ZUCIYA CHAPTER 5
Nafi tanannan zaund har Little ta fito ta kalli Nafi cikin takaici ganin tana murmushi ita kad’ai tace ” Nafi bakiji haushin abinda su Umma sukai ba? “+ Cikin rashin kulawa da abin tace ” name fa? ” Little ta zauna a gaban madubi tace ” kina gani sunzo sun dauki lace mai tsada da sunan wai aike akai? ” Nafi ta kalleta tace ” lalai Maryam meye abin jin haushi? Kika sani ko da gaske suke? Sannan ko d’auka ma sukai ai sun isa ne naga ita zai aura? ” Little tai d’an karamin tsaki tace “Wlh ba wani kayansu, sannan dan ita zai aura sai akace tazo ta d’au abinda ba nata ba? ” Nafi ta mike tace ” kafin ki shirya bari na anso miki abinci. ” Bata jira amsarta ba tai waje da sauri, Little ta bita da kallo a fili tace ” lalai wato dan indaina maganar shine zaki gudu? ” Nafi kam tana fita tai murmushi tace ” ni da naga kaya daga sama? Dan an d’au d’aya menene? ” Kitchen ta wuce, ta amso abincinsu kenan zata shiga bangarensu taji ance “Ke!” Juyawa tai dan tasan Umma ce, Umma tace ” zo nan. ” Ajiye tiren tai sannan ta karasa gunta, Aneesa ta maka mata hararra tare da juya kai gefe. Nafi ta karasa tare da rusunawa tace “gani. ” Umma ta mata wani kallo tace ” munafuka kinje gun aikin ko kuwa? ” Da sauri Nafi tace “Naje wlh. ” Duk da dama Umman ta riga ta tambaya ankuma shaida mata taje amma sai cewa tai “in kika min karya na tambaya wlh kinji na fad’a miki jikinki sai ya fad’a miki. ” Nafi tai kasa dakai ba tare da ta sake magana ba, Umma ta kara kallanta sannan ta ce ” me Little tace bayan mun fita? ” dama wannan shine dalilin kiran wancan burga ne so take taji me akace bayan sun fita. Nafi da mamaki ta kalleta tace ” Bangane ba. ” Da kuwa Umma ta mata ta kara da kinci gidanku, ni zaki kalla kicewa baki gane ba? Nafi tai kasa da kanta a hankali tace “kiyi hakuri. ” Cikin takaici Aneesa tace “Dalla malama kara gaba. ” Nafi wacce bata fahimci me ake nufi da kara gaba ba tace “Naam? ” Cikin kuluwa Umma takaimata wani wawan mari wanda sai da Nafi tai baya tare da rike kuncinta. Umma ta nunata da yatsa tace ” kin bar nan ko sai na karya ki? Shigeya wacce asalinta bashida tabbas. ” Nafi ta juya ta fara tafiya sai dai tana tafe hawaye nabin kuncinta, haka ta d’au tiren tare da goge hawayenta ta shiga. Little har tana shirin fita sai ga Nafi ta kalleta tace ” lalai Nafi sannu da zaman hira. ” Nafi tai murmushi kawai batace komai ba sai hanyar toilet data nufa. Tana shiga ta tsugunna sai kuka, itakam Little abincinta taci ganin Nafi bata fito ba yasa taje bakin kofar toilet d’in tace ” Nafi na tafi. ” Da kyar ta daure tace “To. ” Sai dataji alamun fitarta sannan ta dawo ciki, ta dade kafin hawayen su tsagaita taci abinci sannan ta fara gyara d’akin. _A Company_ Kawu zaune a kan kujerar dake tsakiyar dogon tabirin, gefe da gefe mutane ne kowa zaune akan kujerar sa, Wanda ke daga b’angaren hagu na kusa da kawu ya kalleshi yace ” A gaskiya Chairman mun gaji da abinda Chief Director(Asim) yake mana, a duk sanda muka bukaci sa hannunsa akan wani aiki ko meeting a b’angaren mu ya dinga mana wala wala kenan, sam baya yin aikinsa na Chief Director.” STORY CONTINUES BELOW Kawu ya kalli Asim wanda yaketa juyi a kujera cikin rashin damuwar abinda ake kararsa dashi, ran kawu ya kai koluluwar b’aci ya kallu wanda yai maganar yace ” kar ka damu Director idan har Asim bai canza halayensa ba nan da one month ni a matsayina na shugaban wannan company d’in zan saukeshi daga matsayinsa. ” A zabure Asim ya kalli mahaifinsa wanda yana gama magana ya mike yai waje, Asim cikin tsagali da raini ya kalli mutanen gun yace ” ni kuka had’a da mahaifina? Lalai ran kowa in yayi dubu sai ya b’aci. ” shima yabi bayan mahaifinsa. Office d’in kawu ya shiga, yana shiga yaganshi a tsaye kusa dashi ya karasa yace “Abba…. ” Littafin dake hannun kawu ya makamai iya karfinsa, Asim ya fad’a kan kujera cikin tsoro yace ” Yahkuri Abba amma sharri suke…… ” Yatsa kawu ya nunamai idanunsa sunyi jaa yace “kai dakikin ina ne? Meyasa sam kwakwalwarka bata aiki? ” Yai wani hucci sannan ya cigaba “Company d’in nan na Waye? Kana tunanin dan na rike shi na shekara ashirin yana nufin ya zama nawa? ” Kai ya jijiga sannan ya cigaba ” A’a, da zarar Ashraf yaso zai zo ya amshi matsayinsa ne babu kuma yanda zamuyi. ” Asim cikin b’acin rai yace ” ta ina zamu barshi? ” Tsaki kawu yai yace ” 50% d’in yaya(mahaifin Ashraf) gaba d’aya a gunsa yake, kai kasan duk karshen wata kud’in dake shiga account d’insa ya ninka nawa mai 20%?” Asim wanda ya fara huccin takaici ya kalli Mahaifinsa, kawu yacigaba “In baka rike matsayin ka ba ka nuna ma mutane zaka iya kana tunanin Ashraf mai taurin kai zai bakka ka cigaba da abinda kaga dama in har ya fara aiki anan? ” Asim ya mike cikin takaici yace ” shiyasa duk duniya ba wanda na tsana irin yaron nan, mahaifinsa kaf arzikinshi sunan sa yasa, kai daka wahala gurin taimakama uban sanda yana da rai bai ma kara ya barma ko da wannan companyn ba. ” Kawu ya zauna kan kujera cikin b’acin rai shima ya kalli Asim yace ” Ka kula sannan ka dinga kokarin b’oye tsanar da kakema Ashraf dan naga kamar kanka na rawa baka kunyar nuna mai. ” Shiru Asim yai baice komai ba……. _A Gida_ Nafi bayan ta gama komai tai wanka dama Little ta fito mata da kaya hakan yasa ta saka ta fito domin zuwa kitchen yin aiki. Ta d’anyi tafiya kad’an taji ance “Ina Zaki? ” Tsayawa tai cak ta kasa juyowa, shima bai sake magana ba hakan yasa ta daure ta juya a hankali, daga gefe ta ganshi zaune akan d’aya daga cikin kujerun gun, gani tai ba kallanta yake ba hakan yasa tad’an kuramai ido, duk da bai kalleta ba jitai yace ” Kallan fa? ” Da sauri ta d’auke idanta tace ” na fito ne kawai” Ya kalleta sannan ya mata alama da hannu akan tazo, a hankali ta karasa inda yake, ya kalleta yace ” So nake kimin wani abu. ” Cikin mamaki ta kalleshi tace ” Me kakeso yaya? ” Ya bud’e baki zai magana sai ga Aneesa ta karaso cikin salon tafiya da yanga, tana zuwa ta shagwab’e murya tace ” Cwt Yaya kaifa nake nema. ” Ashraf ya kalli Nafi sannan ya kalleta yace ” Anie ya akai?” Baki ta turo tace “ni dai banasan Anie kacemin Neesah na. ” Kunne yad’an sosa sannan ya kalli Nafi wanda da alama zaman gun ya isheta yace ” Nafeesa jeki kawai. ” Wani kasalalen kallo tamai wanda ita kanta batasan ta iya ba, so take ta tambayeshi me yakeso tamai? Ga Aneesa agun ita kuma duk ta rasa mai zatace, Aneesa ta maka mata harara sannan tace ” Nafi yace kije zamuyi magana ne. ” Kamar tai kuka haka ta juya ta fara tafiya, me yake so? Abinda ke mata yawo kenan. Itakam Aneesa zama tai ta shiga mai salo, wani abun ya biyeta wani kuwa ya juya kai kawai. Nafi kam duk aiki take amma hankalinta nakan Ashraf har suka kammala girki, nan Goggo tace “A d’au na Ashraf akai mai. ” Da sauri Nafi ta amshi tiren tace “bari na kaimai. ” Goggo ta kalleta tace ” kinsan b’angarensa ne? ” Haka kawai tasamu kanta da yin karya tace na sani. Nan Goggo ta bata. Fitowa tai tana ta kalle kalle, nan Allah ya had’ata da Amrah murmushi tai ta karasa gunta tace “Amra inane b’angaren Yaya? ” Nan Amrah ta nuna mata, karasawa tai tana tafe tana tunani da fatan Allah yasa yana nan. Knocking tai a hankali, Ashraf dake kwance akan doguwar kujera yana kallo a falo yace “in abinci ne ajiye zan d’auka.” Nafi ta kalli kofar kamar tai kuka har ta ajiye zata tafi sai kuma ta koma gefe ta zauna a kasa. Shikam ya dade kafin ya taso ya bud’e kofar, mutum ya gane a zaune ya jingina da bango cikin mamaki yace “lafiya? ” Da sauri Nafi ta mike ta kalleshi, kallan mamaki ya mata yace ” kece? ” Kai ta d’aga kawai, yace ” D’auko abincin ki shigo. ” D’auka tai sannan tabi bayansa, tana shiga ta tsaya a bakin kofar, ya karasa kan kujera yace ” turamin kofar. ” Rufe kofar tai sannan ta kalleshi, da hannu ya mata alama akan ta ajiye abincin a dinning, nan ta kai sannan ta kara tsayawa tana wasa da hannunta, ya kwanta ba tare da yace mata komai ba, itama shiru tai dan batasan me zatace ba. Shikam kwanciyarsa yai yana jiran tai magana, sun dade sosai a haka shikam bacci ne yai gaba dashi. Nafi tana nan a tsaye jitai kafarta ta fara amsawa, a hankali ta d’an matso kad’an cikin in ina tace “dama d’azu ne…. ” Sai kuma tai shiru, Jin shima baice komai ba yasa ta kara daurewa tace “naji kace zan ma abu? ” Nan ma shiru, lekashi tai kad’an, gani tai bacci yake, a hankali ta matso inda yake ta kuramai ido, a ranta tace “na sashi yai bacci baici abinci ba. ” Kallansa ta karayi, itadai haka kawai tun sanda ta ganshi takesan taga tana kallanshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba ta juya tai waje. Sai yamma Little ta dawo, abinci kawai taci suka shiga bubud’a kaya nan Little ta ware mayafai da jaka suka had’a kayan da za’a kai d’inki.+ Nafi sai murna take a ranta zataga cikin gari. Driver d’in mumy ne ya d’aukesu, a hanya Nafi sai kalle kalle take can ta tuno tahowarsu a mota itada Ashraf murmushi ta saki wanda Little ta kula dashi. Little ta d’an harareta tace “Nafi na kula yau dai a farin ciki kikeyi.” Murmushi ta sake sannan ta kalli Little tace “Little dan Allah tambaya. ” Inaji kawai little tace sai dai ta maida hankalinta kan Nafi, Nafi tai kasa dakai cikin alamun kunya tace ” in mutum yace yanaso kamai wani abu, me zai kasance? ” Dariya sosai Little tai ta dade kafin ta tsagaita tace “Hala Ya Ashraf ne ya fad’a? ” Nafi ta d’an turo baki kadan tace “shine to menene kike dariya ?” Little tai d’an karamin tsaki tace “in kikaji yaya ya fad’i haka wallahi aiki yakesan saki. ” Nafi ta kalleta tace “aiki shine yanasan inmai wani abu? ” Little ta girgiza kai tace “Tab bakisan mutumin nan ba, amma duk da haka nayi mamaki dan ni kad’ai yake sawa aiki ni kuma ba abinda na tsana a rayuwa irin inji yaya yace zan mai wani abu. ” Nafi ta d’an jujuya kai sannan tace ” Meye abin tsana? Nikam dadi zanji inya sani aiki ma. ” Little ta mata wani kallo na yarinya da sauranki tace “Nafi bakisan waye Ya Ashraf ba, duk aikin da zakimai bazai tab’a burgeshi ba sannan bazai tab’a cemiki ko sannu ba. ” Nafi ta d’an tabe baki tace ” to mezai sa sai yayi miki sannu bayan ke kanwarsa ce? ” Kallan mamaki Little take ma Nafi itakam Nafi ina ta sani cigaba tai da cewa ” Sanna? N da alama ba a mai aikin yanda yake so ne. ” Duka little ta kai mata,Nafi tai saurin sa hannu agun, Little ta rike hab’a tace “Lalai ashe kina magana haka? ” Nafi tai murmushi batace komai ba, Little ta kalleta tace “Naji ni kanwarsa ce sannan naji d’in bana mai yanda yakeso, ke tunda kinanan sai ki mai yanda yakeso ki kuka tabbatar yacemiki sannu. ” Nafi murmushi kawai tai batace komai ba, Little tace “Kinga da Ya Habib ne? Wayyo Allah na. ” Da mamaki Nafi ta kalleta tace “Ya Habib? ” Little ta saki wani fara’a yacigaba “D’an yayan mumy ne yanazuwa gida sosai ya dad’e yanzu ma na tabbata kila karshen satin nan ki ganshi. ” Nafi ta maida kanta titi kawai, Hannu little tasa ta juyo da ita tace ” Nafi kinsan me? ” Kai Nafi ta girgiza alamar a’a, Little ta cigaba cikin zakuwa “Ya Habib ko Opposite d’in Ya Ashraf ne. ” Nafi da mamaki tace “Oppo? ” Little ta dafa goshi tace ” Kinsan me? Kinga Ya Ashraf bai da san magana shi kuma ya Habib akwai surutu, sannan Ya Ashraf akwai zafin rai shikuma Ya Habib Saukin kai gareshi. ” Nafi ta d’an bata fuska tace “Zafin rai? ” Little tace ” naji ba zafin rai ba, sannan kinga Ya Habib akwai san wasa da mutane, ga mutunci. ” Nafi wanda ta rasa dalilin jin haushi Little datai tace “Little da wa kuka fi kusa? ” Cikin rashin kulawa tace “Ya Ashraf. ” STORY CONTINUES BELOW Nafi tai shiru batace komai ba jitai Little tace “Amma Ya Habib zan aura. ” Juyowa tai cikin tsananin mamaki ta kalleta, Little ta harari Nafi ta juya. Nafi kam ta kasa magana sai shiru tai. Tanaji Little ta d’aga waya suna hira da wata kawarta akan Lesson d’in da suke zuwa, saboda shirye shiryen Exam d’in Qualifying da zasuyi, ga makarantarsu anyi hutu kuma suna komawa za’a fara jarabawa. Nafi kam sai kallan sha’awa take mata, har suka isa gun d’inkin. An gwadata sannan suka bada kayan akai sai nan da sati d’aya za’a amshi wasu daga baya sai a zo a amshi sauran. _A gida_ Ashraf ya dad’e yana bacci kafin ya tashi, wanka yai sannan ya ci abinci, ya gama kenan Amra ta shigo tace Mumy na nemansa hakan yasa ya mike yai waje. Yana ganinsu Asim da kannensa a zaune d’auke kai yai kamar bai gansu ba yai gaba, yana wucewa kuwa sukaja tsakin takaici. Sun gaisa da Mumy sannan ya gaida Kawu, shiru ne ya biyo baya kafin kawu yace ” Ashraf dama maganar auranka ne da Aneesa. ” Kallan Kawu yai sai dai baice komai ba, Kawu ya cigaba “saura wata biyu a d’aura auren shine nakesan jin ra’ayinka akan abubuwa guda biyu.” Ganin Ashraf bai da niyyar magana yasa yace ” Da farko inda zaku zauna, anan kake so ko kuwa a d’aya daga cikin gidajen mahaifinka zaka duba d’aya? ” Ashraf kam tambayar ta d’an b’atamai rai sai dai bai nuna ba kawai cewa yai “A tsarin mahaifina yafisan inzauna anan cikin ‘yan uwana. ” kawu yai murmushi yace ” yauwa haka ake so dams banasan tauyema hakki ne, tambaya ta biyu maganar aiki fa? ” Ashraf ya kalli Kawu ga mamakinsu murmushi sukaga ya saki, Mumy ta daure tace “Ashraf me kenan? ” Kallan Kawu yai yace “Kawu so kake in fara aiki? ” Gabab Kawu yad’an fad’i badai yaron nan yasan basaso ya fara aiki ba? Mumy ce tace “wani irin zance kakeyi haka? ” Bai amsa mata ba sai maganar sa ta d’azu daya maimai ta “Kawu so kake na fara aiki? ” kawu ya saki murmushi yace “in banda abinka Ashraf tun yaushe nake cema ka fara aiki? Ga mahaifiyar ka nan duk ta damu akan rashin aikin ka.” Bai kara magana ba kawai kansa ya maida gefe, Mumy kam abin nan na damunta ganin zata sake magana yasa Ashraf yai saurin cewa “Kawu zan shiga ciki akwai abinda zanyi. ” Kawu ya kalleshi sannan ya kalli Mumy wanda jikinta yai sanyi, bai jira amsarsu ba yai waje, Umma dake tsaye a kofa tanajin me ake cewa sam batasan Ashraf zai fito ba tana ganinshi ta shiga borin kunya, ko kallan ta baiyi ba yai gaba, duk ransa na dadi. D’akinsa ya wuce ya d’au waya ya kira Little, nan ta sanar dashi sun dawo gasunan shigowa, yace “kuzo keda Nafeesa. “abinda ya fada kenan ya kashe wayar. Little ta girgiza kai tare da kwaikwayan abinda yace, Nafi tace “to me kikeso yace? ” Little tace “Inkun iso to kuzo ke da Nafisa ina nemanku. ” Nafi ta juya kai tace “meye marabar hakan da yanda ya fada? ” Little ta harareta tace “Lalai nafi na kula bakyasan indinga kushe yayan nan nawa.” Nafi ta kalleta kawai batace komai ba, Little tai murmushi tace “ko da yake dole ne ganin yanda ya taimakeki. ” Sun isa ko bangarensu basuje ba suka wuce bangaren Yaya, a zaune sukaga su Ya Asim hakan yasa suka rusuna suka gaidasu, harsun yi gaba Asim yace “Ke yar kauye? ” Nafi ta juyo cikin tsoro alama ya mata da hannu kan ta matso, a tsorace ta matsa inda suke. Asim cikin izgilanci yace “Nemanki yake ne? ” A tsorace tace wa? Dariya yasa irinta rashin mutuncin nan ya kalli kannensa yace “kun yadda Ashraf haka kawai ya kawo ta nan ba da dalili ba? ” Nafi cikin mamaki ta kalleshi dan bata fahimci inda ya nufa ba. Dariya suka kara mata d’aya daga cikin su yace “amma wannan kwailar? Kalli fa kirjin? ” Dariya suka kara sawq hrda tafawa, Nafi kam yanzu tafara ganewa, kasa tai da kanta a hankali hawaye suka zubo mata. Little ce ta matso wacce batasan me suke cewa ba sai dai ganin suna dariya ya nuna mata iskanci suke mata. Tana karasowa tace “Ya Asim yanzu Ya Ashraf ya kira muje ko ince mai ka tsaida ita? ” Hararar Little din yai sannan ya kalli Nafi yace dalla bani guri. Nan Little ta kamata sukai gaba, tambayarta tai meya faru? Kai kawai Nafi ta girgiza alamar ba komai, haushi ya kama Little tace “to na fadama ya Ashraf inyaso sai ki fadamai. ” Da sauri Nafi ta rike hannun Little tace “Maryam karki fad’amai dan Allah. ” Da mamaki Little ta kalleta, Nafi ta goge hawayenta tace “dan Allah mubar maganan nan in yaji ransa ne zai b’aci. ” Little tai shiru sai dai tana jinjina hakuri irin na Nafi. Sun kwankwasa sai dai jin muryar mace sukai tace ku shigo, ba sai an fada ba sun san wacce. Fuskar Nafi ce ta canza, a falo suka ganta ta baje a kasa tana cin abinci shi kuma yana gefenta amma a saman kujera yana kallo. Jin sun shigo yasa ya kallesu itama kallansu take ganin Nafi yasa tace “me take anan?” Ashraf yace “d’akinki ne? ” Cikin shagwab’a tace “Amma ai ya kusa zama nawa. ” Idanunsa akan Tv yace “sai kijira inya zama naki sai ki fad’i haka. ” Mamaki ne ya cika Nafi wai haka itakam saurayi yake ma budurwa magana? Jiya da suka dawo sai taga kamar bada wannan zafin yake mata magana ba to ko abin zuwa yake? Ashraf ne ya katsesu da cewa “so kuke inta d’aga murya? ” Nafi kam bata fahimceshi ba, Little tace ” mu shiga. ” Sun karasa Little ta zauna kusa da Aneesa tace “Yaya Neesa nan kika gudu cin abincin? ” Ta kalli Ashraf tace “nafisan inci abinci a plate din dayaci tunda bayasan muci tare. ” Kasa Nafi tai da kanta da sauri, Ashraf ya kalli Aneesa sai dai bai ce komai ba. Little ta kalleshi tace “Yaya munkai.” Gud kawai yace, Little ta kara cewa “Gamu to. ” Nafi ya kalla yace “Nafeesa so nake gobe ki gyaramin b’angare na. ” Murmushi tai sannan ta d’ago ta kalleshi tace “Toh. ” Little tai kwafa aranta tace “kiyi murmushi da kyau. ” Aneesa ce ta harareta hakan yasa tai saurin maida kanta kasa, kanta ta maida kan Ashraf tace “Ya Ashraf yanzu me wannan zata maka? ” Cikin rashin damuwa yace “to ko zakiyi? ” Da sauri tai shiru dan ba abinda ta tsana irin aiki, Ashraf ya kallesu yace “Little kuje.” Little wacce dariya ta kusa kamata da yaba Aneesa amsa ta mike itama Nafi ta mike, har sun fara tafiya Nafi ta juyo tanasan tambayarsa. Kallanta yai yace “d’azu yaushe kika tafi? ” Aneesa ta kalla cikin tsoro tace ” ban dade ba ai. ” Kai ya d’aga kawai, ta daure tace “Goben karfe nawa zanzo? ” “Sanda kika gama abinda kike. ” Juyawa tai bayan ta amsa da to. Aneesa ta rakata da hararar tsana…. Suna fita ta shagwab’e ma Ashraf wai ya dizgata a gaban nafi. Murmushi yai yace “kinsan banasan irin tambayoyin nan ai amma naga in bakimin ba bakyajin dad’i. Habib shima mamakin ganin Yarinya ta fito daga d’akin Ashraf yake, itakam Nafi duk ta rikice duk da bata kawo komai a ranta ba amma ganin ga mumy da su Ashraf yasa jikinta ya shiga tsuma.+ Mumy a zuciye tace”Ashraf wani salon iskanci ne kuma hakan? Kanada hankali kuwa? ” Ashraf ya mike tsaye sannan yai wani murmushi ya kalli Mumy sannan ya kalli Nafi yace “Me kike nufi da kalamanki Mumy? ” Cikin takaici da fada tace “au tambaya ma kake? Yarinyar da ka kawo inganta ta fito daga d’akinka kace wai me nake nufi? ” A zuciye ta karaso kusa da Nafi wace ta rakub’e da jikin bango jikinta banda tsuma ba abinda yake, hannu ta d’aga a zuciye zata kai mata mari, Ashraf da sauri ya rike hannunta sannan ya kalli Nafi wacce kana gani kasan a gigice take ya maida dubansa gun Mumy yace “in kuma kika daketa ba da hakkinta ba fa? ” Mumy ta kalleshi cikin takaici tace “hakkinta?” Ashraf cikin takaici yace “kina tunani ni Ashraf zanyi tarayya da wacce ba matata ba? Bare wannan? Me take dashi? Me kuma nagani? Dan kawai yarinya ta fito daga d’akina bazakiyi tunanin komai ba sai zargi??” Mumy ta kuramai ido sai dai da alama bata gamsu ba. Ashraf ya runtse ido zuciyarshi ba dadi, Habib ya kalla ya mai alama daya fita da Nafi, nan Habib ya matso yace mata muje. Nafi duk ta gama rud’ewa tama manta mai ma ya kawota Ashraf kawai take kallo idanunta a hankali suka fara zubarda ruwa. Suna fita Ashraf ya kalli Mumy idanunsa shima sun kada sosai ya shafi kansa sannan ya matsa kad’an daga inda take, yace ” Ko a mafarki ban tab’a tunanin haka kika d’aukeni ba. ” Yana kainan yai waje a zuciye, jikin Mumy ne yai sanyi sai dana sani ya shigar mata, sai a lokacin ta kula da tsintsiya da abin mopping, kai ta dafe tace “dama yana nisanta kansa dani yanzu kuma na kara jan wani layin. ” Nafi kam suna fita kanta kp d’ankwalli babu tafiya kawai take, Habib ya kalleta yace ” Karki damu ba abinda zai faru. ” Juyowa tai ta kalli Habib sannan ta tsaya tace “Ba abinda Mumy zata mai ko? ” Hawaye suka biyo bayan kalamanta, dariya Habib yai yace “wa? Ashraf? Ke kiji da kanki bawai ki tsaya tunanin wanda kila yanzu yama manta abinda akai ba. ” Juyawa tai kawai ta cigaba da tafiya, Habib ya matso yace “ban sanki ba amma. ” Nafi tace “tare muka dawo da yaya taimakona yai. ” Dariya sosai Habib yasa anda sai da Nafi ta tsaya tana mai kallan mamaki tace “menene? ” Sai daya tsagaita yace “taimako? Wa? Ashraf? Don’t make me laugh. ” Nafi ta juya batace komai ba dan bata fahimceshi ba. Habib yace daga wani gari kike? Rigar Datti. Maimaitawa yai cikin mamaki yace ” ina kenan? ” Ita kanta batasan ina zata ce ba dan bata sani ba, ganin sun iso ta kalleshi tace “Nagode.” Murmushi ya sakar mata sannan yace “in Little ta dawo kice mata Habib yazo sai dai yanzu zan koma zan dawo nextwk. ” Kallansa tai a ranta tace “shine Habib d’in kenan? ” Ido d’aya ya kashe mata yace “what? Badai har kinji labari na ba? ” ya d’aga mata gira yace “ahh kinsan nid’in akwai farin jini ga masoya. ” Batasan sanda ta murmusa ba, Habib ya nuna ta da hannu yace” kinyi dariya ko? ” Juyawa tai da sauri tai ciki wani sansanyan murmushi ya saki yace ” she is soo beautiful and funny. ” gashin kanta ya tuno wanda aka mai kitso manya sak dai ya kwanta har bayanta, yai murmushi sannan ya juya a ransa yace “inta girma za’ai mace anan. ” Nafi kam tana shiga ta zauna a kasa, kalaman Ashraf ne kawai ke dawo mata, Me take dashi? Me na gani? Me yake nufi da kalamansa? Shiru tai kawai, Jitai ana kwankwasa kofar cikin zafi, ta mike da sauri ta bud’e, batai auni ba bakuma ta kula da waye ba taji mari gauu a fuskarta, da sauri ta rike gun wanda marin taji kwarai kuma har idanta na hago, dage idan tai cikin tsoro ta d’ago, jitai ance “Dan kut…….. Ke har kin isa in saki aiki yau ki k’i zuwa? “ Nafi ta kalli Umma sai dai ta kasa cewa komai sai kai kawai datake jijigawa, Umma ta sa kafa ta turata ciki, tace”wlh kinji ma fada miki ko da wasa akace kinyi fashin zuwa gun aiki sai na sa an kwantar dake a asibiti saboda duka. ” Tana kainan ta juya, Nafi ta zube a gun sai kuka, sosai take kuka tana kuma tuno mahaifinta da mahaifiyarta, sai dataci kuka ta koshi sannan ta mike tai kitchen dan basu hakuri. Sai dai me? Idanta kankace me ya kumbura saboda marin datasha a gun. A b’angaren Ashraf kuwa yana fita ya fizgi mota da gudu kawai yana tafiya meyasa Mumy zata mai haka? Ita fa Mahaifiyarsa ce inda wani ne da sauki amma mahaifyarsa? Meta d’aukeshi? Ko zinar zaiyi mai zaiyi da wannan kwailar? Yar kauye? Wacce kila bama tasan me tarayya yake nufi ba. A zuciye yai wani Rv ya kwantar da kansa a kan sitiyari wanda yaji yana saramai sosai. Nafi kam bayan taje kitchen Goggo ta taso da sauri ta karaso gunta tace “Nafi me ya sami idanki? ” Nafi tai murmushi tace “bigewa nai. ” Shiru Goggo tai sannan tace “d’azu Hajiya tazo nemanki, amma da alama wani munafikin ne a nan ya fada mata bakizo ba. ” Nafi tai murmushi tace ” Laifinane ai Goggo daban zo ba ” Cikin tausayi Goggo tace “Nafi idan nan naki fa ya kamata ko kankara asa a tsumma ki dan gasa ko kuma kisa lemon tsami kiyi ta mulmulawa. ” Nafi tai kasa da kai tace “Kiyi hakuri Goggo. ” Hannunta ta kama tace “kamar ‘yata haka nakejinki karki damu da komai kinji? Ki kula da kanki. ” Nafi ta d’aga kai sai ha hawaye sun silalo mata, nan Goggo ta shiga bata hakuri, ta dad’e kafin ta amso abincinsu itada little ta fito. Tazo wucewa ta ga motar Ashraf ya gangara yai parking tsayawa tai tare da yin kasa dakai dan karyagaidanta, sai dai ga mamakinta gani tai ya d’auke kai yayi gaba, Nafi ta kakaro murmushi kawai tayi tabi bayansa da kallo, ta sani laifinta ne mai ya kaita yin bacci? Ita kanta batasan ya akai ba. Tana shiga d’aki Little tace “Nafi tun d’azu nake jiranki. ” Nafi ta ajiye abinci, zata zauna Little ta taso da sauri ta riketa tace “Nafi meye hakan? Meya sameki? ” Nafi tace “bigewa nai. ” Little zatai magana taji karar wayarta ta d’aga ganin Yaya, bayan sun gaisa yace “Little in anyi magrib ki d’au Nafi kuje asibiti sannan kice ta bar aikin sai ta warke. ” abinda ya fada kenan ya kashe wayar. Nan Little ta fada mata gani tai Nafi ta shiga yin murmushi tana kasa da kai, zuciyarta taji tayi wasai kenan ba haushinta yaji ba? Kenan zata cigaba da mai aiki? ” Little ta saki baki tana kallanta, me kenan? ”