ZABIN SAMHA CHAPTER 9

 ZABIN SAMHA CHAPTER 9

Samha tafiya take ita kadai, tazo daidai wurin shiga department dinsu kenan taji ana kwada mata kira. “Samha! Samha!!…”

Tsayawa tayi ta waiga, Zack ta gani tafe cikin sauri yana kokarin karasowa inda take “Samha kizo da sauri, ga Sabah can ya jiwa kanshi ciwo” ya fada mata hankalinshi a matukar tashe.

Gaban Samha ne yayi wani irin mumunar faduwa ta dafe kirji tana fadin “innalillahi Ciwo kuma? Garin yaya?”

“Wlh nima ban sani ba, na ganshi hanunsa nata zubda jini, kuma nasan shine zai jiwa kansa wanan raunin”.

“Akan me zai jiwa kansa rauni?” Samha ta tambayeshi hankalinta a tashe.

I don’t know, but i think yana son ya dawo da halayensa nada ne, wanda tun muna high school. Babu wanda ya isa ya tunkareshi, ko muna tare dashi he always seems alone…. that withdrawn look….Samha idan hakan ta cigaba, Sabah will move farther and farther away from us”. Ya karasa maganar cike

damuwa.

Samha itama cike da damuwa ta soma girgiza kai tace “ina Sabah bazai taba barinmu ba”.

“Wlh Samha zai iya, nasan halinsa sarai and i’m really worried about him, bakisan yanda Sabah yake bane a da”.

Hankali a matukar tashe Samha tace “toh yanzu ina yake?”

” yanzu na ganshi yayi hanyar staff quaters. Ina mishi magana ma ko tanka mun baiyi ba”.

“Bari naje na same shi toh” cikin sauri ta bar wurin tayi hanyar staff quaters don neman Sabah.

Tana zuwa daidai wurin staff quaters, ta hangon shi tsaye shi kadai yayi zurfi cikin tunani. Gashi wurin yayi tsit babu kowa sai bishiyoyi da karan kukan tsuntsaye keta faman tashi.

Tsayawa tayi cak tana kare masa kallo, Hannunsa dake faman zubda jini ta kurawa ido, nan take taji hankalinta ya kara tashi.

A hankali ta tako har tazo ta tsaya dab da inda yake. Yana sensing presence dinta nan da nan jikinsa yayi tense.

A hankali ta kira sunanshi “Sabah….. daman kana nan?”

“Menene kuma….What is it?” Ya watso mata tambayar ko juyowa baiyi ba ya kalleta.

“I heard you were hurt”. Ta fada mishi muryarta kasa kasa.

Tsaki yaja ya juyo a fusace yana fadin “so nawa zan fada miki ki daina maganata a bayana?! Eh?”

“Ba maganan ka nakeyi a bayanka ba, i’m just worried about you ne kuma bani kadai ba, harta su Zack kowa hankalinsa a tashe yake Sabah, everyone is worried about you”

Sabah ya katseta da “Ba wani ciwo naji sosai ba, kawai kujewa nayi a hanun”. Ya fada yana kawar da kansa gefe.

“To mugani” ta fada tana kokarin kamo hanunsa daya ji ciwon.

Fizge hanunsa yayi daga rukon da take kokarin yi, ya watsa mata wani irin kallo sa’anan ya juya ya soma tafiya.

Nan take Samha taji wani iri game da  abunda yayi, amma still bata bari abun ya dameta ba ta juyo tana fadin ” How can you mistreat your own hand Sabah?! Hanun dake buga basketball, hanun dake creating websites, hanun dake taimaka ma wasu, hanun dake share mun hawayena a duk sanda na riski kaina cikin kunci? How can you mistreat it?” Ta karasa maganar hawaye na zuba mata bisa kuncinta.

Sabah tsayawa yayi cak yana sauraronta. Samha ganin ya tsaya, bata san sanda ta karaso a guje tazo ta rungumeshi ta baya tana sheshekar kuka ba.

Sabah murmushi ya dan sake nan take yaji wani irin sanyi ya ratsa jikinsa, jinta manne a bayansa. Amma bai bari ta gano hakan ba yace “ki sake ni”.

“Naki” ta fada a shagwabance tana kara matso shi jikinta.

“So kike a zo a ganmu a hakan?” Ya tambayeta.

“Ban damu ba, I just don’t want you to be alone, kuma nayi maka alkawari bazan sake tambayarka abunda ya faru tsakaninka da kaninka ba. please don’t do this to yourself kaji… dan Allah karka sake taba lafiyan jikinka”.

Ta fada tana kara kwanto da fuskarta bisa bayansa.

A hankali Sabah ya juyo yana kallon cikin kwayar idanunta, wani irin sonta ne yaji yana kara samun mazauni cikin zuciyarsa.

Hannu yasa cikin aljihunsa ya ciro wani kyale ya mika mata yana fadin “ungo nan, daure mun hanun dashi”.

Kyalen jakarta ne daya taba cira a lokacin da zata fita tare da Amjad zuwa funfair. Samha tana ganin kyalen murmushi ta sake cike da jin dadi tace “har yanzu kana nan rike da wanan kyalen?”.

Sabah fuskarsa dauke da murmushi yace “I consider this my lucky charm, always tana nan tare dani, bana rabuwa da ita”.

Samha karban kyallen tayi ta soma daure masa hanun nasa dashi.

Sabah ya kura mata ido yana kallon yanda take daure masa ciwon da kyalen. Tausayinta ne yaji kamashi yace “kanwata kin cika tausayi dayawa, you take everything to heart. Yanzu mai abun kuka a wanan lamarin?”

Samah ta turo dan karamin bakinta ta dago tana dubansa sa’anan tace “bazan iya juriyar ganinka cikin wanan halin bane. Taya zan ganka a hakan, naji hankalina ya kwanta?”

Kalamanta ba karamin taba shi sukaya ba yace ” a duk sanda nake tare dake, you eventually force my true feelings out”. Yana gama fadin haka ya janyo ta jikinsa ya rungumeta tsab yana sake ajiyar zuciya mai cike da tarrin sonta, kyakyawar fuskarsa dauke da murmushin jin dadi.

Sunfi two minutes a hakan, yana rungume da ita. Dagowan da zaiyi idanunsa sukayi ido biyu da Jabbar dake tsaye daga can gefe ya kura musu ido yana kallonsu.

Nan da nan Sabah ya sasauta rukon dayayi wa Samha ya dago, idanunsa kyam akan Jabbar. Samha ma dagowa tayi ta juyo, tana kokarin taga abunda ya daukewa Sabah hankali.

Jabbar yana ganin Sabah ya dago yana kallonsa ya juya a guje ya bar wajen.

Sabah bin bayansa yayi shima ya kwasa a guje itama Samha ta mara musu baya. kafun kace meye, Jabbar har yayi nisa ya bace musu daga gani, nan Sabah yaja birki ya tsaya ya soma waige waige ko zai ga ta inda yabi, amma bai ganshi ba.

Har Samha tazo ta tadda shi, sai faman ajiyan numfashi sukeyi suna hakki saboda gudun da suka sha.

Sabah ya juyo yana dubanta sa’anan yace “Samha, daman kinsan cewa Jabbar ne yayi hacking project dinmu yayi crashing dinsu?”

” eh mana, Daman kaima ka sani?” Samha Ta tambayeshi.

“Na sani amma Kiyi hakuri ban fada miki ba na sakaki cikin damuwa”.

“Hakurin me kake bani kuma Sabah? You’re the one who is hurting ai. Duk jabbar ne ya janyo haka”. Ta fada mishi tana sunkuyar da kanta kasa.

Sabah yace ” banga laifinshi don ya aikata hakan ba gareni, tunda nima mai laifi ne a wajensa. I hurt him first”.

Cikin sauri Samha ta dago tana dubansa tace “ban gane ba”.

Sabah ya cigaba da fadin “Tun lokacin muna kanana, akwai wata rana ina rike da yar takarda ina rubutu a parlour. Jabbar yazo ya kwace pencil daga hanuna, ya juya ya tafi a guje, ni kuma na bishi na kamo shi, sai faman kokari nakeyi na kwata pencil din daga hanunsa amma yaki sakewa, haushi naji na tureshi ya fadi kan wani glass dake kan dining.

Yana faduwa glass din ta yanke shi a wuya, sai ga jini kota ina yana zuba. Toh in takaice miki, Har yau in kin kurawa wuyan Jabbar ido zakiga shatan inda glass din ta yanke shi, kuma Banjin wanan scar din zatayi fading. So kinga tsanar dayake mun it’s justifiable. Banga laifinshi ba don yace ya tsaneni”.

“Tsana kuma Sabah? Abubuwan dana gani cikin kwayar idanun Jabbar a game da kai sunfi karfin a kira su da tsana”. Samha ta fada tana tuno yanayin dataga Jabbar ranar da Sabah ya wuce shi ko kallonsa baiyi ba.

Suna cikin wanan maganar sai ga Jabbar nan ya bullo from nowhere ya tsaya yana kallonsu fuskarsa dauke da murmushi. Poster dake hanunsa ne ya warware sai ga hoton Sabah da Samha ya bayana inda suke rike da hanun juna Sabah yana share mata hawaye.

Sabah yana ganin poster din hankalinsa ya tashi, cikin sauri ya karaso inda Jabbar yake tsaye ya fizge poster din daga hanunsa ya yaga. Yana gama yagawa yazo ya tsaya dab da fuskar Jabbar yana kallon cikin kwayar idanunsa ransa a bace yace ” meye matsalarka ne? Me kake kokarin yi?”

Wani irin dariya Jabbar ya sake sa’an yace “kana so na tura gidanku ne ko kuma kawai na tura social media kowa ya gani. Then you two will be done for. Surutu da maganganun mutane kadai ma ya isheku ku rabu, tunda kai da ita kun kusan zama wa da kanwa”. Ya fada yana cigaba da dariya.

Sabah ji yayi kamar ya make shi a wajen amma yayi kokari ya danne yace ” kai a tunaninka wanan ya isa ya raba nida ita ne? if it were possible da ban zabe ta tun farko ba. Maganganun mutane bazasu taba canza yanda nakeji game da ita ba!” Ya karasa maganar yana hucci.

Murmushin dake bisa fuskar Jabbar ne ya bace, shima a tsawace ya soma fadin “why does nothing i do faze you? Meyasa duk abunda zanyi baya damunka? Sai ka dinga nunawa ko ajikinka?”

“Saboda babu abunda zai canza”. Sabah ya fada ya juya ya soma tafiya ya barshi tsaye a wajen.

Yana zuwa inda Samha take ya ruko hanunta yajata suka soma tafiya.

Jabbar a fusace yabi bayanshi da ihu yana fadin ” ka manta har yanzu ni kaninka ne? I’m still your brother fa!”

Sabah ya tsaya cak yana sauraronsa.

Jabbar ya cigaba da fadin”Saboda kai nakeyin waenan abubuwan, Saboda kai babu abunda banayi don kawai naga naja hankalinka gareni amma kai ko ajikinka. I’m doing all this so that you’ll stand by me and see me as your brother. I really want a brother”. Jabbar ya karasa maganar cikin karyayan murya kamar zaiyi kuka.

Sabah shiru yayi bai juyo ya kalleshi ba ya bashi ansa da ” bana bukatan na sake ganinka, saboda a duk sanda na ganka kana tuna mun da abubuwa da dama waenda bana son na sake tunawa dasu”.

Samha ce ta katse shi da “Sabah meye haka, meyasa kake fada mishi waenan maganganun, don’t you know you’ll only hurt him further? You’re hurting his feelings”.

Jabbar hannu yasa ya shafo tabbon dake manne bisa wuyansa, wanda ya ji tun lokacin yana karami ya soma fadin “Daman tun muna kanana kakeson ka kasheni kaga bayana”.

Samha ce ta juyo tana dubansa ta katse shi da “Jabbar wani irin maganace wanan? You know that’s not true.”

“Its okay, ki kyaleshi kawai. Baiyi karya ba, don tun muna kanana nakeson naga ya bace daga cikin rayuwarmu”. sabah ya fada mata.

Haba magana da Sabah yayi ba karamin taba Jabbar yayi ba, wani irin kuna da zafi ne ya ziyarci cikin zuciyarsa yace “wato har admitting ma kakeyi cewa kana so kaga bayana. Toh shikenan, before I disappear sai na fara kasheka tukuna”.

Zuciyane ya debi Jabbar, Wata katuwar dutse dake kusa dashi ya laluba, ya sake wani irin kukan kura ya nufo inda Sabah yake tsaye gadan gadan da niyan kwada masa dutsen.

Sabah ko gizao baiyi ba yana tsaye yana jiran ya karaso. Wani irin razananen ihu Samha ta sake tana kiran sunan Jabbar amma bai saurareta ba.

Sabah lumshe idanunsa yayi, ba abunda yake masa yawo a ka in banda abunda ya faru a tsakaninsu lokacin suna kanana zuciyarsa cike da tarin nadama.Saukan dutse a kasa da kuma karan da Samha ta sake ne yasa Sabah ya bude idanunsa.

Ganin Jabbar yayi a durkushe a kasa, ya rike kirjinsa sai faman nishi yakeyi da kyar.

Hankali a tashe Sabah ya durkusa ya rukoshi yana “Jabbar! Jabbar!!”

Amma ina Jabbar har ya soma fita cikin hayacinsa don numfashinsa sai sama sama yakeyi yana fita da kyar.

Samha itama hankalinta a tashe ta soma salati tana tambayar Sabah abunda ke damun Jabbar.

“Asthma dinsa ne ya tashi” Sabah ya fada mata duk yabi ya rikice, bai tsaya wata wata ba ya dauki Jabbar cikin sauri yayi dashi parking lot inda yayi parking din motansa yaja sai asibiti.

Suna isa asibitin nan da nan likitoci suka karbe shi aka kaishi emergency.

Sunyi kusan hour daya suna tsaye a waje suna jiran likita ya fito yayi musu bayani.

Samha ce ta dubi Sabah wanda duk yabi ya tadda hankalinsa, gabadaya ya gagara samun sukuni.

“Sabah ka kwantar da hankalinka insha Allah babu abunda zai sameshi, zai samu sauki bi izinillah”. Samha ta fada mishi.

Ajiyar zuciya ya sake yayi shuru bai ce komai ba.

Sake kiran sunanshi tayi tace “Sabah……”

juyowa yayi yana dubanta da idanunsa da suka kada sukayi ja saboda tsabar tashin hankali, ga kwantaciyar sumar kansa da duk tabi ta hargitse. Hannu yasa yana shafo sumar a hankali yana kallon cikin kwayar idanunta ya soma fadin ” Samha bazaki gane irin tashin hankalin danake ciki bane a yanzu, idan na rasa shi ban san yanda zanyi ba. A da ina tunanin Jabbar ya kwace soyayyar mahaifiyar mu zuwa gareshi don tun muna yara ta fifitashi akaina kuma tafi bashi kulawa saboda rashin lafiya dayake yawan fama dashi. Da wuya ayi sati ciwon nashi bai tashi ba, kullum tana kan hanyar asibiti. A lokacin ban fahimce hakan ba don haushinsa kawai nakeji ina tunanin shi tafiso, amma dana girma nayi wayo sai na gane cewa ba hakan bane. Ina son dan’uwana har can kasan raina dukda dai bana nuna masa hakan, a duk sanda na ganshi cike nake da nadamar abunda ya faru tsakanina dashi muna kanana. Na san yanzu haka cike yake da tsanata”. Sabah ya fada yana kawar da kansa gefe.

Cike da tausayinsa Samha ta karaso tazo ta tsaya a gabansa tana kallon cikin kwayar idanunsa ta soma fadin ” Sabah nasan duk waenan abubuwan da suka faru tsakaninka dashi duk yaranta ne ya janyo hakan, yanzu duk kun girma. Jabbar dan’uwanka ne na jini. Bazai taba tsanarka ba asalima nasan a yanzu haka yana cike da kwadayin son ganin dan’uwansa a kusa dashi. Sabah ina so kayi mun wani alkawari na cewa bazaka sake kyaran dan uwanka ba, ina so ka janyo shi jikinka, kar ka sake barin aji kanku. Kuma bi izinillah Allah zai daga kafadarsa, zai samu lafiya. Addu’a kawai zamu cigaba dayi masa”.

Suna cikin wanan maganar likita ya fito daga dakin da aka kwantar da Jabbar. Cikin sauri Sabbah ya karasa yana tambayarsa lafiyan jikinsa.

Likita yace ya kwantar da hankalinsa sun samu sun shawo kan abun, yanzu haka ma idanunsa biyu. Godiya sukayi mishi a tare shida Samha likitan ya juya ya tafi.

Sabah ya tsaya yayi shiru yana tunanin shiga cikin dakin. Samha ta bude baki zata mishi magana kenan sai ga dr Sageer nan ya taho cikin sauri yana tambayansu abunda ya sami Jabbar don yaji labarin cewa an kwantar dashi a asibiti.

Sabah banza yayi dashi ko tanka mishi baiyi ba ya kawar da kansa gefe. Samha ce ta bashi ansa da yana cikin dakin.

Cikin sauri Dr sageer ya bude kofar dakin ya shiga, nan ya tadda Jabbar kwance a kan gado idanunsa biyu.

Karasowa yayi yana fadin “Jabbar ya jikin naka, garin ya ka bari ciwon naka ya tashi. Baka fita da inhaler dinka bane? “. Dr Sageer ya tambayeshi fuskarsa cike da damuwa.

“Uncle Sageer…. kayi hakuri na saka cikin damuwa, nima ban san ya hakan ta faru ba. Ina tare dasu Yayah Sabah sai ciwon ya tashi. Amma yanzu ya lafa mun likita yace zan iya tafiya gida amma zasu sake rubuta mun wani sabon inhaler na siya na dinga amfani dashi”.

Dr Sageer ajiyar zuciya ya sake sa’anan yace ” meyasa zakayi irin wanan Sakacin ka fita babu inhalern ka? kuma nasha fada maka duk inda zakaje ka dinga fita dashi. Wai Meyasa baka jin magana ne Jabbar?”

“I know uncle Sageer, i’m sorry bazan sake ba. Kayi hakuri”.

Jikin dr Sageer ne ya danyi sanyi dayaga yanayin yaron ya gyada kai yace ” it’s okay, daman i just want you to be happy kuma lafiyanka shine number one priority dina. Da kuma farin cikin mahaifiyarka”.

Jabbar ya dan nesa sa’anan yace “Uncle sageer kayi hakuri, nasan kanata hakuri dani ne saboda mahaifiyata. Kuma gashi inata faman causing problems wa Yayah Sabah”.

Murmushi dr Sageer yadan sake sa’anan yace ” karka damu, ai shima yanzu ya san dalilin dayasa kayi hakan”.

“Amma uncle baka jin Yayah Sabah ya tsaneni?”

” Banjin Sabah ya tsaneka don dakaga irin damuwa da tashin hankalin dana riske shi ciki shigowa na dinan da bazaka mun wanan tambayar ba.”

” Dan Allah uncle? Daman yayah Sabah ba tsanata yayi ba? Wlh uncle ban san taya zan fada mika irin dadin danake ji kasancewarsa yaya na ba”.

Murmushi Dr Sageer ya sake bai sake cewa komai ba.

Sabah dake tsaye wajen kofar shiga dakin yana jiyo duk maganganun da sukeyi. Wani irin sanyi ne yaji a ransa da jin kalaman kanin nasa.

Samha ce ta karaso inda yake tsaye ta dubeshi tace tana zuwa, har ya bude baki zai tambayeta inda zata sai tayi saurin juyawa ta bar wajen. Sabah Girgiza kansa kawai yayi ya karasa shiga cikin dakin.

Samha tana barin wajen bayi taje ta zaga, tana fitowa ta biya wurin wani hadaden shop plaza dake kusa da clinic din tace a bata lemun schwepps mai sanyi.

Har ta zira hannu cikin jakarta zata ciro kudi ta biya taji kanta yayi mata wani irin sara, jiri ne taji ya soma debanta ta soma ganin duhu duhu, nan da nan ta yanke jiki ta fadi kasa a sume.

Masu shagon ne suka zo sukayi ca a kanta suna salati.

****************

Bangaren su Sabah kuwa, Jabbar yana ganin Sabah ya karaso cikin dakin ya zaro ido yana gyara kwanciyarsa.

Dr Sageer yana ganin Sabah ya dubi Jabbar yace bari yaje ya karbo takardan sallama wurin likita, Jabbar yace toh.

Dr Sageer yana fita, Sabah ya dubi Jabbar ya soma tambayarsa ya jikin nasa.

“Da sauki sosai yayah, alhamdulillah”.

“masha Allah, Allah ya kara sauki”.

Jabbar ya ansa da “Ameen”

Shiru ne ya dan ziyarce su, daga bisani jabbar ya dubeshi yace ” uncle Sageer yaje karbo mun takardan sallama don likita yace zan iya komawa gida yau”.

shiru Sabah yayi daga bisani yace ” Toh shikenan yayi kyau”. Ya juya ya soma tafiya, har ya kai daidai bakin kofan fita daga dakin, Jabbar ya mike daga kan gadon cikin sauri ya dakatar dashi yana fadin “Yayah!”

Sabah ya tsaya cak sa’anan ya juyo yana dubansa. Jabbar ya marairace fuska ya soma fadin ” kayi hakuri yayah”.

“Name kuma?” Sabah ya tambayeshi.

“Na abubuwan dana dinga aikatawa cikin kwanakin nan, nasan na tafka baban kuskure gareka, i’ve been so childish inata causing maka problems amma yanzu cike nake da nadamar aikata su

dan Allah kayi hakuri ka yafeni” jabbar ya fada cike da rawar murya.

jikin Sabah ne yayi sanyi a hankali ya soma takowa har yazo ya tsaya a gaban kanin nasa yana kallonsa.

Idanunsa ne suka sauka kan tabbon dake manne bisa wuyan Jabbar ya soma fadin “har yanzu tabon yana nan”

A hankali jabbar ya dago hanunsa ya soma shafo tabon dake wuyansa.

Sabah ya kawar da kansa gefe ya cigaba da fadin ” maganar gaskiya ban taba jin tsanarka cikin raina ba, kawai dai na rasa yanda zanyi na fuskance ka ne don ganinka yana tunasar mun da abubuwan da suka faru a baya, don duk saboda ni ne kaji wanan ciwon”.

“Ba haka bane yayah”. Jabbar ya fada yana fashewa da kuka, yazo ya rungume Sabah ya cigaba da magana cikin sheshekan kuka ” wlh yayah baka san irin farin cikin da nakeji kasancewarka kai yayah na bane. I really want you to see me as your brother.”

Murmushi Sabah ya sake ya soma fadin “well this feels nostalgic, har ka tuna mun da lokacin kana karami sai kayita kuka kana bina ko ta ina”.

Jabbar dariya ya sake cikin kuka ya dago yana duban yayan nasa cike da farin ciki.

Dariya suka sake a tare, Sabah yana bubuga kafardarsa.

Suna cikin haka sai ga Dr Sageer nan ya karaso ciki hade da sallama, hankalinshi a tashe ya soma fadin “Sabah kazo da sauri ga Samha can ta fadi a waje a sume.

Haba wani irin dammmm Sabah yaji game da furucin Dr Sageer. Duniyar ne ta tsaya masa cak na yan sakkoni daga bisani ya dawo cikin hayacinsa.

A guje ya bar cikin dakin hankalinsa a matukar tashe har baya iya ganin gabansa da kyau. Dr Sageer ne ya mara masa baya suka fito daga cikin asibitin a tare. Sabah Babu abunda yake karantowa cikin ransa illa addu’oi na Allah yasa babu abunda ya sami Samha dinsa.Samha farkawa tayi ya tsinci kanta cikin parlourn gidansu, lulube take cikin bargo, tana kwance kan daya daga cikin three seaters din parlourn. Mika ta soma yi tana salati.+

Tana Juyowa sukayi ido hudu da Sabah dake tsugune a gefenta, ya kura mata ido, fuskar nan tasa a tamke kamar bai taba dariya ba.

Gaban Samha ne ya tsinke ya fadi cikin sauri ta mike ta yaye bargon dake jikinta tana fadin “Na shiga uku, Sabah meye haka, kar dai…”

Sabah yayi saurin katse mata maganar da take kokarin yi yace “ban gane kin shiga uku ba? Ina tunanin naki yake zuwa?”

Samha shiru tayi bata ce komai ba ta soma turo dan karamin bakin tace ” ina Ammi?”

“Bata nan, nazo na tarar da gidan babu kowa sai mai gadi. Ina yar aikin gidan naku take?” Ya tambayeta.

“Anty lami bata nan, ta tafi gida wai danta babu lafiya”.

Sabah ya dan tabe baki yayi shiru  sa’anan yace ” wai Shekarar ki nawa ne da har zaki dinga suma wa mutane saboda gajiya? Jibeta, tsohuwa kawai”. Ya karasa maganar yana hararar ta.

Samha kara cinno bakinta tayi gaba ta  sunkuyar da kanta kasa tana fadin ” bazaka gane bane, wlh cikin yan kwanakin nan, zuciyata ta kasa samun sukuni. Bana iya bacci saboda tsanani tunani da tashin hankali”

Sabah shiru yayi yana kallonta, jikinsa ne yayi sanyi ya sunkuyar da kansa kasa, zuciyarsa na masa wani irin soyuwa dajin maganganunta.

Samha ta cigaba da fadin ” zuciyata batada wani tunani illa naka dana dan uwanka Jabbar da kuma aikin project dinka da aka bata maka… da kuma……” sai kuma tayi shiru tana kallonsa sa’anan tace “wai tsaya tukuna Sabah, kaine ka dauko ni ka kawo ni gida?” Ta karasa maganar tana zaro ido.

Cikin sauri Sabah ya dago yana dubanta sa’anan yace “haba sai kace wani majiyin karfi? Taya zan dauko ki na kawo ki gida tun daga asibiti?”

” Ba haka nake nufi ba, kawai fa tambayarka nake ko…….”

Murmushi Sabah ya sake ya katse ta da ” iyakacin daukan dana miki shine, daga mota zuwa kan kujeran nan don haka kima kawar da wanan tunanin da kikeyi”.

Samha bata ce mishi komai ba sai faman turo baki takeyi tana kunkuni.

Sabah bai tanka mata, fine eyes dinsa ya kura mata yana kare mata kallo sama da kasa sa’anan yace “Da inai miki kallon karama karama, ashe kinada nauyi haka ban sani ba?”.

A harzuke Samha ta juyo zata bashi ansa yayi saurin kamota ya kwantar da ita bisa kan three seater din.

Ajiyar numfashi suka sauke a tare, Sabah ya kuro mata kyawawan idanunsa. Itama shiru tayi tana kallonsa.

Idanunsa ne suka bar cikin nata suka sauka kan karamin soft lips dinta, ya kura musu ido.

A hankali ya soma matsowa da fuskarsa zuwa dab da nata har suna iya shakkar numfashin junansu.

Samha wani irin feelings ne takeji yana tasomata a lokacin. Ga kamshin dadaden turensa daya mamayeta.

Kirjinta ne ya soma bugun uku uku, don a lokacin wani irin tsoro ne ya soma ziyarta ta saboda yanda take ji a game da Sabah a lokacin, She can’t seem to control those feelings towards him don ya rigada ya zame mata tamkar jinin jikinta dashi take rayuwa. Ji take idan babu Sabah a yanzu bazata iya rayuwa ba.

Sabah lumshe idanunsa yayi a hankali sa’anan ya budesu ya zubesu cikin nata, yana kallonta ya hango tsoro da fargaba karara a idanunta.

Murmushi ya sake sa’anan ya kai lips dinsa ya manna bisa goshinta yayi mata soft kiss a wajen sa’anan ya dago yana dubanta yace  ” ki samu ki huta, ina zuwa”. Yana gama fadin haka ya juya ya bar parlourn.

Samha lumshe idanunta tayi a hankali cike da fargaba, da tunani kala kala na mata yawo a ka har bacci ya samu nasaran awon gaba da ita.

Bayan kusan hour daya Samha ta farka, taga ita kadai ne cikin parlourn. Idanunta ne suka sauka kan agogon jikin bangon taga karfe uku saura, dube dube ta farayi bataga Sabah ba.

A hankali ta yaye bargon jikinta ta mike, motsi ta soma ji yana tasowa daga cikin kicin ta karaso cikin sauri.

Sabah ta gani tsaye cikin kitchen ya daura ruwan zafi a kan wuta.

Kallonshi ta tsaya tana yi cike da mamaki, toh me yake kokarin yi? Ba dai girki ba?

A hankali ta kira sunansa “Sabah…..”

Sabah yana jin ta kira sunanshi ya tsaya cak. Bai juyo ya kalleta ba yace “bana ce ki kwanta ki huta ba?”

“Kayi hakuri, i’ve caused so much trouble for you”.

“Kin cika sawa kanki damuwa, shiyasa ma kika suma”.

“Bawai ina sawa kaina damuwa bane, duk saboda kai ne ai”.

“saboda ni meye? Baki gama kula da kanki ba zaki wani fara damun kanki akan wasu”.

Samha turo bakinta tayi tace “toh na damu din, sai meye?” Ta karasa maganar tana murguda masa baki.

Sabah juyowa yayi cikin sauri ya daure fuska sa’anan yace “wa kike murgudawa baki?”

“Oho”. Ta bashi ansa tana kawar da kanta gefe.

Kafun ta ankara taku biyu yayi sai ganinshi tayi a gabanta, har ta juya zata gudu yasa hannu ya capke ta.

Zaro ido tayi ta soma mutsu mutsun kwatar hanunta. Sabah ya girgiza mata kansa yace “karki ma fara don kema kin san sauran zance”.

Dakatar da abunda takeyi ta tsaya tana kallonsa, shima shiru yayi yana kallonta.

A hankali ya bude baki yace “Kanwata?…..”

Kafesa tayi da manyan idanunta tace “na’am?”

“Meyesa kike exerting kanki dayawa. Kinsan yanda naji kuwa a lokacin da aka ce mun kin suma? Kin san irin tashin hankalin dana shiga ciki a lokacin ? Kusan fa zaucewa nayi”

Murmushin samha ta sake tace “Haba da gaske? Ashe ka damu dani haka ban sani ba?”

Harara Sabah ya watsa mata ya sake rukon dayayi mata, sa’anan ya juya mata baya ya karasa inda ya daura ruwan zafin akan wuta.

Murmushi Samha ta cigaba dayi ta karaso inda yake tana fadin “lah Sabah wai girki kakeyi?” Ta fada tana kokarin leka cikin tukunyar.

“Mafarki kikeyi ne ko me? Waye zai miki girki?”  Ya fada yana bude carton din indomie dake cikin cupboard. Guda biyu ya ciro taga ya kurawa ledan indomien ido yana karanta abunda aka rubuta a bayan ledan.

Samha dariya ta fashe da tana fadin “wai daman baka iya dafa indomie ba kake kokarin dafawa?”

Ajiyar zuciya Sabah ya sake ya juyo yana dubanta cike da takaici yace ” Toh sai me? Likita yace kina bukatan kici abinci kuma kisha magani. Naga babu wani abincin a gida Shiyasa nake kokarin na dafa indomien”

Cikin dariya ta soma mishi bayani tana fadin “Kawai fasa indomin zakayi cikin ruwan zafin ka zuba su seasoning din a ciki”. Ta fada mishi tana cigaba da dariya.

Sabah bude ledan indomin yayi ya fasa cikin ruwan zafin. Ya bude sauran maggin indomin suma ya juye su ciki.

“Sabah is this your first time cooking? Ka taba yin girki kuwa?”

Bai bata ansa ba, yana gama juyewa ya dauko murfin tukunyar ya rufe tukunyar.

Juyowa yayi ya soma takowa inda take tsaye. Bata ankara ba, ji tayi yasa hannu ya sunkuto ta ya dauke ta cak yana fadin ” kin cika surutu, nace ki kwanta ki huta amma kinzo nan kinata cika ni da surutu”.

Wata yar’ kara Samha ta sake ta soma mutsu mutsu tana fadin “Sabah meye haka? Ka ajiye ni kasa”.

Bai saurareta ba ya cigaba da tafiya da ita yana fadin ” wai wanan irin nauyi haka?”.

Mutsu mutsu ta cigaba dayi ta bata fuska tana fadin “ni banida wani nauyi ka ajiye ni nace”.

” anqi, baza ajiyeki ba, gwanda ma ki fara dieting”.

Daidai wurin three seater din ya kaita ya kwantar da ita ya janyo bargon ya lulubeta daga bisani ya koma kitchen din ya juyo indomie din ya kawo mata.

Haka ya sata a gaba sai daya tabbatar taci sosai ya dauko magungunanta ya bata tasha. Sa’anan ya mike yace shi zai wuce gida, yace zai kirata a waya zuwa anjima. Tun bai tafi ba Samha ta soma jin kewarsa don ji takeyi kamar kar ya tafi. Nan sukayi sallama ya juya ya tafi.

Bayan tafiyar Sabah, Samha tana kwance tayi shiru tana tunani akan relationship dinta da Sabah.

It kanta tasan abunda yake faruwa tsakaninta dashi akwai ayar tambaya akai amma, Sabah dinne idan yana tare da ita sai yasata ta manta da komai, duk yabi ya mamayeta, a yanzu haka bata jin zata iya nesanta kanta daga gareshi.

A kwana a tashi, babu wuya wurin Allah, don lokaci har yayi aka sa ranar daurin auren mahaifin Sabah da Anty fanneh.

Ranar daurin auren, mutane kalilan ne suka halarci wurin, sai Yar karamar walima da akayi.

Yan’uwan Anty Fanneh da suke Maiduguri da kuma Bariga duk sun zo.

Dukda dai wanan ba shine aurenta na fari ba, hakan bai hana yan’uwanta yi mata kaya na musamman da kuma abubuwa na gyaran jiki irin na tasu yan’ shuwan Maiduguri ba. Anty Fanneh tayi kyau sosai, farar fatar jikinta har fittar da wani irin shekki takeyi da kamshi na musamman.

Akwai wata kanwar Anty Fanneh katibe, da suke uwa daya, uba daya. Kana ganinta da Anty Fanneh kamar an tsaga kara don kamanin nasu ya bace. Sai dai katibe tafi Anty Fanneh dan jiki.

Rabon katibe da Nigeria shekara takwas kenan don ita tunda tayi aure ta koma Dubai da zama saboda aikin mijinta da business dinsa duk yana can. Auren Anty Fanneh ne kawai yazo da ita, tace bari tayi surprising dinta. Ai kuwa ba karamin murna da jin dadi Anty Fanneh taji ba data ga yar’uwarta tazo.

Suna rungume da juna suka fashe da kuka don tuno da mahaifansu da sukayi, daman su uku ne kawai suka rage a duniya, daga su sai babban yayansu Alhaji Abubakar Abiso amma shi yana zama tare da iyalensa a Maiduguri. Ba karamin murna sukayi ba son sake ganin junansu da sukayi.

Autan katibe namiji mai suna Azirak ne kawai tazo da, sauran yaran guda biyu namiji dana mace wato Abubakar wanda suke kiransa da Amire sai kuma Habboba wace take binsa, duk sun girma sunyi wayo don Amire shekaransa bakwai ita kuma Habbo shekaranta biyar, sai kuma Azirak mai shekara biyu.

Ai tunda Samha ta daura idanunta kan Azirak taji gabadaya son yaron ya shiga ranta. Gashi kyayawa sosai kuma fari don kamaninsa daya da uwarsa, very cute baby dashi. shima dayake bayida kiyuwa, yanada son mutane yasa nan da nan suka saba da Samha, duk inda zata tare suke zuwa. Yawanci tambayarta akeyi ko kaninta ne saboda dan kamanin dake tsakaninsu abunka da jini.

Washe garin daurin aure, Anty Fanneh ta tare a gidan mijinta.

A Sabon gidan Alhaji daya siya a Liverpool ta tare, tsayawa describing gidan ga mai karatu tamkar bata lokaci ne, don duk Apapa GRA babu gidan daya kaita.

Drivers guda uku aka zube, ya kara hiring bodyguards na musamman da zasu dinga kula da komai na shiga da fitan gidan.

Yar aikinsu guda daya ce wace daman ta jima tana aiki tare dasu ta biyo su don Anty Fanneh tace bata son yan’aiki dayawa.

Anty Lami ma, tsohuwar yar’aikinta nada ta salameta, tayi mata abun arziki sosai don matan tayi mata kokari sosai kuma sun jima tare.

A daren ranar da kyar Samha ta runtsa don ba karamin kuka taci ba don tunawa da mahaifinta datayi.

Anty Fanneh ce ta dinga rarashinta itama tana kuka har suka hakura suka share hawayen junansu.

Bayan kwana biyu da auren, katibe ta shirya zata Maiduguri don tasa anyi mata booking flight na rana, tana son taje ta gaida sauran Yan’uwa don ta jima rabonta data gansu.

Samha tace mata ta bar mata Azirak har taje ta dawo, Anty Fanneh tace a’a gwanda a tafi dashi, yan’uwa su ganshi.

Samha har da dan kukanta don anki barin mata Azirak.

Katibe tayi dariya tace ai bazasu jima ba sati daya kawai zasuyi su dawo.

Da kyar dai Samha ta hakura haka suka tafi da alkawarin dawowa next week.

*****************************

Yau sati daya da kwana uku kenan da tarewan su Samha gidansu Sabah.

Tunda suka zo gidan Samha bata cika ganin Shi ba, don sai suyi kwana biyu bata sanya shi a ido ba, sai dai da safe in ya fito zaiyi breakfast. Shima wanan nan da nan yake kamalawa ya wuce makaranta abunsa. A school ma, most of the time yana tare dasu Shinoh.

Alhaji ma cikin satin da aka daura musu aure yayi tafiya zuwa England, saboda tafiyar gaggawa daya taso masa akan aikin business dinsa. Anty fanneh ita daman batada damuwa. Tana zuwa aikinta kullum taje ta dawo. Alhaji ma yace mata ta bar aikin amma tace tafi son ta dinga zuwa aikin don a ganinta idanta zauna a gida ma mai zatayi? Gwanda kawai ta dinga tafiya aiki abunta.

Yau misalin karfe uku da rabi na rana, Samha sun gama lectures kenan suka fito tare da khadija, Amina bata samu shigowa school yau ba saboda batada isashen lafiya.

Khadie ta dubi Samha tace ” Samha inajin zaki fara tafiya, zanje na sami Amjad yanzu don munyi dashi zamu hadu bayan lecturers”.

Samha cike da sanyin jiki tace ” toh shikenan sai mun hadu gobe kenan”.

Khadie tace “Allah ya kaimu”

Samha ta ansa mata da “Ameen”.

Nan sukayi sallama ta tafi. Samha ta nema wuri ta zauna kan daya daga cikin seats dake zube a kusa da department dinsu, ko ina yayi shiru don dalibai sun soma watsewa an gama classes, zama tayi tana tunanin, babu abundake mata yawo aka illa tunanin Sabah da kuma kewansa daya bi ya adabeta cikin yan kwanakin nan.

Lalubo wayarta tayi daga cikin jaka, tasoma nemansa a layi.

Sai dayayi ringing sau biyu ya daga. A hankali Samha ta kira sunansa tace “Hello Sabah…”

“Ya akayi?” Taji ya tambayeta kai tsaye.

Samha ta ‘dan bata fuska kamar yana gabanta ta soma turo dan karamin bakinta gaba tace ” Bakomai”.

Sai kuma tayi shiru bata sake cewa komai ba.

“Ya kin kira ni kuma kinyi shiru kinki cewa komai. Ko akwai wani abu ne?”

Nan ma ta sake cewa “babu komai”

“Toh tunda bakida abun fadi shikenan” ya fada yana kokarin katse kiran.

Cikin sauri Samha ta dakatar dashi tana fadin “Sabah wait….”

Ajiyar zuciya ya sake sa’anan yace”Ehen ina jinki”.

Shiru tayi sa’anan ta fada a hankali muryarta kasa kasa tace” I’ve missed you….”

Wani irin sanyin dadi Sabah yaji ya ratsa shi jin abunda ta fadi, don gani yakeyi yama fita jin kewa don kawai yana kokarin danewa baya son ya nuna hakan. Tunda suka dawo gidan nasu, yake avoiding anything dazai hada su, don yanda yake jinta a ransa bai jin zai iya hiding kuma yayi controlling feelings dinsa.

Tunda yake a rayuwarsa bai taba soyayya da wata ya’ mace ba, dukda yanda yan’mata suke rububi a kansa, baya kulasu ballantana su samu fuska a wajensa don tsoron tunkaransa ma sukeyi.

sai kuma gashi tun farkon ranar daya soma daura idanunsa akan Samha yaji duniyarsa ta tsaya cak, komai ya canza masa. Yarinyar tayi mugun shiga ransa da tafiya da imaninsa. A yanzu haka ma bai jin zai iya rayuwa da wata ya’ mace in ba ita ba. She’s his breathe of life, ta rigada ta gama masa katutu ta gama samun mazauni cikin zuciyarsa. Gashi kuma yanzu ta zama kanwarsa, suna zaune gida daya under the same roof. Anya zai iya cigaba da dannewa yana hiding feelings dinsa kar iyayyensu su gane?

A hankali sanyayen muryanta ya sake dokan kunnensa tace “Sabah kayi shiru?”

“Ina jinki kanwata. Kina ina? Ya tambayeta.

“Ina gaban department” ta fada mishi.

“Okay wait for me there. I’m coming”. Yana gama fadin haka ya katse kiran.

Bafi 5 minutes sai gashi nan tahowa, yau ma kamar kullum sanye yake cikin shigarsa na kananan kaya all black.

Yana karasowa, daddaden kamshi turensa wanda ta saba ji a kullum ne ya doki hancinta ya mamayeta. A hankali ta dago kanta tana dubansa. Suna hada ido ta kawar da kanta gefe tana turo baki.

Ido ya kura mata na kusan 10 minutes, fine face dinsa babu yabo babu fallasa s’anan yace “Kanwata ya naga kin bata fuska. What’s wrong?”

Shiru tayi bata tanka mishi ba.

Ajiyar zuciya Sabah ya sake sa’anan ya rage tsawo ya tsuguna a gabanta yana sake tambayarta abunda ke damunta.

Juyowa tayi ta dan watsa mishi harara sa’anan tace ” bakai bane, nace maka nayi missing dinka amma no reply, kai ko ajikinka. Daman baka damu dani ba, Nice kawai nake wahalar da kaina akanka”. Ta karasa maganar tana murguda masa dan’ karamin bakinta.

Sabah dariya ya dan sake sa’anan yace ” shikenan laifin danayi? Waya ce miki ban damu dake ba?”

Harara ta sake galla masa ta soma kunkuni.

Girgiza kansa yayi yana murmushi sa’anan yace ” Kanwata kenan. Tsayawa fada miki yanda nake missing dinki cikin yan’ kwanakin nan tamkar bata lokacine. Ni kaina i can’t explain it but let me tell you something, kece number one a cikin zuciyar Sabah, da tunaninki da sonki yake kwana kuma yake tashi, zuciyar Sabah ta damu dake kuma ke kdai ce a cikinta. Don haka ki kawar da wanan tunanin and smile for me”. Ya fada yana kamo lalausar hanunta cikin nasa.

Nan take Samha taji wani irin sanyin dadi kuma taji sonsa da kaunarsa na kara fusgar zuciyarta yana kara samun mazauni a cikin zuciyarta.

Murmushi ta sakar masa a hankali, shima murmushin ya mayar mata sa’anan yace mata taso mu tafi.

Babu musu ta mike suka soma tafiya, har suka karasa wurin parking lot na students inda yayi parking motarsa.

Suna shiga ciki ya tada motar suka dau hanyar tafiya gida.

Suna cikin tafiya Samha ta juyo ta dubeshi sa’anan tace “Sabah ya Jabbar fa, har yanzu yana gidan Dr Sageer ne?”

Sabah ya gyada kai yace “eh yana can.”

“Amma dai kun shirya yanzu dashi?”

“Wani irin shiri kike so muyi kuma? Goya shi keke so nayi ina yawo ne ko meye?”

Ajiyar zuciya Samha ta sake sa’anan tace “ba haka nake nufi ba, nufi na kaga dai Jabbar kaninka ne na jini, ai ya kamata ka jashi a jiki ku zama very close. Kuma kaga yanda Jabbar yake sonka yan bukatan dan’ uwansa a kusa dashi. I think it’s time daya kamata kai dashi kuyi settling differences dinku. Kaji sabah, pls promise me you’ll do that”.

Sabah yace “toh fine. I’ll do that. Insha Allah i’ll find time naje na ganshi”.

Samha cike da jindadi tace “toh shikenan, amma shi bazai iya zuwa gida bane?”

Sabah yace “zai iya zuwa mana. Kawai dai yabi rudin mahaifiyar mune, itace take hanashi zuwa. Don ko data dawo dashi Nigeria, a hannun Dr Sageer ta damka shi, Abbah bai sani ba sai daga baya. Toh Abbah dai kinsan bashida wani lokaci na zama ballantana ya dinga sintirin zuwa dubashi. Ni kuma kinga ba wani shiri mukeyi ba.

Samha tace ” well i think lokaci yayi daya kamata komai ya canza. Amma before that, ina so kai dashi ku samu ku shirya sosai, daga nan we’ll proceed with the rest.”

“Toh Sannu matchmaker. Allah ya taimaka” Sabah ya fada mata yana aika mata da harara cikin wasa.

Itama hararan ta watsa masa tace ” Ameen, nidai na fada maka. Just try please.”

Sabah shiru yayi yana nazari bai sake cewa komai ba ya cigaba da driving har suka karasa 

Samha kwance take akan lalausar gadonta tana kwasan bacci, cikin baccin ta soma jin saukan numfashin mutum dab da ita ana shafar fuskarta.
A hankali ta bude idanunta, Sabah ta gani zaune a gefen gadon, kyawawan idanunsa kyam a kanta yana aika mata da tsadaddar murmushinsa.
Idanu itama ta kura masa, tana tunanin yanda akayi ya shigo cikin dakin.
“Sabah what are you doing here?” Ta tambayeshi.
Bai bata ansa ba, taga ya Kara matsowa kusa da ita yana kokarin hada bakinsu wuri daya, cike da tashin hankali Samha ta dakatar dashi tana fadin “Sabah meye haka?! Me kake kokarin yi?” Ta karasa maganar tana zaro ido.
“Haba my sister, nine fah, let’s be a pair of dangerous siblings “.
Yana gama fadin haka yayi sauri ya hade bakinsu wuri daya, ya soma mata wani irin kiss na fitan hankali.
Wata yar kara Samha ta sake, ta soma kokarin kwatar bakinta.
Kokuwa suka soma yi akan gadon suna birgima, Sabah ya sake janyota jikinsa gam, yana cigaba da kissing lips dinta babu sasautawa.
“Wayyo Allah Ammi!” Samha ta fada cikin bakinsa tana kokarin tutureshi.
Jin haka ne yasa Sabah ya tsaya cak, ita kuwa tana ganin ya saketa, cikin sauri tayi wani irin juyi bata ankara ta kai karshen gadon ba. Sai dimm kawai taji kanta a kasa. Wani irin razananen kara ta sake.
Firgigit tayi ta farka, taga kanta a kasa. Mikewa tayi ta soma sallati, tana waige waige.
Ganin kanta tayi ita kadai cikin dakin. Wani irin nanauyar ajiyar zuciya ta sake kirjinta sai faman bugun uku uku yakeyi tana tunanin mafarkin data gama yi.
Sabah shi kam har ya gama shirinsa na zuwa makaranta, ya fito har ya kai daidai wurin dakin Samha zai wuce yaji wani irin dira a kasa kuma an sake wani irin razananen kara.
Bai tsaya wata wata ba, ya murda kofar dakin ya shiga.
Ganinta yayi zaune a kasa, ta zabga uban tagumi zufa sai faman karyo mata yakeyi duk da sanyin ac dake cikin dakin.
Tana ganinshi ta soma kokarin janyo bargon dake kan gado don ta lulube kanta, saboda sanye take cikin kananan kaya na bacci.
Harara ta watsa mishi tana fadin “Sabah meye haka zaka wani shigo mun daki kai tsaye babu sallama ko knocking?”
Tsayawa yayi yana binta da wani irin kallo sa’anan yace “ihun me naji kikeyi? Na zata wani abu ne ya sameki ai”. Ya fada mata.
Sunkuyar da kanta kasa tayi bata ce komai ba don bazata iya fada mishi cewa ga abunda ya sata ihu ba.
“Ka fita mun kawai daga daki Sabah”.
Gira daya ya daga mata sa’anan yace “in fita fa kikace?”
“Eh ka fita ai nan ba dakinka bane da zaka wani shigo mun”.
“Idan naki fa?”
“Wlh sai na sa ihu har sai Ammi taji ta hauro sama”.
Sabah girgiza kansa yayi, bai sake cewa komai ba ya juya yayi hanyar fita daga dakin.
Samha tana ganin ya fice daga dakin tayi sauri ta mike ta daura hijab dinta itama tabi bayanshi suka sauko kasa.
Anty Fanneh ce take kokarin shirya kayan breakfast akan dining.
Tana ganinsu cike da farin ciki tace “my babies, har an shirya zuwa makarantar ne”.
Sabah ne ya karaso inda take yace “eh wlh, ina kwana Ammi”.
“Ina kwana Sabah, an tashi lafiya?”
“Lfy lau”. Itama Samha ta karaso tana gaidata tace “Ammi ina kwana”.
“Antashi lafiya? Yau bazaki je school bane?”
“Zanje Ammi, ai tunda asuba nayi wanka, yanzu idan nayi breakfast zan shirya na wuce “.
Anty Fanneh tace “toh ku zauna ku karya bari sophie ta kawo ruwan zafi a flask sai a hada shayi. Ga soyayyen kwai nan cikin plates”.
Suka ce “toh Ammi”.
Samha ce ta juyo suka hada ido da Sabah, ta sake watsa mishi harara tana fadin “Sabah gaskiya ni fa bana son abunda kake mun cikin gidan nan”.
Cike da mamaki Sabah da Anty fanneh suka juyo suna dubanta.
“Ban gane ba me kuma na miki?” Ya watso mata tambayar.
Kunkuni ta soma yi tana magana kasa kasa.
Tsaki Sabah yaja bai sake bin ta kanta ba.
Itama Anty fanneh tabe baki tayi don tasan halin yaran nata sarai da wuya su zauna basuyi fada ba.
Suna cikin haka sai ga Abbah nan shima ya sauko, sanye yake cikin manyan kaya da alamun ya gama shiri shima zashi office.
Cike da murna Anty Fanneh ta mike taje ta tarbe shi, shima murmushi ya sake yana kallonta cike da so da kauna. Baya gajiya da kallonta kuma A kullum kara godewa Allah yakeyi da wanan kyautar daya bashi a matsayin mata don Anty Fanneh ba karamin so da kulawa take nuna masa ba, ko aurensa nafari bai taba samun kwanciyar hankali da jindadi irin haka ba.
Magana ya soma yi mata kasa kasa suka soma dariya har suka karaso wajen table din. A tare Samha da Sabah suka gaishe shi ya ansa musu gaisuwar cike da fara’a.
Tare sukayi breakfast din as one family. Samha ce ta mike tace zata je ta shirya, bafi 10 minutes ba sai gata nan ta gama shiri ta sauko rataye da jakar makaranta.
Mota daya suka hau da Abbah, yana zaune a gaba driver na jansu, ita kuma da Sabah suna zaune a seat din baya.
Har suka isa school Sabah bai ce mata kala ba, itama bata ce masa komai ba don cike take da jin haushinsa.
Daidai wurin senate builiding driver yayi parking motar.
Zuwa yayi ya budewa Abbah kofa ya fito, Sabah bai jira yazo ya bude masa ba, ya bude side din kofarsa ya fito, fuskar nan tasa a daure tamau.
Samha cike da sanyin jiki itama ta fito don tasan yanzu idanun mutane zasuyi ca a kansu.
Kuma ba karya don students suna ganinsu sun fito tare daga motar aka soma gulma.
Wani ne yana tafiya ta abokinsa zasu class ya tabo abokin nasa yana fadin “kai wancan bashi bane yaron VC ba?”
Abokin nashi tace “eh shine, waya sani ko shima nan gaba zai Zama VC din”
Sabah da Samha da suke tafiya a tare sukayi kamar basu ji ba suka cigaba da tafiya.
“Amma wancan yarinyar fa? Wacece ita? Naga rai da rai tana nan makale dashi”.
“Ai kanwarsa ce. Baka san VC ya kara aure cikin kwanakin nan ba?”
“Au haba? Dan Allah fah?”
“Wlh nake gaya ma”.
Haka suka cigaba da gulmacensu har su Sabah suka bace musu daga gani.
Basu lura ba, wani kyakyawan saurayi, matashi ne sosai don ashekaru bazai wuce shekara ashirin da takwas zuwa tara ba.
Tsaye yake yana sauraron duk abunda waenan suka fadi shima idanunsa nakan Sabah da Samha yana kallonsu har suka bace masa da gani.
Shiru yayi yana nazari, kirjinsa na masa wani irin mahaukacin bugu dayaga Samha tare da wani.
Samha kuwa tun a gaban department dinsu suka rabu da Sabah, ta soma haurawa sama zuwa class. Daidai first floor ta hadu dasu khadie da Amina.
Bayan sun gaisa ne khadie ta soma tambayarta ” wai nikam Samha ya kuke ciki ne keda Sabah?”
Samha ta tabe baki sa’anan tace ” muna nan dai yanda muke babu abunda ya canza”.
“Ban gane ba, ba yanzu kuna gida daya ba? Ya kukeyi toh?”
Samha ta juyo tana dubanta sa’anan tace ” kinsan Ammi da Abbah suna nan, so dole nidashi muyi taka tsantsan kar su gano akwai wani abu a kasa. Kuma kinsan halin Sabah sarai, wani irin miskilin mutum ne sai a hankali”.
Khadie tace ” hmm lallai. Kedashi ai wanan relationship din naku is toxic”.
Jikin Samha ne yayi mugun sanyi jin abunda Khadie ta fadi Nan kuma ta tuno da mafarkin datayi da safe. Wani irin kunya ne taji ya lulubeta.
Amina ce ta lura da hakan tasoma tambayarta “Samha ya naga kina wani mutsu mutsu kamar bakida gaskiya. Meye haka?”
Samha tayi saurin girgiza kai tace babu komai. Wani irin kallon tuhuma khadie da Amina suka soma binta dashi amma basu sake cewa komai ba. A hakan suka karasa cikin aji suka nema seat suka zauna.
Ba jima ba Lecturer dinsu Dr Sabrina ta shigo cikin ajin ta soma musu bayani kamar haka “good morning students, wanan semester munada sabon event da zamuyi. So nayi inviting guest speaker da zai muku lectures da bayani akan wanan course din, so i hope you’ll pay attention and gain from it”.
Duk maganagun da Dr Sabrina keyi, Samha jinta kawai takeyi amma kanta na sunkuye tana tunanin abunda khadie ta fada mata na cewa relationship dinsu is toxic. Toh me khadie take nufi da hakan?
Dr Sabrina ta cigaba da fadin “So with that, yanzu zan muku inviting dinshi. Bisimillah, you can come in” dr Sabrina ta fadawa guest speaker din dake tsaye a wajen kofar shigowa fuskarsa dauke da murmushi.
A hankali guest speaker din ya soma takowa har yazo ya tsaya a gaban ajin.
Maganganu kasa kasa ne ya soma barke a tsakanin daliban, musaman yan’matan ajin. Don mutumin ba karamin tafiya da imaninsu yayi ba, ba kowa bane ila matashin saurayin dazu daya tsaya yana binsu Sabah da kallo.
Amina dake zaune kusa dasu ne tace “kai kai what a handsome teacher! Kunga lecturer dinan kuwa?”
Maganan Amina ne ya katsewa Samha tunanin da takeyi, ta dago kanta a hakali tana duban lecturer din daya shigo wanda har ya soma introducing kansa ga students din yana fadin “Good morning students, first of all sunana Sameer Yusuf and i’m glad to be here at this school and i hope in future classes we’ll get along”.
Wani irin mumunar faduwar gaba Samha taji, nan take ta gagara yin kwakwaran motsi. Sai faman zari ido takeyi tana kallonsa.
Shima sameer yana cikin magana idanunsa suka sauka kan Samha sukayi ido biyu nan take ya dakatar da maganar da yakeyi yana kallonta.
Samha tayi saurin dauko littafin dake gabanta ta soma kokarin kare fuskarta dashi, muryarta na rawa ta soma fadin “No! It can’t be”.
Khadie ce ta juyo tana dubanta sa’anan tace “Samha what is it? Meye haka?”
Samha taki dagowa ballantana ta bata ansa.
Sameer ne yayi saurin farfadowa daga kallon da yake mata ya cigaba da bayanin dayake yi ” well let’s begin. Kowa ya bude littafinsa zuwa chapter 4…. page 75″. Ya fada yana bude textbook dake hanunsa. Suma students din suka some budewa.
Samha wace taketa faman kare fuskarta da littafin hannunta, satan kallonsa ta somayi, tana ganin zasu hada ido sai tayi sauri ta boye. “Wayo Allah, it’s Sameer….ya zanyi?”. Haka tayita aiyanowa a zuciyarta.
Khadie da Amina sai faman aika mata da weird looks sukeyi don sun gagara fahimtar abunda yasa takeyin haka.
Ai kam ana gama wanan lectures din suka fito daga cikin aji a tare, nan suka sata gaba suna tuhumarta abunda yake faruwa. Nan ta soma zayano musu.
Zaro ido sukayi a tare suna maimaita abunda ta gama fadin “kina nufin kice Teacher Sameer shine first love dinki? A ina kika sanshi kuma Ya kayi bamu taba sanin haka ba?”
Amina ce tace “wai tsaya ma tukuna, i thought Amjad shine first love dinki?”
“Oh Allah ki bari mana tayi mana bayani”. Khadie ta katse Amina wace ta kosa taji daga bakin Samha.
Samha cike da sanyin jiki ta soma yi musu bayani kamar haka ” he was my first crush in middle school don tun ina jss 3 nake crushin akansa. A da ya kasance dalubi wajen mahaifina don kusan kullum yana gidan mu yana karatu wajen mahaifina”.
“Dalibi kuma?” Khadie ta tambayeta.
“Eh mana kin manta mahaifin Samha babban mallami ne, kuma ana zuwa wajensa daukan karatu?” Amina ta bata ansa.
“Eh kuma fa haka ne”. Khadie ta fada tana jinjina kai.
Suna cikin haka from nowhere sukaji magana a kusa dasu ana fadin “Samha?”
Juyowa sukayi a tare sukaga Sameer tsaye kyakyawar fuskarsa dauke da murmushi yana kallonsu.
Gaisawa suka somayi, Samha tace “Sameer kwana dayawa daman kana nan?”. Samha ta tambayeshi tana murmushi.
“Wlh kam kwana dayawa Samha, shekara nawa yanzu gashi duk kin girma kaman bake ba”. Ya fada yana dariya.
Suma dariya sukayi a tare. Su khadie sai faman binsa da kallo sukeyi cike da sha’awa don ba karamin burgesu yayi ba. kana ganinshi kaga asalin bafulatani gashi he’s looking so fresh and young bazaka ce ma lecturer bane.
Samha sai faman murmushi takeyi tana kawar da kanta gefe cike da jin kunyarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *