ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 10  by Sumayyah Abdul-kadir

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

neman dacewa duniya da lahira”. 

Da ace Fa’iz yasan tashin hankali da bala‘in da kalaman dake fita daga bakinsa suke kara jefani da ko da wuka a makoshi bai yi gigin furta su ba. Domin kalamai ne da ban taba jin mafi muninsu a duniya ta ba. (Hada rayuwa ta har abada da shi FA’1Z-ABUBAKAR) koko ince makiyina. Mugun dan uwa da kullum ketowar alfijir da faduwar rana sai nayi dakacen INAMA ban hada jini da shi ba. 

Wani kwayan mutum guda daya da ya maida mahaifiyata marainiyar wayonsa, ya maida ni kwallon takawarsa a duk sanda ya so, ko gare-gare abin wasan yara. 

Mikewa nayi gaba daya na littafin KWANA SITTIN ya fado daga ruwan cikina, na ce. 

“Da uwar wa Zaka tafi wurin direbancin?” 

Tsalle daya nayi sai gani a bakin kofar dakin nayi maza na rufe na murza ‘key’ na zare shi na cilla shi waje ta taga cikin wani irin zafin nama da ni kaina ban san inada shi ba. 

Ya yi maza shima ya cafe mukullin cikin irin nashi (exceptional) zafin naman wanda yafi nawa kafin ya kai ga ficewa ta tagar. Ya shiga sosa keya da (key) din ya daure fuska sosai kamar ba shi ne ya gama maganar da yayi cikin raha ba. “Meye haka? Gafara ki bani hanya na wuce”. 

Na ce, “Wucewa kam zaka yi ta, tunda har ka yi nasarar amsar mukulli. Amman fa bayan rubutun saki uku ris a gareni FA’IZA A.A GIWA”. Murmushi ya yi, “Wannan ne kuma ba zaki samu ba har abada Fa’izah, har kuma yaumil-ardhi. 

—= 

Domin ban aureki don in saki ba. In haka ne tun farko ba zan fara ba. Karewa ma, ni ba lallaminki nazo yi ba kamar wancan karon, UMARNI ne ki hada kayanki ranar litinin za ki tare a gidanki kamar kowacce mace mai aure. Ba kuma neman afuwarki ko kiyi min uziri nazo ba tunda ke abu ba ya karewa a wajenki kamar cin kwan makauniya. 

Ki matsa na ce, tun hannuna bai kai fuskarki ya yi mata tabon da bata da shi ba…”. 

Sunkuyawa nayi kafin ya kai karshen maganarsa na dauko littafin da Walida ta kammala rubutu dasu, na yago takarda a ciki na mika mishi. 

“Ko da can babu wani wasa makamancin ‘game’ ko ‘April-fool’ da ya taba shiga tsakaninmu balle yanzu da kowannen mu ya mallaki hankalin kansa. Za ka wuce din babu haufi, kuma babu makawa, amma fa bayan ka yi rubutun nan”. Na sake mika masa takarda. 

Fa’iz ya sanya (key) cikin aljihun kaftanin shaddar dake jikinsa. 

“Kenan har wani hankali kika mallaka yanzun? Ko daya! Kina nan yadda kike; Jiya ‘1 yau, kazama, dakikiya, ‘yar kauye, mummuna. Don haka daina cewa wani wai kin mallaki hankali, ina hankalin yake nan kana tura kanka cikin jahannama kana ji kana gani?” 

Na ce “In shiga wutar mana, tunda ba tare za’a sanya mu ba ina ruwanka?” 

Ya ce, “Naga alama abin naki nema yake ya wuce na rannan, to ba zan rubuta ba kiyi duk abinda za kiyi”. 

Anan kam dankwalina na janyo nayi dammara dashi a kuguna kamar wata sabon hauka, na doshi Fa’iz da takarda har na iso gabansa. Sai dai kuma zuciyata cike da taraddadin murdaddun damatsan Fa’iz da na hango ta cikin kayan jikinsa. Ina tunanin idan ya cafke ni da su wa zai kwace ni? Babu kowa a gidan sai yara na kuma kama kofa na kulle? Da alama shima ya shirya yau. 

Idona ya kyallo min biro a aljihun gaban rigarsa, na cizgo shi, na matsa gabanshi sosai har muna iya jin hucin numfashin juna. Kallon zakaru masu shirin dambacewa muka tsaya muna yiwa juna. Sai na samu kaina da ganin wautata anan, shin in nayi duka ta ina zai shigi wannan ‘giant’ din? Fa’iz kato ne sosai mai tsayi da kauri, kaurin da ba kiba ke haifar dashi ba ‘diet’ ne da hutu na yanayin rayuwa mai nagarta. Don haka na fashe da kuka tabbacin Fa’izun yafi karfina kamar yadda ya ce, babu yadda zanyi dashi. Sai na ce a raina. 

“bari kawai kaifin harshe na ya zama makamaina”. 

Cikin kuka na ci kwalarshi amma fa kada ki so ki tona bugun da zuciyata ke yi, na ce. 

“Idan har ka haifu cikin uwa da ubanka ka rubuta min takardar nan Fa’’iz…”. 

Ban kai karshen kalamina ba ya fidda hannu ya shimfida min wasu irin gigitattun mari hagu da dama. Na nemi ji na da ganina na wucin-gadi na rasa. Naga giftawar wasu taurari masu hasken dake tafiyar da ganin dan-Adam na lokaci mai tsawo, ji kake fauuu! fauu!! fau!!! Yasa 

tsayayyun kafadunshi ya ingije ni gefe guda na fadi warwas akan dandagaryar kafet. Ya nufi kofa ya zaro dan mukullin a aljuihunshi yana kokarin sanyawa jikin kofar, nayi kukan kura na wawuri abin zaman kwalliya (stool) na jefe shi dashi, ya same shi a baya. Yasa hannu ya rike kafadarshi ya kuma juyo cikin dan bude ido ya ce. 

“Kin gama?” 

Na tsala ihu na taso nayi kanshi da duka da duk iyakacin karfina da hannayena hagu da dama. Ganin duka wannan bai min ba, domin kamar ba jikinsa nake duka ba, sai na kai kaifafan hakorana damtsenshi shi, cewa yake. 

“Fa’izah baki da hankali ko?” 

Irin bude kofar da aka yi ba zato ya sanya Fa’iz hankadani tsakiyar gado wanda ke nufin da can dukan nawa da cizon nawa bai dameshi ba sai gudun kada a shigo a ga ina dukanshi. Gaba dayanmu muka bi kofar da kallo cikin firgita. BABA NE! 

Ya ce, “Kai amma Fa’izu anyi sullutun banza! Ka tsaya kanwar bayan ka na lallasa ka kana tsaye sororo, shashasha, sahorami”. 

Cikin kuka na ce, “Baba shi fa ya mareni, yayi min dukan tsiya har da rufe kofa don ma kada wani yazo ya taimakeni, dubi yadda ya dauki tebirin nan ya kwada mini a baya…”. 

Baba kam bai tsaya saurarona ba ni da karerayi na ya dauko dorinar da yakewa su Walida barazana da ita in sunyi laifi yayo kaina. Fa’iz ya kama bulalar da karfi ya rike, ya ce. 

“Haba Baba! In Fa’izah na haukan shirmenta bai 

—_= 

dace kowa ya biye mata ba”. 

Na ce cikin gunjin kuka, “Kai ne shirmammen, mahaukacin, amma ni lafiyata kalau”. 

Baba ya yi salati, ya fisge bulalar daga hannun Fa’iz ya shiga tsula mini ta ko’ina ina ihu ina zagin Fa’iz ban fasa ba. 

Fa’iz ya sake damke bulalar ya ce, “Baba ya isa haka nan. Ka yiwa Allah da darajar marigayi kayi hakuri”. 

Idanun Baba sun rine da bakin ciki da takaici, ya ce. 

“Fa’iz ko ka cikani ko in kakkarya Fa’izah da hannuna, ina amfanin wannan jarababbiyar yarinya cikin A.B?” 

Ya fisge bulalar daga hannunshi, ya ci gaba da shimfida mini da iyakacin karfinshi. Da Fa’iz yaga Baba na shirin illata ni (and he has no regret for it) Sai ya fado kaina gaba daya yayi min rumfa da faffadan kafadunshi, ya zagaye ni da hannayenshi ya rungume ya ce. 

“Sai dai ka nakasta mu tare Baba! Amma ba zan zuba ido a kashe Fa’izah akan gaskiyarta ba!!”. Baba ya yada bulalar ya fice yana fadace-fadace, bai dai yi min baki ba, sannan bai yi tir da haihuwarta ba amma ya ce ni zakka ce a cikin A.B, wake daya mai shegen doyi, mai son bata musu zuri’a, to nayi kadan, ba’a haifeni ba. 

Na tattara dukkan karfina da yayi mini saura wurin ture Fa’iz da lullubar da yayi mini da jikinsa, na mike duk jikina yayi rudu-rudu yayi birdin-birdin nayi hanyar kofa. 

Fa’iz mikewa yayi ya riga ni isa ga kofar ya 

rufeta da nashi mukullin, cikin kuka na ce. 

“Ko kai maye ne Fa’iz ka saki kurwata hakanan! Bar ganin ka hadani da iyayena, Hajjah da dukkan ‘yan uwa na har yanzu ina da sauran mai mara mini baya wajen ganin ka rabu dani ka sakeni da ka ki da ka so. 

Shin wai ni kadai ce mace a duniya ne? Koko cewa akayi daga kaina an daina haihuwar ‘ya’ya mata? Ka matsa ka bani hanya in wuce tun baka jawo an fitar min da raina daga gangar jikina ba”. Fa’iz yayi murmushi hadi da rausayar da kai cikin ginshirar tasa, ya gyara tsayuwarsa hannuwansa duka biyu zube cikin aljihu ya ce. 

“Ba ke kadai ce mace a duniya ba Fa’izah, kuma ba’a ce daga kanki an daina haihuwar ‘ya’ya mata ba. Karewa ma, akwai mata da suka fiki komai a ko’ina cikin duniya. Sai dai ke kadai ce wadda aka jarabci zuciyata akanta, aka jarrabeni da sonta da kaunarta. Don haka ina mai baki hakuri ki saurari abinda nake son bayyana miki, ki daina daukar fansa a bisa abinda baki sani ba…”. 

“Mene ne abinda ban sanin ba? Na kwana na hantse da sanin cewa ni ce mutum ta farko da ka fi tsana a rayuwarka. Dalilin ka na zuwa kace kana son nawa yanzu ne ban sani ba, ba kuma na bukatar sani. Abinda nayi amanna dashi shi ne… makiyin ka baya taba dawowa ya zama masoyinka sai in yana da wata boyayyar manufa akanka. To ALLAH YA FI KA!!!”. 

Na karashe cikin rishin kuka wanda ke tafe tun daga karkashin zuciyata. 

Shiru Fa’iz yayi, bakina kawai yake kallo cikin 

— = 

mamaki, nawa da na kansa. Wata zuciyar na gaya masa ya hakura da Fa’izah ko ita ce autar mata, wata na tankwabe hakan. Cikin wannan_ halin kalamaina suka ci gaba da dukan dodon kunnensa. 

“Wanda duk ya baka shawarar wadannan gayyar tsiyar da tarin akwatunan shirgin ka za su sayi zuciyata wallahi yayi maka karya, domin ba tsirara ka ganni ina yawo ba, ka baro gini tun ran zane. Wanda duk ya ce maka hadani da iyayena suyi ta dukana shi ne zai sa in soka ya yi maka hudubar banza, domin babu abinda dukan Baba ke karamin baya ga TSANAR KaA…! Aure kuma kaje ka rike, kayi ta rikewa. Ka ninka shi ba sau uku ba, sau dari. Sai dai fa kama daina mafarkin zan bika ko kofa ta kashi. In Allah Ya yarda, insha-Allah ba zan sake cewa ka sakeni ba. 

Sai dai jikin Fa’izah da ya kwadaitar da kai ga AURENTA ba zai taba zama mallakin ka ba. Ya gwammace ya zama na arnan bariki, ‘yan daudu da ‘yan ashana…da dai ya zama mallakinka”. 

Ban rufe baki ba daga furucin naji saukar tafukan Fa’iz a fuskarta, mari ta ko’ina hagu da dama. Ya fisgoni ya angiza ni na fadi akan kafafuna, kamin in wartsake in gane abinda ya ci gaba da gudana babu Fa’iz a dakin sai takalman shi. Kamin inyi tunanin abin yi (next) Fa’iz ya shigo tare da Baba fuskarshi tayi jajawur idanunshi sun rine har wani blue-blue suke cikin bala’in da ban taba gani ba. Ya ce, “Fa’izah ga Baba, maimaita abinda ki ka fada mini yanzu a gabansa”. 

Na fashe da kuka, “Ni me na ce? Nace ne ba inda 

— = 

zani, ba zan bikan ba”. 

Baba ya ce, “To-to ya isa haka”. 

Ya duka ya dauki dankwalina dake yashe a kasa ya rufa mani aka, ya ce. 

“Oya, ku tafi kusan nayi, kada wanda na kara ganin kafarshi cikin gidana, in ba harkar arziki ta kawo ku ba. Tunda ka hana a dake ta me zan iya yi mata? Ni wannan yarinyar ta isheni jarabarta ta isheni, Ku wuce ku tafi gidanku don Allah don kiyayya kusa masu ku soke junanku, aure ba za’a kwance shi ba. 

Ke kuma Fa’’izah inji kin saka kafarki wani wuri ba inda Fa’iz ya aje tasa ba sai na tsine miki albarka… Sai na yafe ki!!!”. 

A firgice na cira kai na dubi Baba. Kuka nake har naji babu dadi, na gyara dankwalina, bana ko batun takalmi balle mayafi, tuni na riga Fa’iz kaiwa bakin mota, na bude baya na shige. Na kifa kaina jikin kujerar gaba ina rusa kuka na gani kasheni! 

A can cikin gida kuwa gardama ce tsakanin Fa’iz da Baba. Ya ce shi ba zai tafi dani ba a yanzun ya fasa. Ayi duba da halin da nake ciki. Wane farin ciki zai tsinta a tare dani?” 

Baban ya ce, “To Fa’iz in ka saki auren ne kamar yadda take so ka bani takarda wadda zan nunawa Hajjah da sauran dangi Fa’iza tayi zama mai dalili a gidana, domin Hajjah har ta fara nuna fushinta da zaman Fa’izah tare da mu bamu mikata Kaduna ba. In kuma kana aure, to Fa’izah bata kara zamar min gida ta kara kwana daga yau. In 

baka tafiya da ita inda kake kasan inda zaka ajeta amma ba dai gidana ba! 

Yarinya daya tal na neman zautar dani kamar ita kadai na haifa? Na gaji wallahi””. 

Fa’iz ya sake kwantar da murya ya ce, “Baba Fa’izah ta rantse ba zata zauna dani ba. Ta yaya zan kaita inda ake ganin mutunci na ake girmamani ta dizgani ko ta rufe ni da duka don Allah Baba? Ni kam a kyale Fa’izah, ayi mata addu’a ta samu saukin bacin ranta kafin mu tafi. Amma bai dace in tafi da ita cikin wannan hali ba”. 

Baba ya ce, “Na gama maganar nan Fa’’izu, Fa’izah ba zata sake kwana mini cikin gida ba sai in baka aure. To wannan kuwa, bani da yadda zanyi da ita”. 

Fa’iz ya fice fuuu shima nashi ran a bace. Ba haushin Baba yake ji ba, zuciya yayi mai cewa ya yiwa Fa’izah duk abinda take so don a zauna lafiya. Kamar yadda Baba ya gaji shima ya gaji. In so cuta ne to hakuri ma magani ne. Bai taba ganin yarinya mai taurin kai da taurin zuciyar Fa’izah ba da kullaci wanda baya jin lallashi. 

Ya bude kofar motar ya shiga ya zauna, har ya tayar da ita ya juyo yaga ban rufe kofar ba. Ya fito yazo ya rufe ya sake ta da motar aguje, ban san inda ya nufa ba sai dai jikina ya bani ba Kano bane, ba Kaduna bane. Ya manta shaf da Shu’aib dan rakiyarsa. Shima Shu’aib din yana kallon mu muka fita bai yi gigin binmu ba. 

Nayi kuka nayi kuka har na gode Allah, na kuma ba uku lada. Hawaye sun kafe, murya ta dishe, haka idanuna sunyi luhu-luhu. Don haka nayi 

— —_ 

shiru na zubawa sarautar Allah ido ta hanyar kurawa tsirrai halittar Ubangiji ido dake giftamu aguje suna tsere da junansu (bishiyoyi da dazuzzuka). Ko ma mahalaka Fa’iz zai kaimu, a wannan Jokacin ban damu ba. Domin na fidda rai da rayuwar farin ciki tunda iyayena da suka haifeni ma basa so na, na kuma tsani rayuwar ita kanta muddin tare da Fa’iz zan yi ta. Na kuma tsani wani abu wai shi farin ciki ya sake ratsowa cikin rayuwata. 

28K ok 

an tashi kaduwa da al’amarin Fa’iz ba sai da na ganni cikin jihar Niger (Minna). Ya samu gefen wani titi yayi (parking) ya doshi wasu masu kirar wukake da ludaya na garin Minna ya yi cinikin wata sharbebiyar wuka gayawa jini na wuce, irin ta yankan shanu, suka yi ‘yar magana da makerin, sai naga an fara rubutu a jikin wukar. Ya kunso wukarshi cikin takarda ya biya kudi ya shigo ya ajeta a gefenshi ya kunna mota. A raina na ce. “Eh, gara kayi min yankan rago ya fiye mini da hada rayuwa da kai. Mugu, azzalumi, munafiki, mara imani. Ko kuma kayi min yankan kifi gunduwa-gunduwa zai fiye min kwanciyar hankali fiye da in karashe rayuwata matsayin matar Fa’iz Bamalli Giwa. 

Uhh! Daga wurin masu wuka kun san ina Fa’iz ya dosa? Fa’iz shahararren kogin Nigeria da nake ji cikin tarihi da ‘Geography’ sanda nake sakandire, wato ‘RIVER NIGER’ ya nufa damu wanda an 

tabbatar yanki ne daga kogin Nilu (Nile). Can ya dosa damu gadan-gadan ya zagaye masu kamun kifi zuwa can inda babu mutane ko daya. Ya danna wani madanni jikin motar glassai bakake suka maye gurbin farare (tinc) suka rufemu ruf. Ya kwantar da kujerarshi baya sosai ya bita ya kwanta yayi matashi da hannayensa ya yi ‘facing’ dina (fuskantata) sai kuma ya yunkuro ya taso ya dauko wukar nan ya cireta daga cikin takardarta tana walwali da walkiya. 

Duk da abinda na ce a baya na gara min ya kashe nin, yayi min yankan rago ko na kifi gunduwagunduwa amma a wannan lokacin da matuwar ta iso muraran sai na samu kaina da matsawa gefe na soma marmasa kalmar shahada tare da duk irin addu’ar da tazo bakina. Walwali take da walkiya inba za‘a ce idona bane yake min gizo da sai ince har huci wukar take yi. 

Sunan Allah nake kira a halshena da zuciyata, idanuna sun kankance sunyi wuri-wuri, amma babu hawaye a cikinsu sai firgita da razana. 

Na tabbata yanzu Fa’iz ya fini hauka, na dubi rubutun da aka yiwa wukar a sace, “FA’EEZAH”. Na fiddo ido kuru-kuru na sake makurewa jikin kofa. Fa’iz ya cillo mini wuka akan cinyata ya tube riga baki daya, har singiletin jikinsa itama ya cire yayi kira da kakkausar murya. 

“Fa’izah!”. 

Subhanallahi-subhanallahi, Hasbunallahu wani’imal wakeel kawai na shiga furtawa, na runtse idanuna. Ban taba ganin namiji a tube ba balle kato mai girma irin Fa’iz, yayinda haiba da kwar

— = 

jini na Fa’iz Giwa yayi min lullubi, ya kara fuskantata ya ce. 

“Dauki wukar nan ki caka mini ko ki yanka ni karewar kiyayya kenan, ko kya huce bakin cikin zamowa na miji a gareki, ko kya yafe laifin da kike ikirarin na miki, wanda kika kasa yafewa! Kika kuma ki saurarona inyi miki bayaninsa. Idan kika yi hakan na tabbata zaki huce ba karya…”. Nayi salati na dire ba tare da na kai karshen sa ba na dauko sabo. Na ture wukar daga cinyata ta fadi kasan kujera, na soma murda murfin motar ko na samu ya bude in san inda dare yayi min amma ko gezau kofa bata yi ba, yasa (lock) ya kulle ta gaba daya. Cikin dakiya da tsare gida ya ce. 

“Haba Fa’izah, (be brave) mana! Babu wanda zai sani, babu wanda zai ganki. Na tabbata in kin yankani zaki huce kiyi rayuwa mai dadi da nagarta. Ki samu rangwamen kullaci na dake zuciyarki na zagin Momi, mugunta da azabar dana kwashe shekaru ina yi miki, takardar saki dana hanaki, tare da huta auren direban tasha tunda ni dai hannuna ba zai iya rubuta saki ga Fa’izah ba ko da ace na iya rubutu!!!”. 

Idona rufe na ce, “Fa’iz ka bude min kofa in fita, naga alama ka haukace. Wallahi ba don komai na yarda na sanyo kafata a motar ka ba sai don furucin Babana, na yafeni da ya ce zai yi”. Na fashe da kuka. 

Ya sake matsowa ya dauki wukar dana yasar, ya ce cikin taushin murya. 

“Fa’izah, ki kwantar da hankalinki ki yanka ni, kinga in ba hakan kika yi ba baki huce haushi na 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *