ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 10 by Sumayyah Abdul-kadir

 ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 10

by Sumayyah Abdul-kadir


Na yi iyaka_ tunanina amma hankalina bai bani ba. Baban ku ma ya yi tambayar duniyar nan amma ta kafe sai ana saura kwana uku daurin auren sannan kowa zai j1”. 


Na ce, “Kai wannan tsohuwa da rigima take, ke Zanirah to mene ne abin kuka? Muma muna tafe, kin sani dai ko ba yanzu ba mawuyaci ne Hajjah ta kyale ki zuwa jami’a da shekaru kusa da ashirin, kai Hajjah ta yi dai-dai….” 


Zanirah ta taso kamar za ta make ni, ko me ta tuna? Sai ta juya ta yi bed room din Mama tana sharbar kuka wiwi kamar ranta zai fita. 


Ni dai Allah-Allah nake karfe uku ta yi na bar gidan zuwa Zaria kafin Yaya Aliyu ya dawo ya taddani, duk da Aunty Hauwa ta ce in bi umarnin makaranta duka gidajen biyu ba zan iya zama ba, can Ummi mun yi fada, nan Yaya Aliyu zai tirke ni. Ya kasa ganewa cewa nauyinsa da girmansa da nake gani ba zai barni in ba shi amsar 

wasikarsa ba. Na yi kokarin hakan amma na kasa. 

Karfe ukun na yi na dauki jakata na yafa mayafi, na yiwa Mama sallama na roke ta tasa Malam Garba ya kai ni Zaria. Zanirah ma ta dauko kayanta ta ce, ba za ta kwana a gidan ba ta fasa tunda Mama ta goyi bayan ayi mata aure da mijin da ba ta sani ba. 

Malam Garba ya ja mota, bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidanmu, yana aje mu ya juyo Kaduna. 

‘Yan kannena kam sun yi farin ciki da ganina, suka shiga gyara mana daki. Daga momi har Baba babu wanda ya dawo aiki, Abdallah mai bi mani ya girma, yanzu yana aji uku na sakandire. Yayin da Walida ke aji shidan firamare ‘yar shekaru goma, Kausar na aji hudu, sai auta Walid yana Nursery. 

Yaran gidanmu akwai nutsuwa da kyakkyawar tarbiyya, suna masifar son junansu, ko ina suna tare. Idan Momi da Baba sun tafi aiki su kulle kansu a gida suyi ta karatu, in sun gaji 

suyi game suyi kallo, ga son baki, kula da sallah da son zuwa Islamiyya nan cikin (Area One). 

Walida ke fiddo ire-iren aiken da Yaya Fa’iz ke musu na kayan wasa masu aiki da batir da jirage masu tashi sama sosai na Abdallah masu aiki da (remote control). Zanirah ce kawai ta nuna sha’awarta ni ido kawai na bisu da shi. 

Momi kan yi abinci ne mai yawa ta cika musu cooler, don haka mun samu abinci mai rai da motsi, mun ci mun yi kat! Mun yi wanka ina shafa a gaban madubi daure da faffadan tawul, ya yin da Zanirah ke gefe ta mike kafafunta cikin ‘sofa’ sanye da doguwar riga a jikinta, ta zuba min ido kurum. 

Walida ta kyalkyale da dariya ta ce, “Aunty Fa’izah Yaya Zanirah fa kallon ki fa take yi’. 

Na dan juyo muka yi ido hudu da Zanirah, na ce, “Ya dai amarsu? Ko ta 

Samu ne?” Ta tabe baki kamar taliya ta ce, 

“Amma kuwa wannan ango ya debo da zafi. Imagine Fa’izah yadda za ki yi zaman aure da wani alhalin zuciyarki, ruhi da gangar jikinki duka suna ga waninsa’’. 

Na dube ta na ‘yan sakanni, na ce, ‘““Hakuri da juriya ya zama dole gareki Zanirah, rashin so daga mace na dan lokaci ne, na namiji shine ke lasting”. 

Ta ce, “Ta ya ya zan yarda cewa mutumin da Hajjah ta badani gare shi yana sona?”’ 

Na ce, “Zanirah cewa nake Maman Kaduna da Baban Kaduna, Baba Na’ibi da Maman Yaya Aliyu, Yaya Hauwa da mijinta, su Baba Barau da Yaya Ibrahim, Sadi, Salisu, Sani, Aunty Rabi da Yaya Muftahu kadai sun ishe ki ishara. Zanirah babu yadda za ayi HAJJAH HADIZA GIWA ta hada aure ayi dana saninsa ko ayi dakacen wanzuwarsa, ko kuma ya zama mara dadi tsakanin ma’auratan. Sai dai ma daga baya a zo ana gode mata. 

Saboda haka ki kwantar da 

hankalinki ( a ganina fa) Hajjah ba za ta kai ki inda za ki wulakanta ko ki tozarta ba. Insha Allahu babu komi cikin wannan auren face alkhairi. Ko ni da nake ganin zamu yi auren “So” da Yaya Aliyu ina gudun kada in zo auren bai mani dadi ba kamar na sauran zuri’ar A.B ba. Don haka har yanzu na kasa bawa Yaya Aliyu amsa”’. 

Ban juyo ba ina kallon ceiling ne dalili kenan da ban ga halin da kalamaina suka jefa ‘yar’uwata Zanirah ba. Ashe Zanirah fiddo ido ta yi warwaje, dafe kirji tare da bude baki duka a lokaci daya. Idanuwanta suka jirkice cikin dan lokaci tare da wuntsilowa daga cikin ‘sofa’. 

Sai dai ‘yar’uwa ta gaskiya wadda ZUMUNCHIN har cikin zuciyarta yake ta yi kokarin controlling kanta ta hanyar komawa cikin sofa ta kalmashe ta runtse ido, tare da dafe kanta dake neman rabewa gida biyu saboda sarawa da juyawar bazata da ya yi mata. 

Cikin sassanyar murya mai dauke da yankewar buri na rayuwa ta ce, “Wane Aliyu Fa’izah?” 

Na mai da hannuwana baya na sarkesu na doshi taga a hankali na tsaya ina kallon waje ta tagar ina murmushi, na ce, “Aliyu nawa muke da shi cikin A.B. Zanirah? Baya ga Aliyu Haydar Na’ibi A.B Giwa?” 

Na juyo gaba daya na fuskanceta ba tare da na gane rikicewa da gigicewar da Zanirah ta yi ba na isa ga jakata na zuge na fiddo wasikar Aliyu na mika mata ina fadin “Ban iya soyayya ba Zanirah balle kalamanta masu sanyi. Ban san soyayya ba Zanirah, ban san kalamanta ba. Na shafa duka duniyar kwakwalwata in nemo kalaman da suka fi kowanne dadi ga masoyi a duniya in rubutawa Yaya Aliyu na rasa baya ga (I love you too). Taimake mi ‘yar’uwa ki rubutawa Yaya Aliyu kalaman soyayyar da suka fi kowanne dadi da gardi a duniya ko da layi biyu ne kacal, ya san cewa ‘I do care for him too much’ ya san cewa ruhi, kalbi 

da gangar jikin Fa’izah gaba daya yana kaunar Yayanta Aliyu!”’ 

Hawaye wani na bin wani_ sharatsharaf a fuskar Zanirah, a ya yin da take karanta wasikar Aliyu ga Fa’izah, tasa gefen rigarta ta share da sauri ta yagi wani gefe a karshen takardar ta ce, “Bari in rubuta maki amsa Fa’izah, ko dama can wauta ta hana ki gane Yaya Aliyu na mutuwar son ki, amma kowa ya sani. Ki rike Aliyu da kyau, ki yi mai rikon magnet. 

Yaya Aliyu ba irin mazan da ake yiwa rikon sakaka bane. He has all the qualities and all the attribute to be love upon. Ina da kyakkyawan zaton cewa, muddin Yaya Aliyu ya zamo miji a gare ki babu ke babu ganin wulakancin namiji da “‘yan’uwa mata ke suffering, saboda Yaya Aliyu na daban ne. Babu ke babu kalmar nan da mata suke kira kamar ayar Alkur’ani wai “Duk wadda ta ce namiji uba ne…..” Domin Aliyu uba ne, uwa ne, aboki ne, dan’uwa ne, miji ne abin so da duk wata diya mace za ta yiwa kanta burin samu”’. 

Sakin baki na yi da kunne duka ina sauraron Zanirah. Me ya kawo duka wannan dogon sharhin? Ya ya aka yi muryarta ta canza haka kamar ba muryar Zanirar dana kwana na tashi da sani ba, tana magana cikin fidda rai da yankewar buri? 

Na ce, “Za ki rubuta min amsar ne ko dauko diro zan yi in aje miki ki hau ki ci gaba da fadin how lucky I’m for having Aliyu as a husband?” 

Ta yi murmushi ta ce, “Zan rubuta mana sister nah’. 

Ta kammala cikin sakan biyu. Ta taso har inda nake tsaye jikin taga ta bani, ta juya ta shige toilet. 

“If all my body is full of mouth, it’s not enough to expess the kind of love I had on you Yaya Aliyu”. 

Na yi murmushi na rungume takardar ina fadi a cikin daga murya, “Na gode Zanirah…..” 

“Da ta yi miki me?” 

Gaba daya muka duba kofa ni da Walida, Yaya Aliyu ne! 

Walida ta bude baki tana dariya, ni kuma na yi wuf! Na shige uwar daki cike da takaicin a yanayin sutturar da ya same ni na sanyo riga da zani da dankwali. Ina kokarin sanya dan kunne ya tsaya a bakin kofar sai na samu kaina da kasa hada ido da Yaya Aliyu a yau, sai sunkuyar da kai nake. Ya yi dariya ya juya yana fadin ina jiranki main falo. 

Da ya fito dai-dai toilet sai na jiyo shesshekar kuka. La shakka Zanira ce take kukan da ba ta so a ji, ko a gani, shi yasa ta shige toilet take yin sa. Na tabbata ba zai wuce a kan aurenta bane. Ban yi mata magana ba, domin Zanirah mutum ce da ba ta son fadin damuwarta ga kowa, ba kuma ta son shisshigi cikin al’amuranta. Sai na fita falon a hankali duk jikina ya yi sanyi. 

Yaya Aliyu ya dubi Kausar da Walid da suka yiwa cinyoyinsa dabaibayi ya ce, “Oya!” Ya fiddo alawar Zanirah a da (Bounty) ya mikawa kowannensu, ya ce, “A tafi wajen Yaya Abdallah ga shi can yana exercise kuma ku yi, ko 

kwa rage wannan kumburin naku”. Duk suka ware da gudu. 

Abu ne da Hajjah ta raine mu da shi wato muddin bako ya zo kowanne iri ne abu na farko da zamu yi mishi shine, ba shi ruwa da lemo. Ban yarda mun hada ido ba har yanzu na yi kitchen na dauko lemon ‘Chivita’ da gorar ruwan ‘Faro’ masu sanyi da kofi na ja karamin center table gabanshi na aje mishi. Baya komi sai bina da ido, kamar yau ya fara ganina. 

Na daga gorar ruwan da har raba take don sanyi ina budewa na soma tsiyayawa cikin tambulan, amma kallon da Yaya Aliyu ke bina da shi ya haifar min da karkarwar jiki, na tsula mai ruwan a cinya. Ya mike da sauri ni kuma na saki kofin bisa tayal ji kake taratsatsatsa….. 

Muka yi tsaye cirko-cirko kamar zakaru, cikin murya mai sanyi ya ce, ‘“Yaushe Fa’izah ta koma mara imani ne?” 

Ban san sanda na saki dariya ba. Duk yadda Yaya Aliyu ya kular da kai sal 

ya san yadda ya yi ya baka dariya. Na ce, “Ni da imanina bai je ko ina ba. Bari in baka wani”. 

Ya ce a harzuke, “Ke look! Bana bukatar ruwanki ba shi ya kawo ni ba. In shi ya kawo ni ai na san hanyar kicin din, kawai Malama ki bani amsar takardata. Da kuma _ dalilin wulakancin da kike min tsahon wata uku? Tun daga Legas na tako na kawo takarda a baki. An tabbatar min an bakin, to mene ne dalilin kin bani amsa just a single yes or no? 

Duka cikin kwanakin aikina nake jele daga Legas zuwa Giwa don kawai na karbi amsar ki amma Fa’izah babu. Anya akwai sauran imani cikin ranki? Na ce kar ki bar Jabi Road sai na dawo daga Giwa, na je na tarar kin gudo nan. Nan din ma ban yi fushi ba na biyo ki kin jike ni sharkaf da rawan sanyl, anya Fa’iza ke ce?” 

Yadda yake maganar cikin sanyi, sai ya yi bala’in bani tausayi. 

“Fa’izah magana nake fa?” “To Yaya Aliyu ba ka zama?”’ “Ba a zaman, kawai ki bani amsata, 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *