ZUMA CHAPTER 5 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 5 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Nanah na manta na fada miki ya kamata ki fadawa Aliyu ke wacece, ya yanayin gidan ku yake saboda bana son a kara maimaita case din Mariya, Mariya zata iya hakura amma ke dinnan a yadda kike son Aliyu dinnan bana tunanin zaki iya tawakkali.”+

Kaina na shiga gyada ma Anty Sumayya nace

“Nima Nayi tunanin haka Anty amma ni na rasa ya zan fada masa tunda shi ya dauka I’ve lost my mom”

“Then se ki kirashi kiyi masa bayani saboda gwara a bakinki akan a bakin wani, kinsan yadda muke a idon kowa a unguwar nan, wama yasan me aka fadawa Zunnun din Mariya? Allah kadai ya sani so gwara ki fada masa, gwara duk abinda zakuyi should be based on gaskiya”

“To Anty right away zan kira shi idan na koma school na fada masa”

Kanta ta gyada tace

“Allah ya tabbatar da alkhairi, also ki tambaye shi inda yake da unguwar auren shi da kuma unguwar shi, Abban Arfaat tun ranar yake cemin na fada miki saboda ayi bincike kowa yasan we’re in a safer place”

Nanma kaina na gyada sannan tace min

“Nanah ke bazaki tambayi Daddy inda Anty A’isha take ba, bakya jin ya kamata kisan inda take”

Ajiyar zuciya na sauke nace

“Na tambaye shi yace min wai is not the right time, idan yazo base na tambaye shi ba”

“To Allah ya kaimu lokacin”

Anan gidan ta na wuni ranar se yamma na koma school tayi min dambun nama da miya. Ina shiga daki na rage kayan jikina sannan na watsa ruwa na daura spaghetti naci. Wayata na janyo ina chatting nayi wajen mintina talatin sannan kuma na fita na fara kiran Aliyu, bai jima yana ringing ba ya dauka yana fadin

“I’m sorry ban kira ba”

Murmushi nayi nace

“Ni gashi na kira, ya aiki?”

Haka mukai exchanging gaisuwar mu kamar ko yaushe, sannan nace

“Akwai maganar da nake so muyi can you make time?”

“Yaushe kenan?”

“Ko zuwa gobe tunda Sunday ce”

“Allah ya kaimu, so ya kika baro Anty din da yara?”

“Duk suna lafiya lau, tana gaisheka”

Daga haka muka koma wata hirar lokacin karatu yayi mukai sallama ma maida hankalina akan studying handouts dina.

Washegari misalin karfe goma na fita wajen Aliyu, munada specific gurin da muke haduwa ni dashi, yana zaune har yayi order ruwa da drink, nasan drink din nawa me dan shi yace he’s 40 ba yadda zai dinga shan carbonated drinks masu sugar da yawa saboda health dinsa. Da murmushi na karasa na zauna ina fadin

“Sannu da zuwa,”

Murmushi yayi min yace

“Morning how was your night?”

“Alhamdulillah ya yara, nayi tunanin zaka taho dasu”

“Naso yin hakan amma Fatima ta fita dasu”

Cikin rashin fahimta nace

“Who’s Fatima?”

Se yayi dariya yace

“Maman su ce”

“So sunan mu daya kenan?”

Na fada sounding amuse, kanshi ya shafa yace

“Yes! Ke Fatima ita Fatima ina haifar yarinya mace zan saka Fatima”

Kaina na gyada nace

“To Allah ya yadda”

Lokacin da na fara masa bayanin gidan mu da abinda  Anty tace nace

“An samu matsala a auren ya Mariya shiyasa nake fada maka, Daddy yayi aure da yawa kuma….”

Se nayi shiru ina dan sunkuyar da kaina. Se shima Yayi shiru sannan yace

“To ai ke nake so, aure auren Daddy has nothing to do with you, kowa akwai path din da Allah ya kaddara masa zai bi, ita yaya mariya hakan ce tata”

Se na saki ajiyar zuciya tareda jin karfin gwiwa, haka nan na cigaba da fada masa not like he expected mamana bata da rai na fada masa ban taba ganin ta ba, mun rabu ranar da aka haifeni.

“Don’t you miss her?”

Ya tambaya da wata irin murya me cikeda murmushi, dariya nayi na girgiza kai na

“Some years back ina yawan fadan you don’t miss the person da baka sani ba, amma bayan na kara girma se naji I’m missing her so much, so nake na ganta sede ina jin tsoron ko bata da rai!”

Na fada ina sunkuyar da kaina tareda jin wani abu ya tokaren wuya na, lallashi na ya dinga yi da kalamai masu dadi harse da ya tabbatar my mood was lighten up a little. Kamar yadda Anty ta saka ni haka nayi bai boye min ba ya fada min nima na fada mata kuma a binciken baa samu matsala ba.

Aliyu wani jigo ne a rayuwa ta wanda bazan taba mantawa dashi ba, ban taba son wani abu kamar yadda na so shi ba. Ya zame min wani jigo na rayuwata, ya zame min tamkar wani tsani da zan dafa ya kaini higher step, akwai lokuta da baka gane potentials dinka har se wani ya haska maka to me Aliyu shi ne ya gwada min potentials dina abubuwan da kaina zan iya achieving.

Bayan wannan haduwar mun jima bamu kara haduwa seda Mom da Anty ta fadawa Daddy ya saka ni na tura masa Aliyu sukai magana man on man, ya bashi izinin zuwa guri na, ranar da hakan ta faru ji nayi tamkar an ma mallaka min shi din gaba daya sede we’ve a long way to go.

Ranar Saturday na gama karatu dan mun fara second semester exams. Wayata na dakko na kira Aliyu dan munyi dashi zan kira shi idan na gama. Time na kalla naga goma da minti daya. Dan tsaki nayi na aje wayar ina fadin

“Matsalar dating me mata, ba kada damar kiran shi lokacin da kake so”

Sake dauka nayi, bayan na kalla number dan ban mayi saving ba a raina nace ya kamata na samo sunan da zan masa saving. Na shiga tunani ina tuna dukkan wasu sunaye dana sani amma se inga kodai an jima ana amfani dasu ko kuma it’s too rampant. Baby yayi yawa kowa haka yake fada, sweety se na girgiza kai ina yatsina fuska kamar me shirin amai, na kusan mintina talatin ina abu daya kafin hannuna yayi typing Sahibi❤️. Da haka sunan ya fara, naje nayi shirin kwanciya lokaci ya nuna sha daya saura se kawai na tura masa text

Sahibi, na kira ka baka dauka ba, I guess ka shiga gida. We talk later, night!

Shi kenan content din na tura masa sannan nayi juyi na kwanta ina addua Allah ya bamu alkhairi. Akwai lokutan da zakai bacci ko ka farka cikin dare se kaga tamkar baka jima kana baccin ba. Cikin bacci naji vib din wayata, idanuna na bude tare da yin mika na janyo wayar, Sahibi❤️ ke yawo kan screen din, ban duba time ba banyi komai ba kawai nayi swiping thinking se yanzun yaga message dina. Koda na dauka saboda baccin dake idanuna banyi magana ba, shima haka, shirun na wajen 10 seconds kafin nayi breaking da fadin

“Hello!”

Muryar da naji tasa na bude idanuna baki daya, lokaci guda naji duk wani bacci ya tafi bat, se idanuna ya koma tamkar ban taba jin bacci ba, if I’m not mistaken a wannan lokacin muryar mace naji, ban gama gaska ta wa ba naji ta cigaba da fadin

“Kece karuwar da kike damun mijina da kira ko? To tsaya na gaya miki mijina nawa ne ni kadai, babu wata sh
egiya da ta isa ta shigo gidan nan wallahi, kinga miji dan cifcif shi ne zaki nace masa. Kije kiyi karuwancin ki amma banda mijina! Jaka kawai!”

Kit ta kashe wayar ta barni da waya a kunne na kasa saukewa, abin ya kasa sinking cikin kwallwata banda amsa kuwwa babu abinda maganar tata ke mini!Gaba daya kaina ya kulle na kasa cire wayar da kunne na, kuma na kasa yin tunani, se can wajen mintina da suka shude sannan na tashi na zauna wanda ya bawa wayata damar sulalowa tayi zaman dirshan kan gadon, dauka nayi na duba lokaci naga ashe asuba ma ta kusa tunda hudu da mintina goma. Nasan bazan kara komawa bacci ba duk naci na. Se kawai na tashi naje nayi alwala nazo dam nayi karatu, ni kaina nasan ba iyawa zan yi ba amma wani lokacin kana bawa zuciyar ka benefit of doubt. Se da nasa takaddar karatun a gaba kafin kuma na fara tunani. Me ya faru har ta dauki wayar shi? Kenan tunda ya koma gida suke ta fada har ta fi karfin shi ta dauke wayar ta zazzageni? Kaina na girgiza Aliyu bazai taba barin Fatima ta zageni a gaban shi ba. Amma to me ya faru? Meye laifina anan? Kiran shi da nayi, soyayyar da muke yi ko ko me? Kaina na girgiza ina ayyanawa banida laifi ni a zaman mu kullum kokari nake ganin ban shiga hakkinta ba amma ita me yasa zatayi haka?

Se na dauki wayar na duba lokaci naga har mintina ashirin sun karu, to ko nayi dialing number tunda nasan tana hannun ta se inyi knocking senses cikin kanta? Se kuma na ayyana to zan biye ta ne? To kuma idan ya zamana ta goge nata kiran ni tayi min sharri! Se kawai na girgiza kai na ina fadin. Komai zai tafi daidai. Mikewa nayi nayi sallah na jima ina addua sosae sannan kuma na tashi sauran roommates dina na tafi wanka. Lokacin da na dawo gari ya fara washewa se na dama cerelac na sha. Sofy na cemin

“Ni fa Nanah idan naga kina shan cerelac dinnan kunya nake ji”

Murmushi nayi nace

“Haba dai. Da baki je gidan mu ba da kinyi kallo”

Ina gamawa na shirya na dauki abunda zan dauka nayi musu sallama se class. Kadan na samu a class din se na zauna ina duba littafi na. Kafin na shigo class din na kira Anty Sumayya dan fada mata halin da ake ciki, midway wayar ta fara ringing na tuna Hibba ta taba cemin anyi irin haka da sister dinta, matar saurayin ta ta kira ta zage ta ita kuma ta fadawa Mami, mami ta fadawa babansu se aka fasa bikin wai matar tafi karfin mijin kenan. Tunawa da nayi yasa nayi saurin katse call din ina ayyana idan haka ta faru dani bazan kara numfashi ba, kamar yadda relationship din namu zai zama tarihi nima hakan ce zata kasance dani.

Inata kokarin concentrating haka dai na samu na dan taba har Hibba ta zo. Da mamaki ta zauna gefe na tace

“Kora akai daga hostel?”

Harara ta nayi nace

“Na canja ne na daina latti”

“Kamar gaske”

Ta fada tana ciro foil paper daga jakarta, miko min tayi sannan ta miko min kunun aya cikin water bottle me sanyi tace inji Mami. Naji dadi har cikin raina sannan naci naman da samosa na jefa sauran a jaka shi kuma kunun na shanye tas ina lashe baki nace

“Allah ya sakawa Mami da aljanna”

“Ni kuma fa? Ni na kawo fa?”

Se nayi dariya nace

“Har dake mana”

Inata son na fada mata amma na kasa gani nake bazan iya fada ba. A haka ranar tazo ta wuce zuciyata babu dadi, bawai na tsorata da empty threat din ta ba, aa shi da bai kirani ba shi ne matsala ta, ni kuma na kasa samun kwarin gwiwa na kirashi , matar shi sau daya a tarihi taci nasara akaina, duk masifa da fada irin nawa se na gagara bata amsa balle ma na rama, baa taba haka dani ba, bana barin fada saboda ni mafadaciya ce amma imagine wai yau ni ce a hakan.

Wajen karfe tara na dare ina zaune ina kallo saboda na rasa me zanyi ya dauke min hankali amma na rasa, kimai na fara se naji ya isheni, nayi game, nayi chatting amma duka se naji babu armashi se kawai na kunna kallo ina forcing kaina nayi din. Wayata ce ta fara ringing cikin sauri na juyo da ita a raina ina adduar Allah yasa Sahibi ne. Se addua ta ta karbu shi dinne yake kira. Na dauka na masa sallama ya amsa yana fadin

“I’m sorry Sahiba, yau dukka ban kira naji yadda kike ba, kema kuma shi ne kika share ni ko?”

Kaina na girgiza kamar yana ganina, lokaci guda naji ina mantawa da abinda ya faru ina jin anya a yadda Sahibi yake zai ajje dakikiyar mata irin Fatima dama tuni naji na raina class din ta, na zata she can’t stoop to the lowest point da zatai haka ba.

“Nasan kana abu ne shiyasa.”

“To ya kike kinyi missing dina?”

“Dole ne ai I’ve to miss you koda minti daya nayi banji muryar ka ba”

Se yayi dariya daga haka muka dan taba hira mostly ta yaran shi ce daga karshe nace masa

“Nikam kayi saving number ta ne?”

“Of course nayi mana na saka miki Sahiba”

Kaina na gyada nace

“Zaka iya deleting?”

“Saboda me?”

Se nace

“Kawai ina son peace ne, idan na maka waya kai deleting a log dinka haka ma message dina!”

“Then dole akwai dalili kenan, me yasa da baki fada haka ba se yanzun”

Se na kasa cewa komai amma ni bana son kai karar matar shi, wannan shi ne karo na farko da tayi hakan ya kamara na mata uzuri, kowacce mace zata iya haka dan ganin ta mallaki abinda take so, amma hakan ba bullewa bane. Ko sallama kirki bamuyi ba ya kashe nima se nayi kwanciya ta kawai nayi bacci.

Washegari wajen karfe uku na yamma ina class naji alamar message, dubawa nayu naga Sahibi ne

Ki same ni inda muke haduwa after your class!

Ban mishi reply ba na cigaba da sauraran karatu na, amma kunsan me kusan rabin hankali na baya class din, yana can wajen shi, ina ayyana me ya kawao shi tunda ko kafin na shiga lecture dinnan seda mukai waya amma bai cemin zai zo ba, kuma munyi agreeing zamu hadu only da weekend banda lectures amma nasan koma menene it’s urgent. Seda nayi har sallar laasar kafin nace da Hibba muje gurin shi daga nan ta wuce gida, haka muka sane shi yana zaune yayi shiru too far daga hayyacin shi, yayi nisa cikin duniyar tunani, sede ina masa magana ya jiyo tare da kalkalo murmushi yayi mana yana fadin

“Aminiyar mu se yau na kara ganin ki kenan”

Ta danyi dariya tace

“Kaga yawancin ai da weekend kake zuwa shiyasa”

“Hakane” ya yadda sannan ya tambaye ta mutanen gida itama ta tambayi yaran shi, daga nan se ta mana sallama ta tafi. Se lokacin na tattara dukkan hankalina na bashi,

“Me ya faru tsakanin ke da Fatima jiya?”

Yadda yayi maganar muryar shi cike da bacin rai. Ni kuma se nayi murmushi saboda na danyi calming dinsa nace

“Shi ne kazo a fusaace haka?” Se Nayi dariya nace “To ka saki fuskarka mana ai ba a haka zan fada maka ba”

Ya jima yana kallona wondering only God knows what, se yayi murmushi yace

“Ki fada min mana”

Hakan yasa nace

“Ta kira ni ta zageni tace na rabu da kai, kai mijin ta ne ita kadai da sauran zancen mata na kishi! Ya akai kasan ta kira”

“Kiyi hakuri kinji , nasan baa kyauta miki ba amma wannan shi ne karo na karshe da hakan zai faru. Da kanta ta fada min ta kiraki, kuma ita bacin ranta me yasa kikai mata shiru. Bakida masaniyyar hukuncin da kika yanke yadda ya kara miki daraja a idanuna. Idan wata ce zata rama zagin confirm, tun da sassafe zata kirani ta fada min amma ke se kika nemo mana solution da kike ganin shi ne zai mana amfani baki daya. Ina son ki sani zuciyata zata cigaba da son ki har zuwa karshe.”

Waye baya son a yabe shi babu shi, so naji dadi kuma haushin Fatima da nake ji se ya kau nayi mata uzuri da soyayyar minjin ta amma ni fa bazan iya zubda girma na nayi hakan ba, matsayina matar shi kadai ya isa ya fadawa budurwar tashi
ni ce gaba da ita.

Bata kara kirana ba, ban kuma kara kawowa akai na zata kirani din ba, saboda a ganina bamu da wani abu daya rage mana, tunda ya riga da yace min sunyi sorting maganar. Kuma ta riga da tasan da magana ta, tunda ta tuhume shi akan me Zaiyi soyayya da wata bai fada mata ba, ya kamata kowa zai kula se da iziinin ta, se yace mata ai ba ita ta haife shi ba dan haka bata isa ba, hakkinta ne ya sanar da ita idan magana ta kankama yadda zata zama cikin shiri amma bawai ta tursasa shi ba ya fada lokacin ni da shi kawai muke abinmu. Da yazo yake cemin+

“Fatima tana gaishe ki, tace wai ayi ayi ayi bikin ita bata son jira”

Na bata rai shi kuma yana ta murmushi yana jin dadin ta saki jikin ta, se nace masa

“Meye matsalar ta dani da zata ce ayi ayi bikin”

Se yayi murmushi yace

“Bata da matsala, tace min ita bata son doguwar soyayya gwara dai ki shigo hankalin ta zaifi kwanciya”

Na fahimci nata salon kishin, wato gwara ace ya aureni akan ace ni budurwar shi se nayi murmushi nace

“Aure kam zaayi shi sede idan Allah bai nufa ba”

“Kamar kina gurin hakan nace mata, ai tayi dana sanin kiranki tace min bata san da gaske auren ki zanyi ba shiyasa”

Kallon shi nayi da mamakin furucin bakin shi nace

“To ka taba yin budurwa ne baka aure ta ba”

In surrender ya daga hannunsa yace
“Ko daya, ni fa tunda na aura Fatima ban kara zuwa gurin wata mace da sunan ina son ta ba balle har nace zan aure ta ba, seke shi yasa hankalin ta ya tashi dan tasan koda ina saurayi banyi yan mata ba.”

A hanakli na saki ajiyar zuciya nace

“To maganar tayi haka, ina fata hakan bazata kara faruwa ba”

“Ba zata kara faruwa ba, kishi ne kawai na mata, dama ba halin ta bane nima bansan ya akai tayi haka ba”

Tabe baki nayi nace

“Ai baka sanin true image din mace se zakai aure, a lokacin duk wasu locked characters dinta zasu bude ta fito da ainahin halinta.”

Se yayi shiru dan baida abin cewa kuma yasan gaskiya na fada, nace
“Ni banida tashin hankali, ko sau daya ban taba jin haushin taba, ni nasan inada fada amma se an taba ni, dana hadu da kai nasan tunda kana da mata dole nayi adjusting sabida zaman lafiya amma ka sani bazan taba tsayawa matar ka ta takani ba, tayi kadan bata isa ba!”

“Haba Nanah inace maganar ta wuce?”

“Of course ta wuce amma ina fada maka ne.”
Saboda na gaji da topic din gaba daya, anything to do with her bana bukatar shi, a hankali zuciyata ta fara developing kishi da ita saboda yanzun na san son Sahibi nake tsakani da Allah. Na kanyi tunanin se ace Sahibi ya yaudare ni! Tashin hankali kenan na ayyana a raina, na kance kashe shi kawai zanyi yadda zan bawa wasu mazan insight din yaudara ba abu bace me kyau, wani lokacin kuma se nace to idan wani natural cause yazo ya raba mu fa? Tunanin wannan se na shiga bargo saboda haka kawai se naji na fara shivering ina neman shidewa. Son shi nake with all my being, kaunar shi nake with all my might!

Wayar shi ce tayi kara wadda yasa ni dawowa hayyacina, seda yayi excusing kansa kafin ya dauka call din, it’s something business ya gama discussing kafin ya aje yace min

“Zan samu 10000 cash a gurinki?”

Shiru nayi ina lissafin kudi na na hostel amma bazai kai ba se kawai nace

STORY CONTINUES BELOW
“Se muyi amfani da atm dina, kudin bai kai ba”

Shiru yayi na wani lokaci sannan ya dauki wayar shi yayi dialing tareda karawa kunnen shi, baa jima ba naji yace

“Kin dawo gida?….ok! Akan bedside drawer na bar wayata da wallet dita, ki buda salisu zai zo ki bashi 10000…..nace miki na fita bana kusa…..Fatima wayake auren wani ni dake?……idan na dawo mayi maganar”

Hanging yayi sannan yayi dialing number salisu yace yaje gidan shi ya karba kawai, duk abinda suke ina jin shi amma se nake danna wayata kamar bana jin abinda suke fada.

A hankali rayuwa ta cigaba da tafiya, kwanakin na shudewa suna komawa sattittika haka suma suke juyawa suna komawa shekara, with every passing second ji nakeyi tamkar zuciyata kara rura son Sahibi ake a cikin ta. Kullum rana soyayyar kara karfi take and i always wonder dama haka kowacce mace keji ko kuma ni kadai nake Dan dana wannan zazzakar ZUMAr? Idan kuwa har ni daya ce to tabbas zance mutane da dama sunyi missing.

A lokacin na shiga level mun koma university campus na cikin akth, lokacin karatun ya fara gangarawa amma kuma the higher we go the hotter it gets, amma duk da haka bana taba barin space a tsakanin mu, inata maintaining relationship dinmu haka shima a nashi bangaren. Na fahimci soyayya ba kyauta bace, bawai ayi ta showering dinka da materialistic abubuwa bane, aa rai na son me kyautata masa, sede mu bamu gina tamu kaunar akan hakan ba, mun gina shi akan fahimtar juna dan ko a lokacin na aure shi abu kadan ne ban gama sani akan shi ba, he’s too open, he’s accommodative, zuciyar shi me girma ce shiyasa nake kara son shi a koda yaushe. He has always been a support cikin rayuwata, ban taba fada masa matsala ta ba baiyi min sorting ba, harta yan gidan mu sonshi suke basu son jin laifin shi, ko mun danyi fada se sun shirya mu dukda yawanci ni nake zuciyar shi sede yace min yarinta na damu na. Na hadu da maza kalakala amma duk wanda ya fara nuna interest dinsa a kaina zan taka masa burki, a ganina bazan taba iya hada soyayyar Sahibi da ta wani ba, bazan iya accepting wani ba not when Sahibi na da rai!

Ranar monday early na tashi na shirya dan tafiya class, na riga da na fara project dina so zanje zan kaiwa supervisor dina chapter one. Na fito ina kokarin kiran Sahibi amma wayar taki shiga kawai se na maida kiran kan Hibba, tace min tana shigowa itama. Class na wuce na zauna inata kara dubawa saboda mutumin is very strict kuma bana son a samu matsala dani. Se wajen 2pm na samu naje na kai masa yace na tura masa softcopy cikin mail dinsa zai duba sannan na aje hardcopy zai neme ni. Ajiyar zuciya na sauke na fita lokacin Hibba ta fito daga office din nata, ranta a bace ta fito tana ta kumburi tace min ya mata rashin mutunci, na bata baki sannan muka tafi hostel. Zama nayi kan gado ina stretching kafata nace

“Hibbatu….”

Ban karasa ba naji wayata na ringing se na dauka amma se naga restricted number, tun dazun ake kirana da ita, se kawai na dauka
“Fatima!”

Aka kirana suna na, se nayi shiru ban amsa ba tunda kadan suka san asalin sunana kuma ma ni fadima nike

“Ko bake bace?”

Aka katse ni, se nace

“Ni ce, waye?”

“Bakiji warning din da nayi miki ba ko? Bakiji abinda na fada miki akan tarrayyar ki da mijina ba ko? To bari na fada miki idan karywanci kike ji kije can kiyi abin ki amma mijina yafi karfin ki, ni matarsa ce ni kadai jaka jahila dabba kawai.!”

Kafin na bude baki nayi magana tuni ta kashe wayar, wanu irin bakin ciki naji ya tokare min kirjina, cikin sauri na fara kokarin returning call din, na manta restricted numbers baa iya kiran su, ganin hakan raina ya kara baci Hibba ta dafa ni tace

“Menene? Me ya faru?”

Kawai se na fara kuka ina fada mata
“Matar Aliyu ce ta kirani ta zageni”

“Shi ne kike kuka? Ke naki shashan cin kenan? Haka zaki kwaci kanki!”

Nima bansan me yasa nake kukan ba amma inaga saboda ban rama ba shiyasa, Hibba ta dinga min masifa har taji haushi ta kyaleni. Seda na hakura dan kaina sannan na wanke fuskata na kwanta se bacci yayi gaba dani. Ina farkawa kiran Sahibi ya fara shigowa na riga na gama deciding abinda zanyi, Hibba ta riga da ta tafi gida. Dauka nayi ko gaisawa bamuyi ba

“Turo min number Fatima!”

“Sahiba are you there?”

Se naji shima haushin shi nake ji musamman da yace min Sa
hiba ji nayi kamar ya daba min wuka a kirjina, raina ya kara baci nace

“Baka ji ba, nace ka turon number Fatima”

“Nanah wacce Fatima kike nufi”

“Matar ka!”

Na fada a harzuke, se yayi shiru bai cemin komai ba ni kuma inata huci, se can yace

“Kiyi hakuri Fadima, fada min me ya faru?”

“She called me, ta zageni tace min karuwa, this time around na gaji da hakuri kawai ka turo min number dinta nima se na rama zagin da tayi min!”

Inajin hucin da yake fitarww ta wayar, muryar shi sounding broke yace min

“Ba halin ki bane kinaji? Kiyi hakuri nasan bata kyauta ba amma bana son ki biyeta kuyi fada, ki bari ni zanyi handling issue dinnan”

Kaina na girgiza nace

“Nifa idan ban rama ba zuciyata baza taba min dadi ba, gwara ka barni kawai na rama”

Baice komai ba se ya kashe wayar na cigaba da ayyana irin zagin da zan musu shi da ita, nayi ta kiran shi yaki dauka nanma se laifin nasu ya karu akan nada!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *