ZUBAIDAH COMPLETE BY Sameena Aleeyou.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Garin Dukku jihar Gombe, gari ne wanda akasarin mutanen dake zaune wajen fulbe ne, ma’ana fulani ne. Ni Sameena tafe nake cikin garin ina bin tsarin garin da kallo yayinda zuciyata ta cika da nishad’i. Can na hangi wata matashiyar budurwa wacce ak’alla bazata gaza shekaru goma sha shida 16 a duniya ba. Daga yanayin halittarta zaka fahimci cewa bafulatana ce ta usul. Bata da matsanancin tsayi snn bata a layin gajeru, farinta irin mai d’auke idon nan ne don saida ta matso kusa sosai na fahimci hakan. Yanayin suturan dake jikinta zai tabbatar maka iyayenta talakawa ne sosai. Silipas din dake k’afufunta kuwa duk ya b’ule yaji jiki.
“Sauri take tamkar mai shirin tashi sama, yanayin tsoro da firgici da ya wanzu a fuskarta zai tabbatar maka cikin matsanancin tashin hankali take. Kaman ta zunduma a guje haka take tafiyar, Yar da d’an karan dake hannunta tayi ta soma sassarfa hadi da gudu gudu sakamakon jiyo muryar dake sata firgici koda a mafarkinta ne tana k’walla mata kira har waje ake jiyowa,. *ZUBAIDAH! ZUBAIDAH, ZUBAIDAH!!!
“Ni kuwa Queen Samy nace ” Bari na bi wann yarinya na rubuto wa d’inbin masoyana labarinta mai cikeda tausayi, Al’ajabi da kuma ban mamaki had’i da darrusa masu girgiza zukata.
“Dan ubanki sai yanzu kika daman dawowa daga karuwancin naki? Macen dake tsaye tsakar gidan rik ‘e da guga ta fad ‘ tana watsa wa Zubaida mugun kallo me nuni da cewa zaki yaba wa aya zak’inta.
“Bakinta na rawa take fad ‘in Yaya Hadiza wllhi ban sami Yayan a kasuwa bane shine na k’arasa bakin tasha….. Ai bata gama cewa tasaha ba Yaya Hadiza ta jefa mata gugan dake hannunta ji kake tum ya fad ‘I a tsakar kanta.
“Durk’usawa Zubaidah tayi tana rik’e da tsakar kanta hawaye na zuba bisa k’uncinta.
Hadiza ta k’araso gamida mak’urota tana fad’in” Dan ubanki ni na aikeki bakin tasha, wani munafurcin ne ya kaiki bakin tasha, auho kice mun karuwanci kika tafi, shegiya Me suffan mayu da aljanai. Rankwashin da ta sake mata a tsakar ka yasa Zubaidah sakin k’ara sabida azaban dataji.
“Hadiza ta shiga janta a k’asa tana fad’in” Au kuka ma zakiyi shegiya munafuka saikace wacce na bugeki toh bari kiga na tapkeki sosai sai kiyi mai dalili.
“Duk kukan da Zubaidah take tana rok ‘on Hadiza tayi hak ‘uri ko gizau bata fasa jibgangta ba kaman Allah ne ya aikota.
“Inna Furera mak’ociyarsu ce ta shigo a guje don ceton Zubaidah dama mak’ota sun saba shigowa kawo mata d’auki, tunda Hadiza ta tsefe ido taci mutuncinsu tsaf suka daina, saiko Inna Furera ce kawai bata fasa ba.
“Da sauri tayi tsalle ta kwace Itacen da Hadiza ke jibgan Zubaidah dashi, dama Jadiza irin ingarman matan nanne.
“Ta shige tsakani tana fad’in” Haba, haba Hadiza, anya kina kuwa tuna mutuwa, kullum sai ki kama wann ‘yar marainiya kita jibga ke ko tsoron kamuwar Allah bakya yi. Cewar Inna Furera .
“Galala take Kallon Inna Fure kafin ta gyara tsayuwa ta soma fad’in” Fure! Fure!! Fure!!? Billahilazim hawainiyarki ta kiyayi ramata, banda munafunci irin taki ina ruwanki da ita, ci kike bata ko sha, cikin biyu babu d’aya. Toh wllhi wllhi ki fice a idanu na.
“Inna Fure tai murmushin takaici kafin tace ” Lokaci ne, da zaran lokacin da Zubaidah zata sami kulawata yazo zata samu kuma ke baki isa kiyi komai ba.
“Shewa Hadiza ta kwashe dashi kafin tace ” Ai dama nasan wajen munafukin wann d’an naki me matse yaran mutane a lungu take zuwa, bacin haka babu abinda zai kaita bakin tasha, Toh wllhi idan ni Hadiza ina numfashi Zubaidah bazata auri Ummaru dreban tanka ba. Ke na tak’sita maki zance Zubaidaha bazata tan’s aure a rayuwarta ba, makarantar data samu na bari tayi ya isheta, amma aure kam saidai tayitaji k’annen bayanta suna tafiya d’akin miji amma banda ita, tunda dama sa ‘anninta Sun k’are k’annenma sun kusa k’arewa. Ta juyo ta narkawa Zubaidah da har lokacin kukan zuci take hawaye na bin k’umcinta tace ” Ke kuma bak’ar munafuka ki tashi ki min wanke wanke kafin ki d’aura sanwa don yau islamiyar ma ba zuwanta zakiyi ba. Daga haka ta wuce d’aki fuuu kamar me shirin tashi sama.
“Inna Fure ta girgiza kai ta k’arasa ga Zibaidah wacce ke faman mik’ewa da k’yar sabida raunin da Hadiza taji mata da itace, tsugunawa Inna Fure tayi tausayin yarinyar ya cika zuciyarta, a hankali tasa hannu ta goge k’wallan da ya zubo mata. Hannu tasa ta shiga sunce d’aurin da Hadiza tai ma Zubaidah da igiyan guga.
“Suna had’a ido Zubaida taji wani sabon kuka na shirin kufce mata, ……..