ZUMA CHAPTER 9 BY SHATUUU
Gabana nata faduwa na fita zuwa inda nasan tabbas zan same shi, inda kamar ance dole dole wajen zamu dinga zama muyi hira. Saboda gurin akwai haske saboda security light din yasa tun daga nesa na hango shi ya tsareni da idanu yana kallona, se naji yau idanun nashi sunfi kaifi akan ko yaushe, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da yatsuna a haka ina tafe har na karasa. For some unknown reason se naji mun zama tamkar wasu strangers, kamar ranar ne haduwar mu ta farko dashi, na tsaya naki zama kuma na kasa daga idanuna na kalle shi balle nayi magana. Ajiyar zuciya ya sauke yace+
“Sahiba kinyi shiru, it’s been long ma da naji muryar ki. Talk to me!”
A hankali se naji hawaye sun fara gangaro min kan kuncina, se naji maganar tashi tayi min fami, ban sani ba ko a cikin ku akwai wanda ya taba jin ciwo gurin ya fara warkewa kuma kawai se aka daye fatar aka kara maida gurin sabo, to wannan zafin haka na jishi cikin zuciyata. Bai lura da hawayen da nake ba sede ya damu sosae da rashin maganata, can yace
“To Sahiba ki koma tunda naga you are not ready for us to talk”
Hannuna nasa na goge fuskata amma kamar tuttudo hawayen ake, se naga ya mike da sauri da alamun ya lura da kukan da nake, gabana ya karaso fuskar shi cikin tsananin damuwa wadda ban taba gani ba hakan se ya kara karyar dani, se sautun kukan ya fara fitowa.
“Sahiba kiyi hakuri kinji? Wannan ita ce rayuwar da Allah ya tsara mana, may be dama we were not meant to be…”
Nayi mamakin maganar shi, kenan yana nufin ya hakura dani kenan? To banda abu na shima ya zaiyi? Dukkan mu hakuri zamuyi, amma fa daga baya nayi wannan karatun a lokacin i was so desperate nace masa
“I can’t live idan muka rabu, bazan iya cigaba da rayuwa ba sahibi!”
Duk lokacin da na tuna ni na fada wannan abin se nayi dariya, hmmm that’s then dole na fada haka.
“Sahiba ya isa kukan haka kada wani yace na miki wani abun ne”
Ko sauraron shi banyi ba kawai na nufi hostel fuskata dunkukune cikin karamin veil din dana yafa a kaina, gado na na fada ina kara sakin kuka me ciwo and God so kind babu wanda na hadu dashi. Babu wani a gurin balle ya lallashe ni ko kuma ya bani baki tun ina yi ina jin sanyi a raina har na dawo ina jin kaina kamar zai cire, bansan lokacin dana dauka ina kuka ba. A hankali kuma nayi shiru naje na wanke fuskata na dawo na kwanata a lokacin na nutsu ina kuma bukatar nayi tunani se kiran Aliyu ya shigo ya katse min hanzari. Bazan iya kallon wannan kiran na share ba dole se na dauka haka kuwa nayi swiping da karamin yatsa na na kara a kunne na.
“Kin daina kukan? I know you are hurt, tuna zafin da kike ji shi ke kara tada min hankali Sahiba, ki daure Kiyi hakuri dama haka rayuwar take ba komai kake so kake samu ba, wasu abubuwan Allah na hana mu ko dai dan ba alkhairi bane ko kum dan ya jarabce mu.”
Maganar shi se ta fara tasiri a kai na, na fara tuhumar kaina akan kukan me nake? Ina son yin fito na fito da abunda Allah ya rubuta min, na shiga saka meye Aliyu what’s so special about him, shima dai he’s an ordinary person kamar dukkan mazan da nake gani a titi, but amma a kasan zuciyata haushin kaina nake ji da nake gwada Aliyu da sauran maza, kasancewar shi na daban shi ne dalilin son da nake masa idanu rufe bana ji bana gani, son da nake masa yasa na rika shanye duk zagin da Fatima tayi min, for me saboda ina son shi!
“Zuciyata zafi take min Sahibi, ji nake kirjina yayi nauyi”
Na fada ina goge hawayena, muryar shi a hankali yace
STORY CONTINUES BELOW
“Zata daina yanzun kije kiyi alwala zan kiraki”
Haka na mike na nufi toilet nayi alwala sannan na dawo na samu kaina da yin nafila rakaa biyu nayi addua wadda ta zama kullum akan harshe na take akan Allah ya dube ni ya zaba min mafi alkhairi.
Washegari na tashi da asuba nayi sallah, ina zaune kan sallaya ban tashi ba se gyangyadi da nake yi dukda da dare nayi bacci, bacci sosae nayi dan ni idan ina bacci my problems are kept aside se na tashi sannan na dakko su. Wayata ce ta katse min tunanin da nake ciki, nasan waye ko ban duba ba nasan Sahibi ne jin ringtone din dake playing. Hannuna na mika na dakko, muryar shi a sarke tayi kasa sosae ya amsa min gaisuwar da nayi masa, bayan nan se mukai shiru ni ina tunanin me yasa ya kira tunda jiya da daddare ya nuna min mu hakura shi ne solution, amma gashi yanzun ya fara kira.
“Nanah kin iya yin bacci daren jiya?”
Kaina na gyada masa kamar yana gefe na nace
“Nayi Alhmdllh!”
Muryar shi cikeda tausayi yace
“How i wish zan iya yin kuka Nanah, na tabbatar idan nayi zanji saukin radaddin dake cikin zuciyata, gashi ke kin iya yin bacci”
Ban ce masa komai ba sede tausayin kaina da shi sun lullube ni, ta yaya a wannan dimbin son da muke ma juna zamu iya nisantar kanmu har ma kuma mu yanke alaka? Ina ganin hakan bazai faru ba
“Nanah, bayan nayi tunani sosae da daddare naga tabbas bazan iya hakura ba, zuciyata ji nake kamar is ripped apart, bazan iya jure rashin ki ba”
Idanuna na lumshe ina kara jin bugun da zuciyata take yi sede na kasa tantance farin ciki nake ko a kasin hakan,
“Kina ganin akwai wani wanda yake uncle din ki ko abokin Daddy wanda zai iya yiwa Daddy bayanin ya kamata muyi aure”
Anzo gurin! Dan ni dai a iya sanina babu wani da Daddy yake jin kunya ko kuma zai ma barshi ya shigo masa sabgar gida, in fact ban taba ganin abokin Daddy a gidan mu ba, sede su tsaya a waje ko kuma a office shikenan.
“Sahibi ban gan shi ba duk duniya, mu a iya rayuwar mu Daddy kadai muka sani shi ne kadai baban mu, sede abinda zan ce kawai muyi addua Allah ya zaba mana mafi alkhairi”
“Kema kin ce wani abu, so muyi addua Allah ya duba niyyar mu ya zaba mana mafi alkhairi! Ina sonki sosae son da nima ban san iyakar shi, may be kice it’s old fashioned zama kana using kalamai wajen bayyana son da kake ma mace, ni a yau zan fada miki. Tunda nake a rayuwata ban taba jin abinda naji akan ki ba, from the very first second da idanuna suka sauka akan ki har abada i will continue to love you and protect you, bana tunanin ko Fatima nayi mata irin wannan son, ke kadai ce wadda ta shammace ni lokaci daya”
“Sahiba a son da nake miki babu wani manufa marar kyau cikin zuciyata, ina sonki ina son na aureki dan ki zama wani bangare na rayuwa ta sede Allah shi yasan daidai, bazan so dalilin hakan ki samu matsala da Daddy ba, I’m not here to cause you harm ko wani confusion a rayuwar ki. So mu jira lokacin da Daddy zaiji ya yadda dani matsayin sirikin shi semuyi aure, know that zan jira ki kowanne lokaci ne!”
Daga haka muka maida wannan problem din gefe guda muka bude sabon babin relationship, se nake ganin kamar bayan abinda ya faru kamar kara shakuwa muke day by day. Bayan sati daya da faruwar abin hankalina ya kwanta, koke koken da nakeyi duk na daina tunda dama saboda shi nake kukan to kuma tunda muna tare zance ya kare. Muna tareda Hibba bayan mun gama lectures tace min
“Babe ina Aliyu ne?”
Dan yatsina fuska nayi nace
“Yana nan a ind
a yake”
“To ke kin hakura kenan?”
Kaina na girgiza nace
“Kinga ina son rabuwa dashi wallahi, amma zuciyata taki bani dama. Ko yini yayi bai kirani ba Hibba ji nake kamar zanyi hauka!”
Murmushi tayi tace
“Iyeeeee! Nanah masoya yanzun Kin fahimci dalilin da yasa mutane ke zaucewa ko?”
Kaina na gyada tareda gyara zama na, nace
“Hibba na fahimta sosae, kinsan a yanzun dana son menene so nasan komai akan shi ina jin banga laifin matan da suke guduwa su bar gida ba, indai haka zafin separation yake to Hibba ko me kayi akan so worth it!”
Hibba ta fara dariya harda wani drop na hawaye saboda mugunta tace min
“Allah mutuniyar!”
Tsaki na mata na cigaba da wata sabgar, tana dariyar tace
“Ok I’m sorry, ni a ganina kada ki rabu dashi ku cigaba da dating kilan watarana se kiga Allah yayi kunyi aure kinga love story ku is spiced up ko”
Na kalleta nace
“Daddy fa?”
“Kada ki damu da Daddy kede Kiyi addua kawai”
A haka rayuwa ta cigaba da tafiya har kwanaki suka shude abubuwa suna ta tafiya wasu yadda kake so wasu kuma akasin haka. A wannan lokacin nayi ibada bata wasa ba, na kai ma Allah kuka na ba kadan ba nidai kullum addua ta Allah yasa idan babu aure tsakanin mu to mu rabu, idan kuma akwai aure Allah ya fahimtar da Daddy ya amince muyi aure, kullum addua nake amma kullum kara son Aliyu nake seda takai ta kawo bana cikakken mintina biyar ban tuna dashi ba, idan ko hakan ta faru to tabbas bacci nake, nayi ta imagining munyi aure muna tafiyar da rayuwar mu cikin kwanciyar hankali da soyayya.Ranar Thursday, ita ce ranar dana kammalla final exams dita cikin BUK, paper safe ce so wajen karfe goma mun gama mun fito, muna tsatsaye gaban hall din se pictures muke yi wanda muka dan kara sabawa dasu muna exchanging contacts da social media handles. Wajen sha daya Hibba taja hannuna mukai sallama da sauran muka nufi hostel dan na kara tattara kayana saboda Daddy yace min se wajen 2 zasu daukata. Muna dab da karasawa hostel naji ringing din wayata , da sauri na ciro wayar ina sakin murmushi me kayatarwa, banma dauka ba se wulla idanuna da nake across gurin dan nasan zuwa yayi shiyasa yake kirana. Can na hango shi jikin wata bishiya tsaye ya kara wayar shi a kunnen shi, from all indications bai ma hango ni ba, kallon Hibba nayi dake cemin na daga wayar ita karar ta dame ta, nace+
“Kinga Sahibi ne yazo muje gashi can”1
Tabe baki tayi tace
“Kauna jaraba”
And i smiled saboda nasan gaskiya ne abinda ta fada, ni kaina ina yawan mamakin wannan kaunar dake tsakanin mu, kullum ina cikin ayyana ya kamata na rabu dashi kodan Daddy amma kullum we’re getting more and more closer to each other. Wajen shi muka nufa har lokacin bai lura damu ba seda muka zo gab dashi sannan ya dago ya kalleni ya sakar min murmushi nima banyi wata wata ba na mayar masa da martani wanda seda ya lumshe idanun shi. Hibba suka fara gaisawa sannan nima na gaishe shi ya amsa mana yana mana murna tareda mana adduar clearing dukkan papers dinmu.
“Hibba biki ya matso ko?”
Murmushi tayi tana dan kawar da kanta irin najin kunya dinnan. Se ni nace masa
“Two weeks kawai ya rage”
Kanshi ya gyada yace
“Allah ya sanya alkhairi, saura a manta dani baa gayuace ni ba”
Wanann karon tace
“Kai! Zaa gayyace ka ma, su waye a gaba idan ba hanci ba”
Dariya sosae yayi jin abinda ta fada, daga karshe ya mika mata wata katuwar paper bag dake gefen shi wadda ni banma lura da ita ba se yanzun. Godiya ta masa ta wice hostel ta barmu muna ta hira, ko daga nesa ka hango ni kasan ina cikin madaukakin farin ciki, nidai a rayuwata babu wani mood turner irin kasancewa ta dashi, ko na ayyana nayi aure indai na hassaso wani namijin se inga kwata kwata he doesn’t fit indai ban hasaso sahibi ba, se giggling nake. Akwai abinda ni kaina a tarrayyata da Sahibi dake bani mamaki, deep down cikin raina nasan ba auren shi zanyi ba, saboda nasan Daddy is man of his word, he meant dukkan abinda ya fada, amma na rasa dalilin da yasa nake kula shi, na take dukkan maganar da Daddy yayi min akan shi.
“Idan kika tafi se yaushe zamu kara haduwa kuma?”
Se na danyi jim dan nasan yanzun ba lalle mu kara haduwa ba tunda gashi zan bar kano na koma dutse baki daya.
“I dunno buh ai zan zo bikin Hibba zamu hadu lokacin”
Cikeda gamsuwa ya gyada kanshi se muka kara fadawa cikin hira wadda ta mantar dani cewar Daddy yana hanya zai zo dauka na, Hibba na daki itama tana jirana, gashi nayi kuskuren bata wayata ta tafi da ita, da at least ko da yazo zai kirani. Can naji hankalina yaki kwanciya se ina jin kamar one person da bana fatan ya ganni tsaye da Aliyu na tsaye yana kallona, cikin sauri na juya, Daddy na hango tsaye jikin motar shi ya zuba mana idanun shi masu kaifi, a take naji yawun baki na ya kafe haka kuma ilaharin jikina ya dauki rawa, and I know it cewar attack zan samu, hannuna na damke inajin yadda zuciyata ke bugawa numfashi na yana kokarin ficewa haka gumi ya min shrkaaf, Aliyu da bai lura da tsayiwar daddy ba dukda cewar shi ke facing Daddy din.
“Sahiba menene? Subhannallah!”
Ya fada hankalin shi a tsananin tashe, idanuna sun firfito waje kamar zasu fadi saboda yadda numfashi na ke kai kawo, Cikin sauri Daddy ya karaso gurin tareda kama ni na zauna sannan yace
“Take a deep breath dear”
Hannun shi na matse sosae sannan naja dogon numfashi a hankali se jikina ya fara daidaita har na dawo normal, sannan na saki hannun Daddy ina gaishe shi, Aliyu shima ya gaishe shi ya amsa normal sannan ya mana sallama ya tafi, na dubi Daddy wanda ke waya da Doctor daya taba duba ni yana ce masa na kara samun attack din, se yace masa yana jin tsoron kada ya zame min jiki dan repeated episode na panic attack yana komawa panic disorder.
Bai ce min komai ba naje hostel na dakko kayana muka fito da Hibba dake ta kokarin nuna min babu abinda Daddy zai min tunda kowa yasan menene soyayya kuma dole ayiwa wanda yake cikin ta uzuri, amma ina ni duk hankalina a tashe yake, ko sallamar kirki bamuyi ba ta gaida Daddy muka nufi dutse, saboda tsoron kada yace min komai na lumshe idanuna kamar bacci nake shima se ya maida hankalin shi akan wayar shi, time to time na kanji ya amsa kira.
Muna isa gida na manta ma abinda ya faru saboda yadda na samu su Amal an shirya min wani dan karamin get together hatta dasu Mom su Anty Sumayya duk suna gida da yaran su, Daddy ma ya shigo cikin mu yana ta taya ni murna amma duk lokacin da muka hada idanu da Daddy se naji kamar wani panic attack din zai so, a haka dai muka gama muka ci abinci sannan mukai picture na karba gift dina.
Da daddare Sahibi ya kirani, ina kallon kiran nashi na kasa dauka, se fargabar haduwata da Daddy da nake, mikewa nayi na ciciro gift dina ina dubawa, se naji hawaye ya sulalo min saboda yadda kowa ya tsara words jikin greeting card din da aka hada min a gift, na dudduba sauran sannan na dakko ta Aliyu abubuwa da yawa a ciki mostly perfs ne designers, tattarawa nayi na aje a gefe na fada duniyar tunani, anan kiran Daddy ya shigo wayata, saboda yadda gabana ya fadi kadan ne ban fado a gadon ba, kamar bazan dauka ba haka nayi amma ya zanyi dole dole haka na dauka.
“Ina parlor ki sameni yanzun!”
Se ya kashe wayar jikina a sanyaye na mike na saka abaya saman kayan jikina na fita, yana zaune akan sofa yana kallon network news, zama nayi bayan ya bani izini tun kafin yayi magana nce
“Daddy kayi hakuri dan Allah”
Kallona ya tsaya yana yi sannan yace
“So baku rabu dashi ba all this while? Nanah nayi tunanin idan nace ki bar abu ko meye zaki bari”
“Daddy wallahi it was a mistake kayi hakuri”
“Kina ganin ban miki adalci ba? Saurin me kike ? Saboda Amina zatayi aure ta barki gida….”
Na tsani
wannan maganar nifa bawai aure nake so ba, ni Aliyu nake so kuma son shi ya fara kissima min nayi aure, a matsayina na yayar Aminatu dole tayi aure banyi ba zanji babu dadi tunda a society da muke hakan ma kamar wani kasawa ce daga bangaren ka ko kuma irin abominations ne.
“…Aure lokaci ne Nanah idan yazo ban isa na hana kiba, nasan kina cikin So shiyasa, but ina son kiyi amfani da kwakwalawar ki, duk matar da zata fito daga gidan ta ta taho uwa duniya dan tayi warning akan mijin ta ba tareda sanin shi ba to tafi karfin shi, bai isa da gidan shi ba, kina ganin saboda son da kike masa zai saka nayi trading dinki for that, bazan iya aura miki shi ba, aure is not a one year pleasure, it’s staying with a single soul for eternity, waking up and looking at that face, it’s beyond duk tunanin ki Nanah. Ina son kiyi hakuri kiyi addua nima as your father ina yi miki!”
Hannuna na damke ina maida numfashi, amma na kasa cewa Daddy komai se na tashi na koma dakina, ina jin hirarrakin su a parlo amma ko lekawa banyi ba saboda i wasn’t in the mood, kwanciya nayi ina jin ringing din wayata, amma na kasa dauka.+
Washegari bayan na idar da sallar asuba na dakko wayata ina going through call log dina, missed calls yawanci na Hibba ne da Aliyu, kifar da wayar nayi ina jan carbin hannuna dan na samu saukin zuciyata, wanka nayi na fito tsakar gida naga tarin wanke wanken da aka tara, saboda get together da mukai jiya, sleeve din rigata na tattare na fara aiki duk dan na dauke hankalina daga tunanin da nake, amma hakan ya gagara, abubuwan se kara yawo suke min a kaina, a haka inata making decision har na kammalla wanke wanken nazo na share terrazzo dake shimfide a tsakar gidan mu, na kammalla sannan na wanke tas, aje tsintsiyar hannuna nayi a gefe tareda shakar iska me sanyi ina kuma jin yadda take kewaye dukkan jikina. Daki na wuce na dauki wayata cikin sauri dan na fada masa hukuncin da na riga na yanke, i felt heartbroken lokacin da wayar ta fara ringing alamar wayar ta shiga, idanuna suka cicciko da kwalla amma ko kadan se naji sabida Daddy ya kamata na juri dukkan wani kunci da zuciyata zata shiga. Kamar yasan me zan fada masa se bai dauka ba haka na zauna gefen gado ina jiran kiranshi amma har na fara jin muryoyin mutanen gidan suna fitowa kowa yana yaba min kokarin aikin da nayi, Anty hauwa ta shigo tana kare min kallo tace
“Ke lafiyar ki kuwa? Ya naga kinyi zuru zuru?”
Kaina na girgiza nace
“Babu komai, ina kwana?”
“Lafiya lau Nanah, na zata zaki huta keda kika gama exams”
Dan murmushi kawai nayi na mike nace mata zanyi wanka sannan na aje wayar na shiga wanka, seda na fito sannan na tadda missed call dinsa guda uku, zama nayi sannan na fara returning call din shi, se ya katse ya kirani, muryar shi dake sanyaya min jiki duk lokacin da muka samu matsala, a muryar shi nake fara jin akwai matsala.
“Sahiba a soyayya precisely fadin gaskiya shi ne komai! Ya zan dinga kiran ki amma baki dauka ba at least talk to me mana.”
“Nasan ban kyauta ba kayi hakuri, ina neman alfarma a gurin ka dan Allah muyi quitting relationship dinnan…..”
“Nanah! Kin san me kike fada kuwa? Kinsan me kike cewa kuwa? Muyi quitting relationship kike cewa fa?”
Ina lumshe idanuna hawayen suka gangaro, wai haka soyayya take? Kowa haka yaci wannan dacin a zuciyar shi? Na shiga uku se yaushe zan daina wannan kukan da nake, tun ranar da Fatima ta fara kirana nake ganin aka bude sabon babin kaddara na cikin rayuwata, a farkon soyayyar mu gani nake ZUMA nake dandana me zakin gaske amma a halin da nake ciki da radadin da nake ji cikin zuciyata da ruhi na na tabbatar kudan zuma ke min dalli son ranshi, kuma dallin a guri daya kawai akeyi not minding gurin ya huce daga zugin ko akasin hakan.
“Nasan me nake cewa, ina ganin hakan zaifi mana sauki, saboda…”
“Ba zaki iya jira kiga abinda Allah zaiyi ba kenan? Kin gaji kenan”
Cikeda kosawa nace
“Ba haka bane kasan cewar nafi kowa mafarkin ganin na zama matar ka, to ya zanyi da kaddara dake neman datse alakar tamu, ya zanyi banida wani option dole zanyiwa Daddy biyayya!”
Kawai se naji yayi kit ya kashe wayar, na ciro wayar cikeda dimbin mamaki ina jujjuya wayar a hannuna, se kawai na share hawayena na mike na aje wayar hakan, ya kamata na hakura hakanan, ya kamata na kyalle Aliyu haka, abin ya isheni haka nan.
Wanke fuskata na kuma yi na shafa lotion jikina na saka kaya dan tunda na fito daga wanka nake zaune bakin gado, shiryawa nayi na fito na shiga cikin yan uwana dake shirin komawa gidajensu , nayi kokari sosae wajen ganin na boye damuwata, se ya zamana hirar duk ta shirin bikin su yaya Mariya ne, na dakko kayan da na karbo wajen tailor din, aka zauna aka bude kowacce cikin su ta gwada nata kuma bai bani kunya ba kayan sunyi, ninkewa nayi na dakko katon trolley na ninke na zuba a ciki, muka fito da su clutch dinsu da takalma dasu jewelries komai muka hada sannan muka tashi muka raka su suka tafi.
Bayan maghrib na gama hada dinner Aminatu da yaya mariya na tafasa musu maganin su na juye cikin bath sannan na koma daki, wayata na dauka na duba se naga message din Aliyu
“Nagode sosae da kika ce haka, ko kadan banyi niyyar rabuwa dake ba amma tunda kinyi insisting se mun rabu, ina miki fatan alkhairi amma ki sani kin yaudareni kuma nagode amma kin cuce ni!”
Na kalla na karanta, na kara na nanata na kuma nanatawa, gaba daya kaina ya kunce ina ayyana gaskiya bashi ya turo min wannan sakon ba, kawai se nayi dialing numbers din shi dan naji tabbacin abin, he picked up nace a sanyaye
“Sahibi me message din ka ke nufi?”
“Abinda idon ki ya gani”
“I just want you to say it da bakin ka”
Na fada calmly, ko so yake ya tunzura ni kawai seya rufe ni da masifa ya kara maimaita min abinda na riga na karanta a text dinsa, raina a bace nace
“Ni ban yaudare ka ba, Allah ya sani, dakikiyar matar ka ita ta ja komai, ita ya kamata kayi blaming bani ba, Allah ya sani na soka son da nayi maka tsakani da Allah banida wani buri daya wuce auren ka, bansan hallacin da nayi maka naki bin maganar Daddy will lead….”
Se naji ya katse ni da fadin
“Ya isheni haka, karki kara tunawa someone like me yayi dating dinki”
Daga haka ya kashe wayar shi, na rasa ina zan saka zuciyata naji sanyi, na rasa me zance wa zan fadawa, kukan gaba daya ya tafi bana jin i can shed more tears akan wanda baiyi deserving. Se na mike na koma kitchen na tarar Amal tana karasa sauce din dana bar mata tayi, A’isha na hadawa Daddy ganye, seda muka kammalla na dauki tray din na tafi gurin Daddy, na samu sauran suna zaune suna hira, ina zama aka fara maganar furniture da akai order akan wani week zasu zo, se na dan ware muna ta maganar da kudin komai da Daddy zai saka account dina na hidimar bikin, kai ka rantse ni na haife su, dan shirin bikin ni ce akan gaba komai se an fada min. Se wajen goma mukai sallama zamu tafi mu kwanta, har mun kai kofa yace
“Nanah zo!”
Komawa nayi na zauna ina jin yadda gabana yake faduwa bansan this time me zai ce ba, ga mamakina se naji yace
“Nanah are you ok?”
Kawai se na fara kuka, kowa yasan are you ok tambaya ce da wanda suke cikin halin kunci suke avoiding, saboda ita sede ta kara tada maka hankali,
“Subhannallah! Menene kuma?”
“Daddy dan Allah ka barni naga Mom dina, dan Allah dan annabi”
Na fada ina kuka sosae tareda hade hannuna guri daya alamar riko, shiru yayi treda tsira min idanu, da gaske kenan zan nemi uwata ya ayyana a ranshi, a nashi ganin bazan taba nemanta ba tunda bansan dadin ta ba, amma kar ya manta dukda ban kwanta jikin ta na kwanta cikin ta, it’s nature and no one can cheat nature! Bai ce
komai ba seda nayi kuka sosae har abinda Aliyu yayi min ya fara disashewa a raina kafin na rage kukan se hawaye da suke dan zuba kadan kadan a kuncina.
“Fadima kiyi hakuri komai da kike gani lokaci ne, very soon zaki je gurin A’isha, amma ni bani zan kaiki gurin ta ba, da kanki zaki je idan lokacin yayi. Bana son ki takurawa kanki akwai abinda nake jira, i sworn se kin samu abubuwan kafin kije gare ta, yanzun kin hada 75% na abubuwan da nake bukata, saura the most important one, ki na samu da kaina zan daura ki hanya kije”
Se na kara sakin kuka, menene wannan abin se kace wani quest? Ko kuma puzzle ko adventure ne da zaa ce se nayi defeating zaki kafin naje gareta, kwana biyunnan mafarkin ta nake sosae dukda bana ganin fuskarta amma a mafarkin uwata ce, ga wannan mental breakdown da nake ciki.
“Daddy kar ta mutu ko na mutu bamu hadu ba, Daddy dan Allah kayi hakuri naje”
Shafa kaina yayi yace
“Kiyi hakuri zakije, kuma ina tabbatar miki A’isha is safe and sound babu abinda zai sameta, lokaci nake jira”
Ganin magi yata da wani abu na bazai saka ya yarda ba yasa na hakura na fawwalllawa Allah, amma naji gaba daya diniyar ta isheni, ko ina a jikina radadi yake min. Haka na cigaba da shirin bikin Hibba da kuma nasu Aminatu.