ZUMUNTAR KENAN BOOK 3 CHAPTER 9 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
kansa, don ma anfi karfinta ne amma da ko kusa baka cancanci auren Fa’izah ba, Aliyu shi ne mutum mafi dacewa da auren Fa’izah ba kai ba Fa’iz!”.
Banda Mama ce, UWA! Wa ya isa ya dubi tsabar idonsa ya gaya mishi haka
Ya yi kwafa kamar zai hadiyi zuciya ya mutu don takaicin kalaman Mama, ya yi shiru yana gwama numfashi kamin ya dubi Mama cikin sanyin jiki. “Wa yafi karfin nata? Gaba daya cikin ku wa yafi karfin nata a yanzu Mama? Cikin ku duka an rasa mai sanya baki a bani matata kamar yadda aka baiwa kowa tasa, saboda ita ishasshiya ce kowa yana tsoronta. To ni kam na zo daukar aurena ne (dead or alive)!”
Mama tayi dariyar da ta kara kular dashi, ta ce. “Kofar hanyar Zaria a bude take ai kullum Fa’’iz, kai da baka tsoronta sai ka je ka dauki abarka, munji mu tsoron ta muke ji kada muje ta fasa mana kai kamar yadda ta fasawa jarumi Fa’izu Abubakar”.
Haushin maganganun Mama koko ya ce shagube ko gugar zana yasa shi mikewa ya nufi dakinsa ba tare da ya kara tofawa ba.
Yayi wanka, ya zuba shaddah ‘‘getzner’ koriya sharr. Ya bi jikinshi da turaren (212). Bai dauki sanya hula da muhimmanci ba kasancewar sa mai tara sumar kai da bata (extra) kulawa, don haka yau din ma bai sa ba. Ya zura lafiyayyun takalma budaddu bakake sidik kirar Thailand. Ya jawo kayanshi da ya zo dasu ya ware tsarabar da yayowa Fa’izah wadda dama ya wareta cikin (troller)
—=
guda.
Ya daga ido ya dubi jerin akwatunan dake girke a gefe masu suna lefen Fa’izah wanda har yau babu wanda yace ya kawo a kai mata duk da an kai na Yaya Bash da alama ma da baya nan anzo an bude an zari wasu.
Ya kwalawa su Shu’aib kira, ya ce su fidda akwatunan su zuba mashi a ‘Roll-Royce’ din Baba da ita zai fita. Suka kwashe har ta tsarabar, ya fito ya nufo dakin ya isa sashin Mama ya shiga ya Zauna cikin lumtsuma-luntsuman (leathers) dinta. Tana jera kayanta a sif ta amsa mishi sallamar kafin ta juyo. Tayi murmushi ganin yadda ya hade kamar wani angon so, nan kuwa angon ki ne, shi kuma sai ya fara sakin tsaki.
Ta ce, “Ya akayi? Sai ina kuma ango sha kamshi? Ko sai Zariyan?”
Ya ce, “No Mama, ina son zuwa gidan yaya Bashir ne, bana nan suka tare”.
Ya sha mur sosai ya ja fasali ya ce.
“Yanzu Mama da ita mutuniyar kirki ce da bamu je tare ba?”
Tayi dariya ciki-ciki kamar bata gane wa yake nufi ba, ta ce.
“Ita wa?”
“Fa’izah mana!””.
Tayi ‘yar dariya, “Mutuniyar kirki ce mana”.
Ya yi tsaki, “Ban ga alama ba. Yanzu don Allah Mama da gaske kike ba zaki sa baki Fa’izah ta sakko mu tafi tare ba? Na gaya miki British Airlines sun dauke ni aiki, zan fara sati biyu masu zuwa don haka (most of my stay now will be in
Wales, London and Scotland) ba zan iya zaryar zuwa gida akai-akai ba sai bayan watanni ukuuku.
Zai fi sauki idan muna tare a duk inda nake don samun cikakkiyar nutsuwa da kwanciyar hankalin gudanar da aikina yadda ya kamata. Ki taimaka min Mama, ni kadai ba zan iya ba, kunyi min aure amma kun barni ni kadai da yakin kwatar sa, baku cika ladar ku ba”.
Mama ta ce, “Kaga babu ruwana cikin rigimar ku, can muku. Wanda ya jawo ruwa shi kadai zai doka. Yadda Fa’izah ke ganin bakin kowa kan maganar auren nan banda ni, sannan kazo ka tsoma ni ciki, salon ta ce na bi bayanka don ba ita na haifa ba? Bayan sanda kake tsula mata tsiyar ka baka nemi taimakona ba idan kuma na hana ka ba ka ji. Kowa ya debo da zafi, bakinsa”.
Kamar zai fashe da kuka, “Amma Mama haka za’a zuba mata ido tana yin abinda taga dama, ni me na yi mata da zafi haka? Don kawai ina cewa ta dinga tsafta kamar su Zanirah? Ni ba dukanta nake ba, ba zaginta nake ba…”.
Ta tare shi, “… in ita baka zageta ba, ai ka zagi uwarta, kana tsammanin ‘ya’ya mata suna yafe wa in an taba musu uwa?”
“To ba na ce ayi hakuri ba? Waye kuruciya bata sa shi yin kuskure? Babba ma yana aikata kuskure balle yaro karami kamar Hafizin Hajjah!”.
Sai ya bata dariya a yanayin yadda ya yi maganar, ya kuma bata tausayi duka a lokaci daya. Ta dan dube shi tayi murmushi, da gaske cikin
damuwa yake, duk jarumtakarsa damuwar ta kasa buya.
Lallai ta yarda SOYAYYAH halitta ce mai zaman kanta, kuma (reality of man’s existance)… sannan bata shawara da kai idan ta shirya yin awon gaba da kai, da ta tabbata bai barta tayi wannan tasirin mai yawa a kansa ba, kasancewarsa namiji daya da daya mai ra’ayi da akidu da ‘principles’ masu zafi.
A yanayin yadda tayi magana yanzu ya fahimci ta fara jin tausayinsa ta kuma fara fahimtarsa amma bata so ya gane hakan. Cewa tayi.
“Kai da baka tsorontan me ya hana ka yin maganar? Ba matarka bace? Ko ko zaman dadiro ka nema ba hakkin ka ba?”
Ya yi wani irin murmushi, yanzun kam ya fuskanto inda Maman ta sa gaba, wato itama zaman Fa’izar a gidansu ya dameta illa alkunya da kara irin ta mallawan usli don haka ba zata bari aji daga gareta ba sai dai shi din. Ya mike zai fita, wannan karon cike da kuzari, sai ta ce.
“Akwai kudi a aljihunka ne? Motar babu mai, naji Hadi yana fade dazu”.
Ya shafa aljihunshi akwai kudi, amma ‘pounds sterling’.
Ya ce, “Ban je canji ba sai zuwa gobe insha Allah”.
Ta bude jakarta ta fiddo bandirin ‘yar Sardauna dauri uku ta mika masa, bai yi musu ba ya sanya hannu biyu ya amsa yayi godiya. Ita kuma tayi hakan ne don sanin halin sa, ya gwammace ya zauna baya da ko sisi da ya tambaye su ko kwan
dala.
Ummi da angonta Yaya Bashir suna cikin (kitchen) suna hadin (burger) da suke so su ci. Da ya fito sashen Mama a bakin kofa suka yi karo da Shu’aib ya tambaye shi kwatancen gidan Yaya Bashir.
Ya ce, “Yaya Fa’iz muje mana in raka ka, nan ne Kabala Custain ba nisa”.
Ya ce, “Amma da kanka za ka dawo? Don ni daga can ba gida zan dawo ba”.
Shu’aib ya daga mishi kai suka jera suka fito suka shiga motar Baba, Fa’iz ya ja motar a hankali suka fita daga gate din gidan nasu.
Ummi ce ta fara hango shi ta tagar (kitchen) din wadda ke santar harabar adana motar su. Tayi ihu harda dan tsalle ta ce.
“Ya Fa’iz in town”.
Suka fito da sauri ita da Bashir suka game dashi a main falonsu. Daga matar har mijin bakin su yaki rufo sai jera masa sannu da zuwa da yaya hanya suke yi yana amsawa da ka, yana dan yatsine fuska. Ya bi daya daga cikin lafiyayyun kujerun falon ya nitse. Takaici ko kishin yadda yaga Ummi da Bashir ne suna rayuwarsu babu abinda ya dame su duk sunyi haske sunyi kiba, koko tunanin tashi ‘yar bala’in amaryar ne yasa shi yatsine fuska oho! Da irin tarbar da shi zata masa? Allah kadai Yasan ZUCIYAR MUTUM (sunan wani littafin TAKORI).
Suka zauna kusa da shi suna manne da juna. Ya dube su sai ya saki fuska.
“Mr. and Mrs.”.
Suka hada baki wurin cewa, “Allah Ya taimaki angon Fa’izah!”.
Ummi har da jinjina da hannunta.
Bashir dariyar shegantaka yake mishi ganin yadda ya zabge amma ba zai fasa halinsa na rainawa mutane wayau ba da ginshirar babu gaira babu dalili ya ce.
“Shin Pilot Giwa yayi ciwo ne?”
Yace, “Lafiyata kalau, me ka gani?”
Tare da cin laya kada su kawo mishi shegantakar da ba zai dauka ba, amma sai da Ummi ta ce. “Kaima dai dear! Fa’izah’s calamity mana! “Yar banza Bakin Bunu Bata Baibaya…”.
Ji yayi kamar shi ta zaga, kuma dai shi baya son a dinga shigar masa rigimarsa da Fa’izah ko ace tayi ba dai-dai ba, zai fi son ka zauna a gaban sa kayi ta yabonta kana bashi labarin rayuwarta fiye da nuna kana taya shi takaicin abinda take yi akansa. Ya share zancen da cewa.
“Shin kuna lafiya? Na same ku lafiya?”
Bashir ya ce, “Gani ya kori ji”.
A yayin da yake tuttula mishi (fresh milk) din Peak cikin tambulan din dake hannun Ummi, ta mika mishi ya daga mata hannu.
“Barshi, bana tare da yunwa, Mama ta bani abinci na ci”.
Ummi cikin rashin jin dadi ta ce, “Amma ta yaya zaka shigo gidanmu ka fita ko ruwa baka kurba ba?”
Kamar zata fashe da kuka, sai ya mika hannu ya karba ya shanye ya dire kofin bisa (center table).
“Na yaba da tsarin gidanku, Allah Ya ba da zaman lafiya. Ni zan wuce”. Ya mike.
Dan uwa rabin jiki, Yaya Bashir sai yaji tausayin Fa’iz ya kama shi duk da basu cika shiri ba ya gano damuwar dake tare dashi da halin da ya shiga ganin irin rayuwar da suke yi shi da Ummi suka mike suka fito tare da shi.
Bashir ya ce, “Wai ina Fa’izar ne?”
Ba tare da ya juyo ba, kamar yadda bai fasa tafiya ba ya ce.
“Tana nan”.
Ummi da Bashir suka hada ido suka yi murmuishi, shi kuma ya sake hade rai da fuska har da tsuke baki kada su kara tambayarsa game da Fa’izah, kowa yayi (minding business) dinsa. Ita kuma Ummi bata fahimci hakan ba, sai ta ce. “Don Allah ka kawo min ita mu wuni yaya Fa’iz, na matsu in ganta, nayi-nayi tayi hakuri ta ki saurarona…”.
Sai kawai ya samu bakinsa da furta, “Me kika yi mata?” Alhali bai yi niyyar yin furucin ba.
Ummi ta ce, “Matsalar mu ce, amma ka tambaye ta mana, ai kunfi kusa”.
Sai yaji kamar shaguben da yake gudu suka yi masa. Ita kuwa Ummi tsakaninta da Allah ta fada, ta kara da cewa.
“Sai yaushe za ku tare mu zo rakiya?”
Ji yayi kamar Ummi ta zage shi, ya ce.
“Ummi, ina wasa dake? To babu rana babu wata!”.
Dai-dai sanda suka kawo inda ya yi (parking), Shu’aib na zaune bencin megadi suna hira yana
jiransa. Ya bude boot din motar yasa Shu’aib ya fitar musu da tsarabar da ya kawo musu. Electronics ne na amfanin (kitchen) cikin kwalayen su guda biyar samfurin ‘Binatone’ microwave, juicer, mixer da ‘rice boiler’ sai ‘blander masu karshen (quality).
Shu’aib ya shigar musu da su gida ya dawo suka shiga motar suka tafi, Ummi da Bashir na godiya suna daga musu hannu har suka fice daga harabar gidansu suka hau titi.
Yana tukin ya dan juyo ya dubi Shu’aib ya ce. “Yo kai in haka ne ai zaka yi min amfani wajen sauke kaya, shige muje Zaria kawai”.
aE OK RK
A ZARIA
A
wannan rana wadda ta kasances asabar din karshen watan Agusta cikin ‘Area One’, Walida da Abdallah duka suna gida sunzo hutun karshen zangon karatu na biyu daga makarantun su daban-daban.
Ina kwance cikin dakin Walida wanda yanzu ya zama nawa tunda ita ba zaman gidan take ba, sanye da riga da zani na atamfa mai karshen tsada (Exclusive Sharaton) ruwan ganye mai ratsin hoda, kaina ban daura kallabin atamfar ba yana dai ajje gefen gadon, na hade gashin kaina cikin tafkeken ‘hair-bound ina karanta sabon littafin Takori ne mai suna ‘KWANA SITTIN’. Zuciyata ta tafi gaba daya cikin rayuwar (schezophrenic_Safeenah) mai tsananin ban tausayi. A
wani bangaren, ba Safeenar nake tausayawa ba kamar Kabir Danbatta, na rasa shi da Dr. Dangi wa yafi dacewa da amsar ragamar rayuwar Safeenah? Kowannen su masoyinta ne na hakika. Muryar oyoyon da Walida ke yi ya katse min karatun, na bi hadaddun jakunkunan da Shu’aib ke shigowa da su dakin namu yana dora daya kan daya da kallo ina kissimawa cikin raina, wane irin baki ne muka yi masu tafe da jakunkuna ‘classic’ haka kuma har dozen? To kwana nawa suke nufin za suyi a gidan namu?
Kamshin sassanyan turaren (212) na maza ya sirnano cikin hancina, wani irin kamshi da ban taba jin mai sanyi da dadinsa a duniya ba. Wadanne irin baki ne momi tayi haka? Abinda nake tambayar kaina kenan.
Daga inda nake kwance na jiyo muryar ma’abociyar ginshira, na tambayar Walida ina Momi da Baba?
Walida ta ce, “Momi na gurin aiki, Baba na cikin makaranta. Amma Yaya Fa’izar tana ciki tana karatu”.
Da murmushi fal a fuskarsa ya ce.
“Karatu? Ko dai kuka Walida?”
Ta ce, “Wallahi karatu take, kullum ma karatu take, ta je kasuwa ta sayo littattafan TAKORI na da dana yanzu, su take karantawa kullum, ta daina kukan tuni…”.
Muryar FA’TZ, FA’IZ GIWA, FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA!
Da kwarin gwiwarsa ya yi sallama a dakin cikin ‘husky voice’ din da Allah Ya yi musu baiwarta
zuri’ar Abubakar Bamalli Giwa bakidaya. Ya samu wannan kwarin gwiwar ne daga labarin da ya samu a bakin Walida masu nuna na kwantar da hankalina tunda har ina karatu? Duk da kwakwalwarsa bata fahimci littattafan TAKORIN da Walida take bayani akai ba, ya dai fahimci NOVELS ne wanda ba zai ce na Hausa ne, na Turanci ko na Larabci ba, tunda bai san mene ne ma’anar TAKORIN ba, bai ma taba jin kalmar ba cikin kowanne yaren. Abinda ya fahimta shi ne TAKORIN ‘is an author’ tunda yaji ance NOVELS dinta. Banda wannan kwarin gwiwar da ya samu ya samu karin na Momi da Baba duka basa nan yadda zasu ji dadin babbaka juna a wuta idan ta kama. Babu mai ceton dayansu. Yau za ayita ta kare (he can no longer tolerate it anymore!!! Kamar yadda ya ce da Mama ne ya zo daukar aurensa (dead or alive) haka yake har zuciyarsa.
In har littafin labarin SAFEENAT MAHMOUD ALKALERI wato KWANA SITTIN na Sumayyah Abdulkadir ya amsa, to nima Fa’izar da ake yiwa sallamar na amsa. Ya shigo kansa tsaye Walida na biye dashi kamar bakinta zai tsage don murnar ganinsa ta iso har gadon da nake kwance, da murnarta take fadin.
“Aunty Fa’izah ga Yaya Fa’iz!”.
Wani irin kallo nayi mata wanda nake jin tunda Momi ta haifeta babu mahalukin da ya taba yi mata shigensa, ba shiri ta juya har tana cin karo da (stool) din madubi, saura kadan ta kifa.
Da sauri Fa’iz ya riko hannunta ya rike gam.
“Ina zaki matas? Ke da nazo muyi zance? Zauna
— >
hira za muyi kafin su Momi su dawo”. Walida a daburce take, ya jata suka isa har gefen gadon da nake kwance suka zauna har rigarshi ta rufe min kafa kadan. In banda kamshin sassanyan turaren shi ba abinda ke tashi a dakin. Ya bige da tambayar Walida sha’anin makaranta tana bashi amsa a darare, kokarin zamewa take ta barmu yana kara shimfido mata tambayoyi akanta da kannenta su Waild, Kausar da yayanta Abdallah da nasu karatun.
Ganin ba zai barta ta tafi ba ta ce, “Yaya Fa’iz bari in kawo maka ruwa da lemo in kaiwa yaya Shu’aib abinci falo”.
Ya ce, “Kada ki damu Walida, na cika cikina a Kaduna, haka shima Shu’aib. Yaushe Momi za ta dawo?”
Walida ta kalli inda nake bamu hada ido ba, amma taga yadda kwayar idanuna suka kada suka yi jajawur, numfashina ke sauka da sauri-da-sauri har wani irin huci nake kamar mesa babu rahma cikin su dai-dai da kwayar zarrah.
Walida ta kara rudewa ta ce, “Na jona ruwa a (heater) Yaya Fa’iz ka barni inje in kashe kada ya kone fada Momi zata yi min”.
Ya ce, “To kiyi sauri nima ba zama zanyi ba, sako zan baki wurin Momi sai mu wuce”.
Tace, “Toh”.
Da saurinta ta fice har tana sake tuntube da dokin kofa.
Ya girgiza kai ya mike ya sauke ido a kaina, tsayin mintuna biyu yana kallona kawai babu ko kiftawa. Nima kallonsa nake, wani irin kallo da ni
kaina na kasa fassara shi, na takaici ne ko na kiyayya koko na gara da Allah Ya kawo ka? Ni kaina ban sani ba.
Daga ni har shi babu mai niyyar daina kallon, duk da shima na kasa fassara nashi kallon. Shi ba kallon so ba, ba na kiyayya ba, ba na jin haushi ba. Yafi kama da kallon iko da raini. Ta wani fannin tamkar kallon, “Baki da yadda za kiyi dani” koko kallon “Nafi karfinki da ke da duk abinda kike takama da shi.
(in another notion) kallo ne na “Yarinya na ci dubu sai ceto, kiyi duk abinda za kiyi” Sai da ya mula don kansa ya ce.
“To ni Aunty Fa’izah zan wuce Giwa, tunda na iso Hajjah bata ganni ba, lefenki na kawo miki, wanda kowa ya kasa kawo miki tunda kin zama Faskari, mai faskarawa mutane kai. Sai tsarabar da nayo miki a tafiyar da nayi, tunda babu gaisuwa ko ta Musulunci a tsakaninmu.
Daman nazo ne in shaida miki zaman nan ya isa haka! Ranar (monday) kwana ki shidda kenan masu zuwa ki kimtsa kayanki da duk abinda kike bukata za ki tare a gidanki kamar sauran ‘yan uwanki, don gaskiya fisabilillahi kin takurawa su Momi da alama har su Walida kin takura musu, nima kuma kin takura min. Haka kawai ina da mata amma bani da maraba da gwauro. Gara mu kauce haka muma mu manta komi, da duk abinda ya faru a baya, mu fuskanci sabuwar rayuwar dake tunkaro mu, muka kuma bude ido rana daya muka ganmu cikinta. Wato rayuwar aure. Sai mu rungumeta, mu kasance cikin godiyar Ubangiji da