ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 2  by Sumayyah Abdul-kadir 

kai da suka ci kwalliya kyawu na bugun kyawu, duk hawaye ya vata kyakkyawar fuskar Bamallin su. Muftahu kam girgiza kai yake. 

Ali Na’’ibi, ya jingina da bango, yayin da maganganun da suka yi da Fa’iza ke nausar kunnensa tamkar a lokacin ne take yi. 

“…ko yankani za kuyi A.B bani auren nan… na gwammace in bi YAWON DANDI… da dai in qarashe rayuwata a matsayin matar FA’EEZ BAMALLI!!!”. 

Aliyu ya kama kai, ya ce, “Kash! Kinyi kuskure babba Fa’izah, ko masu yawon dandin basu da aure akansu, kada kiyi kuskuren da ba zaki iya gyarawa ba mana…”. 

Ya fisgi hannun Miftahu suka yi waje inda ya xauki motarshi aguje suka bar garin Giwa. 

Allah Sarki Aliyu xan uwa na gaskiya, gidan karuwai ya riqa bi kala-kala da Miftahu wai yana neman Fa’izah, yana mai suffanta musu ita tare da nuna hoton ta. Amma babu wanda ya ce ya ga gilmawar ko mai kama da Fa’izah, amma babu alamar gazawa a tare da shi. 

Miftahu kam ko fitowa daga mota bai yi ba, tausayin Aliyu kaxai ya ishe shi. 

Haka ya zage gidajen karuwan garin Kaduna da Zaria kaf yana cigiyar Fa’izah har duhun dare ya shigo, ya ba da cigiya a ofishin ‘yan sanda da kafafen yaxa labaral masu yawa. 

Ya ja birki dai-dai titin Sir Kashim, ya xaga waya ya kira Fa’iz Giwa, a fusace Aliyu ya ce. 

“Ka ji daxi ko xan gata! To tunda baka fasa auren 

nan ta ruwan sanyi ba, zaka fasa in an kawo maka gawarta. A yanzu Fa’izah kwata-kwata bata a Kano, Giwa, Zaria ko Kaduna, sai ka san inda zaka nemo ta”. 

Bai bashi damar yin magana ba ya kashe wayarsa, shi kuma bai kira shi ba. 

2K KK 

a’eez da ya tafi xauko Yaya Bashir a Airport a washegari wanda ya sauka ta Kano, qarfe huxu na yamma suna kan hanyar Kaduna daga Kanon. Bashir ya yi kwance a bayan (Henessy) yana kwarara hamma, yayin da Fa’ez ke ta tuqi kamar Allah Ya aiko shi ba mai magana da xan uwansa cikinsu. Tun can Fa’iz da yayanshi Bashir ba sa ga maciji. 

Bashir ya fiddo taba ya cinna mata (lighter) wadda aka yi da qgarfen azurfa ya soma fesar da hayaqi. Sanye yake cikin (Italian suit) baqage, da gani kaga baqon Russia cikakken Injiniya a vangaren wutar lantarki Eng. Bashir Mukhtar Abubakar. 

Fa’iz ya yi maza ya toshe hanci da hannunshi, yayin da ya rage gudun motar ya sauka bakin kwalta ya kashe motar gaba xaya, ya fito ya mai da gofar ya rufe ya zauna a saman bannet xin motar. Tunanin halin da ya baro Fa’izah a asibiti jiya yake yi, wata zuciyar na ce da shi kawai in ta farfaxo ya haqura ya saketa. 

To amma abin tambayar anan shi ne, idan ya biye ta zuciyar ya saketa yaya zai yi da soyayyar da ta 

zamo masa qaqa-nikayi? Shekaru xai-xai har goma sha… yaya zai yi ya xinke zumuncin iyalin Abubakar Giwa da ya yiwa givi saboda wauta da quruciya? Yaya zai yi ya xinke varakar da ya wanzar a A.B House? idan ya saketa tayi nasara kenan akansa wannan karon? (She’s always a loser on him and so she will remain till eternity…. Wata rana na zuwa insha Alla da Fa’iza zata san babu mai sonta duk duniya kamar shi da ta riqa maqiyin da babu ya shi a duniya. 

Shi kam ya tabbata alhakin mahaifiyarta ne da nata Allah Yake hukunta shi da shi ta hanyar xora mashi azabar SOYAYYAH… soyayyar kuma ba ta kowa ba ta Fa’iza Ahmad Abubakar Giwa. Wata yarinya da ya addaba, ya kyara, ya hantara babu gaira babu dalili sai a dalilin KABILA NCI, wauta da quruciya. 

“To in ka qi sakinta ta mutu fa a dalilin qiyayyar ka?” 

Wannan kam bai san makomar shi ba a wurin Ubangiji. 

Bai tava faxawa a soyayya ba, bai tava son mace ba a kafatanin rayuwarsa, mata kala-kala kuma iri-iri ya gani a rayuwarsa musamman abokan aiki da ke qarqashinsa da ake kira ‘yan matan jirgi (Caterers) na qasashe daban-daban, musamman yankin Asia inda yafi yiwa jigila da suke binshi da tayin soyayya ta banza ko ta aure, amma tunanin kucakar qanwar nan da ya baro a qauyen Giwa, ya dishe hasken duk wata xiya mace daga qwayar idanunsa. 

Har zuwa tahowarsa yanzun, bai manta da Alicia 

—_= 

ba, wata (caterer) dake aikinsa shi kaxai ransa, da zai iya cewa ya tava kulawa da soyayya a dalilin abotarshi da Yayanta pilot Johari, mutanen Berlin ne. Da qyar ya samu ya taho gida shi kaxai a dalilin kafewa da tayi sai ta biyo shi Nigeria sunyi aure a garin nasu Giwa, iyayenshi su MusuJuntar da ita. 

Alagar shi da Johari, ta faro ne tun daga karatu a (Ukranian Institute of Aviation) wanda shi yazo karantar tuqin jirgi Rasha daga Berlin ne, shi ne kuma ya samar mishi aikin da yake yi yanzun da kamfanin tashin jirage na mahaifarsa (Berlin Airlines) aka xauke su take, abinda ya hana shi dawowa gida kenan bayan kammala karatunsa. 

Don haka zai iya cewa idon Johari ne yasa yake kasa (ignoring) Alicia har kowa dake tare da su ya xauka soyayya yake yi da ita. Shi kuma yana biye mata ne don Johari yafi garfin komai a wajensa in yana da iko. To sai dai mutum bashi da iko da ZUCIYA, barta akan abinda take so, komin munin shi da wahalar samunshi. 

Abubuwa da yawa sun faru waxanda zai ce su ne silar soyayyar da yake yiwa Fa’iza ko ba sune ba. Muhimmi a cikinsu shi ne, bayan SO na haqiqa akwai son ya gyara wannan qasaitaccen zumuncin na A.B family da yasa almakashi mai kaifi ya farka ya zama wound wato (gyambo) a zuciyar FA’IZAH AHMAD ABUBAKAR, yana so ya warkar da wannan gyambon ne da SOYAYYAH. Ko da zai rabu da Fa’izah zai rabu da ita ne (only) in ya yi nasarar warkar da wannan gyambon da shi ne silar samuwarsa a zuciyarta, 

— = 

wadda itama bata da ikon sarrafata, domin SO da QIYAYYA duka halittar Allah ne da basu tava zama wuril guda. 

Wani sashe na zuciyar Fa’iz Giwa ya ce. 

“Shin me Fa’iza take taqama da shi ne haka da yasa ta ci galaba mai yawa haka a kansa, in ba don sharrin SO ba? In ba don son ta ba da ya sameshi rana xaya baiga abinda ma zai sa shi yin aure a halin yanzu ba, bai shirya masa ba (at all) yana cin kuruciyarsa ne. 

In ba don so da ba ya shawara ba, bai ga dalilin da zai sa ya baro aikinshi wanda kullum ranar AIlah samu ne mai xumbin yawa a gareshi, ya zauna yana ganin baqin ciki ba. Ko ma me zata yi tayi ta gama, however, yana son matarsa, saki a tsakaninsu yana ganin wataqila shi ne abu na qarshe da ba zai tava yi ba a rayuwarsa, sai in mai yanke hanzari ce ta cika umarnin Ubangijinta (mutuwa). 

Mutuwar tashi ma, zai so ace daga hannun Fa’iza ce ba don Allah baya yafe haqqin rai ba, a ganinsa in tayi hakan wataqila gyambon zuciyarta zaya warke. 

Tunani na qarshe da ya ziyarce shi, shi ne ta gama suman, qgafarshi qafarta, kwas xin nan da zai tafi Amsterdam sati uku masu zuwa, tayi ta suman tana farfaxowa yana da ruwan da zai yi ta yayyafa mata, indai ba mutuwa zata yi ba Falillahil-hamdu. 

Bai kai qarshen tunaninsa ba Bashir ya buxe murfin motar da qarfi, ji kake butt! Ya fito yana faxin. 

“Kai, don ubanka ance ma ni bawan gidanku ne da za ka tsaida ni a gefen titi zafin rana na duka na?” 

Fa’iz ya yi tsaki ya ce, “Kada ka sake zagar min uba Yaya Bash! Ta yaya zaka kunna min hayaqi cikin mota in zauna ina shaqa, na tayaka sha kenan? Iyaye kuma tunda ba ka ganin darajar su ni ina son kayana, kada ka sake ka sake zaginsu a gabana, na rantse ba zai yi maka daxi ba”. 

Bashir ya dubi Fa’iz sosai yana cikin wani irin yanayi na tashin hankali da bai tava ganinsa ciki ba, har wata rama ya yi, kafin ya baro Russia ba haka ya sanshi ba sam. Jikin Bashir ya yi sanyi, ya koma mota ya zauna ba tare da ya yi magana ba sai da Fa’iz ya mula, ya kammala shan qamshinsa da harare-hararensa kana ya ja motar aguje tare da sakin qira’ar Abdurrahman-Sudaith a rediyon motar cikin Suratul Nisa’i. Wannan ya taimaka wajen sanyaya zuciyarshi dake tafarfasa babu gaira babu dalili. 

Bashir dai binsa yake da ido, da zuciya, ya kasa shiru, bayan sun jima suna tafiya yana kallon Fa’izun wanda idanunshi suka kaxa suka yi jawur. 

“Wai kai me ke damunka ne?” 

Fa’iz ya harare shi ta cikin madubi, “Ai ni babu abinda ke damuna face tawa matar da ta tsane ni tamkar mutuwarta, duk da bani da wani hali abin qi, baya ga shirmen quruciya na can baya, wanda da ace zata saurare ni ta saurari kalaman dake qunshe cikin baki da zuciyata da ta fahimce ni, kai kuwa ke da damuwa. 

Baya ga baqin munanan xabi’un da kayo guzuri, shan giya, taba da bin matan bariki tamkar tsohon bunsuru, kai da wai an kaika ne domin ka zama ubana, mai xorani bisa hanya sahihiya, ka rikixe ka zamo tantirl, wacce irin qiyayya ce ba zaka gani daga taka matar kamila Hadizatu ba?” Bashir ya tashi zaune daga kishingixar da ya yi a kujerar baya tare da wurgi da abinda ke hannunsa ta taga gaba xaya, ya antayo ashariya cikin harshen (Ukrain) wadda Fa’izun a duk zamansa a Russia shekaru goma vai tava jin wani ya yi ba, haka ya lailayota da turanci wadda Fa’izun bai san akwai ba ma, sannan ya shimfixota da Hausa ji kake. 

“Abu kazan uban nan! 

Uban waye ya xaura min auren? Sharrin da zaka je kayi min a gida kenan Fa’iz? Wato dama ido ka sa min a duk motsina ko me? Duk tambaxar da kake yi da Alicia na tava xaga ido na dube ka da zaka ce ina neman mata? Ai dama gwano baya jin warin jikinsa…”. 

Fa’iz ya yi saurin miqa hannu ya kashe qira’ar da ya kunna na karatun Alqur’anin dake tashi, ya juyo ga Bashir bayan ya kashe motar baki xayanta. Ya yi rantsuwa da Allah ya sake rantsewa ya ce. 

“Wallahi-wallahi ka sake zagar min iyaye sai na sauke ka a dajin nan yaya Basheer!”. 

Basheer ya dubi qwayar idon Fa’iz sosai har wani blue-blue take, jijiyoyin kansa sun tashi raxa-raxa saboda fushi da mazantaka, ya ce a ransa. 

“Anya Fa’iz qanina ne?” 

Fa’iz gato ne qwarai murzajje mai wasu irin garfafan damatsa da ginannen jiki na Bamallin usli tamkar (Late) Abubakar Giwa a sanda yake nashi tashen quruciyar, yana nome manyan gonakinsa da hannunsa ba tare da ya nemi mai tayashi ba. Irin mazan da jarumtakar su ce kaxai tasa duka rabin rayuwar su cikin iska suke yinta, ruwa, hazo, zafin rana, sanyi ko duhun dare baya hana su lulawa cikin sararin samaniyar Subhana. Wanda duk ya yi qoqarin dambe da su, mace ko namiji labudda uwarshi ta haifi wani kawai amma ba shi ba. 

Savanin shi Basheer da (gulder), hayaqi da zina da ya jefa kanshi a Russia rana xaya suka haxu suka tsotse masa jiki da kuzarinsa. Sai xan banzan bakin tsiya da kauxi wanda ba a kashe shi a magana. Inda suka bambanta da Fa’iz kenan, wanda kafin ya yi qwaqqwarar magana ma aiki ne jawur, sai lokacin da ya sa kansa. 

Bashir ya ja bakin (glass) ya mannawa idanunsa, ya koma yadda yake da, wato kishingixa, yana ta huci shi kaxai kamar kumurci, bai gara magana ba. Fa’iz ya ja motar a guje, bai tsaya ba sai a qofar gidansu dake unguwar Jabi Road cikin garin Kaduna. 

28 OK RK 

uwar dakin Mama take lallashin Bashir yana kunkuni cewa yake. 

“Aure? Aure?? Wane irin aure yanzun nan haka sabida Allah, mutum yana tsaka da cin kuruciyar 

sa, ko an gayawa Hajjah zamanin da irin na yanzu ne? Kuma a rasa wanda za a aurawa wannan lukutar yarinyar mai shegen qarfin tsiya sai ni? Salon in na mata ba dai dai ba ta hau ruwan cikina yadda take danne su Zanirah? 

To ni yanzu ma daga gama karatu ban kama aiki ba anzo an xora min aure, ku ne za ku dinga yi min xawainiyar auren? 

Sannan ni wallahi ba zama nazo yi ba, na zo ne kawai in ganku in koma. Dama ace ‘yar siririyar ku ka aura mini ‘yar wajen Baban ABU sai in karva da godiya, me ma take ne da suna Fa’eez?” Fa’eez dake gefe ya juya musu baya yana kallon tangamemen hoton Fa’izah da Zaneerah, sun sha goggoro ranar bikin Zanirah da Mama ta kafa a falon, ya wani irin juyo cikin (slow-motion) ya qwalalowa Bashir kyawawan idanunshi, ya ce. “Yaya Bash! Ahir! ‘yan iskan idanunka bisan matata! Na gaya maka, na qara (warning) xinka, 0.k?” 

Mama ta dafe kai, “Fa’iz, yaushe ka koyi rashin kunya ne for Allah’s sake waye baya kuskure a bisa rashin sani? Ka bari Bashir ya xora idonshi bisan ummi kamin ya yi waxannan sambatun banzan mana. 

Bashir, kana magana ne akan wasu kwailayen yara mitsi-mitsi daka tafi ka bari shekaru takwas a baya da suka wuce. To wadannan…”. 

A yayin da ta mige ga xaya ‘enlargement’ din dake can hanyar kofar fita na Zanirah da Ummi, shima ranar bikin Zanirah ne sun sha ankon beig swiss laces mai ratsin silver da goggoro kalar 

_

adon leshin, wato (silver), wanda in ba ka daga idonka sama ba baza ka hango shi ba saboda anyi (placing) dinsa da nisa, ta taka kujerar cin abinci, ta dauko ta sauko fuskarta cike da annuri ta xora ma Yaya Bash akan cinyarsa. 

“Ga Ummin Hajjah”. 

Bashir ya kurawa Ummi ido na ‘yan dakiku yayin da kalmomin da suka shiga fita daga bakinshi bai san dasu ba… 

“How does this girl turn to slim?” 

Duk da tension din da Fa’iz yake ciki wanda Bashir din ya hada masa sai da dariya ta kama shi, ya yi murmushi cikin takaici ya tashi ya bar dakin yayin da Mama ke kyalkyala dariyar jin dadi tana kallon idanuwan Bashir da ke neman zazzagowa akan hoton. A ranta ta ce. 

“In banda anfi karfin Ummi me zata yi da Bashir don Allah? Ita kam tana fatan Ummi ta zam silar kimtsuwar xanta daga halin da ya tsunduma kanshi babu gaira babu sabar, don duk komi yana dawowa kunnenta, duk da Fa’iz ba duka yake gaya mata ba sai dai ya ce tayi masa addu’a, ya canza hali rana xaya. 

Ta daga hannu sama ta godewa Allah Al-khaliku sarkin qaga halitta da ya suranta Ummi kirar da ta fi karfin namiji ya wulakantata. 

Ta sani da yawa kamilallun mata ‘ya’yan gidan tarbiyya suke shirya mazajensu masu mugayen dabi’u irin na Bashir, don haka ta kara godewa Hajjah tare da binta da kyakkyawar addu’a a zuciyarta na Allah Ya ja kwananta cikin zuri’arta har kansu (junior) ko ana so ko ba a so. 

—_ 

Allah Sarki Maman Kaduna, a wannan ranar bata yi bacci ba, kwana tayi akan kafafunta tana kai sunan Fa’iza ga mai duka, kan ya karkato da hankalinta taso Fa’izu. 

Mama hawaye take da idanunta, a yayin da take rokon mai cusa soyayya da ya cusa soyayyar Fa’iz a zuciyar Fa’izah. Soyayyar da babu kamarta a duniya wadda ta fi gaban wadda take yiwa Nazir Galadanchi. 

Babu abinda ke damun Mama irin ganin yadda Fa’iz ke neman ya susuce kamar baya ji sosai, sai kayi magana sau uku kafin yasan da kai a gabansa, tunani yake ko da yaushe. Tun dawowar shi bai iya ya tsaya ya ci wani ginannen abinci ba kullum sai tea, lemo, snacks. Jiya kam da ta shiga boys qutarers nemansa yana wanka ta tadda hotunan Fa’iza sunfi kala goma anyi enlarging dinsu an kafa a kowanne kusurwa na daki da falonsa, musamman cikin bedroom, tayi tunanin ina ya samo hotunan? Da ta tambayi Yahya ya ce shi ya aika ya karba mishi wurin Walida. 

Mama kam ta tabbatar hakkin Fa’izah ne ya kama Fa’iz. Babu mamaki in ya tuka jirgi a wannan lokacin ya saito shi cikina garin Giwa wanda hakan babu makawa zai murkushe musu dan garin na iyaye da kakanninsu da bai taka kara ya ba balle ya karye. 

Mama ta tabbatar nutsuwar Fa’iz kawai samun zuciyar Fa’izah, ko da bai furta ba bai kuma nuna (weakness) dinsa ba, har gobe Fa’iz Abubakar, namiji ne mai amsa sunan namiji ko a cikin daruruwan maza baka fiya gane (weakness) dinsa ba, 

— = 

balle akan mace. Ita din ma don ta sa mai ido ne, amma da fatar bakinsa bai furta mata ba. Wanda hakan kuma (samun zuciyar Fa’iza) ba shakka ba karamin aiki bane ga duk wanda yasan Fa’izah da Fa’izun wurin kafiya da taurin kai. Wadannan sune halayen da Hajja ke hange har take ganin hada masu irin halayyar gamayyar aure shi ne dai-dai. 

A yau kam Mama ta qalubalanci tunanin Hajjah akan-kanta. Hada masu halayya daya aure cikin A.B ba dabara bace so-karvau. 

Zanira da Aliyu kam hadi ne na Allah, laushi na dukan taushi. Amma masu taurin zuciya da kafiya ba dai-dai bane hadasu aure, in daya ya taso daya ba zai sauka ba, haka in daya ya hau daya ba zai yarda ya fado kasa ba yayi lallami ya kaskantar da kai ba ga dan uwansa. 

Yadda Fa’izah ke ganin ta watsar da kanta inta kwantar da murya ta roki Fa’iz SAKI, haka Fa’eez Giwa ke ganin zub da kima ne da aji, muddin ya kwantar da kai ya baima Fa’izah haqurin abinda ya yi mata a baya. Duk da abin ya zo ya zame masa jidali, ya hana shi ci, sha da sukuni da jin dadin komai dake cikin rayuwar duniyar baki daya. Ya hana shi barci da walwala balle komawa bakin aikin shi. Don haka Mama ke addu’ar Allah Ya sauke na Fa’izah, domin muddin Fa’’izah ta sauke dole ne shima Pilot din ya sauka. 

To a washegari ne kuma Aliyu ya kada mata ‘ya’yan hanji da albishirin gudun Fa’’izah. Bata iya ta fadiwa Fa’iz ba sai dai shi a lokacin ya damu da ya ga Fa’izah ko da gani da ido ne a kalla zai 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *