ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 8 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 8  by Sumayyah Abdul-kadir

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

iyaye da ‘yan uwana. 

Daga uwata har ubana kowa fushi yake dani, Walida kadai ke kula ni a gidan, haka nan kullum Baba zai fita sai ya ce. 

“Tunda haka kike so, wato ga dakin uwarki ga naki, inta wuce dakina ki bita da ido kina kissime-kissime ai sai kiyi ta zama”. 

Wannan magana ba karamin kona min rai take yi ba, tun ina kuka har na saba. A zuciyata kuwa Allah Ya isa ga Fa’iz tafi dubu biyar. 

Na rame, na fige, na zama ‘yar firit dama jikin ba wani jiki ba. Nayi niyyar komawa Giwa amma na kasa saboda kurarin da nayi a baya cewa ba zan sake zuwa gidan Hajjah ba. Wuri daya ne nake tunanin idan naje zanji sanyi, wato wurin Maman Kaduna, to amma in ina da kunya ai bana dosheta ba alhalin kiyayyar danta na neman zauta ni. Ko babu komi ranar da Fa’izun ya ga damar dawowa me na isa nayi mishi akan idon uwarsa? Gara dai ya kwaso jiki ya kawo namu gidan. 

Haka Zanirah da Aliyu suka yo min waya wai hakuri suke bani abinda suka yi min ranar bikinmu a Giwa su wasa ne suke min. Tsaki nayi na kife wayar nayi tagumi da hannu bibbiyu. 

Bayan kwana biyu kuma, sai Ummi da Bashir suma suka bugo, amma su ba hakurin suke bani ba, korafi suke wai naki inje inga gidansu, to inzo in raka Ummi awo tana da ciki dan sati biyu. 

Na ce, “Sai ku bari ya cika wata daya tukunna mu fara zuwa awo, kunji ko ‘yan abu kazan uba marassa kunya”. 

Ummi ta ce, “Da fatan (this very big) ashar (is for 

—_= 

me alone not with my husband) don mu albarkar miji muke nema ba ma zaginsa””. 

Watanni biyu suka shude tun ana zuba ido har kowa ya gaji babu Fa’iz babu duriyarshi, babu ko wayarsa. Don haka na yanke shawarar tunkarar Baba da shawarar da na yanke, wato komawa karatuna a Kano. 

Da farko baban ya fara ne da zunduma min zagi bayan ya gama saurarona, kana ya ce. “Sai dai in karuwanci kuma za ki sannan in barki, tunda kin ki zaman aure. Sannan ina mai tabbatar miki muddin ya kasance wani mummunan abu ne ya samu Fa’iz sakamakon raunin da kika yi mishi da kwalba, to ki tabbata sai na rotsa miki kwalbar 7up a wannan kodaddiyar fuskar da kike tinkaho da ita. Kazalika in Fa’iz yayi zuciya ne yaga cewa gara ya fasa auren, sai na dauke ki ke da kayanki na kai mishi sadaka, ko aikace-aikacen gida ne kiyi masa. 

28K RK 

A WALES (UK) 

bakin wani (swimming pool) dake cikin hotel din da suke ciki cikin birnin Wales din kasar Ingila, bisa fararen kujeru da ‘yar jar lema da tayiwa kujerun inuwa ta rage hasken hantsi daga idanuwan wadanda ke zaune cikinta. 

Pilot Fa’iz Giwa ne da Maajid da Johari tare da wasu abokan su wadanda duka matuka jirgin 

sama ne ke zaune suna karya kumallo bayan sun fito daga (interview) din da ta kawo su kasar Ingila da British Airlines. Maajid na shan (tea) cikin wani kankanin kofi, amma hankalin shi naga Fa’iz dake faman juya cokali cikin (coffee) mai zafi idon shi na kan wata siririyar baturiya dake sanye cikin dan kamfe da ‘bra’ kadai, tana tafiya lange-lange kamar zata karye saboda rashin kauri da kumari ko kuwa kamar da an busheta da baki zata fadi don sirinta. Amma a zahiri, idan ka dubi cikin kwayar idanunsa ba ita yake kallo ba, idanunshi ne kawai a saitin da take, tsabar tunani ke jagwalgwala kwakwalwarshi wanda kuma ke neman fitar da shi daga duk wani jin dadi da yake ciki ya kuma zamo barazana kuma ga walwala da farin-cikin sa, harma da nutsuwarsa da hayyacinsa cikin duk al’amuran da yake gabatarwa tun barowarshi gida wanda ba wani abu bane face kanwarsa/matarsa FA’IZAH A.A GIWA. 

Wadda damuwa da al’amarinta da neman sanin hanyar warwarewar damuwar al’amarinta da shi ya zamo wani abu kadai da ya tsaya ya yi karantsaye ya addabi rayuwarsa. Har yake neman zautashi ba don ya kasance jarumi akan komai ba musamman wajen shanye damuwa komin girmanta. 

(Still) idanunshi na kan Ba’ireshiyar cikin rashin sanin abinda yake yi ya dauki attaruhun kwalba ba tare da ya ankara ba ya zuba cikin kofin Gahwarsa ga zatonsa sukari ne yake zubawa. Maajid na kallon shi bai hana shi ba sai ido da ya gwalo kamar za su fada cikin kofin shayinsa. 

— = 

Pilot Javed Saddyqy ya dubi Maajid cikin yamutsa fuska tare da nuna Fa’iz din da abinda yake yi da baki. Maajid ya kada masa ido alamar ya kyale shi. Idon shi daina kan Baturiya wadda ke ta faman yi mishi gizo da Fa’izah surarta na rikidewa tana zama Fa’izah. Ya sake daukar cokali ya motsa shayin yana shirin kaiwa bakinsa. Anan ne Suhayl Khan mutumin India ya ce da Saddiqgy wanda shima Ba’indiyen ne cikin harshen Tamil. 

“Fa’iz ya samu makuwa ne halan?” 

Alama Saddyqy yayi mishi ta yayi shiru ta hanyar daura dan yatsarsa bisa lebensa, a lokacin yana rike da kofin ne a hannunsa amma tsayin mintuna uku bai kurba ba idanunshi akan Baturiya. Anan sai Javed ya sanya kafa ya dan take mishi yatsun kafarshi dake kusa da tasa, ya ce. 

“Ba zaka sha bane?” 

Fa’iz ya kai kofi da azama bakinshi ya yi mishi kyakkyawar zuka. Ba shiri ya saki kofin a kan tebirin ya ce. 

“Aaah!”. 

Suka kwashe da dariya gaba daya, wadda zafin gahwah da zafin attaruhu suka hadu suka hana Fa’iz jinta duk da karfinta (dariyar tasu). Maajid ya samu abinda yake so, ya buga tebirin da hannunsa da karfi yana fadin. 

” Woman na nufin WO! MAN, ka shiga uku kenan. In har baka dauko Fa’izah ba kun zauna a garin nan tare Fa’iz kai ba namiji bane ungulu ne da kan zabo, duk wannan cika da batsewar naka. Shin wace ce Fa’izah? Me take takama da shi da 

take neman haukatar mana da Fa’iz haka? I dare you (Ina baka karfin gwiwa) kafin Fa’izah ta haukata ka, ko ta maida kai Fa’izah ta koma Fa’izun”. 

Su da basu san dawar garin ba sai abin ya basu dariya da yake da Turanci yake maganar. 

Fa’iz ya kufula, a fusace ya ce. 

“Uban waye ya ce da kai tsoron Fa’izah ne ya hana ni tahowa da ita?” 

Maajid ya ce, “Yo in ba tsoro bane mene ne wannan? Yarinya tana matarka, karkashin ikonka amma ka tsaya kana shayinta? Anya kuwa zaka iya lankwasa Fa’izah Fa’iz? Ni wannan so ya yi yawa, ka bata (power) sosai ko da ace laifin naka ne kamar yadda kake ikirari. Muna da sati biyu kwarara na kintsawa kafin mu fara aiki da British Airlines, kayi amfani da su kaje ka dauko Fa’izah ta zauna a damanka zuwa duk inda ka cilla kafa cikin duniya ko ma samu nutsuwar ka, ko da ace haukan gaske zata yi ba na karya ba, a Turai akwai (psychiatrics) da (Asylums) iri-iri (gidan mahaukata). 

Fa’iz kam tsiyar Maajid ta ishe shi, yana neman tona masa asiri gaban abokan su bayan ya kasance mutum mai son sirri a rayuwarsa, musamman idan abin ya hada ne da (personal-life) dinshi ba harkar karatu ko aiki ba. 

Sai ya mike ya dauko robar ruwa ya kuskure bakinshi ya furzar. Amma bai daina mishi azabar yajin da yake mishi ba,,. 

Maajid ya ciro karan sigarin dake bakinshi ya mika mishi. 

“Sha wannan, zai kashe ‘shatter’ (yaji)”. 

Ya dalla mishi harara, sai Javed Saddyqy ya tsiyaya sanyayyen lemun ‘shany’ cikin tanbulan ya mika mishi. Ya karba ya kwankwade ya dire kofin Javed ya kara bincire hancin ‘Rany’ ya cika tambulan again ya sake mika mishi. Wannan karon ma ba musu ya amsa ya kwankwade ya dire kofin. Sunyi haka har sau hudu, sannan Fa’’iz yaji dai dai, ya ce. 

“Shukran Yaa Siddiqy”” wato (thank you Saddyqy). 

Ya wuce su ya nufi (lifter) da zata kaishi dakinsa dake hawa na goma sha uku. Ya bude dakin ya shiga ya maida ya rufe. Kai tsaye na’ura mai kwakwalwa ya nufa, yana duba tsarin tashin jiragen su cikin satin inda ya samu akwai jirgin British da zai tashi zuwa Abujar Nijeriya a safiyar gobe. Kuma a goben ne hutun kintsawarsa zai fara. Kafin ya dawo ya kama aikin da aka dauke shi cikin nasarar da dukkaninsu basu zata ba. 

Ya tabbatar aurensa da Fa’izah alheri ne a gareshi, domin daga ranar da ya furtawa Hajjah yana son Fa’izah a aura masa ita don ya gyara zumuncinsu da ya bata yake ta ganin fatahi wato budi ta kowanne bangare cikin hanyar samun abincinsa, kai har ma da wata irin nutsuwa cikin zuciyarsa., 

Zama yayi a bakin kayataccen gadon dakin yayi shiru, ya rasa abinda ke masa dadi, haka ya rasa abinda ke cunkushe masa zuciya. Baya farin ciki da komai kamar yadda ya rasa walwalar sa dungurungum. 

Kada dai zancen Maajid ya kasance gaskiya ya zama FA’IZAH maimakon FA’EEZ. Tabbas yana tsoron haduwarsa da Fa’izah a karo na biyu, amma haduwar (is something inevitable) wato wani abu da ba makawa sai ya faru, don haka ya zama dole ya aro jarumtar dake neman kufce masa ya koma ya kawo karshen kalubalen da suke ciki shi da Fa’izar da gidansu baki daya da kowa cikin zuri’arsu da suka zame musu wake daya mai shegen doyi. Don haka cike da karsashi ya shigar da kanshi cikin jerin fasinjojin da jirgin British zai kwasa a safiyar gobe zuwa kasar haihuwarshi Najeriya. 

Da ya kammala ya janyo jakar tafiye-tafiyen shi ya soma shirya kayansa, cikin tarin nutsuwa da Ubangiji Ya halicce shi da ita. A karo na farko yayi tunanin gwada daya cikin (theories) din Maajid na lallashi ga Fa’izah duk da ya san ba wani tasiri zata yi ga Fa’izah ba. 

Rufe jakar yayi ya mike ya sauya kayan jikinsa, ya dauki wayoyinsa da (mastercard) dinsa ya fito daga dakin ya rufe. Mota ya dauka a harabar adana motocin dake cikin hotel din wadda ta kasance ta haya ce kirar ‘camry’ ya hau bisa kwalta a hankali. Bai tsaya ba sai a bakin wani (Jewellery shop) a tsakiyar birnin Wales ya fito cikin wandon jeans ruwan kasa-kasa da riga ARMANI itama ruwan kasar ce amma mai haske, yayin da wandon ya ciza sosai, saye a idanunshi gilashi ne ‘prada’ baki mai duhu wanda bai faya amfani dashi ba in ba a lokacin aiki ba. 

Ya tabbatar ajiyar da yake da ita cikin (master

— = 

card) dinsa sun isa da ya shiga wannan kantin domin ba kantin (fashion jewellery) bane, kanti ne na duwatsu masu madaukakiyar daraja (diamond, sapphire, gold, emirald) kadai. Kamin ya isa ga kofar shagon wadda ta kasance ta gilashi tuni ta bude kanta. Ya tsaya yana nazarin siraran sarkokin farin ‘diamond’ a wani bangare dake cikin shagon, ya zabi wadda yake ganin zata yi dai-dai da siririn wuyan Fa’izarsa, haka zoben dake hade da ita yayi bala’in dacewa da zarazaran yatsunta daya gani ranar da suka kantara masa kwalba… 

Ya yi murmushi shi kadai, ya kai hannu ya shafo lallausar sumar kansa daidai inda kwalbar ta huda, ya kame yazama tabo, ya dauka ya biya. Aka sanya su cikin gidansu mai martaba aka bashi tare da risidi (reciept) bayan an ciri kudin daga (credit-card) dinnasa. 

Akan hanyarsa ta komawa hotel din da suke, ya shiga shagon “NEXT” ya yiwa Fa’izah sayayyar sutturun NEXT samfuri daban-daban, riga ne, siket ne, wando ne, jacket ne, sweater ne duka ‘yan gidan ‘NEXT’ masu daraja ko daga kallon su a ido ba sai an tambaya ba. 

Daga nan shagon turaruka ya tsaya ya daukar mata gigitattun turarukan ESCADA (sentiment and magnetism) sannan ya dawo hotel ya hada cikin kayansa. 

A daren ya hada komai nasa cikin jakunkuna manya har uku, daya sayayyar Fa’izah ne taf, daya na Mama da kannensa, sai ta kayansa. Washegari ya biyo jirgin British mai zuwa Abuja. 

38 KOK 

a ya sauka a Abuja waya ya yiwa Yaya Sa’id yaje (airport) ya dauko shi, kasancewar Yaya Sa’idu Na’ibi kani ga Yaya Aliyu aiki yake a Abuja da (Federal Ministry of Agriculture) zuwa gidansa. Ya kwana ya huta suka sha hirarsu ta zumunci duka akan ‘yan uwa washegari ta kama asabar dama Sa’idun zashi gida Giwa, sai suka taho tare. Ya sauke shi Kaduna (Jabi Road) shi kuma ya wuce Giwa. 

Ba zato Mama ta ga Fa’iz yana sallama a kofar falonta. Wani dogo kuma katon saurayi (giant and gentle) ma’abocin kwaryjini, cikar zati da kamala da ya gama zama mutum, wanda in ka kalle shi dole ka sake, mace ne kai ko namiji saboda wasu ilhamomi da Allah Ya yi masa da ba duk maza Allah Ya mallakawa ba. 

Abubakar Mukhtar Abubakar (Fa’iz), kamar yadda cikakken sunansa yake, mutum ne (extraordinary) tun yana kankaninsa har girmansa, komai nasa daban yake da na sauran maza tsararrakinsa cikin A.B Bamalli House. Mutum ne mai matukar kyau da kwarjinin da idan ya shigo wuri sai kowa dake wurin ya ji shi (inferior) wato kasa dashi, ko da ya girme shi da shekaru, sai an san ya shigo saboda haibarsa, sai an san yana wuri saboda zatinsa. Sai an san namiji ne saboda kamalarsa. 

Duk da ya kasance mai kin ji da kiriniya a lokacin kuruciyarsa, shi ne da mafi soyuwa a zu

ciyarta cikin ‘ya’yanta guda tara, wanda kuma tafi shan wahala akansa kafin ya tsaya ya ginawa kanshi (future), wanda sai da ya shekara goma bai iya rubutu ba, ya kuma yi karatu ba tare da rubutu ba. 

Idan ta hada rayuwar Fa’iz gaba daya, daga yarinta zuwa girma, akwai baiwarwaki masu yawa a ciki. Ya kuma ci ace tun yana yaro sun gane yana da karama a fannin sarrafa abin hawa da (passion) akan duk wani al’amari da ya shafi injin hawa. Kai dai barshi da kabilanci da wariyar 

launin fata ga wanda ba ahalinsa ba ko ba jinin sa ba. 

Ta sauke idonta cikin nasa a hankali tana murmushi, shi kuma sai ya zarce da dariya yana fadin. 

“Ga bakon Mama babu sanarwa”. 

Ta amsa, “Ina maraba da wannan bako nawa duk da nasan wannan zuwan ba nawa bane”. 

Sai ya yi dariya cikin bagararwa ya zauna kasan kafafunta suka shiga gaisawa. 

Mama ta kasa zaune ta kasa tsaye da hidimar saukar (unexpected) bakonta, Abubakar-Fa’iz. Fitinannen danta (a da) amma dan lele a yanzu tunda ya auri abin sonta Fa’izah, ya kuma tsaya ya fuskanci rayuwa ya gina kansa irin yadda, ko ma fiye da yadda suke so ya fuskanta. 

Kalolin abinci har biyar da ta jere a gabansa sai da suka bashi dariya cikin jin dadin kulawar mahaifiyarsa gareshi yake fadin. 

“Duk ni kadai, ni Abubakar dan gatan Mama!”. 

Ta harare shi idanunta cike da kauna. 

“Ko kunya baka ji ba da abinda kake fada wai dan gata na, ina ruwana da kai, (after all) nasan ba wajena kazo ba. Amfani nayi da Hadisin Manzo da ya ce, “Bakonka-Annabinka…” da kuma kasancewar mai yin bata kusa da ina ruwana da hidimar ka?” Dariya yake yi wadda ya manta rabonshi da yin irinta, watakila tun kafin Fa’izah ta shigo tayi sallama cikin sabuwar rayuwarsa ta baya. 

Ya ce, “ya yi min yawa ne Mama”. 

Ta yarfar da kai, “Ko da baka cinye duka ba dai ka daure ka dan tsakura, don wadda kake rawar jiki da dokin ganin ba baka zata yi ba”. 

Murmushi ya yi, ya dauki (spring roll) mai taushi ya sanya a bakinsa ya gutsira yana ci. ‘Yan kannenshi su Junior duk sun zagaye shi suna tambayar shi yadda sama take. 

Ya ce, “Kuje ku tambayi malamin ‘Geography’ dinku (I’am not an astronomist)”. 

Shu’aib ya ce, “Yaya Fa’iz nine planet suna yi muku magana a sama?” Shi kuwa Yahya cewa yayi, “Wai Yaya ta saman su kuke bi ko ta kasansu?” 

Junior ya ce, “Yaya bakwa take su?” 

Ya zuba lemu ‘Don-simon’ cikin tambulan ya ce. “Kai don Allah ku saurara mini, na ce (I’m not a geographer, neither an astronomist) amma ku bari na muku alkawari ranar dana shiga duniyar wata (journey to the moon) na dawo zan amsa muku wadannan tambayoyin naku”. 

Sai Yahya ya ce, “Amman da Fa’izan gidan Ba

ban ABU ce ta tambaye ka da ka gaya mata ko Yaya?” 

Fa’iz ya dauke wuta, cikin mamakin kalaman yaron, dariya ta kama Mama amma bata yin ba sai a zuci. Ya tsurawa yaron ido yana kallo cikin hada amsar da ya kamata ya bashi, kafin ya samu ya harhada sai Shu’aib ya ce. 

“Kasan ko tun ranar da Fa’izah suka zo da Aunty Ummi daga Kano muna gyaran dakinka ta zo ta leka dakin ta tambaye ni na ce mata ku za ku dawo, bata kara zuwa gidan nan ba”. 

Yahya ya ce, “Ai bata son sa, kaga wannan tabon na goshinsa ma ance ita ta ji masa”. 

Junior ya ce, “Kai ya akayi ka sani?” 

Ya ce, “Rannan ina dakin Aunty Zainab (Maman su Yaya Aliyu) naji Ummi na gaya mata har tana cewa tayi asara…”. 

Da sauri Mama ta cira ido ta dubi goshin Fa’iz a hanzarce, Fa’iz bai san sanda yasa kafa ya kaiwa Yahya wani mugun hauri ba, Mama tayi sauri ta rike kafar gam, ta ce. 

“Kada ka karya min yaro, ba shi ya kar zomon ba balle ka rataya masa, ba a bakinsa na fara ji ba. Waye bai san Fa’izah ta kwada maka kwalba ba? Ni dai rokona akan ka duk rintsi kada ka biye mata domin ka cancanci hakan daga gareta ko ma fiye. Ka ringa yi kana TUNA BAYA… domin TAKORI ta ce “TUNA BAYA SHI NE ROKO” sai dai ina da yakinin yadda komai a rayuwa ke zuwa ya wuce (with time) kiyayyar Fa’izah mai wucewa ce tunda kaima sanda kake kinta baka kayyade lokacin daina kin nata ba. Zuwa ya yi da 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *