ZAFIN RABO CHAPTER 4 BY SAKIEYY
Sakeena bata koma gida ba sai kusan 9 na dare, yanzu hankalinta ya kwanta tun bayan maganar da hamida tayi mata, ita kuwa ba abunda zata ce ma da k’awartata sai dai Allah ya biya ta, da bata da hamida a duniya bata san yarda zatayi ba. Tana shiga d’akin ta taji wayar ta na ringing wacce ta bari a kan gado tayi gidan hamida, saurin k’arasawa wurin ta tayi kanta katse, tana isa ta d’auka sai ga sunan shaheeda a kan screen d’in, ji tayi gabanta yayi mumunar fad’uwa, a hankali ta latsa kan green button d’in tare da saka wayar a kunnanta, sallama tayi bayan ta samu wuri akan gadon ta ta zauna,
+
“Da aka cemun kina nema na a waya har da cewa in nemi ki in wayata ta dawo abun ba k’aramin mamaki ya bani ba”
Abunda shaheeda ta fara ce mata kenan ko sallamar da tayi bata amsa ba, Sakeena wata harara ta saki sai kace shaheedar na gabanta,
“Ke bakya amsa sallama ne?”
Shaheeda dariya ta saki, “daman shirin da muke har ya kai mu amsa sallamar juna?”
Tsiyar ta da shaheeda akwai wawta da shahanci, shi ya saka bata tab’a biye mata in tana irin wannan abun dan sai ta zama irin ta, share tayi ta fara cewa,
“Wani abu daman nake son na tambaye ki”
Ko da tayi maganar sai da gabanta ya k’ara fad’uwa, anya ta shirya jin labarin Kamil, amma kuma rabi da kwanta zuciyar ta na mutuk’ar san jin labarin tsohon saurayin ta, muryar shaheeda ce ta katse ta daga tunanin da take,
“Mene abun da kike son tambaya ta?”
Shiru tayi ta kasa bud’e bakin ta ta bata amsa, ga zuciyar ta ba abunda take sai faman bugawa, sai can da kyar da iya furta,
“Labarin Kamil”
Tsit daga d’ayan b’angaran, ta tabbata itama shaheeda mamaki abun ya bata, Sakeena kuwa ji ta hannunta ya jik’e da gumi ita kanta bata san me ya saka duk tabi ta rud’e ba haka kawai, da taga kamar shaheeda bata da niyar magana ta dake ta k’ara cewa,
“Kada kice mun biki sani ba, nasan kin san komi kin san shi wane”
Ji tayi ta k’ara sakin dariya, “me yasa kike san sanin labarin shi?, duk zama na dake baki tab’a tambaya ta ba, ko shekaru takwas da suka wuce bayan abun ya faru dashi ko da wasa baki tab’a tambaya ta ba, me ya saka sai yanzu”
Ita kanta bata san me ya saka take son sani ba, maybe ta gaji da zama cikin duhu, maybe tana san sanin me tak’amaimai Kamil ya b’oye mata game dashi, ji tayi shaheeda tace,
“Ki saurare ni da kyau dan bazan k’ara mai mai ta miki labarin nan ba”
Gabanta ne ya k’ara fad’uwa, amma a haka ta kasa kunnnta dan jin labarin shi.
LABARIN
Mahaifinsa UMAR ADAMU DATTI haifaffan d’an garin yola ne, bafulatani ne gaban shi da bayan shi, shi kad’ai iyayen shi suka haifa, ya tashi a garin yola har ya kai shekara goma, iyayen mahaifin shi wato kakanun shi basu da wani k’arfi dan kakan shi me suna ADAMU DATTI manomi ne, kakan shi yana da wani babban aboki ALHJ JAMILU wanda yayi zaman yola a daa daga baya ya sami arziki sakwamakon kasuwan cin da ya fara a garin kano, bayan babban abokin kakan shi yayi arziki yaje gun kakanshi dan neman alfarma ya bashi mahaifin shi su koma kano ya saka shi a makaranta dan a lokacin shine kawai gatan da za’a mai, kakan shi ya so ya hana saboda shi kad’ai ne tilon d’anshi a cewar shi zai dunk’a taimaka mishi, amma da saka bakin matar shi kakar su Kamil kenan me suna HABIBA har ya barshi suka koma kano tare.
Bayan sun koma kano ALHJ JAMILU ya saka shi a makaranta har ya samu ya gama secondary school, a lokacin Allah yayi ma baban shi ADAMU DATTI rasuwa, abun ba k’aramin girgiza su yayi ba, kakan shi na da wata d’aya da rasuwa Allah yayi ma kakar shi rasuwa, HAJ HABIBA, daga lokacin ya koma gaba d’aya wurin ALHJ JAMILU dan bashu da kowa a yola, bayan ya kamala karatun shi na jami’a, Alhj jamilu ya saka shi a hanyar kasuwan ci, a haka shima har ya fara samun arziki, yana da shekaru 28, ya had’u da Haj rahima, wace take balarabiyar egypt, haj rahima wacce tazo nigeria tun tana y’ar shekara uku tana zama wurin yayar ta wace take auran d’an kano, sakwamakon rashin iyayen su, soyyaya mai k’arfi ta shiga tsakanin su basu dad’e ba sukayi aure.
STORY CONTINUES BELOW
Auren su baiyi shekara d’aya ba ta haifo y’an biyu kyawawa maza identical twins, wanda ranar suna aka saka ma Hassan KAMAL, Husaini Kuma KAMIL, sun tashi cike da so da kulawa amma sai dai they’re polar opposite, Kamal baya san jama’a, baya san surutu da hayaniya, shikuwa Kamil na mutuk’ar san jama’a, dukda halin su yasha babban bai hana shak’uwa mai k’arfi ta shiga tsakanin y’an biyun ba, suna mutuk’ar san juna su, in ka tab’a d’aya kamar ka tab’a d’aya ne, suna da shekara takwas a duniya haj rahima ta k’ara haifo santaleliyar mace, wace take a matsayin gambon su aka saka mata suna Kamila, a lokacin kud’i masu yawa sun zauna ma Alhj umar datti yayi mugun arziki kuma sunana shi yayi fuce a nigeria saboda harkar kasuwan cin sa, kuma a lokacin yayi sha’awar shiga siyasa, bayan gwagwar mayar siyasa ya samu ya hau reps anan yola, shekara biyu da samun muk’amin nan, lokacin kamila nada shekara shida, Kamal da Kamil nada shekar sha hud’u, aka haifi auta Kausar, sun tashi dukan su suna matsayin san junan su, ga Allah yayi musu wani azabbabn kyau, ga sun had’a ruwa biyu, bayan Alhj Umar datti ya sauka a reps suka tattara suka koma abuja da zama ya bar harka kasuwancin shi gurun wani babban yaran shi da ya yarda dashi.
Kamal da Kamil basu tab’a kasancewa wuri d’aya ba, dan ko makaranta ba d’aya sukayi ba, abokanan su daban ne sai dai guda d’aya me suna Imran wanda yake d’an babbar k’awar haj rahima, Kamal akwai miskilanci, akwai kuma taurin kai, shi kuwa Kamil akwai san wasa da dariya, sakwamakon rashin san jama’an Kamal shi ya saka ba wanda yasan shi, ko abokan Kamil sai sun saba dashi sosai suke sanin shi y’an biyu ne, lokacin da suke da shekara sha bakwai a lokacin baban su ya hau gwamnan Adamawa wato yola kenan, Kamil ko da wasa bai tab’a nunawa baban shi gwamna bane in har ba full sunan shi kaji ba, zai shiga cikin na k’asa dashi ya saje dasu, zai kuma shiga cikin talakawa suma ya saje dasu, ya iya zama da ko wane irin mutum, ya d’auki wannan dab’iar ne dan ya tantance masu sanshi tsakani da Allah da masu sanshi dan kud’in babanshi, shi ya saka ma ya zab’i yayi university d’inshi a k’asar da ba nigeria ba, baban shi yayi shekara takwas yana governor a adamawa, yanzu ne ya zama minister of agriculture.
———
Sakeena da tayi shiru duk jiki yayi sanyi ta k’ara jin shaheeda tace,
“Lokacin da kika had’u dashi lokacin ya gama degree d’inshi a dubai ya fara masters d’inshi a makaran tar ku”
Ta kasa cewa komi kawai tana zaune tana wasa da rigar da take jikinta, labarin ya girgiza ta saboda bata tab’a sani baban shi nada mugun arziki ba, ji shaheeda ta yi ta k’ara cewa,
“Ina ji abunda ya saka Kamil bai tab’a gaya miki shi wane ba saboda yana jin tsoro in har kinsan wane baban shi zaki canza mishi”
D’aga kanta tayi saboda ta yarda da maganar shaheeda, a makaranta bai tab’a nuna mata iyayen shi nada kud’i ba, kuma baban shi gwamna ne, dan sau da yawa ita take siya misu abinci, har kayan sawa ma wani sa’in ita take siya mishi saboda sai ya saka k
aya d’aya sau uku a jere, dukda bai tab’a amsar su ba komin mitar da zatai, ran 18th birthday d’inta dab ta zai koma nigeria da ya bata wani agogo mai mugun tsada birthday gift sai da abun ya bata tsoro, ta dunk’a tambayar shi inda ya samu kud’in sai dai kawai ce mata yayi da kud’in part time jobs d’inshi dan ba guda d’aya bane ya tara ya siya mata, bata tab’a doubting abunda ya fad’a mata ba a lokacin saboda tayi mutuk’ar yarda dashi,
“Kamil mutumin kirki ne, ban tab’a ganin mutum irin shi ba a rayuwa ta, duk wanda na san ya sanshi yaban shi yake” shaheeda ta fad’a a hankali,
Kwalla ce ta cika idanunta, jikinta ya k’ara yin sanyi, duk da shaheeda ta gaya mata abunda take son ji amma baza ta tab’a iya manta abunda tayi mata ba, har yanzu tana jin zafin abun saboda shaheeda jinin ta tace ba bare ba,
“Yaushe zaki bani hak’urin abunda kikayi mun?”
Sakeena ta fad’a muryarta na rawa kamar kuka nasan kub’oce mata, dukda hakur’in da zata bata bazai saka ta manta ta rad’adi da ciwon da zuciyar ta tayi mata ba lokacin da tasan suna tare, lokacin da tasan y’ar uwar ta jini taci amanar ta,
“Kinyi snatching d’inshi daga wuri na yana taka kaf’ar shi a nigeria, saboda kina kishi dani? Ko kuma saboda kinsan baban shi nada arziki ba d’an k’arami ba? Ko kuma saboda kina jin haushin na samu me sona tsakani da Allah?”
Dukda ranta a b’ace yake a hankali tayi mata magnar, har lokacin in ta tuna abunda ya faru sai ranta yayi mugun b’aci, kwana da kwanakin da tayi tana kuka tare da neman Kamil a waya kamar tab’arbiya, anya zata yafe ma shaheeda abunda tayi mata,
“Sau nawa zan gaya miki ba laifi na bane shi ya fara cewa yan…”
Saurin dakatar da ita sakeena tayi, dan ko sau nawa zata gaya mata Kamil ne ya fara cewa yana santa baza ta tab’a yarda ba, duk da shekara d’aya da rabi kawai sukayi tare zata iya cewa tasan halin shi, tasan abunda zai iya aikatawa da abunda bazai iya aikatawa ba,
“Ya isa haka, naji duk abunda zaki ce, na gaji yanzu bani da lokacin sauraron shirman da zaki gaya mun, sai anjima”
Tana fad’ar haka ta kashe wayar, shiru ta zauna a d’akin ta, sai hawayen da suke zubowa a fuskar ta, zata iya yafe ma Kamil koda ace laifin daga wurin shi yake, amma baza ta tab’a iya yafe wa shaheeda ba sai in har tazo da k’afunta ta nemi gafarar ta, haka ta zaune tana ta zubar da hawaye masu zafi sai can daga baya ta mik’e ta fad’a bathroom danyin alwala takai kukanta ga mai duka, danshi ne kad’ai zai saka ta sami nutsuwa.
ce ta k’arasa cikin d’akin ba sallama, sakeena wata harara ta daka mata, yanzu shaheeda ta iso gidan daga lagos amma har zasu fara fad’a,