ZABIN SAMHA CHAPTER 7
Wuri suka samu suka zauna suka yi shiru barin ma khadija da jikinta yayi bala’in sanyi ganin tsohon saurayinta Alamin.
Hawaye masu zafi ne suka soma gangaro mata ta sa hanu ta soma gogewa. Amjad yayi shiru yana kallonta.
Cikin sheshekar kuka ta soma fadin ” ban san me nayi dana cancanci haka ba, wai kawata da saurayina suci amanata, musamman Alamin wanda nabashi zuciyata halak malak, meyasa zasu ci amanata haka? Me na musu?. Da acan baya nace bazan kara soyayya ba amma everything changed when i met you Amjad” ta karasa maganar tana rushewa da kuka.
Amjad shiru yayi yana dubanta tana kukanta daga bisani ta cigaba da fadin ” nasa rai a wanan fitan namu, komai zai tafi yanda ya kamata, nida kai zamu samu mu fuskanci juna sosai, amma gashi wancan yazo ya bata komai.”
Amjad ya cigaba da dubanta daga bisani ya kira sunanta a hankali ” khadija….”
Khady ta dago kai tana dubansa da jajayen idanunta still bata daina kukan ba. Amjad yace “ki daina kuka khadija, inaso ki share hawayenki ki manta da komai. Abunda ya faru ya rigada ya faru kinji, i’m glad you’ve loosened up kuma daga yanzu ni Amjad na miki alkawari zan zame miki madafa a rayuwarki because daga yanzu kin daina fuskantar irin wanan kalubalin a rayuwarki kenan insha Allah, bakisan meye ba, a yanzu haka babu wace nakeso naji na kasance tare da ila khadija”. Amjad ya karasa maganar yana sakar mata lalausar murmushi.
Khady wani irin dadi ne taji ya ratsa duk ilahirin jikinta da kalamansa, murmushi itama ta sakar masa tasa hannu ta soma goge hawayenta.
Amjad yana gama fadin haka ya juya ya dauko ledar daya ruko ya ciro wata kwali daga ciki daga bisani ya tsuguna a gabanta yana kokarin bude kwalin takalmin ya soma fadin ” takalmanki basu miki daidai ba, meyasa kika tilasta wa kanki sasu?”. Ya karasa maganar yana bude kwalin, wasu takalma shigen irin nada ya ciro daga cikin kwalin.
Hannu yasa ya kamo kafanta na dama ya soma saka mata takalmin kafa daya. Khady shiru tayi tana kallonsa tana cigaba da goge hawayen da suketa faman zuba mata bisa fuska.
Bayan ya gama sanya mata takalmin, ya mike yana dubanta sa’anan yace ” ki share hawayanki ki daina kuka, insha Allah daga yau kinyi bankwana da heartache don daga yau Amjad ya rigada ya zama naki”. Ya karasa maganar yana sakar mata lalausar murmushi.
Wani irin farin ciki ne ya lulube khady, nan take taji duk damuwar dake tattare da ita ya gushe. Ta kura mishi ido tana cigaba da kallonsa dan wani irin sonsa ne ke dadda karuwa cikin zuciyarta.
Bangaren su Sabah kuwa tafiya sukeyi shida Samha tana janshi da wasa tun yana dakewa har yazo ya soma sakin jiki, sunata faman wasa da dariya tare.
Samha ta dubeshi tace “Sabah zo muje mu hau roller coaster.”
Sabah ya dubeta yace “Anya kuwa zaki iya? Duba yanda mutane suke faman ihu a ciki.”
Samha ta marairace fuska tace “Sabah please, just once kaji muje mu hau”.
Sabah Ajiyar zuciya ya sake sa’anan yace “toh shikenan, let’s go.”
Suna karasawa wajen Sabah ya siya musu tickets na hawa ride din. Suka je suka hau suka zauna a ciki. Ga wasu mutane suma tare da family dinsu suna zaune a sauran seats din dake sama. Amma banda yara don ba’a bari yara su shiga saboda height din roller coaster din, komai zai iya faruwa.
Tunda suka shiga suka zauna jikin Samha ya soma bari, Sabah ya dubeta sa’nan yace “Idan kin san bazaki iya ba mu sauka”.
Samha ta dage tace mishi babu komai zata iya. Can sai ga daya daga cikin masu tayar da engine roller coaster din yazo ya soma duduba karfen da aka rufe seat dinsu dashi ko ya rufu da kyau. Sai daya tabbatar dana kowa a rufe yake tukuna ya koma suka tayar da engine. A hankali roller coaster din ya soma tashi sama dasu.
Suna kaiwa can sama, jiri ya soma diban Samha ta rufe idanunta gam. A haka gudun roller coaster din ya soma karuwa.
Da gudun ya kai iya gudu, Samha bata san sanda ta bude baki ta soma kurma ihu ba, Sabah yayi sauri yasa hannu ya toshe mata baki yana fadin “keh meye haka?”
Samha bata saurareshi ba ta cigaba da ihu, ta sa hannu ta rike gefen rigansa gam tana fadin “wayyo Allah Ammi! Ki zo ki taimake ni! Wayyo zan fadi!”.
Abun dariya ya soma bawa Sabah don maganganun da takeyi babu kai kwata kwata, hannu yasa ya kamo lalausar hannunta cikin nashi ya soma rarashinta yana bata baki.
Ba Samha kadai ba, hata sauran mutanen da suke cikin roller coaster din ihu sukeyi saboda gudun abun.
Sai da sukayi kusan 10minutes akai tukuna gudun abun ya soma raguwa. Nan aka samu saukin ihun, Samha ajiyar zuciya ta soma sakewa tana nishi.
Sabah ya juyo yana dubanta ya soma kwaikwaiyon ihun data dingayi. Harara ta watsa mishi tana kawar da kanta gefe.
Sabah ya tunsure da dariya yana fadin “o ni, kinji ihun da kike ta sakewa kuwa? Ai kin gama lalata mun kunne yanzu” ya fada yana shafo kunnensa.
Samha ta sake watsa mishi harara tana murguda masa baki. Sabah sai faman zolayenta yakeyi har roller coaster din yazo ya tsaya. Masu aikin wurin suka zo suka fara kwance musu karfen seat din. Sabah dubanta yayi yaga ta hade fuska sai faman kumburi takeyi, murmushi ya sake sa’anan yace “kanwata, ko zaki kara ne?”
Babu shiri Samha ta mike ta fita daga ciki lilon, Sabah shima mikewa yayi ya mara mata baya yana tayi mata dariya.
Sun danyi nisa tukuna yace “toh tunda mun hau choice dinki dazu, Yanzu sai muje mu hau choice dina. Muje mu hau water splash” ya fada yana kamo hannunta.
Babu musu Samha ta bishi don tasan wanan bashida wahala da abun tsoro kamar roller coaster. Suna zuwa Sabah ya siya musu tickets din suka karasa inda hake hawa. Kanan jirage ne na engine a zube a cikin ruwan wanda zai iya diban mutane biyu zuwa uku.
Suna shiga ciki suka zauna, Sabah ya juyo yana dubanta sa’anan yace ” Big sis, kiyi hakuri kinji, wanan bashida tsoro kamar wancen. You’ll enjoy it”. Haka ya dinga bin Samha da baki har ta samu ta sauko.
A hankali aka kunna injin, jirgin ruwan suka soma motsawa suna tafiya a cikin ruwan. Wani irin iska mai sanyi da dadi ne ya soma busowa ta ko ina. Samha ta dago kai tana duban Sabah, shima kyawawan idanunsa ya zube cikin nata yana kallonta.
Lalausar Murmushi ya dan Sakar mata itama ta mayar mishi, ta dora kanta bisa kafadar shi don a lokacin wani irin sonshi ne ke dada karuwa cikin kahon zuciyarta yana ratsa ko wani sashi na jikinta.
“Sabah…..” Samha ta kira sunansa a hankali.
Bai bata ansa ba, ta cigaba da fadin ” yanzu wasu mutanen idan sun ganmu a tare haka ni da kai, zasu dauka nida kai mata da miji ne ko kuma budurwa da saurayinta”.
Sabah bai ce komai ba, murmushi ya sake yana sauraronta itama ta cigaba da fadin ” Amma dazun da muke tare dasu Abba, duk wanda ya ganmu zai zata real family ne”.
“Ban gane ba” Sabah ya katseta.
“Kaga, ga Ammi, ga Abba, ga ni ga kuma kai, waye zai dubemu yace mu ba family daya bane?” Ta tambayeshi sa’anan ta cigaba da fadin “Amma ban san meyasa ba a duk sanda muke tare dasu, kuma kana wajen, i can’t seem to be my true self”
“Toh sai meye? You can be your true self if you want. Ni dai a yanzu haka, my only wish bai wuce ace waenda nakeso, su kasance tare dani ba”
Samha murmushi ta sake ta dago tana dubansa sa’anan tace ” ina daga cikin waenda kakeso su kasance tare dakai din?”
Sabah ya juyo yana dubanta, sai daya kalleta na kusan 2 seconds daga bisani handsome face dinsa ta barke da murmushi ya kawar da kansa gefe yana fadin “of course kanwata, kina daya daga jiki mana”.
Wani irin dadi da farin ciki suka lulube Samha, ta lumshe idanunta a hankali. Ita kanta bata san wani irin so take yiwa Sabah ba don kullum sonshi dadda huda tsokar dake makale bisa kirjin ta yakeyi. Amma idan ta tuno iyayensu da zasuyi aure, sai jikinta yayi mugun sanyi don tasan soyayyarta da Sabah bazatayi lasting ba, sai dai suyita a boye amma bazata taba bari iyayensu su sani ba.
A haka suka cigaba da wasa da dariya, jirgin nata yawo dasu cikin ruwan. A ranar dai ba’a cewa komai don they had fun sosai. Su Ammi ma suka zo suka tadda su, hotuna suka dadauka tamkar real family guda, abun sha’awa. Daga bisani suka hau mota suka wuce gida.
********************
Washe gari a school da safe, Samha dasu khady suka karasa wurin locker dinsu don ciro takardun su na next lecture.
Samha tana sa hannu ta bude kofar locker dinta, wasu takardu da envelope ne suka zubo warwass a kasa a gabanta. Nan take ta tsaya cak don wani irin sanyi ne taji jikinta yayi ta kurawa papers din dake zube a gabanta ido.
Khady ta kalli papers din dake yashe a kasa sa’anan tace ” oh Allah, yanzu Samha zata sake zama yar’ aike kenan” ta karasa maganar tana rufe kofar locker dinta daga bisani ta juyo ta jingina da jikin locker din, hannunta duka biyu ta manna bisa kirjinta ta cigaba da fadin “gaskiya i can’t stand this anymore, haba su yan matan nan basu da hankali ne? Sai su zauna su tsarawa Sabah rubutun soyayya, amma bazasu iya bashi da kansu ba sai dai su kawo mata ta bashi, ai wanan shashanci ne”.
Samha shiru tayi ta kurawa letters din dake zube a gabanta ido bata ce komai ba.
Khady ta juyo tana duban Amina sa’anan ta cigaba da fadin “wlh Amina, tunda aka sake waenan hotunan a group, students suka gane cewa Samha kanwar Sabah ce, yan’matan nan suka rikice, yanzu letter suke rububin rubutawa sai suyita kawo mata wai ta kaiwa Sabah. Suna so su mayar da ita yar’aike karfi da yaji”.
“Kai amma aiki ya samesu”. Amina ta fada tana tabe baki.
“Aiki ma ja kuwa”. Khady ta fada.
Samha haushi ne ya dibeta ta tsuguna ta kwaso letters din a hannunta straight hanyar waje tayi. Bata tsaya ko ina ba sai department dinsu Sabah. Tana shiga cikin ajin ta hango shi can gefe zaune kan kujera, kafar sa daya kan daya yana hira dasu Zack.
Yau shigar jikinsa ta daban ce, Sanye yake cikin farar T shirt da bakin wando, sai black p cap daya daura bisa curly hair dinsa wace tasha gyara ta kwanta bisa kansa sai shekki takeyi, yayi kyau sosai.
Samha tana hangoshi ta karasa inda suke zaune ta dire mishi letters din a gabansa tana hucci.
Sabah dasu zack da suke zaune basu ga shigowarta ba sai kawai sukaga an watso musu papers a gabansu. baki suka sake suna kallon papers din daga bisani suka dago suna kallonta cike da mamaki.
Sabah ya dago ya kafe ta da kyawawan idanunsa bai ce komai ba yana kallonta.
Samha sai faman hucci takeyi ta soma fadin ” ga letters din yan’matan ka nan na kawo maka”
Sabah ya daure fuska yace “So nawa zan gaya miki ki dinga zubar dasu a shara?”
“Bazan iya ba”. Ta fada mishi tana kawar da kanta gefe.
“Ban gane bazaki iya ba? Idan sunada abun fadi, suzo su fada da kansu mana” Ya fada yana watsa mata harara.
Samha ta dawo da dubanta gareshi sa’anan tace ” kai yanzu tunaninka bai taba kawo maka cewa kilan ma kasa bacci sukeyi don dai su rubuta maka letters dinnan su aika maka dasu ba? And you won’t even look at them, wlh you’re so mean Sabah” ta fada tana watsa mishi harara.
Sabah abun nata mamaki yake bashi don haka yasa hanu ya ciro daya daga cikin letters din yana juyawa a hankali daga bisani ya sake murmushi yana fadin ” Toh yanzu duk surutun nan da kika tsaya kinayi, kilan ma wata ta saka nata a ciki bata sani ba kamar yanda ta taba bawa wani letter dinta amaimakon ta bawa wanda takeso”.
Samha ta bata fuska kamar zatayi kuka murya a dage ta soma fadin ” akan me zaka dauko wancan maganar bayan komai ya rigada ya wuce. You’re so annoying!”.
Zack wani irin dariya ya sake yana kawar da kansa gefe. Samha tayi kamar zata kai mishi duka don takaici.
Shinoh ya tabe baki yace ” ai kuma sai kuyi, ni dai karkuyi wasting letters dinan, idan Sabah baya so ku tattaro ku bani su killan nayi dace na samu wata hot chick a cikinsu”. Ya fada yana kokarin tattaro letters din.
Samha hannu tasa ta bige mishi hannu tana fadin “kul, karka kuskura”.
Tana gama fadin haka ta fuzge letter din dake hannun Sabah ta tattaro sauran tayi gaba ta fita ta bar musu ajin tana kunkuni.
Sabah bayanta yabi da kallo yana wani irin shu’umin murmushi ya soma girgiza kansa.
Samha kenan.”Wow, amma gaskiya guy dinan ya hadu”.
“Kai he’s so handsome, dan Allah waye shi?”+
Haka yan’matan department suke ta rububin fadi suna karewa wani hadadden guy daya shigo cikin department dinsu kallo. Ba matan ba harta mazan ma binshi da kallo sukeyi.
Sanye yake cikin wata haddiyar black kaftan anyi mishi dinkin riga da wando. Sumar kansa ta kwanta bisa kanshi. Fari ne sosai yanada haske, kuma yanada madaidacin tsawo bashida jiki. Hancinsa straight ga dara daren idanunsa farare tass dasu sai dan karamin pink lips dinsa. A fuska zaka ganshi kamar yaro yaro amma yanada jikin manya.
Tafiya yakeyi shi kadai handsome face dinshi dauke da murmushi ya soma haurawa staircase din, kowa sai binsa da kallo yakeyi saboda tsabar kyau da kwarjinin da Allah yayi masa.
Har ya haura yazo dab da corridor da zai sadaka da lecturer halls din department din yaja ya tsaya.
Samha ce ya hango tana dab da karasowa, tafiya takeyi kanta a sunkuye cike da tunani da takaicin Sabah hannunta still rike da letters din tana tafiya cikin sauri.
Ganin mutum tsaye a gabanta ne yasa taja birki ta tsaye tana dubansa. Murmushi ya sakar mata yana kallonta. Gabanta ne yayi wani irin mumunar faduwa da idanunta suka ci karo da takardan dayake rike dashi a hanunsa.
“Har da maza ma? Shima so yakeyi na bawa Sabah sako ne ko meye?” Ta tambayi kanta kirjinta na bugawa.
Guy din still yana murmushi ya dago hanunsa ya mika mata letter din yace ” This is for you”.
Cike da mamaki Samha ta sona binshi da kallo sa’anan tace ” Ban gane ba”.
Bai tsaya wata wata ba, kai tsaye yace mata “Sonki nakeyi”.
Wani irin dummm Samha taji a cikin kirjinta ta bude baki tana kallonsa.
Guy din ya cigaba da fadin “ina sonki Yan’mata”. Ya sake maimaitawa Still hanunsa na rike da letter din.
Samha duk tabi ta rikice tunani kala kala suna mata yawo a ka, anya kuwa wanan ba wasa da hankalina yazo yi ba. Yama za’ayi ace yana so na. Ina bazai yu ba”. Ta fada a zuciyarta.
Kamar ya jiyo tunanin da takeyi yace “da gaske nakeyi baby girl, ina sonki”
Wani irin kallo ta watsa mishi sama da kasa, nan take tunanin Sabah ya fado mata ta soma fadin ” haba mallam,haka kawai ban sanka ba kuma ban taba ganinka ba kazo kace kana sona? An taba soyayya haka? gaskiya bazan iya ba”.
Tana gama fadin haka ta kara gaba ta tafi ta barshi tsaye a wajen. Har ta danyi taku biyu ko mai ta tuna? Sai kuma ta sake dawowa tazo tace mishi ” kayi hakuri”
Nan kuma ta sakeyin gaba tana tafiya cikin sauri, guy din yana tsaye ya bi bayanta da kallo yana wani irin shu’umin murmushi.
***************
Lecture hall din Cosc403 yayi shiru, babu abunda yake tashi illa karan AC dake zube cikin lecture hall din, sai kuma muryan lecturer din dake tsaye wajen projector yana yiwa students din bayani.
Sabah yana zaune tare dasu shinoh a seat dake row na biyu ya kishingida akan kujeran, hankalinshi a kwance sai faman zabga bacci yakeyi abunsa kai kace yana parlourn gidansu ne.
Lecturer din ya dage yana musu bayani akan cewa yanason students din suyi wata web design amma as a group project, kuma ko wani group za’ suyi submitting project dinsu zuwa ga wani babban company toh duk group din da suka ci sa’a, company din ta zabe web design dinsu, company din zata iya awarding dinsu scholarship na zuwa karatun masters.
Surutu da hayaniya ne ya barke tsakin students din kowa yana murna da wanan zancen.
Lecturer din ya cigaba da fadin ” kuma wanan project din zai zame muku kamar upgrade ne na wanan semester din. So daga ni har school management din muna fata ko wanen ku zai dage yayi participating akan wanan project din. I hope you won’t let us down”.
Zack dake zaune kusa da Sabah ne ya soma fadin “SB… ina Abbanka shine VC din makarantar nan, so wani management kuma wanan mutumin yake magana akai?”
Shirun dayaji ne yasa ya waigo yaga Sabah yayi nisa da baccinsa, baya ma cikin ajin bai san wainan da ake toyawa ba. Daman tun da lecturer din ya shigo ya soma koyarwa Sabah ya soma gyangyadi.
Zack ya tabe baki ya juyo ya cigaba da sauraron lecturer din yana musu bayani.
************
Bangaren su Samha kuwa suma zaune suke cikin class ana musu lectures. Magana sukeyi a tsakaninsu kasa kasa yanda lecturer din bazata iya jiyosu ba. Khady ce take fadin ” yanzu Samha kina nufin wani yazo yace miki yana sonki kuma baki sanshi ba?”
Samha ta gyada mata kai, Kamar daga sama sukaji ana fadin “su waye suke mun surutu cikin aji?”
A firgice suka dawo da dubansu ga board kamar basu suke surutun ba. Lecturer taja tsaki sa’anan ta juya ta cigaba da rubutun da takeyi a board.
Amina dake zaune a bayansu ta soma magana kasa kasa tana fadin “amma ya guy din yake, yanada kyau?”
Samha itama kasa kasa ta bata ansa da “sai ma kin ganshi, wallahi ya hadu kuma yanada bala’in kyau. Kyaunshi ma har tsoro ya bani”
Su khady kai kawai suka gyada suna jinjina maganarta.
“Toh yanzu dayace yana sonki, kin amince masa ne?”. Khady ta tambayeta.
“Akan meye zan amince masa khady? Sai kace ban san me nakeyi ba?”
Haka suka cigaba da maganar da sukeyi kasa kasa.
Lecturer din tana juyowa sai su dauke wuta kamar basu suke surutun ba. A haka har suka gama lectures din suka fito a tare, suna tafiya suna hiransu from nowhere sukaga anzo an sha gabansu. Wanda yasha gaban nasu direct a gaban Samha ya tsaya yana murmushi yana kare mata kallo. Guy dinan ne na dazu, Samha tana ganin shine tasha mur, ta tamke fuska.
Guy din idanunshi kyam akanta ya soma fadin “yan mata akan me kika dawo kina bani hakuri dazun dan nace ina sonki. Please ki amince mun wlh ina bala’in sonki”.
Samha kirjin ta ne ya soma bugawa da karfi ta bude baki soma fadin “meye haka kuma zaka zo ka sake tsare ni akan hanya. Bakaga ina tare da kwayena bane? Dan Allah ka rabu dani”.
Guy din yayi shiru yana dubanta da kyawawan idanunsa daga bisani ya bude baki ya cigaba da fadin ” har yanzu baki ansa mun tambayoyina ba. I want to be your boyfriend. Can I?” Ya sake tambayarta.
Samha a fusace ta bashi ansa da “Dallah mallam ban sanka ba haka kawai zaka zo ka dameni da cewa kana sona!”
Guy din bai damu ba, still yana murmushi ya cigaba da fadin “indai sani na kike son kiyi, wanan ba matsala bane. Sunana Abdul-Jabbar amma yawanci anfi sanina da Jabbar, ina faculty din Enviromental design ina karanta Architecture”.
Ya kara matsowa kusa da ita, Samha ta matsa da baya. Murmushi ya sake sa’anan ya cigaba da fadin ” sai meye kuma kikeso ki sani game dani? Ni har yau ban taba ganin wata ya’ macen dazan tunkareta ince ina sonta, taki yarda ba. Nan da nan zata amince mun.”
Ya sake matso kusa da ita sa’anan yace “so kefa? Kin yarda Zaki amince mun?”
Samha ta marairace fuska sa’anan tace “Gaskiya sai dai kayi hakuri, bazan iya amince maka ba. Inada wanda nake so already”.
Jabbar ya dan saki dariya sa’an yace “bazan yarda ba har sai kin fada mun wanda kikeso”
Khady da Amina tsaye suka a gefe suna kallon ikon Allah. Khady ce da fusata tazo ta tsaya a gabansa tana fadin “baza’a fada maka ba, ina ruwanka da wanda takeso. Toh bari kaji na gaya maka kayi taka tsantsan don saurayin Samha baya ragawa kowa, yanzu nan zaiyi maganinka”. Ta fada tana watsa masa harara.
Wani irin kallo Jabbar ya watsa mata wanda yasata shan jinin jikinta, daga bisani ya dawo da dubansa ga Samha yace ” wanan saurayin da kuke magana akai shine Sabah?”
Ba Samha kadai ba harta su khady binshi da kallon mamaki suka soma yi.
Jabbar ya cigaba da fadin “ina yawan ganinku tare dashi ai”.
Samha tayi saurin katse shi da ” waya gaya maka Sabah ne? Baka taba haduwa da wanda nakeso ba”. Samha ta fada mishi tana kokarin kareshi.
Oh haka ne?” Ya tambayeta yana daga mata gira daya.
“Toh kije ki fadawa wanda kikeso cewa ni Jabbar nace ina sonki, ke tawace. You’re mine”. Yana gama fadin haka ya juya yayi tafiyarsa. A firgice su Samha suka bi bayanshi da kallo cike da mamakinsa.
Ba abunda ke yiwa Samha yawo aka illa maganganunsa na karshe inda yake fadin “ke tawa ce….. ke tawa ce….. ke tawa ce”.
“Na shiga uku. Wanan wani irin damuwa ne ke shirin kuso kansa cikin rayuwata ina zaman zamana”. Ta tambayi kanta.
Su khady da Amina kasa cewa komai sukayi saboda tsabar mamaki.
shiru sukayi suna cigaba da tafiya kowace da tunanin dake mata yawo a ka, barin ma Samha wace jikinta yayi mugun sanyi.
Amina ce ta dubi Khady tana fadin ” yanzu Samha ta samu hadadden guy kamar wanan yana mata magiyar yana sonta amma taki amince masa. Wallahi taji dadi, her life is so magnificent. Yanzu ni kadai ce a cikin ku banida saurayi kenan?” Amina ta fada tana marairace fuska.
Khady ta tabe baki tace “Gaskiya kam Amina, i feel your pain”.
Samha tana biye dasu a baya tana jin abunda suke fadi. Kamar daga sama taji an janyo ta anyi gaba da ita.
Amina ce taji shiru ta waigo tana fadin “Samha…ina….” sai kuma taga wayam babu Samha babu Alamunta.
“Ina Samha taje kuma?” Ta tambayi khady.
Itama khady ta waigo tana dube dube babu alamun Samha. “Ba yanzu muke tafe da ita ba? Ina kuma ta shiga.
Samha kuwa wasu yan’mata ne suka jata gefe suka soma sauka kasa da ita, suna karasa saukowa suka sata a gaba da tambayoyi suna fadin “wai dan Allah kece kanwar prince?”
Daya daga cikinsu ma tace “kin samu kin isar mana da sakon mu kuwa?”
Samha ajiyar zuciya ta sake sa’anan ta saka hanunta cikin jakarta ta ciro letters din tana mika musu sa’anan tace ” gaskiya ina ganin gwanda kuje ku bashi da kanku”
“Toh taya zamu soma tunkareshi? Baza mu iya bane shiyasa muka zo wurinki dan ki taimaka mana.
“It won’t be convenient wlh, bazaku gane bane”. Samha ta fada musu.
Daya daga cikinsu ce tace “ban gane it won’t be convienient ba, ba yayanki bane?”
Samha ta marairace fuska ta soma fadin “eh toh based on my familiarity with him, baya so ina kawo mishi letters dinan”.
“Toh ai ba ke bace zaki zaban mishi abunda yakeso ba”.
Daya ma tace “ai bashida budurwa ko?”
Samha tayi shiru tama rasa mai zata ce musu, kamar daga sama sukaji ana fadin “waya baku daman da zaku tasa Samha a gaba kuna gaya mata maganganu haka?!”
Cikin sauri dukansu suka dago, nan suka hango Sabah zaune akan rail na staircase ya daura kafansa daya kan daya. Yan matan ne suka sha jinin jikinsu suka soma matsawa da baya.
Sabah ya cigaba da fadin “ko tayi muku kama da yar aiken ku ne?
Yana gama fadin haka Sabah ya mike tsaye ya soma saukowa a hankali har yazo ya tsaya dab da inda suke ya fizge letter din dake hannun samha yana fadin “She’s not your personal delivery service, don haka ina baku shawara ku fita daga harkanta, daga yau sai yau, kar in sake ganin wata a cikin ku ta kawo mata wata banzar sako ta kawo mun.”
Yana gama fadin haka ya watsawa na kusa dashi letters din ya kamo hannun Samha ya soma tafiya da ita yana haurawa saman matakala da ita.
Har sun danyi nisa Samha ta fizge hanunta daga rikon dayayi mata ta juyo tana dubansa sa’anan tace ” wani irin wulakanci ne haka Sabah? Akan me zaka aikata haka? Waenan letters din cike suke da tarrin so da kaunar da suke maka!”
Wani irin kallo Sabah ya watsa mata sa’anan yace “kanki daya kuwa? Ba shiyasa nace bana son su ba”.
“Ni bance kayi accepting dinsu ba! Amma abunda kayi yanzu zaiyi hurting feelings dinsu. Bai kamata ba!” Ta karasa maganar tana kallonsa kamar zatayi kuka.
Wani irin haushi ne ya soma tasowa Sabah ya kawar da kansa gefe yana kokarin controlling anger dinsa. Ajiyar zuciya ya sake daga bisani yace “fine naji, I’m going to read every letter amma ki sani disappointment is inevitable. Hurt is not. Don haka kar su sa rai”.
Hannu yasa ya tallafo gefen fuskarta ya matso da ita dab dashi har suna iya shakar numfashin juna sa’anan ya cigaba da fadi, muryarsa kasa kasa ” kirkin ki yayi kanwata”.
Lips dinsa na kasa ya kamo ya soma ciza a hankali yana karewa kyakyawar fuskarta kallo. Idanunsa ne suka sauka kan soft lips dinta ya kura musu ido daga bisani ya zube idanunsa cikin nata, ya sake murmushi sa’anan yace ” Idan kin gama, ki sameni a restroom na department dinmu” yana gama fadin haka ya saketa ya juya ya kara gaba ya tafi ya barta tsaye a wajen. SeeBayan tafiyan Sabah, cikin sauri Samha ta dawo inda yan’matan suke tsaye tazo ta tsuguna ta kwaso letters din, hakuri ta sake basu sa’an ta kara gaba tabi bayanshi.
Tana zuwa restroom bata sameshi ba, su Zack ta tadda, nan suka sanar da ita cewa yana wajen senate taje can zata sameshi.
Tana isa senate building , nan ta hango shi kishingide akan daya daga cikin seats da aka zube wajen flowers din jikin senate building, ya lumshe idanunsa kamar yana bacci.
Tana karasowa inda yake kwance ta tsaya tana kare mishi kallo daga bisani tayi gyaran murya tana fadin “Ga sakkoninka nan na kawo maka”.
Sabah ya bude idanunshi a hankali ya zube su cikin nata yana kallon cikin kwayar idanunta. Bai ce mata komai ba illa hanunsa daya mika mata alamun ta bashi letters din.
Babu musu Samha ta mika masa, nan ya gyara kwanciyarsa ya soma karanta sakkonin dayan bayan daya. Samha tana tsaye tana kallonsa sai faman kaiwa da kawowa takeyi, duk tabi ta rasa sukuni kirjinta na bugun uku uku.
Sai daya gama karanta sakkonin tass ya dan sake murmushi ya dago yana dubanta sa’anan yace ” wai ku mata gani kukeyi waenan shirmen da kuke rubutawa zasuyi tasiri akan mutum ne ko meye?”
Samha shiru tayi tana kallonsa daga bisani ta bashi ansa da “eh mana. Kai yanzu daka karanta baka ji komai ba?”
Sabah ya bata ansa da ” Mai zai hana, ko wani sako dauke yake da kalamai masu sanyaya rai”.
Gaban Samha ne taji ya fadi nan take kuma ta soma jin wani iri tace ” da kanata yi kamar baka so yanzu kuma ka canza ra’ayi ne ko me?” Ta tambayeshi tana kawar da kanta gefe. Kar dai sakkonin da’ya daga cikinsu ya kwanta masa a rai ne? Ta tambayi kanta gabanta na faduwa.
Sabah ya katse mata tunani da ” toh kefa da kike tayi kamar wata babbarsu duk kinbi kin tayar da hankali akansu. Yanzu me naki a ciki idan nace na canza ra’ayin”
Samha bata damu tace “sai ka fada mun, da kake karanta letters din ya kaji?”
Sabah shiru yayi yana nazari daga bisani ya dago ya bata ansa da “kishi na dinga ji”
Murmushi Samha ta sake tana maimaita abunda ya fadi “kishi ka dinga ji?”
Sabah ya mike daga inda yake zaune ya karaso yazo ya tsaya dab da ita yana fadin ” A lokacin da nake karantasu, ba abunda ke mun yawo aka illa tunanin irin feelings din da kika dinga ji game da Amjad a lokacin da kike rubuta mishi wanan letter din”
Samha ta marairace fuska ta sunkuyar da kanta ta soma magana a shagwabance” wai dan Allah kai baka mantuwa ne? Abunan fa ya rigada ya faru tun baya shekaru aru aru, sai ka dinga dauko maganar daya rigada ya wuce”
Sabah shiru yayi ya kura mata ido yana kallonta bai ce komai ba. Samha ta kara marairacewa tana fadin “toh shikenan naji, da farko tunanina ne yasoma zuwa wani direction idanuna sun rufe ban san me nake tunani ba”.
Still shiru yayi yana kallonta bai ce komai ba. Dataga Kame kamen nata bazaiyi tasiri ba yasa ta soma fadin “badai hakuri kakeso na baka akan wanan abun ba? Toh shikenan kayi hak…..”.
“Lafiyan ki?” Ya katse ta “kin wani sunkuya Kinata faman kallon kasa, taya zakiga hasken gabanki?”
Samha a hankali ta dago ta zube kyawawan idanunta cikin nashi. Shima kallonta yakeyi sa’anan yace “kina ganin hasken yanzu?”
Samha murmushi ta sake idanunta kyam a kansa don ta rigada ta gano nufinsa. Wato yana nufin shine hasken gaban nata kenan. Murmushin fuskanta ne ya dadda karuwa ta cigaba da kallonsa tana jin feelings dinta akanshi yana dadda karuwa.
Dayaga kallon ya soma yin yawa ne yasashi fadin “oya kallon ya isa haka, kin wani bude idanu kinata faman bin mutum da kallo. Taya kike so nayi kissing dinki a hakan?”
Samha tana jin abunda ya fadi tayi sauri ta matsa da baya tana fadin ” tabdijan, wa zakayi kissing? Ba dai a nan waje cikin bainin jama’a kakeso kayi kissing dina ba?”
Sabah ya daga mata gira daya yace “Toh sai meye. Kema kin san bana shakkan kowa anan”.
Samha tace “toh ba dani za’ayi wanan aika aikan ba a idan duniya”.
Sabah murmushi kawai ya sake ya juya ya soma tafiya. Har ya danyi nisa sai kuma ya juyo yana dubanta sa’anan yace ” ki sani kanwata, bazan taba iya kyaleki ba, ko ba da’di ko ba jumawa ina nan tare dake a duk inda kike, saboda ni nan Sabah, nine zan zamo *Zabin ki*” yana gama fadin haka ya juya ya cigaba da tafiyarsa.
Wani irin dadi da farin ciki ne ya lulube Samha da jin kalamansa. Cikin sauri ta soma bin bayansa har tazo ta tadda shi, suka soma tafiya tare suna hiransu yana tsokananta.
Basu lura ba, Jabbar yana tsaye a jikin motarsa daga can gefe yana kallonsu. Wani irin kishi ne yaji ya taso masa dayaga Samha da Sabah suna tafiya tare. lips dinsa na kasa ya kamo ya soma ciza a hankali yana aiyano abubuwa kala kala a ransa har suka bace masa daga gani.
Da yama bayan an gama lectures, misalin karfe shida na yamma. Samha na tafiya ita kadai cikin layinsu. Don yau Ammi bata samu lokaci tazo ta dauketa a school ba tace mata ta dawo gida kawai da kanta.
Tafiya takeyi cikin sauri don ta samu ta isa gida da wuri, ga ko ina yayi shiru sai motoci dai dai da suke wucewa kasancewar unguwan nasu GRA ne, yamma nayi zaka ga mutane sun ragu kowa na cikin gidansa.
Wayarta ce ta soma ringing, tasa hannu ta ciro daga cikin jakanta, bakuwar number ta gani a rubuce a gaban screen din, ajiyar zuciya ta sake, ta daga kiran ta kara a kunnenta hade da sallama.
Bakon murya ne taji ya ansa sallamarta yana fadin ” Ajiyar zuciyar me kuma kikeyi yan’mata”.
Cikin sauri Samha ta daga wayar daga kunnenta tana karewa screen din kallo sa’anan ta sake karawa a kunnenta “Taya kasan na saki ajiyar zuciya?” Ta tambayeshi.
From nowhere taga an jefo gwangwanin barasa a gabanta. Dagowan da zatayi kawai taga mutum tsaye a gabanta. Kuma ba kowa bane illa Jabbar da waye shima ya kara a kunnenshi, kyakyawar fuskarsa dauke da murmushi yana kallonta.
Gaban samha ne yayi wani irin faduwa data ganshi, nan da nan ta soma matsawa da baya.
Jabbar dariya ya sake ya soma fadin “Haba yan’mata, matsawa da bayan me kikeyi kuma sai kace kinga wani dodo?”
Samha bata bashi ansa ba sai faman zaro ido takeyi tana kallonshi.
Jabbar dayaga taqi bashi ansa ne yasa ya cigaba da fadin “ya naga kina tafiya ke dai, ki zo muje na rage miki hanya” ya fada yana kokarin kamo hannunta.
Samha ta fizge tana fadin “Dallah mallam meye haka? Yanzu kuma bibiyata ka koma yi? bana fada maka ka fita daga harkata ba? Nace maka bana so ka rabu dani mana!” Samha ta fada mishi a tsawace ta juya ta soma tafiya cikin sauri.
Har ta danyi nisa wayarta ta soma ringing, ta dan tsagaita da saurin nata ta duba wayan taga shi dinne ke kiranta. Tsaki taja ta cigaba da tafiya, sai daya mata kira kusan so bakwai sa’anan ta daga, zata balbale shi da masifa kenan taji muryansa ya canza ya somayin magana kamar wanda yake cikin maye yana fadin “Samha meyasa kike mun haka? ki taimaka wa rayuwata mana ki saurareni, wlh zan iya mutuwa idan baki soni ba”.
Samha ranta ne ya bace ta bashi ansa da “ai sai ka mutu din”.
“Haka ma zaki ce? Toh shikenan, gwanda ma da Allah yasa baki shiga cikin motan don yanzu haka a bige nake kuma komai zai iya faruwa.” Yana gama fadin haka taji ya katse kiran.
Gabanta ne ya fadi ta waigo cikin sauri ta hango shi nan tahoha da mota yana sharara wani irin gudu har yazo ya wuce ta.
Samha a rikice ta soma fadin “Jabbar! Jabbar dan Allah ka tsaya, amma inaaaa bai ma san tana yi ba.
sai daya zo daidai karshen layin yayi wani irin shan kwana da motar yazo ya daki wata katuwar pipe dake kan gefen hanya. Nan da nan pipe din ta fashe ruwa ya soma fesowa tako ina, da kyar ya samu ya taka birki motar ta tsaya.
Samha cike da faduwar gaba, kirjin ta na bugun uku uku ta soma gudu har tazo inda motar ta tsaya. Gani tayi kofar gaban ya budu, Jabbar ya fito da kyar. Cikin sauri Samha ta karaso inda yake, cike da damuwa ta soma tambayarsa ko yaji ciwo.
Wani irin dariya Jabbar ya sake yana fadin “Ashe kin damu dani. Daman nasan kin damu dani Samha, kinada kirki sosai kuma nasan bazaki mun karya ba. Na jima ina kishi da Sabah amma shi bai sani ba. kuma gashi kin kusan zama kanwarsa, so babu wani zancen soyayya a tsakanin ku don idan kuka aikata hakan ba karamun matsala hakan zata janyo masa ba, tunda kinga mahaifinshi shine mai makarantar mu, kuma sanane ne sosai a kasan nan. Idan hakan ta faru meye kike tunanin mutane zasu ce idan suka gano cewa ‘danshi yana soyayya da yar’matanshi? Uhmm?” Jabbar ya karasa maganan yana wani irin dariya wanda bashida ma’ana.
Samha ji tayi gaba daya maganganunsa sun cika mata kai. Babu shiri ta tureshi ta juya ta soma tafiya cikin sauri ko waigawa batayi ba. shi kuma ya cigaba da bin bayanta da dariya har ta bace masa daga gani. Dariyan ne ya canza ya soma dawo masa tari, yasa hannu ya dafe kirjinsa yana wani irin tari har ya fadi a kasa. Da kyar dai tarin ya samu ya lafa masa, ya kamo kofar motar da kyar ya mike ya shiga ciki ya zauna yana fitar da numfashi sama sama.
Samha kuwa da kyar ta samu ta karasa gidansu hankalinta a tashe sai faman haki takeyi. Bata tarar da Ammi ba, nan da nan ta haura sama zuwa dakinta, babu abunda ke mata yawo a ka illa maganganun Jabbar. Tasan tabbas maganganusa akwai gaskiya a cikinsu don babu yanda za’ayi soyayyarta da Sabah ya dore in har dai iyayensu sukayi aure. A daren ranar dai Samha da kyar ta runtsa.
Washe gari da safe, Sabah ne zaune akan dining yana karyawa shi kadai, Alhaji muazzam ne ya karaso hannunsa rike da plates din soyayyen kwai yana fadin “Babyboy, ga abincin nan ka kara, kasan breakfast yanada muhimanci sosai a jikin mutum don haka kaci ka koshi kaji koh” ya fada yan ajiye plate din a gaban sabah shima yaja seat daya ya zauna.
Sabah bai ce mishi kala ba ya cigaba da cin abinci dake gabansa.
Alhaji muazzam ya murmusa yana kallon dan’ nasa sa’anan ya cigaba da fadin “Baby boy karka manta fa yau’ kakarka zata zo daga lekki.”.
Sabah bai dago ba ya bashi ansa da “Allah ya kawota lafiya amma gaskiya yau akwai aikin school project dina dazan yi. Bazan samu lokaci ba”. Ya fada yana cigaba da cin abincin dake gabansa.
Alhaji muazzam ya saki ajiyar zuciya sa’anan yace “Sabah… meyasa kake haka ne? karka manta fa mahaifiyata ce kuma itace kakarka. Tun kana karami ita take kula da kai har ka kawo haka”.
“Naji Abbah, Amma kamar dai yanda nace Allah ya kawota lafiya.”
Alhaji muazzam ya ansa da Ameen sa’anan ya cigaba da fadin ” Sabah inaso ka sani wanan zuwan da mahaifiyata zatayi ba komai bane zai kawota illa akan maganar aurena da mahaifiyar Samha, inaso tazo su samu su gaisa. Nayi magana ma da kawunka shima yace yana nan tafe cikin satin nan. So nake a samu a tsayar da magana.”
Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci zuciyar Sabah daya ji mahaifinsa ya dauko batun maganar aurensa da mahaifiyar Samha amma yayi kokari ya danne ya cigaba da cin abincin dake gabansa tunani kala kala na masa yawo aka.
Anya kuwa wanan auren bazai kawo musu karshen koma meye dake tsakaninsa da Samha ba? Ya tambayi kansa amma bai samu ansa ba.
Toh Readers me kuke tunanin zai faru tsakanin Sabah da Samha da kuma auren da iyayen nasu zasuyi?
Kuma shin wanene Jabbar daya shigo musu kwatsam cikin rayuwarsu?
I need your inputs too.🥰
A ranar Samha na dawowa daga makaranta, Ammi tace ta Shirya zasu je gidansu Sabah su gaishe da surukarta wato Hajiya Bilkisu.
Samha jikinta ne yayi matukar sanyi data ji cewa zasu gidansu Sabah su gaishe da kakanshi kuma tasan wanan zuwan da zasuyi, na so ne a gana kuma a samu a tsayar da maganar aurensu.
Jiki a sanyaye Samha tace “toh Ammi”.
mikewa tayi ta shiga bayi tayi wanka, ta fito ta soma shiri cike da sanyin Jiki. Bakar Abaya ta sanya hade da bakin gyale, fuskarta babu makeup don powder kadai ta shafa.
Bayan ta gama ta sauko kasa ta tadda Anty fanneh zaune kan kujera tayi jugum sai faman tunani takeyi.
Cikin sauri Samha ta karaso ta nema wuri ta zauna kusa da ita tana tambayarta “Ammi? Ya kuma naga kinzo kin zauna kinyi tagumi. Meya faru?”
Anty fanneh ta saki ajiyar zuciya sa’anan ta dago tana dubanta tace “Samha ban San meyasa nake tajin faduwar gaba a game da haduwar nan da zamuyi da mahaifiyar Abban Sabah ba. Kuma na samu labari cewa matan tanada tsauri dayawa. Anya zamu shirya da ita kuwa? Ni fa dabadin Abban Sabah ya matsa mun da muzo mu gaisa da ita ba. Babu inda zani”
Samha ta suke nanauyar ajiyar zuciya sa’anan tace “Ammi ki kwantar da hankalinki, insha Allah komai zai tafi yanda akeso. Baza’a samu wata matsala ba”.
Itama Samha jikinta ne ya karayin sanyi data tuno kalaman Jabbar a game da soyayyar dake tsakaninta da Sabah. Cike da sanyin jiki ta cigaba da kallon Ammi tana fadi can kasan zuciyarta “Ammi kiyi hakuri, ni kaina ban san ya akayi hakan ta faru ba na fada tarkon son dan’ wanda zaki aura. Son Sabah ya rigada ya gama kama ruhina, yayi mun kamun kazan kuku, ban san taya zan cire sonshi a raina ba. Ki gafarce ni Ammi don ina fargaban abunda zai faru nan gaba”.
Ammi ce ta katse mata tunanin da takeyi ta mike tana fadin “Baby, kin gama shiri? Driver din gidansu na kan hanya shi zai zo ya dauke mu”.
Samha tace mata a shirye take, bafi minti goma ba sai ga kiran Alhaji muazzam nan ya shigo wayarta, ta daga yace mata gasu nan sun iso. Haka suka fito tare samha na biye da ita a baya suka shiga mota.
Driver ne da Alhaji muazzam zaune a seat din gaba, Samha da Anty fanneh suna zaune a baya. Suna isa gidan, mai gadi ya bude musu gate suka shiga sukayi parking.
Alhaji Muazzam ya fito yazo ya budewa Anty fanneh kofar bayan ta fito. Murmushi ya sakar mata, itama ta dan sakar masa amma still cike take da fargaban haduwa da mahaifiyar nasa.
Shima ya lura da hakan, nan ya soma binta da baki yana janta da wasa yana kokarin kwantar mata da hankali har suka karasa ciki, Samha na biye dasu.
Sallama sukayi suka shiga cikin parlourn. Babu kowa a ciki suka karasa suka samu wuri suka zauna. Alhaji Muazzam yace musu Hajiya tana sama.
Yar aiki ta shigo ta kawo musu kayan motsa baki ta jera musu a gabansu sa’anan ta koma kitchen.
Alhaji Muazzam ne ya haura sama. Samha ta matso kusa da Anty fanneh ta kamo hannunta tana shafawa a hankali ta soma kokarin kwantar mata da hankali.
Can bayan minti biyar suka soma jin sautin saukowa daga saman matakala. Wata dattijiwar mata ce wace akala zata kai shekara saba’in zuwa sama ta sauko, Fara ce sosai matan kuma tana da kyau don daga gani tayi tashen kyau lokacin kuruciyar ta. Sanye take cikin wata tsadaden lifaya, ga fararen glasses manne bisa fuskarta. Hajiya Bilkisu kenan, mata ce wanda ake ji da ita sosai a garin eko, yar boko ce sosai don har P.h.d ne da ita tazama proffesor har tazo tayi retire.
Karasowa tayi cikin parlourn tazo ta samu wuri ta zauna akan daya daga cikin kujerun.
Anty fanneh da Samha suka gaisheta cike da girmamawa “Sannu da zuwa hajiya, kin zo lafiya. Ya mutanen gida?”
fuskar hajiya Bilkisu babu yabo babu fallasa ta ansa gaisuwar idannunta kyam akan Anty Fanneh.
Suna cikin gaisawa sai ga Sabah nan ya sauko, sanye yake cikin kaftan blue da hula blue, yayi kyau sosai sai faman baza kamshi yakeyi.
Yana karasowa cikin parlourn ya wani sha mur ya daure fuska, sama sama ya gaishe da kakan nashi, Anty fanneh ma ya gaisheta sama sama, bai ma bari sun hada ido da Samha ba ya juya zai tafi.
Har ya kai bakin kofar fita daga parlourn, Hajiya Bilkisu ta kwada mishi kira, fuskarta a daure tace ya dawo nan.
Babu daman musu, haka Sabah ya dawo sai faman cicin magani yakeyi. Hajiya Bilkisu ta dubeshi sa’anan ta dawo da dubanta ga Alhaji Muazzam ta soma magana ranta a bace tana fadin “Muazzam kaga ‘dan naka ko?ai gashi nan, ka bari yaro ya girma ya bandare sai abunda yaga dama yakeyi baka tsawata mishi, ka zuba ido kana kallonshi. Ace yanzu ya ganmu zaune da baki a parlour ko kyakyawar gaisuwa mun gagara samu ya kada kai zai fita? Don ya mayar da kowa sa’aninsa?!
Alhaji muazzam hakuri ya soma bata yana kokarin kwantar mata da hankali. Ya juyo yana duban Sabah dake tsaye yana jinsu yace “kai jeka nema wuri ka zauna. Ana magana ka tsaya kana jin mutane”.
Sabah bai ce komai ba yaje ya nema wuri ya zauna sai faman cicin magani yakeyi, ya daure fuska sosai. Shiyasa tunda tazo gidan yaketa faman kakauce mata don yasan halinta sarai da masifa bata taking nonsense. Duk iya abunda zaiyi a gidan nan Abbanshi ne kawai yake iya shanyewa amma da zaran sauran yan family dinsu sun zo gidan sun dinga surutu kenan akan Sabah wai shi baya son mutane. Shi kuma ko ajikinsa don baya takansu har su gama abunda ya kawosu su bar gidan.
Hajiya Bilkisu bata tsaya nan ba sai faman zazaga balai’ takeyi. Anty fanneh ce ta soma bata hakuri tace “Hajiya kiyi hakuri. Kin san halin yaran namu na yanzu sai a hankali”.
“Ai kuwa kema zakiyi fama indai akan Sabah ne, yaro kwata kwata bai ganin kowa da gashi? Bai san girman na gaba dashi ba?”.
“Mami kiyi hakuri insha Allah zan zaunar dashi nayi mishi fada. Bazai sake ba”. Alhaji muazzam ya fada mata.
“Ai kuma sai kayi. Tunda ba’ayau nake jin haka ba”. Ta fada ranta a bace, sai data danyi nesa tukuna ta dawo da dubanta ga Anty Fanneh tana fadin “sai kin hada da hakuri, tunda tun yanzu kin soma ganin halin dan’ naki. Sai addu’a”.
Anty fanneh murmushi kawai ta sake sa’anan tace “babu komai hajiya. Insha Allah zai canza. Kuruciya ne kawai ke damunsa”.
Nan Hajiya Bilkisu ta samu ta sauko, aka dan soma taba hira da sauran su. Sabah dai bai ce musu kala ba kuma bai sa musu baki cikin maganarsu ba. Wayan shi ya ciro ya soma lalatsawa.Itama Samha shiru tayi tana jinsu bata ce komai ba, sai faman satan kallon Sabah takeyi.
Hajiya Bilkisu ce ta dinga lura da yanayin Anty fanneh kuma taga yanayinta kamar baza’a samu matsala ba. Daman ita matsalar ta daya, a samu wace takeda hakuri don tasan yanayin dan’ nata kuma tasan auren dayayi na farko ba aji dadinta ba, shiyasa wanan karon, take so ya samu wace zata fahimce shi sosai, su zauna lafiya. Hankalin kowa ma ya kwanta.
Bayan sun dan taba hira, Anty fanneh tace zasu wuce. Daman sunzo ne su gaisheta tunda sunji tazo. Hajiya Bilkisu tayi godiya, nan sukayi sallama. Alhaji muazzam ya mike suka fito har cikin gida yayiwa driver magana, suka shiga cikin mota yaja su suka tafi.
Bayan tafiyan su Anty fanneh, Sabah mikewa yayi ya haura sama. Hajiya Bilkisu tabi bayanshi da kallo tana girgiza kai.
Alhaji Muazzam na dawowa cikin parlourn ta soma tambayarshi tana fadin
“Toh ya kuka tsayar da magana, kaninka yace zai dawo cikin satin nan. Kuma nayiwa kanin mahaifinku magana da sauran yan’ uwa, sunce suma zasu zo sai a samu a tsayar da magana. Kaga wanan ba shine aurenka na fari ba, daga kai har ita ba yara bane, so za mu samu a gana da mutanen ta sai a tsayar da lokaci kawai, kuma baza wani dau lokaci ba. Ana daura auren sai ta tare, Ko ya ka gani”.
Alhaji muazzam yace “haka ne mami, don jiya ma nayi magana da kawu Aliyu yace ko cikin wanan watan da zamu shiga sai a samu a daura kawai.”
Hajiya bilkisu tace “Toh shikenan, Allah ya tabbatar da alkhair, kuma na lura da ita kamar bazata baka matsala kamar mahaifiyar Sabah ba. Naga wanan tanada nutsuwa sosai ga hankali.”
“Haka ne Mami, nima haka nake gani, insha Allah baza’a samu wata matsala da ita ba”.
Hajiya Bilkisu tace ” yayi kyau, Allah yasa. Toh yanzu ya batun maganar karatun ‘dan naka da, nasan yanzu yana gab da karasawa, kuma kasan kayida ne a wanan family din. Ko wani babban da’ namiji idan ya kai ga shekaru kuma ya kammala karatunsa dole ne yayi taking over na family business. Ga kamfaninunka birjik Allah yasa albarka sai kara bunkasa sukeyi, don haka tun wuri ka sanar dashi, ya kama kanshi don naga kanshi na rawa. Ya shirya yana kammala degree dinan nasa zai kama business”.
Alhaji muazzam yayi shiru yana jinta daga bisani ya dan sosai kai yana fadin “Mami, nasan da hakan, amma kinga Sabah har yanzu yaro ne, duka duka Sabah guda nawa yake dazai rike family business a yanzu haka?. A dan bashi lokaci koda nan gaba ne, har ya samu ya kara da masters dinshi tunkuna”.
“Ai kaga irinta, idan nace kana bata yaron nan kace ba haka ba, kace Sabah yaro ne, kana nufin kace mun yanzu Sabah bai mallaki hankalin kansa da zai iya rike daya daga cikin companies na family dinnan ba? Sao’insa nawa ne yanzu suna tafiyar da aikinsu kuma har suna rike da iyalai?eh?”
“Haka ne mami, na san da haka amma…”
“Yimun shuru, banso na kara jin komai daga bakin ka. Kuma na gaya maka, Sabah yana kammala degree dinsa shi zai kama family business dinan. Tunda shi ne baban da namiji a cikin jikokina. Ina yaran kaninka duk mata ne, kuma nan da kankanin lokaci duk aure za ayi musu. Don haka ban san naji komai. Daga kai har shi kuje kuyi shawara don decision na rigada na yanke babu gudu babu ja da baya”.
Alhaji Muazzam babu yanda ya iya haka yace mata “toh shikenan mami, za’ayi yanda kika ce”.Washe garin ranar, Samha tana zaune cikin daki tana shafa mai a jikinta don bata jima da fitowa daga wanka ba.
Wayarta ce ta soma ringing, ta dauko taga sunan Sabah a rubuce a jikin screen din.
Nan da nan ta daga ta kara kunnenta, don rabon data jishi ko ta sanya shi a idanu tun jiya a gidansu.
Dadaden muryan shi mai sanyaya mata rai ako da yaushe idan taji ne ya doki kunnenta yana fadin “Kanwata?”
“Na’am?”
“Ki fito yanzu, gani a kofar gida”.
“Ban gane ba, wani kofan gida kuma?”
” oho, in zaki fito ki fito”. Yana gama fadin haka ya katse kiran.
Dago wayar tayi daga kunnenta tana kare ma screen din kallo.
Anya kuwa da gaske yake? To meya hanashi shigowa, ya tsaya a waje? Ta soma tambayar kanta.
Nan kuma ta soma tuno da abubuwan da suka faru a jiyan. Jiki a sanyaye ta soma sa kaya tayi shirinta tsab cikin wata doguwar riga Ash da kuma black veil, power tadan shafa a fuskarta da dan shafa man baki, sa’anan ta dauko turaruka ta feshe duk ilahirin jikinta dashi, ta fito daga dakin ta sauko kasa, tana isa kofar gida ta hango shi tsaye ya jingina da jikin motarsa.+
Sanye yake cikin black jeans da black tshirt sai black face cap.
Komai na jikinsa black ne harta, motarsa ma baka ce.
A hankali Samha ta tako har inda yake tsaye jingine a jikin mota. Yasa hanunsa duka biyu rungume bisa kirjinsa ya kura mata ido har tazo ta tsaya a gabansa.
Itama ido ta kura masa, tasa hannunta duka biyu ta rungume bisa kirjinta kamar yanda yayi ta tsaya tana kallonsa.
Sai da suka kalla juna har na kusan minti biyar, kowa da yanda yakeji game da dan uwansa.
Barin ma Samha, wanda ganinshi yanzu yasa ta kara jin wani irin sanyi a ranta. Anya kuwa zata iya rayuwa babu Sabah? Don sonshi a yanzu ya gama kama duk gabobin jikinta, da sonshi take kwana da sonshi kuma take tashi a kullum.
Jiki a sanyaye ta kira sunansa a hankali ta soma fadin ” Sabah…..bansan yanda zanyi ba, na kasance inada zuciyar da take matukar sonka Sabah. Kuma banjin zata iya daina sonka.” Ta fada mishi kwalla na ciko mata cikin idanu. Don a yanzu haka tausayin kanta takeji.
Bata tsaya nan ba, ta cigaba da fadin “a kullum sonka dadda karuwa takeyi cikin zuciyata, Amma a duk sanda na kalli ammi na sai naji kamar banida kirki bai kamata ace na fada tarkon son dan’ wanda zata aura ba. Gani nakeyi kwata kwata ban kyautata mata ba. Da wani ido zan kalli ammi idan ta gano haka? Wani irin kallo mutane zasu dinga mana? Ni nasan bazan taba daina sonka ba Sabah, nasan kanada burden sosai a rayuwarka wanda ba kowa bane yasan dashi ba, ni kaina i’m feeling helpless gani nakeyi I won’t be enough for you. Ban cancanci ace ni ce nafi kowa muhimanci a cikin rayuwarka ba” Samha ta fada tana rushewa da wani irin kuka mai tsuma rai.
Wani irin tausayinta ne ya lulube Sabah yaji gabadaya shima jikinsa yayi sanyi. Hannu yasa ya janyota kusa dashi ya soma rarashinta yana fadin ” shhh ki daina wanan kukan kanwata, kuma waya fada miki cewa kinfi kowa muhimanci a rayuwata?” Ya tamabayeta cike da zolaya yana mata murmushi.
Itama murmushin ta dan sake tana sheshekar kuka tace “ban sani ba. It’s just that i like you too much, i want to say it out loud, kowa ma yaji”.
“Then say it! Nasha fada miki ki daina bari tunanin abunda mutane zasu fadi ya dameki. Don ni a shirye nake da kowa ma ya sani”. Ya fada mata yana kallon cikin kwayar idanunta.
Hannu yasa ya soma share mata hawayen dake gangarowa bisa kuncinta ya cigaba da rarashinta.
Basu sani ba, Jabbar zaune yake ta daga can kasan layi cikin motarsa yayi parking hanunsa rike da camera yayi zooming sai faman musu video yakeyi. Tun daga fitowarta, da maganganun da sukeyi, da kuma rarashinta da Sabah ya dinga yi yana share mata hawaye duk yayi recording.
Har Sabah ya gama rarashinta sukayi sallama ta shiga cikin gida, shi kuma Sabah ya shiga cikin mota yaja ya bar layin Jabbar sai faman recording yakeyi basu sani ba.
Wani irin shu’umin murmushi Jabbar ya sake don yana ganin cewa ya kusan cima burinsa.
*******************
A kwana a tashi, yau kwana biyar kenan rabon su Samha da gidansu Sabah inda sukaje suka gaisa da Hajiya Bilkisu.
Yau ta kasance safiyar ranar litinin, su khady suka hadu a school sukaga Samha gabadaya yanayinta sai a hankali gashi jikinta duk yabi yayi sanyi sai faman yin abubuwa takeyi cike da sanyin jiki kamar wata mara lafiya.
Ita samha babu abunda yake damunta illa batun Sabah da yanda soyyayarsa yake ta faman horuwa cikin zuciyarta, ga kuma Jabbar daya sata a gaba, a kalla a rana daya sai yayi mata kira da sakoni fiya ga hamsin, wani sa’in ma idan abun ya isheta, kashe wayanta takeyi gabadaya.
Su khadija da suka lura da yanayinta, basu sake cewa komai ba, haka suka karasa lecture hall don suyi next lecture dinsu.
Bangaren su Sabah kuwa, zaune suke cikin class, lecturer din daya basu project Dr Sageer ne yake tsaye a gaban aji yana musu magana akan aikin project dinsu, yace sunyi kokari sosai don har makaranta ta zaba group din da za’a turawa company project dinsu. Nan ya soma announcing results din kamar haka.
“Number one position goes to group 5, which includes Zakari dan fulani, Abba suleiman, Sabahudeen Muazzam Arrayan, Sanusi Sani Sakatare” lecturer din ya soma lissafo sunayensu, Zack dasu Shinoh cike da murna da farin ciki suka mike tsaye. Amma banda Sabah wanda yake faman bin lecturer din da kallo cike da mamaki, don shi bai taba tunanin group dinsu zasu zama na daya a wanan project din ba. Anya kuwa? Tunani kala kala ne suka soma masa yawo aka.
Suna hada ido, dr Sageer ya aika masa da wani irin kallo, nan Sabah yaja jinin jikinsa don yasan akwai wani abu a kasa. Haka kawai bazasu zo na daya a wanan competition din ba.
Nan wata zuciyar ta soma ayano masa cewa anya babu hannun Abbansa ko ma lecturer din a cikin wanan? Bawai shida abokananshi basuyi kokari bane, a’a yasan sun raba dare suna fama akan aikin project din amma zuwansu na farko gaskiya its suspicious.
Sabah ba don yaso ba haka ya mike tsaye, sauran yan ajin suka soma tafa musu ana congratulating dinsu.
***************
Bayan an gama lectures, khady da Amjad suna zaune a cafetaria suna shan lemu suna dan taba hira, Amjad yaga khady tayi shiru tayi zurfi cikin tunani ya soma tambayarta “sweetheart lafiya? Yanaga duk kinyi shiru gabadaya kinyi wani iri ba yanda na saba ganinki ba.”
Khady ta dan saki ajiyar zuciya sa’anan tace “ai dole ka ganni haka”.
“Meya faru?” Ya tambayeta.
“Samha ce, gabadaya mun kasa gane kanta wlh”.
“Samha kuma? Toh meke damunta?”
” nima ban sani ba, amma bazai wuce soyayyarta da Sabah ba”.
Amjad ya dan tabe baki sa’anan yace ” toh ai duk wacce tace zatayi soyayya da Sabah, ai ba karamin aiki ta dora wa kanta ba”.
Khady ta dan kai mishi hararan wasa tana fadin ” ai bama wanan ba, akwai wani yaro ne daya sata a gaba, wai sunanshi Jabbar duk yabi ya adabi rayuwarta ya hanata sukuni wai shi yana sonta”.
“Wani yana son Samha? Toh shi Sabah din me yace?”.
“Ai banjin ya san da haka. Don nasan Samha bazata fada mishi ba, sai dai yaji a wani wurin”.
Amjad ya saki ajiyar zuciya sa’anan yace “Allah ya kyauta. Nan suka cigaba da hiransu.
*******************
Bangaren Samha kuwa, bayan sun gama lectures, jiki a sanyaye ta karasa wajen locker dinta zata kwaso sauran takardunta. Tana bude kofar taga wata yar karamar takarda anyi rubutu ciki an ajiye mata, Hannu tasa ta dauko ta soma karanta abunda aka rubuta a ciki kamar haka.
“Ki same ni a restroom, in jiranki”.
– Sabah.
Cikin sauri Samha ta rufe locker dinta, tasoma saukowa kasa tayi hanyar department dinsu Sabah. Tana shiga restroom din ta tadda babu kowa, tana tsaye kamar ance ta juya sai ga mutum nan a bayanta. Jabbar ta gani tsaye da camera a hanunsa yana recording dinta.
Gabanta ne ya fadi ta soma fadin “daman kaine ka rubuta sako ka ajiye mun cikin locker?”
Wani irin shu’umin murmushi ya aika mata bai bata ansa ba ya cigaba da recording dinta da cameran dake hanunsa.
*************
Bangaren su Sabah kuwa, tsaye yake shi kadai a wajen departmental garden dinsu yayi shuru yana nazari, zuciyarsa sai faman tafarfasa yakeyi, ba abunda yake bashi haushi ila tunanin group project dinsu da zuwansu na daya da kuma shi karan kansa lecturer din. Don shi sabah ya jima baya son lecturer din, kwata kwata basu shiri.
Amjad ne yazo wucewa ya hango shi tsaye shi kadai. Ya karaso yazo ya tadda shi yana fadin “Sabah, ya naga kazo ka tsaya a nan kai kadai? Daman inata nemanka tun dazu, inada magana da kai”.
Sabah ko juyowa baiyi ba ya kalleshi ya bashi ansa da “ka fada ina jinka”.
“Batun maganar competition na match da zamuyi next week ne, karka manta, nama rigada nayiwa sauran yan’ team magana”.
“Naji bazan manta ba”. Sabah Ya bashi ansa still bai juyo ya kalleshi ba.
Amjad ya sake ajiyar zuciyar sa’anan ya cigaba da fadin ” Sabah, I understand you’re feeling bad, na fahimce yanda kakeji, amma muna bukatan ka wajen practice dinan, we can’t afford to loose this competition”.
“Ban gane you understand i’m feeling bad ba. Ya nakeji?” Sabah ya jefo mishi tambayar.
Amjad yace ” Au baka sani ba, ai ance wani guy a cikin makarantan nan yana bibiyan Samha. Na zata ka sani”
Haba wani irin bugawa kirjin Sabah yayi, nan take yaji haushin da yakeji ya karu ninkin baninki, hanunsa ya soma dunkulewa, yana jin zuciyarsa na masa wani irin tafarfasa.
Amjad bai tsaya nan ba ya cigaba da fadin “toh nidai ban san ya sauran zancen yake ba amma khadija ta fada mun cewa guy din ya saka Samha a gaba duk inda taje yana biye da ita, kuma naji wai guy din babu laifi yanada kyau sosai”.
Maganganun Amjad kam sai kara harzuka Sabah sukeyi. Suna cikin haka sai gasu Zack dasu Shinoh nan tahowa suka karaso inda su Sabah suke tsaye, shinoh bai lura da yanayin da Sabah yake ciki ba, yazo ya sakala hanunsa bisa wuyan Sabah cike da wasa, ya soma fadin “SB, kaga mun zo na daya, makaranta sun zabe project dinmu za’a turawa company din ko? kai amma naji dadi wallahi, it’s so exciting ” Ya karasa maganar yana jijiga kafadar Sabah.
Haba Sabah wanda ya cika ya gama yin fumm, wani irin turi ya kaiwa Shinoh, ya saka kafa daya ya kai mishi naushi a ciki, shinoh yayi tangal tangal yayi kamar zai fadi.
“Dallah ku rabu dani karku cikani da wani surutu!” Sabah ya fada mishi a tsawace ya juya ya soma tafiya.
Zack bai daddara ba, shima yazo ya sakala hanunshi bisa kafadan Sabah yana fadin “Haba Sabah, ai wanan abun farin ciki ne ya samemu, ko irin dan murnan nan bazaka nuna ba?”.
Shima kyautan naushi ya samu a kirji, Sabah ya tureshi gefe ya fadi a kasa.
Ya cigaba da tafiyansa zuciyarsa na mashi wani irin tafarfasa. Abbah dake tahowa bai san abunda ke faruwa ba, ya tsaya zai mishi magana, Sabah ya hankada shi gefe, babu shiri shima ya kauce ya bashi hanya.
Cike da tashin hankali Abbah ya karaso inda su Zack suke kwance a kasa yazo yasa hannu ya taimaka musu yana tambayarsu “what’s wrong with Sabah, meke damunshi?”
Zack wanda yake rike da gefen kirjinsa inda Sabah ya kai mai naushi, yabi bayansa da ihu yana fadin “Wai meye matsalarka ne?! An bata maka rai shine zaka zo ka jibge akan mu?”
Sabah daya danyi nisa ya ji abunda zack ya fadi ya juyo ranshi a matukar bace, ya hada fuska kamar hadari ya soma fadin ” Dan uban mutum kar wanda yazo ya dameni, wlh duk wanda yayi mistake yazo inda nake sai nayi dai’dai dashi!”.
Yana gama fadin haka ya juya ya cigaba da tafiyansa. Su zack ne suka bi bayansa da kallo cike da mamaki da takaici don su a zatonsu Sabah zai fi kowa murna da wanan nasaran da suka samu.