ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 3  by Sumayyah Abdul-kadir 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

samu sauki daga azabtuwar da zuciyarshi ke yi a dalilin rashin ganin nata, inyaso ko ganinta ya yi kawai daga nesa ya haura takalmansa ya bar mata garin da kasar baki daya, in ta rage bala’in ta bishi Amsterdam su zauna. Indai sun kasance gida daya ai maganar kafiya da kiyayya sai ayi ta yin mai dalili, ba yanzu da ko harararta baya hange ba. 

Ya kurawa jerin jakunkunan da ya danqara dalolin shi ya sayo da sunan lefe ido. Shin wacce Fa’izah yake tunanin za ta daura zaninshi? Ko da yake a lokacin yana kan aiki a Istanbul ne, giyar son ta buge shi, ya shiga hada su a kasuwar (AKMERKEZ Shopping Mall) ba tare da ya yi shawara da kowa ba ko yasan ‘size’ da take amfani da shi a yanzu. Ya dubi shekaru ne kawai ya kintata, kuma da ya ganta bata zarce yadda ya kintatan ba. 

Ya bude yana duba su a hankali har da (underclothes). Fadin abinda ya kashe akai bata baki ne, amma ta wace hanya zai bata ta karba tunda a zuri’ar su ba’a lefe? Shi ne abinda ke damunsa. 

Ya mayar ya zuge ya koma ya jingina da filo ya lumshe idonsa, abin duniya ya bi ya dame shi, ya rasa ta hanyar da zai bullowa matsalar aurensa. Hausawa kan ce, “Tun ran gini ran zane”. Haka “Juma’ar da za tayi kyau tun daga Laraba ake ganeta”. Sannan “Kowa ya sayi rariya yasan zata zub da ruwa”. Kuma “Tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka”. (So he has to bear the outcome of his wrong doings…) 

Ya nisa “Ba abinda lokaci ba ya magani”. 

— = 

Wani sashi na zuciyarsa ya yi (whisphering) wato rada. 

Dai-dai lokacin da wayarsa dake kan bed-side take ta tsuwwa. A fusace ya dauka domin bai son wani abu ya katse tunanin nan da yake yi, tunanin kaxai sassauci yake saukar mishi tunda ba zai iya gayawa kowa halin da yake ciki ko abinda ke damunshi ba, sai dai su tattauna shi da zuciyarsa su baiwa juna shawara, su kuma lallashi juna tunda babu mafita sai jajircewa, ya rike igiyoyin aurensa gam-gam har zuwa lokacin da Allah zai tausasa zuciyarta wadda babu wanda ya san yaushe ne? Sai Zuljalali wal ikrami. 

“Na’am!”. 

Abinda ya ce kenan ba tare da ya duba fuskar wayar ya ga wane ne mai Kiran ba. 

“Ka ajiye duk abinda kake yi haka ka taho gobe. Yanzu na samu sakon ana kiranmu (interview) jibi da British Airlines. Ka sani wannan dama ce ba ta wasa ba, don Allah Abubakar ajiye komai ka taho don Allah. Night flight na gobe zamu bi zuwa Great Britain”. 

Abokinsa ne Ba’indiye Maajid Abduljalal ke magana kamar zai fashe da kuka. 

“Amma Maajid za ka cuce ni, ka san abubuwan da suke gabana kuwa?” 

“Zan cuce ka ko zan taimake ka? (This is a lifetime opportunity) Abubakar, ina shawartarka (don’t miss it…) koma mene ne ke a gaban naka ajiye shi, ba Fa’izah bace? Don Allah kada ka ba da maza (achievements are greater than women). Ka yarda dani, ka karfafa zuciyarka muyi wannan 

fafutukar tukunna, sai ka dawo ka ci gaba. Na yi maka alkawarin (I’ll stand by you) inga cewa kun dai daita da matarka idan mun dawo (and I promised to help you to the end of the battle my friend, be a man) Fa’iz, ina jiranka. Akwai (morning flight tomorrow) daga Abuja, nima shi zan bi daga Berlin zamu hadu a Airport din Wales, ina jiranka””. 

Ya kashe wayar ba tare da ya bashi damar ya yi korafi ko musu ba. 

Ya ajiye wayar cikin matuwar jiki, sai kuma ya daga ya kira British Airlines ya yi ‘booking’ duk da jikinsa a mace yake. Wani sashe na zuciyarsa ya yarda da Majid babu tantama zai halacci wannan (interview) to amma wani iri yake jin jikinsa kamar in ya tafi ba zai dawo ya tadda Fa’iza ba. Halin rai da karfen nasara. 

Ya duba agogonshi ‘Jovial’ mai ruwan kasa-kasa ya tadda karfe uku na yamma. Dole ne yaga Fa’izah ko daga nesa ne kamin ya tafi Birtaniya. Domin a yadda yake jin jikinsa da zuciyarsa da kyar ne in zai dawo ya tadda Fa’iza. Don haka maganar ginshira da jan aji babu su yanzu, zai fuskanci Fa’izah (no matter what!) 

Ya mike kamar wanda aka yiwa allurar kuzari ya fito da sauri ya kwalawa kaninsa Shu’aib kira. “Ka rufe kofar nan ka kwashi jakunkunan nan dake daki na ka zuba min a boot ka aje mukullin, zanyi tafiya sai na dawo”. 

Ya isa sashen Mama yana yi mata bayani a gurguje, sai ga hawaye a idon Mama. 

“Ni dai raina baya son tukin jirgin nan Fa’iz, han

—= 

kalina ba ya kwanciya, kullum kana kan iska. Me zai hana ka dawo gida kwata-kwata ka nemi wani aikin mai sauki kayi?” 

Ya yi dariya ya ce, “Kai mama kenan, insha AIlah ba abinda zai faru. Ki bar mutum da zuciyar sa akan abinda suke so, kiyi addu’a Allah Ya tsare, Ya dafa mana, Ya kare miki mu a duk inda muka shiga. Ki cire duk wata fargaba da tsoro, mutuwa daya ce tak! Hanyoyinta ne yawa gare su, amma inevitable ce (mara makawa). Yanzu ina zan ga Fa’izah inje Mama ko da _ babu gaisuwar arziqi?” 

Mama gabanta ya ragargazo ya fadi. A irin wadannan kalaman masu tsinka zuciya da Fa’izu ke furta mata da halin da yake ciki a fuska da zuci zata iya kara masa damuwa da sabon labarin gudun Fa’izah? Ko da yake wani sashe na zuciyarta na gaya mata wai Fa’izah na Zaria, amma ya akai tasan hakan? Ya za’ayi ta tabbatar da hakan? Yadda Fa’izah taki jinin auren nan ina ne ba zata ba don ta guje masa? 

Fa’iz ya sha jinin jikinshi da shirun Mama, ya ce cikin raunanniyar murya. 

“Mama Fa’izah ta kashe kanta saboda kiyayyata ne ki ke jin nauyin gaya mini? Na tabbata Fa’iza in akwai abinda yafi haka zata yiwa kanta, indai akaina ne Mama…”. 

Ya kasa karasawa, muryarshi na karkarwar da ta baiwa Mama tsoro akan wanda take ciki. Tayi hanzarin katse shi. 

“Lalalala! Fa’iza ta warke tuntuni. Hasalima ka samu sauqin tafiya domin tana A.B.U”. 

Ta hasaso ne kawai ta fada, domin ta rantse ba za’a ji mutuwar sarkin nan daga bakinta ba, ya je wani ya gaya masa. 

Tayi saurin dauke kanta daga kansa, saboda hawayen da ke neman fallasa ta sun ciko idanunta, kiris suke jira su malala. 

Ya yi dan murmushin tausayawa kansa, amma yafi tausayin Mama da matsalar shi ta zo tayi mata karan tsaye bata ji ba, bata gani ba. Ya juya ya doshi kofa, a zuciyarsa babu tsoron Fa’izah ko miskala-zarrah. Babu tunani ko fargabar abinda zata yi masa. To me zata yi masa da ya wuce zagi na fatar baki tunda dai a doke ba zata doke shi tayi nasara ba, sai dai hannunta ya yi ciwo. Zagi yana tofo? Ko yana tsiro a jikin xan Adam? “Kuskuren Pilot Fa’iz Giwa kenan na farko, da ya sani da ya tafi neman aikinshi salin-alin shi ya fiye mai ALHERI”. 

Inji Sumayya Abdulkadir (Takori). 

36 KOK 

A ZARIA 

aya Rabi da suka taso daga Kano ita da direban Ya Muftahu ta yiwa direban umarnin ya tsaya a Zaria zata ajiye tsarabar Momi na ta Gurasa data yo mata daga Kano kamin su wuce Giwa su hadu ita da su Yaya Aliyu su shiga neman Fa’’izah. Malam Garba direban Muftahu yayi (parking) dai-dai kofar shiga falonmu kasancewar gidajen malamai na Jami’ar Ahmadu Bello falo zaka fara taddawa da ka zo gidajen. A dai-dai wannan 

lokacin na kammala cin abincin rana da Walida ta lababo ta kawo min ne. Na daga labulen dakin Abdallah ina kallon daidaikun motocin dake giftawa suna wucewa ta kofar gidanmu da yake titi ne a shimfide wanda in ka bishi zai shigar da kai cikin makaranta don ko kusa nasan ba lokacin dawowar Baba bane, don shi sai wajejen taran dare yake shigowa. 

Nikam wannan zaman kadaicin ya fiye mani zaman Giwa ina kallon bakin ciki kala-kala. Sai dai tunanin halinda N.S ke ciki ya addabeni ko a wane hali ya samu kansa da jin wannan bala’i da ya fada mana babu zatonmu ba tsammani? Naji haushin barin wayata da Nazir ya bani da nayi a Giwa, ko banza da yanzu ina magana da N.S muna neman mafita. Ko da yake ko da na taho da ita din babu katin da zan ke saka mata tunda ko giyar wake nasha ba zan aiki Walida wani waje ba balle har Momi tayi (spotting) dinmu. Shin a duniya ina da masoyin da ya kai Walida a yanzu? Tun bullowar bakin al’amarin nan gareni ita kadai ta tausaya min, ta taimaka min ta kuma bani goyon baya don ita ta yarda nice tata, kuma farin cikina take so ba na kowa ba. Duk da itama da fari ta so ta tirje amma Hausawa sunyi gaskiya da suka ce ce naka sai naka. 

Na sa hannu na share hawayen da suka zubo min. Babu zato babu tsammani naga shigowar motar su Ya Rabi, kafin inyi wani motsi na neman buya munyi ido hudu da ita, tana rungume da jaririnta Sadiq mai sunan A.B da ta haifa. 

Wai sai na saki labulen da sauri na kwanta a kasa 

ina haki. Yaya Rabi ta fito daga mota tayi kofar falo tana danna kararrawa, Momi tazo ta bude, ta ce. 

“A’ah! Manyan baki daga birnin Dabo, saukar yaushe?” Rabi ta ce, “Ke tsaya Momin Walida, ina Fa’izar da aka ce ta gudu?” 

Momi ta ce, “Wai ‘yarki? Ai, ashe gurinki ta gudu?” 

Yaya Rabi ta dubeta shekeke abin har da alamun raini a ciki, ta ce. 

“Wurina ko wurin ki? Amma Aunty Maimuna baki kyauta ba, kina ganin yadda hankalin bayin Allahn nan ya tashi musamman Hajja, Baiwar Allah me tayi muku da zafi haka, don ta nufe ku da alheri? Shin dama tsakanin Fa’iz da Fa’izah akwai bambanci ne da za ki goyi bayan Fa’izah ta ki zaman aure da Fa’izu? 

Ai dama shi bare a cikin A.B har abada sai ya nuna shi bare ne. To sai dai ki bar naki auren akan na ‘yarki, amma wallahi baki isa komai ba. Mtsw! Ni bani hanya in wuce”. 

Momi na ta dubeta galala kamar ta ga hauka sabon kamu, duk da maganganunta sun mata zafi amma ta danne zuciyarta, a tausashe ta ce. 

“Shin Rabi ina ruwana da harkar Fa’izah balle aurenta? Tukunna ma da kika zo kika sani a gaba kina zagi Rabi ina kika ga Fa’izar a gidana da har nake goyon bayanta?” Rabi ta doka tsaki ta ce, “Yanzu fa naga Fa’izah da idona, yanzu nayi ido hudu da Fa’izah, kina tunanin ina da matsalar ido ne?” 

Momi ta ce, “Kayya Rabi, ba dai gidana ba, in 

kuma kina musu to ga hanya shiga ki duba ko’ina” Rabi tayi tsaki ta shige har tana bige kafadar momi tana fadin. 

“Biyo ni in nuna miki Fa’izar”. 

Ba musu Momi ta bita salaf-salaf kamar ana janta, yayin da Rabi ta murda marikin kofar dakin Abdallah, sai gani kwance a dandaryar kasa bisa (carpet) nayi flat duk na jeme nayi zuru-zuru nayi baki kamar ba ni ba. 

Momi ta shiga salati da sallallami tana fadin. 

“Na rantse da Allah ban san da Fa’’iza cikin gidan nan ba, bansan ta ina ta shigo ba, bansan yaushe ta shigo ba”. 

Yaya Rabi kam bata bi takan momi ba, kallona take cike da takaici, yayin da nake barware wani irin kuka, ta ce. 

“Amma kin bata wayonki Fa’izah. Yanzu kan mutumin da ya kusan sati a makwancinsa ki ka kode, kika moje, kika sukurkutar da kyawun halittar ki haka alhalin baki san iya nisan taki rayuwar ba? Kaicon kafaffiyar zuciya mara amfani irin taki. 

Dr. Naziru kam ya amsa kiran mahaliccinshi tuni, don haka baki da sauran hujjah ta kin karbar aurenki da hannu bibbiyu kuma baki da sauran kaunar da zaki baiwa Nazir bayan binshi da kyakkyawar addu’a”. 

Kwakwalwata ce ta debi wata ‘yar hayaniya, tana yi min hargagi, tana yi min ihu-ihu, kararraki har da rugugi da taratsi da kalaman dake fita daga bakin Ya Rabi. 

Rarrafe na shiga yi akan gwiwoyina zuwa inda 

take tsaye ina tambayarta cikin kwanciyar hankali. 

“Ke Rabi, wanne Nazirun ne kike cewa ya mutu? Naziru Galadanci na?” 

Na fashe da dariya duka a lokadi daya, na dubi Momin Walida. 

“Kiji muguwa Momi, wai taje sun hada baki sun kashe min N.S don in auri dan uwanta. Ta lallabo nan tana fadin bani da sauran madafa ko hujja ta kin danta. 

To ko babu Naziru kina zaton zan bar shima Fa’izun da rai ne? Idan har babu Naziru kisa a ranki Fa’iz zai bishi ne duk ranar da ya shigo hannuna… na rantse, na kuma rantsewa da wanda raina yake hannunsa Rabi, shima Fa’iz sai na kashe shi idan da gaske ne kina ikirarin Naziru ya mutu”. 

Na kara saka dariya har da hawaye, a hankali kuma sai na koma kuka tun ina yinshi a hankali da shassheka har muryata ta dushe ta daina ba da amo. 

Na ciro dankwalin kaina na rufe fuskata da shi. “Wayyo Naziru, wayyo Nazir me yasa kayi min haka a dai dai lokacin da nafi bukatar ka? Ka tuna alkawarurrukan da kayi mani baka cika ko daya ba? Kana so ka tabbatar min da gaske ba zan taba cimma duk wani burina a rayuwata ba? Kana so in tabbatarwa kaina banzo duniya cikin masu sa’a ba? Kana so inyi amanna da cewa ba zan taba samun duk abinda nake so a rayuwa ta ba? Kana so in rasa imanina na cewa nima Ubangiji na so na kamar sauran bil’Adama da Ya halicce mu 

tare? Ko ko ni Allah baya so na…”. 

Da sauri Momi ta juya man baya tana hawaye. “Yi maza ki gyara furucinki Fa’izah, ce ne Astagfirullah, fadi da babbar murya na tuba Ya Ubangiji, na tabbata Kana sona, son da kake yi min ne ya sanya baka barni da _ dabarar kaina…ba”. 

Rabi ta fashe da kuka ta kama ni zata rungume ni, na ingijeta da karfi. 

“Kada ki kuma zuwa kusa dani, yau na tabbatar ba Fa’iz ne kadai mai kina da mahaifiyata ba har da ke Ya Rabi”. 

Na soma ja da baya, Momi ta miko hannu. 

“Ji ni nan Fa’izah, ki daina fadin maganganun da kike fada, Rabi tayi abu ne akan rashin sani, Allah baya kama laifin da aka yi bisa rashin sani, kuma babu mai laifi sai ke, ko me Rabi ta ce min ke kika jawo min, ke ki ka shafa min kashin kajin da bani da yadda zanyi in goge shi cikin danginku. Baki kyauta min ba, kin sani cikin bala‘in da ba zan iya fitar da kaina ba”. 

Ta soma kuka, Ya Rabi ma kukan take da na durkusa na saki wata kururuwa dukkansu ficewa suka yi daga dakin da gudu. 

Fa’iz Mukhtar Abubakar Giwa, ya yi parking mota kirar ‘Sienna’ ta Baban Kaduna da ya tuko daga Kaduna zuwa Zaria. Ya fito sanye cikin wata shadda-shadda boyel-boyel ruwan madara kirar (filtex) kanshi babu hula, sakamakon hakan, tarin sumar kanshi ta bamallin usli wadda bai fiya tajeta ba sai dai kula da ita ta kwanta tayi linkif a kansa sai sheki take bakikkirin, murdaddiya 

kuma kamar yana (relaxing) dinta, kamar kuma haka take a halicce. 

Ya yi sallama a falon gidanmu inda ya tadda Momi da Ya Rabi na kuka da girmansu da komai. Da sauri Rabi ta ce. 

“Ka koma Fa’eez, Fa’eezah TA HAUKACE! Muddin kaje inda take a halin yanzu abin ba zai yi kyau ba. Duk ni na jawo da na fada mata rasuwar Dr. Nazir, ni Rabi’atu wa ya aike ni?” 

Fa’iz ya yi dan dawurwura da manyan idanunshi akansu. 

“Waye haka Nazir?” 

Ba kuma tare da ya tsaya jin amsarta ba ya murda kofar dakin Abdallah gaba dayanshi ya shiga gaba gadi ba tare da tunanin komai ba ko wata fargaba cikin ransa. 

Durkushe nake akan gwiwoyina na aza kaina bisa gadon Abdallah ina sharar kuka babu ji babu gani, fatana kawai adai-dai wannan lokacin nima mutuwar tayi min adalci ta zo ta dauke ni, ta sada ni da masoyina, muyi aurenmu a kiyama ya fiye min wannan rayuwar da bani da sauran masoya a duniya sai rundunar makiya da burinsu a duniya shi ne zubar hawayena da shigata cikin kakanikayi, wato iyaye da ‘yan uwana na jini. 

Na dago ido shargab da hawaye, jajur kamar gauta, don naji alamar tsayuwar mutum a kofa, ya kuma jima cikin dakin ba tare da ya yi motsi ko magana ba. 

Ban tabbatar ba, amma wannan matashi mai jini a jika ya yi min kama da FA’IZ BAMALLI dana sani wasu shekaru masu yawa a baya. Fari sol, 

har da surkin jaja-jaja kamar Bahurghade, ingarman mutum dan asalin garinmu Giwa, kuma jika ga Hajja Da ga Baban Kaduna da mama Asma’u. “Yau ko ni ko kai tunda Dr. Nazir ya tafi kai din zaman me zaka yi a duniyar banda zaman ka ci gaba da kuntata mini?” 

Da na mika hannu ga bangaresn dama na sai naji ya fada kan kwalbar lemo (7up) da Walida ta kawo mini na gama sha dazu,, na riketa katamau ina kallonshi kallon kura taga nama, kallon tsintsu daga sama gasasshe. 

Ya soma daga min hannu yana fadin cikin lumana. 

“Ki saurare ni tukunna… (just once) Fa’izah, kada ki aikata abinda zai sa kizo kina da kin sani. Na roke ki, ki saurari kalaman fatar bakina tukunna, daga nan na yarje miki ki zartar da duk hukuncin da ya yi miki….”. 

“Ko uban da ya haifeka ban sauraron shi balle kai, kai da duk wani dan A.B ma kwansu da kwarkwatar su indai akan na karbi aurenka ne”. Na daga kwalbar nan na wulwula na faskara mashi a goshi, ya yi saurin sunkuyawa ta wuce ta saman kanshi ta daki tsakiyar kansa. Kan kace meye wannan jini ya wanke shi tun daga tsakar kansa, goshinsa har zuwa wuyansa, amma don rashin zuciya zance ko bakin naci Fa’iz bai fasa dosoni ba, sake dosoni yake yana fadin. 

“Ashe da gasken kin haukace? Fa’izah (are you lunatic?)” 

Ya warware hannu ya shimfixa min mari. Wani irin marin da ya tafi da ji da ganina na wucin 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *