ZEHRA CHAPTER 3
Haka dai Mustapha ya cigaba da kai Zehra makarantar koyon girkin ta a duk safiya akan tilastawar Mummy yayinda direba yake dauko ta. duk yadda ta so su dan dinga yin hira da shi abun ya faskara. Kullum haka suke zama babu mai yi ma wani Magana.+ A bangaren Mustapha ma idan zaka yanka shi bazai iya tantance kamarnin Zehra ba domin kuwa ko kallon ta baya yi. A lokacin da zasu koma gidan su Zehra kuwa Fadeela ta cika da murna a dalilin zata koma kusa da masoyin ta. ita kuwa Zehra bata ji dadi ba a dalilin zata yi missing studying Mustapha for a while. ABU-YAZEED RESIDENCE A yau kwanan su biyu da dawowa gidan su Zehra. Tana kwance a dakin ta rungume da pillow yayinda take fama da ciwon ciki. A yau dai tun da safe take ta fama da ciwon ciki. Khadeeja ce ta qwanqwaso qofar dakin ta shigo riqe da tea cup na ruwan lipton. Tana qarasowa wurinta ne ta zauna a gefen gadon sannan tace “Anty Zee, your Tea” Zehra wadda idanuwan ta suka yi ja ne ta tashi zaune ta karba tare da fadin “thanks Deejah” Ta kai cup din bakin ta tayi sipping tea din ne Fadeela ta shigo dakin. Da sauri ta qaraso kan gadon tace “Allah sarki Zee ya cikin? Ya rage ciwo??” Zehra ta dan yi murmushi tace “yana sauka Dee, ya kika baro masoyin naki??” Tana murmushi tace “lafiya lau, ya tafi asibiti yanzun nan aka kira shi” Ta gyara zama tace “hmm, kin san waye ya zo gidan nan yau?? Ya Musty..” Da sauri Zehra ta dago kai tace “are you serious??” gani suka yi ta ajiye kofin tea din a kan bed side drawer tare da sauka daga kan gadon ta janyo hijabi dogo tace “bari in je mu gaisa” Fadeela da Khadeeja wadanda suka saki baki suna kallonta kuwa sun cika da mamaki. Wadda take kwance cikin bargo tun da safe saboda ciwon ciki amma daga jin zancen Mustapha ta tashi looking strong and healthy. Fadeela tana murmushi tace “babes there is something you are not telling me, you sure you don’t have a crush on my brother??” Zehra wadda take gyara hijabin da ta sa ne tace “babes kawai gaishe shi zan yi, yana ina??” tace “yana falon Papa” Bata bi ta kan su ba ta fice yayinda ta bar su cike da mamaki. A lokacin da Zehra zata haura falon Papa ne ta hadu da Baraka mai aikin su riqe da tray na kayan motsa baki zata kai ma Mustpha. Da sauri tace “kawo nan Baraka, bari in kai mishi” Baraka kuwa ta miqa mata cike da girmamawa sannan ta koma. Zaune yake a kan one seater kujera yayinda Papa da Anty suke zaune a kan three seater suna hira. Dukda dai Papa ne ke yi mishi tambayoyi yana amsawa. Zehra ce ta shigo falon cikin sallama wanda suka amsa. tana tafe yayinda ta kalle shi. Sanye yake cikin wani farin yadi mai kyan gaske da hula ta zamani mai kyau. Kamar ko dayaushe yayi masifar kyau. Zuciyarta ce take ta bugawa yayinda ta qaraso wurin shi ta ajiye tray din a kan stool din da ke gefen kujerar da yake zaune. Cike da natsuwa tace “ina wuni Ya Musty” STORY CONTINUES BELOW Kamar kullum bai kalle ta baya ce “lafiya” Anty ce tace “Zehra ya aka yi kika fito? Jikin ya sauka kenan?” ta koma kujerar da take fuskantar Mustapha ta zauna tare da fadin “ya dan warware Anty” Papa ne yace “babu lafiya ne Baby??” ta dan yi murmushi tace “yes Papa, but I am getting better” yace “ko dai a kira Zain ne??” tace “No Papa, I am okay” Bata ankara ba ta ji muryar shi yace “Allah ya qara sauqi” Ba Zehra ba hatta ni sai da nayi mamaki.2 Da sauri ta kalli fuskar shi wadda kamar kullum babu expression tace “thank you Ya Musty, I missed you” Gni nayi ya dan bata rai yayinda ya cika da mamaki. Bai gama processing abinda tace bane ya ji tace “I mean I missed going to my Cooking school with you” Papa yana murmushi yace “wato kai ta mayar direban ta kenan” Mustapha ya dan yi murmushi yayinda Papa ya cigaba da fadin “ai tun lokacin da mahaifiyarta ta rasu a car accident take tsoro, you know she was in the car with her…” Papa bai qarasa maganar shi ba Zehra ta fashe da kuka. Cike da tausayawa Mustapha yake kallon ta yayinda Anty ta tashi ta rungume ta tana bata haquri. Papa ya girgiza kai yace “stop crying my Baby, Insha Allah Momma is in a better place kin ji” Muryar Mustapha suka ji yace “Allah ya jiqan ta da Rahama” suka amsa da “ameen” Yana kallonta yace “stop crying Zehra, all she needs is your prayers. A duk lokacin da kika tuna ta ki dinga karanta Allaahum-maghfir lahu Allaahumma thabbithu. there is a much longer Du’a, I will send it to you through Dee” Sossai Zehra ta ji dadin kalaman shi. tana share hawayen ta tace “nagode sossai” Ajiye cup din da ke hannun shi yayi yace “its okay dear” yayinda ya miqe yace “Papa ni zan koma gida” Papa yace “kayi qoqari ai tunda ka zo har gida” Murmushi yayi yace “sai da safe” ya kalli Anty yace “Anty Good night” Zehra dai tana nan zaune tana kallon shi har ya tafi yayinda take mamakin wai Mustapha ne ya kira ta da “dear” wata zuciya ce tace “maybe he didn’t even realize he said it..” can kuma tace “I doubt, people like them are aware of whatever comes from their mouths” Aikuwa a ranar Fadeela tayi ma Zehra tsiya sossai. A qarshe ma addu’a ta dinga yi akan Allah yasa su fara soyayya a daura musu aure tunda dai dama Zehra tace tana son halin shi. Ni kuwa nace ameen… *********** Ranar da suka koma gidan su Fadeela kuwa ran Zehra yayi masifar baci jin cewar Mustapha yayi tafiya, Ya je Kaduna. Gaba daya ma duk sai ta ji komai baya yi mata dadi. Ita kanta lokutta da dama har mamakin kanta take yi yadda ta damu da mutumin da bai ma san ta ba. Har suka gama zaman su a gidan suka koma gidan su bai dawo ba. tun tana sa ran ganin dawowar shi har ta cire. A kullum kuwa Addu’a take a kan Allah ya sassauta mata yawan tunanin shi da take yi domin kuwa it’s getting out of hand. ************* OMAR TAFIDA RESIDENCE A yau kwana uku kenan da su Zehra suka dawo gidan su Fadeela. Direban gidan ne ya dawo da ita gida daga Cooking school wuraren qarfe biyar saura na yamma. STORY CONTINUES BELOW Ganin Mummy tayi ta fito tare da Furera wadda take riqe da Tray na abinci. Zehra tace “Mummy ina zaku je ne haka?” Mummy wadda hankalinta yake a tashe tace “Mustapha ne ya dawo babu lafiya, kin san Mura tana bala’in bashi wahala, ta sakar mishi zazzabi, shine zan je in duba shi idan jikin bai lafa ba mu tafi asibiti” Zehra dai tuni ta shiga tsananin damuwa yayinda ta saita murya da qyar tace “bari in bi ku mu duba shi” Mummy tace “haba Zehra shiga gida ki huta abinki, yanzu kika dawo” Tace “no Mummy, mu je” Kwance yake a cikin duvet yana ta bacci a dalilin maganin muran da ya sha. Ko da suka shiga dakin Mummy ce ta zauna a gefen shi ta dafa kan shi wanda da alama ya sauka. Ji nayi tace “Alhamdulillah, da alama zazzabin ya sauka” Furera dai bayan ta ajiye tray din ne ta fita yayinda Zehra take tsaye tana ta kallon shi. Gani tayi ya bude idanuwan shi wadanda suka yi ja yayinda Mummy ta shafa kanshi tace “sannu, ya jikin?” Cikin low tone yace “fine Mummy” Muryar Zehra ya ji tace “Ya Musty Sorry” ahankali yace “thanks” Mummy ce tace “ga abinci nan an kawo maka. Tashi ka ci” Gyara kwanciya yayi yace “Mummy sai anjima” Tace “sam, ban yarda ba, yanzu zaka tashi ka ci” Idanuwan shi ya rufe yace “Mummy pepper soup din Cat fish nake so, it’s the only thing I can eat right now” Da sauri Zehra tace “bari in je in dafa maka Ya Musty, just give me few minutes” Kafin yayi Magana kuwa har ta juya ta fita. ************ A lokacin da Zehra ta dawo tuni Mummy ta koma sashen ta. Zuciyarta ce take bugawa yayinda ta tsaya a bakin qofar dakin nashi tana ta qoqarin composing kanta. Kusan minti uku tana nan a tsaye ne tayi gyaran murya tace “salamu’alaikum” Jin kamar bai ji bane yasa ta sake yin sallama. A na uku ne ta ji muryar shi yace “wa’alaikis salam, come in” Zaune yake a kan gadon shi amma fa cikin bargo yana duba wayar shi. Dukda kuwa he is disorganized yayi kyau as usual. Shigowar Zehra yayi daidai da dagowar shi ya kalle ta cikin ido. At a point in time kuwa sai da zuciyar shi ta buga. Yau ita ce rana ta farko da Mustapha ya kalli Zehra directly. A ran shi ne yace “Subhanalillah.. me nake gani?? it’s her… I mean My angel eyes?? I… I just can’t believe this…” Abin mamaki kuwa tunda ya sa mata ido bai daina kallonta ba. Zuciyar Zehra kuwa sai bugawa take yi yayinda ta kasa kallon shi. Hannun ta kuwa sai rawa yake yi ta qarasa ta ajiye tray din a kan bedside drawer dinshi. Juyawa tayi zata tafi yayinda ta ji muryar shi yana fadin “please serve me” gani nayi ta zaro idanuwa yayinda ta kasa motsi. Bugun zuciyarta kuwa yayi tripling a yanzu. Bata ankara ba ta sake jin muryar shi yace “please Zehra…” da sauri ta juyo ta kalle shi ta ga har wannan lokacin kallonta yake yi. Ajiyar zuciya tayi tace “okay” ta qarasa wurin tray din ta zuba mishi a plate. Har zuwa wannan lokacin kuwa Kallonta yake yi kamar mai kallon TV. wasu abubuwa ne suke ta yawo a qwalwar shi a game da Zehra. Sossai ta tafi da imanin shi. A ran shi kuwa babu abinda yake fadi illa “Oh my God, I have finally found her, Alhamdulillah my search is over” Bayan ta miqa mishi ne ta juya zata tafi ta qara jin muryar shi yana fadin please stay with me for a while mana” ba tare da ta juyo ba tace “Uhm, Ya Musty zan je inyi wanka ne yanzu na dawo…” Yace “you are still looking fresh Zehra, please stay” Zehra kuwa saboda bala’in rudewa banda kyarma babu abinda jikin ta yake yi. Mamaki take yi anya wannan Mustaphan da ta sani ne kuwa. Gani nayi ta koma kan resting chair din dakin ta zauna yayinda ta duqar da kanta tana wasa da yatsun hannuwan ta. Murmushi yayi yayinda ya fara shan pepper soup din wanda yayi masifar yin dadi. Yana ci yana ta kallon ta har ya gama. Ita dai Zehra ganin cewar zaune kawai take ba hira suke yi ba ne yasa tace “please Ya Musty in tafi?” yi yayi kamar bai ji ta ba. Dago idanuwa tayi ta kalle shi cikin shagwaba tace “Please..” Gani tayi ya lumshe idanuwa tare da shigewa cikin duvet yace “you can go Zehra, thanks for the peppersoup” Miqewa tayi tace “can I take the dishes??” yace “no, just go” In a confused state ta fita daga dakin. A yadda yayi reacting kuwa ta tabbatar cewar bai so ta tafi ba toh amma kuma ai ba hira sukeyi ba plus idan dai Mustaphan da ta sani ne ai babu ruwanshi da ita. Meyasa ya ji haushi don tace zata tafi????3 ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE A bangaren Zehra dai gaba daya ta kasa fahimtar yanayin kallon da Mustapha yake ta yi mata.+ A tunaninta baya son kallonta amma kuma sai gashi a yau ya kasa dauke idanuwan shi daga kanta. Tana zaune a kan gado tayi tagumi ne ta ji muryar Fadeela tana fadin “ke Zee, what are you thinking about ne haka? Ko kin samo mana prince charming din ne?” Ajiyar zuciya tayi tace “wallahi Dee your brother got me confused this evening” Da sauri Fadeela ta haye gadon tace “me yayi Zee, bani in sha” Zehra ta bata labarin abinda ya faru. Tunda kuwa ta fara bata labarin ta saki baki cike da mamaki. Aikuwa tana kaiwa fullstop Fadeela ta fashe da dariya sannan tace “OMG, Zee kin kuwa san cewar you have done something extra ordinary akan Ya Musty? Kin tabbata ba son ki ya fara yi ba kuwa??” Kafin Zehra tayi Magana kuwa na ga ta sauka da sauri tace “aikuwa dama yanzu zan je in gaishe shi da jiki kuma daga nan sai nayi interrogating dinshi akan ki” Da sauri Zehra ta riqo ta tace “don Allah ki bari Dee, kada fa ya mare ki” Fadeela tayi dariya tace “na tabbatar bazai mare ni ba Zee, ai kin fara canza shi. lallai kuwa na tabbatar ke mayya ce” Zehra ta fashe da dariya yayinda tace “you are crazy Dee” Fadeela tayi mata gwalo tare da fadin “nagode Zee” Daga nan ta wuce ta fita yayinda Zehra ta shige dressing room don shirin yin wanka. ************** Zaune yake a kan Chinese Rug na dakin shi yayinda yake riqe da Sketch din. Tun da Zehra ta bar dakin ya dauko sketch din ya riqe yayinda yake ta tunani kala kala. ji nayi yace “I can’t believe these eyes really exists, toh yanzu da na gano ta ya zanyi? Kawai ce mata zanyi ina sonta saboda idanuwan ta ko kuwa?? Do I even like this particular girl??” Haka dai ya cigaba da saqe saqe kala kala akan Zehra. Bai ankara ba ya ji muryar ta a kusa da shi tana fadin “laaa, Ya Musty wannan sketch din kamar idanuwan Zehra” ta zauna kusa da shi tace “dama ka san ta ne?” Hararar ta yayi yace “me kike yi a nan? ko sallama babu kika shigo mun daki” Murmushi tayi tace “yi haquri My best Yaya, na zo gaishe ka ne da jiki kuma I swear nayi sallama har sau uku baka ji ba” ta qara matsawa daf da shi tace “but I realise cewar you were so busy” Ajiyar zuciya yayi sannan yace “hey tell me about your friend” Zaro idanuwa tayi tace “what?? Dagaske yaya?” tayi pinching hannun ta tace “Allah yasa ba mafarki nake ba” Ji tayi yace “I will slap you fa” da sauri tace “yi haquri bros, I will tell you everything about her” Daga nan kuwa ta faro mishi labarin Zehra tun farko har qarshe. Ko da ta gama ta kalle shi sai gani tayi ya jingina bayan shi da Ottoman din dakin yayinda ya lumshe idanuwa. Murmushi tayi tace “Ya Musty kana ji na kuwa??” Idanuwan shi ya bude yace “I heard you Dee, thanks” Fadeela ta zaro idanuwa tace “as in shikenan?? You didn’t tell me if you love her or not” Ganin yanayin fuskar shi ne tayi saurin cewa “yi haquri, amma please tell me inda ka samu wannan sketch din, ka san ta ne dama??” STORY CONTINUES BELOW Juyowa yayi ya fuskance ta sannan yace “Dee, I really don’t know your friend. The thing is I have always imagined a lady with these eyes” ya shafa sketch din sannan ya cigaba da fadin “ban taba sanin cewar zan ga mai irin su ba…” Bata bari ya qarasa maganar ba tace “toh Ya Musty just tell her you love her, wallahi Zee is a nice girl. Nasan ka sani ai…” Miqewa yayi yace “what the hell Dee, She only has the eyes I like and it doesn’t mean cewa ina son ta” Fadeela ta miqe tace “shikenan Ya Musty, Allah ya baka lafiya” Fadeela tana fita daga dakin kuwa Mustapha ya fada kan gadon shi yace “I like what I just heard about her, kyakyawa ce, she has the eyes and most importantly the character. Then what??” Ni kuwa nace then make a move… ah toh2 ************ Fadeela kuwa ko da ta koma dakin su ta samu Zehra zaune a gaban madubi tana shafa mai. Cike da murna ta qarasa ta rungumeta ta baya tace “I am so happy Zee, wallahi bazan yi kaffara ba Ya Musty has a crush on you. Ina kyautata zaton kwanan nan zai gaya miki yana son ki” Zuciyar Zehra ce ta buga da jin kalaman Fadeela. Sossai ta rikice yayinda Fadeela ta zagayo ta gabanta ta jingina da Vanity table tace “kin san ya tambaye ni everything about you?” Zehra wadda zuciyarta take ta bugawa tace “dagaske? Why?” Fadeela tana dariya tace “ah toh Zee, son ki yake yi kenan. Hmm, I even asked him about that sketch fa and he told me wai its just his imagination. The bottom line dai is that ya gan ki da idanuwan da yake so kuma ya afka tarkon ki” Ta bugi kafadar ta tace “gaskiya kin yi qoqari da kika sace zuciyar yaya na” Zehra ta miqe tace “you are just imagining things Dee..” ta wuce dressing room yayinda Fadeela ta bi bayan ta tace “toh yanzu lets assume dagaske yace yana son ki, ke kina son shi??” Da sauri Zehra ta juyo ta kalle ta tace “stop it Dee” Fadeela tana dariya tace “okay sorry, ni dai na san yana son ki” daga nan kuwa ta juya ta fita yayinda ta bar Zehra dafe da qirjinta, idanuwanta a rufe ta saki ajiyar zuciya tare da fadin “idan dagaske ne ya zanyi??” A yau kuwa bacci ma gagarar Zehra yayi domin kuwa ta takura ma kanta da tunani. ita kam ta san cewar Mustapha yana affecting dinta sossai, muryar shi kadai idan ta ji sai zuciyarta ta dinga bugawa, idan ta gan shi kuwa bata son dauke idon ta daga kan shi sannan haka kawai sai ta tsinci kanta da bata lokaci tana tunanin shi. What is happening to her??5 ♤♤♤♤♤♤ A yau ranar Saturday Fadeela da Zehra suna gida. Da yamma ne hadari ya hadu sossai. Zehra wadda take tsaye a wurin window na dakin su tana kallon harabar gidan. Dayake dakin nasu a sama yake tana da clear view na harabar gidan. Ji nayi tace “Dee kin ga hadari kuwa??” Fadeela wadda take kwance a kan gadonta kuwa qara shigewa bargo tayi tace “perfect weather to relax ba” Zehra wadda take hangen garden din gidan daga dakin su ce ta hango Mustapha zaune a daya daga cikin kujerun garden din, Kanshi a kwance bayan kujerar yayinda fuskar shi take kallon sama. Idanuwan shi a rufe yayinda yayi zurfi a tunani. Zehra wadda ta qura mishi idanuwa kuwa mamaki take yi akan yadda bai damu da hadarin da ya taso ba. Tana nan tana kallon shi ne aka fara iska yayinda hadarin ya taso gadan gadan. Bata ankara ba ta ga an fara yayyafi. Tun tana sa ran zai tashi har aka fara ruwan saman bai motsa ba. Hankalinta ne yayi masifar tashi. Ba tare da tunanin komai ba kuwa ta juya ta fita a guje wanda har Fadeela tana fadin “hey ina zaki je??” “ina zuwa” abinda kawai ta fada kenan. ********** Ruwan sama ne mai qarfi yake sauka a jikin shi amma ko motsawa bai yi ba. Mustapha dai gaba daya tunaninta ya hana shi saqat. Tun jiya da ya kalle ta sannan ya ji labarinta ya shiga confusion akan ta.1 Kamar daga sama ya ji an taba hannun shi wanda ya sa shi saurin bude idanuwan shi. Zuciyar shi ce ta buga a dalilin ganin kyakyawar fuskar ta. Cike da mamaki yake kallon ta yayinda ruwan yake sauka a kanta itama. Zuciyoyin su kuwa sai bugawa suke ta yi. Da qyar ta saita muryar ta tace “Ya Musty me kake yi anan? Kasan kana mura, please ka tashi ka shiga cikin gida” Shi dai Mustapha tunda ya sa mata ido ya kasa motsi, gaba daya ma bai ji abinda take fadi ba domin kuwa ta dauke hankalin shi gaba daya.2 A ran shi kuwa yake fadin “Ya salaam, why do I feel this way?? Me ke damuna ne??” Zehra dai ganin kamar bai ji ta bane tace “please yaya ka tashi, ruwan fa zai sa maka zazzabi sannan…” Ji tayi yace “please go” Cikin rashin fahimta tace “na’am??” kauda kan shi yayi da sauri yace “I said go..” Jiki a sanyaye ta juya amma ko kafin ta daga qafar ta kuwa ta ji ya riqo hannunta wanda ya sa tayi saurin juyowa yayinda duk ta bi ta rikice. Saurin sakin hannun nata yayi yayinda ya miqe yace “uhm, I am sorry, thank you” Daga nan kuwa ya fara tafiya yayinda ta tsaya tana ta kallon shi. Juyowa yayi ya ganta a tsaye inda ya barta. Ajiyar zuciya ya saki sannan yace a ranshi “why is she not moving??” Dawowa yayi yace “bazaki shiga gida bane?? Ko so kike kiyi zazzabi kema?? Please get inside coz bana so kiyi blaming dina idan wani abu ya same ki” Zehra dai murmushi tayi tace “whatever happens to me will be your fault Ya Musty, remember that” Daga nan kuwa ta wuce ta bar shi anan tsaye yana analysing statement dinta. ♤♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Wuraren qarfe goma sha daya na dare tana kwance a kan gado cikin bargo tana ta kyarmar sanyi.+ Jikinta yayi zafi kamar wuta. Fadeela wadda take a rikice ce tace “Zee kin dai san cewar laifin ki ne ko? Me zai sa ki shiga cikin ruwan sama bayan kin san cewar Papa yayi warning dinki? You know perfectly well cewar duk lokacin da kika shiga ruwa sai kinyi jinya. Toh wai tsaya ma in tambaye ki, me kika je yi a cikin ruwan?” Miqewa tayi tace “gaskiya zan je in fadi ma Mummy, you need to go to the hospital. thank Goodness My sweetheart, your brother is on night shift” Muryar Zehra qasa qasa tace “I am sorry Dee, please don’t tell Mummy, zan samu sauqi” Fadeela dai bata saurare ta ba ta wuce ta fita. Aikuwa ba da jimawa ba sai gata nan ta dawo da Mummy harda Daddy. Ganin yanayin jikin ne basu wani bata lokaci ba aka tarkata ta aka sa ta mota. Sanin cewar Mustapha yana fama da nashi zazzabin ne yasa suka tafi asibtin ba tare da an neme shi ba. NATIONAL HOSPITAL Sossai Zehra take jin jiki domin kuwa a duk lokacin da ruwan sama ya bige ta sai ta kwanta. Zain ne ya bata taimakon gaggawa wanda kuwa har allurar bacci yayi mata. Bayan kusan awa daya gaba dayan su suna zaune a waiting room na dakin da aka kwantar da Zehra. Fadeela ce ta basu labarin abinda ya faru wanda ta tabbatar musu da lallai bata san meyasa ta shiga ruwa ba. Papa wanda ran shi ya bace ne yace “wallahi Zehra bata jin magana, kin sani cewar kina samun matsala idan kika shiga ruwa me zai sa ki shiga?? Idan ta farka I will deal with her” Su Anty da Mummy ne suke ta bashi haquri. Zain wanda ya shigo waiting room din riqe da takardu a hannun shi ya samu kujera ya zauna yace “Papa I am going to keep her here zuwa gobe mu gani, so I think zaku iya komawa gida. Dee da Deeja zasu zauna da ita but she will be fine Insha Allah” Ya kalli Anty yace “Anty ki hada mata ‘yan kayayyakin da zata buqata sai ki ba driver ya kawo mata” Da wannan ne su papa suka yi musu sallama suka tafi. ************ OMAR TAFIDA RESIDENCE Kwance yake a cikin bargo yayinda jikin shi yayi zafi sossai. Zazzabi ne ya saukar mishi a dalilin ruwan saman da ya sauka a kan shi. Da qyar ya lallaba ya dauko PCM a cikin first aid kit ya sha domin kuwa Mustapha ya tsani Allura a rayuwar shi. Shi kam mamaki yake yi yadda kawai mutum zai je asibiti a yi mishi allura, wannan ne yasa da zarar ya ji jikin shi babu dadi yake saurin shan magani don kar ciwo ya kai shi ga kwanciya. hahaha.. Musty an ji kunya🤣 Cikin ikon Allah kuwa kafin safe ya dan warware. ♤♤♤♤♤♤ Wuraren qarfe tara na safe ne Mummy ta shigo sashen shi. ta tarar da shi kwance kan kujera yana kallon News a TV. Sallamar ta ce tasa shi dagowa ya tashi zaune tare da fadin “Mummy ina kwana” Mummy ta qarasa wurin shi ta taba wuyan shi tace “lafiya, ya jikin?” yace “da sauqi, yi haquri ban shigo na gaishe ki ba” Murmushi tayi tace “babu komai Mustapha, Furera zata kawo maka breakfast dinka, ni zan je asibiti in dubo Zehra babu lafiya” STORY CONTINUES BELOW Zuciyarshi ce ta buga yayinda yace “subhanalillah, Mummy me ya same ta?” Mummy tace “wallahi ruwan sama ta shiga jiya kuma ta sani sarai a duk lokacin da ta shiga ruwa sai ta kwanta jinya. Na rasa dalilin da yasa tayi hakan” Tunda Mummy ta fara Magana kuwa ya shiga tsananin damuwa domin kuwa ya sani sarai laifin shi ne. Kalaman da tayi mishi jiya inda take fadin: “whatever happens to me will be your fault Ya Musty, remember that” Ji nayi yace “inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un..” Mummy ce ta dafa shi tace “are you okay??” Saita murya yayi yace “I am fine Mummy, wane asibiti ne?” tace “National hospital” yace “Allah ya bata lafiya” Mummy tayi murmushi tace “Ameen Mustapha na, kaima Allah ya baka lafiya” Bayan Mummy ta fita kuwa ya kasa tsaye ya kasa zaune. Gaba daya ya shiga damuwa. Ji nayi yace “duk ita ta janyo hakan, da bata yi stucking a cikin qwalwa na ba all these wouldn’t have happened, toh yanzu ya zanyi??” Ni kuwa nace zuwa zaka yi dubiya… Ah toh🤣 ************ NATIONAL HOSPITAL Wuraren qarfe takwas na dare dukkanin su suna dakin da aka kwantar da Zehra yayinda take cikin bargo idanuwan ta a rufe dukda ba bacci take yi ba. Daddy ne yake fadin “ai na ga jikin nata ma babu laifi, bari Zain din ya shigo mu ji” Papa yace “ai da ya barta ta qara koda kwana uku ne in yaso yayi ta zabga mata allurai, gobe ta qara” Cikin shagwaba Zehra tace “Paaaapaaaa” yayinda aka fashe da dariya. Haka dai suka cigaba da hirar su yayinda bacci ya dan kwashe Zehra. Su Papa sun miqe suna shirin tafiya ne suka ji an qwanqwaso qofar dakin yayinda Anty tace “yes, come in” Cikin sallama ya shigo dakin yayinda gaba dayan su suka juyo suna kallon shi. Papa ne yace “ah ah, Soja ne??” Zehra ta bude idanuwan ta da sauri ta kalle shi. Sanye yake cikin qananan kaya, yayi kyau sossai. Wani murmushi ta saki yayinda tace “Ya Musty you came??” tayi maganar cikin tambaya. Papa ne yace “au, dama ba bacci kike yi ba kina jin mu ashe?” Mustapha wanda ya rasa me zai ce ne na ga ya dan yi mata murmushi sannan ya gaishe su. Anty ce tace “ya jikin ka??” yace “da sauqi Anty, thanks” Papa yace “banda abinka ina ka taba ganin marar lafiya ya je duba marar lafiya, ai da kayi zamanka ka huta” Murmushi yayi yace “ai na warware Papa” Mummy da Daddy kuwa sun ji dadin zuwan nashi domin ko ba komai ya nuna ya damu da familyn Papa. Fadeela wadda take cike da tsananin mamaki ce tace “Ya Musty come and sit” Ba tare da yace komai ba ya je ya zauna. Zuciyar Zehra kuwa sai bugawa take yi yayinda ta sa mishi ido. Bayan su Mummy sun tafi ne ta cigaba da kallon shi yayinda take cike da murnar zuwan da yayi. A yanzu kuwa ya gama clearing doubts dinta gaba daya. STORY CONTINUES BELOW Ji tayi yace “hey, ya jikin??” tana murmushi tace “Alhamdulillah, thank you very much for coming. Na ji dadi sossai da ka zo Ya Musty” Daga nan bai sake fadin komai ba ya fiddo wayar shi yana ta latsawa, ita kuwa idanuwa ta sa mishi. Ko sau daya kuwa bai dago kai ya kalle ta ba. Fadeela da Khadeeja wadanda suka dawo daga rakiyar su Papa ne suka shigo dakin. Fadeela kuwa sai kallon Zehra take tana murmushi. Wallet dinta ta dauka tace “deeja zo mu je ki raka ni mu siyo Pizza” ta kalli Mustapha cike da tsokana tace “Ya Musty please look after my friend before I return” hahahaha… Kusan minti goma da fitan su Fadeela ne tari ya sarqe ta yayinda ta dafe qirjin ta. Sossai take ta tari yayinda ya dago kai yana kallonta. Da sauri ya tashi ya dauko goran ruwa ya bude ya miqa mata yana fadin “sorry..” Tashi tayi zaune wanda yayi daidai da faduwar hular kanta yayinda kitson kalban ta ya warware. Tsayawa yayi cak yana kallon gashin nata da yadda tayi bala’in kyau. A ranshi ne yace “Subhanalillah, how could she be this beautiful??” Zehra wadda take ta shan ruwa bata ma san yana kallon ta ba. Bayan ta gama sha ne ta miqa mishi tace “thank you” Ko da ya karba ya ajiye komawa yayi ya zauna. Bata ankara ba ta ji muryar shi yana fadin “Meyasa kika shiga ruwa bayan kin san abinda hakan ke janyo miki?” Murmushi tayi tace “I guess I wasn’t thinking straight ne” Kai tsaye yace “don’t do it next time” tace “Kai ma kar ka sake…” Da sauri ya dago kanshi yana kallonta cike da mamakin abinda tace mishi wanda kuwa kafin yayi Magana ne Zain ya qwanqwaso qofar ya shigo. Ganin Zehra zaune ne yayi mamaki sossai har yana fadin “like seriously?? Daga zuwan Romeo din naki har kin warke?? Dama can pretending kike yi ko??” Zehra ta fashe da dariya tace “Ya Zain ba shi bane fa, wannan yayan sweetheart dinka ne, your Inlaw” Zain ya kalli Mustapha yace “Oh my Goodness, sai yau Allah yayi muka hadu” Mustapha ya miqe tare da miqa mishi hannu suka yi musabaha sannan yace “ranan da na je gidan ku ance ka je hospital, how are you? Ya aiki?” Yace “Alhamdulillah, ya naku aikin?” yace “fine” Bayan ya zauna ne Zain ya qarasa wurin Zehra yace “how are you feeling??” cikin shagwaba ta kwanta a jikin shi tace “Good, don Allah kayi discharging dina na gaji” Yana murmushi ya ja kumatun ta yace “I will, Akwai Allurar ki ta qarshe gobe da safe, daga nan shikenan” Su Fadeela ne suka shigo dakin, aikuwa tana ganin Zain tace “Sweetheart ashe ka shigo” Yana murmushi yace “yes sweetheart, ina kika je ne?” ta nuna mishi kwalin da yake hannun ta tace “Pizza na je siyowa across the street, ko zaka ci ne?” yace “sure I will, let me just finish up here then we go to my office” Mustapha wanda yake sauraron su yana ta mamakin yadda suke ta zancen su ba tare da damuwa cewar akwai mutane ba. tunani yake yi yaushe zai taba yin haka da budurwa. hehehe… Gani nayi ya miqe yace “uhm, ni zan tafi” ya sa hannu a aljihun shi ya ciro chocolate guda daya ya miqa ma Zehra yace “sorry I didn’t get anything for you, Allah ya qara lafiya” Cike da murna ta karba tace “nagode Ya Musty” Ya kalli Zain yace “toh my inlaw sai da safe, looking forward to knowing you better” yace “insha Allah zan zo har gida mu gaisa” Yana fita kuwa Fadeela tace “yessss, I swear something is about to happen” Zain ne yace “me kike nufi” Ta kalli Zehra tace “My brother surely has a crush on your sister and I think she does too. Sanin halin shi yasa ban taba tunanin zai zo duba Zehra ba amma kuma sai gashi ya zo dukda fa shima baya da lafiya” Da sauri Zain ya kalli Zehra wadda take kallon Chocolate din da Mustapha ya bata yace “wai haka ne Zee, do you like him??” Murmushi tayi amma bata ce komai ba. Gani suka yi ta bare chocolate din yayinda Khadeeja tayi saurin fadin “ci zaki yi Anty Zee?? I thought ba kya cin chocolate??” Zehra ta Harare ta tace “wallahi sai na ci wannan” Fadeela wadda take dariya tace “dole ki ci ai… banda Ya Musty ma ya za’a yi ka kawo ma marar lafiya chocolate guda daya??” Zain Wanda yake dariya yace “Ba soja bane?? ai komai nasu daban” *********** Zaune yake a cikin motar shi yana qara maimaita kalaman da ta fadi “Ya Zain ba shi bane fa, wannan yayan sweetheart dinka ne, your Inlaw”2 Sossai wannan maganar take yawo a qwalwar shi. Gani nayi ya kwantar da kanshi a kan stirring yayinda yace “it means she has a boy friend kenan??” can kuma yace “toh wai me ya ruwan ka??” tsaki yayi tare da tada motar ya ja ya fita daga asibitin.2 ♤♤♤♤♤♤♤ Hehehehehe… Wani fa ya zurma a soyayya… Zehra fa ta kama zuciyar mazaaa🤣🤣