ZABIN SAMHA CHAPTER 5
Jikin samha ne yayi sanyi dataga yanda sabah ya karbawa Aliyah baki a wajen yan matan. Gabadaya sai taji wani iri. Tunani kala kala ne suka soma mata yawo a ka. Suna cikin haka, Amjad yazo wucewa ta gabansu, khadie na ganinshi ta kwada mishi kira daga sama. waigowa yayi ya hangota a sama tare dasu samha. Amjad yana ganin samha ya kura mata ido yana kallonta, suna hada ido yaga ta kawar da kanta gefe. Amjad ya mayar da dubansa ga khadie wace take daga mishi hannu alamun ya hauro sama ya samesu. Sabah kam yana tsaye ta gefe yana binsu da kallo har amjad ya haura sama yaje ya tadda dasu. Khadie ce ta dan turo samha gaba tace taje ta sameshi suyi magana. Samha ta rikice ta rasa yanda zatayi don a lokacin wani irin kunyar amjad takeji. Shi kanshi amjad yana tsaye ya rasa abunda zai ce mata. Su khadie da sukaga shirun yayi yawa babu mai niyar magana a tsakaninsu, khadie ta matso kusa dasu fuskarta dauke da murmushi ta soma fadin ” Dan Allah kuyiwa junanku magana ku daina wanan abunda kukeyi, haba meyasa kukeyin haka, karku manta fa haryanzu we are still friends, duk ana tare, kuma…”+
Samha bata bari ta karasa maganarta ba ta katse ta da “ai daman ban sa komai a raina ba. Kawai dai ban san me zance bane”. ta karasa maganar tana sunkuyar da kanta kasa.
Khadie tace ” kar ki sa komai a ranki, ki sake jikinki samha, kuma ki daina yi kamar kin aikata wani babbar laifi.”
Ta dawo da dubanta ga amjad ta cigaba da fadin “Kai kuma kana namiji, ai gaba ba nake bane. Abunda ya rigada ya faru, ya faru, so a manta da komai mu cigaba da kamar yanda muke a da.” ta karasa maganar tana duban amjad wanda ya kasa kallon kowa, don gabadaya sun sashi a tsakiya.
“Kaga idan ka cire komai a ranka, ba karamin kyau zaka kara bama”. Khadie ta fada tana kashe mishi ido daya.
Amjad dariya yayi ya dago yana dubanta sa’anan yace ” ai babu wata matsala, komai ya wuce insha Allah.”
Khadie ta aika masa da tsadaddar murmushinta sa’anan tace ” toh bayan haka, samha tanada wata alfarma da take so ta nema a wajenka”.
“Me kenan?”
“Tunda ka kasance kaine captain din basketball dinku, me zai hana ka mayar wa samha aikinta nada a matsayin manager”.
Amjad shiru yayi yana nazari daga bisani yace “toh shikenan babu matsala bari yaje ya tambayai yan team nashi, yaji ta bakinsu, idan sun amince toh.
Haka suka yarda da wanan tsarin suka soma saukowa kasa tare.
Daman sabah tun lokacin da amjad yaje ya same su samha, gabadaya sai ya dinga jin wani iri. Wuri ya samu a gefen gym din ya zauna yana nazari don gabadaya hankalinshi da tunaninsa na can wurinsu samha.
Yayi zurfi cikin tunani sai ga Aliyah nan ta nufo inda yake zaune hanunta rike da bottle water tazo ta tsaya kusa dashi. Kurawa kyakyawar fuskarsa ido tayi tana murmushi. Wani irin dadi takeji a ranta a duk sanda taganta a tare dashi.
“Prince, ga ruwa nan na kawo maka idan kana bukatan sha” ta fada tana aika mishi da wani irin kallo mai cike da so da sha’awa.
Sabah dagowa yayi yana kallonta sa’anan ya bata ansa da “A’a ban bukatan sha, kuma bana miki kashedi akan wanan sunan da kike kirana dashi ba?”
Aliyah ta tabe baki bata ce mishi komai ba. Suna cikin haka, sai ga amjad nan ya dawo yana fadin ” oya kowa ya matso akwai maganar da nakeso mu tattauna kuma ina bukatan kowa yasa baki ya fadi ra’ayinsa akai”.
Gabadayansu suka matso suka tsaya kusa dashi suna jiran suji mai zai fada “gamu nan captain, kayi magana muna sauraronka”.
Amjad ya dan nesa sa’anan ya soma fadin ” yauwa, ina fatan kowa ya lura da yanda wanan club namu na basketball tayi suna kuma tayi fice cikin yan’ kwanakin nan, don haka ina…..”
Khadie bata bari ya karasa maganar ba ta turo samha gaba tana fadin ” yauwa daman muna so mu sanar daku cewa basketball manager din ku wato samha zata dawo ta cigaba da aikinta kamar da, idan bazaku damu ba”. Ta karasa maganar tana bin kowa da kallo fuskarta dauke da murmushi.
Aliyah ce cikin zafin rai ta katseta da”Mene?! Ban gane basketball manager ba. Gaskiya ban yarda da wanan tsarin ba”. Ta karasa maganar tana watsa musu wani irin kallo cike da tsana.
Itama khadie hararar ta watsa mata tana fadin ” ke kuma asuwa? Ce miki akayi muna bukatar amincewarki ne ko yaya?”
Ko ina ya dau shiru aka soma kallon kallo, shi kanshi ma amjad shiru yayi ya rasa abunda zai ce .
Samha ce ta juyo ta dubi khadi ta soma magana a hankali ” a’a khadie, ba haka za’ayi ba kema kinsan duk laifina ne, ai ban fadawa kowa ba lokacin dana bar aikin manager din ba, kuma kinga hakan danayi bai dace ba”.
Cikin zafin rai khadie ta katseta da ” ya kike magana haka samha?! So kike wancar banzar taci galaba a kanki ne ko me?”
“Dukda haka khadie ni ce na fara barin aikin manager din”.
“Ni bama wanan ba, wlh Samha kina zaune wancar banzar yarinyar mai bakar zuciyar zata kwace miki sabah kina ji kina gani”.
Samha na jin maganar za’a kwace mata sabah, ta rikice. Aliyah ce ta karaso inda suke tsaye tazo ta tsaya a gaban samha tana fadin “mallama tun wuri gwanda ma ki canza tunani don a yanzu hakan da kike ganina, ni ce sabuwar manager na team dinan”.
Khadie ce ta katse ta da “toh wai tsaya ma tukuna, wani aikin manager kika iya da har kike da bakin magana. Ai mun san abunda ya kawoki nan kuma idan baki bi a hankali ba sai mu koreki anan don Samha itace asalin team manager na club dinan.” Khadie ta karasa maganar kamar zata rufeta da duka. Shiru akayi ana kallon drama dake faruwa. Hatta sabah shima shiru yayi yana kallonsu bai ce komai ba, amjad ne ya matso inda suke ya soma fadin” Khadija ai wanan maganar ta yan wasan basketball ne. Ku bar wanan maganar da kukeyi don yan team ne zasuyi deciding akan manager din”.
Yana gama fadin haka ya dawo da dubansa ga yan team dinsa da suke tsaye suna kallon abunda ke faruwa ya cigaba da fadin ” toh yanzu ku ya kuka ce? Kunga dai babu wace za’ace tafi dayar iya aikin don haka muyi voting kawai. Duk wanda yakeson samha ta cigaba da aikin manager to sai ya daga hannu, duk kuma wanda yakeson Aliyah ta zama manager din toh shima sai ya daga hanu ayi zaben?” Gabadaya yan team din suka yarda da wanan tsarin. Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci zuciyar samha barin ma Aliyah wace gabadaya hankalinta a tashe yake don tasan da wuya taci zaben don babu abun arzikin data tsinana musu tunda ta fara in banda zagi da bakar magana da take jefawa kowa.
Amjad ne yace “Toh bari mu fara da Aliyah, duk wanda yakeson Aliyah a matsayin manager toh ya daga hanu”. Ko ina ya dau shiru anan kallon kallo babu wanda ya daga hanu. Zack ne kadai ya mika hannu zai daga sai sabah ya katse su da “wayace manager daya ne kawai zata iya yin aikin? Samun mutane biyu as manager ma ai duk bata bace ba”.
Samha na jin abunda sabah ya fada, ta dan saki ajiyar zuciya. Juyowa tayi tana kallon yan team din fuskarta dauke da murmushi ta soma fadin ” nagode sosai da hadin kan da kuke badawa, insha Allah wanan karan zan zage dantse naga nayi aikina da kyau a matsayina na team manager dinku.” Tana gama fadin haka ta juyo tana duban sabah fuskarta still yana dauke da murmushi, suna hada ido taga ya dauke idanunsa yaki kallonta, nan take murmushin dake bisa fuskarta ta dauke ta sunkuyar da kanta.
Aliyah kam sai faman tafarfasa takeyi don ita a ganinta ita kadai ce tafi dacewa data zama manager din team din. Khadie kam sai faman aika mata da harara da gwallo takeyi tana mata dariya don itama taji dadin abunda sabah yace.
Bayan an gama zaben kowa ya kama harkan gabansa. Khadija ce ta fito daga cikin gym din taje ta samu karshen matakalar haurawa zuwa gym din ta zauna tana jiran fitowar amjad. Bayan mintina kadan sai gashi nan ya fito rataye da school bag yana saukowa daga saman matakalar a hankali nan ya hangota zaune ita kadai. karasowa yayi yazo ya tsaya dab da ita yana kiran sunanta. Juyowa tayi a hankali, tana ganinshi fuskarta ta barke da murmushi ta mike tana fadin ” yauwa daman ina zaman jiranka ne, akwai abunda nakeso na fada maka”
“Inajinki” ya bata ansa
“Kayi hakuri game da abunda ya faru dazun a cikin gym nasan wanan alfarma da muka tambaya yayi nauyi sosai, kuma babu yanda ka iya ne shiyasa ka amince”.
Amjad ya dan nesa sa’anan yace “karki damu nasan saboda kawarki ne kika aikata hakan, amma ina fatan nan gaba bazaki sake kawo rigimarku irin na mata zuwa basketball practice ba. Irin waenan kananan maganganun a dinga barinsu a waje kawai”.
Khadie ta gyada masa kanta sa’anan ta mayar da dubanta kasa tana fadin ” naji bazan sake ba. Toh yanzu a bar wanan maganar. Batun maganar date dinmu fa? wace rana zamu saka? Ko zamu iya fita jibi? Ta karasa maganar tana cizon lebenta na kasa don batasan wani irin fasara zaiyi wa maganarta ba. Tsoro ne ya ziyarci zuciyarta don tana tunanin karta zo ta wuce gona da iri.
Amjad shiru yayi na dan lokaci daga bisani fuskarsa ta barke da murmushi ya gyada kai yana fadin ” babu matsala jibin ma tayi, Allah ya kaimu”.
Wani irin dadi khadie taji da taji amjad ya amince da fitar nasu jibin. Cike da murna ta juya ta soma tafiya tana waigowa tana daga masa hanu har ta bace mishi daga gani. Amjad girgiza kansa yayi fuskarsa dauke da murmushi ya karasa zuwa library.
Su zack dasu shinoh zaune suke cikin game center na cikin makarantar su suna buga game sai faman musu sukeyi akan samha da Aliyah. Zack ne ya katse su da
“wlh kowa ya ajiye kudinsa ni na tabbata sabah yana son Aliyah”
sauran ne suka katse shi da “haba wace Aliyah kuma ana zaune kalau, kaima kasan da wani abu zai faru tsakanin sabah da Aliyah da tuni ya faru, shekara nawa tana ta faman bibiyansa har yanzu ta kasa gano kansa. Da dai samha kace wanan shine zan baka goyon baya amma Aliyah kam inaaaa.”
Zack kam ya dage akan cewa Aliyah ce tafi dacewa da sabah, sauran suka ki yardan masa, haka suka dinga musu tsakaninsu.
Washe gari bayan lectures da rana, su samha suna can gym suna fama, samha ce tsugune a gefen basketball court ta tattaro balls din da ake kwallo dasu tana gogewa tana jefasu cikin basket inda ake ajiyesu. Ita kam madam Aliyah babu aikin da takeyi in banda bin sabah da kallo, duk inda yayi idanunta na kanshi. Daya daga cikin team players dinne yazo ya sameta a inda take zaune ya soma fadin ” team manager, dan Allah zaki iya taimakon mu da mop? Akwai inda ruwa ya dan zube acan muna son mu goge”.
Wani irin kallo Aliyah ta watsa mishi wanda sai daya sha jinin jikinsa. In’ina ya soma yi yana fadin “ba..ba wai nace ki..yi mana mopping ba ne”.
Aliyah ce ta katse shi da ” dakata mallam, naga alama har yanzu baku fahimce abunda ya kawo ni nan ba. Nifa banzo nan da niyar muku wani aikin boyi boyi bafa, Na dauki wanan aikin ne don kawai naga na kasance tare da prince. Don haka karka sake tunkarata da wata aiki don ni ba boyi boyinku bace. Ga wace tafi dacewa da wanan aikin, ka ganta can kaje ka sameta”. Ta karasa maganar tana nuna inda samha take tsugune tana arranging balls din cikin basket.
Samha tana jin duk maganganun da takeyi, amma bata tanka mata ba tayi kamar bata jita ba ta cigaba da aikinta. wani irin abune taji ya taso mata amma tayi kokari ta dane. Team player dinne ya karaso inda samha take tsugune yace dan Allah ta taimakesu da mop da za’a goge ruwan daya zube. Samha tace mishi babu matsala ta mike taje can store room taje ta dauko mop din ta kawo, player din zai karba a hanunta tace mishi karya damu, yaje ya cigaba da practice dinshi zata goge. Haka ya mata godiya ya bar wurin.
Samha ta sa mop din ta soma goge ruwan, Aliyah na zaune a can gefe kusa da sabah sai faman yiwa samha dariya takeyi. Sabah kam a zaune yake yayi shiru yayi zurfin tunani, gabadaya yanayinshi a ranar dai sai a hankali don tunda ya shigo baiyi wa kowa magana ba.wuri kawai ya samu ya zauna shi kadai yanata faman tunani.
Bayan yan mintuna kadan ya mike daga inda yake zaune ya tako a hankali yazo ya dauko ball ya soma bugawa shi kadai. A lokacin samha ta gaman mopping, ta samu wuri ta zauna tayi tagumi tana kallon yanda sabah yake buga kwallon yana jefata cikin ragar cike da kwarewa. Itama Aliyah sai faman binshi da kallo takeyi kamar zata hadiye shi. Don ita Aliyah bata jin kunya ko shakkar kowa, nunawa takeyi kuma a gaban kowa cewa tana son sabah.
Samha na juyowa taga irin kallon da Aliyah take ta faman bin sabah dashi, wani irin tukukin bakin ciki taji ya soma taso mata. Taja tsaki tana zagin Aliyah can kasar ranta.
Tunani kala kala suka dinga yi wa samha yawo a ka. Tana cikin wanan tunanin taji muryar sabah ya kira sunanta “samha, kawo mun towel”. Kamar daga sama taji maganar nasa, ta juyo taga Aliyah wace tayi kicin kicin da fuska jin sabah ya kira samha ta kawo mishi towel ba ita ba.
Da kallo na kisa da tuni samha ta hankada lahira don wani irin banzar kallo Aliyah ta dinga watsa mata.
Samha ta mike daga inda take tsugune jiki babu kwari don gabadaya jikinta ya rigada ya gama yin sanyi. Wani tunanin ne yazo mata nan ta kudiri niyan bazata bari Aliyah ta samu nasaran kwace mata sabah ba kuma dole tayi accepting din soyayyar dake tsakaninta da sabah.
Wanan tunanin ne ya bata karfin gwuiwa, zuwa tayi ta dauko towel din fuskarta dauke da murmushi ta soma takowa a hankali har tazo ta tsaya a gaban sabah ta mika mishi towel din.
Sabah murmushi ya sake ya karba towel din sa’anan yace ” kanwata yau babu rigima kenan, an sauko ana bada hadin kai”
Samha murmushi ta sakar masa tana binsa da kallo cike da so da kauna, ita kadai tasan yanda take jinsa a cikin zuciyarta.
Bayan an gama practice, Samha ta fito daga cikin gym din zata sauka kasa, kamar daga sama taji murya Aliyah na fadin “keh dinan naga alama kinada taurin kai har yanzu kin kasa sanin matsayinki, bayan duk kashedin dana dinga miki.”
Samha ce ta juyo tana dubanta daga bisani ta bude baki tace “Amma wlh ke dinan kinada katuwar matsala, wai me na miki a rayuwar nan da zaki saka ni a gaba haka?”
“Ni din ce keda katuwar matsala? Tukuna, Ai baki ga komai ba, indai akan prince ne babu abunda bazan aikata ba, so tun wuri ina kara miki kashedi, idan kina son kanki sa zaman lafiya ki fita daga harkarsa kuma ki tsaya a matsayinki na kanwarsa”. Ta bata ansa kai tsaye.
Samha ce ta dan nesa sa’anan ta cigaba da fadin ” nikam ban ma san mezan ce miki ba amma ina son ki san wani abu guda daya, kinga wanan kiyayyar da kike nuna mun bashi zai sa na daina son sabah ba”
Wani irin dariya Aliyah ta sake tana duban samha sa’anan tace ” Har kin bani dariya amma idan baki manta ba nasha fada miki ke dinan abar wasa ce wurin prince, idan ya gaji zai rabu dake ne don banga abunda zai saka shi ya so yarinya kucaka irinki ba, me zai ci dake”
Cike da jin haushi samha tace ” Ban gane ba. Me kike nufi”.
Aliyah ta bata ansa da ” Bakisan cewa komai wuya komin runtsi prince yana tare dani ba. Sa ido kiyi kallo saboda a karshe ni dinan da kike gani ni zai zaba”. Aliyah ta karasa maganar tana aika mata da wani irin shu’umin murmushi, tana gama fadin haka, ta kada kai tayi gaba ta bar samha tsaye a wurin.
Aliyah bata yi nisa ba, samha na tsaye tana bin bayanta da kallo cike da takaicin kalamanta. Kamar daga sama taga wasu yan mata sun bullo from nowhere sun sha gaban Aliyah. Daya daga cikinsu ce ta daga hannu ta wanke Aliyah da wata irin wawan mari tana fadin ” keh jahilar banza jahilar wofi, yau Allah ya kamaki, sai munyi maganani wanan shegiyar bakin naki da kike yiwa mutane tsiwa dashi, daman mun jima muna timing dinki cikin makarantar nan, yau dubun ki ya cika”
Daya daga cikin yan matan ne ta kamo kan Aliyah ta hade da jikin bango, wani irin jiri ne ya dibi Aliyah ta fadi a kasa, nan da nan yan matan suka rufu a kanta, naushi da duka suke ta sakar mata ta ko ina, tana ihu.
Samha ganin abunda ke faruwa tazo a guje tana kokarin ta kwace Aliyah daga dukan da yan’ matan ke mata.
Daya daga cikin yan’ matan ta ture samha gefe tana fadin “keh mallama ki kauce mana a nan ki bamu wuri don ba dake muke ba”
Samha dataga da gaske suke kuma bazata iya kwatar Aliyah ba, yasa ta kwasa a guje ta bar wurin ta koma cikin gym don ta kira su sabah. Bata tsaya ko’ina ba sai inda ta barsu kafin ta fito, nan ta ganshi tsaye tare da zack suna magana. A guje ta karasa gabansu tana haki tana fadin “sabah kuzo ku ceci Aliyah, ga wasu yan’mata a waje sun kamata da duka”.
Sabah yana jin wasu yan’mata sun kama Aliyah da duka bai tsaya yaji sauran maganganunta ba ya kwasa a guje yayi hanyar fita daga cikin gym din. Gudu yakeyi zack na biye dashi a baya. Itama samha bin bayansu tayi tana gudu. Basu tsaya ko’ina ba sai wajen gym din, nan ya hango inda yan’matan suka rufu akan Aliyah sai faman bugunta sukeyi.
“Kai me kukeyi haka, bazaku kyaleta ba, idan na karaso wurin nan sai na babalaku yasin”. Yan’matan najin muryarsa suka dago nan suka hangoshi ya nufo su gadan gadan. Haba nan da nan suka bar abunda sukeyi, cikin sauri suka kwasa a guje suka bar wajen.
Sabah ne yabi bayansu yana kirarin cewa idan ya sake ganinsu kusa da ita sai ya kashe su. Basu waigo ba suka karawa gudunsu wuta.
Aliyah wace tasha duka ga bakinta da goshinta duk sun farfashe, jini sai faman zuba yakeyi a fuskarta, ga kafarta daya data rike yana mata radadi, hawaye sai faman gangarowa suke bisa kuncinta. Cikin sauri Sabah ya karaso inda take zaune a kasa ya durkusa a gabanta yana fadin” Aliyah meya faru?” Ya jefo mata tambayar fuskarsa cike da damuwa.
Samha tana tsaye tana kallonsu, yanda taga Sabah ya rikice yana tambayar Aliyah abunda ya faru cike da damuwa yasa duk taji wani iri.
Nan take maganganun Aliyah suka soma dawo mata, inda take fadin ” Bakisan cewa komai wuya komin runtsi prince yana tare dani ba. Sa ido kiyi kallo saboda a karshe ni dinan da kike gani ni zai zaba”.
Wani irin kishi ne Samha taji ya taso mata.Tana tsaye tana kallo taga Aliyah ta dago tana duban sabah sa’anan ta bude baki ta soma fadin “prince, you’re my hero. Kai kazo ka ceceni. Nagode sosai my prince”
Aliyah na gama fadin haka tasa hannunta biyu ta zagaye wuyan sabah dashi ta rungumoshi gam a jikinta.
Wani irin bugawa kirjin samha yayi, shi kanshi zack dake tsaye kusa da ita, shima bude baki yayi yana kallon abunda ke faruwa a gabansu cike da mamaki da tashin hankali.
“Mezan gani haka?” Samha ta tambayi kanta don ganin abun takeyi kamar a mafarki.
Gani tayi Aliyah ta sake matso sabah kusa da ita hawaye na gangaro mata bisa kuncin ta cigaba da fadin “prince karka tafi ka barni, wlh tsoro nakeji”
Sabah ne ya bata ansa da ” ai keh kike jawo ira iren haka na faruwa dake, kiyita zagin mutane, ai ga irinta nan. Gashi yanzu sunzo daukan fansa. Daga yanzu kar ki sake kinji ko”.
Kai kawai ta gyada masa tana kara matso shi jikinta. Samha wani irin rawa jikinta ya soma yi ganin abunda ke faruwa. Ta rasa ma abunda ce. Gani tayi sabah ya mike ya ruko hanun Aliyah yana fadin “taso muje ai kaiki asibiti sai a duba ki”.
Aliyah ta taso tana kokarin mikewa, wata yar kara ta sake ta sake komawa kasa ta zauna tana girgiza kanta alamun bazata iya ba.
“Meye haka kuma?” Sabah ya tambayeta.
“Wlh prince kafata, bazan iya takawa ba. Wayo Allah kafata” ta karasa maganar tana rike kafarta.
Sabah ne ya dubi zack yace mishi “kasan me za’ayi yanzu? ka tayani diban takarduna da jakana ka kaimun gida, bari na kaita asibiti.”
Yana gama fadin haka sukaga ya sunkuto Aliyah a hanunsa ya dagota kamar wata yar baby Ya soma tafiya da ita, har ya danyi nisa sai kuma ya tsaya ya juyo yaga samha a tsaye tana binsu da kallon takaici.
Bude baki yayi ya soma fada mata “kina iya tafiya gida, ni zan wuce asibiti da ita” yana gama fadin haka ya juya ya cigaba da tafiyarsa.
Aliyah wace take hanunsa, juyowa tayi tana duban samha,wani irin shu’umin murmushi mai cike da makirici ta aika mata, daga bisani ta juya ta kwantar da kanta bisa kafadar sabah.
Samha tana tsaye tana kallonsu har suka bace mata daga gani. Kwalla ne suka ciko mata idanu. Wani irin zafi taji kirjinta nayi mata ta soma fadin a zuciyarta. “Daman jikina yana bani cewa a duk sanda Aliyah take tare da sabah, sai na dinga ganin wasu halaye na daban a tattare dashi. Toh gashi zargina ya zama gaskiya”. Da wanan tunanin Jikinta a sanyaye ta juya ta soma barin wurin.
Sabah kuwa kai tsaye school clinic din ya kai Aliyah, wata nurse ya tadda, ta karbi Aliyah ta soma duba mata raunin data ji. Sabah yana tsaye yana kallon yanda ake gyara mata ciwon, nurse din na gama gyara mata ciwon ta dauka bandage ta mana mata, kafarta ma data soma kumburi inda taji ciwo nan ma ta saka mata bandage daga bisani ta dauko maganin ciwon jiki ta bata tasha ta fita waje. Sabah ne ya dubi Aliyah yana fadin “toh Allah yasa abun ya tsaya a hakan baki ji ciwo sosai ba, idan kin isa gida ki samu kankara kina manawa a goshinki, kumburin zai lafa”.
Duk maganan nan da yakeyi Aliyah binsa da kallo kawai takeyi cike da so da kaunarsa. Wani irin sonsa ne taji yana karuwa cikin ranta, gani takeyi bazata iya rayuwa babu shi ba.
Bude baki tayi ta soma fadin “prince kanada kirki sosai, indai kaga mutum yana cikin damuwa sai ka tsaya ka taimaka masa.”
Shiru sabah yayi yana kallonta bai ce komai ba. Aliyah ta cigaba da fadin ” ka tuna lokacin da muna yara a secondary school da kake nuna mun kulawa sosai, baka son ka gani cikin damuwa? A lokacin kanada zafi sosai, duk wanda yasha gabanka baka raga masa amma indai kagani cikin matsala sai kazo ka taimakamun”. Ta karasa maganarta tana kallonsa cike da matsanancin so da kauna.
Sabah still shiru yayi bai ce mata kala ba.
**************************
Bangarensu Samha kuwa, tafiya takeyi ita kadai kamar wace kwai ya fashe mata a ciki, gabadaya jikinta yayi sanyi. Wuri ta samu ta zauna a Saman matakalar gym din ta zabga uban tagumi, Tunani kala kala na mata yawo a ka. Kamar daga sama taji takun mutum a bayanta. Tana juyawa taga zack yana tahowa shima jikinsa a sanyaye. Wuri ya samu ya zauna kusa da ita. Shiru ne ya ziyarce su daga bisani ya bude baki ya soma fadin ” A da can baya lokacin da muke sec sch, Aliyah tana yawan fadawa tarkon mutane kuma ana yawan cin zalinta sosai. Aliyah kwata kwata bata son jama’a batada aikin yi sai zagin yan’ matan ajinmu, sai tayi ta musu tsiwa da rashin kunya. Su kuma ba kyalewa sukeyi ba, sai su kamata suyimata dan banzan duka. Kuma wanan dukan da kikaga tasha yau, ba shine na farko ba, don ira iren haka sun jima suna faruwa da ita”
Samha shiru tayi tana sauraronsa bata ce komai ba.
Zack ne ya dan nesa sa’anan ya cigaba da fadin ” A duk lokacin da hakan ta faru, toh Sabah zakiga yayi iya kokarin sa yaga ya kareta, don haka a idanun Aliyah tamkar prince take ganinsa mai cetonta a duk lokacin data fada cikin matsala. Ni kaina dukda ina namiji, ina son sabah sosai. Da zan samu na zama kamanshi dana more”
Samha shiru tayi daga bisani ta bude baki tana fadin “Na fahimci komai zack, kuma nasan yanda Aliyah take ji game da sabah. Amma bari na tambayeka, kana son Aliyah?”
Zack yayi shiru na yan sekoni daga bisani ya bude baki yace ” nidai farin cikinta kawai nake bukata, Indai Aliyah tana cikin farin ciki toh banida sauran wata damuwa.”
Samha shiru tayi tana nazarin kalamansa, yamma ne taga ya soma yi ta duba agogo taga karfe biyar na yamma har ta gota. Tace ma zack zata wuce gida, sukayi sallama ta tafi. Tana tafiya akan hanya ma bata cikin hayacinta don gabadaya abunda ya faru da kuma tinanin sabah ne ya cika mata kai.
Koh data isa gida ma bata tadda ammi ba, ta haura sama zuwa dakinta ta ajiye jakar makarantar ta. Yunwa ne taji ya tasomata don rabonta da abinci tun safe. Bayan ta shiga bayi ta watsa ruwa, ta sauko kasa ta shiga kitchen domin samun abunda zata ci. Gani tayi ba dafa komai ba. ta bude cupboard ta ciro indomie leda biyu ta kunna gas ta daura a wuta. Ciro kayan miyan tayi daga fridge ta soma yanke yanke. Tana gamawa ta juye kayan miyan cikin tukunyar indomie ta soma juyawa a hankali. Allah Allah takeyi abincin yayi don wani irin azababen yunwa ne ke cinta.
Tana cikin juya indomie kamar daga sama taji ana fadin ” ya nake jin kamshi kamar na indomie? Kar dai ki cika mata ruwa don ni bana cin indomie da aka cika mata ruwa”.
A firgice ta juyo tana duban mai maganar, Sabah ta gani tsaye yana dubanta. Yau kam ya canza shigar da yakeyi na bakaken kaya. Sanye yake cikin t shirt mai ratsin white and blue sai kuma black jeans. Kayan sun masa kyau sosai. Ga sumar kansa data sha gyara, har wani irin shekki take fidawa, baki wuluk dasu sun kwanta bisa kansa.
Wani irin murmushi wace ta bayanar da ainin kyaun halittar fuskarsa ya sakar mata.
Ita kam hada fuska tayi ta kawar da kanta gefe.
Me kazo yi a gidan nan?” Ta tambayeshi ko kalonshi batayi ba, don har yanzu tana cike da jin haushinsa.+
“Abba baya nan yayi tafiya. Nazo cin abincin dare”.
” kazo cin abincin dare? Wai tsaya ma tukuna, ya akayi ka shigo cikin gidan nan kai tsaye?” Ta tambayeshi.
“Mai gadi ya bude mun gate, kuma nazo naga kofar parlour a bude shiyasa na shigo kai tsayen”.
“Kuma hanunka na maka ciwo baka iya kwankwasa kofa azo a bude maka ba” Ta karasa maganar tana harararsa.
Shima hararar ya watsa mata ya juya zai bar kitchen din, tazo tasha gabansa tana fadin ” ina kuma zaka? Ai Ammi bata gida, bata dawo daga aiki ba. kuma babu abincin da aka dafa a gidan nan, shiyasa na daura indomie. Idan zaka iya jiran indomie toh sai ka jira. Yanzu zata nuna”.
“Oho dai, koma meye kika dafa zan ci, nidai na gaya miki kar ki cika mata ruwa, don bazan iya cin jagwalgwalo ba. Zan shiga parlor na kalla Tv. Idan ya nuna sai ki sanar dani.” Yana gama fadin haka ya gyada kai yayi hanyar fita daga kitchen din.
Samha takaici ne ya ishe ta, tabi bayansa da ihun tana fadin ” wai bazaka daina yi kamar nan ne gidan ku ba”.
Bai juyo ya kalle ta ba ya bata ansa da “ki dai ji da abunda kike dafawa, karki cika ni da surutu.” Yana gama fadin haka ya fice daga kitchen din.
Wuri ya samu ya zauna akan daya daga cikin three seater’s din kujerun parlourn, ya daura kafarsa daya kan daya yana kadawa a hankali, yana kallon programme din da ake nunawa a Tv.
Samha ce ta leko ta hango shi zaune yana kallon tv hankalinsa kwance, kamar bashida wata matsala. Harara ta galla masa tana fadi can kasan ranta ” Dubeshi yanda ya zauna yana kada kafafu kamar babu abunda ya faru dazu. Wato bai ma damu da halin danake ciki ba” tsaki taja ta cigaba da aikinta.
Bafi minti biyar ba, Samha ta gama dafa indomie ta juye a kwanu guda biyu, ta kwaso tazo ta jera akan dining.
Karasowa cikin parlourn tayi ta sanar dashi cewa abincin ya nuna, ta juya ta koma wurin dining ta nema wuri ta zauna. Mikewa yayi shima ya zo ya nema wuri ya zauna. Har ya dauki cokali zai fara cin abincin, samha ta katse shi da ” ka bari abincin ya dan huce mana, kaga akwai zafi”.
Harara ya galla mata yana fadin ” Meye haka kuma kina abu saikace ke kika ajiyeni. Kefa kanwata ce bafa uwata ba”
Yana karasa maganarsa ya dauki cokalin ya soma cin abincinsa.
Samha ajiyar zuciya ta sake ta dauko cokali itama ta soma cin abincin. Shiru ne ya ziyarcesu, kowane da abunda ya damesa. Shi kam sabah ko ajikinsa sai faman cin abincin dake gabansa yake.
Samha kallonshi tayi sa’anan ta bude baki ta soma tambayarsa ” ya jikin Aliyan?”
Sabah ya juyo ya dubeta ya bata ansa da ” Zata rayu tunda goshin tane ya dan fashe da bakinta sai kuma kafarta data dan goce, munje nurse ta dubata so karki damu bazata mutu ba”.
“Amma sabah, Aliyah tana yawan cin duka sosai, Wanan ba shine karo na farko da hakan yake faruwa da ita ba ko?”
“Ah lallai zack ya iya zuba, wani sa’in ban san meyasa yakeda surutu haka ba”.
Samha shiru tayi daga bisani tace ” yace idan kaga Aliyah cikin matsala sai inda karfin ka ya kare don baka son kaganta cikin damuwa”.
Sabah har ya kai abinci bakinsa sai kuma ya dakata dajin kalamanta. Shiru yayi yana nazari daga bisani ya soma fadin ” A duk lokacin danaga Aliyah tana cikin damuwa koh makamanci haka, hankalina tashi yakeyi. A da lokacin muna kanana, Aliyah tamkar ni take, bata son mutane kwata kwata, kuma bata bari wani yazo kusa da ita, kuma abun sai yazo ya hade mata da rashin kunya, wanan rashin kunyar shine yake yawan janyo mata take samun matsala da mutane.”
“Kai kuma bazaka iya kyalewa ba, sai ka taimaka mata”. Samha ta karasa maganar tana kawar da kanta gefe.
Sabah kallonta yayi fuskarsa dauke da murmushi sa’anan yace ” Toh menene a ciki dan na taimaka mata? Ko dai kishi kikeyi ne kanwata? Ya tambayeta yana daga mata gira daya.
Samha ta dan rikice ta marairace fuska don batayi tsamanin zai tambayeta ko tana kishi bane. ” kishi kuma? Kishin me zanyi da ita. Babu wani kishin da nakeji”.
Gani tayi ya matso kusa da ita, fuskarsa dab da nata yana kallon cikin kwayar idanunta.
“Meye haka kuma?” Ta tambayeshi.
“Kince babu wani kishin da kikeji, so nake na tabbatar da hakan”. Ya bata ansa yana karewa fuskarta kallo.
Samha wace ta rasa abunyi, Tray din dake gefen dining din ta janyo ta buga mishi a kai tana fadin ” ka rabu dani nace maka babu wani kishin da nakeji”.
Cikin sauri Sabah ya mike daga inda yake zaune yana shafan inda ta buga mishi kai yana fadin ” meye haka! kasheni kikeso kiyi da zaki buga mun wanan karfen a ka?”.
“An buga maka tray din, me zakayi akai”. Ta karasa maganar tana kokarin barin wurin dining din ta haura sama. Har ta haura saman sai kuma ta Sake saukowa ta laiko dining din inda yake tsaye yana shafan kansa, ta watso mishi gwalo da harara ta sake komawa.
“Tababiya kawai” Sabah ya fada yana kara shafo inda ta buga mishi kai.
Samha tana shiga daki ta samu gefen gadonta ta zauna. Tray din dake hanunta ta samu ta soma bugawa teddy din ke gadonta kirjinta sai faman bugu yakeyi. Takaici ne ya isheta ta rasa abunda zatayi, babu abunda ke mata yawo aka illa kalamunsa inda yake cewa tana kishi.
Babu shiri ta dauko wayarta ta fara neman layin khady. Bugu daya khady ta daga tana tambayarta lafiya? Nan samha ta zaiyane mata komai tana fadin “wallahi khady na rasa yanda zanyi, na rasa gane kan sabah, sai ya dinga abubuwa kamar bai damu dani ba, gashi ni kuma nan danan yake dago ni”.
Khady tace “ki kwantar da hankalinki Samha, kawai kina wanan tunanin ne don har yanzu baki tabbatar da ko yana sonki bane, so yanzu me zai hana kije ki sameshi ki tambayeshi yanda yakeji game dake?”
“Gaskiya bazan iya ba, ta ina ma zan fara? Kinsan halinshi sarai, yanzun nan sai ya sake mun gwuiwa.”
“Keh kinji ki samha, ga maganin matsalar ki amma kince bazaki iya ba, kawai rufe ido zakiyi ki tambayeshi. Kina jina ko, yanzu ina ‘dan yin wani aiki ne, kije ku tattauna, duk yanada kukayi sai ki kirani ki sanar dani”.
A haka suka yi sallama, samha ta katse waya. Wani irin tagumi ta zabga tana tunanin yanda zata tunkari Sabah da wanan maganar. Idan ta tambayeshi bai bata ansar da take so ba fa? Ya zatayi?”
Nan take kuma wata zuciyar ta ce ta je ta sameshi ta tambayeshi. Mikewa tayi ta sauko kasa, tana isa dining ta tadda babu kowa, babu alamunsa. Sai kwanukan daya ci abinci, dube dube ta farayi nan ma bata ganshi ba, wata yar karamar takarda ta hango kasan plate din daya ci abinci dashi.
Karasowa tayi ta zaro takardar ta fara karanta abunda aka rubuta a ciki kamar haka ” wanan jikakken indomie da kika kawo mun, na dai ci ne kawai don yunwa amma ban taba cin indomie mara dadi irinta ba, amma still danake ci sai na tsinci kaina cike da tarin farin ciki. Ni dai na wuce gida, Ki kula da kanki”.
Samha tayi shiru tana nazarin kalamansa. Wato yana nufin na saka shi farin ciki kenan?” Ta tambayi kanta zuciyarta na mata wani irin sanyi. Nan take farin ciki ya lulubeta.
“Amma Aliyah fa? Tana saka shi farin ciki?” Samha ta tambayi kanta. Haka tayi shiru tana tunani, ganin bazata samu ansa datayi wa kanta ba yasa ta haura sama zuwa dakinta.
Washe gari da safe a school, khady ce take saukowa daga saman matakala cikin sauri, sanya take cikin wata hadadiyar gown mai ratsen jan flowers, tayi kyau sosai. Amina ce ke biya da ita cikin sauri tana kwada mata kira, cikin sauri khady ta juyo tana dubanta, Amina tace “khady ina zaki kuma, kin manta test din Proff da zamu rubuta jibi, kizo muje library mu danyi karatu mana”.
Khady ta girgiza mata kai tana fadin ” Gaskiya sai dai ki fara tafiya don ni yanzu banida lokaci. Bye” tana karasa maganar ta juya ta bar Amina tsaye, wace taketa faman binta da kallon mamaki don Gabadaya ta rasa gane kan kawayen nata. Tunda aka gama lectures din safe bata sake ganin Samha ba, Ga khady ma yanzu tayi takanta. Cike da sanyi jiki Amina ta soma saukowa daga saman matakalan.
Khady har tayi nisa da tafiya, ko me ta tuna sai ta sake dawowa cikin sauri tazo ta tadda Amina tana fadin “Yauwa Amina daman wanan powder da kika bani nayi amfani da ita ranar nake bukata ki ara mun, powder tayi mun kyau sosai”.
Babu musu Amina ta bude jakarta ta ciro powdern ta mika mata, cike da zumudi Khady ta karba powder din tana mata godiya ta sake tafiya ta barta tsaye a wurin.
Bangaren Samha kuwa, tafiya takeyi ita kadai tana saukowa daga saman matakala a hankali. Kamar daga sama taji muryan wasu yan’ mata sunzo wucewa suna magana tsakanin su, jin sun ambato sunan Aliyah yasa ta mayar da hankalinta kan hirar da sukeyi. Daya daga cikinsu ne take fadin “Amma baku tunanin cewa wanan yarinyar Aliyah wata irin mutum ce? Ni fa har yanzu mamakinta nakeyi datazo ta bamu kudi tace mu mata wanan dukan. Anya kanta daya kuwa, wani riba zata ci da wanan dukan datasa mukayi mata?”
Daya daga cikinsu ce ta bata ansa da ” ke ku kyaleta, irin waenan mutanen mugun karfin hali ne dasu. Toh yanzu meye namu? mudai bata biya mu ba?, idan taga dama tayi hiring hirekillers su kashe ta wanan damuwarta”.
“Keh ku rabu da ita mu manta da zancenta muje muyi abunda zai fishe mu”
Haka yan’matan suka karasa suna ta hirarsu.
Wani irin dammm Samha taji kirjinta yayi, tsayawa curuss tayi tana nazarin maganganun yan’matan. Anya abunda kunanta suka jiyo mata gaskiya ne? Aliyah ta biya yan’matan kudi suyi mata duka don kawai ta janyo hankalin Sabah gareta? Anya kuwa?”
Wata zuciyar da bata ansa da “zata iya mana, badai Aliyah bace? Abunda yafi hakan ma zata aikata”.
Wani irin haushi ne ya turnuke zuciyar Samha, cikin sauri ta karasa saukowa daga saman matakalan tayi hanyar waje, straight department dinsu Aliyah ta wuce ta duba aji bata ganta ba. Ta tambayi daya daga cikin yan’ ajin ya sanar da ita cewa Aliyah tana library. Cikin sauri Samha ta karasa library din, tana shiga ciki daidai wurin bookshelf’s ta hango ta tsaye tare da Zack yana kokarin kwashe takardunsu. Samha ranta a bace ta karaso ta tadda su.
Zack yana ganin Samha ya bar abunda yakeyi ya tsaya yana kallonta. Samha ta dube shi tace “Zack dan Allah zaka iya bamu wuri? Inaso nayi wata yar’magana da Aliyah.”
Zack yaje babu komai haka ya fita ya basu wuri. Samha ta juyo tana fuskantar Aliyah wace take kallonta fuskarta a daure ” me kuma ya kawo ki nan? Kinga ni banson wata damuwa, har yanzu ban gama warkewa ba don haka kar kizo ki kara mun zafi, ki barni naji da abunda yake damuna”.
Wani irin kallo Samha ta watsa mata daga bisani ta bude baki ta soma fadin ” wato Aliyah daman kinsa waenan matan suzo su miki duka ne? Akan meye zaki aikata hakan”.
Aliyah ta zaro ido amma nan danan ta dake ta kikiro murmushi a fuskarta tana fadin “Wow da kyau, an gano ni kenan, toh suwaye suka fallasani haka?” Ta karasa maganar tana daga mata gira daya.
Samha cike da baccin rai ta cigaba da fadin “Tambayar ki nakeyi meyasa zaki aikata hakan, kisa a miki duka a jimiki ciwo har da targade? Wani irin tunani ne gareki? Kinsan irin damuwar da kika saka Sabah ciki kuwa? Harda zack, duk gabadaya kin jefa su cikin damuwa amma ke ko ajikinki”.
Aliyah ce ta dakatar da ita tana fadin ” ki saurareni kiji da kyau, kina ganin na dinan? Babu abunda bazanyi ba indai akan Sabah ne, zan iya yin komai ke hatta nakasa, rauni ba abunda bazanyi wa kaina ba, in har zan kasance ina acikin zuciyarsa .”
Samha cike da tsoro da tashin hankali take kallonta da jin kalamanta don abun nata ya soma wuce ji da tunanin dan Adam
Bangaren su Sabah kuwa, sun shigo cikin gym shida su shinoh da sauran yan’ team suna dan motsa jiki da exercise kafun su fara practice. Amjad ne ya shigo, rataye da school bag a bayansa, sanye yake cikin jar sweater da bakin wando, sumar kansa tasha gyara sai shekki da daukar ido takeyi. Karasowa yayi yazo ya tadda su Sabah yana fadin “yau kam zan barku da wuri, zakuyi practice banda ni”.
Bayan ya karasa maganar ya juyo yana duban Sabah sa’anan ya cigaba da fadin
“Sabah please tunda kaine team leader, sai ka sa ido sosai akan practice din. Ni sai na dawo”.
Sabah ya gyada kai sa’anan ya bashi ansa da “Babu matsala, amma ace Captain guda yana fashin practice, me kenan akayi?”
Amjad shiru yayi ya ma rasa ansar da zai bashi ya juyo yana duban sauran yan’ team din yana fadin ” me ma nake cewa? Yauwa, kar ku manta in case ban dawo da wuri ba, idan kun gama practice ku tabbatar kun rufe windows da kofofin gym din, wai tsaya ma tukuna ina managers din suke, ban ji duriyarsu ba?” Ya karasa maganar yana dubansu.
Zack ne ya bude baki ya bashi ansa da ” sun dan fita tare ne, amma sunce yanzu zasu dawo”.
Sabah ne ya dago yana dubanshi jin yace sun fita tare, tunani kala kala ne suka soma masa yawo a ka. Amjad bai damu ba yace ” Toh shikenan babu matsala, ni zan wuce yanzu. Ku kula please”. Yana karasa maganar ya juya ya bar wurin.
Bangaren su Samha kuwa tsaye suke suna fuskantar junansu, kowace cike take da jin haushin yar’uwarta. Samha ce ta bude baki ta cigaba da fadin “Amma Aliyah bakida kirki, saboda kinga Sabah yanada tausayi shiyasa kike amfani da wanan damar?”
“Toh wai ni meye naki ne a ciki? Kinzo kin wani tsareni da tambayoyi, kawai dai kina kishi ne don kinga ni yake nunawa kulawa bake ba, yanzu dai kin gane cewa ni ce cikin zuciyar Sabah ba ke ba ko?”
Samha shiru tayi tana kallonta da dara daran idanunta, bata ce mata komai ba.
Wani irin haushi taji yana tasomata da jin maganganunta, don maganganun sun rigada sun kaita bango.
Murmushi Aliyah ta sakar mata sa’anan ta cigaba da fadin ” Nasan abun zai baki mamaki, don a ranan kin tafi a guje domin kije ki kirashi, Amma a karshe sai kikaga an manta da ke, Sabah ko ta kanki bai bi ba. Sai kika ji kanki tamkar wata banza an tafi an barki, na tabbata da kinyi kuka koh?” Aliyah ta karasa maganar tana jefo mata murmushin mugunta.
Samha da zuciya ya dibeta bata san sanda ta daga Hannu ta watsa ma Aliyah mari ba. Dai dai lokacin sai ga Sabah da zack sun shigo cikin library din. Aliyah na ganinsu ta fashe da kukan makirci tana dafe kumatunta inda Samha ta mara. Da sauri Zack da Sabah suka karaso suna tambayarta abunda ya faru.
Aliyah ta marairaice fuska cikin muryar kuka ta soma fadin ” wlh ban mata komai ba haka kawai ta daga hannu ta watsa min mari” tana karasa maganar ta fashe da wani irin kuka.
Zack ne cikin zafin rai ya kalla Samha ya soma fadin ” Me tayi miki da zaki daga hannu ki mareta haka eh?”
Samha kanta duk yabi ya daure, cikin i’ina
ta bude baki tana kokarin ta musu bayani, Sabah ne ya katse a tsawace yana fadin ” Da gaske ne kin mareta ba tare da ta miki komai ba?! Ko baki lura da har yanzu tana da raunika a jikinta bane?!”
Aliyah cike da makirci ta matso kusa da Sabah tana fadin “Prince kayi hakuri ka kyaleta hakan, i’m okay babu abunda ya sameni, ka kwantar da hankalinka “. Ta karasa maganar tana sakar masa murmushi.
Sabah wani irin huci yakeyi don gabadaya abunda Samha tayi ya rigada ya gama bata mishi rai. Samha cikin zafin rai ta bude baki ta soma fadin “wato Sabah baza ka tsaya kaji ta bakina ba kenan, why do you always have to protect her? Kana ganin Abubuwan da takeyi marasa kyau, amma kana overlooking, idan ka cigaba da bata wanan daman, it’ll only get worse”
Sabah ne ya katseta da ” Ya isheki haka!. Wai meke damunki ne? Daman abubuwan da kike ta fada akanta da gaske kike, ban san me kike tunani ba amma kar in sake ganin kin daga hanu da niyan bugunta.” Ya karasa maganar yana watsa mata wani irin kallo cike da jin haushinta.
Itama Samha ganin abunda yake faruwa yasa ta daka mishi tsawa tana fadin ” Kaima Ya isheka haka Sabah, gabadayanku abubuwan da kuke mun ya isheni haka, haba duk kun bi kun raina mun hankali? Musamman kai Sabah, kwata kwata bana gane kanka, ka mayar dani tamkar abar wasan ka kana mun yawo da hankali, toh bari kaji in gaya maka daga yau sai yau babu wanda zan sake bari ya raina mun hankali”.
“Toh sai meye? In har hakan kikeso karki damu babu wanda zai sake raina miki hankalin naki. No one will toy with you anymore”.
Wani irin hawaye ne masu zafi suka soma gangaro wa Samha bisa kuncita, jin kalaman Sabah.
Zuciya ne kawo mata cikin sauri tazo ta bangaje shi da Aliyah ta kwasa a guje ta bar musu library din. Gudu takeyi tana kokarin share hawayenta, amma hawayen sun gagara tsayawa sai faman zubowa suke bisa kuncinta, ta soma haurawa saman matakala tana zubar da hawaye tana fadin “Duk laifi nane dana bari suka gama raina ni, i’m so stupid, da na zata Sabah yana bukatata cikin rayuwarsa amma yau gashi ya tabbatar mun da ba haka bane, ni ce kawai naketa wahalar da kaina akansa” ta karasa maganar tanata faman zubda hawaye zuciyarta na mata wani irin kuna akan abunda Sabah ya mata a gabansu Aliyah.
Tana cikin wanan Saurin sai ga Amjad nan yana kokarin saukowa, ya hangota tana tafiya ita kadai tana kuka har taje ta tsaya a bakin balcony tanata faman zubda hawaye. Amjad ya tsaya yayi shuru yana kallon yanda take ta faman kuka.
Bayan barin Samha cikin library din, Sabah ya tsaya yayi shiru yana nazari, sai kuma zafin zuciyar nasa ya dan ragu don baiji dadin yanda yaga Samha ta bar wurin tana kuka ba. Aliyah data lura da yanayinsa tazo ta baya tasa hannunta duka biyu ta rungumeshi ta kwantar da kanta bisa bayansa tana fadin ” karka damu prince, insha Allah zan cigaba da zama a kusa da kai, i’ll always be by your side” ta karasa maganar tana kara manewa a jikinsa. Zack cike da faduwar gaba yake kallon yanda Aliyah ta makale a bayan Sabah.
Aliyah ta cigaba da fadin ” Bazan taba barinka ba prince, akanka ba abunda bazan iya ba don na kasance tare da kai. I’m willing to do anything, as long as you’re here, zan shayar da kai farin ciki mara misaltuwa, zan kasance…”
Sabah bai bari ta karasa sauran maganar nata ba, cikin zafin nama ya finciko hanunta dake zagaye dashi ya daka mata tsawa yana fadin ” kema ya isheki haka! Aliyah bari kiji in gaya miki, in har zaki cigaba da dawama kina sa hope akan irin rayuwar da mukayi a da, komai ki ce sai ni toh tun wuri ki canza tunaninki don rayuwarki zata cigaba da maimaita kanta ne, babu abunda zai canza a tsakanina da ke”.
Aliyah ta marairace fuska tamkar zatayi kuka tace ” Prince kai kadai ne a cikin zuciyata kuma babu yanda za’ayi na daina sonka! Indai kana cikin rayuwata prince, bana bukatan komai kuma, wallahi da gaske nake, ka dubi lamarina prince zan iya yin komai don naga na mallakeka, wanan shine irin tarrin son da nake maka”.
Sabah ya kura mata kyawawan idanunsa, handsome face dinsa a murtuke kamar bai taba yin dariya ba ya soma fada mata a hankali “Toh nidai na gaya miki, idan ma mafarki kikeyi gwanda ma ki farka don babu abunda zai faru a tsakanina dake, so don’t expect anything more than a friend, don bazai taba yu’ wa ba, saboda a wajena thats all you are, you’re just a friend to me.”
Kalaman nasa kamar saukan dalma ta ji a kawon zuciyarta, amma tayi kokari ta dane tace ” haka zakace? Toh ita kanwar taka fa Samha, me ka dauke ta? Wani irin farin ciki kake tunanin zata kawo maka cikin rayuwarka?” Sabah nasan kana fadin haka ne don kawai Samha taki yin yanda kakeso, shiyasa kake jin haushi.Nasan Samha tamkar abar wasa take a wajenka, nasan baka bukatar ta a rayuwarka amma kai kuma kaqi ka kyaleta tayi nata rayuwar”.
Wani irin tsawa Sabah ya daka mata yana fadin “Shut up! Ki rufe mun baki!” Yana gama fadin haka ya kama hanyar waje.
Maganganun Aliyah suka dakatar dashi inda take fadin ” Don’t get confused Sabah don Samha bazata taba mayar maka da gurbin mahaifiyarka data tafi ta barka ba”
“Bana ce miki kimun shiru ba? Yanzu kinyi wanan maganar ne don ki kara harzuka ni ne ko meye? Mtchwww…” tsaki yaja ya fice ya bar musu library din.
Aliyah wani irin hawaye masu zafi ne suka soma gangaro mata, don ta rasa yanda zatayi Sabah ya saurareta. Ya zatayi da rayuwarta da kuma matsanancin tarin son da take mishi?” Cike da tausayin kanta Aliyah ta cigaba da zubda hawaye. Zack ya juyo yana dubanta shima cike da tausayi da tarin sonta. Hanunsa ya zira cikin aljihu ya ciro wata yar’ karamar hanki yana mika mata.
A hankali Aliyah ta kira sunan Zack tana fadin ” Zack na zama abun tausayi ko? Dubi yanda naketa wahalar da kaina akan Sabah amma shi kwata kwata baya ganin hakan, zuciyarsa da hankalinsa gaba daya basu tare dani, na rasa yanda zanyi da rayuwata. Me zanyi Sabah ya saurareni? Me zanyi na samu zuciyarsa ta karkato zuwa gareni? “. Ta karasa maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai.
Zack cike da jin tausayinta ya bude baki ya soma fadin ” Aliyah, please ki daina kuka kinji? Insha Allah zan taimaka miki, Sabah zai dawo gareki kinji? Ki share hawayenki, I won’t let anybody to hurt you.” Aliyah dagowa tayi tana kallonsa da jajayen idanunta da jin kalamansa.
Bangaren su Samha kuwa tana tsaye sai faman sheshekar kuka takeyi, Amjad ne ya karaso yazo ya tsaya inda take, tana ganinshi ta kawar da kanta gefe tana kokarin share hawayenta.
Amjad ya bude baki ya soma fadin ” Samha badai kuka kikeyi ba? Akan me zakiyi kuka bayan har yanzu baki Samu 3 leaf clover dinki ba?”
Samha ta juyo tana dubansa don bata fahimci inda maganar nasa ya dosa ba.
Amjad ya cigaba da fadin ” kin tuna ranan da muke tare dake a waya kika fada mun cewa kina neman 3 leaf clover dinki baki gani ba, ce mun kikayi tun kina karama idan kika shiga cikin damuwa, da 3 leaf clover dinki kike wasan ‘tug of war’ har kiji damuwan naki ya ragu”. Amjad yana gama fadin yasa hannu cikin aljihu ya ciro wata yar karamar 3 leaf clover da akasa igiya aka daureta. Ya dago yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi yace “taho muje mu buga”.
Itama Samha murmushin ta sakar masa tabi bayansa suka bar balcony din. Suna tafiya Amjad yana janta da hira sai faman dariya takeyi.
Duk wanan da sukeyi Amjad ya mance da batun fitan da zasuyi shi da khady, wace take can wurin parking lot tana tsaye tanata faman jiranshi, duba agogon hanunta tayi taga har biyar ta dan gota babu alamun sa. Nan take taji duk babu dadi kwalla suka ciko mata idanu. Tace bari ta mishi uzuri ta dan kara masa koda 30 mins ne, hakata cigaba da zama tana faman jiranshi.
Shikam Amjad zaune yake kan grass din garden din department dinsu shida Samha sunata faman buga game din ‘tug of war’ da 3 leaf clover din. Yana jan igiyan itama Samha tana ja har tazo ta cinye shi, cike da murna ta mike tsaye tana ta faman tsallen cewa ta cinyeshi. Amjad shima dariya ya dinga mata. Bayan ta gama murnan nata ta samu wuri tazauna suna fuskantar junansu. Samha ta dago tana duban Amjad wanda yayi shiru ya zuba mata ido yana kallonta, ta bude baki ta soma fadin ” Nagode sosai Amjad, gashi yanzu duk damuwan da nake fama da ita naji ya gushe. Thanks for been there for me”. Ta karasa maganar tana kallon cikin kwayar idanunsa.
Amjad ya dan murmusa sa’anan ya bata ansa da “Yayi kyau, a matsayina na friend dinki, bai kamata ace na ganki cikin damuwa kuma na tafi na kyale ki a hakan ba”Samha jikinta ne yayi sanyi da jin kalamansa nan take kuma maganganun data fada mishi, da kuma yanda suka rabu a baya suka soma dawo mata. Tayi shiru tunani kala kala na mata yawo a haka. Ta juyo tana kallonsa daga bisani ta bude baki ta soma fadin ” Amjad ai ban cancanci haka daga gareka ba, ko ka manta abubuwan dana fada maka can baya? I hurt you”. Ta karasa maganar tana sunkuyar da kanta cike da nadama.+
Amjad shiru yayi bai ce komai ba daga bisani ya bude baki ya soma tambayar ta “yanzu kina nadamar sonshi ne?”
Cikin sauri Samha ta dago tana dubansa, zata bashi ansa kenan Amjad ya katseta yana fadin ” To be honest Samha, ban san meyasa kike sonshi ba. Amma a yanzu na fahimci dalilin dayasa kika zabeshi”.
Murmushi Samha ta dan sake sa’anan tace ” Har ga Allah Amjad, ni kaina ban san meyasa na zabi Sabah akan ka ba, kayi hakuri”.
Amjad ya dan nesa sa’anan yace ” it’s okay, babu damuwa. Amma ki sani saboda shi na rasa ki so ni dashi baza mu taba wani shiri ba amma duk da hakan na kasa tsintar kaina da tsanar Sabah” Amjad ya karasa maganar yana tuno fadan da sukayi shi da Sabah a cikin gym, don yasan Sabah ya kawo kanshi ne don shi Amjad din ya duka, ya kuma huce takaicin rashin Samha akan shi.
Amjad ya dan nesa sa’anan ya cigaba da fadin “Ni sai yanzu na fuskanci yanayin Sabah, shi wani irin mutum ne mai cike da jin tausayin dan Adam kuma yanada nasa hanya da tsarin da yake taimakawa mutum, shiyasa har yanzu kika kasa gane kanshi. Ace mutum da irin shekarunsa amma yanada irin wanan tunani da hankalin? Abun yana bani mamaki sosai”.
Samha tayi shiru tana nazarin abunda ya gama fadi.
Amjad ne ya dubeta yace ” muje na dan taka miki”.
Haka suka soma tafiya suna hira tsakaninsu.
Amjad ne ya lura da yanayinta kamar bata cikin walwala ya bude baki ya soma fadin “c’mon cheer up, naga har yanzu kina bata rai, Ni kuma in ce me?” kin manta ke kika ci game din da muka gama bugawa? Bayan haka gashi kin gano cewa kinada saurayi mai hankali”.
“Wa kenan?” Samha ta tambayeshi.
Sabah mana, da waye. Ko kin manta yanzu ni dake we are just friends”.
Samha ta juyo tana dubanshi sa’anan ta bashi ansa da “Amjad kenan, karka damu insha Allah kaima zaka samu budurwa mai kirki da hankali wace zata kawar maka da duk wata damuwa dake cikin rayuwarka”.
Amjad ya dan murmusa sa’anan ya bata ansa da “na sani”. Sai kuma yayi shiru yana nazari nan da nan kuma ya tuno da khady da kuma fitan daya kamata suyi shi da ita.
Gabansa ne ya fadi don gabadaya ya manta shap, yasan yanzu kilan ta gaji da jiranshi ta tafi abunta. Cikin sauri ya juyo yana duban samha ya soma fadin “Samha ni zan wuce yanzu, wlh nayi mantuwa, i have to go”. Cikin sauri sukayi sallama ya juya ya tafi ya barta a wurin.
Samha ta bi bayanshi da kallon mamaki, ajiyar zuciya ta sake sa’anan ta cigaba da tafiyarta ita kadai tana tunanin zuci. Tana tunanin Sabah da kuma Aliyah da kuma yanda abubuwa zasu kasance tsakaninsu nan gaba. Wata zuciyar ce ta soma tambayarta da anya kuwa zaki iya? Ga Aliyah data kudiri niyan ganin bayan duk wanda zai zo ya tsaya a tsakaninta da Sabah. Wata zuciyar ce ta bata ansa da “Gwanda ma ki dage karki taba bari Aliyah ta samu nasara akanki. Da wanan tunanin ne hankalinta ya dan kwanta ta kudiri niyan itama zata tashi ta mike tsaye akan abunda takeso.
Bangaren khady kam har ta gaji da jira, ta mike daga inda take zaune, jiki a sanyaye ta soma tafiya kamar zatayi kuka, wani irin tausayin kanta takeji tana tafiya tana matse matsen kwalla har tazo ta karya kwana ta shiga wata layi, sai ya zamana da daidai lokacin da shima Amjad ya karaso suka samu sabani, yazo yanata faman waige waige bai ganta ba.
Cikin sauri ya zira hanunsa cikin aljihu ya ciro wayarsa ya soma neman layinta. Sai da kiran ya kusan tsinkewa tukuna ta daga.
Amjad yana jin ta daga nan da nan ya soma bata hakuri yana fadin “Hello khadija, dan Allah kiyi hakuri kinga na sake yin late yau ban zo da wuri ba, na barki kinata jirana. I’m so so sorry please”.
Khady cikin sanyin murya tace mishi “babu komai”.
“Yanzu kina inane?” Ya tambayeta.
“Ina hanya zan koma gida”.
“Kinyi fishi ne?”
Khady tayi shiru daga bisani tace mishi “Banyi fishi ba ai na fada maka babu komai. Sai anjima”. Tana gama fadin haka ta katse kiran. Ta dago wayar daga kunenta ta kurawa screen din ido, hawayen da take ta kokarin danewa ne suka samu nasaran gangaro mata bisa kunci, tasa hanu ta mayar da wayar cikin jakarta.
Ta soma tafiya tana share hawayen dake gangaro mata bisa kunci, tana cikin tafiya sai ta hango wani bill board mai dauke da advertisement na Coca-cola. Matar da ke jikin billboard din rike take da wata bakar lema tana shan coke akayi mata hoton. Khadija na ganin hoton ta soma tuno bet din da sukayi ita da Amjad akan lema da kuma alkawarin daya mata na cewa zai samo mata mazauni cikin zuciyarsa. Jikinta ne ya kara yin sanyi tunani kala kala suka soma mata yawo a ka.
Wani tunani ne ya fado mata tasa hanu ta ciro wayar daga cikin jaka ta soma rubuta mishi text kamar haka ” Na maka uzuri na yau zan daga maka kafa amma idan ka sake yin late ka sani jiranka irin haka, toh ni da kai ne”. Tana gama typing ta tura mishi da sakon.
Amjad yana cikin tafiya jikinsa a sanyaye yaji karar shigowar sako, ya ciro wayar daga cikin aljihu ya bude sakon ya soma karantawa, murmushi ya dan sake daya gama karantawa yana fadin ” Khadija kenan”. shima ya soma mata typing reply nan da nan ya tura mata.
Khadija na tsaye taji shigowar sakonshi, jikinta na bari ta bude ta soma karanatawa kamar haka ” Toh ayi hakuri a yafe mun Gimbiya Khadija. Insha Allah bazan sake ba. Ya next week Sunday zata kasance kina free? Sai mu sake fixing date dinmu zuwa ranar. And I promise not to disappoint you this time around. Insha Allah”.
Khadija na gama karanta text din wani irin sanyi taji a ranta, taji duk damuwarta ta nema ta rasa a lokacin. Cike da farin ciki ta karasa zuwa gida.
Washe gari misalin kare goma na safe, bayan an gama morning lectures. Su Sabah da sauran yan team sunata faman practice. Sabah kam tunda yayi practice so daya ya nemi wuri ya zauna, sai wani shan kamshi yakeyi, kyakyawar fuskar nan nasa a daure murtik, yayi shiru yayi zurfi cikin tunani, tunda ya zauna bai sake cewa kowa kala ba kuma babu wanda yayi yunkurin yi masa magana dan sun san sauran zancen.
Samha ce take tsaye sai faman binshi da kallo takeyi, tana so tayi mishi magana amma tana shakkan abunda zai biyo baya.
Itama kanta Aliyah sai faman binshi da kallo takeyi itama tana shakkan yi mishi magana. Sai zack dake tsaye kusa dasu yana kallon duk abunda yake faruwa. Suna hada ido sai ya wayance yayi kamar yana exercise.
Samha kam tabe baki tayi ta tafi ta basu waje, nan ta karasa inda sauran team players din suke, ta ciro biro da kuma wata yar’ karamar takarda daga cikin jakarta tana tambayarsu abunda suke so suci taje ta siyo musu, daya bayan daya haka suka soma fada mata tana rubutawa.
Bayan ta gama dasu ta juyo tana tambayar ko akwai wanda yake bukatan wani abu. Idanunta ne suka sauka kan Sabah wanda har zuwa lokacin bai dago ba yanata faman tunanin nasa. Samha jiki a sanyaye ta juyo tace ” toh shikenan, tunda babu wanda yake bukata wani abu kuma, bari na tafi” tana gama fadin haka ta juya ta tafi har tazo dab da inda Sabah yake zaune ta tsaya ta kura masa ido daga bisani ta fice daga cikin gym din.
Zack ne ya kalle ta ya kalli Aliyah sa’anan ya sake dawo da dubansa gareta, haka yabi bayanta da kallo har ta fice mishi daga gani. Nan da nan ya soma kitsa abubuwa a ransa.
Daya daga cikin yan team dinne yace ” kai ya naga kamar akwai hadari za’a soma ruwa”.
Amjad ne ya dago yana duban window yaga garin duk yabi ya rikide alamun za ayi ruwa, gashi samha ta fita ko lema bata rike ba. karasowa yayi inda Sabah yake zaune ya soma fadin ” Samha ta fita taje siyo wa yan’team abunda zasu ci kuma gashi garin ya rikide za’a soma ruwa yanzu. Ko zaka je kazo da ita?”
Sabah ya dago ya bashi ansa da ” Kaima zaka iya zuwa ka dauko ta mana, duk bai bace ba”. Yana gama fadin haka ya juya yayi shiru ya cigaba da tunanin da yake na fama.
Amjad bai sake cewa komai ba ya juya ya bar wurin yana fadin ” nama bata lokacina da naje na sameshi, dana sani ma banje ba” ya karasa maganar cike da takaicin Sabah.
Zack ne yazo ya sameshi yana fadin “Captain bari naje nazo da ita”.
Amjad ya dubeshi yace “Toh shikenan babu matsala”.
Haka zack ya gyada kai yayi hanyar waje. Aliyah tana tsaye tana kallon komai, nan take jikinta ya bata cewa Zack da wani manufa ya fita zai je yazo da Samha. Nan take taji hankalinta ya tashi data soma tuna kalamansa inda yake fadin ” Aliyah ki kwantar da hankalinki, i’m going to help you”. Nan take ta soma girgiza kai tana fadin Badai abunda nake tunani bane zack yake kokarin yi? Anya kuwa?”. Cike da tashin hankali ta soma tunani iri iri.
Samha har ta gama siyayar ta tana hanya runwan ya riske ta, gashi ana ruwan da karfi, cikin sauri take tafiya don ta samu ta karasa zuwa gym, har ta kusa, kamar daga sama taga mutum tsaye a gabanta. Zack ta gani fuskarsa a daure tamau, hanunsa rike da wata katuwar sandar karfe, yana kallonta cike da tsana.
“Zack, meya faru?” Samha ta tambayeshi.
Bude baki yayi ya soma fadi ” komai ma ya faru, gani nai lokaci yayi daya kamata ace kin fita daga cikin rayuwarmu. Aliyah tana son Sabah dayawa kuma har yanzu ta gagara samun kansa duk saboda ke, don in har kina raye Aliyah bazata taba samun farin cikinta ba, ni kuma bazan taba barin hakan ya faru ba don farin cikin Aliyah, shine farin ciki na. Don haka it’s better kawai ace baki nan.”
Samha tana tsaye tayi shiru tana sauraronsa. Tama rasa mai zatayi. Me zack yake nufi yanzu? Kasheta yake son yayi akan Aliyah ne ko me?
Aliyah wace gabadaya tunaninta ya rigada ya karkata zuwa zack, tunani kala kala ne ke mata yawo a ka. Anya kuwa? Nan da nan maganar da sukayi na karshe ita da zack suka soma dawo mata. Inda yake tambayarta “yanzu idan Samha ta bace daga rayuwar Sabah, zaki samu farin ciki. Hankalin Sabah zai dawo gareki koh? Karki damu, i’ll make you happy. Indai Sabah ne toh ya rigada ya zama naki, ki kwantar da hankalinki.”
Haka maganganun nasa suka dinga dawo mata. Jikinta ne ya soma bari don duk yanda ta tsani Samha bazata so hakan ya faru da ita ba. Cikin sauri ta mike tazo ta sami Sabah inda yake zaune ta soma fadi cikin i’ina muryarta na rawa “Sabah… z..zack ya…”sai kuma tayi shiru.
Sabah ne ya dago yana dubanta yace “Ehen ina jinki, Zack din meya samesa”.
“Sabah. Z..zackk yace akaina zai iya… ku..kuma gashi yabi ba..bayan Samha. Tso..tsoro nake kada ya…” sai kuma tayi shiru hawaye na gangaro mata bisa kunci.
Cikin sauri Sabah ya mike tsaye yana fadin “Aliyah calm down, ki kwantar da hankalinki ki fada mun abunda ke faruwa. Ban gane ba, me kike kokarin fadi?” Ya karasa maganar yana dubanta.
Cikin sheshekar kuka Aliyah ta bude baki ta cigaba da fadin ” Na fadawa Zack cewa ina son Samha ta bace daga cikin rayuwar mu bansan na kara ganinta kuma”.
Ai kam Sabah yana jin haka bai bari ta karasa maganarta ba ya kwasa a guje ya bar cikin gym din.
Bangaren su Samha kuwa, zack ne ya yake karasowa inda take gadan gadan hanunsa rike da sandar karfen yana fadin ” kinga idan kika tafi, Aliyah zata samu ta sake”.
Samha ce ta katse shi da ” Zack anya kanka daya kuwa, ka san me kake fadi kuwa?”
“I don’t care, in dai akan Aliyah ne toh babu abunda bazan iya yi ba”.
“Zack, na sanka. Na san duk waenan abubuwa da kake fadi ba dagaske bane don ban yarda zaka iya mun wani abun akan Aliyah ba. You’re not that kind of person Zack”.
” ki daina wanan tunanin akaina don zan baki mamaki.”
Samha ta girgiza masa kai tana fadin ” kana tunanin wanan abun da kake shirin aikatawa shine mafita, yanzu idan ka kasheni mai kake tunanin zai faru? Meyasa kai da Aliyah bazaku koyawa zuciyar ku dangana ba, yanda kuke nuna so ba haka ya dace ba. Irin wanan soyayyar da kuke yi wa mutum bata da amafani don kuna jefa rayuwar mutum cikin hadari. Kaso mutum tsakani da Allah ba tare da kasa komai a ranka ba, shine asalin so don haka kai da ita kunada aiki ja a gabanku”.
Wani irin tsawa Zack ya daka mata yana fadin”Kiyi mun shiru ki fita daga cikin rayuwar mu!” yana karasa maganar a tsawace ya dago karfen dake hanunsa yayi saitin kanta. Samha rufe idanunta tayi tana jiran taji saukan karfen akanta.