ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir
da ‘yammata, ko saka wando ga wasu matan Hausawa duka abin kallo da waiwaye ne a gare mu kafin mu saba.
Mu kam bamu saba gani ba a inda muka taso, don haka muka shiga dari-dari. Sannu a hankali idonmu ya zo ya bude tangarau muka fahimci (reality) na rayuwar jami’a ba (peer group infuluence) bane (koyo abokan karatu ko tsararraki) kawai (imitation) ne wato (kwaikwayo) ‘to fit together’ (a zama iri daya).
Akwai wadanda karatu ne ya kawo su ba (imbibing) wato kwaikwayon abubuwan da canjin zamani ya kawo ba. Akwai kuma ‘yan ‘imitation’ din ko da a ce ransu bai so don kar a ce musu kauyawa. Irin wadannan su nake gani a matsayin kauyawa ba wadanda suka kalla a kauyawan ba. Su kuma ina kallon su ‘yan ra’ayin rikau. Irin wadannan mutanen a duk inda suka tsinci kansu basa canza ‘doctrines and principles’ dinsu kuma da wuya a rinjaye su daga kan abin da suka riga suka yarda da shi.
Yau bamu fito lacca da wuri ba sai wurin karfe biyu na rana, in ban da kururuwa ba abin da cikina ke yi, don ko karin kumallo ban dauka ba. Babu yadda Yaya Rabi ba ta yi dani ba don in zauna in karya amma na ki, saboda sanin halayyar Dr. Ramadhan Alkali, muddin ya riga ka shiga aji to ka rasa laccar sa kenan. Ni kuma ba zan so in rasa laccar ba, don a cikinta ne zai fadi (exam concentration area) din kwas dinsa.
Tafe nake a hanzarce don kokarin isa ga ‘coke village’ in samu abin da zai warware min hanji.
Idanuwana sun rufe saboda yunwa ban kula da budurwar dake tsugune tana goge takalminta da ya yi kura da tishu don ganina ya dushe tsabar yunwar dake addabata, muka yi karon ba zato da budurwar saura kadan ta kifa.
Ta mike a hanzarce za ta yi bala’i. Wa zan gani? Haulatu Shehu, kawarmu (Head-Girl) a Queen Ameena, Haulatu S. Shehu. Na ce, “Haulatu Sani?”
Ta ce, “Fa’izah Ahmad?’
Na ce, “Ya Jamilal Munzar! (wato ya mafi kyawun masu gani)” A guje muka sheka muka rungume juna tare da juyi rikija-rikija muka rankaya coke village tare. Hirarraki da tambayoyi tamkar su kashe mu. Kamin wannan ta kai aya wannan ta antayo tata tambayar.
Ta ce, “Fa’izah kuna cikin garin Kano amma ko ki neme ni?”
Na ce, “Ayya Haulatu, ban san gidanku ba, kin ganni nan bayan unguwar su Aunty Rabi Gadon Kaya (Yarda Avenue) ban san ko ina ba, ban da kantuna da muke zuwa sayayya”’.
Ta ce, “Ina address din da na baku tun muna makaranta da phone no?”
Na ce, “Mun baro su cikin littafinmu a Giwa”. Daga nan hira ta barke. Ta ce, “Lallai ne Ubangijinmu ke nufin mu da zumunci tunda har ya sake hadamu a nan. Allah abin godiya. Ina Ummi?” Na ce, “Ummi tana makarantar nan ita ma a Hausa Department”.
Ta ce, “Ni ina Mass-Communication, kai ni Haulatu na zo jami’a a sa’a tunda na kara haduwa
ku. Tun rabuwarmu babu ranar Allah da za ta o ta fadi ban tuna ku ba”. a ce, “Duk kin canza Haulatu, kin yi kiba kin ara kyau da haske, ko kin yi aure ne?” a ce, “Har da albarkarsa na like jikina. Matar .bdullahi Yakasai ce. An daura min aure bayan andynmu. Bikin ne dai ba ayi ba har yanzu Abjullahi ya tafi (Law School) sai ya kare nan da wata shida”’. Na ce, “Sunan kanina, Allah ya sanya alkhairi Haulatu. Sunan kanina mai bina kenan”. Ta ce, “Kwarai, kin taba gaya min kina da kani Abdallah, yanzu ajinshi nawa?” Na ce, “Abdallah ai an zama samari, yana SS I, Walida na JSS 2”. Ta ce, “Me kike karanta?” Na gaya mata harshen Larabci. Ta ce, “Kin burge ni Fa’izah, Allah ya kara fahimta, ya kara mana kaunar Manzo (S.A.WY’. Kai hirar da muka kwarara ni da Haulatu a ranar tana da yawa. Duk tarihin mijinta Abdullahi wanda ya kasance dan’uwanta ne ta bangaren mahaifiyarta sai da ta gaya mini. Sai da muka yi (missing) lacca guda saboda dadin hira, dama Haulatu uwar surutu ce barin in sun hadu da Ummi. Haduwar Ummi da Haulatu sun kusa shidewa don murna. Daga ranar amintarmu ta ci gaba da Haulatu daga inda muka tsaya a sakandire school. Naja’ atu na ABU Zaria in ji ta. Duk inda ka ga Zarah ka ga wata wato ni, Ummi da Haulatu. Mun je gidansu a ‘Yankaba ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ita ma
ta zo mana, har kwana take in lokacin jarabawa ne mu yi karatu tare, musamman da gidan Aunty Rabi ya fi kusa da makaranta. Ta saba da Aunty Rabi sosai.
Albarkacin Haulatu babu inda ba ma takawa a cikin Kano, daman an ce sai da dan gari a kan ci gari. Ummi ta yi manema har ba adadi, ni kuwa rashin sakin fuska da kora da hali wanda ya fi kora da sanda shi ya sanya duk wanda ya zo wajena da sunan so baya marmarin sake dawowa. Ummi kan ce lokaci ne, lokacin abu ayi shi. Ni ba auren su zan yi ba kawai suna rage min lokaci. Sai in kama baki in yiwa Ummi kallon mamakin yadda jami’a ta sauya ta lokaci guda.
A haka muka kare 100 level bayan jarrabawar da ta kusa tsaga mini kwanya muka fara 200 level. Idon mu ya kara budewa sosai a sanadiyyar ratsawar ilimi da cudanya da masu shi. Hausar bakinmu ta dai-daita da ta ‘yan Kano, kai ka ce nan ce mahaifar mu.
Mu muna using N a muhallin R, wannan shi ke sa Haulatu da sauran abokanan karatunmu ke cewa muna Hausar Giwa. In Haulatu ta tashi tsokanata sai ta ce, “Kin tuna Ummi ranan nan a anguwan sarki? Ba za ku bar wannan maganan ba? Yaya Rabi kin ga Ummi na tsokanana ko????”
OB KKK
Ranar litinin din nan rana ce da ba zan taba mantawa da ita a tarihin rayuwata ba, domin wani dan karamin bangare da ta taka cikin tarihin nawa. Na shigo aji a makare ainin domin sai da
muka biya muka ajiye Yaya Rabi a asibitin Malam wajen awon tsohon cikin da take dauke da shi, muka kuma mai da ita gida sannan Yaya Mufty (sunan da Yaya Rabi ke kiran mijinta Muftahu) ya kawo mu ya ajiye ya koma (office). Jikina har bari yake domin na ji jiya ‘yan ajinmu na fadin anyi sabon lecturer mara daukar wargi, madadin Farfesan dake daukarmu darasin. Sanye nake da shudiyar danyar atamfa (exculusive) mai ratsin ruwan hoda da mayafi launin sararin sama mai haske. Bayan wannan babu komai a fuskata sai farar powder da na muttsika da vaseline (lip balm) a siraran labbana wanda ya kara musu taushi da kyalli.
A rayuwata bana rabo da zizara kwalli a idanuna, kwallin (kajal) baki yana kara lafiyar ido, yana kuma kara fiddo min da gazar-gazar din gashin idona.
Ina kokarin zama a kujera ya ce, “Get out please….. (fita waje don Allah)”.
Wata kunya ta taso ta lullube ni ganin yadda idanuwan maza da matan ajin ya dawo kaina. Malam ya sake daga murya ganin na yi kasake! Na kasa zama na kuma kasa fita. Ya ce, “Get out I said (fita na ce)”.
Na daga ido cike da kwalla a hankali na dube shi. Baki ne mai kyau na a buga a kalanda ko ayi tallan advertisement board da fuskarsa. Bai da tsayi can-can, yana tsaka-tsaki. Fatarshi goge da zuzzurfan ilimi a kananan shekaru. Gwiwoyina suka sage tamkar an rarrade su da murfin kwano haka na cira kafa kamar kazar da kwai ya fashewa a
ciki na yi tattaki a hankali na bar ajin.
Wani abin mamaki sai ya kasance ban ji haushin mutumin nan ba a bisa korar karen da ya yi min a kan lattin awa daya. Sai ma haushin kaina mai tsanani da na bar Yaya Muftahu ya fara kai Yaya Rabi awo maimakon ya fara kawo ni.
Haka nan na samu kaina da gwada yadda yake magana a sarke “get out…. get out I said!” Na yi murmushi na kwashi takarduna na yi (main library) don in yi assigment maimakon in zauna zaman tunanin malami mara daukar wargi, mai magana a sarke da in’ ina.
ae ak ok
A gida nake bai ma Yaya Rabi labarin karonmu da sabon laccara mai tangardar harshe. Ummi ta ce, “Na ko so in ganshi, baki dan kakkaura mai yanayi irin na Yaya Bash yana driving wata (vauxhall) shudiya. Gaskiya gayen ya yi a rayuwa Aunty Rabi. Sai dai na yi mamakin yadda karamin yaro kamar wannan ya kai ga matsayin senior lecturer?’
Rabi ta ce, “Meye abin mamakin a ciki? Mai first class ko 2.1 zai iya zama lecturer komai kankantar shekarunsa. In kuma a waje ya yi karatun speed din ba daya bane. Mufty shekara daya kacal ya yi masters a Aston University”.
Ummi ta zaro ido ta ce, “One year Aunty Rabi?” Ta ce, “Baki bina bashin rantsuwa ki shafa ki ji wai shafa-labari shuni”.
A washe gari ma cikin ikon rabbi na yi latti.
Malamin jiya shine a ciki, sai na ji hantar cikina na rawa, kafafuna suka fara hardewa. Tun ganina na farko jiya da mutumin nan wani sabon al’amari ya bakunci ruhi da zuciyata, ba zan ce so bane, zan iya cewa kwarjini yake mun, kuma yana razana ni da kwarjinin.
Yadda zuciyata da hantar cikina basu bar karkarwa ba, haka kafafuna basu bari ba. Yau ma dai ta jiyan aka kwata, wato ya koroni waje. Wannan karon kam raina ya baci, domin karkarin lattin nawa na mintuna goma ne kacal.
Muna cin abinci a (Al-Amir) na aje cokali na ce, “Wallahi Ummi wulakancin dan iskan malamin nan fa ya soma isata, asarar lacca biyu kenan ya yi mani”.
Haulatu ta ce, “Wai wane ne?”
“Oho! Na san sunan shi? Yana nan wani dan kakkaura”’.
Ummi ta ce, “To mu ji alkhairi tunda tsiwar taki ta iso kan malamai. Wani ya ce ki makaran?” Wannan ta wuce.
Haulatu ta gayyace mu cin abincin dare a gidansu a washe gari ta taya Abdullahinta murnar kammala (Law-School) lafiya.
Muka shirya tsaf muka cakare muka cancare cikin swiss lace rawan kwaiduwar kwai (beig) da ratsin silver. Haulatu ta riga ta gaya mana za ta turo direban gidansu ne ya tafi damu, don ya Mufty ya je Giwa, matar gidan kuma tana fama da kanta ba ta (driving).
Don haka da Abdoul ya shigo ya ce, “Wai wadanda Haulatu ta turo a dauka su fito”.
Sai na zuba mishi rankwashi aka, muka zari mayafi muka yiwa Aunty Rabi sallama muka fita. Ni dai na ga mota ‘Vauxhall’ (one door) ba Honda din gidan su Haulatu ba. Kofar direba a bude ya zuro kafafunshi waje, sautin Abdurrahaman Sudaith na tashi a hankali a motar, ya sanya (ear piece) yana bi idanunshi a rufe ya jingina bayansa da kujerar kamar mai barci.
Kamshin turaren ‘oud’ na mota na tashi kadankadan. Ganin bai da niyyar bude idon, bai kuma san da tsayuwar mu a wurin ba sai na yi masa sallama a hankali. Tare da cewa, “Mun fito”.
Duk idanun ya bude wal! A kanmu. Hasken lantarkin farin bulb din da ya haskake harabar gidan ya haska mishi fuskokinmu. A sannu a hankali ya dauke ido a kanmu ya yi dan murmushi yana yiwa motar key yana fadin “Bismillah ku shiga muje, kamar ma na taba ganin daya daga cikinku”.
Tuni zuciya da ruhi suka shiga aikin da suka saba a duk lokacin da suka yi arba da wannan bawan Allah. Lecturer dinmu ne (Mr. No name), don ban san sunan shi ba, mai kora ta a bainar jama’a in na yi latti: Meye hadin sa da Khaulatu?
Ganin na tsaya na kasa shiga motar saboda mamaki sai ya dago ya dube ni muka hada ido na yi hanzarin russunar da nawa domin sun zama masu rauni kwarai a cikin nasa.
Ya ce, “Ki shigo mu tafi, tana jiranku, 0.k?’
Na bude bayan mota na zube. Ummi ta shiga gaba. Ya rufo kofar side dinsa cikin taushin murya ya ce, “FA’IZAH NAKE SO TA DAWO
GABA BA UMMIN AUNTY RABI BA!”
Wani sauti kululuuuu! Da cikina ya bayar kenan na mamaki, tsoro da tu’ajjabi. Ummi na dariya ta bude kofar gaba ta fito ta dawo baya ta zauna tana min alamar in fita ina girgiza mata kai alamar a’a. Ya ce, “Bana sayar da kai Fa’izah, ni aminin Barister Abdullahi Turaki ne. Shi ya turoni in taho daku an aiki Malam Saleh, ina fatan Fa’izah ta gamsu?”
Ni da Ummi duka sai da muka murmusa. Na bude mota na fito na koma gaban. Ya ja motar a hankali muka bar harabar gidan, ya hau titi dodar. Daga ni har Ummi mun yi tsit kamar a ce kyat! Mu bude murfin mota mu arce. Sunayenmu da ya ambata wai har ma da Aunty Rabi. Na yi murmushi kadan daga aikin ( talkative ) Haulatu. Mun yi nisa da Gadon Kaya mun hau titin Audu Bako, jefi-jefi yana karkata mudubin shi don hango motocin dake bayan shi. Da danja ta tsai damu sai ya juyo sosai ya dube ni ,’Are you 0.k?”
Daga mishi kai na yi. Har muka zo ‘Yankaba bai kara magana ba, sai ni da Ummi kan yi magana na abin da ya shafe mu.
Haulatu da Abdullahi ke zaune a harabar gidan bisa fararen kujerun roba suna hirar su hakora na shining (dariya). Kai da ganin wadannan ma’aurata ka ga masoyan da ke ji da juna. Har dai-dai inda suke ya yi parking, ya yin da duk suka mike suka nufo motar suna dariya. Ya zagaya ya budewa abokinsa, Haulatu ta bude mana ni da Ummi.
“Mr. and Mrs”. In ji lecturer. “Na cika uzurinku, kyawun alkawari cika shi’.
Abdullahi ya ce, “Wannan lazim ne Sadiqy (aboki)”.
Haulatu ta ce, “Ni dai ba ruwana, kada ku shafa min kashin kaji, daman ta ce Dan iska ne”.
Na dafe kirji da hannuwa biyu na ce, “Ke Haulatu!”
Yadda na yi din da irin fiddo idon da na yi cikin razana ta gaske ya sa gaba daya har Ummi suka tuntsire da dariya.
Abdullahi ya ce, ““Kada ki jawo mata ‘carry over’ Sweetie”.
Ya ce, “Ko spill over’ ba ta karasa a gidan mijinta”.
Da wadannan hirarrakin muka rankaya dakin saukar bakin su Haulatu.
“Tt’s a get together dinner of five….”
Haulatu ta fada tana wara yatsunta biyar tare da janyo warmers guda biyar Arabian cuisines, kabsa, kebabs, manakees cikin biredin (pita), sai mankees, shawarmah da burger.
Ta bubbude kowanne tana serving a plate, cewa take “I did it to you with my naked hands my dear Abdullahi! Congratulation on becoming a Lawyer”.
Gaba dayanmu bamu san sanda muka zuba tafi ba, ni Ummi, da Mr. Lecturer. Shi kuwa Abdullahi murmushi yake bakin kamar ya tsage.
Na kasa sakin jiki ko kadan abubuwan duk sun daure min kai. Sanda Mr. Lecturer ya bude wata foil paper ya turo gabana saura kadan in saki fit
sari don mamaki.
Gasasshen naman saniya ne mai romo da ya ji tumatir da albasa, har da cabeji sai turiri yake. Ya kuma dakatar da Haulatu daga serving dina shi ya yi serving dina da kansa, wannan gasasshen naman da ‘kebabs’ (tsire) plate dina wato har appetite dina ya sani, wa ya gaya masa ina son gasasshen nama?
A yadda ya saki jiki a gidan na fahimci ba bakon zuwansa bane. Har wajen su Hajiyar Haulatu tare da shi muka je muka gaishe su muka dawo falon. Ya dauki tambulan ya cika da lemun matsattsun kayan itatuwa (tropical juice) ya miko min cikin lumshe ido da bude shi duka a lokaci guda.
Ban iya na yi musu ba na karba, amma kurba daya na kasa saukewa saboda gardin lemon, ko ko in ce gardin hannun da ya fito daga gare shi. Cikin duka (Arabian Dishes) din nan gasasshen naman da ‘kebabs’ kawai na iya ci saboda na zama bakuwar zuciyata. This is the exact stranger I’m dreaming of. Sannan actions and emotions dinsa sun nuna abin da ke karkashin zuciyarsa, tun kafin ya furta, he care too much, sai shisshigi yake yi mun. Shishshigin da ba zan iya tankwabewa ba.
Zuciya da gangar jiki duka sunyi amanna, sun karbi shisshigin sun dora a kan kujera mai matsayin da baya kwatantuwa. Watakila da zai iya lashe ni zai yi saboda kulawa. Hakan yasa duk na bi na takura na kasa sakin jikina daga sanya baki cikin hirar shi da Ummi, wanda duka tambayoyi ne a kan abin da ya kawo mu Kano.
Haulatu ta ce, “Fa’izah fa ta bi ta takurawa kanta saboda malaminta”’.
Gaba daya suka maido hankalinsu gareni suna murmushi. Ta ce, “Dama kin saki ranki, kin saki jikinki wannan malamin….”
Ya yi hanzarin cewa, “Abdullahi killace bakin matarka kafin in bubbuge shi’.
Abdullahi ya miko hannu ya rungumo kwibin matar shi yana fadin “Kada ki kara magana Honey. A yiwa Yaya Malam biyayya don tare zan tafi in barku. Sai dai ban goyi da bayan a buge min bakin amarya ba tun ban biya farashinsa ba (siyen baki)”.
Ban san sanda na yi dariya ba, ni dai haka nan soyayyar Haulatu da Abdullahi ta ke burge ni. A gaban kowa basa 1ya boye su masu begen junansu ne, sai dai in ba za ka iya gani ba ka kau da kanka.
Haka yake yi in ya je wajenta a makaranta ya yi ta bamu kunya, wani zubin su bamu sha’awa, wani zubin su bamu dariya. Tattalin Haulatu yake kamar kwan da aka nasa yanzu-yanzu. Haka ita ma.
Ganin dariyata sai Abdullahi ya ce, “Ko ke fa? In ya sake ce miki ‘get out’ ki zo nan ki gaya mun ni dashi ne kin ji Fa’izarmu”.
Cikin dariya na ce, “Ai ban ga laifin shi ba Yaya Abdullahi. Ni ya dace in nemi afuwar shi a bisa lattin da nake mishi, wallahi ba halina bane yin latti akasi da uzuri aka samu. I’m sorry Malam”. Wani irin lumshe ido ya yi bai ce komai ba. Ya kara kwanciya a cikin kujerarsa. Wannan karon
wayar hannunshi yake latsawa kamar bai san bikin da muke yi ba.
Haulatu ta cika baki da shawarma cikin tsokana, “Wallahi Ummi wulakancin dan iskan malamin nan fa ya soma isata? Ko kin san asarar lecture biyu ya yi min? Oho! Ina na san shi? Yana nan wani baki dan kakkaura mai in-ina”.
Na kai tafukana da suka sha adon jan lalle na rufe fuskata suna ta dariya. Shi kuwa murmushi kawai ya yi. Yace, “Haulatu ba a sirri dake?”
Na ce, “Daman kin san shi ai kika rufemu a baibai?”
Ta ce, “Ah toh! Ba ga shi yanzu na baku mamaki ba”.
Abdullahi ya ce, “Lallai dan iska, yau kuma ‘yan iskan idanun bisa aminiyata suka fada?”
Ya dago kai daga kan wayarshi ya ce, “Ya ishe ka haka nan Abdullahi! Kai ka tashi ma ka tafi lokacin tafiyar ya yi ko a nan za ka kwana yau?” Ya ce, “In na kwana na yi laifi ne?”
Bai kula shi ba, suka ci gaba da kwasar girkin Haulatu sai da kowa ya yi kat. Shi da kansa ya yi serving dina. A yadda yake sarrafa hannayensa wajen serving din za ka fahimci lallai namiji ne wanda zai tattala matarshi matuka, wanda zai lallaba matarshi fiye da Abdullahin Haulatu. Abdullahi ya mike yana fadin “Haulatu zan wuce, zo ki ji mana”.
Ummi ma ta mike ta ce, “Ni toilet za ki nuna mani a cikin gida”.
Gaba daya suka fice. Daga ni sai malamina Mr. no name. A sannan ne na fahimci sun fita ne duka
don su barmu mu biyu.
Ya dan motsa a cikin kujerarshi sannan ya ce,
“Fa’izah!”
Wannan kira ya dade yana amsa kuwwa a sassan
jikina. Ban iya na amsa ba sai kara dukar da kai
ina murza zoben hannuna.
“Har yanzu ban yi abin da zai sa a sake dani ba?
Ko sai na kai ga durkuso bisa gwiwoyi na?
Domin wannan afuwar Fa’izah?”
Na dan fiddo ido, “Ta ya ya malami zai durku
sawa dalibinsa?’
“Ta dalilin yana SON dalibar soyayya mai ”
Ya fadi cikin kwaikwayar muryata. Da a ce ban
ga yadda yake ciccijewa yana cin magani a aji ba,
sai na rantse cewa ba shi bane. Lallai so ba dama
ne.
Jin na yi shiru ina tauna maganarsa sai ya katseni
da cewa, “Shin Fa’izah ta tsai da gwani ne
tsakanin Giwa, Zaria, ko Kaduna?”
Sai na yi dariya cikin jin kunya, “Don me ka yi
tunanin wannan? Mu ‘yan Giwa bama hada taura
biyu a baka”.
Murmushi ya yi tare da girgiza kai, “Mu ‘yan
Kano muna hadawa, kenan rabon kanawa ne ya
hana?”
Murmushi na yi cikin jin shauki.
“Fa’izah I’m serious. I’ve interest on you. Shin za
ki iya auren malamin makaranta?”
Dagowa na yi na dube shi da dukkan idanu, “Ba
bana ma malamin makaranta ne”.
“But you are born with a silver spoon in your
mouth (kin fito daga gidan masu hannu da shuni), kaman hakan zai zama takura”. Ya fadi cikin murmushi.
“A’a, ban fito daga (silver spoon) ba, na fito daga BABBAN GIDA (point of correction) mai babban suna”’.
Tafi ya yi min sau uku, “Mene ne bambancin guda biyun?”
“Akwai bambanci da yawa. Babban gida kudi bai yi yawa ba, amma babu yunwa babu rashin suttura a cikinsa. Sannan masu shi dattijan kwarai ne masu magana daya. Idan kuma ka ce tajirin gida kana nufin gidan hutu’’.
Wannan karon dariya yake yi sosai wadda ta sanya ni shagaltuwa a kallon sa, kyawunsa na kara kayatar da zuciyata.
“Na yarda dake Fa’izah, to amma fa sai kin ki ji kin ki gani a tafiyarmu. Abin da na gani ina so da zuciya guda ba zan iya munafuntar shi ba, ina da tabo Fa’izah, wanda na san as soon as an fara ganinmu tare za a kawo sukar sa. Duk da an ce waka a bakin mai ita ta fi daxi, ina jin kunyar kaifin idanunki….”
Ya yi dan murmushi…. “Ina son mata Fa’izah, ina son su da yawa….. na yi amanna da cewa har gida za a biyo ki a gaya miki wannan, sai in ba a ganmu tare ba. Amma na yi miki alkawari Fa’izah tsakanina da mahaliccina from you it will cease to exist (son matan) na yi miki alkawarin bari har abada in har kin amince ki zamo uwar iyalina.
Daga ganina dake na farko zuciyata ta gaya min
ke ce (life-companion) dina mafi cancanta. Kaunarki ta fara ne daga ganina dake na farko (love at first sight) na rasa nutsuwar zuciyata a tsayin wunin ranar da daren baki daya.
Da nake kwatantawa Haulatu kamanninki da level din karatunki take ce min ke best friend dinta ce tun a secondary, da take yawan bani labari. Shine ta hada mana wannan dabarar ta dinner (to dine here together) ta kuma turani in dauko ku. Gaba daya tarihinki na jishi wurin Haulatu, na kuma kara tabbatarwa kaina INA SON FA’IZAH! Shin Am I accepted Fa’izah?” Kaina na sunkuyar ina murmushi. Abin nan da masu iya magana ke cewa, labarin zuciya a tambayi fuska, don zuciyata ta yi na’am tun ma kafin ya furta. Har nake jin cewa, ba son mata ba ko mata dari gare shi zan iya zama ta casa’in da tara in har nice uwar ‘ya’yanshi. Domin yanada duk abubuwan da za a so shin a kansu. Ga dai ilimi, ga kuruciya, ga kyau na a manna a jarida, ban ga makusarsa ba.
“Ko da ban furta ba, kallo daya za a yi min a tabbatar da na fada a matsananciyar kaunar ka. Daga lokacin da idanuwana suka fada a kanka Malam”. Magana nake a zuci, ban san cewa a fili nake yi ba.
Ganin ya lumshe idonsa ya bude ya ce, “Na gode”. Ya tabbatar min ya ji abin da na ce. Wannan sai ya tuna min da lokacin da na karbi tayin soyayyar Yaya Aliyu a Zaria, ga shi ban ci ribar waccan ba, na amsa ta biyu, kada Allah ya kara dandana min dacin ta.