ZEENAT YAR JARIDAH
CHAPTER 11
Kabir ne yai ma Ahmad Wani kallo yace” kaban kunya Wallahi, gaskiyane ruwa bata tsamin banza Ahmad Kuwa binshi da kallo yayi Dan beda ta cewa, Duk Wanda yazo ya gani abun da
zaiyi zargi kenan Itako Zeenat tana daki tana jinsu
Kabir ya kara da cewa” ya maka kyau, Ni na tafi sai wata rana, haryajuya Ahmad yace” ka tsaya kaji Wallahi tun da nake ban taba aikata zina da wata mace a duniyan nan ba, abun da zuciyarka ta fada maka ba daidai bane Kabir yace” Bana son karya please, ya Isa haka!
Ahmad yace Ashe abotarmu, bana gaske bane, Tunda harzan fada maka Abu ka ki yarda, Kabir yace” to dama ya za’ai in yarda nidai abun da nasani kawai ka kawo mace daki, yai tsaki mtsww
Zeenat CE ta fito sanye da hijab har kasa, tace” Haba Malan abun da Ahmad ya fada
maka gaskiyane, Kabir yace” rufemun baki bake na tambaya ba, Ai duk wani karya zakuyi dan Ku kare kanku
Zeenat wani dariya tai da ba Kabir kadai ba hatta Ahmad saida abun ya bashi mamaki, sannan Tace” Wallahi Da ka San me ya kawo ni nan seka tausayamun, meyasa wasu mazan nan take suke yanke hukunci? Idan mun boye maka ai bazamu boye ma Allah ba ko? Kabir wani kallo ya bita dashi, A Zuciyarshi yace munafuka
Har ya mik’e zai tafi Ahmad ya dafa kafadarshi yace” Kabir ka Tina da amanar da iyayena suka baka, idan ban manta ba kyawun halina yasa har ka kusanceni muka fara Abota Wannan Zeenat daka gani Nasan insha Allah kaji labarinta seka tausaya mata, but trust me wallahi ba abun daya shiga tsakani da ita
Wani numfashi Kabir yaja ya kalla zeenat da hawaye ke gab da zubomata, girgiza kai tai kawai ta shige daki shi kuma Kabir ya zauna yace” Ahmad banfa fahimce ka ba!
Nan Ahmad ya soma bashi labarin Zeenat from A to Z be boyemai komai ba har zuwa yanzu
Kabir yace” I’m so sorry kai Kasa na fara zarginka tun ba yau ba, Tuntuni ai da se kamun bayanin kauyen da Kke zuwa ga dalilin nan, Kasan komai da bayani ai yafl
Ahmad yace” nasan nayi kuskure amma afuwan, ko yanzu a shirye nake da Neman temakonka Mu hada hannu Mu temaka Yarinyar nan
Kabir yace“ karka sama damuwa, Nan Ahmad ya kira zeenat idanuwarta duk sun kunbura saboda takaici, ltama tasan confirm za’ai zarginta amma ya zatai?
Nan ta fitojikinta a sanyaye, Kallovdaya zakai mata kasan taci kuka sosai, kasa ta samu ta zauna, Kabir na bata hakuri akan abun da yai musu
Zeenat tace“ ba komai, daganan bata sake magana ba, Ahmad da Kabir Kuwa se tattauna yanda zasu bulla ma abun suke, se a time din ta kara tabbatar da Ashe Ahmad babban Lawyer neh, Yana ma gaba da Kabir sosai, nan dai suke ta hirarsu har Kabirya fito Ahmad
ya rakoshi, Kabirya kalla Ahmad yace” kamar yanda kace zaka aureta plz ai gaggawar abun
sbd ni hankalina be kwanta Ku dinga zama waje daya ba gaskiya,
Ahmad yace” karka damu in shaa Allah zan kiyaye
Bangaren Mahaifiyar Mudansir Kuwa tai Kiran duniya nan wayan Mudansir yaki shiga, tsaki tai tace wannan Dan banzan yaron Ina ya shiga sai anzo an tafi dani hankalinshi zai kwanta,
nan hawaye yazobo mata tace” wadaran yaron nan,
ooooooooooooooooooooooo
Washe Gari Yaran Mudansir sun shirya kamar yanda ya umurcesu suyi, akan suzo su Tare hanya sunsan may be su zeenat suzo wucewa!
Aiko shuru shuru har kusan yamma ba su ba alamunsu, Ran Mudansir yai matukar baci yace” Ku Wuce gidan mahaifiyarta ta fada muku lnda zeenat take idan tayi musu Ku kasheta kawai
Aiko Nan suka wuce ba wani bata lokaci, Dakin suka shiga suka matsa mata ina Zeenat tace” ita wallahi batasan Ina take ba, sukace zaki fada mana Ko sai mun kasheki?
Nan cikinta ya tsure ta rasa yazatai, Wani ya buga mata bindiga akai nan ta fadi warwas, Ganin ta fadine suka fara bincika dakin har karkashin gado wai ko Zeenat ta boye hatta bayi ba lnda basu duba ba
Mudansir Kuwa yadan Shugo cikin Garine yasama service a wayarshi, nan call din
mahaiflyarsa ta shugo Yana gani seda gabanshi ya fadi saboda Rabon da suyi waya ya kusan wata daya kenan
Ya dauka call din yace” hello swthrt I’m sorry nasan nayi laifl, shesshekan kuka yaji daga bangarenta yace” mum what‘s wrong? Tace wannan Mayyar yar jaridan ne still ta kara kai kararka kotu jiyan nan aka kawo mun takardan sammaci gashi duk sun mammanna a layin kana shugowa zaka gani! Kutumar uba! Yace” mum ganinan zuwa! Ajiyar wayar tai tayi tagumi duk abun duniya ya isheta Yana gama wayarya kira yaranshi yace” suna ina?
Sukace suna gidan tsohuwar zeenat suna Operation, sun ma buga mata bindiga akai, taki ta fada lnda zeenat take
Mudansir yace very good a haka zata k’arasa, Kuyi sauyi Mu hadu daku a Layin gidan Mu wai Zeenat ta kara kai ni kara a high court Tohfaa Me amsar wayan yace” sannan yace masu su fito dukansu oga ya kirasu, maman Zeenat na kwance, radadin da kanta ke mata yasa duk ta kosa su fita
Suna fita daya yace” case dinnan ya kara tsaho fa, ‘Yar jaridan“ nan ne still ta kara kai kara nan suka shige motar suka bar unguwan a guje,
Yan unguwan wasu suce talaka nacin wahala da tozarci a rayuwa, Wasu kuma suce mata Allah ya kara, Dan wasu magulmatan har shugowa sukai sukace Allah ya kara Yar talaka ta dakko abun dayafi karfinta gashi nan ta gudu an kusar kashe mata Uwa Sedai mamanta ta kallesu Itadai tana ma yar ta Zeenat fatan alheri, Allah kuma ya kara tsare mata yarta
Ita ko Zeenat na kwance taji gabanta na fadi Fitowa tai tazo ta sama Ahmad dake zaune a pallow yana kallon TV, tace” Dan Allah ka aramun waya naji muryan mamata Yace” au dama tana da waya ne bansani ba? Yanzu nake tinanin Nace zuwa anjuma zamuje Mu gaisheta
Zeenat tace” eh rannan na bata nawa da mukaje Aran Ahmad Kuwa yace” Allah sarki, Nan ya mik’a mata wayarshi ta shiga daki tai dialing numbern
Ringing biyar ba’a daga ba aran Zeenat Kuwa tace” halan mama nacen tana aiki tabar wayar a daki,
Bayan minti uku ta kira dakyar mamanta ta samu ta dauka wayan tana dauka zeenat tace mamana Tace” na’am cikin wani irin yanayi, zeenat tace” baki da Lfya ne, dakyar ta samu ta sanar
da ita abun da yaran Mudansir sukai
Hankalin tane yai matukartashi ta fitO pallow tana kuka tace” zasu kashe mun mama Dan Allah kakaini gidan Mu
Ahmad na tambayarta meya faru, Da sauri ta nufa hanyar waje,
Yana ganin haka shima ya kasheTV ya biyo bayan ta ya tada mota zeenat se kuka takeyi ta ta shiga motar suka nufa hanyar gidan
Ahmad gudu yakeyi sosai kamar zai tashi sama, yanda yaga zeenat tayi ne hankalinshi ya tashi yace” please ba Kuka Zaki ba Ko kallonshi batai ba ita Kam tunani barkatai take tayi a mind dinta tace” idan mudansir ya kuskura ta sanadiryarshi uwata ta rasu wallahi se ya sani
Parking yayi a kofar gida zeenat da sauri ya bude motar ko tsayawa rufewa batai ba ta shige gidan, dakin Kai tsaye ta fada yanda taga mahaifiyarta kwance Jini na malala takanta Yasa Tai wani Ihu ta zube kasa Ahmad ne ya Shugo, shima ganin jinin ba karamin daga mai hankalin yayi ba Amma zuciyarshi tace” mai. be strong Mana Kai fa namijine
Daukar maman Zeenat yayi Dan bazata iya tashi ba yayo mota da ita, ita Kuma zeenat na biye dashi a baya har Suka shiga motar
Tada motar yayi Yana Shirin barin unguwarse ga wasu samari, kana ganinsu kasan irin yan daban nan ne sukazo ta daidai windon da yake sukace”dama ka Dena wahala da wadannan in ba haka ba se sun goga maka, Dan Mudansir be kyale kowa ba… Kallonsu yai bece komai ba, itako Zeenat ta wani Galla musu harara tace” munafukai, Sukace eh dama ance Mana baki da kunya, Yar isss…
Jin maganar da Ahmad yayi ranshi a bace” I don’t have your fucking time yaja motarshi sai Nagarta Hospital..
Suna Shiga Nan nurses din sukaga yanda Jini duk ya wanke mata fuska nan akai kokarin tsayar da jinin, then suka Shiga kwaje kwaje,
Ahmad yace” ganatan ko nawane zan biya Amma Dan Allah kuyi kokari sosai, idan ma da wata matsalar ne ku fada Mana…Sukace” Ok An Shiga da ita dakin, duk wani kulawa sun bata ashe bama wata matsala bane kan jijiyane suka buga mata, kunsan jijiya da Jini sai Yasa kan mace meye Jini nata ambaliya but Alhamdulillah jikin da sauk’i Suna Zaune a reception da Ahmad da Zeenat suna Dan hira akan yanda gobe zata kasance
Sukaga all eyes on them Dan wanna secret labari ne ba kowa za’aso yaji Dan haka suka koma mota sukaci gaba da hirar karshe dai hirar soyayya tsantsa aka koma, Su Zeenat se rufe fuska take. Lol Suna cikin hirar ne, Kabirya Kira Ahmad yace” Sarakan soyayya yau Ina akaje Kuma Ahmad yace” I’m sorry muna Asibitine, mum din zeenat ne ba lafiya buh da sauk’i, Nan ya bashi labarin Abun da ya faru, Kabiryace” Amma wadennan mugayene, Allah ya kyauta
sai na Shugo, Ahmad yace” 0k
oooooooooonoooooo
Mum Din Mudansir ne se up n down takeyi a cikin daki ta kosa Mudansir din yazo idan
akwai wani Abun da zasu iya, gefe, kallo dai mum dinshi Tai ta juyar da Kai gefe tace” Kai Ni Salame Allah ya shirya kawai Zubewa duka a kasa sukayi
Suna gaisheta tace” duk na amsa hope dai kunsan me yake faruwa? Sukace Eh
Mum ta kalla Mudansir tace” yanzu meye za‘ai kasan gobe ne fa Shiga court dinku, ranshi a bace yace” Mum baki da kudi ne a tura ma lawyern mu Wani kallo Tai mai tace” bandashi Kai fa? Yace ina da dan wasu 50K a acct Dina bari na Kira lawyer naji ya za’ai Nan ringing daya biyu lauyan ya dauka, Mudansir ba respect ba komai yace” inasone fa a kashe maganar Nan ‘
Lauyan yace” tab No way fa saboda ta riga da ta kama kafa da duk manyan mu kaga zaiyi wahala, Mudansir najin haka Cikin tsawa yace” to dalla malan ya Isa, banza Wanda beson aikinshiba
Lauyan yana cire wayan a kunne kallon wayan yayi yace ikon Allah yau Dan cikina ke fadamun magana, lalle, mudai munce Allah ya Kara saboda tun farko baka dau hanyar gaskiya ba
Mudansir yai wani Ihu yace” it’s tommorow ya zanyi sai hawaye, Mum dinshi yadan Bata tausayi ta kalla yaranshi tace” kome kukeso zan muku Amma ku tabbatar gobe Kun sace yarinyar Nan
Tunda ance Ga hanyar da sukebi kar ku kuskura ku Bata lokaci duk yanda zakuyi kuyi make sure Kun sace ta kunga ba yanda za’ai takai camera dinnan Nasan dashi take takama Sukace” Mum angama karki damu, tace” 0k Nan dai suka shirya Abun da zasu Shirya sukai gida °°°WA$HE GARI”° Mudansir kana ganin idonshi yaci Kuka sosai, Dan ba wani isheshen bacci ya samu ba, Yaranshi kuwa Duk wani kayan mugunta da cutar da mutun sun tanada sun dakko bakin mota me tint tek, haka kayama baki sukasa ko wannin su da bakin glass aka nufa hanya
Zeenat kuwa dama wajen mamarta ta kwana tun asuba tana idar da sallah, gari dai beyi haske ba Tai mata sallama, mum dinta tace” to Zeenat, Allah ya daura ku akansu, Allah ya tsareki Zeenat na murmushi tace” Amin mamma
Fitowa daga Asibitin tayi Nan take taji gabanta fadi, Bata kawo komai a ranta ba har ta sama Dan achaza taje gida ta shirya, Nan Ahmad yace” dama ke nakejira mu tafl ko?
Dan 8 na safe yakamata muna Chan Dan case din Mudansir za’a fara, Tace” eh na kintsa Bari na Sha ruwa yace” ok Ki sameni a waje
Suna tafe suna hira ga garin lokacin sanyi kowa na gida ko ka fito hazo ne Dan in ba ma’ai kata ba se akai 10 na safe a gida Dan ko ka fito baza kaga hanya sosai ba
Zeenat ne tace” na manta da camera din a gida da zansha ruwa, Ahmad yace karki damu,Nan take ya Kira Kabiryace” sunyi nisa sosai da gida plz yaje ya dakko mai camera din su hadu a court, Kabir yace” 0k Aiko Ina kan hanyar zuwa gidan mutafl tare, tunda Kun kuce mu hadu a chan kawai Ahmad yace ok
Sun shugo wani titi ba alamar kowa, Ga Shi 6:20 ba mutane sosai ji sukai an sasu a tsakiya ta ko Ina mota, innalillahi wa in na ilaihir rajiun suke ta ambatowa, Zeenat kuwa tana Kuka tana addua tasan karshen su yazo, Wani ne yace” Dan ubanku zaku fito ko bazaku f’Ito ba, sukaga dai Basu da alamar fltowa Kuma suna ganin zasu Bata musu lokaci Nan Suka fesa musu hodar da aka taba fesa ma zeenat Nan take Suka fara bacci, Bushewa da dariya sukai aka dauka zeenat aka kaita bayan sit Shi Kuma aka mingirashi
zuwa kujerar zeenat
Hmm