ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 11 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
ba, baki kuma ci nasarar kiyayyarki ba. Kamar yadda bakin cikina ba zai kyale zuciyarki ta samu sassauci ba don kuwa ni ba sakinki zanyi ba…”.
A yayin da ya zura min kotar wukar cikin hannuna, nayi maza na yi baya da hannuna na kwalla kara tun karfina. Ihun da ake kira kunu a makota babu wanda yasan ina yi. Ihu nake ina karawa ko Allah Zai kawo wani giftawa yaji ya kawo min dauki. Sai dai ga dukkan alamu ihu na ya tsaya ne cikin motar kadai ko ta taga baya fita.
Ya ce (in subdued) wato cikin raunin murya.
“Ki yiwa Allah ki aikata abinda na umarce ki, sai ki jani ki tura cikin kogin nan. Babu wanda zai ganki, wukar ma ki jefata cikin ruwan. In yaso ki samu wani ki roke shi ga kudi zan bar miki ya tuka ki zawa Kaduna ko Giwa tunda baban ABU yasan tare muka fita…”.
Na girgiza kai da sauri, “Ko da nake kinka babu yadda za’ayi in kashe ka da hannuna tunda ba ni nayi maka ran ba. Sai dai na kasance cikin addu’ar Allah Ya kashe ka in huta wannan bala’i”. Wannan karon murmushi ya yi, sannan ya cira ido a hankali ya dube ni.
“Kin kasa gane abinda nake ankarar dake har yanzu, wato babu wanda zai ganki, ki kashe ki tura RIVER NIGER shi ne maganin kiyayyarki ga Fa’iz. To tunda kina tsoron kama wukar taki…”.
“Ka daina cewa wukata, ba tawa bace, kai ka san inda ka samo abarka…”.
“Ai don ke aka yi ta. Ko baki ga sunanki ne a jiki ba? Wai ma shin, ina haukanki da rashin
=
imaninki yaje ne da kike yin baya-baya dani yanzu ba kamar dazu da wannan bakin ke gartsa min cizo ba?”
“Na rantse da Allah ka isheni, ka maida ni inda ka dauko ni, ko kuma ka bude min na fita”.
Ya sha mur sosai, “Ki fita kije ina? Wajen ‘yan daudu da ‘yan ashana? Fa’izah babu wannan damar in har kin barni da rai. Baya ga wannan kyakkyawar dama da na baki, (remember that opportunity comes only once in life!) Muddin kika bar wannan damar ta subuce miki, to kiyayyarki ta karya ce… Kina son FA’IZ BAMALLI.
Ba kuma zaki iya kaiwa ‘yan bariki, ‘yan daudu da ‘yan ashana jikin da ya zam mallakin Fa’iz ba! Za ki bar mishi abinsa ne ya yi yadda yaga dama da shi daga yanzu har gaban abada! Muddin baki aikata abinda na umarce ki ba kina son rayuwar Fa’iz Bamalli Giwa ta ci gaba da wanzuwa a doron kasa…!”.
Ai jin hakan da ya fada, ya sani daukar wukar na riketa gam-gam cikin yatsuna amma na kasa motsa hannuna ko kadan. Sai Fa’iz ya matso gaba gareni sosai har hucin numfashinsa na dukan fuskata tare da sassanyan kamshin 212 dake tashi sannu a hankali daga jikinsa. Ya daga gira, tare da dan ware ido, ya kuma buda hannuwansa. “Uhm? Ina jiranki, (I’am ready)”.
Na runtse ido tamau, yayin da hawaye suka shigo kwaranya babu kakkautawa, a kundukukina, fadar Ubangiji (S.W.T) ke zuwa mini cikin kunnuwa na ta “WANDA YA KASHE A KASHE SHI” haka wanda ya kashe kansa ya mutu kafiri
— =
da sai in kashe nawa kan kowa ya huta, shi ya huta ni in huta, iyayenmu su huta. Sannan muddin na kashe Fa’iz dukkan dunguma-dunguman zunuban da na tabbatar ya wanzu yana dauka a rayuwarsa rubdugowa za suyi kaina. Baya ga haka in Baba ya nemi bayanin inda Fa’iz ya shiga bani da hujjar kare kaina. Ga wuka an rubuta sunana a jiki, idan ma na cilla ta cikin ruwan wani ya tsintota fa, ko masu kamun kifin nan?
A hankali na saki wukar kasa, na sanya kaina cikin cinyoyina na shiga shakar kuka. Fa’iz murmushi yayi.
“I achieved what I want to achieve, … all of a sudden… it’s obvious that you LOVE ME! (A fili ya ke kina so na, na cimma abinda nake son cimmawa)”.
Ya dauki wukar ya sauke (glass) ya cillata waje, ya mayar dashi yadda yake. Ya dauki farar (singletinsa ya maida, ya kuma maida shaddarsa. Ya tsallako ya dawo kusa dani ya zauna kafadunmu na gugar juna, ya shiga wakar “YAN ASHANA’ wadda marigayi Dr. Mamman Shata ya rera. lyakar zuwa wuya na zo, ga yunwa dake cina kamar me. Babu abinda na iya baya ga rufe ido da yin shiru. Na kuma saddakar na saduda duk iskancina Fa’iz ya dameni ya shanye. Da Aunty Rabi na nan da ta kada mishi tutar da tayi alkawarin kadawa WINNER, ya tabbata ni ce na fadi ‘game’ din, (I’am the LOSER!!!)
Wasu hawaye masu zafi suka shiga biyo kuncina. A lokacin ne naji ni cikin danshi sosai a inda nake zaune, alamu ne na isowar (period) dina
—_=
wanda ban zata a wannan lokacin ba. Na tabbata tashin hankali ne ya kawo shi ba wani abu ba, don lokacina bai karasa ba. Na jike sharkaf kamar wadda tayi fitsarin zaune. Don haka ko wani kwakkwaran motsi na kasa, nayi fiki-fiki dani idanuna sunyi ciki sun zurma don bala’i da kaduwa. Na kai idona ga agogon motar ya nuna karfe shidda na yamma. Shin yaushe zamu kai gida in mun fita jihar Neja yanzu? Gani da shegen tsoron ‘yan fashi, bansan sanda na sake tsandarewa da kuka ba.
Duk dai ni na jawowa kaina, da na kama Fa’iz na kulle a dakin Walida. Da na barshi ya wuce abinsa tun shigowarsa da ya nemi tafiya da duk hakan bata faru ba.
Akuyar cikina ta sake yin kukan yunwa da karfi, ji kake farrr! Fa’iz ya dan saurara kana ya yi dariya, ya ja kujerarsa ta koma dai-dai ya yi tsalle ya haure ya koma mazauninsa ya tashi motar. Bai tsaya ko’ina ba sai tsakiyar birnin Minna.
Ya karya kan motar ya shiga wani katafaren gidan saukar baki, a samansa an rubuta (MINNA GUEST INN). Ya yi (parking) a wuri na musamman da aka tanada don adana motoci cikin wata rumfa kamar tanti
Hankalina ya kara tashi, me Faiz yake nufi? Hotel ya kawoni? Ni karuwa ce?
Tunanina ya kasa boyuwa cikin raina sai da ya bayyana a kunnensa.
“Ni karuwa ce da zaka kawo ni hotel?”
Wani irin kallon biyu ahu yayi mini bai ce komai ba. Ya kashe motar ya soma tattara ‘yan shirginsa
—_
dake cikin motar ya ce.
“In zaki fito, ki fito. Gara da na kawo ki hotel ki zama babbar karuwa mai (class) ban kaiki matattarar ‘yan daudu da ‘yan asahana ba, ki zama (low level or classless prostitute)”.
Na kara tsananta kuka na, baki shi ke yanka wuya, da na sani banyi furucin nan ba da Fa’iz ya mayar garkuwarsa a komai. A wannan lokacin (I’m speechless) kalma ta kare a bakina.
Alal hakika ina tsoron kwana cikin motar ni kadai saboda ina da labarin garin Minna cike yake da mayu tare da tunanin koda na kulle motar ba za’a rasa masu (master key) ba.
Ya ce, “Ke kina bata min lokaci fa, abinda kike tunani ba shi bane, dube ki don Allah, me zan dauka anan kayan najasa? Dubi yadda ki ka batawa Baba motarsa, ni taimakon ki zanyi, a kuma wankewa Baba motarsa…”.
Idan na ce banji kunya ba kema kin san nayi karya. Eh, Fa’iz na da damar fada min duk abinda yaga dama. Nayi Allah Ya isa tafi cikin carbi, amma a zuciyata.
Na mike da kyar, duk kafafuna sun kumbura suntum saboda zama, ya zaro ido sanda na idasa fita a motar, ya ce.
“Kai-kai-kai! Ke tsaya nan, koma ki zauna kada ki bata masu (tiles) ki jawo min idon mutane, sai nayi (booking) daki tukunna zan dawo”.
Ban yi musu ba na koma na zauna, ko ni naso hakan sai dai babu wani alamun sassauci a fuskata.
Na koma inda na tashi na zauna nayi tagumi, na
gama saki da al’amarin Fa’iz ni yanzu tsoron shi nake ji ma. Tunanina na ya gangaro yadda zai yiwu in kwana daki daya da Fa’iz? Na kama kaina da hannuwa na biyu na rike, saboda barazanar tsage min da yake yi. kaina sarawa yake ta ko ina, ga kugin da cikina ke yi min babu sassautawa. Kuka ya kafe daga kwayar idona, nayi amanna babu yadda zanyi da Fa’iz yafi karfina a wannan lokacin duk ma wani yunkurin hauka ko tashin hankali da zanyi akaina zai kare don haka na alkawartawa kaina kunshe bakina don mu wanye lafiya.
Nayi zama na kamar awa daya, in saka wannan in kwance kamin ya dawo ya bani zani na bakin yadi da ake kira kofilin ko (plain yard) ya dora bisa cinyata ya ce.
“In kinga dama kina iya fitowa””.
Ban yi musu ba na fito na daura, na kwanto dankwalina na daura daga wuya. Sai a wannan lokacin ne Fa’iz ya lura ko takalmi babu a kafata balle mayafi. Ina kallon sanda ya kada kai, ya saci kallona ta gefen ido.
Haka nake tafe tamkar mai tafiya bisa fasassun kwalabe saboda hardewar da kafata ke yi, duk da babu mutane sosai ko ince sunyi nesa damu a harabar (guest inn) din ji nake tamkar idanun kowa akaina yake. A lokacin duhu ya shigo, hasken fitilu ya wadata ko ina, haske ne kamar rana. Dadi daya naji da na lura babu wanda ya damu da harkar wani a wajen. Ganin irin tafiyar da nake, sai ya rage taku duk da bai tsaya mun jera tare ba.
Wata sabuwa inji ‘yan caca! Ganin mu nayi a bakin matattakala wanda ke nufin bene zamu hau. Nayi tsaye jimm! Rike da kafar benen ina tunanin ta yaadda zan hau shi. Ban yi aune ba naji Fa’iz ya sunkuce ni ni da kazantata ya soma taka matattakalar dani dauke a hannayensa cikin sassarfa, bai tsaya ba sai a hawa na biyu, daki mai lamba (82) yasa mukulli ya bude sannan ya dire ni, ya ce.
“Ga daki nan, ki kintsa ki huta. Duk yadda naso mu koma gida a yau ba zai yiwu ba sai sanda Allah Yayi. Duk wanda ya buga in ba muryata kika ji ba kada ki bude, ko da yake ‘yan ashana ne ba damuwa”.
Ban tsaya sauraron kalolin rashin mutuncinsa ba na nufi (toilet), shi kuma ya ja kofar ya fita yana murmushi.
Kai Fa’iz sai a barshi, duk abinda zan iya nema dama wanda banyi zato ba na gani a (toilet) din, sinkin (always pad) (pantis) har shidda, dogayen riguna guda hudu, body lotion, brush da macleans har da mouth-wash, da saitin kayan wanka na ‘suddenly’ har da abin tazar kai, ga towels kalakala a (toilet) din. Nan da nan ban bata lokaci ba na hada ruwan wanka cikin kwami na wanke ko’ina na jikina da ya yi tsami ya warware. Na gasa kumburarrun kafafuna da suka suntume saboda zaman mota. Sannan ne na fito daga kwamin na bude ruwan ya tafi na zura daya daga cikin dogayen rigunan da ya aje mani kalar kofi. Na wanke wadanda na tube na shanya. Na dauki brush da maclean ina goge hakorana kenan naji
—_
bugun kofa. Tare da cewa.
“Zo ki bude ni ne”.
Ban san abinda ya ruda ni ba na kasa tsayawa in wanke kumfar baki na ko duk sabon tsoron Fa’iz daya shigeni ne oho! Da burushin a bakina da kumfar duka nazo na bude kofar.
Fa’iz ya shigo rike da manyan ledoji, ban yarda mun hada ido ba na juya na koma na kuskure bakina. Na dubi kaina a madubin bandakin inda na tabbatarwa kaiwa na karamin ramewa nayi ba rana daya kacal da Fa’iz ya sanyani a duniyarsa. Duniyar bala’i da masifa.
Haka na fito ina ciccin magani, inda kamshin wani hadadden gashasshen nama ya bugi hanci na. Miyau na yayi bala’in tsinkewa, na hango shi bisa (three seater) ya ja (centre table) ya dora ledar (foil-paper) mai cike da gasasshen naman mai ruwa-ruwa da yaji tumatiri da albasa yana ci yana korawa da lemon (7Alive).
Na hadiyi miyau, ji kake mukut! Na samu daya kujerar na zauna ina kau da kai.
Ya yi murmushi ya dauko wata ledar ya ja (table) irin nasa ya dora mini, ya mike ya shige (toilet) ya barni ina kintsa hanjin cikina wanda baya yarda aja masa aji. Bayan gashasshen naman akwai (fried sphagetti) da hadin salad.
Na kusa tashi da duk abinda ke cikin ledar nan sannan na mike na isa ga dan firjin dake dakin na bude. An cika shi da nau’in lemuka kala-kala (squash juice) da (fruit cocktails), na dauki kwali daya na kwankwadi iya yadda zan iya nayi wata katuwar gyatsa, sannan nayi hamdala ga Allah.
—_=
Sai naji bude kofarsa daga (toilet) da alama wanka yayi ya sanya ruwan madarar jallabiyya yayi sharr yayi (fresh) (very handsome) da shi. Nayi maza na dauke kaina bayan da muka hada ido. Shima cin magani yayi kada in kawo masa wargi, bai san nayi rantsuwa cikin zuciyata har ya maida ni inda ya dauko ni ba zai ji wani furuci ko wata kalma daga baki na ba.
Ban zauna a kujera ba bisa carpet na zauna na mike kafafuna na dauki (remote) ina canza tasoshi har saida nazo (Bollywood) na tsaya ina kallon shirin da suke yi a lokacin mai suna (Baabul). Shi kuma sai ya dasa sallah bisa dardumar da ya sayo.
A raina na ce, “Lallai direban tasha ya canza, da can mutum ne wanda baya wasa da sallah, amma yau sai da ya zauna ya take ciki yayi wanka sannan zai yi sallolin dake kansa.
Ya jima yana sallar da ban san la’asar ce ko magariba ko isha ba, kamin ya yi sallama ya kunna sautin Abdurrahman Sudaith cikin wayarsa yana saurare cikin Suratul An’ami. Ya kuma shiga gyaran akaifarshi da ‘nail cutter’ yana bin karatun da wani irin sauti mai dadi da na kasa tantance Fa’iz ko Sudaith wane ne hafizin gaskiya? Dole na rage sautin talbijin tunda dai ni ba shaidan bace. A hakan wani irin barci yan soma fisgata, barci mai dadin gaske wanda na tabbata gajiya da samun nutsuwa ne suka saukar dashi.
Ni dai sai juyi nayi na jini bisa tsakiyar ni’‘imtaccen gado, lullube da lallausar bargo. Ban farka ba sai washegari misalin karfe goma na safe. Nayi
— =
mika, nayi salati, nayi tasbihi ga Ubangijina na nufi (toilet) na cika baho nayi wanka. Na tarar kayana da na tube na wanke jiya sun bushe don haka maimakon daya daga cikin dogayen rigunan su na mayar. Atampha ce (exclusive Sheraton) riga, zane da kallabin su. A (toilet) din na shafa (lotion) din E45 cream da ya sayo nayi daurin kallabina tsaf, sannan na fita ina cin magani ina harbin iska.
Zaune yake cikin kujerar zaman mutum daya, ya daura kafa daya kan daya, yayi kyau har ya gaji cikin (light blue) din jeans, na tabbata suma siyo su yayi jiya tare da nawa kayan. Don dogayen rigunan daya sayo min ma kalar makuba maroon, milk da black daga gani sayen (boutique) ne. Rike da ‘yar karamar radio yana sauraren harshen Hausa na Rediyo Najeriya Kaduna. Na samu wuri can nesa dashi na zauna na zuba tagumi. Da alama Fa’iz bai da niyyar tafiya ma kwata-kwata, na dai ja bakina na kara tsukewa cikina ya soma kiran ciroman garinmu Giwa.
Ya rage sautin rediyon cikin sassaucin kallo. “Madam, babu gaisuwa?”
Kokari yake mu hada idanu amma na ki. Ya yi murmushi .
“Kiyi hakuri, na canza miki wurin kwanciya ne jiya saboda kada wuyanki ya kage”. Ya sake yin shiru.
Ya tabbata ba zai samu amsa ba. Hakan bai hana shi karawa ba.
“Me kike son kiyi (break-fast) da shi?” Ya dan canza fuska, wato ya dan sha mur.
“Fa’izah ba zaki magana ba?”
Na sunkuyar da kaina hawaye suka soma mirginowa a hankali ta kasan idanuna. Ya aje rediyon ya taso ya iso har inda nake, ya kama hannuna na dama ya rike cikin nasa, nayi kokarin janye hannuna amma ya rike tamau, gam-gam. “Me zaki ci eye Fa’izah na?”
Da wani irin karyayyen sauti, mai kassara gabban jiki da sanyaya zuciya.
Da hanzari na mike na nufi (toilet), duk da nasan bani da abinda zanyi a ciki. Gaba daya jikina rawa yake yi, haduwar fatar jikimmu wani ‘chemistry’ ne da bazan iya fassarawa ba, mai dauke da wani irin (shock) mai tada tsigar jiki tamkar (electrical shocking). Na maida kofar bayin na rufe, na jingina da ita, na lumshe ido a hankali cikin kokarin (regaining consciousness) wanda ya yi min wahalar dawowa.
Sai da na samu nutsuwa sannan na fito. Wannan karon bashi a falon. Na dauki takarda da biro nayi rubutu layi biyu kacal, ina kokarin ajeta a inda ya tashi ya bude kofar ya shigo da sallama ciki-ciki. Nima ciki-cikin na amsa, ko kadan bai ji ta ba, don dai amsawar ta zama farillah ne.
Ina kokarin dagowa ya dafa ni, “Me ki ke rubutawa?”
Kamshin ‘212’ dinshi da kamshin bakinsa na (mouthfreshner) mai karfi da yayi amfani dashi ya cika hanci na. Ban son irin wannan kusantar da yake son assasawa a tsakaninmu ko kadan kuma ba zan lamunta ba. Nayi saurin aje takardar na ja da baya da zafin nama. Ya yi murmushi ya
—_
dauki takardar ya bude ya soma karantawa a fill. “Don Allah don Annabi Yaya Fa’iz ka kaini Kaduna wajen Mama. In kuma ba yanzu zaka tafi ba, to don Allah bani kudin mota in tafi, ina da abinda zanyi da yawa”.
Ya aje takardar ya dube ni da shanyayyun idanunsa.
“Kina da wani abin yi ne dama wanda yafi mijin ki muhimmanci? Na dauka miji shi ne (foremost) a rayuwar kowacce diya mace indai tagari ce. Nima ina da abin yin na tattara na watsar saboda matata Fa’izah, ko bance ita tafi komai muhimmanci cikin rayuwata ba tana da hakki cikin lokuta na, wani neman duniya ko sabgogin duniya wadanda ba sa karewa basu isa su sa nayi watsi da wannan hakkin ba. Ko da yake nasan ke baki dauke ni a matsayin mijin ba, balle ki bani wannan muhimmancin.
Zamu tafi, amma sai kinyi min magana cikin dadin rai, irin wadda macen da ke son mijinta take masa. Son samu kice I LOVE YOU YAYA FA’EEZ!!! Har sau uku. In ba haka ba, mu karashe sati biyun hutuna anan, daga nan mu wuce Birtaniya, ke da gida sai kinzo haihuwa. Kin san dai ba mai nemanki don an san muna tare. Don haka zabi na gareki”.
Ya juya ya soma fiddo abinciccikan daya sayo a ledar su, yana dorawa a (centre-table). Ya ci abinshi cikin kwanciyar hankali ya dora da Gahwah mai zafi (Coffee). Ya shige uwar dakin ya bi lafiyar gado da yake dakin ciki da falo ne. Amma ya sauke kafafunshi a kasa. Ni fa na kammala, ke