba a yau don an musu rasuwa. Kanwar mahaifiyarta da take can gidansu a Bariga ce ta rasu, dazun aka kirata a waya aka sanar da ita, babu shiri ta wuce can gidan rasuwar. Shiyasa take ta neman layin samha ta sanar da ita. Tunani kala kala ne ke ta mata yawo a ka. Tana cikin tunaninta sai ga kiran wayar mahaifin sabah Alhaji muazzam ya shigo wayarta. Dagawa tayi suka gaisa ” fanneh ya naji muryar ki haka kamar kina cikin damuwa, lafiya?” Ya tambayeta.
“Wallahi rasuwa aka mana, kanwar mahaifiyata ce aka kirani dazu aka sanar dani cewa ta rasu. Yanzu haka ma ina bariga, can gidan mu.”
“Innalillahi waina illaihi raji’un. Allah ya jikanta kuma Allah ya kai haske makwancinta” Alhaji muazzam ya mata addua’a.
“Ameen, Ameen” ta ansa mishi.
“Ke kadai kika tafi ko tare da samha?” Ya tambayeta.
“Ni kadai na tafi, ai tafiyar gagawace ta taso mun, yanzu haka ma inata faman nemanta a layi bata dagawa, gashi yamma tayi duk hankalina a tashe yake. Lami ma yar aikina inata faman kiranta itama bata daga waya ba”.
Daga bangaren alhaji muazzam shiru yayi yana jinta, sai ga sabah nan ya shigo cikin palour zai haura sama zuwa dakinsa. ” sabah zonan, kun hadu da samha kuwa yau dinan a makaranta? ” mahaifin nashi ya tambayeshi.
“Eh abba na ganta a school dazu” ya bashi ansa
“Da aka tashi fah ka sake ganinta?” Alhaji muazzam ya sake tambayanshi.
“Eh na ganta muna tashi ta wuce gida ai” ya bashi ansa.
Alhaji muazzam ya sake kara wayar a kunnensa yana fadin ” toh kinji wai ta koma gida”. Ya sanar da ita.
“Toh dan Allah zaka iya tura sabah ko wani zuwa gida yaje ya dubo mun ita, wallahi jikina yanata mun wani iri tun dazu na kasa sukuni sai nake ji kamar babu lafiya.”
“Toh shikenan bari na shirya da kaina zanje na dubo miki ita” ya fada mata.
Tace toh shikenan, godiya ta mishi sa’anan ya kashe wayen. Mikewa yayi ya dauko daya daga cikin keys din motoccinsa ya fita yaja mota yayi hanyar gidansu samha.
Bangaren su samha kuwa, lami ce ta dawo daga cefanen data je yi, taje ta zube kayan cikin kitchen. Gyaran fallon ta fara yi daga bisani ta haura sama dakin anty fanneh ta soma gyarawa. Bayan ta gama gyara ta fito daga dakin. Dab da bakin kofa ta tsaya tana jin karar waya sai faman ringing takeyi a dakin samha ba daga ba. Zuwa tayi ta soma kwankwasa kofar dakin taji shiru ba ansa ba, kuma tasan samha na ciki don taga alamun ta dawo daga makaranta. Tayi kusan minti biyar tana kwankwasawa ba zo an bude ba, tura kofar tayi taji ta a bude, ta qusa kai ciki tana lekawa ko zata ga samha. Tana karasowa cikin dakin Idanunta suka ci karo da samha a yashe a kasa ko motsi bata yi. Wani irin kara lami ta sake hankalinta a tashe ta rugo da gudu ta tsuguna a inda samha take kwance a kasa. Salati ta sake tana ta faman jijiga samha amma ina, samha ko motsi bata yi. A rude lami ta mike ta sauko kasa tana kwadawa mai gadi kira. Dai dai lokacin motar alhaji muazzam ya sawo kai kenan cikin gidan. A rude lami ta tadda dashi tace yazo ga samha can a yashe a kasa koh motsi batayi. Hankalin alhaji muazzam a tashe yabi bayan lami suka shiga cikin gida suka haura sama yana biye da ita. Suna shiga cikin dakin yaga samha a kwance a kasa a sume. Babu shiri yacewa lami ta sanya mata kaya azo a kaita asibiti. Lami ta ciro kaya ta sanya wa samha. Tare suka riko ta aka sauko da ita zuwa cikin mota. Hankalinsu a matukar tashe suka nufa asibiti. Koh da suka isa asibitin emergency straight aka kaita.
Lami sai faman kuka takeyi tana daura hanu aka, ciro wayarta tayi tana kokarin kiran anty fanneh, alhaji muazzam ya dakatar da ita, yace su tsaya suga sakamako daga wajen likita tuna. Bayan kusan hour biyu suna tsaye sai ga likitan nan ya fito yacewa alhaji muazam daya biyo shi cikin office dinshi. Suna shiga office din suka zauna.
” likita ya jikin nata” alhaji muazzam ya tambayeshi hankalinsa a tashe.
“Da sauki alhamdulillah, tama farfado tana cikin dakin da mukayi admitting dinta. Ba wani abu bane ke damunta illa stress da yawan tunani da takeyi shiyasa jikinta ya kasa dauka ta suma. Gaskiya alhaji yar ka tana bukatan hutu da kwanciyan hankali sosai, don idan ta cigaba da haka zai iya jawo mata matsala nan gaba. Likitan ya sanar dashi.
Ajiyar zuciya alhaji muazzam yayi yana nazarin maganganun likitan.
“Yanzu ga waenan magungunan dana rubuta, a samu a bata tana sha, zata samu hutu sosai kuma zai rage mata tunanin da take yawan yi. Idan drip din da muka sanya mata ya kare zaku iya tafiya gida zuwa anjima ba sai ta kwana anan ba. Likitan ya fada mishi.
Godiya alhaji muazzam ya mishi sa’anan ya mike ya fita daga office din. Lami ce ya tadda a tsaye gabadaya duk tabi ta damu. Yace mata ta kwantar da hankalinta samha lafiyarta kalau tama farfado. Ajiyar zuciya lami tayi ta daga hannu tana godewa Allah. Likitan ya fito yace musu su biyo bayanshi suka nufa dakin da aka kwantar da ita.
Suna shiga cikin dakin da aka kwantar da samha suka ganta kwance duk jikinta yayi weak. Karasowa sukayi ciki suna mata sanu, ita kam binsu da kallo takeyi daya bayan daya.
Alhaji muazzam ne ya matso kusa da ita yana tambayarta ya jiki ” haba samha, yanzu duk kewar amminki ne haka? Ai da kin kirani a waya kince nazo na dauke ki” alhaji muazzam ya fada mata yana murmushi.
Samha binshi da kallo ta dinga yi bata ce komai ba don har yanzu bata gama dawowa cikin hayacin ta ba. Bacci ne ya sake debanta.
Alhaji muazzam ya kale likitan yace kace zamu iya tafiya da ita gida koh? Na fison ma mu wuce gida da ita, don nasan a gida zata fi samun ishashen hutu.”
“Eh zaku iya tafiya, bari na kira nurse tazo ta duba mata drip din kuma ta bata alura. Yanzu zan shiga ciki na rubuta muku takardar sallama.” Yana gama fadin haka ya fita ya barsu a dakin.
Wayar alhaji muazzam ne ya soma ringing, ya ciro wayar daga cikin aljihu yaga Anty fanneh ce ke kiransa, daga wayar yayi ya kara a kunansa. ” ya ka samu ka isa gidan kuwa, tana cikin gidan?” Ta watso mai tambaya.
Ajiyar zuciya yayi ya soma mata bayanin abunda ya faru da yanda yaje ya riske ta, har ma suna asibiti amma ta farfado yanzu za sallamesu su wuce gida. Ba karamin tashin hankali anty fanneh ta shiga ba jin samha tana kwance a asibiti. Alhaji muazzam ne ya dinga kwantar mata da hankali yace ba wani serious abu bane kawai stress ne ya mata yawa. Amma yanzu zai tafi da ita gida, musamman zai sa family doctor dinsu ya zo yana dubata a gida. Ajiyar zuciya anty fanneh tayi data ji cewa samha ta farfado kuma ba wani serious abu bane don tasan samha batada wuyan suma. Tun tana karama Koh rashin lafiya take ta dinga faman suma kenan, saboda jikinta baya iya daukawa. Anty fanneh tace ma alhaji muazzam ya kaita gidansu kawai yana sa mata ido har zuwa ran da zata dawo don tana sa rai sai jibi bayan sadakan uku zata dawo gida. Alhaji muazzam yace babu matsala, kar ta samu damuwa ai samha tamkar yar shi ce zai kula da ita sosai. Godiya anty fanneh ta mishi sa’anan ya kashe wayar.
Koh da drip din ya kare, aka sallamesu, samha sai faman bacci takeyi cikin mota har suka isa gida. Lami ce ta taimaka aka kai samha daki aka kwantar da ita. Alhaji muazzam ya kira likitanshi dr fahad daya zo ya sake duba mishi ita. Dr fahad yazo har gida ya sake duba ta yace lafiyarta lau, idan ta tashi washe gari zata jita garau. Alhaji muazam ya mishi godiya sa’anan ya sallameshi.
Washe gari sai zuwa yamma samha ta farka, don ba karamin bacci tasha ba. Tana bude idanunta ta tsinci kanta cikin wata bakuwar daki. Mikewa tayi ta fara bin dakin da kallo, ko ina a dakin tsab tsab. Kana ganin yanayin dakin kasan ba na karamin gida bane. Saukowa tayi daga kan gadon tana kokarin tuno abubuwan da suka faru a jiyan. A ina nake kuma? Ta tambayi kanta. Karasawa tayi inda kofa yake ta bude a hankali ta fita daga cikin dakin. Taga wani hadadiyar matakala da zai kaita zuwa kasa. Bin matakalar tayi ta soma saukowa ahankali tana bin ko ina na gidan da kallo don kana ganin yanayin gidan kasan ba karamin kudi aka kashe wurin kayace ta ba. saukowa tayi ta karasa cikin fallon taga wani mutum zaune a kan kujera yana kallon tv.
Mutumin yana jin alamun shigowar mutum cikin fallon ya juyo yaga samha tsaye tana kallonsa. Samha kam data ga mahaifin sabah a zaune, zuciyarta ne ta fara bugu da karfi ” kar dai gidansu sabah nake? Me ya kawoni gidansu kuma” ta tambayi kanta.
Alhaji muazzam yana ganin samha ya mike cikin sauri yazo ya tadda ita fuskarsa dauke da fara’a ” samha har kin tashi? Ya jikin naki? Ya tambayeta.
Binshi da kallo da dingayi daga bisani ta bude baki ta soma fadin ” da sauki, a ina nake?” Ta tambayeshi.
” au wai nan kike nufi? Kina cikin gidanku ne mana. Daga yanzu ki dauka tamkar nan ma gidanku ne kina jina koh. Zaki iya shiga ciki ki dauki duk dakin da kikeso a cikin gidan nan babu matsala ?” Mahaifin sabah ya fada mata cike da dauki.
Zaro ido tayi tana fadin ” Gaskiya a’a, ina ammina nidai gaskiya ka mayar dani gida wajen ammina ” ta fada mishi tana kokarin neman hanyar waje.
“Haba samha meyasa kike haka, ai Amminki ce tace na kawoki nan gidan tunda bakida lafiya kuma ita bata nan babu mai kula dake a can gidan naku.” Nan ya zayane mata duk abunda ya faru jiyan. Ajiyar zuciya tayi itama abubuwan da suka faru jiya suka soma dawo mata.
“Yanzu me kike so kici? Fada duk abunda kikeso za a kawo miki.” Ya tambayeta.
Tsayawa tayi tana kallonsa bata ce komai ba. “kinga Ki kwantar da hankalinki ki sake jikinki. Ni dinan da kike gani inaso ki mayar dani tamkar nine mahaifin ki, duk abunda kika ga kina so koh kuma kina bukata ki sanar dani kinji ko”
Gyada mishi kanta kawai tayi.
“Toh yanzu fada mun mai za kawo miki kici” ya sake tambayarta.
“Babu komai” ta bashi ansa.
A’a mutum bashida lafiya ai dole yaci wani abu ya samu karfi a jikinsa. Kinga fa tun jiya baki ci komai ba” ya fada mata.
Kiran mai aikin gidan yayi yace tazo ta hada ma samha shayi tasha da zafi zafinsa. Yar aikin tace toh ta shige cikin kitchen.
Samha ta zauna kan daya daga cikin kujerun fallon sai dube dube takeyi. Alhaji muazzam ne yazo ya dinga janta da hira har ya samu tadan sake jikinta. Tana gama shan tea din da aka kawo mata, yace ta jira shi yana zuwa. Ya shiga cikin daki ya fito da wata babbar album a hanunsa. Yazo ya zauna kusa da ita ya bude album din yace ta matso ta gani. Matsowa tayi tana kallon cikin album din.
“Kalla sabah lokacin yana karami” ya fada yana nuna hoton wani kyakyawan baby. Masha Allah samha ta fada a ranta don sabah tun yana karami yakeda bala’in kyau.
Murmushi ta sake, alhaji muazzam ya cigaba da bude album yana nuna mata hotunan family dinsu. Wani hoto ya gani ya tunsure da dariya. Hoton dauke yake da sabah lokacin yana karami da alamun bai wuce shekara biyu ba yana kuka ga katuwar cake a gabansa. ” bazan taba mantawa da lokacinan nan ba, wai fa nan ranar birthday dinsa ne yana dan shekara biyu sai faman rigima yakeyi yana son ya jawo cake din ya bata jikinsa aka hanashi shine yaketa faman kuka”
Dariya itama samha tayi suka cigaba da kallon hotunan.
Tana cikin kalle kalle sai idanunta suka sauka kan wata mata tare da sabah. Matar balarabiya ce kyakyawa da ita. Murmushi takeyi rungume da sabah aka musu hoton, kuma a lokacin sabah ya danyi wayo sosai. Shima murmushi yakeyi yana rungume da ita.
“Wacece wanan” samha ta tambayi alhaji muazzam tana nuna hoton.
Gani tayi murmushin dake fuskar sa ta bace. Shiru yayi yana nazari sa’anan ya soma fadin ” ban ma san ya akayi hotonan ta sake dawowa cikin album dinan ba. matan nan da kike gani cikin hoton itace mahaifiyar sabah. Sabah tun yana shekara bakwai muka rabu da ita. Na aurota a lokacin danaje lebanon karo karatun masters dina. Anan muka hadu ta amince zata aureni ta biyoni nan Nigeria. Toh tunda mukayi aure da ita muketa samun matsala cewa takeyi banida lokacinta aiki kawai nasaka a gaba. Bazan boye miki ba samha nasan ban kyautata musu ba daga ita har sabah din don alokacin kwata kwata banida lokacin su kuma abubuwa suna mun yawa wajen aiki. Daga karshe dai taga bazata iya ba, tace na saketa ta tafi abunta ta koma kasar su. Haka sabah ya taso shi kadai babu mahaifiyarsa a kusa dashi. Kullum idan na dawo daga aiki zan tadda shi yanata faman kuka yana neman momynsa. Nasan ban kyauta masa ba kuma a kullum kara nadamar abubuwan da suka faru a baya nakeyi.Da zan iya dawo da hanun agogo baya da nayi komai ya dawo daidai. Amma haka Allah yaso. Shiyasa kikaga nake lalaba sabah don bana son abunda zai sashi yaji yana yawan kewar mahaifiyarsa. Ballantana ma yanzu ai ya riga da ya girma. Don ko a yanzu haka zan iya masa aure idan ya kawo mun suruka” alhaji muazzam ya fada yana dariya.
Itama samha dariya tayi tana mamakin abubuwan da mahaifin sabah ya gama fada mata. Tana mamakin halayen mutumin, kwata kwata bashida damuwa, jibi yanda yaketa janta da wasa da hira kamar ba babban mutum ba.
“Samha idan bazaki damu ba, ina so ki sani cewa inason mahaifiyarki kuma da aure in Allah ya yarda. Don tunda na hadu da ita naji duk wata damuwata ta kawar mun dashi. Rabona da insamu farin ciki da nake ciki a yanzu haka tun lokacin muna tare da mahaifiyar sabah. Kuma na sani samha bazan taba mayar da gurbin asalin mahaifinki ba amma inaso ki bani wanan damar, inaso ki mayar dani tamkar nine mahaifinki, ni kuma na miki alkawarin zan kulla dake da mahaifiyarki har zuwa karshen rayuwata. Alhaji muazzam ya fada mata yana dubanta.
Samha bata ce komai ba don jikinta duk yayi sanyi da jin maganganunsa. Sai yanzu ta fara ganin abunda yasa amminta ta amince zata aureshi don ta lura mutumin yanada mutucin sosai kuma bashida matsala.
Murmushi ta sakar masa tace ” Babu damuwa Abbah, Allah ya tabbatar mana da alkhair. Ta fada mishi tana murmushi.
Wani irin dadi alhaji muazzam yaji dayaji ta kirashi ta sunan abbah.
“Bari na tattara album dinan na shiga dasu ciki, kafun sabah ya dawo ya gani, don na tabbatar baza samu zaman lafiya a cikin gidan nan ba idan yasan na nuna miki hotunansa yana karami”. Yana gama fadin haka ya tattara album din ya mike ya haura sama..
Kamar yasan sabah yana tafe don yana shigewa daki sai gashinan yayi sallama ya shigo cikin parlourn, kyakyawar fuskar nan nasa a daure tamau tamkar bai taba dariya ba. Yana ganin samha zaune a fallon ya tsaya curuss yana kallonta. Sanye yake cikin bakaken kananan kaya kamar ko da yaushe. Farin riga da bakin jeans sai kuma bakin jacket daya dora akai, sumar kansa ta kwanta bisa kansa sai shekki takeyi. Karasowa yayi cikin fallon sai ga mahaifinsa ya fito daga cikin daki.
“Abba ga sabah nan ya dawo” samha ta sanar dashi.
Yana ganin sabah fuskarsa ta barke da murmushi “Baby boy ka dawo? Ya lectures yau? Abba ya tambayeshi.
” lafiya lau, sannu da gida abba” Sabah ya gaishe shi yana wani cicin magani. Shi kam baya son sunan baby boy da abbansa yake kiranshi da shi, sai kace wani karamin yaro.
Wuri ya samu ya zauna yana ajiyar numfashi. Samha ta lura da dayan hanunsa taga ya sake daureta da farin kyale. Nan take taji wani iri data tuno da dalilin dayasa yaji wanan ciwon. Kuma tasan har yanzu bai je an duba masa ciwon wa ba.
Abbah ne ya dubi samha yace ” samha ya kamata ki samu ki koma daki ki kwanta don kina bukatan hutu sosai”.
Samha ta gyada masa kanta. Mikewa yayi yace shi zai shiga ciki ya musu sai da safe ya haura sama. Yar aikin gidan ce tazo ta same sabah tana tambayarsa abunda zai ci, yace mata babu komai a koshe yake.
Duban samha yayi yana tambayarta ya jiki. Ta bashi ansa da dasauki, sabah yace shi zai haura sama zuwa dakinsa ya watsa ruwa. Ya mike, har ya soma tafiya kenan samha ta kira sunansa tana fadin “sabah?”. Tsayawa yayi ya Juyo yana dubanta. Mikewa tayi daga inda take zaune tazo ta tsaya a gabansa. ” naga hanunka” ta fada mishi.
Babu musu ya dago hanunsa ya nuna mata, gani tayi hanun har ya soma kunburi da ciwon dayaji.
“Meyasa baka je asibiti an duba maka ba” ta tambayeshi. Bai bata ansa ba ya cigaba da kallonta.
“Idan akwai spirit da cotton wool da kuma bandage ka kawo sai na gyara maka ciwon.” Ta fada mishi.
Gyada mata kai kawai yayi ya haura sama yaje ya watsa ruwa ya saka kayan baccinsa bargo ya ruko a hanunsa, saboda sanyi da akeyi. Ya kwaso kayan data bukata ya sauko kasa tare dasu. Yana zuwa inda take zaune ya ajiye kayakin a gefe. Ya zauna kan kujerar dake kusa da ita yana dubanta. Samha bata ce komai ba, matsowa tayi ta kamo hanunsa mai dauke da ciwon ta soma cire kyallen daya daura ciwon dashi. Gani tayi hanunsa duk ta bace da jini, ga ciwon nan a bude a tafin hanunsa ta kumbura. Cotton wool din ta dauko ta tsoma cikin spirit din ta soma goge masa ciwon dashi a hankali tana hura masa iskan bakinta don kar ya mishi zafi. Sabah kam kura mata ido yayi yana kallonta ko kyaftawa baya yi.
” Akwai zafi?” Ta tambayeshi tana cigaba da goge masa ciwon.
Shiru kawai yayi yana kallonta daga bisani ya gyada mata kansa yace “sosai ma”
Dagowa tayi suka hada ido taga irin kallon dayake binta dashi. Wani irin bugu kirjinta ya soma yi. “Wanan kallon fa da yake mun? Me yake nufi dashi” ta tambayi kanta. Nan da nan ta soma kokarin kawo wa zuciyarta nutsuwa.
Cigaba tayi da goge masa ciwon, daga bisani ta sake tambayarsa “har yanzu kana jin zafi?” .
Matsowa yayi dab da ita har tana iya shakkan daddaden kamshin turaren jikinsa sa’anan ya rada mata cikin kunne. “eh akwai zafi har yanzu”.
Matsawa tayi daga kusa dashi Jikinta sai faman rawa yakeyi.
Murmushi sabah ya sake sa’anan ya soma tambayarta ” wai sanyi kike ji ne?”
“A’a ba wani sanyin da nakeji fa”. Ta fada mishi.
Bai ce mata komai ba kawai taga ya dauko bargon daya zo ta ita ya bude. Kafun tayi wata magana, taga ya rufesu shi da ita cikin bargon.
Hankalinta a tashe ta soma mutsu mutsun fita daga cikin bargon ” na fada maka ba sanyi nakeji ba, meye haka sabah?!” Ta fada tana kokarin tureshi, kirjinta sai faman bugu yakeyi.
Sabah bai ce mata komai ba sai lumshe fararen idanunsa yakeyi kamar mai jin bacci daga bisani yace ” Da kike goge mun ciwon nan sai naji zafin ya ragu kuma duk damuwar da nake tattare da ita naji sun gushe. Nagode kanwata “. Yana gama fadin haka taga ya soma gyangyadi. Gani tayi ya dora kansa bisa saman kafadarta, fuskarsa daidai saitin wuyanta yana shakar daddaden kamshin jikinta. Kafun kace meye bacci har yayi awon gaba dashi.