ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 2 by Sumayyah Abdul-kadir

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Abin ya baiwa Surajo dariya, in wani ne ya bashi labarin Abubakar Mukhtar (sunan da suke kiranshi) zai koma haka akan mace karyatawa zai yi. Soyayya ba karya bace, a yau ya kara yarda da hakan. Ya shiga girgida kai kamar kadangare.

“Tana ina ne? Ban ji motsinta ba. Ga hotunan (cocktail) din ku fa na wanko”.

Ya amsa ya aje gefe ba tare da ya bude ba yayi mai nuni da (kitchen) da girar shi.

Dariya Surajo yayi, “Kace har girki ake mana!”.

Shima dariyar yayi, “Mai dadi kuwa”.

Suka yi ta dariya kamar wasu shashashan madina, sai da suka yi mai isarsu tukunna.

Surajo ya ce, “To yanzu yaya za’ayi batun tafiya UK?”

“Sai yanda ta yiwu Surajo, bani da sauran dabara, duk abinda zan iya nayi, na bada hakuri, nayi fada, nayi wa’azi, nayi nasiha. Zan iya cewa (there are lots of improvements) sai dai bata yi min magana, sannan in nayi bata amsa min da baki, sai dai tayi a aikace. Kuma ba musu, ba rashin kunya, duk abinda nasa ta daga jiya zuwa yau tana yi”.

Surajo ya ce, “To Alhamdulillahi, hakuri (still) ba abinda baya bayarwa. Kuma ina ganin inta bar kasar zuwa inda bata da kowa komai zai tafi (normal)”.

Ya ce, “Nima tunanin da nake kenan, amma Surajo (how easy is that)?”

Dai-dai lokacin da na fito daga (kitchen) dauke da fadi ka mutu ina jerawa akan (dining). Duk suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su. Jikina ya bani zancena suke yi. Zan koma (kitchen) Suraj yayi gyaran murya.

“Madam ba gaisuwa yau ma?”

Ina tafiya ban tsaya ba na ce, “Ina kwana?”

Ya ce, “Lafiya lau, sannu da aiki”.

Na ce, “Yauwa”.

Na shigo don dauko filas din ruwan zafi. Suka dubi juna suka yi murmushi.

Tare suka karya kumallon shi da Surajo yana tambayarsa abinda yaji masa ciwo. Ga ammakin Fa’iz sai ya kasa gaya masa kada yayi masa dariya don a hakan ma bai daina mamakin canzawarsa da rauninsa ba, gani yake yayi min sako-sako da yawa. To abin ne shima yazo amsa ‘beyond comment’ (sunan wani ganyen shayi), idan yana gaban Fa’izah manta kansa yake da (identity) dinsa.

Cewa yayi yankewa yayi da reza ya ce.

“Kai me ya hadaka da reza kamar wani wanzami?”

Ya ce, “Don Allah ka kyaleni haka Surajo, kwakkwafin ka ya isheni”.

Wata irin dariya Surajo yayi wadda ke nuna ko dai bai gano ba to ya kusa ganowar. Ni kyale su nayi na koma daki na kwanta don rama bacci.

***

Ban jima da kwanciya ba bacci ya dauke ni, ba ni na farka ba sai azahar. Nayi wanka nayi (brush) ba don banyi na safe ba sai don inji dadin cin wani abu. Domin da mahaukaciyar yunwa na tashi. Na fito falo na duba (dining) na tarar da (plate) daya da basu taba ba, na hada ‘tea’ mai kauri na fara warware hanji na dashi sannan na zauna na soma ci. Na kammala na kwashe komi na hada da wadanda nayi amfani dasu a (kitchen) na wanke. Na adana komi wurinsa.

Dana kammala sai kadaicin ya isheni, na kasa zama wuri daya. Tunanina ya bani in zagaye gidan cikinsa da wajensa in gani, sai na sanya mayafi da (slippers) na fito harabar gidan na zagaya baya.

Dawisu ne guda biyar (peacock) mata da maza, wasu a kasa, wasu akan katanga sun bude kyawawan jelunansu abin gwanin ban sha’awa. Sai na gane sune ake maganar su jiya sun kwanta da wuri. Na debi dawar da na gani cikin buhu a kofi ina cilla musu da dai-daya. Sai ga wani saurayi ya bullo yayi min sallama, na amsa muka gaisa. Jiya ban kalle shi ba balle in san kamanninsa, da yayi magana ne na gane shi.

“Kai ne Ya’u?”

“Eh, ni ne Madam. Wannan aikina ne, don Allah ki bari zanyi, basu dade da cin abinci ba”.

Nayi murmushi na ce, “Ka dinga share kashinsu daga yau kawai Ya’u. Ina so na karbi ragamar ciyar dasu da hannuna, ina son Dawisu Ya’u”.

Sai yayi dariya ya ce, “Hakan ba zai zama matsala gareni ba wurin Yallabai?”

Nayi murmushi nima, “Ba zai ji ba insha Allahu”.

Ya ce, “To Allah Ya ba da lada Aunty”.

Na amsa, “Amin Ya’u”.

Ya wuce ya barmu, na ci gaba da jefa musu dawa duk suka yo gabana suna dauka da bakunansu masu kyau suna kara baza bindi.

***

Cikin wannan yanayin kwanaki suka ci gaba da mirgina mana har muka kwana goma, ranar Juma’a da yamma naji kugin mota, sai dai ba irin na motar Fa’iz bane. Na mike na daga labulen falo, sai na hangosu Walida, Shu’aib, Yahya, Junior, Abdallah, Kausar da sauransu suna fitowa daga mota, direban Mama Malam Sani ya kawo su, kowanne da ‘yar karamar ‘troller’ din dana tabbata kayan sanyawarsu ne a ciki, yadda dai na gansu a gidan Ummi.

Wani irin farin ciki naji ya rufeni don dama ina fama da kadaici da kewar su. Har da hadawa da gudu wurin bude musu kofa, kowanne yabi lafiyar kujera yana wash-wash, ‘ya’yan hutu malam. Manyan su Shu’aib ne kawai basa cewa wash din, sai gaisheni cikin girmamawa.

Na nunawa Junior dakin dake kusa dana Fa’iz shima (bedroom) ne (single) ba falo, ba abinda babu na ce su mazan su kai kayansu can, matan suzo mu hadu a nawa dakin sai ina-naka-saka nake dasu.

Kausar ta kwantar da kanta a cinyata kasancewarta shiru-shiru ba kasafai ta fiya magana ba.

Na ce, “Wai daga ina kuke ne?” Walida ta ce, “Gidan Aunty Ummi”.

Na ce, “Tun (last week) dana baro ku kuna can?”

Suka ce, “Eh”.

Kausar ta dago kanta daga cinyata ta ce, “Koro mu fa suka yi ita da Yaya Bashir, yau ya dawo bayan hutun mu bai kare ba”.

Abdallah ya ce, “Kora da hali dai ba kora ta ku tashi ku tafi ba”.

Nayi musu kallon son jin karin bayani, dariya na son kama ni. Walida ta dora bayani.

“Saboda Yaya Bashir ya dawo ta barmu a falo tun safe, sannan bata dora mana (break) da wuri ba, suka kyalemu yunwa na cinmu. Da ta fito bata hada mana ruwan wanka ba, ta ce kowa yayi da ruwan sanyi wai hitar (toilet) din gidan duka ta lalace. Ki dubi sanyin nan da ake.

Shi kuwa Yaya Bashir din kai tsaye daya fito ya ce mu hada kayanmu mu koma gida, wai mun cika mishi kunne”.

Dariya nake kamar cikina zai fashe, Walid ya karasa.

“Tunda dama hutun sati biyu muka je sai yaya Junior ya ce muzo nan kawai mu karasa kwana biyun mu sai mu koma gida, don dama Monday duk zamu koma (school) ke kam mun san ba za kiyi mana abinda Aunty Ummi tayi mana yau ba”.

Na janyo autan Momi jikina ina dariya, “Ina kuwa zanyi muku Walid? Ni farin ciki nake da zuwan ku, inma kun dawo gidan kwata-kwata ne (you are most welcome) dakunan gidan zasu ishemu”.

Duk suka hau murna sosai.

Na ce, “Yanzu me zaku ci?”

Abdallah ya ce, “Chicken burger?”.

Yahya da Junior suka ce, “Shinkafa da salad”.

Shu’aib ya ce, “Quaker oat kawai zansha da ‘peak’ ta ruwa”.

Kausar da Walid suka ce, “Wake da shinkafa da mai da yajin tafarnuwa”.

Taashin hankali gobarar gemu, (inji hawwa lawan meturare) tawa ta sameni ni Fa’izah. Na fada cikin raina, naja numfashi.

“Uhm! Gaskiya abin naku (is too much). Dankari! Sunan wata jarida, dole Ummi tayi muku kora da hali har da sandan ma in tana dashi, in haka kuke kullum to tayi bala’in kokarin rike ku har kwana goma. 70% na abubuwan da ku ka lissafo bani da kayan hadinsu, kuma ko inada su jikina akwai jini da bargo ba zan iya ba. Chicken burger da Indomie kawai zan yi muku dukkan ku. Shi kenan?”

Gaba daya suka ce, “Eh, ya isa”.

Banda Yaya babba (Shu’aib) shi harar su ma yake, ya ce.

“Ai basu da hankali ne”.

Na ce, “Naga alama Yaya Shu’aib”.

Gaba dayanmu muka shiga (kitchen) banda Shu’aib, aka zage ana aikin hada burger, mai yanka tumatir da salad daban, mai baking da blending tsokar kazar da za’ayi amfani da ita shima daban. Haka mai tsaga biredin da shafa masa mayonnaise da salad cream shima daban. Nan da nan aiki ya kammalu kowa da (plate) dinsa ina ta rabo Fa’iz yayi sallama ya shigo. Sai kuma ya tsaya turus! A bakin kofa yana kallonmu, hannunsa dafe da habarsa. Yake fadi cikin kidayawa da dan alinsa.

“1,2,3,4,5,6,7… duk a dan gidana? Ina zamu kaiku? Gaskiya ba zai yiwu ba, ba kuma zata sabu ba wai bindiga a ruwa. Banda dukkan ku taron mahaukata ne ana zuwa gidan mutane ba (notice in this century?) Kuma wai kwana? Ba daya ba har biyu? (Look at you all with your noses like hippopotamus’s”. (Dube ku duka hancinanku kamar na bauna).

Suka aje lomar burger hankali tashe, rai bace. Ya samu kujera ya rage tsawo, ya dora kafa daya kan daya yana karkada ‘yan mukullayen motarshi, ya sake fadin.

“Wai da ba gidan Ummi na ganku ba?” Walida tayi rau-rau da ido, “Ai sun koromu…”.

“Au, shi ne ni aka zo aka tare min? Ga gidan dan iska ko? Abokin wasan ku?” Suka yi shiru tsuru-tsuru dasu abin tausayi, da alama wani abu ya bato masa rai a waje yazo ya huce a kansu.

“To kuje kuci abincin duk kuzo in kaiku Jabi Road, ba mai kwanar min a gida”.

Kausar ta sha mur, Abdallah ya turbune, Junior ne mai karfin halin musantawa.

“Haba don Allah Ya Fa’iz! Ka barmu mana? Don kwana biyu kawai?”

Yahya ya yi kicin-kicin da fuska, “Kaima in kaje gidanmu ai Mama bata korar ka, daki ma take baka”.

Fa’iz ya fiddo ido waje saura kadan dariya kufce mana ni da Shu’aib, ya ce.

“Kuji min marasa kunyan yara, ina fade kuna fade? To wallahi ba zaku kwana ba, ko ana dole? Bana son bakuntar, aje na gode. In ba wuni ba kada wanda ya kara zuwar min gida kwana, OK?”

Tsit suka yi, sannan suka karasa cinye abinda suke ci. Duka suka mike cikin sanyin jiki suka dauko jakunkunansu suna ja a hankali duk suka bani tausayi. Wato mai hali baya fasa halinsa. In ka jima baka hadu da mutum ba, tambaye shi wani abin amma banda halinsa. Shi kuma irin tasa ZUMUNTAR KENAN!

Idanuna suka cicciko da kwalla amma na rantse ba zanyi magana ba tunda nasan don inyi maganar ne kawai da bashi da alfarmar samunta haka kawai shi ne yake neman dalili.

Suka yi waje, ya tashi ya bisu yana, “Oya! Kuyi sauri ku shige muje”.

Kamar ya samu wasu tumaki, haushi da takaici ya sake kamani. Na kudurta a raina duk yadda za’ayi yau ba zan gasa kazar da (chips) ba ladan korar min kanne. Sai dai nima ya kore ni.

Anan kan kujerar da nake zaune ina sakawa da kwancewa barci ya kwasheni, har ya dawo ya rufe ko’ina ya kashe kayan wuta ban sani ba. Sai ji nayi yana tashina ta hanyar kiran sunana da jan babban yatsan kafata.

“Yaya banga (chicken) akan (dining) ba?”

Na mike na kalle shi cikin matukar fushi amma na kasa magana, na mike tsam kawai na shige dakina na rufo kofa, garam!

Da safe ma kin fitowa nayi in dora karin kumallo duk da jiya ya ce in dora da wuri zai je Abuja da sassafe kan visar sa. Har bakwai da rabi ban bar gadona ba, duk da ba barci nake yi ba.

Ya tabbatar bazan fito din ba balle in bashi ko ruwan zafi, sai ya iso kofar dakina yana balle ‘links’ din hannun rigar shaddar ‘hilton’ dake jikinsa fara sol.

A bakin kofar ya tsaya yana fafin.

“Ran Aunty Fa’izah ya dade, an tashi lafiya?”             Shiru babu amsa, don haka ya dora gundarin bayaninsa.

“Jiya nasan ban kyauta ba dana kori su Junior. Ina da dalilai na nayin hakan (which are all for our own goodness: Na farko kin sani Allah bai halicce ni da son hayaniyar yara ba. Na biyu ke ba kirki ne dake ba abubuwan da kike aikatawa ba lissafi a cikinsu, yaran nan kuma suna da fahimta sannan basu da mantuwa, gasu da daukar zance komi aka yi akan idanunsu sai ya koma kunnen Mama da Baba. Hatta rotsen da kika yi min  a (Area One) Yahya ya gayawa Mama Junior ya gayawa Baba na kuma rasa ta inda suka jiyo. Haka kike so suje suce kina hararata, ba kya kulani wani zubin har tsaki kike mini komai da ya kamata ace mata na yiwa mijinta ni sai na roka sannan a hagunce ake yi min…”.

Tsakin da baya so na sake saki na juya masa keya na ba banza a ajiyarsa. Kai ni surutan da yake yi ma sun isheni nasa hannu na toshe kunnuwana.

“Ina (breakfast) dina? Na gaya miki Abuja zan tafi”.

“Banga damar girkawa ba”.

Ya ce, “To Allah Ya bamu rai da lafiya”.

Na ce, “Amin Ya Rabbi”.

Ya juya ya fita ya janyo min kofar a fili, na ce.

“Umma ta gaida Assha”.

Bai jima da fita ba na mike nayi bayan gida wurin Dawisu don basu abincin safe. Ina watsa musu hatsi daga nesa suna kara matsowa gareni cikin alamun nuna sabo, wato sun fara ganeni. Ya’u ya iso ya gaida ni ya ce.

“Aunty na kawo cefane yana can kofar falo”.

Na ce, “Ina godiya Ya’u, anjima a sake musu ruwa, wannan ka gani duk yayi kura”.

Dariya abin ya baiwa Ya’u, amma sai ya ce.

“Aunty kina son ‘yan gidan nan naki, zan kara himma wurin kulawa dasu”.

Na ce, “In kayi hakan kaima Allah zai kula da kai”.

Na koma na kwashe cefanen da ya aje dokin kofa na shiga (kitchen) na adana kowanne a muhallinsa.

Fa’iz bai dawo ba sai dare, sanda ya shigo gidanma bacci nake, ban san ya shigo ba. Na fito ne da daren don samawa cikina abinda zai ci naji yana kwalamin kira kamar tashin duniya. Duk da na firgita da irin kiran amma na share na shige kicin sai gashi ya biyo ni (kitchen) din a sukwane hannayensa rike da tulin hotuna. Fusatar dake fuskarsa ba zan iya bayyanata ba.

Ta gefen ido nake kallonsa ina ci gaba da abinda nake yi, sai ji nayi ya finciko ni ta baya, saura kadan in fadi Allah Ya taimakeni na dafa (cabinet) na mike a lokacin na lura hotunan da Surajo ya kawo ne rike a hannunsa, fuskarsa a murtuke, idanunsa sun kada sunyi jajir yake magana harshensa na sarkewa.

“Meye na daukar hoto da Suraj haka (very so close) har jikinku na gugar juna?

Meye na tsayawa kusa da shi haka kusa da kusa a bainar jama’a? Da na ce yazo ya tsaya min cewa nayi kuyi hoto?

Shi kuma Ya’u da kullum kike bare baki kina hira dashi da izinin uban waye? Ina ruwanki da duk namijin da na kawo na aje cikin gidan nan da har kike dafa musu abinci? Cewa nayi dake bana basu kudin da zasu ci abinci ko me?”

 Wani matsanancin haushi da takaici suka taru suka rufe ni, naji in ba rushewa nayi da kuka ba bazan huce wannan cin mutuncin da rainin hankalin na Fa’iz ba. Na kasa cewa komai sai ido dana zuba masa cikin matsanancin haushi.

“Ina magana kin zuba min wadannan kwala-kwalan idanun naki, ba zaki amsa ba? Na ce shi kuma Ya’u ina ruwanki da shi har yake gaya min kince masa kaza da kaza? Na kirashi na aje domin baiwa tsintsaye abinci hirar da kike yi da shi ta mece ce? In hirar kike so kiyi dani mana? (Am I not applicable to meaningful talks than him?) Ni baki yi hirar dani ba sai da wani gardin kauye can daban. Ba zai yiwu ba to! Daga yau Ya’u ya bar gidan nan. Shima buzun in kika sake kula shi wallahi tafiya zai yi, ki zauna ke kadai ba zaki kasheni da raina ba… Akwai masu bukatar rayuwata ba don ke kadai aka halicceni ba!!!”.

Bayan takaici da haushi da buyaginshi ya bani, sai ya dawo bani dariya saboda da iyakacin gaskiyarshi yake wannan hargagin, akwai (gesture) a tare dashi mai nuna abinda yake fadin, haka yake har zuciyarsa.

Dariya ta cika min ciki ban san sanda nayi murmushi ba irin murmushin nan na tura haushi da maida kai shashasha domin na rantse da fari na firgita, matukar firgita kuwa. Ko da kwartaye biyar aka kamani yanayin da ya zo min dashi sai haka!

Ko ni nace a daukemu hoto da wani Surajo oho! Balle kuma bawan Allah Ya’u. Naga idan na kula shi ma (is a waste of time) don haka da sauri nabi ta gefensa zan fice daga (kitchen) din, sai jin hannuna nayi rike cikin nasa, cikin wani irin riko mai tsauri dana kasa fincikewa kamar ba mutum ne ya rike ni ba.

“Ina magana kin maidani dan iska?”

Yanayin da yayi maganar muryar kamar ba tasa ba kuma cikin wani irin ‘tune’ da ban taba jin wani mahaluki yayi magana dashi ba. Abubuwa biyu sautin da yayi amfani dashi din ya haifar a gareni.

Faduwar gaba da wani irin bugun zuciya, hannun nasa da jikinsa duka rawa suke yi yana wani irin tsuma. Wani matsanancin tsoro ya shigeni. Na daga kai a hankali na dube shi don tantance ko dai wani ne ya rikide yazo min da suffarsa don ya cutar dani. Daga idon dana zo ina dakacensa, domin kamar jira yake na dago idon yayi hanzarin ya sanya bakinsa cikin nawa ya soma ‘kissing’ ba ji ba gani kamar wani mahaukacin zaki.

“Na tuba Fa’izah, na bi Allah na biki. Kiyi min duk abinda kike ganin in kinyi shi zaki huce bacin-ranki, amma ki barni in rayu dake muddin rayuwata…”.

Kalaman da yake maimaitawa kenan ba adadi, babu ‘comma’ ba ‘full-stop’. Saura al’amuran da yake kokarin bijiro dasu masu nauyin fada ko misaltawa ne, kuma ban shirya karbarsu ba daga nan har gaban abada. Don haka na tattara karfina da Allah Ya hore min a wannan lokacin wanda ya kasance fiye da nashi na angaje shi na taka da gudu nayi dakina na shige na rufe da ‘key’ ban kuma yarda na zare key din daga jikin kofar ba har safiyar washegari.

Kwana nayi jinyar tsallake rijiya da bayan da nayi jiya wanda ko a mafarki ban kawo shi cikin rayuwar dolen da nake yi da Fa’iz ba. Wanda ya hankaltar dani ga cewa in sauya taku. Hanyar dana dauka ta yin sako-sako ga rayuwar da muke yin bisa tilas ba zata bille dani ba, ba kuma mai billewa bace ba. Idan kuma na ci gaba da binta, la-shakka ina cikin hatsarin da bazan iya maganinsa ba idan ya sameni.

Nayi kuka har na gode Allah. Daga baya bacci mai nauyi ya dauke ni. Can cikin barci na naji yana buga kofar ba da karfi ba. Na bude ido na ga hasken rana ya ratso ta labulen taga nayi mamaki matuka, sallar asuba ta kufce min cikin shagala! Ina rokon Allah Ya yafe mini.

Na fada (toilet) da sauri nayi alwala, saida nayi sallah sannan na koma nayi wanka. Sannan na shiga (kitchen) don kwana nayi da bakar yunwa.

Har kicin din ya biyoni ya tsaya daga kofa yana sanye da kayan wanka na ‘versace’ da alama fitowarshi kenan daga wanka. Daga inda nake ina iya jiyo kamshin ‘bathrobb’ din da yayi amfani dashi na ‘desire dunhill’.

“In kin kammala ki shirya muje Jabi, Area One (Zaria) da Giwa kiyi musu sallama don jibi zamu tafi”.

Na wani irin juyo nayi masa kallon kayi hauka ka warke, na juya na ci gaba da aikina. Ya girgiza kai ya juya ya kyaleni.

Duk yunwar da nake ji sai naji ba zan iya cin abincin ba ma saboda tashin hankali. Amma sai wata zuciyar ta ce bishi kawai kuje wajen Maman, wannan ce kawai mafitarki sai kiyi amfani da damar ta inda bai zata ba.

Sai kawai na aje komi na fito na sauya kaya, kwalliya sosai nayi da ‘pitch swiss-lace’ mai ratsin baki, na yafa bakin gyale na rufo dakina. A falo na cimmasa yayi nasa shirin cikin riga da wandon shadda getzner dark-green dinkin tazarce kanshi ba hula. Sai 212 ke tashi a falon. Ya hadu ya cakude da  ‘escada sentiment’ da nayi amfani dashi wani sanyin ni’ima ya baibaye dukkanin mu, da ganinmu kasan ango da amarya ne ba karya. Ko kallona baiyi ba yayi waje, na bishi a baya naki rufo falon na shige mota. Ina kallon yadda yayi kwafa, ya fito ya rufe ya dawo, sannan ya tada motar muka fita harabar gidan buzu na daga mana hannu muka nufi gidan Baban Kaduna.

Su Yahya dake ball a harabar gidan babu wanda ya taremu da murna ko tsalle kamar yadda suke yi da, tabbacin haushin yayan nasu da abinda yayi musu bai sake su ba. Sun dai yi mana sannu da zuwa suka ci gaba da ‘ball’ dinsu.

Ya kalle su ya gyada kai yayi murmushi bai ce dasu komai ba, muka wuce kai tsaye falon Mama.

Mama waya take sanda muka shiga kafarta daya kan daya a hamshakin falonta. Ta daga ido ta dube mu muna shigowa, fara’arta ta karu, ta ce.

“Kinga ‘yan halak, gasu nan sun zo”.

Ta miko min wayar tana fadin, “Rabi ce daga Kano”.

Na karba sannan na zauna a kusa da ita daga gefe na kara a kunena na ce.

“Hello Ya Rabi”.

Kafin in karasa ta fasa min guda aka mai barazanar tarwatsa min dodon kunne. Da sauri na dubi Mama da danta don tsammani nake suma sun jiyo mahaukaciyar gudarta Ya Rabi, sai naga hankalinsu baya kaina sam, gaisawa suke.

Yaya Rabi ta ce, “Diyata ‘yar albarka, ya aka kare da BOXING? WHO IS THE WINNER?”

Nayi tsaki, “Tsiyarki kenan Ya Rabi, ba a maganar arziki dake”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *