ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
maimakon ya nuna fushin sa na abin da tayi sai ya yi wani irin murmushi yace. “Haana, (smart girl, I like this Attitude)”. Da murnarta ta Karaso gurinsu yadda suka ganta cikin fara’a suma sai suka fara yin tasu fara’ar, tunanin su komai ya dai daita tsakanin su. Zahra ce ta fara tararta da cewa, “Hajiya ta ya kuka yi ne? Da alama dai komai ya saitu? Don naga alamar farin ciki a tare dake”. Murmushi ta yi ta ce, “Yes Zahra na, komai ya dai-dai ta domin yau na amayar masa da dukkan abin da yake raina. Nan ta kwashe duk yadda sukai ta fada musu. . Mamaki ne Karara ya bayyana a fuskar su, nan suka hauta da fada kowa da abinda ya zo bakin su.
Murmushi tayi, ta ce, “Kan ku ake ji, idan za ku zo mu tafi tam, idan ba za ku tafi ba ni kunga tafiya ta, tunda naga alama ranku ya Baci tunda na taba gwaninku”.
Tana fadin haka nan taga malam hamza ya shigo ya nufo inda suke (waving) dinsu tayi tana murmushi babu wand a ya kulata domin tayi matukar basu haushi tun daga nesa ta hangi motar adaidai inda take kamar tun ranar da abin ya faru inda take haka take har yanzu bin motar tayi da kallo kamar tace malam hamza ya tsaya sai kuma ta fasa don ta lura bai ga motar ba, har suka fita tana hangen motar. Cikin ranta take tunanin anya kuwa bata yi ‘ganganci da dukiyar su ba? Kuma bata yi izgili ga abin da ta yiwa Mal. M.J ba? Nan take -zuciyar ta take mata ai ko mene ya faru shi ne ya »jawo dagawar da jin kan da yake nuna mata, shi «ne yasa tayi masa haka. “Zata iya bawa Ya Abba haKuri akan kyautar ‘da nayi da motar sa, nasan ba zai fushi dani ba”. Da ire-iren wannan tunanin ta Karaso gida. , ‘Tana isa gida nan ta ga tarin jama’a sai shiga da Www.bankinhausanovels.com.ng fitowa ake, nan take murna ya kama ta, ‘ta Ce. “Mal. Hamza ba dai Abban mu ya dawo ba?” “Eh mana, ya dawo ne, ai nayi tunani kin sanima Ji tayi wani farin ciki ya shige ta, da sauri , ta ce. “ Bari na duba waya ta”. Tana dubawa ta ga (missed call) har uku, tana dubawa taga duk kiransa ne. Suna (parking) tayi-sauri ta shige gida da murna, nan ta iske shi yana shirin fitowa don tafiya masallaci.
Da gudu ta je ta rungume shi tana murmar ganin sa, haka shima nan yake mata maganar ‘cewa yana ta kiran wayarta bata daga ba, sai ya yi tunanin ko tana aji. Ta ce masa ta sa wayar a (silent) ne shi yasa bata gani ba. Haka dai suka rabu ya fito ya nufi masallacin Juma’a. ~
Yau (Monday) cikin shiri ta fito don
wucewa makarnata domin kada ta makara, don yau ne ranar da suke da (class) din Mal. M.J; yau sati guda kenan da -faruwar tsamar su, ko ma dama ga kashedin da Granny tayi mata tunda ta gaya mata yadda suka Karke da shi Ta fito kenan zata je ta shiga mota, sai ga Ammi nan ta iske ta, ta ce. “Ke ina mukullin motar yayanki? Don na duba ban ganshi ba, tun tuni nake son yi miki magana amma nake mantawa, kuma Abban ku yana son ya yi amfani da ita”Ji tayi gabanta ya fadi, ta rasa me zata ce? Nan ta shiga tunanin me zata ce? Ta shiga kamekame. —
“Ko kece ki ka dauka ne?” ‘ Zata bata amsa kenan sai ga Abbansu ya ZO, yaCe. . “A‘ah Mamana ya akai ba ki tafi ba tun ’ dazu? Ko so kike ki makara?” “Abba tafiyar zan yi yanzu”Nan take ta sulale abinta ba tare da ta bari an sake yi mata maganar ba.
Minti biyar da shigarta (class) sai ga Malam M.J ya shigo, kai tsaye sai taji wani irin faduwar gaba ya zo mata, nan kuma ta dinga jin Kirjinta na bugawa da sauri da sauri. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sanye yake cikin (suit) fari Kal riga da wando hade da farin (glass) a idanunsa, nan ta ga ya Kara yi mata kwarjini. Tabbas shigar ta karbe shi, domin ya yi matuKar kyau.
“Ashe guy din dan gayu ne? Don ya iya wanka”. Abin da ta fada cikin ranta kenan.
Tana ji wata cikin daliban tana cewa, “Kai dadina da Malamin nan ya iya wanka, Rahma dubi yadda kayan nan suka karbe shi kamar don shi aka yi shi. Gaskiya ni dai yana burge ni, ni dai ina son ganin namiji mai jan aji da gayu”. Tabe baki Haana tayi.
– Cikin jan aji da shan Kamshi. ya Karaso ciki, kamar yadda ya saba sallama yake musu sai ‘duk su amsa, daga nan ya fara abin da ya kawo shi.
. Yanayin takunsa, yadda yake yi da jan aji da kuma tsare gida hakan bai sa daliban sun tsane shi ba, sai wani sonshi ma da suke yi. ~
Dogo ne shi sosai amma yana da dan jiki kadan, (black beauty) ne domin yanayin sa yafi kama da mutanen Sudan. Manyan idanu ne da shi da tarin gashin gira, fuskar sa ko ina da saje . yake da Kasumba, gashin ya yi luf a fuskar sa. .Yanayin sa da wuya ka gane wane irin jinsi ne, Hausa Fulani ko dan Sudan, duk da irin Hausar sa kamar ba ta cikakkun Hausawa ba. .
Kyau da fatarsa take dashi shi ne zai nuna maka cewa shi kansa ba daga Karamin gida ya fito ba, don ita kanta Haana bata tsaya ta Kare – masa kallo ba sai yau, don yau a nutse take ba kamar wancan satin ba, don haka yau ne ta samu damar lura da duk irin yanayinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsit ajin yayi ‘ana sauraron sa, duk. hankalin matan ajin ya yi kansa don yau kyan da yayi musu yafi na ko yaushe, domin ‘suna matuKar son (lecture) dinsa duk da kuwa duk dan (law) yana matuKar kuka da (course) din da yake dauka, don matuKar wuya da yake da shi, wato (Commacial law). Ga duk dan (level three) yana matuKar jin wuyar (course) din, amma son da suke masa yasa kowa yake ganewa, don yana bi da su ta yadda kowa zai gane shi cikin sauKi.
Nan take nutsuwa ya fara zuwar ma Haana
‘ don ta ga yadda yake yi bai ma duba gurin da take ba bare ya yi tunanin ko tana gurin.
Rubuta (topic) din da za suyi ya yi, sannan ya fara gaida dalibai, suma suka amsa cikin jin dadi. Nan ya soma dube-dube har idanunsa ya
kai ga abinda yake nema, can ya hangeta, nan ya tsai da idanunsa kanta, ya ce. Raihanatu Mustapha Naseer”, Nan take taji gabanta ya fadi ras! Har sai da ta runtse idanunta, domin bata kawo hakan ba cikin ranta. a “Yes Sir”. Ta fada bayan ta mike. Nan da nan idanun dalibai ya yo kanta, suka yi mata ca! duk sai taji wani iri don bata san me zai ce da ita ba. Cikin jin kai ya ce, “Za ki iya diban kayan ki kizo ki fitar min daga (class), na baki . . (suspension) na sati -biyu, kada ki kuma shigo min (class) sai satin yacika” Ya nuna mata hanya da hannunsa, ya ce. . “Ga hanya nan, za ki iya zuwa ki wuce, ban so na Kara ganinki har sai wa’adin da na dibar miki ya cika sannan za ki shigo”. – Mamaki ne ya bayyana a fuskar daukacin ‘ daliban da suke ciki, to wai me ke faruwa ne? me kuma Malam M.J yake nufi da Haana? Ranar_ . nan idan tayi surutu to yau kuma me tayi masa? _ Nan dai kowa ya shiga surutu irin tunanin – ‘ da yake cikin ransa.
Murmushin Karfin hali tayi, cikin anta tace, ashe ba shi bane idan bai mata baka ba bai nuna kansa ba.
Ta zo gabansa ta wuce bata ce masa komai ba, ya ci gaba da yin bayanin darasin da suke yi.
Tana fitowa sai gida, bata jira komai ba don ta san yau bata da komai, malamin da za su yi (lecture) dinsa tun (last week) ya ce musu ba zai shigo yau ba, don yana da wani Uzuri, don haka sai ta godewa Allah. Tana zuwa gida abin mamaki sai ta hangi motar Ya Abba an (parker) ta a gurin da take, mamaki ne ya yi matuKar kama ta, garin yaya aka yi motar nan ta dawo ba tare da ta sani ba? Da sauri ta daga waya ta kirawo Mal. Hamza, tace masa tana (parking space) ya zo ya same ta. Cikin mamaki ta tambaye shi, “Malam hamza mota na gani a nan, yaushe aka kawo ta _kuma wane ya kawo ta? Ko kasan wane ya kawo ta?” Eh, ni ne”Kai ne?” . Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta tambaye shi cike da mamaki, sannan tace Garin yaya akai har motar ta zo hannun ka?” “Tun ranar Juma‘’a da yamma na kawo ta”. Ka kawo ta kace min, garin yaya nake son ji kawai”. Ta fada cikin Kaguwa,
“Ranar muna dawo dake kina shiga sai ga wani bawan Allah ya zo ya same ni, wai aiko shi akayi‘ na daure na bashi (number) wai wani malamin ku ne ya turo shi yana son zai bani sako. Ban yi musu ba na bashi jin ya ambace ki. Minti talatin da dawowar mu sai naji waya na dauka, shi ne muka fara magana da shi, ya ce shi ne malamin ku don Allah na zo makaranta
yana son bani motar ki na kawo miki. Amma ya — roKe ni da kada na fada miki har sai na zo na dauki motar.
Da naje nan ne yake gaya min cewa shi ne biya wannan kudin dan Sahun ya yi ta binmu har sai ya ga gidan da muka je, sannan ya yi magana_dani ya karbi (number) ta. . Nan yake fada min ga yadda ku ka yi, nan ya roKe ni akan kada na fada miki yadda muka yi, ya ce kada na fada miki an dawo da motar har sai kin ganta da idanun ki. Sannan ya ce idan na
kawo na dawo masa da (key) din, zai baki da hannunsa”, Tsaki tayi ta ce, “Wato mutumin nan ta nan ya biyo? Yaji da shi, kuma zai ga wane zai je ya karbi (key) din? Dan rainin wayo”. Ta fada cikin zuciyar ta. Malam Hamza don Allah wannan ya zama na Karshe da zai Kara neman wani abu a gurinka dangane da ni, ko me zai sake cewa ka yi kace ya neme ni, don wallahi da na sani ba zan barka kaje ba”. “Shi kenan, insha Allah haka ba zata sake faruwa ba”.Lallai ma wannan mutumin, dama ashe. , ga dalilinsa na korata da ya yi? Tunda ya dawo min da mota ta to dole ya yi min rashin mutunci. Ni kuma zan bashi mamaki, indai ni ce zai dade idan yana tunanin zan je gurinsa don na karbi (key) din motar, sai dai ya shekara a gurinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sati biyu ya cika har aka shiga na uku, a tunaninsa zai ga Haana a (class) din amma shiru bai ganta ba, cikin hikima ya gama duba ko ina
bai ganta ba, don haka ya yi tunanin ko makara tayi bata shigo ba.
Haka dai ya hakura har ya gama (lecture) din nasa ya fita, a waje ya hangeta tana ta. nazarin littattafan ta cikin nutsuwa, gurin da zai wuce anan take zaune. Ta gabanta ya wuce, bai ce da ita komai ba. Jin Kamshkin turaren da ya doki hancinta shi ne ya fisgi hankalinta don ta gani, domin turaren duk da na maza ne tana matuKar son
Kamshin sa, don irin turaren Abbanta ne, daga baya ya bar ma Ya Abba ya zamana shi ne ke – am fani da shi. Nan take Kamshin turaren ya tuna mata da Ya Abbanta, nan tayi sauri ta dago kanta don ganin wane ya sako turaren? To ko ma dai wane ya hadu ya kuma san gayu.
_ Tana daga idanunta ta hangi ashe Mal. M.J ne, turo baki tayi gaba tare da dan Karamin tsaki don ta san shi ne ko kadan ba zata katse karatunta ba. Shi din ma bai juyo ba, haka ya wuce abinsa.
. Zaune yake cikin (office) dinsa, haka kawai ya dinga jin wani farin ciki yana shigar sa, tabbas tarkon da ya danawa Haana yana daf da kama ta.
“Abu na farko da nake son dasa mata shi ne Kiyayyata gare ta, daya bayan daya zan gama aika dukkan wannan saKon, daga baya sai na ganar da ita dalili na.
Dole na godewa Allah da nayi nasara akanki, yadda na zo na shigo rayuwar ki ta Karfi da yaji, duk da kuwa wahalar da na sha kafin na samu wannan damar da na samu kuma insha Allah Kuduri na da burina sai sun cika akanki. Www.bankinhausanovels.com.ng
A yanzu bani da wani buri da ya wuce na shiga rayuwar ki, kuma na shiga, domin na shigo: ta hanyar da ba zaki taba mantawa dani ba cikin
. tarihin rayuwar ki. Don haka zan ci gaba da shiga rayuwar ki ta hanyar takura miki da yi miki shishshigi har ta kaini ga cimma burina da ya — kawo ni cikin rayuwar ki. Tunda har Allah Yasa na samu wannan damar, to insha Allah sai nayi nasara, zan cika burin duk wani magoya baya na” “Raihana, na hango wata tsana da Kiyayya mai zafi cikin idanunki, wanda zan yi KoKarin — kawar da su, domin ba su ne burina a gare ki ba, dole ne yasa na fito ta wannan hanyar, domin bani da wata hanya da zan bi don cikar burina sai . tahanyar ki. Don haka zan yi KoKari na kawar da tsanar da na fara fuskanta a gurinki don kada tayi yawa”.“Raihana, na shigo cikin rayuwar ki ne ba don mugunta ba sai don alheri, na tsaya nayi Www.bankinhausanovels.com.ng binciken wane hanya zan bi don ganin na cika burina, ban samu ba sai da na gano ke ce kadai _hanyar da zan bi ta kaini ga ‘samun abin da ya kawo ni Kasar nan, don haka ina neman hadin kanki”,
Duk wadannan kalaman na Malam M.J duk cikin zuciyar sa yake yinsu tamkar a gaban
Haana din yake. – Sallamar da aka yi cikin (office) dinsa ce ta dawo da shi daga dogon tutanin da ya tafi firgigit! ya yi ya dawo duniyar da ya bari, ya taf
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG