ZABIN SAMHA CHAPTER 8

 ZABIN SAMHA CHAPTER 8

Bangaren su Samha kuwa, tsaye take da Jabbar a cikin restroom hanunsa rike da camera din yana cigaba da mata video.


Wani irin dariya ya sake yana fadin “Samha, Samha kenan, wato ina ajiye miki sakon kin zata shine, kika zo jikinki na bari? Ya tambayeta yana wani irin dariya.


Samha ta hada rai sai faman zabga mishi harara takeyi “Haba ki dan saki fuskarki mana, kinsan kinfi kyau idan kina fara’a”. Ya karasa maganar yana cigaba da mata dariya.


Samha ta dago paper dake hanunta ta soma tambayarshi “Daman kaine ka rubuta wanan sakon ka ajiye mun?”


“Correct!” Ya bata ansa yana cigaba da murmushi.


“Ai inata tunanin yanda zanyi na janyo hankalinki zuwa gareni. Shine nace bari nayi amfani da sunan Sabah. Sai gashi nan kinyi tsuntsu kinzo”. Ya fada yana dariya.


“Dakata mallam! Wanan wani irin shashanci da rainin hankali ne? Eh!”

Samha ta fada mishi a tsawace. Nan kuma hankalinta ya dawo kan camera dake hanunsa yana mata video.


Cikin sauri ta kawar da fuskanta gefe tana fadin “me kuma kake kokarin yi? Lafiyan ka kuwa Jabbar? video din me kake mun?”


“Haba sweetheart, meye a ciki kuma dan na dauki video din wace nake so? Ai banga wani aibu a ciki ba”. Ya fada yana cigaba da mata video din.


Zuciya ne ya dibi Samha, cikin sauri ta karaso inda yake tsaye tazo ta bige camera din daga hanunsa, ya fadi a kasa tana fadin “So nawa zan gaya maka cewa bana sonka jabbar! Ka fita daga harkata! Don ko meye zakayi bazan taba sonka ba!” Ta fada mishi a tsawace.


Nan da nan murmushin dake fuskar jabbar ta bace, ya kurawa cameransa daya fadi a kasa ido. Tsugunawa yayi yana tattaro camera din ya soma fadin “Saboda ke fa naje na siyo wanan tsaddadiyar camera din, shine zaki yar mun da ita a kasa?”.


Samha bata saurareshi ba ta cigaba da fadin “wallahi wallahi kaji nayi maka rantsuwar musulmi ko Jabbar, ka fita daga ido na na rufe, in ba haka ba sai na sa an sasaba maka a cikin makarantar nan”. Tana gama fadin haka ta juya zata tafi, har ta danyi nisa ta tsaya cak, don jin muryarta datayi cikin recording tana kuka tana fadin cewa tan son Sabah.

Gabanta ne ya tsinke ya fadi data soma jin muryan Sabah shima yana magana, waigowa tayi cikin sauri taga ya daura Camera din kan table yana playing video, gata a manne a gefen Sabah tana sheshekan kuka.


Tafi Jabbar ya soma yi da hanayensa yana fadin “wow, Samha ban san kin iya acting haka ba, jibi yanda kike zubda hawaye, yanzu duk wanda ya gani yasan da gaske kikeyi. Na daga miki hannu,kuma naji dadi danayi capturing din wanan moments din tsakaninki da Sabah”.


Samha a fusace ta katse shi tana fadin ” wai me kakeso ne Jabbar? Why are you doing all this?”


“So nake ki kyale Sabah ki dawo gareni”. Ya fada yana matsowa kusa da ita.


“Tausayinki nakeji Samha, bana so kiyi soyayya da yayanki don babu abunda hakan zai janyo sai baccin rai da raba zumunci. Ki yarda dani Samha, ni mai son farin cikin ki ne. Wanan sirrin naki zan boye miki shi babu wanda zai sani, don haka ki kyale Sabah ki dawo gareni”. Ya karasa maganar yana kokarin talabo fuskarta.


Wani irin wawan mari Samha ta kai mishi a fuska tana fadin “Bakada hankali, an gaya maka ko giya nasha zan tsaya na saurareka ne ballantana na amince nayi soyayya da kai? An gaya maka haka ake soyyaya, kazo ka adabi rayuwata sai faman threatening dina kakeyi. Kana tunanin zan taba son mutum irinka ne?!” Ta fada mishi a tsawace.


Jabbar yasa hannu ya shafo inda ta mareshi yace “ni kika mara Samha?” Murmushi ya sake sa’anan ya cigaba da fadin ” wai ke yanzu gani na kikeyi a matsayin makiyinki ne koh meye? toh bari kiji in gaya miki, tunda kinki ki saurareni, ki jira ki gani duk abunda ya same Sabah nan gaba ke kika jawo.”


Yana gama fadin haka ya juya ya tafi ya barta tsaye wajen. Wani irin faduwar gaba ne ya ziyarci Samha tabi bayansa da kallo. Me yake nufi da duk abunda ya sami Sabah nan gaba ita ta janyo?


Anya Jabbar dinan kanshi daya kuwa? Ta tambayi kanta zuciyarta na mata wani irin bugu.


************


Bangaren Sabah kuwa, tunda ya tafi motarsa yaja ya bar makarantar ma Gabadaya don zuciyarsa wani irin soyuwa take masa idan ya tuno kalamun Amjad inda yake fadin cewa wani yana bibiyan Samha, bai tsaya ko ina ba sai tribute game house.


Nan yaje ya siya tickets ya shiga ya dinga bugawa da sauran players, sai daya buga iya san ransa yayi releasing frustrations dinsa tukuna, nan ma still bai samu nutsuwa cikin zuciyarsa ba. Tsaki yaja ya mike ya fita ya bar wurin.

***********************


Su zack ne zaune a class suna tataunawa akan matsalar Sabah da kuma abunda ke damunsa.


Shinoh dake zaune a gefe yana dane dane cikin laptop dinsa ne ya zaro ido ya katse musu maganar da sukeyi yana fadin “Zack, Abba, anya ba gizao idanuna ke mun ba? I can’t believe this!” Ya fada idanunshi kyam akan screen din laptop dinshi.


“Menene?” Su zack suka tambayeshi a tare.


“Website dinmu ne da group project da mukayi creating. Kamar anyi hacking anyi crashing dinsa. Kwata kwata baya buduwa” ya karasa maganar hankalinsa a tashe sai faman danne danne yakeyi a keyboard.


“What? Yaki buduwa?” Suka tambayeshi suma suka janyo laptop dinsu. Nan suma suka fara danawa suna son su bude amma still the same thing ne yake nuna musu.


“Ku duba na Sabah ko nashi zai budu?”

Abbah ya fada, nan Shinoh ya janyo laptop din Sabah cikin sauri ya fara dubawa.

Na Sabah kuwa hannu daya website din ya budu. Kallon juna sukayi a tare. Toh me hakan yake nufi? Ya za’ayi nasu yayi crashing amma na Sabah yana buduwa.

Kodai Sabah ne yazo ya kara hucewa akan project dinsu, don sun san halinshi sarai idan yayi fushi koma meye zai iya aikatawa.

Rai a bacci shinoh ya soma fadin “wato bayan ya gama hucewa akanmu shine zai dawo kan project dinmu!”


Zack ne ya bashi ansa. “Haba shinoh, meyasa kake magana haka? I don’t think Sabah zai aikata hakan, duba fa irin wahalar da muka sha tare dashi akan creating din website dinan”.


Suna cikin maganganunsu basu lura ba dr sageer wato lecturer din daya basu wanan project din yazo wucewa ya juyosu suna magana cikin ajin. Tsayawa yayi daga bakin kofan ajin yana fadin ” Sanusi, me naji kana fadi akan project dinku? Meya samu website din?” Dr Sageer ya watso musu tambayar.


Shuru sukayi kowa yayi wuri wuri da ido sun kasa cewa komai. Shurun da sukayi ne yasa shi karasowa cikin ajin yana tambayarsu. Nan ma suka ki bashi ansa, yace su kwaso laptop dinsu su biyo shi office.


A ranar dai, daga Samha hatta Sabah basu kasance cikin dadin rai ba, Har zuwa dare Sabah ya kasa samun sassauci cikin zuciyarsa. Gashi babu daman kiran Samha yaji muryarta ko zai samu sassauci cikin zuciyarsa don ya rigada ya buga wayansa da kasa ta lallace kuma duk saboda baccin rai ne.


**************


Washe gari da safe a school, su Zack suka tasa Sabah a gaba suna tambayarsa ko shi yayi crashing website din project dinsu.


“Muna so muji daga bakinka, in har kace bakai bane ka aikata wanan abun ba, toh zamu yarda dakai” Abba ya fada mishi.


“In kuma ban fada ba fa? Still zaku yarda?” Sabah ya jefo musu tambayar.


Shinoh wanda ranshi ya kai kololuwar bacci ne ya katse shi da “kaga already ranmu ya rigada ya gama bacci, zuciyar mu na tafarfasa, don haka ka fada mana gaskiya kawai”.


“Toh ai sai ran naku ya cigaba da bacci don…..”


Shinoh wanda maganganun Sabah sun rigada sun gama kaishi bango, ya harzuka yazo zai kama Sabah da fada, Zack yayi sauri ya tareshi yana fadin “haba shinoh! Meyasa kake haka ne. Sabah kuma zaka kama da fada ko meye? I don’t think shine fa ya aikata hakan”.


“Ku kyaleni! ai ni bance shine ya aikata ba, kawai haushi nakeji don aikin da muka raba dare munayi ya tafi a banza kenan”. Shinoh ya fada yana hucci.


“Wallahi wallahi idan na kama dan iskan daya zo ya bata mana wanan aikin, sai na karasa shi da hanuna”. Ya cigaba da fadi.


Suna cikin haka sai ga dr Sageer nan ya shigo cikin restroom din tare da chief security officer din makarantar sun shigo tare, suna karasowa chief security officer din ya kallesu daya bayan daya sa’anan ya dubi Sabah yace “Sabah come with me”.


yana gama fadin haka ya juya ya tafi, shima dr Sageer ya mara masa baya. Sabah bai tsaya wata wata ba yabi bayansu, haka suka fito tare students sai faman binsu da kallo sukeyi.

Su Samha wanda labari ya kai musu har department ne suka karaso a guje zuwa department dinsu Sabah, nan suka hango shi tare da chief security officer zasu shiga cikin motan security tare.

Samha hankalinta a tashe, tayi yunkuri zata bi bayansu, khady tayi saurin janyota tana fadin “ina kuma zaki Samha? Ki barsu suje suyi investigation mana, In har babu hanun Sabah a ciki, gaskiya zata bayana. Kuma kinga dole makaranta ta dau abun serious tunda kinga an rigada an sanar da company din, kar suga kamar duk abun scam ne, makaranta tana son ta damfare su akan scholarship. Abar su kawai suyi binciken da zasuyi”.


“Wallahi duk setup ne, wani ne ya aikata wanan abun aka zo aka makalawa Sabah. Don nasan Sabah dina bazai taba aikata hakan ba”. Samha ta fada muryanta a raunane kamar zatayi kuka.


Dagowan da zatayi sai idanunta suka sauka kan Jabbar dake tsaye can gefe ya kurawa motar da aka saka Sabah ciki ido yana wani irin murmushi.


Gaban Samha ne ya fadi zuciyarta nan da nan ya aiyano mata cewa shi ne. He’s behind everything.


Jabbar yana ganin an tafi da Sabah ya juya ya tafi, Samha bata tsaya wata wata ba tace wa su khady tana zuwa. Nan ta bi bayanshi, har ya danyi nisa taga ya shige wani lungu kusa da ITC department.

Bin bayanshi tayi, tana shiga lungun kuma taga ya bace mata daga gani. Haka ta dinga dube dube bata ganshi ba. Nan zuciyarta ta bata dataje department dinshi ko zata ganshi a can.


Tana zuwa faculty din Environmental design, Architecture department nan ta samu wasu students a gaban department din suna tsaye, ta karasa tayi musu sallama ta soma musu tambaya “Dan Allah wake 300 level a cikin ku?”


Mutum daya ne daga cikinsu ya bata ansa da “ni ne”.


Samha tace ” dan Allah ina neman wani guy ne mai suna Abdul-jabbar shima yana 300level”.


Wanda tayi wa tambayan yayi shiru yana nazari sa’anan ya girgiza kai yace “gaskiya I don’t think munada wani Abdul-Jabbar a ajinmu. Ya yake?”


“Eh toh, dogo ne sosai kuma fari. Yanada madaidaicin jiki kuma yaro yaro haka”.


“Kai gaskiya I don’t think i know anyone like that a ajinmu”.


Samha jiki a sanyaye tayi mishi godiya ta juya ta soma tafiya. Basu san wani mai suna Jabbar ba? Toh me hakan yake nufi? Haka ta cigaba da tafiya tunani kala kala na mata yawo a ka har ta karaso wajen old building din industrial design.

Jabbar na tsaye a can saman benen old building din industrial design, yana kallon duk movements dinta. Wayansa ya ciro daga cikin aljihu ya soma kiranta.


Samha tana ganin kiranshi tayi picking ta kara a kunne. Wani irin dariya ya sake sa’anan yace “A duk sanda kike tunanina toh ki sani cewa ina nan tare dake”.


Waige waige ta soma yi bata ganshi ba, kamar ance ta kalla sama, ta dago kanta ta hango shi can sama tsaye a balcony yana aika mata da wani irin murmushiSabah zaune yake a office din chief security officer. Chief security officer din ya tasa shi a gaba sai faman mishi tambayoyi yake. Ga dr Sageer nan tsaye a gefe yana jinsu.


“Sabah meyasa ka aikata hakan? Ko kana tunanin hakan zai saka kaci wanan scholarship din kai kadai ne?”+


Sabah ya sake ajiyan zuciya sa’anan ya dago yana duban officer din yace ” haba sir, sai kace banida hankali? i’m not that dumb ai dazanyi amfani da wanan method din”.


“Kai ka iya bakinka, bar gani kamar kaine yaron VC din makarantar nan kana ganin kamar zaka iya karya doka a kyaleka. Kasan irin bad reputation da hakan zai janyo wa makarantar nan kuwa? Toh idan ba kaine ka aikata ba toh waye?”


” Ban sani ba, wanda yakeson yaga baya na ne zai aikata hakan”. Sabah ya fada mishi kai tsaye.


Dr Sageer dake tsaye can gefe ya karaso fuskarsa dauke da wani irin shu’umin murmushi yace “toh wake son yaga bayanka Sabah?”


Wani irin kallo Sabah ya watsawa Dr Sageer sa’anan ya bashi ansa da “duk ma wanda yayi framing dina nasan yanzu yana can yana jin dadi don yana ganin bukatansa ya biya”


Dr Sageer ya jinjina masa kansa sa’anan yace “wato Saba har yanzu kana nan da girman kan nan naka dana sanka dashi baka canza ba”.


Officer din ne ya juya yana duban dr Sageer sa’anan yace “dr, daman kasan yaron nan sosai ne?”


Dr Sageer ya dan nesa sa’anan ya bashi ansa da ” yes, a da can baya kafun na fara lecturing, nine assistant din VC. Kuma ina yawan zuwa gidansu sosai. A idanuna Sabah ya girma, don komai na childhood dinsa duk na sani”.

Sabah na jin abubuwan dayake fadi ya hada rai, ya kawar da kansa gefe kamar ba maganarsa akeyi ba.


Suna cikin haka, sai ga Alhaji Muazzam nan yayi sallama ya shigo cikin office din, chief security officer na ganinshi ya mike nan da nan suka gaisa ya soma fadin “sir, daman inaso nazo nayi reporting wanan case dinne muna gama investigation.”


Alhaji Muazzam yace mishi “no don’t worry, karka damu an rigada anyi briefing dina tun a office”.


Officer din jiki na bari yayiwa Alhaji Muazzam nuni da kujera daya zauna. Alhaji Muazzam yaje ya zauna yana fuskantar dan’ nashi.

Sabah na ganin ya shigo ya kara hada rai kamar hadari ya taso. Dr sageer ne ya matso inda Alhaji Muazzam yake zaune ya soma fadin “Sir, anyi deciding akan punishment din da za’ayi ne akan wanan case din?”


Alhaji Muazzam ya dago yana dubanshi sa’anan yace “ba kama mai laifi ba taya kuma za yanke hukunci har da purnishment?”


Dr Sageer yayi sauri ya hadiye abunda ya taso masa don yasan halin VC din sarai, da wuya yayi wani abu akai don kwata kwata baya san laifin dan’ nasa. Wani irin kallo Dr Sageer ya watsawa Sabah, shima Sabah ya dago yana dubansa suka hada ido.

Alhaji Muazzam ya juyo yana duban Sabah sa’anan ya cigaba da fadin “karka damu Sabah, duk wanda ya aikata hakan bazai jima a boye ba. Za’a kamashi kaji koh”.


Sabah ne ya sake dagowa yana duban Dr Sageer sa’anan yace “ai daman ban damu ba”. Ya fada still idanunshi kyam akan dr Sageer.


Alhaji Muazzam ya juyo yana duban Dr Sageer da chief officer din yace “Dan Allah a kokarta, ayi hanzari a kama duk wanda ya aikata wanan laifin.”


Babu yanda suka iya kuma bazasu iya musanta mishi ba suka bashi ansa da “okay sir”


Chief security officer dinne yace bari yaje yayi musu magana a investigation room. Yana fita Alhaji Muazzam ya juyo yana duban Sabah sa’anan yace “Sabah zaka iya komawa class ka cigaba da lectures dinka”.


Sabah bai ce komai ba ya mike ya fita ya bar musu office din.


Bayan fitan Sabah Dr Sageer ya juyo yana duban Alhaji Muazzam sa’anan yace ” Amma yan labai, gani nakeyi kamar waenan abubuwan daka keyi a gaban Sabah kamar kana dada bata shi ne. Baka ganin wanan zai iya janyo masa matsala nan gaba?”


Alhaji Muazzam yayi shiru yana dubansa sa’anan yace ” Sageer, nasan tun tasowan Sabah baku samun jituwa tsakanin ku. Amma hakan bashi zai baka damar ka dauki laifi ka dora masa ba bayan baka tabbatar dashi ya aikata ba”.


Dr Sageer ne ya soma kame kame yana fadin “ba haka bane dan labai, gani nai duk da dai Sabah shine zai gaje ka nan gaba amma sai na gani kamar kana sakar masa dayawa, ko har ka manta da dayan dan’ naka ne yan labai?”


Duk maganganun da sukeyi Sabah yana tsaye ta bakin kofa yana jinsu. Gabadaya maganganun Dr Sageer sun rigada sun gama kaishi bango, ranshi a bace ya kama hanya yayi waje.


****************


Bangaren Samha kuwa, katse kiran tayi ta shiga cikin department din ta soma haurawa saman matakalan da zai kaita can sama, gashi ko ina yayi kura ga duhu, saboda department din an jima da barinta don an rigada an gina musu sabo, haka ta dinga haurawa saman matakalan da kyar ta samu ta kai sama tana nishi. Tana isowa balcony din, nan ta tadda shi tsaye yana murmushi har ta karaso inda take tana ajiyan numfashi


Jabbar ya kare mata kallo sa’anan yace “wow Samha. You’re here”.


Samha bata saurareshi ba ta katse shi da ” Daman karya kayi mun, ba’a wanan makarantar kake ba? Wai tsaya ma tukuna. Who the hell are you?”


“Me? Ai ni ya kamata azo a kama, amma kuma sai naga sun tafi da Sabah”.


“So daman kaine ka aikata”. Samha ta fada tana girgiza kai.


” Eh toh it’s very interesting, ko ya kika gani? Ace yaron VC ne aka kamashi da laifin aikata irin haka.” Ya fada yana fashewa da wani irin dariya.


“Toh bari muga, let’s see, what should i do to him next?” Ya fada yana ci gaba da dariyan da yakeyi.


Samha ta katse shi da “why are you doing this Jabbar?


Bai bata ansa ba ya juyo yana dubanta sa’anan yace ” ki bani suggestions Samha. Me kike tunani ya kamata nayiwa Sabah next?”


Samha wanda ranta ya rigada ya gama bacci ne ta bashi ansa da “Bansan meke damun kwakwalwarka ba, kuma banjin kanada isashen lafiya. Amma bari na sanar da kai wani abu daya. Idan har ka sake ka sake yin wani abu da zai taba Sabah, toh wlh bazan taba yafe maka ba”


“Wow, ai ban san son da kike mishi ya kai ga haka ba. Amma abun ya taba ni”. Ya fada yana rike gefen kirjinsa


Samha bata ce komai ba ta cigaba da aika masa da harara.


Gani tayi yasa kafa daya kan railing din balcony din, dayan kafansa na kasa ya cigaba da fadin ” Amma Samha bakida taste a maza, guy dinan yanada matsaloli dayawa, ban san meyasa kike sonshi ba”.


Samha a fusace tace mishi “Baka kan shi ba kuma baka san waye shi ba. Meyasa kake kokarin kaga bayansa? Meya maka?”


“Naga alama har yanzu kin kasa fahimta abunda ke kasa”. Ya fada yana jefa dayan kafarsa a bayan railing din. Ya tsaya dab da karshen balcony din yayi kamar zai fadi kasa.


Ganin abunda yake kokarin yi ne yasa Samha ta zaro ido, bata tsaya wata wata ba, Hankali a tashe ta karaso inda yake tana fadin “Meye haka Jabbar, ka sauko mana, kana so ka kashe kanka ne?”.


From nowhere taga ya zagayo ya janyota inda yake yasa hannu ya shakko wuyanta yana fadin “you’re so gullible and naive Samha. Toh let me tell you Saboda Sabah ne na rasa komai nawa a rayuwan nan, saboda shi na rasa masu sona a kusa dani. Saboda shi Kowa ke kina an guje ni” Jabbar ya karasa maganar muryarsa yana rawa kamar zaiyi kuka.


Samha sai faman mutsu mutsu takeyi tana son ta kwata kanta daga shakkan dayayi mata tana fadin “meye haka Jabbar, ka sakar mun wuya, i can’t breathe”. Samha ta fada numfashinta sama sama.


Jabbar bai sake ta ba ya cigaba da fadin ” na fada cewa banida kowa, that I’m lonely amma har yanzu attention din kowa na kanshi. Babu wanda ya saurareni.”


Da kyar Samha ta samu ta kwaci kanta daga rukon daya mata, ta tureshi gefe, ta juya tana kokarin gudu.

Jabbar yasa hannu ya sake damkota, nan suka fara kokuwa, Samha jakkar hannunta ta samu ta dinga kwada mishi ta ko ina.

Dayaga sai faman kwada mishi jakan hanunta takeyi babu gagautawa ne yasa hannu ya fizge yayi flinging jakkan ta sauka kasa. Hannu yasa ya sake kai mata wani shakkan a wuya.


Students dake tsaye a ground floor ne sukaga fadowan jakkan suka dago suna  kallon sama, nan sukaga abunda ke faruwa a sama.

Su khady ne suka zo wucewa sukaga students sun taru a gaban department din, cikin sauri suka karaso, nan suka ga jakar samha a yashe a kasa. Hankali a tashe suka dago suka ga Samha da Jabbar a sama. Ai babu shiri suka shiga cikin department din suka soma haurawa sama.


Jabbar dake ta faman kokuwa da Samha, wani irin wawan turi ya kaiwa Samha ta fadi a kasa. Ya karaso inda take muryarsa na rawa yana fadin ” tsawon rayuwa na na kasance nine shadow din Sabah, ko me za’ayi sai ace shi. Ni ba’a sako ni cikin lissafi amman shi ko ajikinshi”.


Su khady ne suka karasa haurowa sama suka tadda su a hakan.


Samha tana ganinsu nan da nan ta mike cikin sauri tana kokarin ta karasa inda suke. Jabbar ya kai mata wani irin fizga ya janyo ta. Basu ankaraba Samha taji kanta akan railing din benen, hanunta ya zame wani irin razananen ihu su khady suka saka ganin Samha ta zame zata je kasa.

shima jabbar hankalinshi a tashe yasa hannu ya kamo ta. Students dake kasa sai faman ihu sukeyi a kawo doki.


Jabbar dayake tattace ne, murmushi ya sake yana kallon cikin kwayar idanun Samha sa’anan yace “idan kin amince zaki bar Sabah to zan ceceki”.


“Toh ka sake ni kawai, idan akan wanan kiyayan kakeso ka ceceni toh na gwamace na fadi na mutu a hakan”. Samha ta fada mishi.


“Kina tunanin bazan iya sakin ki bane?” Ya tambayeta.


“Jabbar bari kaji in gaya maka, you’re just a sad person don duk waenan abubuwan da kakeyi basu bane zasu kawo maka farin ciki cikin rayuwarka ba. Bazasu taba kawo maka soyayyar da kake nema cikin rayuwarka ba”.


Ihun su khady ne ya farga dashi inda suke fadin “Jabbar dan Allah karkayi haka, ka taimaka karka bari Samha ta fadi”.


Jabbar ya kalla cikin kwayar idanun Samha yace ” naga alama kinada masoya dayawa”


“Kaima zaka iya samun haka Jabbar. It’s not too late. Bazaka taba rasa masu sonka ba”.


Shuru yayi yana nazari abunda ta fadi, daga bisani ya juyo yana duban su khady dake tsaye a gefe duk sunbi sun rikice sai faman ihu sukeyi a kawo musu doki don suna jin tsoro karda su karasa Jabbar yaji haushi ya sake Samha.


“Ku zo ku sa hannu mana a ciro ta”. Ya fada musu, jiki na bari suka karaso nan suka sa hannu aka janyo Samha. Da kyar suka fiddo da ita, sai faman ajiyan numfashi sukeyi.


Jabbar ya mike bai ce musu komai ba ya juya ya soma tafiya kamar wanda kwai ya fashe mishi a ciki.

Su khady ne suka ruko Samah sai faman rarashinta sukeyi.


Khady ta dubi Samha ta soma fadin “Samha baki tunanin ya kamata a fadawa security din makarantar nan suyi maganin guy dinnan? Ko Sabah ma ki fada mishi mana, duk da dai bamu san meya hadasu ba dayasa ya tsaneshi haka”.


Samha shiru tayi tana nazari daga bisani ta girgiza kai tace “bazan iya fadawa Sabah ba, don nasan halinshi sarai. Yanzun nan hankalinshi zai tashi ya dauki laifin komai ya daura wa kansa. Kamar yanda ya faru da case din Zack. Zanyi iya kokarina naga na kare Sabah daga sharin Jabbar.”


Khady zatayi magana kenan, Samha ta katse ta da ” sai inda karfi na ya kare don bazan taba bari Sabah ya sake shiga cikin damuwa ba”


Su khady basu sake cewa komai ba haka suka taimakawa Samha ta tashi suka fara tafiya.Da dare misalin karfe bakwai da rabi, Anty Fanneh tana kitchen tare da lami ana dafa abincin dare.+


Samha tana parlour tana shirya dining. Tana cikin aikinta taji an soma ringing din door bell din parlourn.

Ta karasa taje zata bude don a tunaninta mai gadi ne. Tana budewa taga mutum ya shigo ciki kai tsaye yana fadin ” akwai abinci kuwa, yunwa nakeji”. Ya fada yana karasawa cikin parlourn ya nema wuri ya zauna.  Samha ta bishi da kallo.


Anty fanneh ne ta shigo cikin parlourn taga Sabah. Fuskarta ta barke da murmushi tana fadin ” ha’an Sabah yau kaine a gidan namu?”.


“Eh wlh anty, ina wuni.”


“Lafiya lau, ya gida. Ya mahaifin naka dasu Hajiya”.


“Lafiyan su lau”. Ya fada mata.


Anty fanneh tace ” Abinci ma yayi bari a zubo maka, Samha kawo mishi ruwa ya fara sha tukuna”.


Samha ta ce “toh Ammi”.


Samha ta karasa wajen fridge taje ta dauko mishi ruwa da class cup ta kawo mishi.

Tsayawa tayi tana kallonshi. Wani irin tausayinsa ne taji ya kamata ta soma fadin

“Sabah ya kake ji yanzu”.


Sabah ya dago yana dubanta sa’anan yace “Ban gane ba. Wani abun ne ya faru?”


“Maganar project dinku mana da akayi crashing”.


Anty fanneh ce ta karaso parlourn hannunta rike da plate din abinci tana fadin ” yawa ya ake ciki da maganar case din, mahaifinka ya kirani dazun yake fada mun abunda ya faru”.


Sabah ya dan nesa sa’anan yace “wani ne kawai yake kokarin yayi framing dina. Amma Abba yasa anayin bincike akan lamarin”.


“Toh ta Allah ba tasu ba insha Allah duk wanda yake kokarin ya bata ka asirinsa zai tonu”.Ta fada tana kokarin mikewa tace tana zuwa. Nan ta sake komawa kitchen din.


Sabah ya juyo yana duban Samha da murmushi manne bisa kyakyawar fuskarsa sa’anan yace ” kanwata ban San cewa kinada farin jini haka ba”.


Gaban Samha ne ya fadi ta juyo tana dubansa sa’anan tace “ban gane ba, wani irin farin jini kuma?”


“Ah toh naji wai wani kyakywan guy yana bibiyenki a makaranta”.


Samha ta soma girgiza masa kanta, ta bata rai kamar zatayi kuka tace ” wlh ba haka ne, karka wani sa kanka cikin damuwa, bana son…”


“Toh ai ban damu ba, ko na fada miki na damu ne?” Sabah ya katse ta.


Samha maganar da take kokarin yi ne ya mutu a bakinta jin abunda ya fadi. Jikinta yayi mugun sanyi.


Sabah ya lura da yanayinta ya dan saki murmushi sa’anan yace ” Ai babu wanda zai taba sonki fiyye ga yanda nake sonki kanwata. You’re mine”. Ya karasa maganar yana kallon Cikin kwayar idanunta.


Wani irin farin ciki ne ya lulube Samha da jin kalamansa bata san sanda ta sake murmushi tana sunkuyar da kanta kasa ba. A haka suka cigaba da hiransu cike da farin ciki da walwala.


**********************


Washe gari a school, Sabah ya kirawo su Zack suna tsaye suna kallonshi ya bude project dinshi a cikin laptop, ya kurawa design din ido ya soma fadin “da ku yarda, da karku yarda, duk uwasu daya ubansu daya, amma wanan shine first time dina na aikata hakan”. Yana gama fadin haka nan da nan ya danawa project dinsa permanent delete.


Cike da mamaki da tashin hankali suka bishi da kallo, Zack ne ya dubeshi yace “Sabah lafiyan ka kuwa, akan me zakayi deleting na wurin naka? Shi kadai ne fa ya rage a group dinmu da za’a ayi submitting.


Sabah ya juyo yana dubansu sa’anan yace ” ina so ko wanen ku ya bude ido ya tashi tsaye yasan me yakeyi. Don wanan competition din ban yarda da ita ba. Ina suspecting Dr Sageer ne ya shirya komai don kawai ya bata mun suna. Kunsan nida shi bamu shiri, kuma na tabbata zai iya yin komai don yaga ya bata ni.”


Su zack suka jinjina maganar nasa don sun san Halin Dr Sageer sarai da mugunta wajen students “wato shine ya bar naka kawai don yana son ya kawo rikici cikin mu?”


“Toh wlh sai munyi maganinsa a wanan makarantar. Zai san mu ya tabo”. Abbah ya fada yana buga kirjinsa.


“Toh yanzu ya kakeso ayi?” Suka tambayi Sabah.


Sabah yace “zama zamuyi mu sake creating wata sabuwar design wanda ya ci uban nada muyi submiting. Sai muga iya gudun ruwansa.


A haka suka yarda da wana tsarin suka zauna suka janyo laptop dinsu. A ranar dai yini sukayi suna abu daya don ko lectures ma basuje ba sukayi skipping.


****************


Washe gari da safe, Amjad ne yake driving da khady zaune a gefensa zasu je school tare yaje yayi picking dinta daga gida.

Sunzo dai dai wajen wata roundabout da zai sada su da point road, khady ta hango wani tsaye a gefen titi. Sanye yake cikin uniform din makarantar Broadway High school yana tafiya cikin sauri shi kadai.


Kura mishi ido tayi sosai taga yanayin tafiyan guy din kamar Jabbar. Sai data kare mishi kallo sosai tayi confirming cewa shine.

Kam bala’i daman Jabbar High school yake zuwa? Ta tambayi kanta.


Amjad ne ya lura da yanayinta sai faman dube dube takeyi.


Ya tambayeta lafiya?. Tace “baby duba can, kaga wancan farin guy din mai kama da halfe caste dake tafiya sanye da uniform?” Ta fada tana nuna mishi Jabbar daya soma yin nisa.


“Eh na ganshi”. Ya fada mata.


“Toh shine guy din dake ta bibiyan Samha ya hanata sukuni.”


“Wancan yaron kike nufi?” Amjad ya tambayeta cike da mamaki.


“Kwarai kuwa wancan yaron. Yanada cikan ido ne kawai da kuma jikin manya amma yaro ne, Naga kamar Broadway high school yake zuwa ko?”


“Haka ne Uniform din broadway ne a jikinsa.”


Khady tasa hannu cikin jakarta ta ziro wayarta ta soma neman Samha a layinta. Bugu daya Samha ta daga nan Khady tace mata taga Jabbar kuma tasan makarantar da yake zuwa, nan ta zayane wa Samha komai.


Samha tace sai ta karaso makaranta tukuna. Nan ta katse kiran.


A Haka suka karasa makaranta.

Zuwa rana bayan an gama lectures. Su Amjad suna cikin gym zasu fara practice, Sabah ya shigo yazo ya tadda Amjad dake tsugune yana kwaso kwallon da zasuyi wasa dasu, nan ya karaso ya soma fada mishi “Captain gaskiya yau saidai kayi hakuri, bazan samu yin practice ba. Bacci nakeji sosai”.


Amjad ya dago daga inda yake tsugune ranshi a bace soma fadin “Haba i’ve had enough, kowa idan ya shigo sai ya bada excuse, yanzun nan su Zack suma suka shigo suka bada nasu. Idan bamu dage da practice ba, za’a cinye mu fa a wanan competition din” ya karasa maganar cike da damuwa.


Sabah yana tsaye yana jinsa sai faman lumshe idanunsa yakeyi cike da jin bacci don jiya raba rana da dare sukayi don su samu su kammala aikin project dinan akan lokaci.


Hannu yasa ya dafa kafadar Amjad yana fadin “i’m sure bazamuyi loosing ba tunda munada capable captain kamar ka. Insha Allah zamuyi wining wanan competition din”.


Amjad ya dubeshi sa’anan yace “kar ma ka bata bakinka don kaima kasan dadin baki bazasuyi aiki akaina ba”


Taku suka soma ji a bayansu ana fadin  “Samha ma bata nan, wato harta manager din ma bata aikinta da kyau kenan”.


Waigowa sukayi a tare suka ga Aliyah tazo ta tsaya a gabansu hanunta rungume bisa kirjinta.


Amjad ne ya soma fadin “Aliyah karki ma fara, don ita Samha tanada kwakwaran dalilin daya hanata zuwa practice. Ta tafi Broadway high school ne amma tace bazata jima ba zata dawo”.


Cikin sauri Sabah ya juyo yana dubansa jin abunda ya fadi.


“Broadway High school?” Aliyah ta fada


“Toh me taje yi a can?” Sabah ya tambayeshi.


“Taje yin bincike ne akan guy din da yake bibiyanta”.


Gaban Sabah ne yayi damm ya fadi. Aliyah tace “wow, tun yanzu har ta fara bibiyan wani?” Ta karasa maganar tana kallon Sabah.


Amjad ne ya katseta yana fadin ” Meye matsalarki ne wai? Bata yarda da guy din bane shiyasa taje tana bincike akansa, tana so ta gano komai, So take ayita ta kare”.


“Wai waye wanan?” Sabah ya tambayeshi.


“Dazu da safe ne, nida khadija muka ganshi a hanya sanye da uniform din Broadway. Wai sunanshi…. Abdul-Jabbar”.


Aliyah da Sabah suna jin sunan, suka zaro ido suka kalli juna.


Aliyah cike da mamaki tace “Abdul-Jabbar? Sabah Ina Abdul- Jabbar kaninka ne?”

Amjad shima cike da mamaki ya juyo yana duban Sabah sa’anan yace “Kani kuma, daman kanada kani ne?”


Sabah bai bashi ansa ba ya juyo yana duban Aliyah sa’anan yace “keh kin cika surutu wlh”.

Aliyah nan da nan ta ja jinin jikinta don bata san sanda maganar ta kubuce mata daga bakinta ba.


Amjad wanda gabadaya kanshi a daure yake ya cigaba da fadin “ban gane ba, Ku fahimtar dani. Yanzu kuna nufin kuce guy din dayazo nan makaranta yana pretending kamar shi student ne yazo ya adabi rayuwar Samha, daman ba kowa bane illa kaninka Sabah?” Ya karasa maganar cike da mamaki.

Sabah bai bashi ansa ba, hankalinshi a tashe yace zai je ya taho da Samha. Bai tsaya yaji me zasu ce ba yayi hanyar waje cikin sauri.Samha tana isa broadway high school taja ta tsaya tana karewa makarantar kallo. Baban makaranta ce sosai kusan 4storey buildings kusurwa kusurwa. Ga ko ina anyi shuke shuken flowers da bishiyoyi, makarantar tayi kyau sosai, kuma daga gani private school ce.+


Tana tsaye dai dai wajen shiga gate din makarantar kusan minti biyar sai ga Jabbar nan ya fito shi kadai rataye da jakan makaranta a kafadarsa.


Samha tana ganinshi da uniform din makaranta mamaki ne ya cikata, sai taga yayi mata kankanta compare to lokacin da take ganinshi cikin manya kaya a school.


cikin sauri ta karasa taje ta tadda shi ta soma fadin “Jabbar daman high school kake zuwa?”


Jabbar yana jin muryanta ya tsaya cak, bai juyo ya kalleta ba, ya bata ansa da ” Toh sai meye? Sabah ne ya fada miki?”


“A’a, Ai ban fada mishi batun ka ba”.


Jabbar yana jin haka ya kama hanya zai cigaba da tafiya, Samha ta dakatar dashi tana fadin “Sabah shima yayi attending wanan makarantar, anan ya gama high school dinshi. Meye halakar ka dashi ne wai? Don yanzu na gane duk saboda Sabah kaketa faman adaban rayuwata. What’s the connection between you two?”


“Meyasa bakije kin sameshi kin tambayeshi ba? Kinzo kina tambayata?” Shima ya jefo mata tambaya. Yana gama fadin haka yayi gaba ya tafi ya barta tsaye a wajen. Samha bata ce komai ba ta tsaya tana bin bayansa da kallo.


Har yayi nisa, from nowhere wasu guys guda uku suka bullo suka sha gabansa, suma sanye suke da uniform irin na jikinsa.


Daya daga cikinsu ne ya hankade shi ya fadi a kasa. Jabbar ya zaro ido cike da takaici ya soma tambayarsu ” what do you want now. Me na muku?”


Wanda ya tureshi ne ya soma tafa hannu ya tsuguna daidai inda Jabbar yake zaune yana fadin “wow, tambayarmu ma kakeyi me muke so?. Ashe kanada rabon cin duka kenan” ya karasa maganar yana kokarin nade hanun rigarsa.


Samha dake tsaye daga can gefe tana kallonsu, hankalinta ne ya tashi data guys din suna nade hanun rigarsu alamun suna so suyiwa Jabbar duka, babu shiri ta karaso inda suke cikin sauri tana fadin ” meye haka? meya muku da zaku taru mishi haka? Jibeku fa, ko kunya baku ji”.


Wanda yake tsugune kusa da Jabbar ne ya dago yana dubanta sa’anan ya bata ansa da “ke kuma ina ruwanki? Bamu san shishigi fa, nan makarantar mu ne kuma duk abunda muka ga dama zamuyi kuma babu wanda ya isa ya hanamu”.


Yana gama fadin haka ya dawo da dubansa ga Jabbar yasa hannu ya soma dan marinsa a fuska yace “kai wanan guy din kana so kayi amfani da tashen da Sabah yayi a makarantar nan a da don kayi suna koh? Toh bari kaji mu gaya maka, baka isa ba indai muna makarantar nan, sai mun taka maka birki.”


Hannu yasa ya soma wasa da tie din wuyan Jabbar sa’anan ya cigaba da fadin “wai tsaya ma tukuna anya kuwa Sabah Yayanka ne yanda kake kirari?”


Samha ce ta zaro ido jin abunda guy din ya fadi “Sabah ne yayan Jabbar?”


Jabbar ne ya fusata ya basu ansa da “wallahi ku jira ku gani, wata rana sai yasa kun dandana abunda kuka mun, ranan tana nan zuwa”.


Dariya suka sake suna fadin “wata rana? Wace rana kenan. Muna nan jiran ranan tazo”.


Jabbar bai sake cewa komai ba, mikewa yayi ya soma tafiya, da’ya daga cikinsu ne yasa hannu ya zungure mishi kai. Samha na ganin haka ta zaro ido tana kallon abunda yake faruwa a gabanta cike da mamaki.


Jabbar bai juyo ya tanka musu ba ya cigaba da tafiya. Guys din suma tsaki suka ja suka kama hanyarsu.


Jabbar har ya danyi nisa, Samha ta soma bin bayanshi cikin sauri tana kiran sunansa amma bai juyo ya tanka mata ba ya cigaba da tafiyansa.


Sai faman tafiya yake ranshi a bace, ko gannin gabansa bayayi da kyau. Yana cikin tafiyan nasa from nowhere yaji yaci karo da mutum, kafada akasa aka hankadeshi sai kawai jin kanshi yayi a kasa.


Dagowa yayi don son ganin wanda ya hankadeshi, Sabah ya gani tsaye a gabansa, wani irin shock ne ya ziyarce shi ya bude baki yana kallon Sabah bai san sanda yace “yayah….” ba.


Samha itama tana ganin Sabah taja birki ta tsaya tana kallonsa.


Sabah ko kallon Jabbar baiyi ba ya tsaya yana kallon Samha, fuskarsa a hade murtuk kamar bai taba dariya ba. sai daya tsaya ya kalleta na kusan minti biyar sa’anan ya soma takowa inda take.


Jabbar yana ganin Sabah ya wuce shi ko kallonshi bai yi ba, yasa gabadaya jikinsa yayi sanyi.


Sabah yana isa inda Samha take bai ce mata kala ba, hannunta ya riko cikin nasa ya jata suka soma tafiya.


Itama bata ce mishi komai ba haka ta bishi har suka zo suka wuce Jabbar dake zaune a kasa, yayi jugum kamar wanda aka aiko masa da sakon mutuwa.


Samha sai faman waigowa takeyi tana kallon Jabbar, yanayin data ganshi ne yasa itama tausayinsa ya kamata nan take ta soma jin wani iri.


Har sun danyi nisa ta fizge hanunta daga rukon da Sabah yayi mata tana fadin “ka sake ni, ka sani a gaba kanata ja na.”


Sabah shiru yayi yana kallonta daga bisani yace “meyasa baki fada mun ba?”


Samha ta rasa me zata ce ta tsaya tana kallonsa. Sabah ya sake ajiyan zuciya sa’anan yace “ina tun wancen satin kuka hadu ke da Jabbar? Meyasa baki fada mun ba?”.


Samha ta turo baki ta soma fadin ” Toh ai ban san cewa akwai wani abu tsakaninka dashi ba……wai tsaya ma tukuna, da gaske Jabbar kaninka ne?”


Sabbah yana jin haka ya hade rai, ya kawar da kansa gefe yana fadin “Eh, shine wanda mahaifiyata ta dauka ta tafi da tun yana karami”.


Samha na jin haka tace “meyasa baka taba fada mun ba Sabah?”


“Saboda bana son damuwa. I don’t want to talk about it. In dai tani ne ma bana son ki sake kulashi ko ki shiga harkanshi. Kina jina ko?”


“Zo mu koma” ya fada yana kokarin jan hanunta.


“Sabah…..” samha ta dakatar dashi.


Sabah ya tsaya cak yana dubanta.


“Sabah in har Jabbar kaninka ne to me zai hana ku…”


Bai tsaya ya saurareta ba ya katseta da”Tunda kin san hanyar komawa ni kinga tafiyata”. Yana gama fadin haka ya juya ya tafi ya barta tsaye a wajen.


Samha tabi bayanshi da kallo cike da takaici, do ta rasa ma me zata ce ya saurareta.


*********************


Samha tana isa daidai bakin makarantarsu, sai ga Aliyah nan ta karaso tazo ta tsaya a gabanta tana fadin “Samha meye hadinki da Abdul – Jabbar?”


Samha ta tsaya curuss tana kallonta sa’anan ta bata ansa da ” kawai inaso nasan dalilin dayasa ya tsane Sabah ne”.


Aliyah ta tabe baki sa’anan tace “kin san irin tashin hankalin da rigiman da Sabah ya dingayi a lokacin da yake wanan makarantar kuwa?”


Samha ta girgiza kai tace “ban sani ba”.


Aliyah ta cigaba da fadin “Toh a lokacin da Jabbar ya soma zuwa wanan makarantar shima lokacin da Sabah yake tashen sa a wanan makarantar kenan. Baya ragawa kowa, he was so volatile don ganin kowa yakeyi kamar makiyinsa. Kullum yana cikin fada da students a school, baya ragawa kowa kuma kowa tsoransa yakeji, duk inda Sabah ya shiga zakiga kowa yana dardar.

Nasha ganin Jabbar yana kallonsa daga nesa. Amma ban taba ganin sunyi magana ba, nasan Jabbar yana mutuwan son Sabah ya kalli koda inda yake a matsayinsa na yayansa, amma Sabah bai taba bashi fuska ba. lokuta da dama zakiga Jabbar ya tsaya daga nesa yayita kallon Sabah cike da sha’awan son yi mishi magana amma Kwata kwata Sabah yaqi jininshi”.

Samha ce ta katseta da “yaqi jininshi? Aliyah kinga fa Jini, yan’uwantaka, soyayyan dake tsakanin wa da kani da kuma family gabadaya bazaka taba guje musu ba don waenan abubuwan suna da karfi. Jini ai ba wasa bane. Taya zaka guje kuma kaqi jinin dan’ uwanka”.


Aliyah ta dube ta tace ” very soon zakisan dalilin dayasa hakan ta kasance tsakaninsu amma gaskiya for now, a wajen Sabah, he’s off limits”.


“Meyasa Jabbar zai kasance off limits a wajensa?” Samha ta tambayeta.


Aliyah kallonta tayi sa’anan tace “Naga alama har yanzu baki san waye Sabah ba. A rayuwar nan babu wanda ya cika goma, duk kallon da zaki yiwa Sabah he’s not perfect. Shima yanada nashi weakness din Samha, he has his own flaws too. Sabah yanada rauni a zuciyarsa da ba kowa bane yake bari ya gani ba ballantana ya fama masa”.


“Rauni?” Samha ta maimata tana jinjina maganganun Aliyah.


“Kwarai kuwa, rauni. Kin zata kowa ne yake da hakuri da juriya irin naki? Not everyone is as resilient as you Samha”.


Samha shiru tayi tana cigaba da jinjina maganganun Aliyah” wato wanan raunin da Aliyah take fadi tana nufin Jabbar kenan. Shine raunin da Sabah yake fama dashi kenan?”


Jikinta ne yayi mugum sanyi ta kasa cewa komai har sukayi sallama da Aliyah ta juya ta soma tafiya gida.


Sabah yana isa school ya kira su Zack a waya yace suzo da laptop dinsu su sake duba aikin project dinsu.


Suna zuwa suka tadda shi a restroom nan suka soma dudubawa sukaga komai yayi kyau, everything is perfect, nan suka soma tafawa kansu.

Sabah ya kurawa screen din laptop dinsa ido yana murmushi, wani irin dadi ne yakeji yana ratsa shi, ba shi kadai ba harta su Zack dadi sukeji, don ji sukeyi kamar sun sauke wani uban nauyi ne daga kansu.


Ajiyar zuciya Sabah ya sake sa’anan ya dago yana dubansu yace “guys i’m beat. Ni na gaji zan wuce gida yanzu. Sai Allah ya kaimu gobe”. Yana gama fadin haka ya kama hanya zaiyi waje.


Zack ne ya kira sunanshi “Sabah!”


Sabah ya tsaya, bai juyo ya kallesu ba yace “wai menene kuma?”


“Cheer up! Ka dan saki ranka mana” Zack ya fada mishi.


Murmushi Sabah yayi ya girgiza kai sa’anan ya cigaba da tafiyansa.


******************


Bangaren Samha kuwa gabadaya zuciyarta ta kasa samun nutsuwa, ba abunda take tunani illa Sabah da kaninsa Jabbar da kuma hanyar da zata bi ta sasantasu.


Wata zuciyar ce tace mata taje gida ta same Sabah su sake tataunawa ko zata samu ya saurareta.


Nan ta yarda da wanan shawaran ta kama hanyar zuwa gidansu.

Tana zuwa gidansu Sabah ta tadda babu kowa a gida, sai yar’aiki da take ta faman gyara gyaran gidan.


Cike da girmamawa yar’aikin ta gaishe da Samha, Samha ta ansa gaisuwar nata tana tambayarta ko Sabah yana nan.

Yar aikin tace tunda ya fita da safe bai dawo ba. Samha tace toh, ta nema wuri ta zauna ta ciro wayarta ta soma nemansa a layi amma layin yaki shiga. Call forwarded ake ta fada mata.


Haka ta hakura ta ajiye wayar, ta juyo tana duban yar’aikin sa’anan tace “idan Sabah ya dawo zai samu abunda zai ci kuwa?”

Yar aikin tace “a’a babu, yanzu nakeso na kammala wanan aikin na dora girki”.


Samha tace “toh bari na shiga na dora girkin. Me Sabah yake son ci?”


Yar aikin tace “yana son golden yam da egg sauce sosai, shine favorite dinsa”.


Samha tace “Toh shikenan”


Haka ta shiga kitchen din taje ta dora girki. Kafun kace me, ko ina ya dau kamshi. Har ta gama soya doyan, tana yanke yanken kayan sauce.


Kamar daga sama tajiyo muryan mutum yana fadi a bayanta “hour nawa zan jira wanan girkin? Don gaskiya yunwa nakeji”.


Cikin sauri ta juyo taga Sabah tsaye a jingine a jikin kofar shiga kitchen din, hanunsa rike da ledan chips yana faman ci.


Samha ce ta bashi ansa da ” kadan jira mintuna kadan yanzu zan kammala”


Sabah bai sake cewa komai ba, yasa ledan chips din a gaba sai faman jefawa a baki yake yana ci.

Samha ta tsaya tayi shuru tana kallonsa.


Maganganun Aliyah ne suka soma dawo mata inda take fadin “naga Alama har yanzu baki gama sanin waye Sabah ba”.


Kallonshi tayi na kusan minti biyu, tausayinsa ne taji ya kamata ta soma fadin “Sabah kabi komai a hankali kaji, don’t push yourself too hard”


Sabah bai ce mata komai ba ya cigaba da cin chips dinsa.


Samha ta cigaba da fadin “Sabah, na tambayeka, saboda nida kai mun kusan Zama family ne yasa kaqi fada mun batun Jabbar ko kuma akwai wani reason na daban?”


Nan da nan taga ya bata rai ya juyo yana dubanta sa’anan yace “wai ina ruwanki ne? Bazakiyi minding business dinki bane?”Samha zatayi magana ya sake katse ta da “kuma ki daina bin bayan mutane kina tambayoyi da cigiya akansu. Babu kyau”.+


Samha ranta ne ya soma bacci tace “ba saboda na damu da kai bane yasa kaga nake yin haka. Ban san meya faru tsakaninka dashi a baya ba, kuma bansan me kake tunani ba yanzu nidai kawai nasan you’re closing off. You’re not allowing anybody in. Ni kuma bazan iya ganinka a haka ba nayi shiru na kyale. Sabah pls ka fada mun meke faruwa tsakaninka da dan’uwanka Jabbar?” Ta  tambayeshi cike da damuwa.


Sabah wanda maganganunta sun rigada sun kawo mishi wuya, a fusace ya jefo da ledan chips din gabanta yana fadin “Wai meyasa kikeda shishigi ne haka?! Eh?! Kin sani a gaba, dole ne sai na fada miki?!Nifa bana son irin haka!” Ya fada a tsawace, tsaki yaja ya tafi ya haura sama zuwa dakinsa.


Samha tabi bayanshi da kallon takaici kamar zatayi kuka. Ta rasa gane meyasa Sabah yakeda zuciya da taurin kai haka. Cike da sanyin jiki ta juya ta soma kokarin kamala girkin.


Sabah yana shiga daki, sai faman hucci yakeyi ya cire jakansa yayi flinging dashi a kan gado.


Wuri ya samu a gefen gadon ya zauna ya dora kansa bisa hanayensa. Wani irin Sara yaji kansa na masa, ji yayi abun duniya duk yabi ya isheshi a lokacin.


Dagowa yayi idanunsa suka sauka kan drawer dake kusa da gadonsa. Bude drawer din yayi, ya ciro wani frame ya kura masa ido.


Frame din dauke yake da hotonsa yana karami, ga Jabbar a gefensa shima lokacin yana karami, sai kuma mahaifiyarsu da take rike dasu itama tana murmushi akayi musu hoton.


Kusan minti biyar ya dauka yana karewa hoton kallo, zuciyarsa na masa wani irin kuna. Shi kadai yasan yanda yakeji a duk sanda yaga wanan hoton.

Tunani kala kala ne suka dinga masa yawo a ka, ga Samha daya gama mata ihu a kasa, gabadaya sai yaji duk babu dadi don yasan so kawai take ta sassanta shi da dan uwansa. Tausayinta ne yaji ya kama shi, cikin sauri ya mike ya fito daga dakin ya soma saukowa kasa.


Yana karasowa yazo ya tarar da abinci kan dining an jera da wata yar karamar takarda da akayi rubutu ciki an ajiye a gefen plates.


Kitchen ya leka, nan ma bai ganta ba. Ya dawo wajen dining din ya dauki takardan ya soma karanta abunda aka rubuta ciki kamar haka

“Ni na wuce, ga abincin nan na gama, ka samu kaci da zafinsa”.

– Samha


Jikinsa ne ya kara yin Sanyi. Ya tsaya yayi shiru yama rasa abunda zaiyi.


************************


Samha tana isa gida, jiki a sanyaye ta haura sama zuwa dakinta. Kayanta ta cire ta fada bayi tayi wanka ta dauro alwala ta fito tasa kaya tayi Sallah.


Tana idar wa ta mike ta fito, dakin Anty Fanneh taje tayi sallama ta shiga ciki. Anty fanneh dake zaune bisa kan gado tana ninke kaya, ta ansa sallamar tana fadin “Baby har kin dawo?”


“Na dawo Ammi, sannu da gida”


Anty Fanneh ta ansa da “yauwa baby, ya makarantan yau?”


Samha ta ansa da “lafiya lau Ammi. Naga yau kin dawo da wuri”.


Anty fanneh tace “wlh kam, babu aiki ne sosai a office, shiyasa”.


Samha tace “toh”


Shiru ne ya dan ziyarce su daga bisani Samha ta dago tana duban Anty fanneh tace “Ammi kinsan Abdul-Jabbar kanin Sabah?”


Ammi cike da mamaki ta dago tana dubanta sa’anan tace “kina nufin dayan yaron Alhaji?”


Samha ta gyada mata kai.


Anty fanneh tace “eh, idan zan iya tinawa ya fada mun cewa yanada wani da’ sunan shi Abdul-Jabbar. Kamar shekara biyu ne tsakaninshi da Sabah. Rabuwan mahaifiyarsu da Alhaji ne yasa ta dauki Abdul-Jabbar ta tafi dashi tun yana karami”


“Toh Amma ya Jabbar yake da yayanshi Sabah?”


“Gaskiya ban sani ba, ya naga kina mun waenan tambayoyin. Meya faru?” Ammi ta tambayeta.


Samha ta dan turo baki tace “ai Ammi gani nayi wanan maganar ya shafi family dinsu Sabah ne, Ko kema baki son kisan wasu abubuwa a game dasu?”


Ammi ta dan murmusa ta kamo hanun samha tana fadin “Abunda ya faru a baya ya rigada ya faru, ni bana son na dami Alhaji da batun maganar aurensa na da. Bawai ban damu bane, a’a kawai bana son na saka shi cikin damuwa ne”.


Samha shiru tayi tana nazarin kalaman Ammin nata.

**********************


Abdul- jabbar zaune yake akan daya daga cikin kujerun parlourn. Sanye yake cikin comfy wears, curly hair dinsa ya kwanta bisa kansa, hanunsa rike da hoton frame din family dinsu ya kura wa hoton ido yana kallo.


Dr Sageer ne ya shigo cikin parlourn ya tadda shi zaune yana fadin “Jabbar, oya tashi lokacin karatunka yayi. Ka same ni a study room”. Yana gama fadin haka ya juya ya haura sama.


Cike da sanyin jiki Jabbar ya mike daga inda yake zaune yabi bayanshi.


Yana shiga study room din ya dauko jakkan makarantarsa, ya soma fito da takkardunsa.

Dr Sageer ya soma koya masa, yana gama nununa masa ya bashi wasu equations yace yayi solving.


Yaja baya yana kallon yanda Jabbar yake solving equations din.


Dayaga Jabbar sai shirme yakeyi ya kasa solving din equations dinne yasa shi fadin “so nawa zan nuna maka formula dinnan ne wai? Ba yanzu muka gama solving din dayan ba? Toh ka sake”.


Jabbar ne ya fusata ya wurgar da biro din kan takardan yace “bazanyi ba kuma, i’ve had enough. Na gaji”. Ya fada yana kokarin mikewa.


Dr sageer yayi shiru yana kallonsa daga bisani ya bude baki ya soma fadin “kana nufin ka gaji kenan. Toh makarantar su Sabah da kake kwadayin zuwa fa, ka hakura dashi ne?”


Maganganun Dr sageer ne suka sake harzukashi, yasa hannu ya watsar da takardun dake kan table din yana fadin ” nace ya isa haka. Bana so!” Ya karasa maganar yana hucci.


Dr sageer cike da mamaki yake kallonsa, hannu yasa ya gyara zaman glass din dake manne bisa fuskansa, yana kokarin danne abunda ya taso masa yace ” Toh shikenan naji, gwanda ma daka hakura, tunda kullum bakada aikin yi sai kokarin hada kanka da Sabah, da kuma kokarin daukan fansa. Daman duk bata lokacinka kawai kakeyi.”


Wani irin kallo Jabbar ya juyo yana watsawa Dr sageer sa’anan yace “me kake nufi? Kana so kayi betraying dina ne ko meye? Baka ce zakayi supporting dina har zuwa karshe ba?”


Dr sageer ajiyar zuciya ya sauke sa’anan ya mike daga inda yake zaune yazo ya tsaya a gabansa yana fadin ” ai kaine naga kanason ka karaya da wuri. Da badin mahaifiyarka ba, meye zai sa na tsaya bata lokacina a nan?”


Jabbar ya juyo yana dubansa sa’anan yace “Nasan kana son mahaifiyata amma wai baka gajiya? Ka jima kana dawainiya da sonta amma ita bata ma san kanayi ba”.


Dr Sageer muryasa a kausashe yace “Meyasa kaga nake barinka kana yin abunda kaga dama? Kana tunanin ban san me nakeyi bane?”


Jabbar murmushi ya dan sake sa’anan yace “Na sani amma bazan taba yafe wa Abbah ba don saboda shi nake facing duk waenan abubuwan. Duk laifinsa ne. Yanzu kuma yana son ya kara aure ya fara wani sabon rayuwa? Bazan taba bari ya samu wanan farin cikin ba” ya karasa maganar yana wani irin murmushin mugunta.


*********************


Washe gari a school, Samha tazo wucewa ta department dinsu Sabah, ta hango shi zaune cikin aji yayi shiru yayi zurfi cikin tunani.

Tsaya tayi tana kallonsa daga bakin window ta kura masa ido. A zuciyarta ta soma fadin “Sabah dan Allah ka bar wanan tunanin da kakeyi. Bana son ganinka haka. Sai na dinga gani kamar kana kara nesanta kanka da sauran mutane. Yanzu haka ma tsoron tunkaranka nakeyi don ban san me zai biyo baya ba”. Da wanan tunanin ta juya, Jiki a sanyaye ta soma tafiya.


Sabah dake zaune cikin aji tare da sauran students suna jiran shigowar lecturer dinsu, shiru yayi yanata faman tunani.


Su zack ne dake zaune a gefensa suka dauki takarda sukayi kamar suna karatu amma satan kallonsa sukeyi.


Zack ne zaune a gefen Sabah shima sai saton kallonsa yakeyi yana kare fuskanshi da littafi. Sabah ya soma ji a jikinsa kamar ana kallonsa. Juyowan da zaiyi sai suka hada ido da zack. Zack yana ganin sun hada ido yayi sauri ya kare fuskarshi da littafin dake hanunsa.


A fusace Sabah ya mike ya kwace littafin dake hannun Zack ya wurga akan table, tsaki yaja yayi hanyar waje ya fita ya bar musu ajin gabadaya.


Abba ne yazo ya zungure kan Zack yana fadin “kai wani irin shashasha ne, bakaga littafin naka upside down ka rike ba? Shiyasa ya gano mana”.


Shinoh ne ya mike ya buga littafin hanunsa kan table har sauran students suka juyo suna kallonsa ya soma fadin “Nifa na kasa gane kanmu cikin yan’ kwanakin nan, haba kullum abu yaki ci yaki karewa? Yanzu me kuma aka mishi da yaketa fushin nan?”


Abba ne ya juyo yana tambayar Zack “wai Zack dan Allah meke damun Sabah ne? Nifa na jima rabona dana ganshi haka”.


Zack shiru yayi yana kallonsu bai ce komai ba.


Sabah yana barin ajin, tafiya yakeyi zuciyarsa na tafarfasa. Yana shan kwana daidai inda zai haura saman matakala. Sai ga Dr sageer nan tahowa zai je aji.


Sabah yana ganinshi ya kara sauri yaje yasha gabansa.


Dr Sageer ya dago yana duban Sabah cike da mamaki ya soma fadin “Sabah lafiya? Meye haka kuma?”


Sabah wanda ranshi yakai kololuwar bacci, daman jira yake Allah ya jefo masa mutumin sai gashi nan ya shigo hanunsa cikin ruwan sanyi.


“Ka daina pretending ka fada mun abunda kuke kullawa kai da kanina. Nasan zuwan Jabbar makarantar nan ba haka kawai bane. Duk da hadin bakinka ne”.


Dr Sageer ya tsaya yana dubansa cike da mamaki sa’anan yace”You think too much Sabah. Nidai kawai nayi accepting din offer din mahaifiyarku na kula kuma na taimaka wurin karatun Jabbar ne amma bada wata manufa ba”.


Sabah ya dago yana dubansa da idanunsa da suka kankance saboda masifa yace ” eh naga Alama kana kula dashi ai, shiyasa kai dashi kuka hada kai kuna so kuga bayana kuma ku bata mun suna”.


“Au ka gano kenan, shine har yanzu kakeyi kamar baka san da zamanshi ba? Meyasa bazaka je ka sameshi ka tambayeshi meyasa yake aikata waenan shirmen ba? A matsayinka na wanshi.


A fusace Sabah yace ” babu ruwana dashi don shi ba kanina bane ba kuma!”


Dr sageer ya gyada kai sa’anan yace “naga alama kana jin tsoron haduwar ka da Jabbar fiyye ga yanda nake tsamani. Don na tabbata a duk sanda ka ganshi yana tuna maka….”


Sabah dunkule hanunsa yayi yana jiran ya karasa abunda yake son fadi.


“Yana tunasar maka da cewa mahafiyarka bata sonka kuma bata damu da kai ba. Tunda tun data tafi dashi ta manta da kai, bata sake waiwayonka ba”.


Haba, yana gama fadin haka, sabah yasa hannu ya hadeshi da jikin bango yana hucci.


Dr sageer bai tsaya nan ba ya cigaba da kokarin harzuka Sabah yana fadin” wlh Sabbah kaine abun tausayi, compare to Jabbar. Ina tausaya maka don…”


Sabah bai bari ya karasa maganar ba, ya dunkule hanunsa,daidai kusa da jikin bango inda kan dr sageer yake ya kaiwa naushi.

Shi kanshi Dr Sageer sai daya firgita da jin Saukar naushin daidai kansa.


Sabah sai faman hucci yakeyi yana kokarin controlling kansa, kallon cikin kwayar idanun Dr sageer yayi na kusan minti biyu, sa’anan ya janye hanunsa. Ya juya ya soma tafiya ya barshi jingine sai faman zaro ido yakeyi.


Sabah nayin nisa Dr Sageer ya juyo yana duban bangon inda Sabah ya nausa, jini ya gani yanata faman gangaro a jikin bangon.


Cike da tashin hankali ya juyo yana duban bayan Sabah dake tafiya har ya bace masa daga gani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *