ZEHRA CHAPTER 4

ZEHRA CHAPTER 4

ABU-YAZEED RESIDENCE A yau kwana daya kenan da aka sallami Zehra daga asibiti. Tunda ta dawo kuwa take ta hutawa domin kuwa Zain ya bata hutun bed rest na kwana uku kafin ta cigaba da al’amuran ta. Wuraren qarfe goma sha daya na safe tana kwance a cikin bargo tana replying messages din mutane wanda suke ta wishing dinta quick recovery yayinda take hira da qawarta Hidaya wadda ta zo gaishe ta. Fadeela kuwa ta je aiki yayinda Khadeeja ta tafi school. Baraka mai aikin su ce ta shigo riqe da wani cute bouquet na white flowers da wata ‘yar qaramar takarda a ciki. Zehra wadda ta sa ma bouquet din idanuwa ce ta tashi zaune da sauri tace “wow, Baraka daga ina haka??” Baraka ta qarasa wurin ta tace “Anty dama Hajiya ce ta bani in kawo miki” Da sauri ta miqa hannu tace “bani in gani” Baraka ta miqa mata yayinda Hidaya tace “I have never seen a bouquet this cute, babes waye ya aiko miki? dama kina da boyfriend kike ta boyewa ko?? Allah ya kama ki” 4 Zehra wadda na ga tana karanta takardar kuwa dafe qirjin ta tayi yayinda ta zaro idanuwa tace “what???” Kafin Hidaya tayi Magana kuwa Anty ta shigo dakin. Tana murmushi ta kalli Zehra tace “ai sai ki fito ki je ki ga kayayyakin da ya aiko miki, kaya tuli guda kamar mai shirin bude shago..” Gani suka yi Zehra ta yaye bargo tare da sauka a guje ta fita. Hidaya ce ta bi bayan ta yayinda Anty take ta yi mata dariya har tana fadin “lallai akwai Magana” ********* Tsaye take a kicin dinsu tana kallon tulin kayan da ya aiko. Sossai ta cika da mamaki domin kuwa Carton Carton ta gani na drinks kala-kala da packets din chocolates da su biscuits masu tsada. Ga su ice cream nan kala kala da su fresh milk. Fruits kuwa kamar an shiga gona an debo. Hannu ta sa ta rufe bakin ta cike da mamaki tace “I can’t believe this” ta kalli qawarta tace “Hidaya please hit me, ina so in tabbatar da cewar ba mafarki nake yi ba” Hidaya wadda ta taba qawarta tace “hey you are not dreaming, tell me waye ne ya aiko miki kaya haka??” Murmushi tayi tace “Ya Musty..” STORY CONTINUES BELOW Hidaya tace “what?? Wanda kike bani labarin halin shi dinnan?? The same soldier that brings you to school da har kike fadin against his wish yake kawo ki?? Dama saurayin ki ne??” Kafin Zehra tayi magana kuwa Anty ta shigo kicin din tace “aikuwa gwara ki tambaye ta, wannan kaya haka fisabilillahi idan banda tsabar barnar kudi me zai sa Mustapha yayi wannan?” Hidaya tana dariya tace “Anty kin san sojoji fa dama haka suke, ina gani kamar rashin zama cikin civilians idan suka tashi yin abu zaki ga daban. Haka Uncle dina yake shima” Anty tace “toh Allah ya kyauta” ta kalli Zehra wadda take cike da confusion tace “sai ki samu lokaci ki kira shi kiyi mishi godiya” tace “insha Allah” ************ Ko da suka koma daki riqe takardar tayi tana ta kallo yayinda take ta tunani kala kala. Hidaya ce tace “babe, its obvious the guy is interested in you kuma fa kema na ga kamar you like him. Maganar gaskiya kun dace sossai. ga ki kyakyawa ga shi kyakyawa. Can’t wait to see your cute babies” Zehra ta lumshe idanuwa tace “I swear Hidaya duk lokacin da Ya Musty yayi abu sai ya bar ni ina ta mamaki. But I don’t believe he is interested in me, I am not his type, its obvious the guy has a high taste, kawai dai I feel karamci ne…” Hidaya tayi murmushi tace “hmmm, hope dai kin san ke first class babe ce?? Anyways muna nan dai zamu ji bayani. Ni kuma ina nan zan taya ku da addu’a Allah ya tabbatar da alkhairi a tsakanin ku” Kafin Zehra tayi Magana kuwa wayar hidaya ta fara ringing yayinda ta miqe ta ja veil dinta ta amsa wayar tare da fadin “Yi haquri Mom, na je gidan su Zehra ne duba jikinta amma yanzu zan qarasa in siyo miki” can kuma tace “Insha Allah zata ji” Bayan ta kashe ne tace “Babes bari in zo in tafi, Mom tana gaishe ki” Zehra ta miqe tare da fadin “ina amsawa, mu je don Allah ki kwashi naki share din ki sa albarka..” Hidaya tace “haba babes, ke aka kawo ma..” Zehra ta fashe da dariya tace “ai wadannan kayan zasuyi wata uku basu qare ba a gidan nan, abeg lets go” Haka dai Zehra ta ba qawarta kayan dayawa wanda masu aiki suka kwasar mata yayinda ta dinga godiya. ♤♤♤♤♤♤♤♤ “…with good wishes and prayers that you get well soon” -Mustapha Omar Tafida. Fadeela wadda take tsaye a tsakar dakin su ta karanta saqon nan ya fi sau goma. Gani nayi ta fashe da dariya tare da fadin “hmmm, lallai ma Ya Musty wato shi nashi style din daban ne kenan” Kallon Zehra tayi tace “babes why do I feel kamar Ya Musty is responsible for what happened to you? There is something you are not telling me” Zehra ta lumshe idanuwa sannan ta bude tace “I am sorry Dee, you are right” Daga nan kuwa ta kwashe mata labarin abinda ya faru ranar da suka jiqe a ruwan sama. Cike da mamaki Fadeela ta matsa kusa da Zehra ta riqe hannun ta tace “Zee tell me the truth, how do you feel about Ya Musty” STORY CONTINUES BELOW Ajiyar zuciya tayi tace “I swear Dee I am confused, the thing is duk lokacin da na ji muryar shi sai zuciya ta tayi ta bugawa. His presence makes me restless, again I just find myself thinking about him most times. I feel kamar saboda I am interested in knowing his kind of personality ne” Fadeela ce ta fashe da dariya tace “uhm, I am sorry to say this Zee, you are slowly falling in love” Zehra ta bata rai tace “haba Dee, if this is called love ashe kuwa abin wahala ne. kema haka kike ji game da yaya na??” Fadeela ta girgiza kai tace “ko kadan Zee, its just the first stage. Relax and allow yourself to fall, ina mai tabbatar miki cewar kin sace zuciyar yaya na. I have never seen this side of him a rayuwa na kuma duk a sanadin ki ne” Ta janyo wayoyin su tace “you know what?? zanyi saving contact din shi a wayar ki, I want you to call him and thank him amma zaki sa a speaker. I want to hear him talk to you” Ajiyar zuciya tayi sannan tace “okay” Bayan Fadeela ta sa mata contact din ne suka yi dialing wanda kuwa zuciyar Zehra sai bugawa take yi. Fadeela wadda take ta yi mata dariya tace “hey relax” Har ta tsinke bai dauka ba. sun kira wurin sau uku amma bai dauka ba, daga nan ne suka yanke shawarar after dinner they will try again. ************ Wuraren qarfe goma saura ne Fadeela ta qara dialing number din, a ringing na biyu ne ya amsa. Da sauri ta miqa ma Zehra yayinda suka sa a speaker. Muryar shi suka ji yace “hello” cikin muryar ta mai dadin gaske tace “hello, Ya Musty ina wuni” Ji suka yi yayi shiru wanda har sai da Zehra tace “are you there??” Gyaran murya yayi yace “hey I am here, how are you?” Fadeela wadda take boye dariyar ta ce ta dago mata hannu alamar good job. Zehra tace “I am fine, ka gane mai Magana??” Yace “yes, your voice is kinda different Zehra” Murmushi tayi tace “I have been calling you tun dazu baka dauka ba” Yace “sorry I was on the road ne” Tace “zuwa ina? Ba dai kayi tafiya ba Ya Musty??” ita kanta da tayi tambayar sai da tayi mamaki domin kuwa bata san ta yi ba. Yace “Yes nayi tafiya, I am in Kaduna” Ji yayi ta dan yi shiru har sai da yace “hey are you there??” tace “uhm.. Yes” Yace “hope kin warke? Please don’t try what you did ever again” Cikin shagwaba tace “toh ai duk laifin ka ne” ji suka yi yace “I am sorry” Fadeela kuwa zaro idanuwa tayi jin maganganun yayan nata. Zehra ce tace “dama fa na kira ka ne inyi maka godiya akan kayan da ka aiko mun dazu. I really love the flowers, they are cute” STORY CONTINUES BELOW Yace “okay” Tace “amma fa Anty tana ta fada wai kayan sun yi yawa, you shouldn’t have bought so many stuff Ya Musty” Ji tayi yace “its no big deal Zehra, I just want you to eat and drink everything so you can recover fast” tayi murmushi tace “I will Ya Musty, ka ci abinci??” Murmushi yayi yayinda yake mamakin surutun ta. shi kam bai saba dogon bayani ba haka sai gashi tana ta sa shi yin Magana. Ji suka yi yace “I just returned to the hotel da na sauka, yanzu zan je in ci” Tace “okay toh bari in barka ka je ka ci” yace “okay thank you, wannan number dinki ne?” Tana kallon Fadeela tace “yes” yace “can I save it?” tace “yes Ya Musty” yace “alright then good night” Tana kashe wayar ne Fadeela ta saki ihu tare da fadin “yessssss, I am soo happy Zee. Wallahi Ya Musty yana son ki. I still can’t believe wai shine yake ta hira haka, I swear Zee ke mayya ce” Zehra wadda take dariya tace “for the first time Dee I was not restless while talking to him, me hakan yake nufi??” Fadeela tace “kar ki damu, zaki samu amsoshin ki real soon” Da kyau namesake…2 ♤♤♤♤♤♤♤ A yau kusan sati biyu kenan da Mustapha yayi tafiya. Tun ranar da suka yi waya da Zehra basu sake yin magana ba. Zehra kuwa tun tana sa ran zata ga kiran shi har ta fitar da rai. Lokutta da dama takan so ta kira shi ko ta tura mishi text message amma sai ta kasa domin kuwa a tunanin ta ba girman ta bane. A yanzu kuwa ta tabbatar ta fara kamuwa da son shi ne. Addu’a take yi Allah yasa yadda take jin shi a zuciyarta shima haka yake ji. ♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Da dare suna zaune a dinning suna dinner ne Daddy yace “wai yaron nan shi dai bazai taba shigowa nan ya ci abinci da family ba?? na rasa wannan irin hali nashi wallahi” Mummy wadda tayi murmushi tace “Ai Mustapha halin shi sai shi” Fadeela ce tace “wai ya dawo ne?” Mummy tace “ya dawo dazu bayan la’asar. Har yanzu ma ban gan shi ba, a waya dai muka yi Magana” Zehra wadda ta cika da murna kuwa babu abinda take fadi a ranta illa “can’t wait to see him” Bata ankara ba ta ji qarar shigowar saqo a wayar ta. daga wayar tayi ta duba sender. Gani nayi ta miqe a razane wanda har sai da Mummy tace “Zehra lafiya kuwa??” Murmushi tayi tace “lafiya Mummy, I need to reply this. I will be back” Daddy da Mummy kuwa suna ta yi mata dariya yayinda Fadeela ta cika da mamakin reaction din qawarta. Zehra wadda ta shiga daki fadawa tayi kan gado tace “Ya Allah, Allah yasa in ga alkhairi” Tana bude saqon kuwa ta ga rubutu kamar haka: “hey, can I see you now??” STORY CONTINUES BELOW Ji nayi ta buga uban tsalle yayinda ta koma kan gadon ta natsu tana tunanin abinda zata ce. Bata ankara ba kuwa ta ji an fizge wayar. Fadeela ce ta karanta message din yayinda na ga tayi typing wani abu ta tura ta kalli Zehra wadda take kallonta cike da mamaki tace “I sent him a reply” Zehra ta qwace wayar tace “na shiga uku, me kika ce mishi??” Mustapha wanda yake kwance a kan kujerar falon shi ne ya karanta saqon Zehra kamar haka: “Ya Musty, can’t it wait till tomorrow??” Girgiza kai yayi yace “me ke damun yarinyar nan ne??” gani nayi yayi typing message ya tura. Zehra wadda take ta yi ma Fadeela masifa akan amsar da tura mishi ne ta ji qarar shigowar wani saqon. Da sauri ta bude ta ga ya rubuta: “I will be waiting for you in the Garden” Aikuwa tana gama karantawa ta miqe da sauri tace “wallahi zan je” Fadeela ta riqo ta tace “Zee tsaya mana, ina zaki je??” tace “Ya Musty ne yake kirana kuma you won’t stop me” Fadeela ta fashe da dariya tace “lallai ma Zee, bazan hana ki ba amma ina da advice” Zehra wadda take gyara fuskar ta a gaban madubi tace “fadi in ji” Tace “please idan kika je kar ki nuna kin damu da shi, ina so ki ja mishi class ko zan samu ki rama mana wulaqancin da yake yi mana a baya” Zehra tace “hmm, in ja class ya tsinke in shiga uku?? zan dan ja dai amma just a little don wallahi bazan yi miki qarya ba ina son Ya Musty sossai ma kuwa” Fadeela wadda take ta kwasan dariya tace “the feeling is mutual Zee” Zehra dai bayan ta gama gyara fuskarta ta shige dressing room ta sanyo wata jallabiya baqa mai kyan gaske. Sossai ta fito kamar balarabiya. Bayan ta feshe kanta da turaruka ne ta kalli qawarta tace “nayi kyau??” Fadeela tace “ai ke first class babe ce qawata, Ya Musty ya san abinda ya gani” Dariya tayi sannan ta fita. ************** Zaune yake a cikin garden din wanda ya qawatu da wutace. Sanye yake cikin qananan kaya. Sossai yayi kyau. Yana riqe da wayar shi yana latsawa yayinda yake addu’a Allah ya bashi sa’a. Ni kuwa nace sa’a akan me??? Kamar daga sama ya jiyo qamshin turaren ta mai dadin gaske yayinda ya ji muryar ta wadda take kashe mishi jiki inda tace “salamu alaikum” Yace “wa’alaikis salam” ta qaraso ta zauna a gefen shi tace “Ya Musty ya hanya?? ban san ka dawo ba ai” yace “fine Alhamdulillah” daga nan kuma sai suka yi shiru. STORY CONTINUES BELOW Kusan minti biyar babu wanda yace komai. toh fa… Zehra dai sai kallon shi take yi yayinda shi kuma yake latsa wayar shi. jin shirun yayi yawa ne tace “Ya Musty you called me here..” “I love you” abinda ta ji ya fada kenan. ni kuwa nace whoa…🙄🙄🙄 Zuciyar Zehra ce ta buga yayinda ta dafe qirjinta. Dukda kuwa abinda take son ji ne daga wurin shi bata taba tunanin zai fadi hakan a nan kusa ba.. sossai tayi mamaki. Gani nayi ta dan yi pinching hannun ta don tabbatar da ba mafarki take yi ba, muryar ta na rawa tace “uhm.. you said??” Juyowa yayi ya fuskance ta tare da kallon ta cikin ido yace “I have fallen in love with you Zehra. Ban san ya aka yi haka ta faru ba, kin shiga qwalwa na kin maqale.. duk abinda nake yi tunaninki nake. You appear in my dreams and my imaginations, muryar ki kullum tana echoing a kunnuwa na. Zuciya ta gaba daya ke take so Zehra. Hey, I had to come back from Kaduna saboda bazan iya cigaba da course din ba without seeing and talking to you…” Tunda ya fara Magana shiru tayi tana sauraron shi yayinda ta cika fal da murna da farin ciki. Today is definitely one of the best days of her life. Kalaman Mustapha sun sa ta ji dama ace zaman da suka yi a yanzu a matsayin ma’aurata suke don kuwa ji take kamar ta rungume shi gam wanda kuwa bazata taba sakin shi ba. Tayi zurfi a tunani ne ta ji yace “please Zehra don’t turn me down, ban san ya rayuwata zata kasance ba idan kika ce No, you have become my everything within this short period of time..” OMG… A ranta tace “hmm, ya ma za’a yi in ce No Ya Musty when I have been craving for this??” Zehra dai bata ce mishi komai ba ta ji yace “do you need time to think??” Daga mishi kai tayi alamar eh domin kuwa gaba daya ma jikin ta ya fara yin sanyi. Yace “okay My Angel, don Allah ki bani amsa zuwa gobe, will you??” yanzu ma daga kai tayi alamar eh. Ajiyar zuciya yayi yace “toh you can go, good night and remember that Mustapha loves you very much” Da sauri ta miqe ta ruga a guje ta bar mishi wurin yayinda ya runtse idanuwan shi yace “Oh Allah, ya zanyi idan tace No???” ********** Fadeela tana kwance a kan gado tana waya da Zain ne Zehra ta shigo dakin a guje ta fada kan gadon ta fashe da kuka. A gigice ta tashi zaune tare da ce ma Zain “sweetheart let me call you back” Bayan ta kashe wayar ne ta dafa Zehra tace “Zee, meyasa kike kuka? What is wrong with you? Me Ya Musty yayi miki??” Cikin kuka tace “he loves me Dee, he loves me…” Fadeela wadda ta zama confused tace “shiyasa kike kuka?? He confessed his love for you and you are crying???” Fashewa tayi da dariya tace “OMG Ya Musty in love? Zee wallahi kinyi deserving special award” Ta dago ta tare da kallon fuskar ta wadda tayi ja tace “toh wai ban gane ba, ba dama abinda muke jira kenan ba? aren’t you supposed to be happy?? Why are you crying??” Tana kuka tace “I don’t know…” Cike da tsokana Fadeela tace “toh ko baki son shi ne?” Gani nayi Zehra ta rungume ta tace “I swear I love him, I love him very very much” Fadeela tana dariya tace “toh tsaya, me kika ce mishi da ya fadi miki yana son ki?” Tace “nothing, yace in je inyi tunani zuwa gobe in bashi amsa” Da sauri ta janyo wayar ta tace “bari ma in bashi amsa yanzu, wallahi son shi nake” Fadeela ta qwace wayar da sauri tace “no my dear, bazaki bashi amsa ba sai nan da three days” Zaro idanuwa Zehra tayi tace “what???” ♤♤♤♤♤♤♤ OMAR TAFIDA RESIDENCE Tsaye take a gefen Fadeela wadda take gyara closet dinta tana ta masifa akan ta bata wayarta tayi replying dinshi amma sam Fadeela ta qi.+ A yau dai kwana biyu kenan da Fadeela ta boye wayar Zehra don kar tayi replying Mustapha.2 Cikin masifa ne Zehra tace “wallahi Dee na tabbatar cewar baki so na, this is very serious fa. Kin kuwa san cewar if I lose him I will die?” Fadeela tana dariya tace “you won’t lose him babes” Ran ta a bace tace “idan baki bani ba zan yi fushi sossai da ke, infact I will break all ties with….” Kafin ta qarasa magana Fadeela tayi mata gwalo tace “you can’t do that Zee, you are stuck with me till forever” Qarar shigowar saqo suka ji a wayar Zehra wanda Fadeela ta boye cikin wani safe dinta. Fadeela tana murmushi yayinda take kallonta ta je wurin safe din ta danna wasu codes ta bude sannan ta duba. Ji nayi tace “this is the 69th message”2 Fashewa tayi da dariya tace “Allah sarki Ya Musty” ta kalli Zehra wadda take hararar ta tace “in karanto miki ne as usual??” Kafin Zehra tayi Magana kuwa ta fara karanto saqo kamar haka: “hey please ki bani amsa, wallahi the wait is killing me. I can’t even do anything… please i beg you don’t turn me down. I love you” Zehra wadda ta ji dadin kalaman gani nayi ta lumshe idanuwa tace “Ya Allah, wallahi har yanzu gani nake yi kamar a mafarki” ta kalli Fadeela tace “you know what?? Yadda kika ce haka zamuyi, bazan bashi reply ba sai zuwa gobe, I would love to read more of this text messages” Fadeela tana dariya tace “yauwa bestie..” Da sauri Zehra tace “on one condition amma, zaki bani waya na but I promise you bazan yi replying dinshi ba” Da farko dai Fadeela qin amincewa tayi amma kuma daga baya ta amince ta bata. ♤♤♤♤♤♤ Yinin ranakun nan biyu kuwa Mustapha ya kasa zuwa ko ina, a koda yaushe yana riqe da wayar shi yana jiran reply din ta. Ko abinci ya kasa ci saboda zullumi. Harkokin shi gaba daya babu wanda yayi. Gaba daya ya rasa me ke yi mishi dadi. Ya kira wayar ta ya fi a qirga amma bata dauka. Text messages kuwa har ya gaji da typing. Hakan kuwa ya tabbatar mishi da lallai bata son shi ne shiyasa ta qi responding. Aikuwa wannan tunanin ya sakar mishi wani azababben ciwon kai. Abu kamar wasa har ta kai shi ga kwanciya.2 Zehra kuwa duk saqonnin da yake aiko mata da missed calls dinshi duk ta gani, sossai suka dinga sanya ta cikin tsananin farin ciki. Daga kalaman da yake rubutowa a messages din shi ta tabbatar burin ta ya cika. Ta samu namijin da yake bala’in sonta. ♤♤♤♤♤♤♤♤ Washe gari da safe da qyar Mustapha ya tashi daga bacci. Gaba daya ya bi ya zama disorganized. Ya zama so weak kamar ba soja ba. soyayya ta birkita shi…🤣 STORY CONTINUES BELOW kallon agogo yayi ya ga qarfe takwas da minti goma. Miqewa yayi ya shiga bathroom dinshi yayi brush sannan ya fito. Sossai yunwa yake ji don haka ba tare da tunanin wani abu ba ya wuce cikin gidan don samun abinda zai ci. Tsaye take a cikin kicin din tana qoqarin rufe warmers, sossai qamshi yake ta tashi na kalolin girkin da tayi. Sanye take cikin dogon hijabi mai hannu har qasa domin kuwa qarqashin hijabin wata gajerar sleeveless nighty ce wadda ta tsaya iya gwiwarta. Mustapha wanda ya dade a tsaye yana ta kallonta cike da so da qauna ne ya dan yi gyaran murya wanda ya sa ta zabura ta juyo da sauri. Hada idanuwa suka yi yayinda ta ji wani irin sanyi a zuciyar ta. Gani tayi ma kamar ya dan rame sannan he is looking disorganized a wannan lokacin. Gashin kan shi wanda a koda yaushe yana cikin gyara a yau it’s looking so rough amma kuma fa dukda haka yayi masifar kyau. Gani nayi ta saki ajiyar zuciya sannan tace “uhm, uhm… Ya Musty ka bani tsoro, I mean sorry, ina kwana..” Kafin ta rufe bakinta ya fara matsowa zuwa inda take yayinda duk ta bi ta rikice ta fara matsawa baya. Bata ankara ba ta ji ta jingina da bango yayinda ta yi saurin runtse idanuwan ta. Jin shi tayi daf da ita yayinda take ta kyarma. Mustapha kuwa kyakyawar fuskar ta kawai yake kallo yayinda son ta yake qara bin kowanne gaba na jikin shi. Muryar ta qasa qasa tace “uhm, please Ya Musty ka bari in tafi” Yace “did I stop you?” Tace “Kar fa Mummy ta shigo ta gan mu” Murmushi yayi yace “me muke yi toh da baki so ta shigo?” Tace “don Allah kayi haquri..” Qara matsowa yayi daf da ita ya sa hannun shi biyu ya dafa bangon yadda bazata iya guduwa ba yace “zan bari ki tafi amma until you tell me what I want to hear” Muryar ta tana rawa tace “me kake so in fadi maka??” Yace “I love you Zehra, me kike so inyi miki da zai tabbatar miki da cewar ina son ki? You have punished me enough.. Please ki sassauta mun haka, I need an answer..” Bai qarasa magana ba ya ji tace “yes..” Yace “yes what My angel?? Please open your eyes and talk to me” Ahankali ta bude idanuwan ta wadanda suka sauka akan nashi tana murmushi tace “I love you too Ya Musty…” Daga nan kuwa ta ture hannun shi ta ruga a guje ta bar kicin din yayinda ta bar shi yana ta gode ma Allah. A kan hanya ne Zehra ta ci karo da Mummy har tana fadin “lafiya kika rugo a guje Zehra?” Murmushi tayi tace “babu komai Mummy, akwai abinda zan dauko ne” daga nan ta wuce yayinda Mummy ta nufi kicin din. Cike da mamaki Mummy take kallon shi yayinda yake tsaye a inda Zehra ta bar shi. Ji yayi tace “ah ah, Mustapha yau kuma kai ne a kicin?? are you okay??” Yana murmushi yace “Mummy yunwa nake ji shiyasa” Girgiza kai tayi tace “hala kai ka kori Zehra daga kicin din??” qarasawa yayi wurinta ya rungumeta ta baya tare da yi Mata kiss a kumatu yace “not really” Cike da mamaki tace “toh bari in zuba maka abincin naka..” Kafin ta qarasa maganar yace “kar ki damu Mummy, let me go and freshen up in dawo, yau tare da ku zanyi breakfast” STORY CONTINUES BELOW Ya fita yayinda ya bar ta cike da tsananin mamaki har tana fadin “akwai matsala”2 ************* Mummy dai sossai tayi mamakin ganin dagaske tare da su zai yi breakfast. Tana kallon shi tace “wai me ke faruwa ne yau??” murmushi yayi yace “kawai I have decided to change ne” Daddy wanda ya shigo dinning din ne ya cika da mamakin ganin shi yace “wai wa nake gani ne yau a dinning din?? ko ba Mustapha bane??” Girgiza kai Mustapha yayi yana murmushi ya tashi ya qarasa wurin Daddy suka yi musabaha yayinda yace “ka tashi lafiya Daddy??” Daddy wanda yake cike da farin ciki yace “ai kai zanyi ma wannan tambayar” Mummy wadda take dariya tace “I am so happy you decided to join us, please ka cigaba da hakan, we are your family and spending time with us will make our relationship stronger kaji Mustapha na??” Shi kam murmushi kawai yayi. Fadeela da Zehra ne suka shigo Dinning din cikin sallama. Fadeela wadda take gaba sossai tayi mamakin ganin shi a zaune, a ranta ne tace “lallai ma Ya Musty, this is all because of Zehra. This is surely a dream come true for my friend” Zehra kuwa tana dago kai ta gan shi sai gani suka yi ta juya ta ruga a guje ta bar dinning din har Mummy tana fadin “ya haka kuma Zehra ina zaki je” ba tare da ta juyo ba tace “ina zuwa Mummy” Aikuwa har suka kammala breakfast din bata dawo ba. ♤♤♤♤♤♤ A lokacin da Mustapha ya kammala shirin shi na zuwa Gym ne ya dauki wayar shi ya tura mata message kamar haka: “Hey my Angel hope dai kin yi breakfast? Get use to having me around you all the time because you are my life. Zan je Gym sai na dawo, I love you” A lokacin da ta karanta wannan message din kuwa gani nayi ta lumshe idanuwa tare da fadin “wallahi Dee yayan ki zai kashe ni da soyayyar shi, wai dama haka feeling din yake da bala’in dadi??” Fadeela tana ta yi mata dariya tace “you never see anything babes, da alama kuwa yaya na Professional ne a fannin soyayya” Gani nayi Zehra ta nufi window din dakin su da sauri ta tsaya. Hango shi tayi riqe da jakar shi yayinda ya sa a boot. Sanye yake cikin wandon sweatpant baqi da baqar T-shirt mai logo din NIKE sai wani sunshade da ya sa. Da alama kuwa ya sa ne saboda yanayi garin a yau, an tashi da rana. Gani tayi ya kira daya daga cikin ma’aikatan gidan yayi mishi Magana yayinda ya tsaya yana jiran shi ya kawo mishi abinda ya aike shi. Lumshe idanuwa tayi tace “Ya salam” 2 Fadeela wadda ta taso ta tsaya kusa da qawarta ne ta hango yayan nata tayi murmushi tace “ko in kira miki shi ne??” Da sauri tace “please no, let me watch him a haka. I enjoy watching him” Rungume Fadeela tayi tace “Babes look at him don Allah. I love his physique. kin san me? na tabbatar bazan iya rayuwa ba tare da shi ba” Fadeela wadda take dariya tace “Alhamdulillah.. I am glad you like my brother this much, Allah ya bar ku tare” ♤♤♤♤♤♤ EM-SQUARE BODY FITNESS CENTRE Yana zaune a lounge din Gym din yana waya da dan uwan shi Muhammad. Ji nayi yace “can’t wait to have you back bro, there are a lot of things we need to talk about” A dayan bangaren kuwa Muhammad yace “wallahi Musty nima na gaji da garin nan. ban taba sanin cewar zan dade haka ba. kasan turawan nan da zarar sun gan ka da talent shikenan” Mustapha yana dariya yace “I am happy kana representing qasar mu well, plus dadewar tayi amfani ai tunda ka zama billionaire” Muhammad ya fashe da dariya yayinda yace “I can give up all the billions for you guys, My family comes first Musty” Mustapha yace “thanks bro, Allah ya dawo mana da kai lafiya” yace “ameen” Bayan sunyi sallama ne kiran ta ya shigo wayar shi. murmushi yayi sannan ya amsa. Kafin yayi Magana kuwa ya ji muryar ta cikin masifa tace “da wa kake ta waya tun dazu?? Your girlfriend ko??” Murmushi yayi tare da jin dadin yadda take nuna kishi akan shi. Jin yayi shiru ne yasa tace “like seriously?? Dama can…” Ji tayi yace “I swear ke ce first, only and last girI Insha Allah my angel” Murmushi tayi tace “are you sure??” Yana murmushi yace “trust me, A yadda nake jin ki a raina babu wadda zata iya maye gurbin ki” A ranta ne tace “Oh Allah, I am so happy” Cike da jin dadi tace “toh da wa kake hira ne tun dazu ake ce mun layin ka is busy?” Yace “My brother Muhammad, kin san shi?” Tace “uhm, mun dai gaisa a waya once. Dee tace he is your favourite person a gidan nan” Lumshe idanuwa yayi yace “sossai ma kuwa, Moha is a definition of greatness. Tun muna yara yake sacrificing komai nashi just to make me happy.. Ina bala’in son shi, and I Pray Allah gives me something I can repay him with for everything he has done for me.. For him I can sacrifice my everything..” Ji yayi tace “hmmm… I am jealous” can kuma tace “wait what?? everything?? Harda ni??” Fashewa yayi da dariya yace “wannan kam bazai faru ba insha Allah” 🤨🤨🤨🤨 Dariya tayi itama tace “I love you Ya Musty” bata rai yayi yace “Angel a canza mun suna don Allah, ni kam ba yayan ki bane” Tana dariya tace “toh zan canza maka” Yace “better, ina kika shiga ne ina ta kiran ki??” Tace “I was in the kitchen ne, yanzu ne da na shigo daki shine na ga missed calls dinka” Girgiza kai yayi yace “hope kin dafa mana special delicacy??” Cikin shagwaba tace “hmm.. kamar dagaske. na kula fa baka wani cin abincin kirki… and you are an Army officer??? kwanan nan zan fara dura maka abinci ai” Dariya yayi yace “yi haquri Angel, for you I am ready to change. Duk abinda kike so inyi shi zanyi” Lumshe idanuwa tayi a ranta tace “Oh Allah..” A fili kuma tace “thank you so much” Ji tayi yace “hey bari in tattara in dawo gida, I am done for today. Hope I will get to see you??” Tace “insha Allah, Allah ya dawo mun da kai lafiya” yace “Ameen my Angel” ♤♤♤♤♤♤♤♤ ABU-YAZEED RESIDENCE+ Zaune yake a cikin motar shi a tsakar gidan yayinda yake Magana da ita a waya. Ji nayi yace “My Angel ya isa haka nan mana, I have spent almost thirty minutes waiting for you fa. Kin dai san ko ya kika fito you will always remain the most beautiful ko??” A dayan bangaren kuwa Zehra tana zaune a gaban vanity table din dakin ta inda take ta tsantsara kwalliya tace “Baby yau ne fa first outing dinmu, I need to look my best so be patient, nan da fifteen minutes zan fito” Yace “what??” Tana dariya tace “sorry my Baby, just keep thinking about me and before you know it minti sha biyar will feel like minti biyu” Murmushi yayi yace “toh ya zanyi da ke tunda dai zuciya ta nace sai ke ai dole inyi haquri..” Sossai kalaman Mustapha suke rikita Zehra. Cike da farin ciki tace “I swear I love you” Yana murmushi yace “toh hurry up” ********** Yana nan zaune ne ya hangota ta fito. Sanye take cikin wata doguwar riga ta atamfar Super wax riqe da hand bag dinta na Gucci. Qafafuwan ta sanye cikin flat shoe na Vincci yayinda ta yafa wani qaramin gyale baqi. Sossai tayi kyau. Mustapha dai tunda ya sa mata idanuwa ya kasa daukewa. Ji nayi yace “Ya salaam, she will be the death of me, I swear I cannot imagine life without her..” yayinda hankalin shi yayi nisa. Bai ankara ba ya ji tayi snapping fingers dinta a saitin fuskar shi. Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya saki tare da kallon ta. Fashewa tayi da dariya tace “Baby me kake tunani haka da har na shigo baka sani ba?” Hararar ta yayi yace “me kika ce inyi??” Tana dariya tace “toh ai I never asked you to get lost while thinking about me” Tada mota yayi yace “I can’t help it, you are looking extremely beautiful” Tana kallon shi tace “and you look handsome. Ka san cewa I always see you in white?? you look different today” A yau kuwa Mustapha navy blue kaftan ya sa na wani tsadadden yadi, hular kanshi kuwa kamar don yadin kawai aka yi ta. Sossai yayi kyau. Murmushi yayi yace “thank you My Angel” A lokacin da suka bar gidan ne yace “ina zamu je??” STORY CONTINUES BELOW Tace “mu je Millenium park” yana kallon titi yace “hope dai babu crowd, kin san fa bana son yawan mutane” Tace “zaka so wurin My Baby, it’s the reason why I chose the location” yace “okay, give me directions” MILLENIUM PARK MAITAMA ABUJA Ko da suka iso park din wani wurin hutawa suka haura sama yayinda suka samu wani Romantic spot for two suka zauna. Zehra wadda take kallon shi ce ta miqe tace “Baby let me get us something to drink” Yana murmushi yace “I thought its my duty to do that” dariya tayi tace “Nayi relieving dinka yau, kar ka damu” Yace “alright my Angel, your wish is my command, I will be waiting for you” Yana kallonta ta sauka daga wurin. Tashi yayi ya nufi wurin balcony na wurin ya tsaya yana hangen ta har ta isa wurin. dayake akwai mutane dole ta bi layi tana jiran turn dinta. Kamar ance mata ta daga kai ta hango shi a saman yana ta kallon ta. A hankali tace “na shiga uku, idan na rasa ka ya zanyi da rayuwa ta??” 14 Bata ankara ba ta ji wani mutum yace “madam, na ga kamar tunanin ki yayi nisa” murmushi tayi tace “uhm, sorry” yace “you are next” tace “thank you” A wannan lokacin kuwa Mustapha wanda yake sama ganin tana Magana da mutumin tana murmushi ne na ga ya bata rai yayinda ya koma kujerar shi ya zauna. Dafe kai yayi yace “what the hell were they talking about?? Meyasa take yi mishi dariya?? toh wai ni ya zanyi da irin wannan??” Sossai zuciyar shi take tafasa. A rayuwar shi yana da bala’in kishi akan abinda yake so. Ya shiga tsananin damuwa yayinda yayi zurfi a tunani. Wata zuciya ce take fadin “Control Mustapha, wannan ba wani abu bane. Babu wanda zai qwace maka ita” Ji yayi an dan taba hannun shi wanda ya sa shi saurin dago kai ya ganta tsaye daf da shi yayinda fuskar ta tayi displaying tsananin damuwa. Ji yayi tace “Baby yawan tunani is not good for your health fa” yana kallonta yace “duk laifin ki ne, I was not like this before” Murmushi tayi tace “hey, Insha Allah ni taka ce har abada so just relax ka ji Baby na??” Murmushi yayi yace “thanks My Angel” Haka suka fara shan smoothie din da ta kawo musu yayinda suke ta hira. STORY CONTINUES BELOW Zehra ce tace “Baby in tambaye ka??” yace “go ahead” Tace “you promise to give me answers to all my questions??” Murmushi yayi yace “I promise” Tace “kasan dai I don’t know much about you, I kinda wanna know even if it’s a little” tayi sipping dn smoothie dinta sannan tace “wane rank kake presently?” yace “Major” Tace “wow, that’s great. Toh how old are you??” yace “thirty, ko nayi miki tsufa ne?? maybe you prefer a younger guy??” Fashewa tayi da dariya tace “Baby ko shekarun ka dubu I still love you” Girgiza kai kawai yayi yana murmushi. Ji yayi tace “bazan tambaye ka ko ka taba harbe enemies ba because I know you have. My question is how many have you killed??” Fashewa yayi da dariya yace “Trust me My Angel, you don’t wanna know that” Tana dariya tace “are you scared idan ka fadi mun zan gudu??” Yana dariya yace “ai baki isa ba kuwa, you are stuck with me till forever” Tana dariya tace “toh tell me” yace “I will tell you some other time, let’s skip this for now” Tace “alright then, since your wife to be is a Chef let her know the kinda food you like so she can meet your taste” Dariya yayi sannan yace “well honestly I love sea foods, home-made drinks, Coffee, fruits, Chocolate….” Zaro idanuwa tayi tace “hey I am talking about normal food….” Yace “well I eat just little of normal food gaskiya, banda choice when it comes to that” Girgiza kai tayi tace “hmm, ai shiyasa nace sai na fara dura maka abinci” Dariya yayi yace “Idan dai ke zaki dinga bani da hannun ki wallahi na amince” sossai ya bata dariya. Ji yayi tace “akwai abinda zaka tambaye ni??” Yana murmushi yace “Nope” cikin shagwaba tace “haba Baby why now?? Kenan you are not interested in knowing about me??” Miqewa yayi ya dawo gefen ta ya zauna yace “I know everything about you my Angel, trust me” Murmushi tayi tace “dagsake??” yace “yes, tashi mu je mu dan zagaya” Da sauri ta miqe tana fadin “yauwa mu je Love Garden din su, its nice” Tsare ta yayi da ido yace “how do you know that?? Tare da saurayin ki kike zuwa kenan?? Wait I think I have a question for you” Ya koma ya zauna tare da fadin “come and sit” Zehra tana murmushi ta zauna tace “I am listening” Yana kallonta yace “ki fadi mun gaskiya samarin ki nawa??” Fashewa tayi da dariya tace “funny question” Fuskar shi a daure yace “its not, just answer me” Shiru tayi tana kallon shi yayinda wata zuciya tace “play a prank on him ki ga reaction dinshi..” Bata qarasa tunaninta bane ta ji ya kamo hannun ta daya ya riqe tare da fadin “My Angel, I need to tell you this. Ina da masifar kishi akan abinda nake so. Gaba daya zuciya ta tana hannun ki, idan ina da hali bazan taba bari ki qara yin Magana da wani namiji wanda ba ni ba ma..” Yayi murmushi yace “but its not possible right?” Ya cigaba da fadin “Your love is all over my soul, I can do anything for you My Angel, I can even die for..” Da sauri ta qara matse hannun shi a nata tace “hey relax, I swear kai ne first boyfriend dina. Ina bala’in sonka kuma I won’t love any other person after you..” Ajiyar zuciya ya saki tare da fadin “thank you My Angel, I will forever love you” tana murmushi tace “Me too” Daga nan suka tashi suka nufi Love Garden din cike da so da qauna. A Garden din kuwa sossai suka yi yawo yayinda Mustapha yake ta faman daukan ta hotuna. 5 Sossai soyayyar Zehra take bin Jini da Jijiyar shi.2 Burin shi kawai bai wuce ya mallake ta a matsayin mata ba wadda zata kasance uwar ‘ya’yan shi. ABU-YAZEED RESIDENCE Kusan minti talatin kenan da Mustapha ya dawo da Zehra gida amma kuma ya kasa tafiya. Ita kanta bata so ya tafi a dalilin zai yi tafiya gobe. Tana kallon shi tace “Baby yanzu sai yaushe zaka dawo? I swear I am going to miss you” turo baki tayi tace “ni wallahi bana ma son irin aikin nan naka, kawai kayi retire ka dawo…” Kafin ta qarasa magana kuwa ya fashe da dariya yayinda yace “Retire fa kika ce” Cikin shagwaba tace “eh mana, that way we will always be together” Ajiyar zuciya yayi yayinda yake fadi a ranshi “this is just a one week trip, what will happen idan tafiyata zuwa Italy ta taso??” 🤨🤨🤨🤨 Ji yayi tana fadin “are you considering my suggestion??” Yana dariya yace “hell no, I love my Job a lot but don’t worry it won’t stop us from having the beautiful thing we have together” Murmushi tayi tace “I will forever be proud of you My handsome Major, may no one cast an evil eye on you” Yana murmushi yace “Ameen Angel dina” Haka dai suka cigaba da hira har sai da suka ji kiran sallan Magrib wanda kuwa suka yi sallama da juna. Bata bari ya tafi ba sai da yayi mata alqawarin kafin ya tafi washe gari zai zo ya ganta suyi sallama. ♤♤♤♤♤♤

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *