ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 7
by Sumayyah Abdul-kadir
gidan da maraice, ina uwar dakin Hajjah ina shirya mata kaya cikin (wardrove), ita kuma tana falo tana sallar walha na ji sallamar Baba Muntari.
Hajjah ba ta amsa mishi ba, nima ban amsa ba kamar wadda akadinkewa baki. Ina jin shi yana waya da Baba Barau, Sadi, Sadisu, Na’ibi, Ibrahim yana fadin duk su hallara falon Hajjah tunda Asabar ce kowa yana gida.
Na ci gaba da abin da nake yi amma daga inda nake ina iya juyo hucin Baban Kaduna da ajiyar zuciyar da yake yi akaiakai. Ba a jima ba suka shiga shigowa daya bayan daya da sallama yana amsawa a wahale.
Zuwa lokacin Hajja ta idar suna ta gaggaishe ta tana amsawa. Sannan ta dubi Baba Muntari da kulawa da kauna ta manyantaka, ta ce, “Wa ya tabo Muntari ne? Wannan sammako da taron gaggawa haka?”
Baban Kaduna bai tanka ba ya ciro takarda cikin breif case dinsa ya mikawa Baba Na’ibi, Baba Na’ibi ya karanta ya
mikawa Ibrahim, Ibrahim ya mikawa Barau, Barau ya mikawa Sadi, Sadi ya mikawa Sani, Sani ya mikawa Salisu, dukkansu suka hada baki suka ce da Hajjah.
“Takardar withdrawal ce (kora daga makarantar Fa’iz Abubakar Mukhtar) daga Polytechnic a bisa hujjar rashin zuwa aji kwata-kwata, rashin contineous assessment (CA), sai za ayi jarabawa kawai yake zuwa. Idan kuma ya je yadda aka ba shi answer sheet haka yake ajiye ta baya iya rubuta komi a ciki, sai sunansa da registration number. An dora shi a kan (probation) tun shekarar baya bai gyara komai ba”.
Duk suka yi shiru suna sauraron cewar Hajjah. Ta jima ba ta yi magana ba, sai daga bisani ta ce, “Ba zan ce komai ba sai na yi magana da Hafizin’”’.
Baba Muntari ya zo iya wuya, ya ce, “Ki gafarceni Hajja, duk lalatar da Fa’iz ke yi don ya samu faragarki ne. Na yi na yi a daina bai wa Fa’iz mota kin ki. Ba shi da aiki sai tukin mota da gyaranta in ta lalace,
duk kanikawan garin nan sun san Fa’iz, in ya ce miki yana makaranta to yana tashar mota.
Jiya-jiyan nan (C.J.D) din da nasa ya dinga bibiyar min shi tun lokacin da ya ce miki ya kama daki a makaranta jikina ya bani ba haka kawai ba, don mutumin da karatun boko bai dame shi ba me ya kai shi tarewa a makaranta? To rahoto ya zo min cewa, Fa’iz ba a makaranta ya tare ba yana Kaduna Express (tashar motar Kaduna) ya zama direban peageout da express masu zuwa gari-gari ba ya makaranta…..”
Gaba daya suka dauki salati har ita Hajjah. Ban san sanda dariya ta kubuce min ba, na yi hanzarin shigewa toilet na sheka abata na more. Ban dai ji karshen tattaunawar tasu ba sai fitar su bayan sunyi mata sallama. A raina na ce, hakki ba karya bane. Ina zaace hakkina ba zai lalata Hafizin Hajjah ba.
Washe gari ina wanka Fa’iz ya shigo falon Hajjah, jikina duk kumfa amma haka na kwara ruwan na fito kar labari ya wuce ni, ina ji Hajjah na cewa, “Ubanka gata yake maka, kyakkyawar rayuwa yake so
maka ba wani abu ba…..
Ina jin sanda yake ce mata, “Hajjah ina da matsala ne, hannuna kyarma yake duk lokacin da na rike biro. Hajjah bana iya rubutu”’.
Abin da ban taba ji ba a duniya, wato shesshekar kukan Fa’iz. Ya ci gaba da cewa, “Hajjah ko wacce makaranta ce na yarda a kaini, amma kada a rabani dake. Ba zan iya rayuwa bakya kusa dani ba Hajjah. Akwai wata makarantar irin ta ai a nan Zariya a kai ni mana. Wallahi na yarda zan je, amma ni bana son in yi nisa daku ko kadan, don Allah ki taimake ni Hayja, ke kadai ce za ki iya lankwasa shi’.
Hajjah ta dauki carbinta tana kokarin ficewa daga dakin kada ya karasa karya mata zuciya. Hajjah Hadija da Hafizinta Fa’iz (Abubakar) sai Allah.
Cikin dauriya ta ce, “Na gama maganar nan dasu tuntuni Fa’iza za ka Rasha (Russia) kana so ko baka so. In kuma ka isa, je ka ce dasu baka so ba za ka ba. Sun ce kasashen da suka ci gaba ba a yin
rubutu da biro ya yin duk wani abu da ya shafi karatu, tafawa ake a computer (typing). Tunda dai ba ni na kawo maganar nan ba Ubanninka ne, to don Allah ka shafa min lafiya’.
Shiru Fa’iz ya yi yana tsane hawayen idonsa da hankici. Abun duniya duk ya bi ya dame shi. Ya san yau an canza masa Hajjansa, “‘ya’yanta sun gama yi mata famfo, kuma ya santa kaifi daya ce, tunda ta ce haka ba za ta taba canzawa ‘ya’ yan nata ra’ ayi ba.
Shi kam bai son ya tafi ne ba don komi ba sai don yarinyar nan Fa’izah ‘yar Maimuna za ta yi farin ciki ta sakata ta wala a gidan, don ya tabbata shine kadai matsalarta a zaman gidan. Shi kuma a duniya mai adawa ne da farin cikin Fa’izah, in da abin da ya ki jini a duniya to ya ga Fa’iza cikin walwala a gidan nan.
To wai shin meye dalili? Me yasa ya tsane ta kamar ba jininsa ba? Me ta yi masa ya tsane tan? Meye laifin ta? Meye aibunta? Me take yi wanda bai so? BAT
SANI BA! Tabbas akwai katuwar (7) alamar tambaya cikin kwakwalwa da zuciyarshi game da yarinya FA’IZAH A.A. GIWA.
Watanni uku da suka biyo baya, Fa’iz ba shi da sukuni duk da yana cikin gidan kullum yana baskwata. Haka kuma a lokacin muna cikin zangon farko aji biyar. Damuwar har ta sabbaba masa ciwo, tun yana yi a tsaitsaye har ya kwantar da shi hajaran-majaran.
Wannan ya ta da hankalin Hajjah ba kadan ba, ta yiwa Baban Kaduna maganar a kyale Fa’iz da tafiya karatun nan tunda abin ya kai ga taba lafiya.
Baban Kaduna ya ce, “Don Allah don Annabi Hajjah ki fita daga maganar nan kada kema ya kwantar mana dake, amma sai dai ya mutu na huta ganin dana yana direban tasha in dai ba zai yi yadda nake so ba’. Sai Hajjah ta yi shiru.
Cikin wani hutu da muka zo Fa’iz na shirya kayan shi cikin troller (akwatin tafiye-tafiyen bature) da muke kira (tura ni
a tiles). Ummi ta yi sallama ta ba shi kaya cikin leda da Baba Na’ibi ya aiko masa ya yl guzurin tafiya.
Ganin yana loda kaya a jaka ta samu kujera ta zauna a gefensa a darare, ga mamakinta bai mata tsawa ba, bai hantare ta ba balle ya kore ta.
A hankali ta ce, “Yaya Fa’iz tafiyar kenan?”
Ya dago ya dube ta ya yi dan murmushi, “Eh, Ummi ya zan yi? Baban Kaduna ya dage. Daga nan Kaduna na nufa, daga nan mu wuce Kano inda zamu tashi ta filin jirgin Malam Aminu Kano ni da shi’.
Ummi hawaye ya cicciko idonta dai-dai sanda idonta ya kai ga wani karamin album saman kayanshi da yake hadawa. Ta dauka ta bude shafin farko ta _ shiga dubawa.
Shafin farko hoton Fa’iza ne ta yi tagumi jikin varanda ‘terrace’ na gidan Hajja. Shafi na biyu kyakkyawan hoton Fa’izah ne ta yi tagumi a falon Hajjah. Haka shafi na uku Fa’iza sanye da koriyar suwaita mai kauri da jan siket kanta ba dankwalli,
wanda hakan ya sakko da jelunan kitson (shuku) dake kanta har bisa dogon wuyanta, tana rungume da (teddy bear) a gidansu dake Zaria. Sai kusan karshe ne ta ga hotunansu da sauran kannensa duka na Giwa da na Kaduna, har da su Walida amma 80% ba album din hotunan Fa’izah
ne. A matukar mamakance Ummi ta daga ido
ta dubi Ya Fa’iz hankalinshi baya kanta yana ta shirya kaya haikan. Ta zari mai rungume da Teddyn ta ce, “Hoton nan ya yi kyau Ya Fa’iz in dauka? Fa’izah ba ta san da shi ba ma sam, don Allah ina ka same shi?”
A lokacin ne ya dago ya dube ta, ya zaro ido ya ce, “Ke! Wa ya ce ki taba mani album? Ina ruwanki da kayana?” Ya fauce album din ya danna a jaka ya ja zif. Ya shiga zuba mata bala’i ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba.
Ummi dariya kamar ta kashe ta san (borin kunya ne yake nannade shi da hauka). Ta ce, “Ka yi hakuri Ya Fa’iz ban san baka so a taba ba”. Ta dauki wasu daga cikin
hotunansa ta ce, “In dauki wadannan Ya Fa’iz?” Ya dube su daya bayan daya ya ce, “Me kika ce?”
Ta mike da hotunan a hannunta za ta fita, har ta kai bakin kofa ya ce, “Tsohuwa!” A kufule ta juyo don ya kirata da sunan da ta tsana a rayuwarta, amma ga mamakin Ummi sai ta ga ya yi murmushi.
“Don mi kike son hotona bayan duk kun tsane ni don kawai ina gaya muku gasiya?”’
Ummi ta girgiza kai tana dariya, ta ce, “Allah Ya Fa’iz bamu tsaneka ba, daman can kai ne ka tsanemu, kuma mu har mun manta ma wallahi. Mun san kuruciya ne ga shi yanzu tunda ka shiga Poly ai baka cika shiga lamarinmu ba balle ka takura mana. Wani abin ma in aka ce ka yi ai ba za ka yi ba”.
Ya ce, “Ko? In ku kun manta ai Hussainar taku ba za ta taba mantawa ba. Domin na zalunceta na wulakanta ta na ci mata mutunci da yawa, wanda nima wallahi ban san dalili ba. Yanzu_ har nauyinta nake ji saboda halin RAI da
muhimmancin ZUMUNCI, kunyarta nake ji wallahi-wallahi Ummi…..”
Ummi ta yi sakatoto! Tana duban sa cike da shakkar ba da Fa’izu (Abubakar) take magana ba, wani ne dai mai matukar kama da shi. Ko kuma mafarki take yi.
Ta ce, “Yaya Fa’iz wai kana nufin Fa’izah?”
Ya girgiza kai ya ce, “It may be itan, it may also be kuma ba itan ba…..”
esses ”’Ban gane ba?” Ummi ta tambaya her voice is trembling (muryarta tana rawa).
Ya ce, “Ba za ki gane ba Ummi, kowa ma ba zai taba ganewar ba, amma Allah ya ga zuciyata na yi nadama da dana sanin abin da na yiwa Fa’izah’’.
Ummi ta dan yi zuruu! Tana dubansa, ta ce, “Na tabbata na kuma hakkake cewar Fa’iza ba ta rike ka ba sam a zuci Ya Fa’iz, kullum addu’arta Allah ya shiryi Ya Fa’iz ya ganar da shi illar ‘KARYA, MUGUNTA, ZALUNCI da muhimmancin zumunci’’.
Fa’iz ya dafe kai ya dubi Ummi duk idanuwansa sun sauya launi, ya ce, “Yanzu
Ummi duk da wadannan sunayen Fa’izah ke kallo na? Kuma haka Ummi?” Tune din muryarshi wannan karon (in subdued) a karye.
Ita ma Ummin ta karaya a wannan gabar, ban da girgiza kai alamar, “A’a’”. Ba abin da ta ce. Ya yi mata alamar ta tafi kawai ta kyale shi.
Washe gari kowa ya shirya za a tafi rakiyar Fa’iz, sai na zari mayafi na yi wuf na shige gidan Baba Barau na buya a kitchen. Neman duniya Ummi ta yi ba ta ganni ba, dole suka hakura suka shiga mota.
Daga tagar kitchen din ina hango shigar Ya Fa’iz mota, yana dan waiwaye kowacce kusurwa ta A.B Bamalli Estate kamar mai neman wani abu. Daga bisani ya shiga motar Ya Aliyu ya ja suka fita a get din.
Na yi wata irin doguwar ajiyar zuciya kamar an zare min kaya a kafa, kamar kuma an sauke dutsen Dala da Gwauron Dutse daga kaina. Na yi wata irin kakkarfar ajiyar zuciya.
2K 3K 2K
BAYAN SHEKARA DAYA
Shekarar ta zo ne da tarin sauyuka masu yawa cikin A.B Bamalli Family. Tafiyar Fa’iz da tafiyar Yaya Aliyu bada jimawa ba jami’ar Lagos yin digiri na biyu.
Don haka a hutu na gaba da muka zo mun yi kewar Yaya Ali ba kadan ba. Na yi kiba na yi bul-bul na dan yi haske dai-dai misali, sai sheki da kyalli nake yi, ke kuwa babu fargabar Fa’iz ko kadan wanda shine kadai matsalata a rayuwa.
A wannan hutun da muka zo ranar wata asabar ina dakin Hajjah ina sallah na jiyo sassanyar muryar Yaya Aliyu a tsakar gida yana gayas da Hajjah. Bai tambayi kowa ba, bai tambayi komai ba daga gaisuwa sai “Hajjah ina Fa’izah ne? Ban ji motsinta cikin gidan nan ba”.
Hajjah ta ce, “Tana ciki, nake jin sallah take. Ka san in aka soma doka nafilfilin nan sai Allah. Ai ma hushi ake da kai tunda ka tafi Lagso ba sako ba aike balle waya’’.
Ya kama kai abin ban dariya, ya ce, “Oh! Ni Aliyu Bamalli na shiga uku!!” Ya yo cikin dakin da gudu-gudunsa. Hajjah ta yi dariya ta ci gaba da abin da take yi.
Zaneerah ta ya da tawul din da take tsane jikakken gashin kanta, ta zaro ido ta wara hannuwa tare da daka tsalle ta dire gabana ta ce, “Yaya Aliyuuu! Muryarshi a tsakar gida Fa’izah!!” Ta yi wuf ta yi bakin kofa zata fita.
Na ce, “Ke Zanirah baki da hankali ne? Haka za ki fita daure da tawul?” Zanirah ta dubi kanta ta ce, “Oh! Na gode Fa’izah, kin san Allah duk na rude sabida murna’”’.
Na bita da kallo a lokacin da take zurma doguwar riga a jikinta, jikinta har rawa yake yi. Ni yadda take rawar jiki a kan Yaya Aliyu da al’amarin sa, ko ni da ya fi nuna kulawarsa a kaina bana yin hakan balle irin wannan zumudin, ni haushinsa ma nake ji wallahi tunda ya tafi bai neme mu ba, ba waya ba sako.
Tana kokarin fita yana kokarin shigowa, sai suka yi karo garam! Ya yi hanzarin ja da baya tare da ware ido.
“Zanirah kin makance ne?”
Da gudu ta nufe shi ya yi hanzarin kaucewa a hankali ya ce, “Zanirah kin girma, shekaru goma sha biyar, kada ki sake ki kara yi min irin wannan oyoyon kin ji ko?”
Ko ni kaina ba don na nutsu ba da ba zan ji shi ba, domin cikin kwantaccen sauti ya fada.
‘“Wannan sai su Hanifa sune yara (diyar Baba Sadi)’.
A raina na ce, “Ai ko Hanifa ba za ta yi haka ba, ita ma Zanirar ban san yau ina ta samo wannan bakuwar al’adar ba wadda sam bamu tashi da ita ba. Amma da na yi la’akari da dadewar da muka yi bamu ga Yaya Aliyu ba, sai ban ga laifinta ba, at the same time, na yi mata uzuri da ajizanci wanda dan Adam baya rabo da shi.
Zanirah na dariya ta ce, “Yaya Aliyu ka rage min fa, da watanni biyar cur!” Ya ce, “Yar gari, ashe kina sane?”
Bai koma ta kanta ba ya shigo ya russuna har inda nake, kamshin daddadan turarenshi ya doki masunsunata.
“A roka damu Alasabbinaki”’.
Na zumbura baki na gyara zaman carbina cikin hannuna na kau da kai. Cikin dariya ya sassauta murya ya ce, “Na yi laifi ne Princess? I’m so sorry. Wallahi ban yi da niyya ba….”
Na kara turo baki na kau da kai. Yaya Aliyu ya yi dariya ya sa hannu cikin bakar leda ya bude, kamshin wani irin lafiyayyen balangu ya doki hancina.
Na hadiye wani tsinkakken miyau ji kake mukut! Dariya ta kashe Yaya Aliyu. Ya sa hannu ya zare carbin ya tura min kunshin balangun gabana. Ai ban bata lokaci ba tuni na ja kunshin leda cinyata na juya mai baya, na manta da fushin na soma dauka ina dannawa wani na bin wani.
Zanirah ta zo ta zauna za ta ci na doke hannun ta, ta ce, “Yaya Aliyu Fa’izah kadai ka sayo wa?” Muryarta abin tausayi.
Ya ce, “Eh, domin shine favourite dinta, kowa ma na sayo mai abin da ya fi so a rayuwarshi’. Ya sa hannu a aljihu ya fiddo alawar cakulet mai kwakwa (Bounty) ya mika mata. Zanirah ta yi tsalle ta cafke ta yi waje, na tattara ledar namana na mike
zan bita amma Yaya Aliyu ya rike gefen hijabina, gaba daya na juyo.
“Wai me na yi ne don Allah Fa’iza? Na taho gari ya gari tun daga Lagos domin ki amma kike zumbura min baki?”
Na bude baki cikin mamaki na ce, “DOMIN NI?”
Ya yi saurin girgiza kai, ya ce, “A’a, DOMIN KU”.
Na ce, “To sakar min hijabin na gaya maka kada Hajjah ta shigo”’.
Ya yi saurin saki. Na koma na zauna na ce, “To don me tunda ka tafi makaranta ba sako ba waya Yaya Aliyu? Don me za ka koma makaranta Yaya Aliyu?”
Ya yi murmushi ya ce, “Fa’iza ke yanzu ba makaranta kike ba?”
Na ce, “To in anyi degree ba shi kenan karatun ya kare ba? Da dadewa na taba jin an ce ka yi digiri”.
Ya girgiza kai “Is just the beginning Fa’izah digiri na farko shine tushen duk wani ilimi. [limi ba shi da iyaka, ba shi da karshe sai dai ka yi iya wanda za ka iya ka bari. Ina so na yi ilimi mai yawa ba digiri