ZUMUNTAR KENAN BOOK 4 CHAPTER 7 by Sumayyah Abdul-kadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
***
Cikin wannan mawuyacin hali da sabuwar rayuwa mai wahalar da dan Adam a zuci da gangar JIKI da RUHI, duk da tarin jndadi da daular da ke zagaye dani, na cigaba da gurgurawa har tsayin wata guda. Ya zamanto ba abinda ke burgeni, ba abinda zan ci inji dandanonsa sai dai inci don in zauna da hanjin cikina lafiya, ba abinda nake son ji da gani sai FA’EEZ da MURYARSA… Wadanda ya haramta min haihata-haihata ya kuma toshe duk wata kafa da zan same su daga iyaye da ‘yan uwa.
Hutunsu Walida tuni ya kare amma nayi tsalle na dire na hana su komawa gida balle su koma makarantar, in sun bar gidan ban san makomar rayuwata cikin wannan fankacecen gida ba. Domin dai komai na gidan tun zuwansu su suke tafiyar dashi, girki da tsaftace shi.
Abinda nasan ina iyawa kawai shi ne jefawa Dawisu kwayoyin dawa da sake musu ruwan sha idan yayi kura. Na daina ado, na daina wannan kwalisar. Hana rantsuwa nasan ina wanka, wannan kullum ne insha-Allahu. To sai dai bayan shi fa ko Vaseline baya ganin tattausar fatar jikina. Don ma Allah Ya so ni lokaci ne na zafi, da ban san yaya fatata zata koma ba, saboda rashin kula da hakkinta.
Ina yin burushi sau biyu a rana, da safe kafin inci komai, da daddare in zan kwanta. Ina sauya kayan jikina bayan kowacce kwana uku, shima idan na gaji da mitar Walida ta cewa bana fesa deo-spray kayana suna tashi.
Na zama wata irin Fa’izatu mara sanin inda rayuwarta ta dosa. Na zama mara lissafi ko tunanin wasu hanyoyi na inganta rayuwa. A ganina duk wani jin dadin, walwalar da ingancin rayuwar zai samu ne idan naji muryar Abubakar Mukhtar, na kuma ganshi da idanuna. Ko da bai sake cewa yana sona ba ‘atleast’ in nemi gafararsa, inyi zaman aure dashi irin na iyaye da kakanninmu. Wanda babu I LOVE YOU din sai tarin mutunta juna da darajja juna da sauke hakkin juna da Allah Ya dora a tsakani. Tunda na riga na bar damar ta kubuce min. Dama na sha jin ana cewa, tana zuwa ne sau daya a rayuwa.
Hatta Yaya Rabi na tambaya lambar Fa’iz, na daure duk wani dizgi, shagube da izgilancin ta. Amma ‘yar tahalikar nan bata bani ba. Ta rantse ta maya idan na sake tambayarta sai ta kwankwatsa wayarta in daina damunta.
Mutum daya ya rage in tambaya ban tambaya ba, wato MAMA, don ita Hajjah bata rike waya, ko tana rikewa ‘issue’ dina da Hajjah a yanzu yafi karfin in nemeta a waya, ko in nemi lambar Fa’iz daga gareta. Ina jin bayan hauka da suka manna min a baya, idan nayi hakan zasu manna min fitowa daga turu. Kafin nan kafin in doshi Hajjaty a halin yanzu wani ‘issue’ ne na musamman mai zaman kansa, ban san da wane kalami, da wace fuska, da wane harshe zan doshi Hajjah in nemi gafararta ba, a bisa rashin kyautawar da nayi ta yi mata har da kauracewa. Anya Hajjar ta cancanci hakan?
Da wannan dumbin tunani marar madafa ko zabi ta kowanne bangare na hada komai na tattara wuri guda na mikawa Subhana, Sarkin da babu abinda ya gagare shi. Ni na raunana, al’amarin ya gagareni iyawa da sarrafawa don haka na mika masa dukkan al’amarin yayi min iko da iyawarsa, bani da tsimi bani da dabara, duk suna ga Sarki ALLAH!
Walida da Kausar suka kasa gane kaina, na farko bana zama dasu muyi hira, kamar yadda muka saba a baya. Bana sanya kaina cikin komai na al’amarin gidan, kullum ina daki nade cikin bargo kamar daddawa, bana umh bana uhm-uhm, sai gululun ido. Wadanda suka fada ciki suka zurma. Fa’iz kawai suka mace da son gani, ko son jin wani abu da ya dangance shi. Bazan iya kwatanta rayuwar da nake yi ba da halin da nake ciki, sai dai ince sunana FA’IZATU!!! Wadda son FA’IZU ke neman hallakarwa!!!
***
Mun wayi gari yau da gingimemen hadari, mai dauke da sassanyar iska, wadda ke kadawa tare da yayyafin ruwa kadan-kadan yaf-yaf akan rufunan gidajen unguwar Malali GRA, wanda hakan ya tada kamshin kasa mai dadi da dadin shaka a hancin kowanne bil’adama.
Dai dai lokacin da nayi wani juyi akan gadona domin gyara kwanciya don karin jin dadin kwanciyar tawa, naji ban zunguri Kausar ko Walida ba wadanda suke kwance gefe da gefe na. Hakan ya sanya ni bude ido sosai tare da tashi zaune. Can na hango su jikin gado suna shirya kayansu kaf a cikin (troller) din da suka zo da ita.
Sosai na wartsake na dube su cikin mamaki, a lokacin da suka gama kintsa kayan suka ja zip suka zuge jakar. Na tashi zaune sosai na ture bargon na ce.
“Ku, lafiya? Ina zaku je?” Walida ta mike tsaye tana gyara lullubin da tayi da mayafin Abaya baka.
“Lafiyar kenan, tafiya zamuyi”.
Na ce, “AMma ba haka muka yi da Momi ba, munyi da ita zaku kara sati daya, na rantse daga shi ko kwana daya ba zan ce ku kara ba. Kuji tausayina Walida, kuyi hakuri mu zauna”.
Idona ya raina fata, ya kuma cicciko da kwallah.
Kausar ta ce, “Allah ko minti daya ba zamu kara ba, balle yaya Fa’iz yazo ya taddamu a gidan nan ya sake korarmu. Tunda yau zai dawo zaman me zamu yi?”
Da farko ban fahimci me Kausar take nufi ba, abinda na fahimta shi ne Kausar yarinya ce mai riko kamar ni, har yau haushin korar Yayan nata take ji. Don haka cikin lissafina ban lissafa da abinda ta ambata ba sai fahimta nayi kawai bata so ta ci gaba da zaman. Ina wannan harhaden ma’anar ne, Walida ta dora da bayanin da ya warware maganar Kausar.
“Tun karfe bakwai ya kira wayarki, ni lokacin na tashi sai na dauka, Ya tambaye ni yaushe muka zo na ce da shi yau watanmu guda a gidan nan. Ya ce in sanar dake yana bisa hanyar dawowa karfe hudu na yammacin yau. A gayawa Yaya Bashir yaje filin jirgin saman Kano ya dauko shi ta can zai sauka.
Ya ce ina kike? Na ce baki tashi ba, ko in tashe ki in baki? Ya ce in kyaleki kiyi baccinki, amma in gaya miki sakon”.
Jina nayi kamar ina yawo akan gajimare, cikin wata alkarya ta madara da zuma saboda dadi, farin ciki, godiyar Ubangiji, murna. Sauran abinda naji a cikin zuciyata a lokacin (unexpressable) ne. Ciki kuwa har da faduwar gaba da bugun zuciya. Wanda suka fito a tare da farin cikin, murna da godiyar Ubangijin suka saukar da wata irin nutsuwa da salama cikin zuciyata.
Na lumshe ido a hankali. Ina rokon Allah a zuci idan mafarki nake kada Yasa na farka sai nayi tozali dashi din. Koda cikin mafarkin ne. Sai kuma na soma jin motsi cikin kaina, mai cewa in tashi in taka rawa, inyi juyi, in kuma rungume ‘yar uwa shakikiya da ta kawo labarin, in bata tukuici da duk abinda na mallaka.
Maimakon hakan, sai na mike na sanya hijabin sallah ta dake bisa darduma, wanda nayi sallar subhi dashi dama da alwalata, na sauko na dungura goshina gaban Subhana, na tsarkake shi, na tsarkake tsarkin mulki da iyawarsa!
Duka walidar da Kausar suna kallona, sai suka kama yi min dariya suna tambaya.
“Duka farin ciki ne Yaya Fa’izah?”
Ban iya na tanka musu ba. Na lula a wata sabuwar duniyar ta daban, ta tunanin wacce irin tarba zan shiryawa Hafizin Hajjah? Fa’izun gidan Baban Kaduna? ‘The one that is always hunting my dream?’ Wanda tunanin ranar dawowar tasa ke zuwa min a farke, wato (ido biyu), cikin barci, ranaku da darare guda casa’in da nayi ba tare da na sanya shi cikin idanuna ba? A yau ga ranar tazo, ‘so it will be a hectic and busy day; that needs planning and coordination’.
Na daga ido a hankali na dube su ina murmushi wannan karon, wani irin murmushi da bana jin na taba yin ni’imtaccen sa a rayuwata.
“To ai tafiya bata ganku ba, ajiye mayafin za kuyi ku tayani aiki ko? Mu gyara gidan, mu yiwa maishi girkin sannu da zuwa. Kuyi min kwalliya irin wannan da kuka caba, mai ‘eye-shadow’ da mascara, jambaki da lip gloss, ko ‘yan matana?”
Walida ta saki dariya, Kausar kuwa zumburo baki tayi da ya sha AVON lipstick yayi jajawur, Walida na fadin.
“Kin burgeni Yayata, baki taba sa ni farin ciki irin na yau ba. Allah Yasa ki dore da hakan, Yasa ki cigaba da hakan har zuwa karshen rayuwar ku, ko mu ma ‘yan baya ma yi koyi dake ko?”
Murmushi nayi cikin matsanancin nishadi, “Sai kuyi ta addu’a ya yarda ya amshi tuban nawa, ba kwa ganin yadda yayi ‘deleting’ dina ‘from the screen of his sight and mind?”
Walida murmushin tayi itama, “Ni na gaya miki zai yafe miki, yana sonki yadda ba kya zato. Idan daso kuma ba aibi, sai dai ‘FUSHI’ wanda ba inda yake zuwa. DOn baki san me ya ce min dazu ba”.
Na kamo hannunta da sauri na zaunar a kusa dani.
“Me ya ce miki Walida? Eye, gaya min? “.
“Cewa yayi “Gyara mata bargon rufar garin da sanyi, tunda ruwa ake”. Da na duba sai naga da gaske bargonki ya yaye daga kafafunki, na gyara miki. Ya ce, “Kin gyara?” Na ce, “Eh”. Sannan muka yi sallama. Don haka zai fi kowa farin ciki da kika gane kuskurenki, ki ka amshi laifinki. Ki ka kuma yi dammarar gyarawa.
Na lumshe ido a hankali ina mai gasgata kowace kalma dake fita daga bakinta.
***
Muna (kitchen), abinda zamu karya kumallo dashi muka fara hadawa, sai dai nasan ko naman Dawisu na ne na gidan nan yau aka soya, aka farfesa min ba zan iya ci ba, farin cikin da nake ciki, doki da kuzarin da har yayi min yawa ba zasu barni in iya kai komai baki na ba, bayan ruwan lipton, shima don ya warware min hanji, ba don ina da ‘appetite’ akanshi ba.
Kausar dake firar dankali ta ce, “UHm! Yaya Fa’izah in miki wani tsegumi mana?” Walida ta sanya bawon kwai da ta fasa cikin ‘dustbin’ ta ce.
“Uwar tsegumi, yau kuma gulmar wa za’ayi?”
Kausar tayi dariya, “Ba na kowa bane, naki ne. Don ni bana gulmar mutum sai dai in fadi akan idonshi don nasan illar yi da mutum”.
Cikin matsanancin nishadi nake wanda har baya kwatantuwa, don haka dariya suka bani.
“Ina jinki Kausar, me ya faru?”
Ta dubi Walida tana dariya alamar akanta zata yi maganar kuma Walidar bata sonta.
Ta ce, “Kwanaki ko? Na ji Baban Kaduna yana gayawa Baban ABU a dakin Hajjah, an yiwa Yaya Walida miji”.
Duka Walida ta kai mata nayi hanzarin boyeta na riketa.
“Wallahi ba zaki dake ta ba, ai ba ke take baiwa labarin ba ni take baiwa. In ba zaki iya ji ba ga hanya ki fita. Ina jinki Kausar, wane ne mijin?”
Kausar dake tuntsira dariya ta ce, “Ki canka”.
“In canka Kausar?”
“Eh, ki canka”.
“A cikin A.B ne?” “Eh mana”.
“Mus’ab?”
“Gaba dai”.
“Abba?” “Can gaba dai”.
“Sani?”
Ta ce, “Saura kiris”.
Na ce, “Shu’aib?”
Tayi dariya, “Wannan ya mata nisa, yafi karfinta”.
Na harareta na ce, “Badar?”
Tayi dariya, “Lallai kin manta magajin Ya Fa’iz wajen ginshira irin na ‘ya’yan A.B”.
Ta fara kular dani, na ce, Ke na baki gari wane ne?”
“A nawa zan fada miki?”
“Au, sai mun tsadance?”
“Eh Mana!”.
Na ce, “To #500 zan baki cash ba cheque ba”.
Ta mere baki, “Allah Wallahi yayi kdan”.
Da yake a zake nake da son jin abinda zata gaya min, na ce.
“To #1,000”.
Murmushi tayi, “Shi kenan sai mun gama aiki”.
Walida dai na jinmu bata kara tofawa ba sai anan ne tayi tsaki, muka ci gaba da aiki duk na kosa a gama ta gaya min don Kausar miskilar yarinya ce, na san ko na ci gaba da na ci ba gaya min zata yi ba sai sanda ta ga dama”.
Muka kammala muka baje a kasa kan ledar cin abinci muka fara karyawa, ko ince suka fara don ni abinda na ci din ba wani na azo a gani bane.
Ganin Kausar bata da niyyar gaya min har suka gama na kwada mata duka a baya, na ce.
“Ke don Allah ki gaya min mana, ko so kike sai jini na ya hau?”
Ta tintsire da dariya, ta kai kofi mug bakinta mai cike da kunun farar shinkafa ta kurba ta hadiye, ta ce.
“Gaskiya sai naci na koshi Ya Fa’izah”.
Don haka nayi zuciya na kyaleta.
Amma da suka gama ta shiga wata sabgar haushi ya kume ni, na ce (kamar zanyi kuka).
“Uhm! Ke nake sauraro fa Kausar”.
Ta ce, “Kai don Allah Ya Fa’izah, kya bari abincin da naci ya tsirga mini mana”.
Ta sha toka abinta muna haka wayata tayi kabbara (call tune) din kenan. Na mika hannu zan dau wayar ina fadin.
“Ke don Allah kada ki fada min in kina kaunar Annabi, ko ba dade-ko ba jima zanji ne ai”.
Kamin in dauka Walida dayake tafi kusa da wayar ta daga, ta ce.
“Hello Yaya!..”
“Eh ta tashi, abinci muke ci ma yanzun”.
“O.k toh”. Ta kashe.
Cikin zabura nake tambayarta, “Wane ne?”
“Yaya Fa’iz ne. Ya ce in kin gama cin abincin ya sake kira”.
Kamar in maketa don takaici, muryata kamar ta wadda ta sha duka.
“Amma ai kina ganin mun gama ko? Tun dazu muka gama ci fa!”.
Na karasa cikin karkarwar murya kukan takaicin Walida na neman kubce min ba da niyya ba. Ga idona ya ciko da kwalla. ‘Yan banzan yaran nan sai suka kyalkyale da dariya.
Karfe goma sha biyu da rabi na rana sai ga Shu’aib, Ya’u ya biyo bayansa niki-niki da kaya, jakunkuna saiti biyu samfurin (Argos).
Na mike ina yiwa Shu’aib sannu da zuwa, Ya’u na shigo da jakunkunan falo. Ya zauna yana satar kallon Walida, ita kuma yana shigowa sai naga ta bar falon bata gaishe shi ba kamar yadda Kausar tayi, sai yasa murya yana kiranta amma bata dawo ba.
“Ke ‘yar kauyen ABU… Ina Yaya Sa’id Na’ibi A.B Giwa?”
Cikin mamaki na ce, “Au, dama Yaya Sa’id ne mijin da Kausar ke fadi tun safe take ja min rai ta ki gaya min?”
Yayi dariya, “Nima haka naji ana fada, ni na ce a bani an hana ni wai tunda ni na furta ba za’a bani ba. Yaya Sa’idu za’a baiwa, amma ai munga wanda ya furta aka bashi ba tare da an tuna cewa shi ne ya furta din ba, saboda mu ne ba’a so kawai sai Yaya Fa’iz”.
Murmushi nayi ya kuma matukar bani dariya da maganarsa. Ashe dai ba ni kadai nasan Hajjah tafi son Fa’iz akan kowa ba kowa ma ya ganeta ayi magana ta ce shima yafi kowa sonta, mu bama mata sai dai ta mana, Hafizinta fa? Komai nashi nata ne, komai ya samo ita yake fara tunowa kafin iyayen da suka haife shi.
Ban kai karshen zancen-zucin nawa ba Shu’aib na tsinkaya yana fadin.
“Ga kayan mijinki nan sun riga shi isowa, yanzu haka daga Airport din Malam Aminu nake, shi sai yamma zai iso wai sai biyar jirginsu zai sauka. Yaya Bashir zai je ya taho dashi ni yanzu haka Giwa zan wuce”.
“Allah Ya kiyaye hanya Yaya Shu’aibu”.
Na fada ina shiga (kitchen) don kawo mishi abinda zai ci a hanya ko da ba abinci bane ya samu na motsawa a baki.
Ya’u ya shigo da kayyakin cefane har da buhunhunan kayan abinci ya shiga (store) dasu wanda hade yake da (kitchen), sai nama nau’i-nau’i, nasa Kausar ta adana kowanne daban a (freezer).
Shu’aib ya mike zai tafi yana godiyar ‘snacks’ da dambun naman da na zuba masa a leda, ya ce.
“Af! KInga ko na manta da sakon Mama a mota, bari inje in dauko”.
Ya koma ya dauko ya dawo ya miko min.
“Ta ce kowanne akwai takarda a cikinsa, yana dauke da yadda za’ayi amfani da shi”.
Na amsa da hannu bibbiyu ina zabga godiya kamar shi ne Maman.
Na ce, “Ka turo min Malam Isah (direban gidan Baban Kaduna) ko ta waya ne zai maida su Walida Zaria anjima”.
Murmushi Shu’aib yayi, “Ai yayarmu, haka za’a kora su ‘so early’ don maigidan ya dawo har an gama cin amfaninsu za’ayi (dumping) dinsu?”
Na harare shi cikin wasa, “NI ban kore su ba, su suka kori kansu. Tun safe suka hada kaya za su tafi da kyar na samu suka kai yanzu”.
Shi dai ya fice yana min dariya, ya barni da guntuwar kunyata a katara. Cewa yake.
“‘Yau Mama zata sha labari idan na dawo daga Giwa, zata yi murna da farin ciki kwatan-kwacin na a zuba ruwa a kasa a sha. Fa’izah, ta sauke tata GINSHIRAR ta Bamalli, saura Pilot Fa’eez Giwa”.
Na ce, “Lala! Shu’aib ba ma haka da kai kada mu soma, kada kayi min sharri. Su Walida su suka nemi tafiya ni ban kore su ba”.
Ya ja motarshi kowannenmu cikin matsanancin nishadi marar misali.
Ni da Walida muka share ko’ina na gidan nan kal-kal, muka goge, muka kade, musamman (side) din Fa’eez, da kaina na wanke (toilet) din shi na kawata da (toiletries) da turaren bandaki ko ina sai tashin kamshi da (atmosphere) mai dadi.
Na canza (bedsheet) din dakin da wani (light-blue) mai hade da (duvet) da Baban Kaduna ya bamu tsarabar Umrah ni, Ummi da Zanirah. Na feshe (bedroom) din da (room-freshner) na ‘HARAMAIN’. Na kunna na’urar sanyaya daki duk da sanyin da garin ke dashi, nasan daga ‘Europe’ zai fito, don haka zai bukaci sanyin.
Sannan muka yi sallar azahar muka fada (kitchen). Da taimakon su Walida komai ya tafi dai-dai cikin dan lokaci, munyi faten acca da bushasshen kifi, baked moi-moi, tuwon shinkafa da miyar yakuwa da alayyahu da kabewa da tantakwashi zallah. Sai gashin ‘Turkey’ wato tolo-tolo.
A fannin abin sha munyi coconut and milk shake, carrot drink, sai zobo mai abarba da pinaplple flavour. Dukkansu fresh da na sarrafa da kaina.
Na ce a raina, “Yau babu ‘chips’, babu ‘chicken’, ‘you need change HAFIZIN HAJJAH, as everything around us would completely change. Babu abinda LOKACI baya canzawa. ‘With TIME change is possible in everything we do”. (Lokaci yana canza komai).
Sannan na koma ‘snacks’, ba tun yau ba, ba tun jiya ba na sha jin Hajjah na ba da umarnin a yiwa Fa’iz (samosa) ‘best snacks’ dinshi kenan. Don haka shi kadai muka yi, muka adana komai inda ya dace.
Walida da Kausar suka gyara min komai suka goge min (kitchen) tas suka wanke duk kayan da muka bata, sannan suka shiga wanka.
Karfe hudu Isa direba yazo suka tafi muna cike da kewar juna, sai da Walida tayi hawaye.