ZABIN SAMHA CHAPTER 4
Ajiyar zuciya samha tayi ta yaye bargon daya lulubesu dashi sa’anan ta gyara masa kwanciya kan kujeran. Fresh bandage ta dauko ta daure masa ciwon hanunsa dashi.+
Tana gamawa ta mike, har ta juya da niyan barin wurin taji abu kamar ya rike mata kafa. Juyowa tayi taga hanun sabah rike da jelar rigarta, dagowa tayi tana dubansa taga still baccinsa yakeyi hankalinsa kwance.
Tayi tayi ta kwace rigarta daga rikkon daya mata ama hakan ya gagara haka ta dawo ta zauna kusa dashi ta kura mishi ido tana kallonsa yana bacci. Baccinsa yakeyi kamar bashida wata damuwa hankalinsa a kwance bazaka ce shine masifafen nan na mai yawan rigima da mutane ba, cigaba tayi da kallon kyakyawar fuskarsa, eyelashes dinsa zara zara dasu ko ita da take mace batada eyelashes masu kyau irin wanan.
Ajiyar zuciya tayi ta kawar da dubanta daga gareshi ta dauko remote ta soma canza tashan tv. Wani programme ake nunawa a telemundo, ta fara bi. Tana cikin kallo itama bata san sanda bacci yayi awon gaba da ita ba tana zaune kan kujerar.
Washe gari da safe cikin bacci ta taji ana fadin “keh sarkin bacci, bazaki tashi bane? Gari fah ya waye”.
Cikin baccin ta turo dan karamin bakinta cike da shagwaba tana fadin ” Ni gaskiya a kyaleni, bacci nakeji” ta fada tana gyara kwanciyarta.
Ko meye ta tuna, sai kuma ta bude idanunta cikin sauri ta juyo tana kallon wanda yazo yana tashinta. Sabah ta gani a tsaye fuskarsa dauke da murmushi yana kallonta.
Zaro ido tayi ta mike tana salati ” nashiga uku, anan muka kwana?” Samha ta tambayeshi tana zaro ido.
Gyada mata kai yana murmushi don gaba daya yanayinta dariya yake bashi musamman yanda duk tabi ta rikice.
“Abba fa? Ina yake karde yazo ya ganmu muna bacci tare a fallo?” Ta tambayeshi hankalinta a tashe.
Murmushi sabah ya cigaba dayi sa’anan ya durkusa daidai saitin kunnenta ya soma fadin “daman haka kike surutu cikin bacci?”
Ido ta zaro tana dubansa ” wake surutu cikin bacci”.
“Toh in fada miki maganganun da kika dinga yi ne cikin bacci?”
Kallon shi kawai ta cigaba dayi hankalinta a tashe tana zaro ido. ” sunana kika dinga ambatowa kina kirarin kina sona” ya fada yana daga mata gira daya fuskarsa dauke da murmushi.
Wata yar kara samha ta sake tana toshe kunnenta da jin kalamansa, hankalinta a tashe ta mike daga kan kujeran ta kwasa a guje tayi sama zuwa dakinta. Bayi ta fada ta fara watsa ruwa a fuskarta. Cike da tashin hankali ta dubi kanta cikin madubin dake cikin bayin tana girgiza kanta kamar zatayi kuka ” na shiga uku ya akayi nayi wanan sakacin nabari sabah yaga yanda nake bacci? yanzu nasan ya ji duk surutan dana dingayi cikin baccina. Wayo Allah ya akayi na bari yasamu wanan daman?” Ta tambayi kanta cike da tashin hankali.
Nan kuma kallon daya dinga mata jiya dadare a lokacin da take goge masa ciwo ya dinga dawo mata cikin kwakwalwa. Gabadaya tunaninta ya soma hargitsewa. Meyasa kwana biyun nan idan sabah yana kusa dani sai na dinga jin zuciyata na harbawa, gabadaya sai na nema nutsuwata na rasa” haka ta dinga tambayar kanta amma ta gagara samun ansa.
Ruwa ta watsa a jikinta ta fito ta soma shirin zuwa school. Abba yace idan tasan har yanzu jikinta baiyi kwari ba tayi zamanta a gida, samha taqi kememe tace lafiyarta lau. Sabah tabe baki yayi yana jinsu bai ce musu kalla ba. suna fita harabar gidan wata hadadiyar mota qirar benz ce ke jiransu da driver. Ga wata camry ma dauke da bodyguards guda uku suna tsaye kusa da motan suna jiran fitowarsu. Suna isa wajen motar, daya daga cikin bodyguard din yazo ya budewa Abba seat din baya shi da samha suka shiga ciki. Sabah shi kuma ya zauna a gaba, driver yaja su suka bar gidan. Ko da suka isa makaranta aka juyo ana kallon motoccin dan ba karamin daukan ido suke ba, musamman benz din. Bodyguards dinne suka zo suka bude wa abba kofa ya fito daga cikin motar. Sabah shima ya bude kofar ya fito. Samha na nan zaune cikin motar taki fitowa. Sabah ne ya dube ta yana fadin ” wai ke me kike jira? bazaki fito bane? Ya fada yana galla mata harara.
Bata fuska tayi tana turo baki ta sauko daga cikin motar.
Dalubai ne suka dinga binsu da kallo suna nuna su da kuma motar da suka fito daga ciki. Gabadaya samha ta dinga jin wani iri da kallon da aketa faman yi musu. Barin ma sabah wanda yayi kicin kicin da fuska kamar hadari, don a kulle yake da mahaifin nasa. Shi yasha gayawa abba bayason ira iren waenan abubuwan. Ko a gida ma bai cika tuka motocin gidansu ba don shi ya gwamace duk inda zashi ya tafi da power bike dinsa. So tari yana gujewa fita da Abbansa don shi bayason yawan kallon jamma’a.
Suna cikin tafiya samha ta dubi sabah ta soma magana kasa kasa ” wai nikam sai nake ganin kamar abubuwan sunyi yawa, jibi yanda aketa faman binmu da kallo”.
Sabah ne ya bata ansa da ” ai duk laifin Abbah ne, nasha gaya mishi idan zamu fita ya daina tattaro mana waenan body guards din. Kuma ba sai lallai a tuko mu cikin waenan motoccin ba” ya fada ranshi a bace.
Suna isa department dinsu samha ta haura sama zuwa ajinsu, shi kuma sabah ya wuce nasu department din. Samha zauna take cikin aji itada su khadija suna hira. Khadie ce take fadin ” yanzu kina nufin dake da sabah da kuma VC kuka shigo cikin makaranta yau?”
“Toh ya zanyi? Bazan iya ce mishi a’a ba shiyasa muka zo tare” samha ta fada tana dubansu.
“Yanzu kina nufin tun shekaran jiya kina gidansu sabah? A can kike kwana? Amina ta tambayeta.
Da sauri samha ta toshe mata baki, tana mata nuni da amjad dake zaune a seat din gaba yana karatu.
“Kiyi magana a hankali mana, kinaso yaji ne?” samha ta fada muryarta kasa kasa.
Khadija ce ta dube ta tana fadin “Amma samha ya akayi hakan ta faru? Ba kun shirya keda amjad ba har kuka je funfair din rockview tare? Ya akayi kuma kika tsinci kanki a gidan su sabah?”
Samha bata bata ansa kawai sukaga ta mike tayi hanyar waje.
“Ina zakije kuma?” Su khadie suka bita da tambaya.
“Na tuna mrs kayode ta aikeni dazu, tace naje library na dauko mata wasu takardu” tana gama fadin haka ta fice daga ajin.
Su khadija kam tabe baki sukayi don Sun san guduwa tayi don karta basu ansa tambayoyinsu.
Amina ce ta cigaba da fadin ” Toh meye aciki don samha ta kwana a gidansu sabah. Ai VC ya kusan zama mahifinta so ni banga wani aibu a ciki ba”
“Eh mana an san da hakan amma amina, abun dubawa anan shine kasancewarta da sabah a wanan gidan. Kinsan halinshi sarai. Kin manta abunda yayi wa samha ranan daya rungumeta?”.
Ai kam maganar karap a kunnen amjad, daman yana zaune a seat din gaba yana jin duk maganganun da sukeyi a baya. Wani irin haushi da kishi ne suka taso masa. Baisan sanda yayi wurgi da takardun da suke gabansa ba ya mike zuciyarsa na tafarfasa ya bar ajin.
Khadija da amina kallon juna sukayi suna binshi da kallon mamaki .
Samha tana tsaye cikin library tana dube dube cikin takardun da aka jera kan shelves. amma gabadaya hankalinta da nutsuwarta basu tare da ita. Tunani kala kala ke mata yawo a ka. Tambayar kanta ta soma yi ” meyasa bana son amjad yaji maganganu da mukeyi akan sabah? Meyasa nakeji kamar na aikata masa baban laifi danaje gidansu sabah?” Duk tambayoyin nan da take yi wa kanta bata samu ansar ko daya ba. Cike da sanyi jiki ta juyo zata bar library din. Tana juyowa taga mutum tsaye a gabanta. A firgice ta dago taga amjad fuskar a daure tamau, Idanunsa sunyi ja sun kankance. Kana ganinshi kasan babu lafiya.
Samha itama hankalinta a tashe ta soma tambayarsa ” Amajad, lafiya? ya na ganka haka?”
Wani irin kallo ya dinga binta dashi daga bisani ya bude baki ya soma fadin ” samha me kikeso in miki a rayuwan nan da zai sa kiga cewa nine nafi dacewa dake?” Ya tambayeta cike da tashin hankali.
” Duk da dai a lokacin nan bake kika bani wanan letter din da hanunki ba amma bakisan irin farin cikin dana shiga danaga cewa yarinyar dana jima ina so itama tana sona ba. Kinsan yanda na dinga ji kuwa a lokacin? Ya tambayeta yana dubanta. Itama kallonshi takeyi hankalinta a tashe.
“Amma sai yau aka wayi gari, yarinyar da nake mutuwar so na ganta rungume a jikin wani”. Ya fada ya soma takowa a hankali zuwa inda take tsaye.
Gaban samha ne ya fadi itama ta soma matsawa da baya don gabadaya a tsorace take da yanayinsa. ” a’a amjad wlh ba haka bane, ka tsaya kaji ba…”
Bai bari ta karasa maganar ba ya cigaba da fadin “kina tunanin banga kallon da kukeyi wa juna bane ranan a wajen funfair din physics department?Babu wanda kike gani a gabanki a ranar illa shi. Ko ta kaina bakiyi kamar bana wajen. Ina ta lura dake kawai shuru nayi bance miki komai ba”
Samha hankalinta a tashe ta soma fadin “Amjad ka tsaya ka saurareni, wlh ba haka bane”.
Wani irin tsawa ya daka mata yana fadin “kimun shiru banson naji komai daga gareki!…. “meyasa bazakiyi nazari ki fuskanci irin tarin son da nake miki bane samha! Ki bude idanunki da kyau kiga nine nan amjad wanda yafi kowa sonki a duniyar nan ba wani ba!”
Kamo hanunta yayi ya jawota da karfi zuwa inda yake sa’anan ya cigaba da fadin ” yanzu haka ba daidai nake jin kaina ba, ina cikin wani yanayi na tashin hankali hade da tsananin kishinki. Amma inaso ki san wani abu guda daya. Ke da sabah kun rigada kun kaini bango, ku bar ganina shuru shuru, don zan iya baku mamaki daga ke har shi cikin wanan makarantar “.
Samha wace hankalinta a tashe yake da yanayinsa, bata san sanda takardun da suke hanunta suka zube a kasa ba. Anya amjad dinta ne a tsaye a gabanta yake waenan maganganun? Gabadaya yanayinsa ya sauya ya canza kamani kamar bashi ba? Ta tuna ranar data fara ganinshi cikin makaranta lokacin tana aji daya, taga yana taimakawa wata yarinya wace ta fadi akan steps takardunta suka zube ya zo wucewa ya ganta ya tsuguna yana taimaka mata. Tun lokacin taji ya birgeta taji ta fara sonshi. Don tun a lokacin tana mishi kallon gentle guy, mai kirki wanda babu ruwanshi. Sai yau kuma taga ashe ba haka bane amjad dinta ya sauya daga gentle guy din data sanshi. Hankalinta a tashe ta cigaba da kallonsa.
Bangaren su khadija kuwa shiru shiru basuji duriyan samha. Khadija ce ta mike tana fadin ” wai har yanzu samha bata dawo daga library din bane? Daga zuwa ta dauko takardu?” Ta fada tana duban Amina.
“Tsaya tukuna kindai ga yanayin amjad dazu, kardai ya bi bayanta ne?” Amina ta tambayeta.
“Kuma fa haka ne. Toh kilan yabi bayanta ne yana son yaje su shirya”. Khadija ta fada mata. Shiru sukayi suna nazari kamar daga sama sukaji tsayuwar mutum a kansu. Sabah suka gani tsaye yana dubansu fuskarsa babu walwala .
“Me naji kina fadi?” Ya jefo wa Amina tambayar fuskarsa a daure.
Bangaren samha kuwa, tana kokarin gudu ta kaucewa amjad don a firgice take da yanayinsa. Kamota yayi ya hadeta da jikin bangon library sa’anan ya soma fadi muryarsa kasa kasa ” kamata yayi ki soni samha kamar yanda nima nake sonki, koh ba haka ba? Ya fada yana zaro mata ido.
Cike da tsoro ta soma girgiza masa kanta “Amjad dan Allah ka bari, wlh yanayinka na bani tsoro ba haka nasan ka ba” ta fada hawaye na gangaro mata bisa kunci.
” toh da ya kika sanni? Idan baki san komai ba, ki dinga shuru da bakinki!” Ya fada yana zaro mata jajayen idanunsa. Sake janyota jikinsa yayi ya tallafo fuskarta yana kokarin hade bakinsu wuri daya. Samha ta Kawar da kanta gefe ta soma kokarin kokuwa dashi tana rokonshi daya kyaleta. Kamar daga sama sukaji ankira sunanshi “kai Amjad!” Nan da nan Amjad ya bar abunda yake kokarin yi ya dago yana duban wanda ya kirashi. Sabah ya gani tsaye, hanuwansa rungume bisa kirjinsa fuskarsa a daure tamau babu alaman wasa.
“Idan kanaso ka aikata abu irin wanan, kamata yayi ka sami wuri inda babu jama’a. In ba haka ba zaka samu matsala da mutanenda bazasu taba amince maka daka aikata ba. Musaman mutane irina” sabah ya fada mishi.
Wani irin kallo amjad ya watsa mishi. Sabah yayi shiru yana kallon yanayinsa. Su khadija ne suka shigo suka tarar ta chakwakiyar da akeyi kowa hankalinsa a tashe. Amjad ya dunkule hanunsa ya soma takowa gadan gadan inda sabah yake tsaye. Sabah kam ko gizao baiyi ba yana tsaye yana jiransa ya karaso.Amjad yana zuwa dab da inda sabah ke tsaye ya wuce shi bai ce masa kala ba, su Khadie dake tsaye a bakin kofa suka bishi da kallo har ya fice daga library din.+
Samha na tsaye duk tabi ta firgita hawaye ne keta faman gangarowa bisa kuncinta.
Sabah ya karaso inda take tsaye yazo ya tsaya a gabanta yana kallonta daga bisani ya soma fadin ” ga abinci nan a takeaway abba ya aiko dashi na ajiye miki a cikin locker na ajinku”.
Kamar ba magana yakeyi ba don samha ko dagowa batayi ta kalle shi ba.
“Magana fa nake miki, ko baki ji ne?”. Shiru ta masa bata ce mishi komai ba, dataga kukan yana neman yaci karfinta ta kwasa a guje ta fice daga library din.
Gudu take ta faman yi bata tsaya ko ina ba sai departmental garden dinsu, taje ta tsaya a gindin wata bishiya sai faman haki takeyi saboda gudun data sha.
Su khadija suka biyo bayanta. Khadija ce a gaba amina na binta a baya sukazo suka tsaya dab da ita. Khadija ta dubi samha ta soma fadin ” kiyi hakuri samha munzo mun katse miki maganar da kukeyi keda amjad, wlh sabah ne yazo ya takura mana yace sai lallai mun fada mishi inda kike. Amma karki damu keda amjad zaku sake samun wani lokaci kuyi magana kinji”.
Samha ta katse ta tana fadin ” ni bama wanan bane Ke damuna, nama ji dadin zuwanku a wanan lokacin, don amjad na kasa gane kanshi, ya canza mun gabadaya kamar bashi ba. A lokacin kuma sai naji duk son da nake mishi a baya na nemeshi na rasa. Gabadaya naji ya sane mun a rai, banjin zan iya kasancewa tare dashi kuma, danaga sabah ya zo sai naji wani irin sanyi a raina” ta karasa maganar tana dubansu.
Amina da khadija binta da kallo kawai sukeyi, khadija wacce ranta a bace yake ta bude baki ta soma fadin “amma samha kina bani mamaki, kema kin san abunda kika fadawa amjad baki kyauta ba, ai ba haka ake soyayya ba. Idan kana tare da mutum dole kayi kishinsa, kin san yanda amjad ya dinga ji kuwa game dake da sabah? Yanzu samha kinyi daidai kenan? Abunda zaki sakawa amjad dashi kenan? Duk so da kaunar daya dinga nuna miki? Meyasa zaki mishi haka samha, ni yanzu ma gabadaya ina nadamar taimaka miki dana dingayi tun farko akan amjad din, dana san haka zakiyi masa daban sa baki ba tun farko!”
Tana gama fadin haka ta juya cikin sauri ta soma barin wajen. Amina ce ta juyo ta dinga kwada mata kira amma khadie ko juyowa batayi ba ta tafi ta barsu a wajen. Samha tana tsaye tayi shiru abubuwa duk sun mata yawa ta rasa inda zata sa kanta.
Washe gari da safe a gym amjad ne tsaye yayi zurfi cikin tunani don tun daya shigo yan team players dinsa suka rasa gane kansa don sai tsawa yake dakawa duk wanda yazo ya tunkareshi. Gabdayansu sai baya baya sukeyi dashi don basu san meke damunsa ba.
Sabah ne ya shigo cikin gym din ya hango amjad a tsaye shi kadai yayi shuru yayi zurfi cikin tunani. cike da karfin hali irin nasa ya karaso ya tsaya inda amjad yake ya soma fadin “amjad kenan, idan kanada abunda zaka fada mun gani nan na kawo kaina sai ka fada mun bawai ka tsaya kana wani ci cin magani ba idan kaga mutane”.
Amjad yayi shuru bai tanka masa ba amma Zuciyarsa sai faman tafarfasa yakeyi.
“Magana nake maka kayi shuru kana jina. Tunda samha bata nan sai ka daina wanan pretending din da kakeyi don ni na rigada nagama karantarka.”
“Me kace?” Amjad ya juyo yana dubansa.
“Cewa nayi gwanda ka ajiye wanan pret…”
Amjad bai bari ya karasa maganar ba ya kai mishi naushi a baki. Sabah yayi tangar tangar kamar zai fadi kasa amma sai ya rike kansa.
Sauran yan kwallon da suke sama suna ganin abunda ke faruwa suka sauko a guje don su rabasu.
Sabah ya mike tsaye yana murmushi gefen lips dinsa ya fashe jini ya soma gangarowa.
A tswace amjad ya soma fadin ” kana ganin zan naushe ka amma ka tsaya baka kauce ba ka tsaya kana mun dariya, meye matsalarka?!”
Sabah murmushi kawai ya cigaba dayi yace “bakomai banga daman kaucewa bane, kawai inason ganinka cikin irin wanan yanayin ne. Kafi kyau a hakan”
“Kana tunanin banida hankali ne ko meye, duk abunda kakeyi ina lura dakai, duk inda mukaje da samha kana nan biye damu ka hana mu sukuni, dabadin kai ba da har yanzu ina tare da ita”.
“Au wanan itace damuwarka? Ai nasha fada maka cewa samha tawace ko ban fada maka ba?”
Amjad a fusace ya taho ya sake kai mishi wani naushin a ciki ya tureshi ya fadi a kasa. Sabah kamar bashi amjad ya gama kaiwa naushi ba ya dago yana dubansa still fuskarsa na dauke da murmushi
“Haba amjad, ai da nazata ka fi haka karfi, ya ka tsaya?” Ya tambayeshi. Amjad zuciya ta sake debansa ya nufo shi gadan gadan zai sake kai mishi wani naushin sai ga sauran yan team din sun karaso suka ririkeshi, sabah ya tashi yana dariya yana girgiza kai yazo ya tsaya dab dashi yana fadin ” Nasan ka jima kana son ka aikata hakan, da fatan ka samu nutsuwa a zuciyarka yanzu. Nidai bazan taba baka hakuri ba don nasan ban aikata laifin komai ba gareka”. yana gama fadin haka ya dafe kafadar amjad kamar wani karamin yaro ya tafi ya barshi a wajen.
Da yamma misalin karfe biyar samha na zaune kan daya daga cikin kujerun shakatawa na garden din gidansu sabah. Ta daura kanta bisa cinyarta sai faman kuka takeyi. Kamar daga sama taji takun mutun yazo ya tsaya a gabanta. Ko bata dago ba tasan wanda yazo ya tsaya don kamshin turarensa daban yake, a duk inda taji wanan daddaden kamshin tasan nashi ne. A hankali ta dago kanta tana dubansa, fuskarta duk ta bace da hawaye. Kyawawan idanunsa ya zube cikin nata yana kallonta. Sanye yake cikin farar tshirt da bakin wando, sumar kansa ta kwanta luu luu akansa daga gani bai jima da fitowa daga wanka ba. Kallon junasu suka dingayi na kusan minti biyar daga bisani ya bude baki ya soma fadin “wai ke wace irin mutum ce? kin wani zo kin zauna anan ke kadai kina kuka?”
Samha shuru tayi tana kallonsa bata bashi ansa ba.
“Kukan meye kikeyi?” Ya sake jefo mata tambaya.
“Ba kuka nakeyi ba”.
“Karki maidani makaho mana, ba kuka na taddaki kinayi ba?”
“Na fada maka ba kuka nakeyi ba” ta fada tana turo masa dan karamin bakinta.
“Kuka kikeyi”.
“Ba kuka nakeyi ba” ta sake bashi ansa.
Shuru yayi yana dubanta daga bisani ya cigaba da fadin. ” kukan nan da kikeyi, ya danganceni ne?
A’a, wanan kuma ba matsalarka bace, matsalata ce.” Ta fada tana sunkuyar da kanta. Shuru tayi daga bisani ta cigaba da fadin ” sabah ban san yanda akayi na zama haka ba, garin na kare kaina gashi na batawa wasu na jefa su cikin wani hali. Harta kawayena ma yanzu sun juya mun baya. Na kasance mara kirki ko sabah? Ta fada tana dubanshi. Shiru kawai yayi yana dubanta.
“Meyasa zakiyi wanan tunanin? Kawayenki suna sonki mana”.
Gigiza masa kanta tayi tace “a da kenan, amma yanzu sun daina”.
“Idan suna zaune tare da ke tsakani da Allah suma zasu gano cewa ba haka kike ba, life is full of ups and downs, kuma kin san dan adam tara yake bai cika goma ba. So ki kwantar da hankalinki. Zasu sauko”.
Samha da danji sanyi a ranta game da kalamansa, sai taji damuwar nata ya dan ragu.
“Sabah kazo nan don ka kwantar mun da hanakali ne ko?” Ta fada tana dubansa.
Nan da nan kuma taga ya bata fuska ya mike yana fadin “haba sai kace banida aikin yi? Daman abba ne yace nazo na kiraki kishigo ciki ki samu kici abinci kisha magani”
Samha Murmushi kawai takeyi tana dubansa bata ce komai ba.
” murmushin me kuma kikeyi sai kace kinyi tsintuwa? Mallama ki tashi mu tafi karki bata mun lokaci. Nima nan yunwa nakeji. Abba na jiranmu”. Yana gama fadin haka ya soma kokarin barin wajen.
samha girgiza kai kawai tayi ta mike tabi bayanshi tana murmushi suka shige ciki.
Suna shiga ciki suka tadda abba na zaune kan dining an jera abincin da zasu ci yana jiran su shigo. Suna shigowa suka zauna tare suka fara cin abinci. Suna gama ci Abba ya musu sallama ya haura sama zuwa dakinsa. Shima sabah yabi bayansa ya wuce dakinsa. Samha kadai aka bari a fallon tana zaune tana kallon wani programme da ake nunawa a tv. Tayi kallon na kusan minti 30 sa’anan taji idanunta sun soma mata nauyi alamun bacci. Ta kashe tv ta mike ta haura sama. Tazo dab da inda zata shiga dakinta sai ga sabah nan ya fito daga dakinsa zai sauka kasa. Sanye yake cikin kayan bacci riga da wando pyjamas. Gabanta ya fadi ta kawar da kanta gefe. Takowa yayi har ya karaso inda take tsaye ya kura mata ido yana kallonta, ita kam ta kasa dagowa ta kalleshi ta kawar da kanta gefe ” keh meye haka kinayi abu kamar wata mara gaskiya?” Ya jefo mata tambaya.
“Babu komai” ta bashi ansa tana kokarin bude kofar ta shiga ciki. Kafa daya yasa ya rike kofar, ya ruko hanunta ya juyo da ita tana fuskantarshi.”Meye haka sabah? Ka cika mun hannu na shiga ciki.” Ta fada tana watsa mishi wani irin kallo. Kirjinta sai faman bugu yakeyi don jin lalausar hanunsa ya riko nata.
“In naki fa? Me zakiyi?” Ya jefo mata tambayar yana kallon cikin kwayar idanunta.
“Wlh sai in sa ihu a gidan nan kowa ya fito. Harta abba ma sai ya jimu dakai”.
Murmushi kawai ya sakar mata wanda yasa dimples dinsa suka bayana ” kanwata kenan. Toh bazan sakar miki hanun ba kiyi ihun muji”
“Oh haka kace? Bazaka sakar mun hannu ba?”
“Eh naki bazan sakar ba.” ya bata ansa.
“Toh wlh zan baka mamaki a gidan nan” tana gama fadin haka ta bude baki zata sa ihu yayi sauri yasa dayar hanunsa ya toshe mata baki yana girgiza mata kansa alamun karta kuskura. Saukan cizon dayaji a tafin hanunsa ne yasa yayi saurin janyewa yana yarfa hanunsa. Tana ganin ya saketa tayi sauri ta shige dakin tasa key a kofar ta kulle tana Ajiyar zuciya. Juyawa tayi ta jingina a jikin kofar. Nan take kuma taji wani irin feelings na taso mata game dashi. Lumshe idanunta tayi har lokacin tana iya hango kyakyawar fuskarsa. Ji tayi kamar ta bude kofar ta fito ko zata sake ganinsa. Amma kuma sai ta sauya tunani. Ta rasa gane meke damunta kwana biyun nan don batada wani tunani sai na sabah. Murmushi ta sake ta bude idanunta a hankali ta daga jinginan datayi a jikin kofa ta karasa cikin bayi ta dauro alwala tazo ta tadda sallah. Bayan ta idar ta bi lafiyar gado, ta kwanta cike da tunaninsa.
shikam sabah bayan shigewarta daki yayi shuru yana bin kofar da kallo daga bisani ya girgiza kai ya dauki hanyar matakala ya sauka kasa ya dauko robar ruwa ya bude ya soma sha. Daman abunda ya fito dashi kenan. Yana gama shan ruwan ya sake haurawa sama ya shige cikin dakinsa.
Washe gari da safe samha da tunanin amjad ta shiga cikin makaranta ta soma neman sa don tana ganin lokaci yayi daya kamata su warware komai dake tsakaninsu. Ana gama lectures zasu fita daga cikin aji ta tsayar dashi a lokacin dayake kokarin fita shima. Juyowa yayi yana dubanta. “Amjad idan bazaka damu ba, inason na danyi magana da kai”. Bai ce mata komai ba ya tsaya yana kallonta. Gefe taja shi don yawancin daluban da suka fito daga cikin ajin suma sun juyo suna kallonsu. Amina na ganin abunda ke shirin faruwa ta bar wurin cikin sauri taje neman khadie ta sanar da ita.
Amjad ne ya bude baki yana fadin “ina jinki, wani magana kikeso ki fada mun?”
Samha ta dago tana dubansa daga bisani ta bude baki ta soma fadin “Amjad kayi hakuri ka yafeni. Nasan ban kyautata maka ba, banida kirki kuma na tafka babbar kuskure a gareka. Shiyasa naga bai kamata mu cigaba da kasancewa tare da juna ba don idan muka cigaba a hakan, ba abunda zan dinga janyo maka ila bakin ciki.”
Amjad kamar saukar guduma yaji a kirjinsa game da kalamanta. Wani irin faduwar gaba ne yaji ya ziyarci zuciyarsa dayaji tace su rabu.
Samha bata tsaya nan ba ta cigaba da fadin ” duk abubuwan da suka dinga faruwa cikin yan kwanakin nan duk laifi nane. Amjad bazan boye maka ba a yanzu haka na kamu da son wani, akwai wanda zuciyata take so. Kuma ba wani bane ila sabah. Na waye gari na tsinci kaina da matsanancin sonsa. Kayi hakuri amjad da waenan kalamun dakaji suna fitowa daga bakina. Naga ya kamata ka sani ne, banson na yaudareka. Kuma ina maka fatan alkhair Allah ya baka wace ta fini.”
Ba amjad kadai ba hatta su khadie da suka labe a jikin kofa suna sauraransu jin maganar sukayi kamar a mafarki.
Sabah da samha?
Anya kuwa samha na cikin hayacinta take waenan maganganun? Su khadie suka tambayi kansu.
Amjad yayi shuru yana dubanta. Shi kadai yasan yanda yakeji a lokacin don maganganunta sun rigada sun gama hargitsa masa tunani. Bai ce mata kala ba a hankali ya soma kokarin barin wajen yana tafiya kamar wanda kwai ya fashe masa a ciki. Har ya kai wajen sauka daga matakala ya kirkiro murmushin karfin hali ya juyo yana dubanta sa’anan yace ” karki damu wanan ba matsala bace, saboda nima naji son naki ya fita daga cikin zuciyata”. yana gama fadin haka ya juya yayi tafiyarsa. Nan ya barta tsaya hawaye na gangaro mata bisa kuncin.
Tafiya yakeyi amma hankalinsa baya tare dashi, har wani irin jiri ne yaji ya soma debansa. Kamar daga sama yaji ana kwada masa kira. Juyowan da zaiyi yaga kawar samha Khadija a tasaye tana kallonsa cike da tausayi. Shima kallonta kawai yakeyi daga baya ya juya yayi tafiyarsa. Khadie ta dinga bin bayansa da wani irin kallo cike da matsanancin so da tausayi har ya bace mata daga gani.
Amjad yana barin department dinsu a lokacin har an soma ruwan sama mai karfi, ga iska nata faman busowa ta ko ina, bai damu ba haka ya shiga cikin ruwan tunani kala kala na masa yawo aka. yana tafiya yana tunanin abubuwan da suka dinga faruwa a da tsakaninsa da samha. Daga farkon haduwarsa da samha, da case din love letter dinta da kuma irin dadin daya dinga ji daya gano cewa tana sonshi, har lokacin daya bi bayanta tana kuka yaje ya share mata hawaye. Da kuma rungumar dayaga sabah yayi mata. Ba abunda bai dawo masa ba. Wani irin razanan kara ya sake, ya kifa guiwowinsa biyu kasa yana nadamar duk abubuwan da suka faru. Yau gashi ya rasa samha, hasken rayuwarsa, Ya zaiyi yanzu don ita kadai yake gani yaji sanyi a ransa toh gashi yanzu ya rasa ta?
Yana nan tsugune cikin ruwan kamar daga sama yaji muryan mace tana fadin “ga lema nan idan kana bukata in kuma kafison ka cigaba da tsayawa cikin ruwan ne toh. Amma Nidai ina gudun maka mura, kada ka kamu da ita.”
Dagowa yayi ya juyo yaga khadie tsaye a bayansa hanunta rike da jar lema tana dubansa. Nan take yaji zuciyarsa na tafarfasa “kinzo nan dan ki gaya mun magana ne ko me?”
“Koh kadan amjad, taya zan gayawa wanda nake tunanin yanada kyau kuma ga hankali magana?”
Maganganunta haushi suka bashi ya mike cikin zafin rai zai bar wurin ta dakatar dashi tana fadin “pls ka tsaya ka saurareni amjad”
Bai juyo ba ya bata ansa da “kinga daga rarashi, tausayi ko tsokana. Duk waenan abubuwan bana bukatan jinsu daga gareki.
“Waya fada maka abunda nazo fada maka kenan? Banzo nan da niyan rarashi ko tsokana ba amjad. Abu daya ne kawai ya kawo ni kuma shi nazo na furta maka. Amjad ina sonka” ta fada tana dubansa kirjinta na bugun uku uku.
Shuru yayi bai juyo ya ce da ita komai ba haka ta dinga bin bayansa da kallo cike da fargaba da tashin hankali.
Bayan yan mintuna ya juyo yana dubanta sa’anan ya soma fadin “taya hakan zata yu’ meyasa zaki fada tarkon son wanda yake cike da matsanacin son wata.”
Bata bashi ansa ba ta matso tazo ta tsaya dab dashi tana kallon cikin kwayar idanunsa. Kallon juna suka tsaya yi na kusan minti biyar daga bisani ta juya jikinta a sanyaye ta soma tafiya. Bai tsayar da ita ba haka ta dinga tafiya har ta bace masa daga gani. Gabadaya yama rasa yanda zai yi, gashi kawar samha tazo mishi da wata bakuwar al’amari.
Khadie tana barin wajen, wani irin dadi ta dinga ji na ratsar duk ilahirin jikinta. Yau ta samu ta furta abunda ta jima tana dawainiya dashi cikin zuciyarta. Murna ta dinga yi har da tsale. A ranar dai ba ‘acewa komai don ta kwana cike da farin ciki.
Washe gari misalin karfe hudu na yamma bayan sun gama lectures Samha ta fito daga department dinsu tana tafiya ita kadai. Kamar daga sama taji tahowar bike yazo ya tsaya dab da ita. dagowa tayi taga sabah zaune saman bike din. Sanye yake cikin kananan kaya kamar ko daya yaushe white tshirt da bakin wando.
“Kanwata, hau mu tafi” ya fada mata.
Samha ta kalli bayan bike din ta sake dawo da dubanta gareshi ” ban gane na hau ba, kallin naje na fadi naji ciwo? A’a wlh” ta fada tana kau da kanta gefe.
“Ni nace miki ki hau mun bike ne? Ai wanan mashin din tafi karfin ki. Ga daidai dake can” ya karasa maganar yana nuni da bayansa.
Su shinoh ta hango kusa da wata hadadiyar bakar SUV da akayi parking dinta a gefen hanya. Duk sun jingina da jikin motar suna kallonta.
Kafin ta sake juyowa tayi wata magana, sabah har ya tayar da bike dinsa yayi gaba abunsa.
A hankali samha ta tako zuwa inda su shinoh sukayi parking din motar, Suka bude mata kofar baya ta shiga ciki ta zauna. Suma suka shigo suka tayar da motar. Basu tsaya koh ina ba sai wata babbar shopping mall nan suka dinga mata siyaya kaya kala kala daga bisani suka wuce saloon nan ma aka mata gyaran gashi. Gidan wata mata suka karsa da ita akayi mata gyaran jiki na musaman ta saka sababin kayan da suka siyo a shopping mall din. Samha tana fitowa ta dawo kamar ba ita ba. Su shinoh da abba sake baki sukayi suna binta da kallo don gabadaya ta kara wani irin haske fatar ta sai sheki takeyi. Shi kam zack tabe baki ya dinga yi don shi bai wani zage kamar yanda su shinoh suka dinga yi ba. Bayan an gama shirya samha tsab suka koma makaranta inda suka saba shakatawa . Ba jima ba sai ga sabah nan ya shigo cikin restroom din sanye da wata hadadiyar kaftan data mishi bala’in kyau. Sai fidda kamshi yakeyi kamar wani sabon ango. Su shinoh suka fara mishi tsiya suna ce mishi ya hadu, suka ciro wayarsu zasu mishi hoto shida samha sabah ya hade rai ” haba SB ka danyi murmushi mana. Ko don kanwar taka ma bazaka danyi murmushi ba” sabah yana jinsu ya basar ya cije kamar ba dashi sukeyi ba yazo ya tsaya dab da inda samha take yana kare mata kallo don tayi mishi kyau sosai. Sanye take cikin wata hadadiyar atamfa da aka mata dinkin riga da skirt, kayan ya amshe karamin jikinta sosai. Itama shi din take faman bi da kallo don yau ya canza mata ya fita mata daban kamar bashi ba.
“Kanwata kinyi kyau”. Ya fada yana dubanta.
Murmushi ta sakar masa tace mishi “nagode”.
“Yau amminki zata dawo daga tafiyan data yi. Kuma abba yace mu shirya zamuje NEW CASTLE muyi dinner a wajen gabadayan mu”.
Samha tace mishi toh shikenan babu matsala, don itama tayi waya da ammi dazu tace mata suna gab da isowa.
Duk wanan wainar da ake toyawa basu sani ba ashe Aliyah ta labe a jikin window tana kallon duk abubuwan dake faruwa cikin restroom din. Wani irin haushin samha taji ya sake karuwa cikin zuciyarta, ta cize lebanta data hango ta kusada sabah. Nan take kishi yaci karfinta ta juya ta soma kokarin barin wurin cike da kudirin maganinta.Zuwa karfe shida na yamma abba ya kira sabah a waye, yace ya samesu a new castle, suna can shi da anty fanneh. Sabah yace mishi toh gasu nan zuwa. Nan ya sallame su shinoh shida samha suka shiga cikin mota. Ya ja suka tafi.+
New castle babban wurin shakatawa ne mai dauke da dinbin jama’a da suke zuwa da iyalensu domin shakatawa.
Musaman abba yasa akayi musu reservation na VIP wanda daga shi sai family dinsa zasu kasance a wurin. Abba da anty fanneh suna zaune suna hira, sai faman janta da wasa yakeyi kamar wani sabon saurayi da budurwa. Anty fanneh itama sai faman murmushi takeyi. Su sabbah suka shigo suka tadda su. Sabah Tabe baki yayi ganin yanda mahaifin nashi yake wani barin jiki kaman wani karamin yaro. Karasowa yayi ya gaishe su ciki ciki ya nema wuri ya zauna. Ita kam samha cike da farin ciki tazo ta rungume amminta tana mata sannu da zuwa, bayan sun gaisa ta nema wuri itama ta zauna. Nan hira ta barke tsakaninsu. Sabah bai sa musu baki ba sai wani ci cin magani yakeyi. Samha ce ta dan buge shi ta gefe tana masa alamu daya sake jiki mana ayi hira dashi, yayi kamar bai jita ba. Har abba ma yayi kokarin janshi da hira ya basar, haka suka kyaleshi.
Daga baya ne ya dan sake ya soma sa baki jifa jifa cikin maganarsu amma yanwanci maganar da yakeyi da samha yakeyinta.
Anty fanneh ta dube abba tana fadin ” kaga abu yayi kyau koh, yara sun hada kansu gaskiya naji dadi, Allah yasa ku dore a hakan. Ta karasa maganar tana dubansu. Abba yace Ameen shima ya nuna jindadinsa.
“Karki damu ammi, Insha Allah zamu cigaba da hada kanmu”. Samha ta fada mata
Sabah ne ya juyo yana kallonta fuskarsa dauke da murmushi ya soma magana kasa kasa yanda ita kadai ce zata iya jiyo maganarsa ” karki damu kanwata, ai nan gaba zamu shirya sosai fiyye da yanda kike tunani don Ke kanki ma abun sai ya baki tsoro.” Ya karasa maganan yana daga mata gira daya.
Samha kirkiro murmushin karfin hali tayi bata ce masa komai ba ila hararar data watsa mishi ta gefen ido don tasan halin shi sarai, idan ta tanka masa zai iya furta wata magana wanda bata shirya ji ba a gaban su Ammi. Haka suka cigaba da hirarsu cike da jindadi da anashuwa.
Aliya tsaye take a wajen reservation din VIP ta kura wa su sabah ido. Yanda suke hira cike da anashuwa da jindadi ba karamin kona mata rai yakeyi ba. Wayarta ta ciro daga cikin aljihu tayi saitin daidai table dinsu inda suke zaune ta daukesu hoto. Tana gama daukan hoton ta kama hanya tayi tafiyarta. Su sabah suna zaune basu ma san abunda ke faruwa ba. Haka suka cigaba da hirarsu har lokaci yayi suka tashi suka wuce gida.
Washe gari da safe su samha suna cikin lab inda ake ajiye computers zasuyi daya daga cikin courses din dasuka dauka daga computer science wanda ya zame musu core course. Lecturer din na gama yi musu bayani yace su fara practical. Suna cikin practical din amina ta tabo samha tana kokarin nuna mata abu cikin wayarta da aka turo a group din ajinsu. Samha ta matso don taga abunda take kokarin nuna mata, hotonsu ta gani ita da sabah da mahaifin sabah da kuma mahaifiyarta a cikin wayar. Daga ganin hoton kasan jiya da dare ne aka yita da sukaje new castle. Samha tana ganin hoton bata san lokacin data mike tsaye a razane ba har yan ajin suka juyo suna kallonta. Ashe ba amina ba harta sauran yan ajin sun ga hoton a group, suna kallon cikin wayarsu kuma suna kallonta suna gulma kasa kasa. Lecturer dinsu ne ya dube ta yana fadin ” keh meye haka? Idan baki shirya yin practical din ba, ki fita ki bar mun aji”.
Samha sunkuyar da kanta tayi cike da jin kunya ta bashi hakuri ta nema wuri ta zauna.
“Waye ya turo da hoton cikin group?” ta tambayi amina muryarta kasa kasa.
Amina ta bata ansa da ” naga kamar wata ta rubuto a group din wai wata Aliya ce daga mass com department ta turo.
Samha najin aliyah ce nan da nan ta mike tacewa amina tana zuwa, nan taje ta dauki excuse a wurin lecturer ta bar ajin sai hanyar mass com department. Tana zuwa 400 level class ta soma tambayar daluban ciki ko Aliyah tana nan. Sukayi mata nuni da can karshen ajin inda take zaune ta hakimce kan kujera kamar wata sarauniya. Aliya tana ganin samha fuskarta ta barke da murmushin makirci, don tasan abunda ya kawota. Mikewa tayi daga inda take zaune tazo ta tsaya dab da inda samah ke tsaye.
Samha tana ganin tazo ta tsaya a gabanta ta watsa mata harara daga bisani ta bude baki ta soma fadin ” wai meyasa kike son mun shishigi cikin rayuwata ne eh? Akan me zakiyi posting din hoton family dina zuwa group din makaranta?”
Aliyah wani irin kallo tayi mata sama da kasa sa’anan ta bata ansa da ” naga na isa ne shiyasa na aikata hakan. Kuma gani nayi lokaci yayi daya kamata ace kowa yasan meke tsakaninki da prince. Kina tunanin bansan cewa prince ya kusan zama yayanki bane? Ai Gwanda kowama ya sani a kau da wani zargin da zai taso nan gaba.
Samha shiru tayi tana kallonta tama rasa me zata ce mata. Aliya murmushin mugunta ta cigaba dayi ganin yanda samha tayi shiru ta kasa cewa komai.
Suna cikin haka sai ga zack nan ya shigo ajin kamar an jefo shi. “Aliyah, sabah yana cafetaria, yace kizo yanzu nan yana son ganinki”.
Aliyah wani dadi taji data ji ance sabah na nemanta ta sunkuyo dab da samha tana fadin ” kin dai ji ko? Prince yana bukatan ganina. Bari naje na ansa kiransa”.
Tana gama fadin haka ta gyada kai ita da zack suka tafi suka bar samha tsaye a wurin.
Koh da Aliya ta isa cafeteria ta tadda sabah zaune ciki ya hada rai kamar bai taba dariya ba. Kujera ta samu ta zauna dab dashi sai faman yauki takeyi. Shikam duk abubuwan da takeyi kara masa haushi yakeyi.
“Meyasa kika tura wanan hoton” ya jefo mata tambayar fuskarsa a daure tamau. Su khadie da amina sun shigo cafetaria zasuyi order din abinci kenan suka ga sabah da Aliyah zaune suna magana. Khadie ce ta dubi amina tana fadin “daman itace Aliyah?”
Amina ta bata ansa da “itace. Daman ita da sabah sun san juna ne?”
“Oho waya san musu. Kinga ni yunwa nakeji, muje mu karba abincin nan muci”. Khadie ta fada tana tabe baki taja hanun amina suka karasa sukayi order abincin, amma sai suka nema table dake kusa dasu sabah suka zauna don su samu su jiyo abunda shi da Aliyah suke tataunawa.
Aliyah ce ta dubi sabah cike da tashin hankali tana fadin “Meyasa kake mun wanan tambayar?”
“Tambayarki nayi meyasa kika aikata abunda kikayi” ya sake jefo bata tambayar babu alaman wasa a fuskarshi.
Cike da damuwa ta soma fadin ” prince, baka san kai sannane ne a cikin makarantar nan ba?”
“Meye kuma prince? Karki kara kirana da hakan!” Sabah ya fada mata a dan tsawace har su zack da shinoh dake zaune a dayan table din suka juyo suna kallonsu.
“Abunda kaga na aikata, na aikata shi ne domin na kare kanwarka daga maganganun mutane banson ta fada cikin matsala, shiyasa kaga na aikata hakan.” Aliyah ta karasa maganar tana dubansa fuskarta ta sauya ta rikide kamar zatayi kuka.
Sabah ya kauda kansa gefe yana fadin ” toh koma meye, ni ban yarda da wanan tsarin naki ba. Kuma ki sani duk abunda zaki fada don kare kanki maganganunki bazasu taba ni ba. I don’t care. Don wanan abunda kika aikata gabadaya ya bata mun rai.
Kwala ne suka ciko mata a ido ta sunkuyar da kanta kasa tana fadin ” kayi hakuri prince, nasan duk abubuwan danake aikatawa basu sakaka farin ciki. Amma inason ka sani ina aikatasu ne domin naga na faranta maka, amma kai baka gani. Kuma ka sani, Bazan taba daina nuna kulawata gareka ba, bazan taba daina sonka ba prince!”
Ko ina yayi tsit aka juyo ana kallonsu. Barin ma sabah daya cika yayi fum kamar zai fashe don maganganunta sun rigada sun gama kaishi bango.
Zack ne ya taso hanunsa rike da robar popcorn yazo ya zaune a table dinsu yana fakewa da dariya, ya dire robar popcorn din a gabansu yana bisimillah muci popcorn.
Aliyah da sabah ko kallonshi basuyi ba. Zack Bai damu ba ya cigaba da fadin ” yauwa Aliyah daman inata so na fada miki, mun fara buga basketball fah. Munyi joining school team din tun wancen satin daya wuce.
Aliyah bata kalleshi ba ta bashi ansa da “Na sani”. Shiru tayi bata sake cewa komai ba idanunta kyam akan sabah.
Zack yayi dariyan karfin hali ganin yanda ta basar dashi amma bai tsaya nan ba ya cigaba da fadin “Toh yaushe zaki zo kallon wasan namu?”
Aliyah ta juyo ta kalleshi ta bashi ansa da “zanzo na kalla, ai ni ce sabon team manager dinku.” Tana gama fadin haka ta dawo da dubanta ga sabah ta cigaba da fadin ” karka damu prince, tunda yanzu ni ce sabuwar team manager dinku zan cigaba da baka kulawa na musaman”
Sabah yana jin abunda ta fada, a kule ya mike daga kujerar dayake zama ya fita ya bar musu cafetaria din gabadaya. Aliyah tabi bayansa da kallo cike da tausayin kanta don Wani irin sonsa ne taji yana kara fusgar zuciyarta. Zack shima binta da kallon tausayi ya dingayi shima kaunarta da tausayinta na kara samun mazauni cikin zuciyarsa.
Samha tafiya takeyi ita kadai sai faman tunani takeyi kala kala musaman maganganun da Aliyah ta fada mata dazun. Itama tasan Aliyah nada gaskiya ta wani bangaren don babu makowa itada sabah sun kusan zama yan’uwa. Toh ya zasuyi. Musaman ita don bata san yanda zatayi da son sabah dayake kara huruwa kullum cikin zuciyarta. Kallon sama tayi taga hadari ya hadu alamun za’ayi ruwansa. A zuciyarta ta soma fadin Allah ya kawo ruwan ko zata samu ya wanke mata duk wata damuwar da take tattare dashi.
Amina da khadie ne suke tafiya a hanya suna taba hira kowanensu rike da lema saboda yayafin da aka soma yi.
Amina ce take fadin “gaskiya samha cikin yan kwanakin nan tana fuskantar abubuwa da dama cikin rayuwarta. Yanzu ya zatayi da wanan uban gurmin dayake kokarin sawo kai? Gashi wancan Aliyah na tabata ta karbi wanan aikin manager din ne don dai ta musgunawa samha. Gaskiya ya kamata mu taimakawa samha.”
Khadie ce ta bata ansa da ” toh yanzu me kike tunanin zamu iyayi akan wanan al’amarin?”
Amina tace “kawai mu leka gidansu samha. Muje mu dubata a gida daga nan sai mu tatauna da ita”.
Khadie tace toh shikenan. Suna cikin maganarsu khadie ta hango amjad ya wuce cikin sauri yana kokarin ya samu inda zai fake daga ruwan saman da akeyi.
Cikin sauri khadie ta mikawa amina lemarta tace ta rike ta fara tafiya zata biyota daga baya. Amina zata fara mata tambayoyi khadie tace mata dan Allah ta fara tafiya akwai inda zata biya ne. Amina Babu yanda ta iya haka ta karfa leman ta soma tafiya.
Khadie na ganin amina tayi nisa ta juya tabi bayan amjad cikin sauri taje ta tadda shi cikin rumfar daya fake. Juyowa yayi ya ganta tsaye kusa dashi, ta sakar masa wata tsadaddar murmushi. Shima murmushin ya sakar mata. Binshi da kallo ta dingayi Sai taga har ya murmure ya dan dawo dai dai ba kamar yanda ta ganshi ranan ba.