ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
Miqa tayi hade da salati lokaci guda, nan da nan takai idanunta kan agogon dake manne jikin garun dakinta. Da sauri ta mike don tabbatarwa da tayi ta makara da abinda suka shirya yi ita da Amminta. Dirowa tayi daga kan gadon tayi sauri ta shiga (toilet), (brush) tayi sannan ta wanke fuskarta.
Dawowa tayi ta shiga duba hotunan da ta mayar dasu abokan kwananta wanda kullum suna Kasan filo dinta, idan ta zo bacci ta kalla tayi kuka tayi musu addu’a, haka idan ta tashi ma da safe tayi musu addu’‘a tayi tana kukatace..
_”Ya Hameed da Yaya Aziza_ anayi (missing) dinku sosai, Ubangiji Ya yi muku rahama, Yasa aljannar Firdausi ce makomar ku”.
Wannan addu’ar haka take kullum a gurinta babu fashi, nan take hankalinta ya tashi domin bata ga hoton ba. .
Da sauri ta fito kai tsaye kicin ta nufa don ta san Amminta na cantana zuwa ta iske bata nan sai kuku ta gani suna ta aikin su.
Kai tsaye dakin Amminta ta shiga nan ma bata nan, sai ta yanke tunanin kawai ta nufi dakin Abbu dinsu,
Zaune ta gansu duk sun yi jigum kamar . wadanda suka samu labarin wata mutuwa mai zafi, yadda ta gansu nan take sai taji damuwa tazo mata, domin bata saba ganin mahaifanta cikin wannan yaneyi ba.
Da sauri ta nufi gurin mahaifinta, ta ce, .”Abbu lafiya duk na ganku haka cikin damuwa? Me ya faru? ‘Ammi ku fada min naga kamar ba kwa jin dadi, ko wani ne bashi da lafiya cikin gidan nan?” . , Kai tsaye mahaifinta ya dauko hoton dake gefensa yace
“Mama na a ina ki ka samu wadannan hotunan?””
Ji tayi gabanta ya fadi dam! Nan take taji ta rude don bata san yadda zata yi ba, gashi kuma ita bata iya Karya ba, sannan ga yadda suka yi da Granny.
Kawai da ta rasa abinda zata ce da shi kawai sai hawaye ya fara fitowa daga idanunta, haba! nan take duk su biyun hankalin su ya tashi,
da sari yaje ya kamo hannunta ya zo ya zaunar da ita, nan ya shiga rarrashinta.,
“Abbu, Ammi me nayi muku da har ku ka Ki fada min tarihin rayuwar ‘yar uwata da kuma sauran Zuri’a ta? Da na sani ba zan taba Kin yi mata addu’a ba duk sallar da nayi, na jima ina tambayar ku abubuwa da dama kuna boye min sai da na dage sosai sannan wata rana nayi sa’a Granny ta gaya min, itama sai da nayé da gaske”,
Duk jikin su yayi sanyi, ya ce, “Mama na kiyi haKuri; damuwa da tashin hankalin ki ne bama so shi yasa ki ka ga bamu fada miki komai ba, domin lokacin kina Karama sosai, don haka yasa bamu fada miki ba tunda babu wani farin ciki a cikin labarin ko kadan” .
“Abbu naji komai na kuma ji abin’ da Zuri’a dinka suka yi; basu kyauta ba, sun yi rashin adalci’sun bi son duniya, sun yi watsi da zumuncin Allah, don haka na san Allah ba Zai taba barinsu ba har sai sun nemi gafarar ka. Amma duk da haka Abbu ina son kayi haKuyri kaje ka nemo mana inda Zuri’a dinmu suke mu dawo muna rayuwa guri daya
Nan da nan bacin ran da Haana bata taba gani ba a fuskar mahaifinta yau shi ta gani, take ta ji gabanta ya fadi, domin take ya daka mata tsawa, yace.
“Mama na! .Kada na sake jin wannan maganar ta sake fitowa daga bakin ki, wane Zuri’a Kike nufi? Bayan wannan Zuri’a din da kike cikin su har kina tunanin wata? To matukar kinason muna shiri dake to kada na kara jin wannan maganar ta fito daga bakinki idan ba haka ba zaki daina ganin farin cikina Jin firicinsa yasa ta mike da gudu ta fice cikin kuka, kai tsaye.sai dakin Granny. Zaune ta iske ta tana lazimi, ganinta cikin tashin fiankali nan da nan ta miqe ta shiga tambayar ta me ke faruwa? Take ta kwashe duk abinda ya furu ta fada mata.
Shiru tayi ta shige rarrashinta, ta ce, “Kada ki damu takwara ta, na gode da Allah Yasa har ki ka nuna musa burinki na son ganin Zuri’a dinki, ko dawowar nan da ya yi duk zaman da za muyi da shi sai nayi masa zancen sai yaita Waskewa”,”Umma ki yi haKuri, ina da delilai masu karfi shi ne yasa ki ka ga ina yin haka”.Muryar sa suka ji, nan take suka dago kai suka ganshi tsaye bakin Kofa, yanayin sa suka gani cikin damuwa. Granny dauke kai tayi daga dubansa, ta ce.
“Raihanatu ki kwantar da hankalin ki, Allah Yana tare damu, kuma da yardar Sa sai burinmu ya cika. Tsawon shekaru kullum addu’a nake Allah Ya nuna min Karshen wannan adawar, to bani da mataimaki, bani da wanda zai gane ina da damuwa da buri akan dangi na da suka janye jikin su daga gare mu, kullum da wannan damuwar nake amma har yanzu babu wani ci gaba”.Sauri ya yi ya zo gabanta ya zauna domin ko kadan bashi da burin ganin bacin ranta, don haka nan da nan ya ji ransa ya baci. ‘
“Umma ki yi hakuri ki yafe min, nasan mu aka yiwa laifi mu ya kamata a nema amma har yanzu babu wanda ya zo sau daya gare mu tsawon wadannan shekaru, mutumin da yake Kokarin dai-daita tsakanin mu yau baya duniyar,
Allah Ya dauki ransa, da yana nan nasan da zai yi wuya idan zamu kai wannan shekarun”.
“Kun ci amanar mahaifin ku, kun saki turbar alheri da ya dora ku, kuma na tabbata da zai dawo ya ganku haka sai ya yi matuKar fushi da ku”.
“Umma. bani da laifi Allah Ya sani shekarun baya na je neman su amma babu wanda na samu duk sun warwatsu, Alh. Jafar da gaba daya ma baya Nigeria shi da iyalansa, domin su kansu ance matsala suka samu a junansu, amma daga baya sun zo sun hade, amma duk da haka shi dai baya Kasar nan, sauran kuma kowaya shiga harkar gabansa.
Umma nayi alKawari insha Allah na debi lokaci cikin yardar allah zamu nemi ‘yan uwanmu ni da dan uwana Mukhtar, kuma da yardar Allah zamu gyara DANGANTAKAR MU”.
Murmushi ne ya bayyana a fuskar su ita da Haana, nan ya zauna ya shiga hira ana ta tuno yadda suka yi rayuwar baya kafin lokacin rashin jin dadin da matsalar ta zo ta faru, haka ammi ta. shigo suka hadu suna ta hirar su.
_Nan take Haana taji ta Kara’ Kaunar ganin ZURI’A dinsu, nan dai suka hadu suka bata hakuri da hujjar da suka bata na rashin fada mata abin da ya faru tun tana Karama.
Ranar daga ita har Granny wunin farin ciki suka yi, Haana ta kira Ya Abba ta fada masa_. duk abin da ya faru shima yaji dadi domin shi ma yana da wannan burin, don haka ya jima da sakawa a ransa da zarar ya gama karatunsa idan ya dawo sai yasan yadda ya yi shima ya nemi ‘yan uwansu.
Gidan Mama me ta fito ta shiga misalin Karfe goman safe, wato gidan mahaifiyar Ya Abba, domin haka take kiranta. Tsananin shakKuwar su da son junansu tun tana Karama hakan ya janyo tsananin sabo da shaKuwa da diyarta Rauda wadda ita ce Kanwar Ya Abba, komai tare suke yi tun suna yara har suka girma, aminan juna suke. Itama tana karatu a nan B.U.K, sai dai ita tana can (New Side) tana karantar fannin (Computer Engineering).
Tun da ta shigo gidan ta shiga Kwalawa Mama Me kira kamar wata Karamar yarinya, ko
da yake idan da sabo ta saba domin tun tana Karama haka take mata har ya zuwa yanzu.
Tare da Rauda suka fito don jin kiran na meye? Ganinta da suka yi cikin farin ciki duk suma sai suka fara farin ciki.
Rike hannun Mama Me tayi suka zauna, ta shiga yi mata bayanin yadda suka yi da su Abbu dinta, domin Haana bata iya Boye wa Mama Me . komai. Tun ranar da Granny ta sanar da ita abubuwan da suka faru baya ta shiga damuwa, yawan Zuwanta gidan yasa Mama Me ta gane matsalarta na ta tambayeta ta kwashe komai ta . fada mata.
Nan itama Mama Me tayi mata Karin wasu bayanan yadda ZURI’A dinsu suke a da,. komai tare suke yinsda mazan su da matan su, lokaci guda sabani da son zuciya ya shigo ciki.
Kasancewar dama itama tana da nata burin na son a dawo yadda ake a da, sai ranta ya yi fari da taji yayanta ya ce zai san abin yi. To amma
.duk da hakan tana da shakkar hakan, domin ta san a yadda ya yi fishi da su hakan yasa bai son kowa ya yi masa maganar su, dama ance mai haKuri bai iya fushi ba.Hira suka zauna sosai suna yi, tana basu labarin tarin rayuwar farin cikin da suka yi a baya, hakar ran su Haana da Rauda ya shiga yin fari don basu da wani buri da ya wuce na son ganin sauran ZURI’Ar su da ta bace.
Haana tace, “Mama Me insha Allahu nice zan yi hanyar dawowar ZURI’A dinmu da yardar Allah, sai kow ya yi farin ciki, sai mun dawo mun hade kamar yadda ake da can mutane su ci gaba da kiranmu ZURI’A DAYA ba biyu ba. domin kullum idan na tashi da wannan (mission) din nake tashi, sai na rasa ta ina zan fara? Amma sai na kasa.
“Mama_-na insha Allahu Allah zai taimaka miki ta hanyoyi da dama tunda ya ga niyyar da kike da ita”. .Sun jima suna hira daga baya ta bar su anan. .
Dakin Rauda suka koma suna hirar su, nan ne take Kara ci gaba da yi mata bayanin yadda suka Karke da Malam M.J, ita dai haka kawai take son wannan tsiyar da suke yi da Malam MJ din, don haka kawai ta matsu ta ganshi ta ga irin jin kan nasa da take bata labari.
Sati uku kenan da fara dai-daituwar Haana da Malaminta, domin yanzu babu laifi tana jin dadin (lecture) dinsa haka shima yana jin dadin Kwazon ta da take nunawa, sai dai tun da ya ga komai ya dai-daita sai ya sake sauyawa, ya shiga yawan tsare gida da shan Kamshi, babu sakin . fuska. Ita kuma sai ta dauka domin duk yadda ya biyo mata haka shima zata biyo masa.
Sam ba ya sakin fuska gare ta a duk lokacin da yake daukar su darasi zai zama yana yinsa cikin farin ciki da walwala, amma da ya ‘fito zai dinga yi musu muzurai da tsare gida. Haana ta kasa gane kansa, domin yadda ta mayar da sunansa a cikin zuciyarta shi ne mai baudadden ra’ayi.
Zaune take cikin (high court) domin zuwanta kenan taje yin wani (research) gunn wanda ta zo baya nan, domin haka Allah Ya yi Haana ta dau himma akan karatun ta, kullum haka take cikin (research) na (case-case) domin ta samu Kwarewa a kan fannin abin da take karantawa.
Zaune take a cikin wani (library) tana ta dube-duben wasu manyan littattafai, abin da take dubawa har yanzu bata samu ba, haushi ya kamata ta shiga sakin tsaki. Duk mutancn da suke gurin dai-dai ne basu dago idanu sun kalle ta ba. .
Daga idanunta da zata yi akan fuskar Malam M.J, bude baki tayi don mamakin ganinsa, nan take ta saki dan murmushi.
Kallon ta yayi don shi bai yi mata murmushin ba sai dai kuma bai tsare gida ba kamar yadda yake musu a (class).
Kasa bayyana yanayin da ya nuna mata tayi, taji kamar ta basar don kada ta je ya kwafsa mata, to amma gudun kada taki kula shi ta zo tayi laifi. .
Mikewa tayi ta je har zuwa gare shi tayi sallama, ya amsa, sannan ta ce. Sir barka darana”.
Sakar mata fuska yayi, ya ce, “Barkan ki dai .rehaa
Yana fadar haka sai ya niayar da idanunsa kan littafin da yake nazarta.
Jin yadda ya furta sunanta sai abin ya yi matuKar bata mamaki, nan take itama ta maimaita wai Rehaa.
Murmushi tayi tace “Kai mutumin nan dan duniya ne”.
Sauri tayi ta ce, “Sir, ashe kaima kana zuwa nan”
“Me zai hana tuda kema daliba kika zo bare ni Malami”. Ya fadi haka ba tare daya dago kai ya dube ta ba.
Zata sake magana ya daga mata hannu, yace “A’ah, ban son yawan magana, kin manta a ina kike ne? Kije ki yi abin da ya kawo ki ba surutu za ki tsaya kina yi min akai ba, don sai mu shiga hakKin jama’‘a”. .
Take taji ya soma bata mata rai, don ta san halinsa abu kadan zaka yi yanzu ya kwafsa maka, ashe ba shi bane. Juyawa tayi abinta ba tare da tayi masa wata magana ba, amma dai ranta ya sosu.
Tana zaunawa kenan sai ga wayarta nan ta fara (ringing) tana dubawa ta ga (number) din
wanda ta zo nema, miKewa tayi ta fice don kadata daga wayar ta dame su.
Gaisuwa suka fara nan ta gaya masa inda take, ya ce ta jira shi anan gashi nan zai zo.
Cikin farin ciki ta dawo ta zauna suna zama kawai tana daga idanunta sai ta ga sun hada idanu da Malam M.J, lokaci guda kowannen su ya yi saurin dauke idanunsa daga kan juna. . Murmushi tayi cikin ranta ta ce, “Mugu, Allah Ya fika, gashi nan wanda na zo nema yazo, kada kayi tunanin zan zo na tambaye ka wani abu tunda kasan neman wani abu na zo. Kaje kayi ta tsare gidan ka wanda babu inda zai kai ka”. Ta saki tsaki cikin ranta.
Tana ganin Malam Yusuf ta saki ranta hade da murmushi, zata mike ya daga mata hannu akan ta zauna bari ya Karaso. Ta ji dadin hakan. . .
Guri ya samu ya zauna, nan ta fara gaida shi cikin ladabi da murya Kasa-Kasa, ya amsa cikin fara’a.
Sun fara magana kenan sai ta ga ya mike, yace,
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG