ZURI’A DAYA BOOK 2 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
daga idanunta sai ta ga sun hada idanu da Malam M.J, lokaci guda kowannen su ya yi saurin dauke idanunsa daga kan juna. . Murmushi tayi cikin ranta ta ce, “Mugu, Allah Ya fika, gashi nan wanda na zo nema yazo, kada kayi tunanin zan zo na tambaye ka wani abu tunda kasan neman wani abu na zo. Kaje kayi ta tsare gidan ka wanda babu inda zai kai ka”. Ta saki tsaki cikin ranta.
Tana ganin Malam Yusuf ta saki ranta hade da murmushi, zata mike ya daga mata hannu akan ta zauna bari ya Karaso. Ta ji dadin hakan. . .
Guri ya samu ya zauna, nan ta fara gaida shi cikin ladabi da murya Kasa-Kasa, ya amsa cikin fara’a.
Sun fara magana kenan sai ta ga ya mike, yace
“Ina zuwa, bani minti daya”.
Kafin ta bashi amsa har ya mike, gurin Malam M.J ta ga ya nufa, ga mamakinta sai ta ga sun daga hannu sun kashe, take ta ga sun rungume juna cikin farin ciki. Ga mamakinta sai ta ga ya ja hannunsa za su fita, ya zo gurinta ya ce.
“Raihanatn dan yi haKuri ina zuwa mu gaisa da abokinA don kada mu dami jama’a bani minti biyar”.
Yana fadin haka sai ya ja hannunsa suka yi waje ta cika da mamaki, ta ce. . . “Toh fa, ashe sun san juna”. TaBe baki tayi ta ci gaba da duba ‘abin da. yake gabanta. Jim kadan sai gasu sun dawo gurinsa da yake zaune, nan ya wuce shi kuma ya tsaya gurinta. Raihanatu ki yi haKuri na. bata miki lokaci ko? Wallahi abokina ne da muka jima bamu hadu ba, tare muka yi karatu, hasali ma shi – sam ba a nan suke da zama ba, a can London suke da iyayensa inda muka yi karatu, amma duk Www.bankinhausanovels.com.ng
‘yan nan kasar ne, shima wani dalili ne ya kawo
shi har ya tsaya yin (lecturing)” “Ayya! Allah Sarki, babu damuwa, to ashe
kuma kaima kasan Malam M.J kenan?”
Baki ya bude; ya ce, “A”ah, ai shi nake miki bayani abokin karatuna ne a can London, dama kin sanshi ko malamin ki ne?” Eh tare muke da shi a nan B.U.K. din Murmushi ya yi, ya ce, “Kayya! To ai ni bai nuna min ma yasanki ba. Hmmm! M.J ba zai taba sauyawa ba
“Muhammad ashe kasan Raihanatu?” Ya fada cikin daga murya, don shi yana dan gaba kadan da su. Girgiza kai ya yi, ya ce, “Eh, dalibata ce Yana fadin haka bai sake cewa komai ba. Hararar sa tayi a fakaice, yana shirin dubanta tayi sauri ta yi Kasa da idanunta don kada ya gane hararar sa take. “Uban ‘yan jin kaihaka zaka Kare da son nuna isa a ko ina”. Ta fadi haka cikin ranta. Nan ya ce ta dauki jakarta su koma inda yake zaune, bata yi musu ba don babu ‘yar haka tsakanin su. Suka zauna ya gabatar masa da Haana a gurinsa na cewa, kamar ‘yar ogansa ce don mahaifinta suna da alaKar mutunci a tsakanin su, nan take ya ce. To ka fanshe ni don haka na damKata hannun ka, tare za kuyi karatun nan da ita domin ina da aiki a (office). Shiru tayi taji abin da zai ce, kawaii sai taji ya ce. Babu matrsala, ka brni da ita ka tashi kaje kada ka makara da abin da zaka yi, idan na gama nawa sai muyi nata”.
Murmushi yayi, ya ce, “Godiya nake, – Raihanatu sai na fito”. Yana gama fadin haka sai ya mike ya tafi. Tunda ya tafi ya barsu bai sake .cewa Kala da ita ba, sai kawai taji zaman ya fara gundurarta, kamar karatu take amma duk cikin abin da take yi babu inda yake zuwa, domin ba a nutse take ba. Minti ashirin ya diba sannan ya ce, “To Bismillah”. – Tsabar haushin da taji sai tayi shiru kamar bata ji ba, don ya yi matuKar bata mata lokaci ba
abin tayi magana ba ya dizga ta, don ‘asan halinsa son jan aji kamar wata mace.
Jin bata amsa ba tana jiran ya Kara yin magana, sannan ta bashi amsa, sai ya janyo wani littafi zai fara dubawa, sai tayi sauri ta ce.
“Sir naji kamar kana magana ko?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Oh kamar ne ma kenan…Ya dan tsegaitar da maganar, sannan ya yi . murmushi a taKaice, sannan yace. Na sani sarai kin ji ki ka share ni, na fa
san halin ki”. Zata yi magana ya daga mata hannu, ya ce. Mu yi abinda ya kawo mu, bana son — Karin bayani”. Hararar sa tayi ta gefen idanunta, ta ce. “To masifaffe, ni yau na gamu da gamona, * wallahi da na sani ban yarda Malam Yusuf ya hada ni da shi ba. Shi haka yake sam bashi da dadin mu’amala, lokaci guda zaka kasa gane kan sa”. Ba su tsaya Gata lokaci ba suka fara abin ‘ da ya kawo su, nan da nan ya ware kamar ba shi
ba. Bayani yake mata sosai tare da tambayoyi tana bashi amsa.
Idan ya Kureta ta kasa bashi amsa sai ya yi ta mata dariya, idan yana dariya sai abin ya mata mamaki ta ga kamar ba shi ba.
‘A ranar dai tayi matukar mamaki da al’amarinsa, duk ya bi ya daure mata kai. Sosai . .suka bata lokaci gurin karatun, da suka gama ya dan fara janta da hira taji ta dan fara sakewa da
Nan ya barta ya tashi ya tafi taji kamar kada ya tafi don zaman sun nan da suka yi har ta dan fara karantar halinsa, shi dai idan kan karatu ne yanzu zaku zamo abokai, domin ta fuskanta yana matukar son ganin mutum yana daukar karatun sa da muhimmanci. .
*******
Zaune yake cikin dakinsa da ya zama mallakar sa, wayar sa ya dauko yana bugawa, bugu biyu aka daga. Murmushi ne ya bayyana a fuskar shi jin muryar da yake muradin ji, ya ce. .
“Assalamu alaikum, Mom kina lafiya? Ya Kwarin jikin naki?” Daga can ta amsa, “Mun gode Allah, Muhammad ya aiki da abokan hulda?” “Momi kowa lafiya, da fatan dai kina kula da dukkan magungunan-ki, (please) mom ki. sha akan lokaci, -wallahi kullum dake nake kwana na tashi kamar na dawo nafasa abin da ya kawo ni”.”Muhammad tunda har ka kai wadannan kwanaki ko nace watanni matuKar ka dawo baka yi nasarar abin da ya kai ka ba ai duk shirin mu – ya warware, ya Kanwar taka? Kun dai-daita?”dan’ Murmushi ya yi, ya ce, “Mom yarinyar_ . nan har yanzu mun kasa fahimtar juna bare har ‘na samu damar bayyana mata wane ni gare ta, Mom babu ta inda zan samu nayi nasara sai ta ° hanyar ta, har yanzu kuma ban samu ba, amma – na dai fara KoKarin hakan”. “Muhammad tsaya, ba dai wannan ra‘ayin naka kake tafiya da shi ba? To muddin shi ne da wuya ka yi nasara. To kai me ya kai ka ma . ’ daukar zafi? Ka duba fa ka ga watannin da ka – diba amma ace har yanzu shiru? Www.bankinhausanovels.com.ng
. Muhammad ka tuna fa wannan ita damar da muke da ita da zata sa mu kai ga cika burinmu na hada kan ZURI’A guri daya, ka tuna ka bar komai naka ka dawo Nigeria don hada ZURI’A dinka, hanyar da na ce ka bi ba ita kabi ba, da ka bita da tuni ka-kai ga cika burinmu. Ya batun zuwa Ranon, ka je ko baka je ba?” Mom ki yi hakKuri har yanzu ban je ba, kar ki damu ki barni nayi amfani da basira da danki Barrister Muhammad Jafar yake da ita, da yardar Allah zai yi nasara ta wannan hanyar da na biyo insha Allah sai kinyi alfahari dani”.
Ina maka fatan alheri, ka dai yi ka dawo don kada mahaifin ka ya gano mu muzo mu samu matsala”. “Mom ki cire wannan tunanin a ranki, insha Allahu Daddy ya daina yin nasara akan duk wani murdadden ra‘ayinsa da burinsa tun da har ya yi yadda ya rabamu da ZURI’A dinmu, mu kuma insha Allah sai mun dawo mun dinke kowa ya gane cewa ZURI’A DAYA ta dawo inda take kamar yadda muke mafarki.
Ko me ya faru Daddy ne sila, ya hana dukkan Zuri’a yin auren zumunci, an yarda an bi
ra’ayinsa, ya ware wasu cikin Zuri’a kada a rayu da su duk an bi don ana tsoron sa da tunanin yafi kowa a cikin su. Har yanzu a haka ake, har ta kai ta kawo ya Kara-batawa da wasu cikin wanda yake so, don haka insha Allah sai mun rusa masa tsarinsa, mun dawo da ZURI’A dinmu guri guda, kowa ya yi zumunci da kowa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mahaifin ka zafinsa ne ya yi yawa shi yasa hakan ya faru, da yana daukar komai da sauki da tuni komai ya wuce a duniyar nan. Har yanzu bashi da makiyi sama da kawun ka Mustapha, don har yau gani yake shi ne ya kashe masa dan’uwanka Hameed tsabar rashin tsoron Allah. Wannan Kiyayyar ita nake so mu kawar, idan mun yi haka mun gama da komai, har yanzu bashi da wanda zai gaya masa gaskiya ne shi ne matsalar”,Mom ki bar komai a hannu na duk na gama komai abu daya nake jira kuma insha Allah zan kai ga cika burinmu ke dai ki yi min addu’a tunda yanzu nayi nasara na shigo cikin rayuwar Kanwata, ina nan ina Kara neman sanin abubuwa masu yawa akanta”
“Muhammad tunda ka dage sai ta wannan hanyar zaka bi to shawara ta daya, ka sauya ra’ayin da kake da shi na ka zamo mai sanyi da saukar da kai, amma matuKar da wannan_ halin naka zaka zo mata ba za ku shirya ba, dole ka janyo ta-jikinka sannan ka samu abinda kake so duk da ban san kuma ya kake so ba”.
“Mom haka ya yi, to ki gaida min da
kowa. Ina Haaya na? Ya karatun nata?”
‘ “Haaya lafiya, sai dai na fuskanta kwana biyun nan tana cikin damuwa, amma dai har yanzu bamu zauna ba na tambayce ta matsalarta, kasan ta da wannan kafiyar”.
, “(Please) mom ki kular min da Haaya na, ban so kuna barinta cikin damuwa don ina son – ‘ ganinta cikin farin ciki, amma duk da haka zan _ nemeta na ji me ke sa ta damuwa? Idan ni ne zan bata hakuri”.
Hira sosai suka yi, daga nan suka yi sallama tare da jaddawa mahaifiyar sa kan tana shan maganinta akan lokaci. Nan ya zauna yana tunani, tabbas ya dage .
yai sanyi, don Haana sosai, domin ita . ce matattakalar da zai bi don ta kai shi ga cika burinsa na son dai-daita Zuri’a dinsu da ta tarwatse
aka daina zumunci da juna aka daina auren zumunci. Domin tun bayan abinda ya faru dokar da aka gindaya cikin Zuri’a din kenan don suna ganin soyayyar da Hameed ya nunawa Azeeza shi ne duk ya janyo faruwar haka, gudu kada hakan ya sake faruwa yasa aka gindaya wannan dokar.
A bayyane ya ce, “Muhammad aiki ne babba gare ka tunda har ka baro aikinka da (rank) dinka ka fito neman sulhu da Zuri’a dinka, to dole ne sai ka yi da gasKe don Hausawa sun ce ba’a boris. da sanyin jiki”.
Nan dai ya tsaya yana ta saKe-saKe da – zuciyar sa don nemo mafita.
Ranar Lahadi da yamma cikin shiri Haana da Rauda suka fito don zuwa (shopping) din su,
kwalliya suka yi sosai su biyu suka fito, Haana ce _ ke jan motar suna tafe suna hira abinsu.
Kai tsaye (Country mall) suka nufa, sun shiga sun dibi duk iya abin da suke so an turo musu a dan keken kaya, har za suyo Kasa sai _ Haana ta ce.
“Rauda, mu dan duba (shop) din can na daukar ma Imran turare, don yace na taho masa da shi”.
Sun shiga suna dubawa don bai fada mata wanda yake so ba, don haka dai ya ce ta zaba masa mai dadi. Hira suke suna dariya. Www.bankinhausanovels.com.ng
““Rauda zabar masa kawai don ni ban san wanne zan daukar masa ba”.
. Murmushi tayi ta ce, “Hmmm! Haana yau da kanki kuma?” .
“Idan ke ba zaki iya ba to ni barni na zabar masa tunda nasan masu dadi da Kamshi”.
Kai tsaye suka ji murya ta doki kunnen su, da sauri suka juya don ganin wanene mai wannan muryar da ya tsomo bakinsa cikin maganar su?
Ga mamakin Haana sai ta ga Malam M_J tsaye gabansu yana murmushi, ya yi matuKar kyau domin shigar da ya yi ta ‘yan gayu ce sosai. Bata yi mamaki da irin shigar ba, don jiya an fada mata cewa a London suke da iyayensa a zaune, don haka don ya yi gayu ba sai an fada ba saboda Bature ne.
. Murmushi itama tayita ce, “Lah Mal MJ kai ne dama?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Girgiza kai ya yi yana murmushi.
Rauda ta bude baki ta ce, “Lallai yau Allah Ya nuna min Malam M.J da nake jin labarin sa kullum”.
Haana tayi sauri ta zungureta akan tayi shiru, ashe a lokacin da tayi mata ya gani. .
Yace “Bari tayi maganarta ka da ki hana ta, wato kullum sai ta baku labarina a gida inatakura mata ko don na hana ta mukullin motar ta”.
Dariya Rauda tayi ta ce, “A’ah Malam M.J ba haka bane, ai tuni tayi laushi ta kuma bi, babu yadda za ayi dalibi ya ja da malamin sa”.
: Yadda ta ga ya sake yana magana da Rauda sai taji dadi kamar sun taba ganin juna ko don ba _ dalibarsa bace yasa ya sakar mata fuska? .
“Raihanatu kin yi shiru ba ki ce komai ba, ko na kashe miki bakine”.
Murmushi tayi ta ce, “A’ah ba haka bane Sir, . “To meye?” Ya fada yana mai kallon ta cikin murmushi. _
Mamaki ne ya Kara kama ta, wai shi wannan mutumin wane iri ne shi? Har yanzu ta kasa gane halinsa. . Babu komai”. Ta fada tana mai tsare shi da ido. .
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG