ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 3 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
Tayi dariya sosai, “Ni kuwa ake maganar arziki dani, ‘yar Abubakar uwar Abubakar da Fa’izah, uwa ga Zanira uwa ga Ummi, sha lelen Muftahu autar Hajjah. Kirarina kenan, na zama duwawu dole a zauna dani.
Tafiya ta tashi ko? Birtaniya ko Murtaniya? Na so ace nazo rakiya Allah bai yi ba, naji tafiyar taku ne ba shiri, a tabbatar in za a dawo da baby aka taho min sai inzo in zauna zaman dabaro mai dalili…”.
Nayi tsaki na katse wayar don nasan in ta Ya Rabi ne sai mu kwana muna yi bata gaji ba. Ga haushin da take kara kuma mini ta barni inji da wanda nake fama dashi.
Mama ta dubemu duka tana murmushi bayan ta karbi wayarta.
“Komai lafiya ko?” Tana duban Fa’iz.
Ya hade gira ya ce, “Tambayeta mana Mama!”.
Mama ta ce, “Fa’izah ta ina Fa’iz ya kuskuro ki ko ince yake bata miki?”
Na girgiza kai kaina a sunkuye.
“Babu Mama”.
Ta dube shi, “Fa’iz Giwa fa?”
Ya ce, “Mama ba sharri ba, tunda dai gatanan a zaune a gabanta zan fada. Da abinda take yi min na kisan mummuke gara min ta bude baki tayi ta zagina kamar da, ko ta ware hannu tayi ta dukana kamar yadda ta faro.
Bata yi min magana, bata shiga sabgata, ba ruwanta dani ko rayuwar da nake yi cikin gidan. Bata yi min biyayya sam, ta maida kanta kurma domina”.
Na dago idanuna da suka yi jawur na ce.
“Wallahi Mama ina iyaka yina, ina masa girki duk abinda ya ce dani bana musawa nake masa, to ban san kuma wace irin biyayya yake nufi ba…”.
Ya katse ni tare fidda ido, “Girkin banza! Mama baya ga girki me take yi min na hakkin maza akan matansu? Fa’izah bata kula ni, bata taba zuwa shimfidata ba, bata gaida ni, ga tsaki da harara kamar wani sa’an wasanta”.
Maganar ta dan girme mu ni da Mama, amma dukkanin mu sai muka yi kamar bamu ji ta ba. Na kawo wata daban.
“Saboda Allah Mama ya yake so nayi? Ya zo ya sani gaba da bala’in wai don me zanke kula Ya’u leburanshi? Bayan a karkashinmu yake, dole ne ko gaisuwa ta hada mu, wai kuma don me zan ke basu abinci bayan ciyarda barori wani abu ne da muka taso muka tarar a gidanmu a matsayin kyakkyawan koyi koda ana basu albashi. Ban kula shi ba sai ya koma wai don me nayi hoto da Surajo ranar Cocktail? Bayan bani na gayyato shi ba, ban kuma je fatin nan don kowa ba sai don kaina ko ku baku san zan je ba.
Ban san ma sanda aka dauki hoton ba da abinshi ya zo. Sannan kannena suka zo min zumunci ya kore su, yanzu duk haushina suke ji kamar yadda suka kullaci Ummi. Sannan ya kawo wata magana wai wani tafiya, ko ina oho! Ni kam kiyi masa magana ya fita harkata, babu inda zani gaskiya in har ba so yake ya kuntata rayuwata ba (by all means from every angle).
Na yarda na amince zan zauna a can Malali ko ni kadai ce yaje duk ranar daya samu dama ya kawo min ziyara babu damuwa”.
Ya fiddo ido cikin kidima, “Baki isa ba, Allah kinyi dan kadan, duk abinda kike ji dashi ina shirye da dauka amma banda wannan”.
Fada yake yi sosai har jijiyar kansa na mikewa kamar ma ya manta da Mama a wurin.
Mama tasa masa ido tana kallo sai da yayi mai isarsa tukunna, daga ni har ita babu wanda ya tanka, sai dai jikina naji ya soma rawa, kuka na son kece mini.
Ya yi shiru ganin na soma sharar hawaye da mayafi na. Sannan ne Mama ta nisa cikin bacin rai ta soma magana.
“To tunda zuwa kayi ka kare mana tanadi ni da ita, to tattara iyalinka ku tafi ka fini iko dasu. Ni dama ban kirawo ku ba balle kuzo ku daga min hankali”.
Ya soma bata hakuri tana kaucewa, daga karshe ta ce.
“Laifi duk naka ne Fa’iz. Meye don Fa’izah tayi magana da yaron gidanta tunda kana da tabbacin ba zata yi maganar banza dashi ba? Don ta girka abinci ta basu domin kyautatawa bai kamata ka nuna jin zafin ka ba, sai ma kayi alfahari da ta zamo mai kyautar abinci ga na kasa da kai ba kace ta daina ba.
Hoto kuwa duk muna tsaye aka yi shi, kasan baka so ayi hoto dashi don me ka turo shi? Suraj ya rufa maka asiri babu wanda yayi zaton ba kaine a wurin ba, meye laifi anan?
Magana da kace bata yi maka ina ce komai sai ta dauro za’ayi? Ka sani Fa’izah ba mai son yawan magana bace tun tuni. Tunda har da bakin ka ka furta bata yi maka musu, sannan tana girka maka abinci, sai me ya saura? Dan Adam da ba’a iya maka har kana fadin gara maka zagi da duka da wannan. Yau da Fa’izah zagin naka take da duka da rashin kunya, ko kuma bata baka abinci dole ne in tsawatar mata.
Don Allah ka koyi hakuri Fa’izu, zafin zuciyar nan baya da amfani ko kadan, kabi komai a sannu, a baya ka zaci wannan din da kake rainawa cikin kankanin lokaci haka? Har kullum addu’armu na tare da ku, komi zai yi dai-dai a gaba insha Allahu”.
Da alama jikinsa yayi sanyi, amma ba duka ba.
Ya ce, “To amma Mama tsaki da harara fa? Gaskiya ba zan jure ba, don ban taso naga kuna yi ba ga su Baba ko wani cikin A.B baki daya. Wannan ai raini ne. Ko don Fa’izah ana sonta kowa na tsoron masifarta?”
Abin ya bawa Mama dariya, amma ta gimtse.
“In ma hakan ne bamu yi laifi ba tunda ai amarya ce, amarya kuwa kowa yasan bata laifi. Kuma ka dinga tausaya mata tunda dai auren nan kasan ba da saninta akayi shi ba, zuwar mata yayi kamar saukar aradu. Don haka ni yadda ta dawo yanzun naji dadi, ta fara nuna mana ta haifu, bata fi karfinmu ba kamar yadda muke zato, huce bacin ranta take yi kuma ta fara hucewar to ka bimu a sannu in kana son mu ci gaba da hucewa”.
Yayi kwafa ya ce, “Me nayi mata? In zaki yankata ta fadi laifin da take ikirarin nayi mata bashi da yawan hukuncin da nake karba. Banda ni din nine Fa’izun Hajjah Abubakar-Saddiqu, na Baban Kaduna da ABU wa zai yi hakurin dana yi? Ko anan aka tsaya an san ni jarumi ne wanda mace bata isa ta girgiza ba ko ta sani abinda ban yi niyya ba. Don haka nayi niyyar mu tafi tare wajen neman abincina, kinyi kadan ki canza min ra’ayi.
Wallahi Mama yarinyar nan ba abar tausayi bace, ki daina jin tausayinta kina ganinta haka kamar wata mumina. Musa ce a baki Fir’auna a zuci, rashin mutuncin dake cikin bakinta da zuciyarta yafi bakinta girma”.
Mama tayi dariya tana mamakin yaushe bakin Fa’iz ya bude yake zaro Hausa haka? Abar da ada sai dai kaji yana yi mata baragada in ya jima yana magana, lallai Fa’iza bata kama kurwarsa da wasa ba.
Ta gyada kai ta ce, “To ke Fa’izah kinji wannan?”
Na ce, “To Mama tunda ya ce tsaki nake masa to yayi tafiyar sa shi kadai mana ya huta da jin tsakin? Maimakon inje ina yi mai ranshi na baci? Tunda cikin hutu su Junior suke sai muyi zaman mu tare a gidan har su Walida a karo, amma ni ba inda zan iya matsawa inbar iyayena da ‘yan uwana zuwa inda ban san kowa ba tunda duk abinda nake yi masa baya gode ko daya, haka idan na bishi rai zai yi ta baci gara inyi zamana”.
Mama ta ce, “Kwarai kuwa, ba inda Fa’izah zata, zata zauna har ka samu hutu. Ni dama bana son yawon jirgin nan, tukunna ma kai da baka zama wuri guda, a tafe kake kwana a tafe kake wuni, meye amfanin bin naka da kake so tayi?”
Kamar zai yi kuka ya ce, “Amma ba kullum nake kwana a tafe ba ko Mama? Abin cikin tsari ne, (we have breaks!)”.
Mama ta ce, “Oho maka! Na gama magana, ku tashi ku tafi don Allah. Allah Ya yi muku maganin abinda ke damun ku, Ya yaye muku shaidanun dake yawo akanku. Duk ‘yan uwanku kowanne na zaune lafiya da abokin zamansa ba mai jin kanshi da dan uwansa sai ku. Ku taka a sannu, duniya ba’a yi mata gaggawa”.
Mun mike kenan Baba ya shigo, zuciyata kamar farar takarda nake gaishe shi. Fa’iz bai bari na dire gaisuwar dana debo ba tun kamin Baba ya zauna ya soma karanto masa yadda akayi, da hukuncin rashin adalcin Mama.
Shi dai Baba da dadin ganinmu tare har ana zancen tafiya Birtaniya sai ya hau hamdala ga Allah a zuci, a fili kuma ya ce.
“Tunda bata so a kyaleta man Fa’iz? Ba a son tilastawa cikin zamantakewar aure, watarana da kanta zata ce zata bika ne”.
Tun daga ranar da aka yi mana aure Fa’iz bai ji na bashi bakin ciki da takaici irin yau ba. Ya mike cikin fushi ya zari mukullin motarshi ya yi hanyar waje. Baba da karin tura haushi ya ce.
“UHm! Na ce ba?”
Fa’iz ya dakata amma bai juyo ba.
“Ka nemo motar hawa a kyale min tawa ta huta. Haba, ya za’a ce in hau abu, kaima ka hau, wannan sam ba tsarina bane. Duk kabi ka zage min gari da motar ma bana so, ka je ka rike ka kirgo kudinta ka biya ni, fakat”.
Ya ce, “Zan kawo abinda ya samu, shi kenan?”
Baba ya ce, “Wane irin abinda ya samu? Naira miliyan biyar cur na sayi mota ta, haka za’a bani ko Naira biyar ban yarda tayi ciwon kai a ciki ba. Mota ta ‘R-Class’ ce kaje ko’ina ka tambaya haka kudinta yake”.
Takaici a wurin Fa’iz baya faduwa, ya ce.
“Haba Baba, ai babu ciniki tsakaninmu. Yaushe ma na fara aikin da har zan tara abinda kake fadi? Duk ajiyar da nake yi ta kananan ayyukan da nayi kai na turowa aka yi aikin gidan nan da muke ciki”.
Baba ya ce, “Kai ka sani. Albarkacin shekara biyu da tayi a hannuna, na shigeta sau bakwai, a kawo min naira miliyan uku, cash ba ta ‘credit card’ ko ‘cheque’ ko ‘internet banking’ ba. Ni nasan bankin da nake mu’amala da abina”.
Mama dariya take har da kyakyatawa. Fa’iz bai kara tankawa ba ya fice. Na bi bayanshi nima dariya ta cika min ciki amma na kame kaina tunda ni ke da nasara. Ina shiga motar kafin na kai ga rufewa ya fisgeta kofar ta rufe kanta da kanta, saura kadan ta guntile min ‘yan yatsu.
Tunda muka hau titin da zai kaimu Zaria bai ce min komai ba, kazalika bai kalleni ba. Ya maida hankali sosai a tukin da yake yi (at a speedy level).
Momi kurum muka samu a gida muka gaisheta, bai iya yayi hira da ita ba duk kokarin da yake na boye bacin ransa. Daga bisani ya tashi ya barmu ya ce zai je cikin (city) ya dawo sai mu tafi.
Bayan fitarsa Momi ta zuba min ido tana kallo.
“Wato mai hali dai baya fasa halinsa. Ana murna kwana biyu an jiki shiru ashe wata sabuwar tsiyar kike shukawa a inda babu mai ganinki balle ya tsawatar. To in kowa baya ganinki ko Fa’izu bai kawowa kowa kararki ba, Allah da Ya halicci kowa da komai Shi Yana ganinki da duk abinda ki ke aikatawa na zahiri da badini. Daga ganin yadda Abubakar yake kumburi wanda ba halinsa ba, kinyi rashin mutuncin naki ne”.
Na ce, “Wallahi Momi banyi masa komai ba, lafiya muke zaune tunda muka bar gidan nan. Tsakanin shi da Mama ne, don kawai ta ce sai ya sake dawowa na bishi inda yake, shi kenan yake fushi”.
Momi ta harzuka, ban kai ga direwa ba ta ce.
“Ubanki za ki zauna kiyi eye? Na ce ubanki za ki zauna kiyi, ke ba zakiyi zaman aure irin na kowacce mace ba? Shashasha maras mutunci.
In don ni kike yin wannan dabbancin wallahi kin dauki alhakina don ni babu abinda Abubakar yayi min wanda ban dauka a yarinta da kuruciya ba tunda dai ni dai gaba da gaba bai taba fuskantata ya zagenin ba sai dai inji a bakinki, wanda tun lokacin ba sauraron ki nake ba, bani kuma da tabbacin ko karya kike don bacin ke ban taba jin wani ya ce Fa’iz ya zageni ko baya sona ba.
Akwai abinda baki sani ba wanda in kin sauke iskokin dake kanki kinbi a hankali watakila nan gaba za ki sani. Baka taba jin ZUCIYAR MUTUM… baka kwantar da hankalinka a kanshi ba. Don masu iya magana sunce ZUCIYAR MUTUM…. BIRNINSA!.
Kin san Allah ki ka sake sako kafarki gidan nan sai nasa Babanku ya kakkaryata, ba dakin Abdallah ba ko cikin kuratandu kika shiga indai a gidan nan ne sai dai ki bi yawon duniyar daga yau babu mai hana ki”.
Idanunta suka cicciko da kwalla amma bata bari sun zubo ba don sanin hatsarin da zubar tasu ke tattare dashi a tare dani.
Nayi murmushin da na tabbatar zai kwantar da hankalinta, gaba daya jikina yayi sanyi kalau.
“Ba gidan nan zan dawo ba. Tunda muka tafi ma ai ba a gidan Baban Kaduna muke ba, Walida bata gaya muku ba? Muna gidanshi ne a Malali GRA”.
Ta dan zuba min ido kamar bata yarda da abinda na ce ba.
Na ce, “Wallahi Momi da gaske nake, kuma ki tambayi Mama. Ko ya tafi a can zanyi zamana nayi miki alkawari, in kin ganni gidan nan ko gidan Baban Kaduna ko Giwa ko Kano wajen Ya Rabi gaishe ku nazo yi”.
Anan ne ta saki fuska ta ce, “Shi kenan. Su Walidar basu dawo bane, daga can suka wuce Lagos wajen su Zanirah”.
Dai dai lokacin da muka ji sallamar shi a dakin, abin mamaki ya saki ba kamar yadda muka zo ba.
Ya ce, “Momi zamu wuce, ni kuma gobe zan wuce Wales din kasar England, na samu aiki da ‘British-Airline’ zan jima ban zo ba sai na samu (break) mai dan tsaho”.
Momi ta sanya albarka tayi addu’a da Allah Yasa matakin arziki ne, Ya kara rufa asiri, Ya kiyaye sharrin karfe da na iska, Ya cire haramun daga cikin abinda za’a samu alfarmar Manzo (S.A.W).
Ya fadada murmushinsa cikin jin dadin addu’arta yana fadin.
“Amin Ya Rabbi Maman Walida”.
Na mike, ta dubeni ba yabo ba fallasa.
“Akwai garin semo da bushasshiyar kubewa da bushasshen kifi in kuna bukata”.
Na ce, “A’ah Momi, ba yanzu ba dai, zan aiko in ina bukata”.
Ta ce, “Ke kika sani”.
Da muka shigo Kaduna ya tsaya wani babban ‘Shopping Mall’ bai yi min ko tayin shiga ba shi kadai ya shiga abinsa. Ya jima sosai kafin naga yaran kantin sun biyo shi da manyan ledoji, suka zuba a bayan motar, sai katon-katon na abin sha (ruwa da lemo) kala daban-daban.
Akan hanyarmu ta shigowa Malali ya tsaya ya tsayi gashasshen nama muka karaso gida duk jikina a sanyaye yake.
Muna shiga Ya’u ya taremu, sai na samu kaina da kara jan lullubina na rufe har rabin fuskata ban san dalili ba ko don ya nuna baya so din ne da gaske? Bazan so ya zamo nayi sanadin hanyar abincin wannan bawan Allah ba, wanda ga dukkan alamu ita ce madogararsa kadai.
Ya kwashe komai daga bayan motar ya shigar (kitchen). Yayi mana sallama ya fita.
Ya maida kofar falon ya rufe da (key) ya dawo ya zauna bisa (carpet) ya kunna t.v tashar CNN yana rike da (remote) ya dawo ya zauna, ya janyo ledar namansa yasa a gaba yana ci yana sauraron labaran, bai kara kallo na ba kamar yadda bai nemi ‘chips & chicken’ ba.
Na mike ba don an sani ba na shiga (kitchen) na soma sarrafa su kamar yadda na saba, amma na yau (with additional aroma and taste) saboda kamar ina neman hanyar shiri ne ko yaya ne dai na kasa gane kaina. Wata zuciyar ta ce tunda ni nayi nasara nawa ra’ayin aka yi masa fin karfi aka bi, bari in dan kyautata.
Dana kammala na aje a (dining) kamar yadda na saba, na ce.
“Ga (dinner) din”.
Kamar ba da shi nake ba kallon t.v kawai yake duk da na tabbatar ya ji ni saboda ba wai yasa muryar t.v din da yawa bane, a’a dai-dai jinsa, raina ya dan baci na wuce na shige daki na sayo kofa amma ban sa mukulli ba. Can naji motsin kwanuka a (kitchen_, na daga labule ta taga ta wadda kana hango duk abinda ke faruwa a (kitchen) sai na hango shi ya dora ‘yar tukunya akan (cooker) ya saka indomie guda biyu bai ko cire ledar maggi da chili din dake ciki ba ya kawo ruwan zafi wajen kofi uku wanda ya sha kan indomin har baka hango ta ya zuba, ya rufe. Ya fita daga kicin din ya koma ya ci gaba da sauraron labaransa.
Kamar inje in duba wannan lamari wata zuciyar ta kwabeni abinda ba ruwan ka ance dadin kallo gare shi, na koma nayi kwanciyata. Anfi minti talatin kafin inji shi ya koma (kitchen) din, ban san abinda ya faru kuma ba bayan nan.
Bayan kamar minti biyar naji fitarsa a mota, tsegumi har tsunkuli na yake nayi (kitchen). Na bude tukunyar daya dora a wuta. Indomin ta hadu ta dame ta zama kunu zance ko koko ko tuwo, gatan nan dai ba suna ba fasali. Na tabbata ba zai iya ko tabawa ba balle ya sanya a bakinsa shi ne ya fita yaje ya sayo.
A raina na ce, “Ashe dai girkin banza na da amfani tunda sai da shi ake rayuwa”.
Na kara duban dabgen da yayi nayi dariya na mayar na rufe na koma daki.
Nayi zaton zan kuma jin duriyarshi kafin nayi barci, amma har garin Allah ya waye banji ba. Haka dana tashi yin sallar asubahi na fita falon ko zan ganshi sai abincina na daren jiya (chips and chicken) kadai na tarar akan (dining table) inda na ajiye shi ko matsar da shi ba’ayi ba.
Daga nan nayi brush na koma daki, ban tashi ba sai karfe tara na safe. Da hanzari na nufi (kitchen) na soma aikin hada masa karin kumallo, amma na yau ‘is special’ kamar na daren jiya duk da raina ya sosu da rashin cin da bai yi ba.
Cikin dan lokaci na kammala ‘scottish egg, plantain with syrup, bread with jubnah’ da ruwan na’a-na’a. Cikin dan lokaci kalilan na kwashe na jiya na shirya su a inda ya saba karyawa a kwanaki goma sha ukun da muka yi tare.
Na koma daki nayi wanka nayi shiri cikin atamfa sufa ja mai ratsin kore da baki wanda dinkin ya zauna a jikina sosai, zanin ya bude daga kasa. Na fesa turare ‘escada sentiment’ na kalmasa dauri sassauka, na dubi kaina a mudubin dogon yaro na yi wani irin ‘fresh’ (looking takeaway) ko ni kaina na baiwa kaina sha’awa. Sai na samu kaina da tambayar kaina kwalliyar ta mece ce? Mene ne dalilinta?