ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir

 ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 5 by Sumayyah Abdul-kadir

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

***

Na wayi gari ne yau cikin matsanancin nishadi, irin wanda ban taba tsintar kaina a ciki ba. Don haka na share ko’ina na goge lungu-lungu da sako-sako na gidan ya zama tas, sai sheki yake kamar lomarka zata fadi ka sanya baki ka side, duk da gidan ba wani datti yayi ba, don akai-akai nake kula da tsaftarsa. Na samu kaina da son shiga dakin Fa’iz, ko na rage kewar sa data addabe ni. A hankali na murda kofar na shiga dakin ga mamakina a bude ya barshi, sallama dauke a baki na.

Fa’eez ya kawata dakin baccinshi da duk wani nau’in kayan jin dadin rayuwa. Duk da A/c a kashe yake, amma dakin da sanyinsa, wanda ya hadu ya cakude da sassanyan kamshin ‘212’n da Fa’eez ke amfani dashi (on a regular basis). Babu komi dake cikin dakin da aka saye shi cikin Kadunan, bayan gidan Fa’iz kadai abin kallo ne, wanda bai cika girma ba. Banda katifar ruwa data mamaye gadon shi, karamin ‘frame’ din dake aje dai-dai santar inda yake sanya kanshi guda biyu kanana su suka dauki hankali na.

Sannu a hankali nake takawa zuwa garesu, yayin da kafata ke nitsewa cikin (center-carpet) mai tsananin taushi dake gaban gadonsa. Wanda ya sha bamban da sauran carpet din dake cikin gidan baki daya.

 A hankali na russuna na dauki ‘frame’ din. Wani dadadden hoto na ne mai rungume da (teddy bear) wanda da alama ya kaiwa gwanaye ne sun wanke shi sun adana a cikin ‘frame’ din ya zama kamar daukar jiya-jiya. A kusa dashi wani hoton nawa ne cikin (swiss-lace) da goggoro, wato ranar partyn ‘Indoor-sport hall’ na nan Kaduna. Na tsuke giran sama da ta kasa wanda hakan ba karamin kyau ya kara min ba tamkar anyi shi ne ‘in-style’ ba bacin rai ba.

Na tambayi kaina wannan shi ne ‘SO’ kenan? Wanda ni bana jin shi? Don ko cikin wayata ba zan iya ajiye hoton Fa’iz ba balle a dakin barci na, inda nake ta da kai da mayarwa, a yayin kwanciya da tashi daga barci.

To me ya hana inso Fa’eez? Babu! Illa shi SO din abu ne wanda ke yin kansa, ko ince yin Allah ne, ko kuma wani hali na mutum ko wasu (personal-attributes) kan zamo sila na samuwarsa, and Fa’iz ‘lack any loving attribute to be loved upon’. Wato bashi da wani hali da za’a so shi don su, sai wani sashe na zuciyata ya ce dani.

“A bisa rashin saninki kenan a da, banda yanzu, da kika fara lakantar ainihin waye FA’EEZ BAMALLI?” (And I came to the conclusion that) ba wani abu ne ya hana ni son Fa’iz ba illa tunanin baya… Inada RIKO, bani da mantuwa, sannan inada gudun wulakanci. Ina son momi na, Ina ganin muddin na sake da Fa’iz nan gaba zai koma min Fa’izun Hajja, wato Fa’izunsa na baya, zai sake sanya ni cikin ‘problem’ sannan zai sake tsanata…

Na cigaba da kallon dakin tare da komi dake cikinsa ba tare da na bude kowacce ma’adanar kaya ba (locker).

Ba don komi ba sai don nasha jin Hajjah na fadin, “Yiwa miji bincike ba ta’ada ce mai kyau ba, duk mai yiwa mijinta bincike wata rana sai ta binciko abinda zai daga mata hankali, ya hana ta bacci, ya sanyata bakin ciki wanda bata da maganinsa. Watarana sai ta binciko abinda ba alkhairi ba!”.

Duk da baya dakin amma kamshinsa ‘permanent’ ne. Turaren ‘212’ tamkar shi kadai aka yiwa. Komi na Fa’iz kamshinsa ne a jiki hatta takardunsa, bedsheet da labulayen dakin nasa. Na kasa fita a dakin Fa’iz, sakamakon wani shauki (emotion) dake dibana, zan so ace a lokacin yana cikin dakin ne ko yana falo yana kwala min kira in kawo masa kaza da ‘chips’ dinsa.

Shaukin dake dibana ne ya debe ni ya kwantar a gadon Fa’iz, ya janyo tattausan bargonsa ya lullube ni dashi. Da filon shi na tada kai na lumshe ido ina cigaba da shakar daddadan kamshin na ‘212’ (men). Na soma zargin kaina da son Fa’iz a karo na farko. Wadannan (emotions) din (are for real!) YAA SATTAR!!! Ya Sattaru, idan mafarki nake ina rokon ka da ka farkar dani. Na bude dukkan idanuna dake lumshe, da karfi nayi wurgi da filon na zauna dabas a tsakiyar gadon ina wurga ido kamar mara gaskiya.

Eh, mara gaskiya ce (in fact!) Domin son karyata ’emotions’ din nawa nake da gangan suna fin karfina. Na sakko daga gadon cikin barin-jiki, amma ga mamakina na kasa fita a dakin Fa’iz! Ina son dakin!! Ina son nayi bacci a dakin ko na samu nutsuwa.

Na koma na kwanta cikin mutuwar jiki da zuciya, naja bargo na rufe har kaina. Bacci mai karfi ya fisgeni.

Tafiya nake cikin wani kungurmin daji, ba gida gaba ba gida baya, na bullo ta gabas aguje nake a dalilin wutar dake bina, wuta bala-bala wadda ke tafe ta hanyar cin busassun kirare na jejin. Ina gudu ina kiran sunan Allah amma wutar nan bata bar bina ba. Gudu nake kamar raina zai fita har na sare, karfina ya kare.

Ina gab da faduwa a yayin da muka iso gab da wani tafkeken kogi, na daga kafata da niyyar in fada ruwan kawai ya cinyeni in huta, ya fiye min cinyewar wutar. Sai ji nayi wani sassanyan hannu ya rungume ni. Wannan hannun ya ce.

“QUL YAA NARU KUNI BARDHAN WA SALAMUN ALA IBRAHEEM… (Yaa ke wuta ki zamo mai sanyi da aminci ga Ibrahim)”.

“Na yafewa Fa’izah dukkan abinda tayi min wanda na sani da wanda ban sani ba, wanda tayi akan sani da wanda tayi bisa kuskure, daga ranar da aka daura mana aure… har zuwa ranar da zan daina numfashi…!”.

Kamin in dago inga wane ne? Wutar nan tabi ruwan. Bata ba dalilinta. Haske ya mamaye duhun dake mamaye dani. Na dago a hankali a lokacin zuciyata tayi fari kal! Babu sauran wani kunci ko wani kullaci a cikinta. 

Na dubi wanda nake rike a kirjin nasa, wani kirji ma’abocin tarin ni’ima da sanyi da sanya salama, ba wani bane FA’IZ ne, FA’IZ MUKHTAR ABUBAKAR BAMALLI GIWA. 

Idona ya bude ‘vivid’ na tabbatar mafarki ne nake yi. In banda gumi ba abinda nake shirbinawa. Illahirin jikina duka rawa yake, na rasa abinda ke min dadi. Na kifa fuskata cikin tafukana na soma kuka.

Wannan mafarki shi ake kira kukan kurciyaa…! Wani irin sarawa kaina ya shiga yi saboda kuka. A hankali na mike na nufi kofa don fita daga dakin ko na samu sa’ida cikin zuciyata. Sai nayi tuntube da wani abu kamar littafi gab da bakin kofar dakin. Na russuna na dauka, littafi ne na ajiye tarihi da mihimman bayanai (Diary) da alama garin fita ya yarda shi ba tare da ya sani ba.

Anan bakin kofar nayi zaman dirshan ina buda shafukan littafin. Rubutu yayi na abinda ya kunshi tun daga ranakun kuruciyarsa, da tafiyarshi kasar Russia. ‘Tittle’ din rubutun shi ne;

 “ONLY ALLAH KNOWS WHAT FUTURE HAS IN STORE FOR US”.

A wani shafi Fa’iz yayi wani rubutu wanda da alama tun tali-talin kuruciyarsa yayi rubutun domin kwanan wata na kalanda wanda aka buga littafin cikinsa ya nuna hakan. Rubutun yayi matukar bani dariya.

“MEYE DALILIN DA YASA NA TSANI FA’IZA? BAN SANI BA! ILLA SAI DON CEWA ITA DIN KYAKKYAWA CE, TA FINI KYAU, A LOKACIN DA NAFI DUK ZURI’AR A.B KYAU SAI TAZO TA DAMENI TA SHANYE, KOWA YA KARKATAR DA KAUNAR DA YAKE YI MIN GARETA; MAIMAKON FA’IZ KOWA SAI FA’IZAH!”.

Murmushi nayi na cigaba da buda shafukan. Wannan rubutun na shafi na gaba ga abinda ya rubuta.

“A Giwa ne. Misalin karfe goma na safe. Ina zaune falon Hajjah ina kallon fadan Isra’el a CNN. Wayar falon Hajjah dake ruri a gefena ban dauka ba sakamakon tunanin da yayi min rubdugu a wannan dan tsukin. Wanda bai wuce SON FA’IZAH ba! Fitowarta da daukar wayarta cikin kumfa ya sanyani kai dubana gareta. Duk da kasancewarta yarinya karama a wannan lokacin, ‘yar shekaru goma sha hudu amman ta mallaki suffa kyakkyawa irin suffar da nake so ga ‘ya macen da nake burin mallaka matsayin matar aurena. Tun daga wannan lokacin son Fa’izah ya ci gaba da ruruwa a zuciyata kamar gobarar daji. 

Nayi kuka nayi nadamar da bata da amfani, musamman da na fahimci kakkarfar soyayyar dake tsakaninta da Yaya Aliyu.

Tsananin kishin Aliyu da nake, ya sanya ni hantarar Fa’izah a kullum a duk lokacin da yake zaune. A wauta ta a wancan lokacin Aliyu yaga bakin Fa’izah ya janye daga gareta, ya daina sonta amma ya ki. Asali ma sai kareta yake, yana bin bayanta cikin kowanne hali.

Akwai ranar da suka amso takardun jarrabawar firamare, don Aliyu yaji haushi kawai nace takardun Fa’izah basu yi kyau ba, komi ‘fail’ ‘poor’!

To Aliyu yaji haushin, amma ba irin wanda nake so ya ji ba. A ranar ne yaga “love colour” na matsananciyar soyayyar Fa’izah cikin kwayar idanuna. 

Hankalin Aliyu ya tashi kwarai domin yana gudun abinda duk zai kawo mishi matsala a soyayyar shi da Fa’izah. Musamman ni dana kasance dan gatan Hajjah, wanda dana furta sai aikatawa.

Aliyu ya dubeni cike da masifa, cikin harshen Turanci ya ce.

“Ina gargadinka Fa’iz! ‘Don’t dare say it’… wato kada ka taba furtawa sai kayi nadama anan gaba”.

Na yiwa Aliyu kallon ko ni ko kai har su Fa’izan suka zargi wani abu. A ranar munyi musayarta ba dadi nida Aliyu da muka fito waje, har saida maganar ta hada da manya. Inda naji dadi shi ne inda Baba Barau ya ce babu wanda zai kuma yin auren soyayya cikin A.B tun daga kan Baban ABU wanda shima yayi ne ba bisa sanin mahaifinshi marigayi Abubakar Giwa ba. Ya kara da cewa.

“Fa’izah ta mai rabo ce. Don haka kada wanda ya sake ya furta mata yana sonta cikin mu duka”.

Akwai ranar da na sanya Fa’izah cikin bacin ran da ya rudata har ta rungume Yaya Aliyu. A ranar ni kadai nasan abinda naji. ‘In fact’ kishi ne matsananci . Abinda tayi min bai bani haushi ba illa haushin Aliyu. A ranar ne nasan na fara kuka ‘for sake of Fa’izah’s love’ (saboda son Fa’izah).

Fa’izah in tana kuka sha’awa take bani, in tana tsiwarta burgeni take, (I drive pleasure in making her cry). In tana kuka kyau take mini, sha’awa take bani. Shi yasa na kasance kullum cikin kirkirar abinda nasan zai sata kuka.

Bakin cikin tafiya ta Russia? Ba na komai bane ba don komi ba illa tsoron kada Aliyu ya aure Fa’izah kafin na dawo.

Na karyata kaina a wurin Hajjah da su Baban ABU, Baban Kaduna da Baba Na’ibi ranar da suka kawo min ziyara ta farko kasar Russia, na gaya musu cewa dukkan abinda nake cewa Fa’izah tayi, don inga hawayenta ne wadanda ke sanya ni nishadi, su kuma sanyani MURMUSHI.

Komai na Fa’izah ina son shi, sannan ‘is special’ agareni. Duk abinda nayi mata nayi ne domin KAUNARTA da ‘pretending’ kaunar, ‘as I have no option’ banda yin hakan. Na farko ban isa in furta ba, na biyu kishin yadda Aliyu ya kankane komai nata, na uku ita kanta Fa’izar ta dauke ni makiyinta ne na a buga a jarida, ba abinda zanyi ya goge hakan daga zuciyarta. A zahiri, na soma son Fa’izah ne daga ranar data dawo Giwa. Ta cinye min naman miya.

Babu abinda na tsana irin inga Baban ABU na dukan Fa’izah. A duk lokacin da naga hakan kukan zuci nake da azabta a zuci da gangar jiki. In shige daki inyi ta kuka.

Akwai ranar da Aliyu ya kamani ina kukan ni kadai a daki bayan na yiwa Fa’izah sharrin da ya sanya Baban yi mata dukan kawo wuka, ya tuhume ni amma sai na ce masa bani da lafiya ne.

Ranar da naji Hajjah ta ce mu tafi da su Ummi Kaduna (party) babu tunanin hanyar da zan bi in soke zuwanta da banyi ba amma na rasa. Cikin ikon Allah ta nemi da inzo rabon fada, anan ne na samu hanya ba don komai ba sai don KISHIN KADA WANI YA SO TA CIKIN A.B saboda yadda tayi kyau.

Duk da kasancewar ta yarinya karama a wancan lokacin, tafi duk ‘yan matan A.B iya tsara kwalliya, tafi su kyau mai daukar hankali. Sau da yawa nakan ji samarin cikinmu na fadin DAMA A BASU FA’IZAH!

Na kan ji kishi kamar in kashe su, amma sai inga bari kawai in batata a wurinsu ta yadda zata yi bakin jini, koda an basun suce ‘a’ah, inyaso ni sai ince a bani in karba da hakuri, don haka nayi furucin tana bin Yaya Aliyu B-Q, ko ince bata da kunya bata da kokari, kazama ce, kuma masifaffiya. Sai kuma tazo tana kazantar kowa ya gani hakan ya nuna ba kage nayi mata ba.

Nayi wauta da tazo ta zame min bala’i, ko ince alhaki ya zame min dan kwikwiyo. Wautar da ta jawo Fa’izah ta tsane ni fiye da kowa a duniya har take addu’ar ALLAH YA KASHE FA’EEZ BAMALLI IN HUTA!

Ni kuma Ya jarrabce ni da matsananin SO irin wanda ban ta ko gani ko cikin hikaya da labarun almara ba.

A zahiri na nunawa Fa’izah kiyayya domin SONTA da yayi min katutu, bani kuma da yadda zanyi dashi. Duk kiyayyar da na nunawa Fa’izah KISHI NE da PRETENDING. Amma da hankali ya zo min, na gane na kuma fahimci wannan ba hanya ce da ake nuna KISHI ba, ga wanda aka yimawa KIYAYYA NE. Bayan ni a wauta ta nayi ne don samarin A.B su ki Fa’izah baki dayansu. Da sun kammala sakandire ni in aureta, tunda ta rasa mai so. Na manta da cewa ma babu batun nagani ina so a cikin A.B, a ganina koda an basun dai suce basa so. Tunda babu wanda zai so mace mai wadannan halaye da na kaga mata, har shi Aliyun, don dai yana da wata irin zuciya ne data sha bamban da ta sauran ‘yan Adam.

Ashe ni ban san wannan na nufin gina kiyayyata mara iyaka a zuciyar wadda na yiwa KIYAYYA DON SO. Ban tashi jin son Fa’izah na neman hallaka ni ba sai da nayi nisa da ita. Na kasa karatu na kasa ci, na kasa sha, barci ya kaurace min fau-fau. Da hoton ta na ‘teddy bear’ nake kwana nake tashi.

Nayi kuka domin son Fa’izah, abinda ban taba yi akan mace ba: Nayi abinda ban taba yi ba a rayuwata domin SON FA’IZAH, wato “NADAMA”.

A shekarun karatuna, baki daya, kowanne sakan, kowanne minti, kowanne dakika da kowanne awa son Fa’izah da kaunarta ke kara habaka a tare dani.

Ba komai ya hana ni yiwa Fa’izah aike tamkar su Ummi ba illa TUNA BAYA… Yadda Fa’izah ta tsane ni, yadda ta ki jinina, na tabbata ba zata amshi abin hannu na ba ko za’a kasheta. Tsammani ma zata yi wata cutar na kunso zanyi mata.

To amma nayi mata aike da abu mai daraja a gareni, nake kwana  nake stashi tare da shi. Nayi mata aike da HANKICI na, wanda ke nufin sakon kaunata zuwa gareta, domin na sanya anyi rubutu da harshen Larabci a jiki, an rubuta ‘AHUBBIK’ wato ina sonki da dukkan zuciyata!

Daga ranar da aka daura aurenmu da Fa’izah na tabbatar Fa’izah alkhairi ce a gareni, kuma wani bangare ce ta cigaban rayuwata. Daga ranar na soma ganin budi takowanne bangare, aikina, nasara da cigaba cikin duk abinda na sanya hannu, mutunci da martabata a idanun iyayena suka karu.

 A dalilin aurena da Fa’izah ne mahaifiyata ta dawo da soyayyar ta gareni wadda ada ta haramta mini saboda na ki karatu kuma na takurawa Fa’izarta. Ta kuma fifitani a tsakanin sauran ‘yan uwana.

Kiyayyar da Fa’izah ke nuna mini tana kara min kaunarta ne a koda yaushe, tana nuna min ta san ciwon kanta, tasan mutuncin mahaifiyarta, tasan makiyinta, ta san masoyinta (in comparison to yaya Aliyu!). Tana hangen abinda ka je ya zo, tana hangowa kanta dacewa da rayuwa da wanda soyayya ce ta hadasu ba kamar ni data rika a matsayin makiyi ba, tunda (that’s the way I proved myself to her). Kuma masu iya mmagana sunce “Makiyinka baya taba dawowa ya zama masoyinka”. Wannan ne dalilin da yasa nake yi mata ‘UZURI’.

A hakikanin gaskiya ba kin Fa’izah nake ba, WAUTA ce ta KURUCIYA domin in samu ABINDA NAKE SO, wato ita FA’IZAH. Idan kowa yace baya so.

Ni kaina nasan mutum ne miskili da akan rasa gane inda yasa gaba, mutane irina ba sa karantuwa (from every perspective). Ubangijin da Ya halicci zuciya Shi Ya sirrantata, Ya sanya ta zamo HIJABI a tsakanin ‘yan Adam da abinda ke zuciyar su. Don su sirrinta al’amuran da Ya boye cikin zukatansu. Ina kaunar Fa’izah da dukkan ruhi, zuciya da bargon jikina ‘but I cant express, neither explain.

Bakin da ya furta sharri, zalunci da rashin kirki, ya dawo yana furta SO  (will never be trusted) don haka Allah Yayi zamu cigaba da rayuwa ni da Fa’izah. Burina ya cika tunda ta zamo mata agareni kuma wani babban JIGO na rayuwata, kuma wani BANGARE na jin dadin rayuwata tunda mallaki na ce ko da har abada ba zata yarda da ni ba. Zaman mu tare a hakan ya fiye min zaman kuncin da na dandana a Ukrain ina azabtuwa daga soyayyarta.

          THE ISSUE OF MOMIN ABU

Sha’ani na da Momin ABU kamar yadda Fa’izah bata fahimce shi ba ko ince bata sani ba. Babu kuma wanda ya taba tararta ya gaya mata, Momin ABU bata daga cikin Zuri’ar Abubakar Bamalli.

Kamar yadda ya faru tun muna kanana, an tura Baban ABU bautar kasa Jihar Taraba, kamar yadda Baban Kaduna yake bamu labari, yana (service) din ne a gidan marayu na Jihar Taraba (Taraba State Orphanage Home).

Maimunatu marainiya ce, da ta tashi ba uwa ba uba, ba dangi a gidan marayu. Kamar yadda Baban ABU ya baiwa su Baban Kaduna labari, ni kuma a lokacin bani da wayo da nayi wayo ne naji labarin a bakin Hajjah.

An tura Ahmadu A.B bautar kasa Jihar Taraba, acan yaga Maimunatu, inda yake (serving) wato Taraba State Orphanage Home. Tana daga cikin ‘yan mata goma a gidan marayun da suka kai minzalin aure, sannan mafi nutsuwa da kamalar cikinsu.

Ya je ne a matsayin malamin (secondary school) dinsu, yana koyar dasu kimiyyar noma, wato (Agricultural Science).

Maimunatu hazikar yarinya ce wadda Allah Ya yiwa baiwar kwakwalwar fahimtar karatu.

Kamar yadda yake a cikin (psychological nature) na kowanne malamin makaranta. Wato kaunar hazikin dalibi da girmama shi hakan ce ta faru tsakanin Baban ABU da Momin ABU har kuma ya rikide zuwa soyayya mai tsafta da inganci. Wadda tausayi da kauna, shi ne tubali da ginshikinta.

Kamar yadda Hajjah ke bamu labari, ta ko’ina Ahmadu A.B ya hanga ya tauna baiga ta inda marigayi mahaifinsa A.B zai amince masa auren Maimuna ba.

Bar ta auren zumuncin gidansu da suka maida shi farillah, kuma shika-shikan rayuwarsu, rashin ASALI wani babban abu ne domin kashi tamanin cikin dari na yaran dake gidan marayu har abada ba’a sanin asalinsu ko ganin wani nasu. A haka suke zuwa duniya su koma, cikin kiyayewar Ubangiji.

Wannan yasa Ahmadu A.B cikin tsaka mai wuya da tunanin abin yi. Na farko ba zai iya barin Maimunatu ba, maganar ma ace ya hakura da ita bata taso ba, domin ba karamin sonta yake ba, kuma shakuwar dake tsakanin su ta wuce tunanin kowa.

Sai ya yi tunanin wadda yake ganin zata fisshe shi saboda KURUCIYA irin wadda ta faru dani akan Fa’izah!

Ahmadu yaje kotun Musulunci an daura musu aure da Maimuna ta yin amfani da malaman shi na Jami’ar Ahmad Bello. Ya dauko Maimunatu ta kawowa Hajjah, a lokacin da cikin Fa’izah wata bakwai.

Mafari kenan dana tashi cikin nunawa Momin Fa’izah wariya da kabilanci a tsakanin su Mama, Aunty Hauwa da tsararrakinta. Shi din ma na fatar baki ne, ko kallon banza ban taba yi mata ba, sannan a bayan idonta musamman idan Fa’izah ta bani haushi.

Hali ne na zuri’armu baki daya (kabilanci) da ‘ethnocentrism’ duk wanda ba daga zuri’ar A.B ya fito ba, to fa ba cikakken mutum bane.

Da Hajjah da marigayi suka ji kowacece Maimunatu hankalinsu ya tashi kwarai, sunyi fushi da Baban ABU fushi mai tsanani, sannan ‘punishment’ dinsa shi ne ‘suspension’ daga duk wani abu da ya shafi zuri’ar A.B zuwa wani lokaci da basu kayyade ba. Duk Ahmadu ya ce yaji ya gani, indai zasu barshi ya cigaba da rayuwa da ita.

A lokacin hatta zuwa daurin auren cikin gida an dakatar dashi, haka itama, zuwa wani sha’ani na mata kamar biki ko suna duk ba’a bukatar su.

Zance ko da Baban ABU ya damu to kadan ne tunda gogaggen dan boko ne wadanda (time matters a lot for them) wato lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a garesu. Sai ya yi amfani da lokacin ‘suspension’ din nasu ya koma makaranta ya nemi (degree) na biyu. Ita kuma ya sanyaata a (school of Nursing and Midwifery).

Ba da bata lokaci ba yana kammalawa A.B.U suka dauke shi ‘lecturing’ ya kuma samu gida a cikin makaranta, domin ada a gidan haya suke domin gidansa na A.B Quaters an hana shi mukullin an rufe. A lokacin tuni an haifi fa’izah har tayi wayo.

Kafin A.B ya rasu ya yafewa dansa Ahmadu, ya kuma karbi Maimunatu a matsayin surukar kaddara, bayan haihuwar danta na biyu, wato Abdallah, saboda kyawawan halayenta da zuri’a da tazo musu da ita mai albarka mai kama da nasu ‘ya’yan. Domin Abdallah sak mahaifinsa, Fa’izah kuma Aunty Rabi ta debo, sai dai ta dauko duhun Maimunatu. Dama kuma abinda basa so kenan na auren bare, domin zai haifar da sauyin kamanni a cikinsu. Amma tabbas da Maimunatu na da iyaye, da sun maida ta ga iyayenta ko Ahmadu zai mutu, sun karbeta ne saboda MARAICIN ta.

Nayi nadama, nadama mai yawa akan duk abinda na yiwa Fa’izah! Nadamar da bani da tabbacin akwai ranar da Fa’izah zata karbeta, tunda ba zata taba tsayawa ta saurari kalaman bakina ba. Fatana Allah Ya bani iko da damar nunawa Fa’izah kuskurena da karbarsa kafin na kwanta dama… Ya yaye min wannan ginshiran, domin ni kaina yana wahalar dani…”.

Da na kawo nan kuka na rikice da shi sosai, na kasa ci gaba da karatun, na ya da littafin. A guje nayi daki na ina kuka wiwi, na fada tsakiyar gadona na ci gaba da rasgar kuka.

Nayi kuka-nayi kuka har naji babu dadi. Wannan shaukin ke kara mamayar zuciyata yana kara habaka. Wanda da nayi tsai da zuciyata na fahimci abinda bana so in fahimta da gangan. Wato SON FA’IZ ne yake mamayata cikin kowanne dakika na bayan da ya barni. Wani irin so mai cin rai,  da tafarfasa zuciya.

***

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *