ZUMA CHAPTER 3 BY SHATUUU
Saura sati biyu na tafi kano, ranar Saturday Daddy na gida bai je ko ina ba, da safe ne ma brothers dinsa Kawu Lawan da Kawu Babandi suka zo daga hadejia mu muna bacci ma se da baba Asabe tazo ta tashe ni sannna naje muka gaisa na daura musu tea sannan nayi pepper soup na kaza. Misalin karfe biyu aka dawo da nepa wadda tun dare suka dauke, tashi mukai muka kwashe carpet din da muka baza a terrace din gaban parlon mu saboda zafi ake bana wasa ba. Zama mukai muka fara kallo kamar yadda muka saba, mikewa nayi naje na hadawa Hudayyan Mom cereals na janyo ta jikina ina feeding dinta, yaye aka kawo mana ita, tana shan gata a gurin mu and I’m sure idan ta koma gun iyayenta zasu ce mun bata musu yarinya. To ya zamuyi duk cikin mu babu wanda bai iya raino ba, idan Hudayya ta tashi tana kuka cikin dare to dukkan mu se mun tashi mu kafa lallashi.+
Seda ta koshi sannan na goya ta a bayana tayi luf tareda fara bacci. Zama nayi se muka ji sallama a kofar parlon mu, Ummu tace ma Baba Asabe ta shigo, shigowa tayi tana binmu da kallo tace
“Hutawa kukeyi?”
Eh muka ce mata sannan ta dubeni tace
“Nanah anyi baki suna nan tsakar gida”
Bata fuska nayi nace
“Wai ni baba Asabe ni meye matsayina a gidannan, kome se kice ni, baga su yaya rahama nan ba”
Tsohuwar ta saba da halin mu ko mun mata abu bata nuna bacin ranta, hakan yasa ta kwantar da murya tace
“Ayya uwar dakina, kinsan kin fi kowa sanin yadda ake tarbar baki a gidannan, kizo muje suna ta jira”
Haka nan babu yadda zanyi na mike bayan na kunce goyon hudayya daga bayana na bawa A’isha tare da mata kashedin saura kuma ta kada ita ko ta tashe ta. Yaya Mariya tana murmushi tace
“Allah dai ya biya Maman yara!”
Ko juyawa banyi ba bare na bata amsa, seriously ni nake playing role din babba a gidan, yaya Mariya da ya Rahma kamar hoto haka suke, so idan ina bada umarnin aiki har su nake hadawa. Jikina na kalla, skirt da riga ne na atamfa, ya min cif a jikina. Kaina babu dankwali se hula dana zura ta rufe min kwakuidan da nake dashi. Ashe na manta bance muku banda gashi ba, ai kaina tamkar afro haka yake se yanzun ne ma da nake ta neman natural boosters naga ya fara mikewa amma da ko kitso ba nayi.
A tsakar gida na samu mata su biyu, daya ba zata wuce yaya nasiba ba, dayar babbar mace ce ta manyan ta sede bawai tsufa ba, amma kana ganinta kasan tana late 40s dinta. Da murmushi na karasa ina gaishe su , suma se suka saki ran su, da kowacce tayi kicin kicin. Iso na musu zuwa karamin parlon da muke saukar baki, a share yake tas yana ta kyallin mopping ga kamshin incense woods me sanyaya rai. Saman kujera suka zauna, fridge din dake parlon na bude na ciro bottled water da kato kwalin exotic masu sanyi, a gefe na dakko tray da tumblers na aje musu, sannan nima na zauna na kara gaishe su, babbar tace min
“Yan mata meye sunanki?”
“Nanah”
Na fada a takaice, kai ta gyada sannan tace
“Babanku fa? Yana nan?”
Kallonta nayi nace
“Ni ban gane ku bafa ko zakuyi min bayani?”
Dan murmushi tayi tace
“Daga kano muke, munzo ganin Aminatu ne, ni yayar babarta ce. Babanku na nan?”
Se kuma data fada se naga suna yanayi da Aminatu, mikewa nayi na shiga parlon suna nan yadda na barsu, Amina na duba da ke tsotsar bigbom nace
“Kije parlon baki ki jirani”
Daga haka na dauki hijab na nufi parlon Daddy, yana kwance ya kinshigida da pillow, idanun shi a lumshe amma nasan it’s not necessary bacci yake, ina sallama ya amsa min, na shiga na zauna gefen shi, kamar wanda yake meditation bai bude idon ba yace
“Nanah ya akai?”
Zamana na gyara nace
“Daddy kayi baki”
“Su waye?”
Ya tambaya yana a yadda yake, nace
“Yayar Maman Aminatu ce tazo”
Ai se yayi zumbur ya mike ya zauna, inata kallon shi da mamaki dannni banga wani abu ba dan anyi baki, se kuma ya mike tsaye yace
“Suna ina?”
Tashi nayi nai masa jagora zuwa can parlon, Aminatu na jikin yayar Maman ta anyi cuddling dinta fuskokin su cike da farin ciki, yana shigowa ya daka mata tsawa abinda ban taba ganin yayi ba, jikinta har rawa yake ta sauka daga jikin matar sannan yace ta fita , nima se na bita. A wannan lokacin ba musan me suka tattauna ba amma sunfi awa tare se can suka fito inajin tana cewa
“Kaji tsoron Allah Ibrahim! Wannan abun da kakeyi bazai bille ba”
Banji muryar shi ba se dayar kanwar tace
“Baka isa ka raba uwa da yarta ba duk balain ka. Kuma an riga an gama da kai tunda ta riga haifi Aminatu”
Bai ce komai ba ko kuma mune bamu ji ba, wannan Antyn Aminatu ta dinga zage zage tana balai se lokacin muka fahimci me yake faruwa, Maman Aminatu Anty Maryam bata da lafiya an kwantar da ita a nassarawa a kano shi ne suka zo tafiya da ita saboda uwar na kiranta shi kuma Daddy yace babu wanda ya isa. Tun muna zaune har dukkan mu muka fito tsakar gida, Aminatu se kuka take a jikin yaya Mariya yayinda babbar Antyn take kuka itama. Baba Asabe ke ta basu baki amma Daddy bai ce koami ba.
“Wallahi se ka sani se kayi dana sanin hana mu tafiya da Aminatu da kayi, se na kaika kotu tunda babu inda aka ce ka yanke alakar uwa da yarta, ka tara uban yara ka rabasu da iyayensu . Hakki bazai barka ba Ibrahim.”
Se lokacin yace
“Ina jiran sammaci, duk shekarun dana dauka ina kula da yayana akeai wadda tazo neman su, se yanzun da suka girma zaku tsiri zuwa dan kuyi min confusing yayana!”
Small Antyn tace
“Aminatu yarka ce babu wanda zai canja wannan amma Anty maryam nada hakki akan ta, ba dan batada lafiya ba waye zai koma ta kanka!”
Hanya ya nuna musu yace su fita mishi a gida, mostly irin wannan abin baya damuna amma yau se naji babu dadi especially irin kukan da Aminatu take it was heartbreaking. Haka nan suka tafi mu kuma muka koma cikin parlon kowa yayi shiru se Amina kawai da har lokacin batai shiru ba. Ranar haka ta kare babu dadi ko kadan amma ya zakai haka rayuwa take. Har wajen kwana uku Daddy baice komai ba, munata zuba ido muji abinda zaice amma baice ba, bayan mun gama breakfast har lokacin Aminatu bata dawo daidai ba ta rage hayaniya da shiga cikin mu, kana kallonta kasan abu na damun ta. Ni da Amal muka same ta tana kuka sosae na zauna nace
“Meey! Kiyi hakuri kinji”
Hannuna ta riko tace
“Bazan iya tuna mamana ba, me yasa Daddy bazai bari naje ba what if idan ta mutu? Shikenan bamu gana ba kenan?”
Ta kara sakin kuka, kanta na shafa nace
“Ya isa haka, zakije inshaaa Allah, I promised you zan ma Daddy magana”
Parlor na koma muak zauna nace musu basa ganin ya kamata muyi wani abu akan maganar reuniting Aminatu da ma
manta. Yaya Rahama tace
“Saboda me? Mu namu iyayen sun zo ne, nidai ba ruwana ke baki jin haushin abinda sukai wa Daddy ba plus Anty Maryam babu irin azabar da batayi mana ba muna yara.”
Nawwara tace
“Kai ya Rahama amma kinsan wannan ya wuce, kuma mu namu iyayen ai basu zo neman mu ba”
Lubna tace itama babu ruwanta, Amal dani da yaya Mariya muka ce mu zamuyi whatever it takes muga Daddy ya yadda.Da sassafe bayan kwana biyu da alkawarin zamuyi ma Daddy magana, se na kasa nasan dai na kira su Mom na fada musu. Kullum aikin mu lallashin Aminatu ne. Ranar was Wednesday kamar yadda ya zama routine sun gama shirin makaranta, suna breakfast Daddy ya shigo, kowa ya gaishe shi se yace dasu su bar makarantar akwai driver nan da 30minutes zai zo dukka mu tafi kano, to muka ce masa ba tareda sanin inda zamu je ba. Ni kadai ce banyi wanka so bai dauki lokaci sosae ba nayi wankan na gama shiryawa. Kowa yasa kayan da yake so muka fito tas damu, kana kallon mu kaga yan mata yan gayu masu gata ta ko ina. Driver na zuwa muka fita bayan munyi sallama da Daddy da baba Asabe, ya bamu kudi koda ace zamu saya wani abin.
Bansan unguwar ba na dai san ba anguwar su Anty Sumayya bace, A kofar wani gida yayi packing yace mana munzo, dukkan mu muka fito muka shiga gidan bakin mu dauke da sallama. Karamin gida ne babu wani space sosae ko ina a kuntace, wata datijjuwar mace tana ta kai kawo a tsakar gidan, gaisheta mukai ta tsaya na wani seconds tana kallon mu, nasan kokari take ta fahimci mu din su waye, bata fahimta ba se kawai tace mu shiga ciki, muka shiga muna rarraba idanu, mu bamu san ina Daddy ya kawo mu ba, tunda bai mana bayani ba. A dakin muka tadda mata su biyu daya a kwance daya kuma a zaune, tana ganina tace+
“Nanah!”
Se lokacin na fahimci inda muke gidan kakkanin Aminatu ne, dagowa ta kwancen tayi ta rame, idanunta sunyi mugun shigewa ciki, ta kankance dukda alamu sun nuna dama can ba wani girma ne da ita ba,
“Aminatu ta zo nan! Zo Amina ashe Allah zai hada fuskar mu kafin na mutu”
Dukkan mu jikin mu yayi sanyi kamar an cinye mu, Amina ta kasa motsawa tana kokarin adjusting da situation din, yaya Mariya tace
“Amina hug her mana”
Lubna ta dan taba ta se ta fara kallon mu idanunta sun kawo ruwa, kanmu muka gyada mata se ta tafi ta fada jikin Anty Maryam dukkansu suka saki kuka, wannan scenario is really heartbreaking sosae. A gidan muka yini se yamma muka tafi, har Aminatu saboda Daddy yace lallae lallae mu taho tare.
Bayan sati daya Daddy ya kaini school, seda ya tabbatar nayi packing a dakina dana siya sannan mukai sallama ya tafi, na koma dakin ni daya a ciki amma bawai ni kadai ba dan akwai beds uku bayan nawa alamar sauran sun fita kenan, kan gado na na zauna na hada kaina da gwiwa na dinga rusa kuka, tunda nake a rayuwata ban taba barin gida ba, ban taba zuwa wani gurin ni daya ba, duk inda zamuje tare muke zuwa da dukkan sisters dina, nayi ta kuka inajin kewar gida sosae a zuciyata. Na kusan awa sannan na wanke fuskata na dawo na fara bude kayana ina jera su yadda ya dace, komai na gyara sannan na shimfida sabon bedsheets saman gadon na, komai na kammalla kafin aka fara kiran sallar laasar kuma babu wanda ya dawo cikin roommate din nawa. A daki nayi sannan na zauna inata tunanin duniya, mostly ma tunanin gida ne ina ayyanawa da ace muna tare da tuni ana can ana wani abin. Wayata na janyo na fara kiran Aminatu kamar jira take ta dauak tana fadin
“Ya Nanah gidan babu dadi bakyanan! Tun dazun Ummu take kuka”
Se naji idanuna sun ciko da kwalla amma haka na cije mukai magana dasu sede ban yadda nayi magana da Ummu ba saboda nasan idan nayi wannan mistake din I’m going to cry again, dukda hakan bayan ‘munyi sallama seda nayi kukan. Se maghrib sannan wata ta shigo ta kalleni sannan ta zauna dayan gadon tace
“Sannu fa! Kece new roommate din tamu?”
Kaina na gyada ina kakaro murmushi nace
“Ni ce!”
Kanta ta gyada tace
“Welcome, I’m Habiba jos”
“Nanah Fadima Hadejia”
Bamu kara magana ba ta mike tayi sallah sannan tace min nazo muje waje, taga nayi shiru. Hijab dina na zura nabi bayanta, anan take cemin ita level 2 take a Biochemistry. Wani eatery mukaje tayi mana order abinci amma naki ci, babu yadda batayi ba nace mata na koshi. Haka taci sannan muka dawo daki na hada cornflakes nasha anan sauran biyun suka dawo, daya Hafiza level 3 tana Nursing duk tafi su faraa se dayar ce ma bata da magana Aisha.
A hankali na fara attending lectures, na fara fahimtar yanzun aka fara rayuwa, jamia bawai gurin wasa bace aa you got to meet different people, anan zaka fahimci mutane yadda suke, zaka fahimci yadda rayuwar take gaba daya. Seda nafi sati biyu kullum nayu waya da Daddy ko kuma sisters dina to se nayi kuka, babu ranar da zata zo ta fadi banyi kuka ba amma a hankali na fara sabwa da yanayin gurin da kuma mutanen da nake tare dasu. Kullum mukai waya se Daddy yace min na kula da kaina, he trust me shiyasa ya yadda ya aikoni wani garin so na tabbatar na rike amana kuma Allah yana kallona idan shi baya kallona. So wannan maganar tashi kept me going kuma ko rudin kawaye yasa nayi niyyar abu se words dinsa su hanani yi.
Rayuwa tabbas tafiya take kuma kowanne abu ya faru daku it happens for a reason, sede lokuta da dama bamu fahimtar hakan har se abin ya faru, bahaushe yace Allah na rufe maka wata kofar kuma se ya bude maka wata.
A hankali first semester ta kare nadan yi sabo da mutane kadan daga cikin course mate dina, sede babu wani da mukai irin shakuwar nan dasu. Munyi exams ranar dana gama da yamma driver da Daddy ya aiko min daga dutse yazo daukata. Muka biya ta gidan kakkanin Aminatu muka dauke ta tazo hutu. Tayi kyau sosae kana kallonta kasan a nutse hankalinta yake, ga wani yanmatanci daya fara bayyana a tare da ita.
“Yaya Nanah baki ganin ya kamata ki tambayi Daddy ina Mom dinki take?”
Kallonta nayi for some seconds sannan nace
“Me yasa?”
Hannuna ta kama tace
“Da ina ganin kamar I don’t need a mother, a ganina Daddy is over sufficient a rayuwata, idan na duba ku matsayin yan uwana se naga what will I request from God again? A ganina babu but bayan haduwata da Ummata se naji I’ve missed alot, uwa daban ce, daban take ya Nanah se kinji ki kusa da ita sannan zaki fahimci me nake fada”
Tabe baki nayi dan maganar ta bata shige ni ba, nace
“Aminatu ni fa Daddy ya gama min komai, bana bukatar kowa cikin rayuwata, ku dinnan kun isheni. Had it been whosoever my momma is ta damu dani da tuni ta neme ni, amma tsawon shekaru nawa? Shekara nawa Aminatu babu wani da ya taba zuwa da sunan dangin Mamana. So you never miss what you never knew”
Kanta ta gyada in defense tace
“Eh nima na dauka hakane amma daga baya na fahimci ba haka bane, Allah kadai yasan abinda yayi stopping Mom dinki from coming to you, ina son ke ki neme ta tunda kin samu dama, Daddy ya barki kin bar Dutse karatu!”
Na jima ina tunanin maganar da ta fada min, se naji ta fara tasiri a cikin raina, ganin yana neman hanani sukuni yasa na hakura kawai da maganar na tattara na barta.
Hannuna nasa na janyo wayata dake ringing karka shin pillow na, Jabir na gani shi ne me kira, mamaki sosae ya kama ni danni bazan ma tuna when last ya kirani ba, nadai san bayan na tafi kano munyi waya yake cemin zaizo nace masa ai na tafi Kano, ya tambayeni me nakeyi acan, nace mishi school nake acan, se ya dinga fada wai saboda ban dauke shi bakin kaomai ba shiyasa ban fada masa ba, tun ina bashi hakuri saboda nima nasan ban kyauta ba kuma lallaba shi nake mu rabu lafiya, amma se naga abin ya wuce yadda nake tunani se wani fada yake min kamar Daddy.+
“Tsaya Jabir! Me kake tunanin kakeyi ne? Ya zaka sani a gaba ka
dinga min fada se kace ka haifeni? Dakata dan Allah you don’t have that right ka gane?”
Nasan yayi mamaki saboda baisan wacece Nanah ba, se yayi shiru ya kasa bani amsa ni kuma ganin hakan yasa na cigaba da fadin
“Dama ance dole se na fada maka abinda yake wakana cikin rayuwa ta? Nawa ne na fada nawa ne na bari….”
Se lokacin ya katse ni yace
“Nanah, a rayuwata abu daya nayi bayan haduwa ta dake shi ne son ki, ina son nuna miki cewar son ki shi ne abinda ya zaunar dani gurin ki, tsakanin da Allah I meant no harm gareki,to amma ina ganin kamar I committed a crime loving you, na fahimci banida space kwata kwata a zuciyarki. Nanah me yasa ba zamu hakura ba? Nidai ina ganin mu hakura kawai”
Seda naji dumm duk iskanci na, amma se na dake nace
“Ok Allah ya hada kowa da rabon shi!”
Banma jira me zaice ba na kashe wayar, na cigaba da harkata, to ina tunanin daga wannan lokacin bai kara kirana ba nima dake ba sonshi nake ba na cigaba da harkata, lokuta da dama ina ganin roommates dina suna waya amma ko a jikina dan har lokacin that mentality is still in me.
Da mamaki na dauki wayar amma se naji bana bukatar jin abinda zaice, seda ya kira sau uku sannan na dauka ina kokarin kwanciya,
“Nanah kina lafiya?”
“Lafiya lau, ya aiki?”
“Alhamdulillah” ya bani amsa sannan yace
“Zanyi aure Nanah shi ne nace lemme call and tell you”
Se daga baya na fahimci Jabir ya kirani ya fada min zancen auren shi saboda naji haushi, a wannan lokacin banji komai ba a raina in fact murna nayi ma saboda at least zai barni ya manta dani. Sosae na masa murna sannan mukai sallama. Yaya Rahama dake gefena tana taje ma Ummu kai tace
“Ke Jabir din aure zaiyi ne? Shi ne na ganki kina wannan murnar?”
Na kalleta da mamaki nace
“Kiji ki da wata magana, kashe kaina zanyi ko me? Ni ba son shi nake ba so yaje yayi ta auren shi mana”
Comb din hannunta ta aje tace
“Kede bakida kirki wallahi, har se yaushe zaki girma ne? Haba ke kuwa Nanah shi din Jabir din korar sa kikai”
Kaina na girgiza exactly abinda yasa tuntuni naki fada musu kenan, saboda ban son wannan lectures din,
“Shi fa yace mu rabu fa, ni bani nace mu rabu ba”
“Ta yaya ba zai ce ku rabu ba bayan baki dauke shi da muhimmanci ba? Dole ya barki yaje ya samu me sonshi. Ki maida hankali yanzun baa yiwa samari haka”
Na manta banza na cigaba da chatting da wata friend dita ta buk. Haka ta hakura ta barni. A haka hutu na ya kare na shiryawa komawa na huta da mitar da yaya rahama keyi akan rabuwar mu da Jabir har Anty Sumayya seda ta fadawa nasha fada kuwa. Wannan karan da zan tafi banyi kuka ba, haka na tafi amma deep down ina missing dinsu sosae. Cikin sati daya lecture ta kankama sosae da sosae se ya zamana I’m do much occupied karatu babu kama hannun yaro. Wajen tsakiyar semester na gama lectures da yamma, muka fito ni da Hibba,
“Hibba se gobe?”
Kanta ta gyada tace
“Allah ya kaimu”
Nayi murmushi nace
“Ki gaida Mami”
Hararata tayi tace
“Bazan fada ba, bayan har yau kinki zuwa”
Hibba rigima na ayyana a raina ina dariya a hankali, tace
“Wallahi bazan fada mata ba, bakida mutunci ai wallahi ko weekend ya kamata ki dinga yi a gidan mu”
Nayi dariya nace
“Kina da damuwa Hibba, ban fadawa Daddy ba so gaskiya bazan iya zuwa ba.”
“To ni ki bani number Daddy se na tambayeshi “
Dariya nayi sosae nace
“Kije gida kawai mayi magana gobe”
Tsaki tayi mukai sallama ina dariya nayi hostel, inata murmushin abinda ya faru Hibba kawa ta ce sosae, ko secondary banyi kawa kamar Hibba ba, ina sonta haka nima tana sona, yanzun ko da yaushe tare muke da ita. Ina zuwa daki na fita na daura abinci amma har ruwan ya tafasa banyi figuring me zan dafa ba, haka kawai na hakura na juye ruwan flask na tsiyaya wani a cup na hada tea nasha. Wanka nayi sannan na dawo na kwanta na lumshe idanuna. Ina nan kwance har akai maghrib da isha ban tashi ba saboda period nake amma a hankali nake jin wani ciwo a ciki na, yana radiating zuwa bayana. Nidai ban tashi ba ina kwancen ina cije lebena. Se wajen 9 sega Anty hafiza ta shigo, ganina bana karatu ko kallo cikin system tasan babu lafiya.
“Nanah bakida lafiya ne?”
Kaina na gyada mata ina juyi kan gadon, hannuna a jikin cikina amma banyi magana ba, hannuna ta kama tace
“Sannu bari a samo pain reliever”
Sakina tayi ta fita gani nake kafin ta dawo zan mutu dan wani irin ciwo ne da ban taba fuskantar shi a iya tsawon rayuwata ba. Tana dawowa tayimin allura ban masan ya akai ta iya ba a wannan lokacin ko me tace zata min bazan yi enquiring ba yadda zanyi dan kuwan gani nake kamar zan mutu ne. Bayan kamar mintina biyar wani wahalallen bacci yayi gaba dani, ban farka ba se cikin dare shima mild ciwon ne ya tasheni amma ban jima ba na kara dozing off. Da asuba na tashi nayi wanka duk jikina babu dadi na dawo na kwanta lokacin su kuma suke kokarin shirin zuwa lectures. Anty hafiza ta hada min tea da noodles ta sani naci amma ko gama kwashe kayan batau ba na fara amai ina kara jin ciwon kamar zan mutu.
Har biyu na rana ina kwance, wayata kuma a kashe amma jikin da sauki duk yan dakin mu duk sun fita se ni daya a kwance, nayi kuka har na gaji saboda ina tuna da ina gida wanne irin gata zan samu, kawai se naji sallamar Hibba, a hankali na kalleta fuskarta a hade amma se naga tayi saurin karasowa tareda zama gefena tace
“Nanah what is it? Me ya sameki! Innalillahi Nanah kin ganki kuwa?”
“Hibba I’m sick cikina ke ciwo ne tun jiya”
“Kinsha magani? Kin ci abinci?”
Kaina na girgiza mata nace
“Anty hafiza ta bani shot din pain reliever”
Mikewa tayi ta ciro wayarta daga gown pocket dinta tayi dialing only God knows who, cikina ya murda na runtse idanuna so bansan me tace ba. Hannuna ta kama tana ta min addua anan ta gano wayata data dauke saboda babu chaji kuma I wasn’t able to fix it. Power bank ta ciro ta saka min sannan tayi turning power on, hijab ta saka min bayan tayi waya ta kamani muka fita. A hallway muka hadu da Mami kamar yadda ta kirata, rikoni tayi ta kara ni a jikina tace
“Sannu Nanah, sannu kinji da kin kira mu tun jiya”
Asibiti suka kaini akai admitting dina, cikin few hours cikin ya lafa, mukai scanning aka kaga result din aka daura ni akan drugs. Mami ta kira Daddy da kanta ta fada masa akan zata tafi dani gidan ta, ya dinga mata godiya sannan zai zo washegari. Kwana biyu naji sauki sosae Daddy dasu sisters dina duka sunzo gani na, su Anty Sumayya ma duka sunzo. Dutse na wuce saboda mun samu hutun mid semester break, na tafi ina matukar ganin girman Hibba da iyayenta, maganganun Aminatu suna min yawo a kaina, tunda naje gidan su Hibba babu abinda ya birgeni kamar yadda suke da Maminsu, komai nasu ita ce, ko se yaushe zanga tawa uwar?