ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 4 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
gadi, na kuma ga gilmawar taurari goma. Amma bakina bai mutu ba.
“Muddin ka iso gareni sai dai wani ba kai ba, baka ba da saki amma idan ka tafi inda Nazir ya tafi na saku ko babu takaba, iyakaci nima a kasheni. Na gwammace mutuwar da zama da kai wai a matsayin miji sau dubu gara mujiya da kai Fa’izu Mukhtar Abubakar Bamalli Giwa”.
Wani irin karfi da ban zata ba ya shigeni, na isa ga madubin dogon yaro dake like jikin bango wanda Abdallah yasa kusoshi shida ya kafa a dakinsa na soma kokarin banbaro shi daga jikin bangon, ban damu da yankewar da tsokar hannuna ke yi da gilashin ba har na samu_ nayi nasarar raba shi da kusoshin da suka tokare shi suka zame masa garkuwa daga fadowa kasa. Fa’izu Abubakar, ya tabbatar tsandara mishi mudubin nan zanyi, wanda hakan na_nufin tsattsagewar jikinshi ta ko ina, alhalin ba karfinsa nafi ba, don haka yayi amfani da wani irin zafin nama wurin isowa gareni, ya kama mudibin ya yi mishi fisga daya ya wancakalar dashi a gefe ya kwankwatse, na sake doka tsalle don isa ga fashasshen gilashin in samo wani bangare daga jikinsa, ya isheni farkewa jikan Hajja ciki babu nadama, ban ankara ba na jini baki daya cikin murdaddun damatsan Fa’iz Giwa, ya rungume ni gaba daya katamau cikin faffadan kirjinsa.
Ban san sanda na tsala ihu ba. Wani irin ihu shi ba na karaya ba, shi ba na razana ba, haka shi ba na mika wuya ba. Ni kawai ban san na mene ne ba, ko mene ne ma’anarsa. Saboda wasu abubuwa
— =
ne naji cikin jikina masu kama da jan wutar lantarki (shocking) tun daga tsakar kaina har (toes) wato babban dan yatsan kafata shocking din azaba ne ake yi min irin wanda kiyayya ke haifarwa.
Gam-gam Fa’’iz ya rike ni.
“Fa’iza saki dai kike so daga gare ni ko?” Zuciyata na bugu tashi na lugude, cikin masifa da bala’in da ba zai kwatantu ba na ce.
“Indai kai dan halak ne cikin uwarka da ubanka… to ce ne an sake ki Fa’izah!”.
Fa ‘iz yayi shiru yana gwama numfashi, kafin da ya tattara dukkan karfinshi yayi watsi dani gefe guda. Yana girgiza kai ya ce.
“In aka yi hakan za’a zauna lafiya?” Cikin gyada kai mai nuna tabbatarwa.
“Har da kwanciyar hankali, za’a zauna cikin A.B family gaba daya, (no more crisis… no confrontations…)”.
Murmushi yayi, wani murmushin da na kasa fassara ma’anarshi ko abinda yake nufi, ya ce.
“Kin san ba’‘a saki cikin tashin hankali, ko cikin fushi, in aka yi hakan sakin bai saku ba. (Words and promises made in anger are like fire… you cannot reverse the damage they have done).
Don haka share hawayenki, kije kiyi wanka ki fito kiyi sallar la’asar, ki kawo min biro da takarda. Shi kenan Fa’izah?”
Haba! Ai ban san sanda na mike nayi toilet ba na sunce na sakarwa kaina shaya, sai a wannan lokacin ne radadi da zugi daga goshi da tsakar ka ya isowa Fa’iz. Ya kai hannu tsakiyar kanshi ya
shafo ya fitar inda yaga yadda jininshi ke ambaliya. Ya murda kofar dakin da sauri ya fito falo inda Momi da Ya Rabi ke zaune jigum-jigum. Momi ta mike tayi salati, ta tsarkake Ubangiji, tayi masa tasbihi, ta kadaita shi. Ta ci gaba da fadin.
“Ba lafiyarta kalau ba, kuzo ku fitar min da ita daga cikin gida, ku kaita (psychiatric) kada tayi mana lahani cikin dare”.
Fa’iz ya samu kujera ya zube juwa da hajijiya suna kwasarsa. Ya yi murmushi.
“Momi da hankalinta fa, bacin rai ne. Kuma tana da gaskiya da babu wanda ya tsaya ya kalla, amma shi kenan komai yazo karshe ai”.
Yaya Rabi ta cire dankwalin kanta ta daure mai goshin, ta sa mayafinta tana share mishi jinin wuyanshi da keyarsa, yayin da Momi ta dauko akwatin taimakon farko (first aid box) da yake ma’aikaciyar jinya ce, ta gyara wurin, ta cire kwalbar da ta nitse a wajen, ta dinke inda ke bukatar dinki duka idanun Fa’iz na lumshe har ta gama. Ta goge duk wani jini da auduga da ruwan (hydrogyn) tas.
Ya mike tsaye sanda ya jiyo murda kofa daga (toilet) alamar na gama wankan na fito, yana ce da Momi ta kai min wasu kayan in sanya.
Momi tana girgiza kai ta ce, “Wanda ke neman kashe mutum za’a kaiwa kaya ya sanya? Ni kam bana kai kaina mahalaka ina ji ina gani ba, kai dai kace kaji ka gani, bari in dauko maka ka kai da kanka, sai ince ga su”.
Ta shiga dakinta ta dauko doguwar rigarta da
=
dankwali na shadda ta kawo masa, ya amsa ya murda kofar Abdallah ya shiga. Na takure can kuryar kuskurwar dakin ina mai kallon ceiling da zani kawai daure iya kirjina. Yau sati biyu kenan rabona da wanka, don haka ji nake ta ko ina wata iska mai dadi tana ratsani. Tsami da tashin da jikina ke ta yi kwana da kwanaki duk na samu saukinsa. Gashin kaina da na jika jagab da ruwa ya taimaka wurin suturta fatar bayana, ya kwanta lamban akan dogon wuyana ya sauka a kafaduna. Bai yi magana ba ya mika min rigar na amsa. Fa’iz ya kalleni na ‘yan sakanni, ya ce.
“Ina takardar?”
Na mike na nufi littattafan Abdallah kan (studytable) dinsa na yago takarda harda daurawa akan littafi, na dauko biro.
Ya zauna gefen gadon ya karbi littafin, ashe ma yana da nashi biron a gaban aljihun rigarshi kyakkyawa dashi (biron) ya dora akan takarda ya soma rubutu.
Na koma jikin bango na tsaya hannuwana biyu sarke a kirjina ina kallonshi kasa-kasa.
Ya ce a hankali, “Nawa kike ganin ya kamata in rubuta?”
Na dan fiddo ido, da sauri kuma na ce.
“Uku mana!”.
Har sai da na bashi dariya, ya yi murmushi, ni kuma na sake hade rai. Sai ya mai da fuskarsa ya kintsa ta.
“Har uku, kina ganin su Baba ba za suyi fada ba?”
“Akan me za suyi fada kai da abinka?”
Murmushi yayi ya kalleni ya maida kai ya ci gaba da rubutu, ya kammala ya ninke ya maida bironsa aljihunsa ya mike ya iso har inda nake, ya miko mini. Hannu biyu nasa na amsa kamar wadda aka bawa damin kudi don rashin ta ido har da cewa. “Na gode”.
Ko da yake ni wannan ta fiye min gida da mota dole in gode in kara godewa.
Ya yi murmushi ya dauki hanyar fita, har ya kai bakin kofa ya juyo.
“To yanzu kin yafe mini?”
Na ce, “Ni me kayi min? Dama auren ne bana so da kai”.
“Ba wannan nake nufi ba Fa’izah.. Na can baya nake nufi, shekaru goma da suka wuce a gidan Hajjah””.
Nayi shiru cikin TUNA BAYA…Wai TAKORI ta ce TUNA BAYA SHI NE ROKO. Fa’iz ya wahalar dani da yawa har yadda mai karatu ba zai fahimta ba. Ya ki ni, ya nunan kiyayya, ya nunawa uwata, ya yi mata izgili kala-kala da kalamai na raini a wancan lokacin wadanda 80% su suka rura wutar kiyayyarsa gareni fiye da wanda ya yi min ni kaina.
Uwa tafi gaban wasa, haka ba’a hadata da komai, ni tawa mai sauki ce tunda na yar da kwallon mangwaro na huta da guda. Fa’iz ya cuce ni sosai, ya bata min sosai (he so much hurt me heart and soul) ya bata min baka da zuci ta yadda a wancan lokacin har nayi furucin BAZAN TABA YAFEWA FA’EEZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI BA!
To amma mutumin da ya hakura da auren da yayi don yana so duk da mugun rotsen da ya sha ai ya cancanci yafiyar tunda dai daga yau shi kenan da kyar ma in wata hulda zata sake hadamu baya ga gaisuwar zumuncin da ta zama dole ko a lahira sai anyita. Sai na daga jajayen idanuna na dubi dan uwana Abubakar (Fa’iz) har zuwa lokacin idanunsa akaina yake. Wani irin yanayi ne cikin kwayar idanunshi mai nuna gajiya, damuwa da matsananciyar yunwa wadda ta ci karfin mutum ta nuna cikin kwayar idanunshi. Ban taba ganin Fa’iz ba tun bayan tafiyar shi ko a hoto sai yau, ya kara wani irin girma da kyau da haiba mai ban mamaki. Ya zama (giant) ma’abocin kwarjini da kamala da alamun samun (exposure) na rayuwa cikin kowanne fanni a fararen kwayan idanunshi. Fa’iz ba Fa’1z ba, in ba don halin ba me zai hana ni inso wannan kyakkyawan kammalallen matashi? Na kau da wannan bahagon tunanin na ce cikin taushin murya. “Ka je kawai, babu komai”. Fa’iz ya tura duka hannuwanshi cikin aljihu, ya ce a tausashe. “Baki yafe din ba kenan?” “Abinda ya wuce ya wuce a wurina, bana son TUNA BAYA…”. Ya lumshe ido, “Har yanzu baki fadi ba da bakin ki Fa’izah cewa kin yafe mini”. Na ce, “To Ya Fa’iz, NA YAFE MAKA DUNIYA DA LAHIRA'”.
A hankali Fa’iz yake lumshe idonsa yana bude su, ya yi shiru ya kasa cewa komai.
“Show me in another way… na kasa gasgata kunnuwana Fa’’izah”.
“Like how? (Ma’ana, ta yaya?” Na tambaye shi. Sai ya zaro hannunshi na dama dake sanye cikin aljihun rigarshi kaftan na yadin (filtex) ya miko mini (yana nufin muyi musabaha).
Abinda bana so din shi ne ya dawo min, wato TUNA BAYA…, “Ba don komai Baba ke son in tafi ba sai don Mama da ta tsane ni kan shegiyar yarinyar nan Fa’izah!!!”
Ban iyawa! Hada hannu da Fa’iz Bamalli… Wani kwayan mutum guda daya da ya takurawa zuciyata a lokacin da bata da kwarin daukar kunci da kuntatawar. Wata zazzafar kwalla ta shiga tsatstsafo min.
Fa’iz idanunshi suka kada, jikinshi ya soma dan shaking a sanda yake fadin.
“Baki yafe min ba, wallahi Fa’izah yafiyar ki bata kai zuci ba. Akwai abinda baki sani ba, ban taba kin Momi ba, ban rainata ba, kuru… kuruciya ce da yarinta amma babu komi a raina a game da Momi ko da take (outsider) amma na yarda nayi kuskure kuma babu wanda ya san gobe sai Allah, kuma kana naka ne Allah Yana nashi. Yanzu babu lokaci, ina kan uzuri da na baki labarin abinda ya faru tun kafin a haife ki…”.
Ya tsuguna a gabana ya dora hannu bisa tafin kafata, amma ya kasa sake furta komi, wani ajin yana motsawa yana so ya maida shi Fa’izun shi yana so har gobe har gaban abada kada Fa’izah ta
—_
juya shi ko ta ga (week-point) dinshi. (Na yaushe kuma Fa’iz? TAKORI).
Sai ya mike a hankali yaja da baya ya juya ya doshi kofa, sai da ya kai bakin kofar sai ya juyo kadan cikin fadin.
“Allah Yaji kan NAZIR S.”.
A lokacin ne mutuwar da Ya Rabi ta ce min Dr. Nazir yayi ta dawo min danya sharaf, tuni hawayen dake makale cikin idanuna suka tsinke baki daya. Addu’a ce mai kyau ya yi ga masoyina na hakika, wato Dr. Nazir Sani Galadanci. Don haka na ce.
“Ameen Ya Rabbi”.
A yayin da ya sanya kafarshi waje zai fita daga dakin. Wani sauti ne ya fito tun daga karkashin zuciyata na zuciyar ‘yan uwantaka ba tare da yayi shawara dani ba.
“Haka zaka fita kayan ka duk jini?”
Sai bayan na furta ne naji kunya da alamun nadama, sosai idanunshi ke nuna cikin juwa yake karfin hali kawai yake na duk maganar da yake yi, a hankali yayi murmushi ya dan juyo ya dube ni.
“Za suke tuna min da irin kyakkyawar sallamar da muka yi da matata (a da) kanwata FA’IZAH A.A GIWA. Don haka kada ki damu da su, ko nazo sanya (uniform) ba zan zubar da su ba, zan tafi da su har Great Britain”. Yayi murmushi (a karo na biyu) “ki sanya kayan da Momi ta baki” ya fice da sauri.
Oho kuma wai inji wohoho! Kai ya shafa, ni dai
tunda na rabu da alakakai falillahil-hamdu. Dama abinda yasa ni tambaya ganin yawan jinin ne tunda haka yake so meye ruwan Fa’izatu?
Momi ta dube shi a yayin da ya kai kofar fita zuciyarshi a jagule, ta ce.
“Yanzun Fa’izu haka za ka shiga cikin mutane kaya duk jini? Ka zo ga na babanku ka saka sai ka tafi”.
Ya yi murmushin da Hausawa ke kira yake. “Babu komai Momi, da naje (Airport) canzawa zanyi Zuwa (uniform) ai”.
Rabi ta ce, “Daga nan sai ina?”
Ya ce, “Ina da (interview) ne Aunty Rabi a kasar Birtaniya”.
Idanun Rabi sukai rau-rau, hawaye na son zubowa ta ce.
“Haka zaka yi tukin jirgi Fa’iz da rauni a cikin kanka?”
Cikin kosawa da son ya tafi kafin likin da yayi ya balle, ya ce.
“Babu komi Ya Rabi, bi’izinillahi Rabbi”.
Ta ce, “To baka hakuri da tafiyar zuwa sati mai zuwa kafin nan Fa’’izar ta sakko ku tafi tare? In ta zauna nan me zata yi mana?”
Fa’iz ya sake murmusawa cikin takaicin kalaman Aunty Rabi, ya ce.
“Shin cikin ku Ya Rabi wa ke da jan wuyan sanyata ta bini ba ma gidana ba har wata duniya a yadda take ji da taurin kan nan? Yanzun ma dabara nayi mata muka rabu lafiya, ki rufa min asiri in tsallake in bar Nigeria Ya Rabi”. Yasa kai ya fice abinshi.
Bai isa (Airport) ba sai ana kiran sallar magariba, a yayin da ya karya motar ya shiga filin jirgin ne zugin da radadin da tsakar kanshi ke yi ya tsananta. Ya kashe motar a wuri na musamman ya fita ya dauko jakar kayanshi na (boot) ya rufe motar, cikin sauri ya gama cike-ciken takardun da zai yi. A yayin da ya shiga (pilot’s changing room) domin sauya kayan jikinsa zuwa na matukan jirgin sama ya tuna da abinda ya ce da Fa’iza, ya yi murmushi. A lokacin ne cikinshi ya soma kugi, wani irin kugi da bai taba yi mishi ba, yana tuna mishi rabon shi da kwakkkwaran abinci tun dirar shi Nigeria daga Russia. Yanzu kam da zuciyarshi tayi sanyi, hankalinsa ya kwanta da samun kalami mai dadi daga Fa’izah yana jin zai iya hadiyar abinci ko abin sha. Abinda bai taba samu ba tun tasowarsu (kalami mai dadi daga Fa’izah) ko da yake shima din haka bata taba samun rana irin ta yau daga gareshi ba. Don haka ya yi (marking) ranar (as precious). Wata rana mai dumbin tarihi a cikin ranakun rayuwarsa.
Fa’izah tayi kuskure da take tunanin zan iya sakinta koda daya ne balle uku rigis, saboda shima haukan da ake zaton mata ya sameshi ko me?
A yadda yake jinta a zuciyar nan tasa, yake jinta a ko’ina na ruhi da bargon jikinsa? Shi kam, bai san ma yana son Fa’izah ba sai yau din nan, ashe ada hasashe yake, ba don wani kyawunta ko kyakkyawan girman da tayi ba, a’ah yin Allah ne kurum, shi ya daura masa ta yadda bashi da harshen da zai fassara soyayyar Fa’izah a zuci
— =
yarsa, tun ranar da ya bar Giwa zuwa kasar Rasha.
Ya tuna rotsen da tayi mishi, sai ya girgiza kai ya yi murmushi. Kuruci dangin hauka kenan. Fa’izah na ganin hargaginta da (power) dinta shi zai kwatar mata ‘yancin da take so, har yaji tsoronta ya sake ta? Tsoron sa Allah-tsoron sa ranar da zai dawo gida Nigera daga wannan tafiya da zai yi wanda ya tabbata idan taji tsiyar da ya shuka mata a takarda ta nemi tsire shi da mashi, wannan ne hukunci na karshe da yake tunanin Fa’izah zata yanke masa in ya dawo.
Bai kai karshen tunaninsa ba (computer) ta shiga ankarar dashi lokacin tashinsu yayi. Za su tashi ne karfe uku na sulusin daren ranar ta Alhamis daga (airport) din Abuja zuwa Wales din kasar England ba kamar yadda ya kintata da farko ba, wato karfe goman dare, don haka_lokacin haduwarsu da Majid ma ya canza don sunyi ‘transit’ a ‘Scotland’.
Karfe sha biyu na safiyar washegari suna Wales. Kowa dake cikin jirgin ya fita in ka dauke (pilot) Fa’iz Giwa, yayi shiru shi kansa bai san me yake tunani ba har saida wani abokin aikinsa ya ankarar dashi za’a rufe jirgin, sannan ne ya daura idon shi akan jakar kayanshi ya dauka ya mike ya fito.
Monica da kawarta Divya, suna daga cikin fasinjojin jirgin da Fa’izu Abubakar ya biyo zuwa Scotland, zai sake kwasa zuwa Ingila. Sunzo ne
musamman daga Abidjan domin halartar kallon wasan kwallon kafa na gani da ido a (Chelsea). Ta gabansu Pilot din ya gifta a (reception) jaye da ‘yar jakar kayanshi a hankali akan (marbles). Tsakanin Monica da Divya, an rasa wadda zata fara dauke ido a kansa har ya kulewa ganinsu ya bi (lifter) zuwa (underground).
Monica ta tabo Divya.
“Kin sanshi ne? Irin wannan kallo haka?”
Divya ta girgiza kai, “Kamar nasan fuskarsa, ya taba debo mu daga Paris zuwa Ukrain”.
Divya ta ce, “Bahaushe ne fa tamkar mu ba Balarabe ba, sai dai ta ko ina babu fuska”. Monica ta hadiyi miyan da ya tsaya a makoshinta, ta dafe kirji ta rufe ido tana ta faman gyada kai kamar kadangaruwa, wata irin soyayya na cinta Fa’izun bai san suna yi ba wai kunu a makota.
Sun hadu da Majid a filin jirgin saman Wales, ba abinda Majid ya fara hangowa sai lafceciyar (plasta) akan Fa’iz da goshinsa. Hannu ya mika ya rungumo kafadunsa suka karasa wani dakin hutawa na musamman dake cikin filin jirgin, suka zauna a tare cike da gajiya da tsamin jiki na kwanan zaune.
Majid Abduljalal Balaraben Syria ne wato (Shaam), tare suka yi karatu da Fa’iz a Russia da Johari da wani bakar fata Solomon Bayaraben Nigeria (they are very close to each other) don haka sun san tarihin juna, sun kuma san damuwar junansu.
Majid bai tabbatar ba, amma jikinshi ya bashi