ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 1 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Bata bari ta bata amsaba ta ce, “(Please) Granny tashi muje ki gani kada ki ce ba zaki ba’Haka ta kamo hannunta suka fito falon suka iske babu kowa, Haana taji dadi don bata son wasu su gansu suce me yake faruwa.
Suna fitowa suka hango shi, Haana ta yiwa Allah godiya don haka tayi saurin nunawa Granny shi. Ita din ma ta cika da mamaki. Granny ba tsaywa zamu yi ba, muje gurinsa muga ko wane”.
Tafiya suke Haana ce kadai ke magane amma ita Granny bata ce komai ba, Allah-Allah take ta je ta ga ko waye? Kuma ya akai har ya samu damar reyuwa cikin gidan ba tare da sun san wanene ba?
Suna zuwa gurin Granny ce ta fara yi masa sallama, juyowa yayi don amsa sallamar. Kash! Sai, ku daka ce ni a nan zan dakata sai mun hadu.a kashi na uku don jin yadda zata kasance,
Cikin murmushi ya juyo ya amsa da cewa, “Wa’alaikumussalamu wabarakatuhu”. Idanuwansa kyar a kansu. Nan ya Kara fadada murmushin fuskarsa, wanda hakan ya nuna cewa murmushin halinsa ne Nan suka shiga kallon junansu. Tunaninsa da hankalinsa gaba daya sun fi karkata ga Haana. Nan da nan kuma sai ya kawar da kallonsa zuwa ga Granny, sannan ya ce. “Hajiya barka da war haka”’.
Idanuwanta sosai a kansa. Tabbas wannan fuskar ba za ta taba mantawa da ita ba ko daga ina ta fito kuwa. Da sauri ta amsa da cewar. “Barka ka dai dan samari. Sai dai kuma ba mu waye ka ba, waye kai, daga ina ka ke, ya aka yi ka samu damar shigowa gidannan, tun yaushe kuma ka ke zaune a ciki?
Samun labarin akwai wanda ya ke rayuwa
Www.bankinhausanovels.com.ng
cikin gidannan, shi ne dalilin zuwan mu nan, don mu tabbatar da waye a ciki, saboda ba mu da labarin an baiwa wani damar shiga gidan”.duk da ta gane mai wannan fuskar, amma ta yi masa wadannan jerin tambayoyin ne don ta gasgata ‘abin da take zargi a kai, idan kuma hakane za ta yi matuKar farin ciki da wannan ranar.
Murmushin dai nasa ya sake yi, sannan ya nade hannayensa biyu a Kirjinsa bayan ya mike tsaye Dogo ne shi, don ya na da tsayi sosai, ya na da jiki amma ba mai yawa sosai ba, wanda ya yi matuKar
yi masa kyau tare da karbar halittar tasa. Fari ne sosai wanda idan wani ya ganshi zai yi.zaton ruwa biyu ne. A yadda Haana taga farinsa har ya fi na Ya Abbanta wanda take ganin kamar ya yi yawa. Farin nasa ba irin bau din nan ba ne, daga gani har da haduwa ma da kuma jin dadi.
Hada idanu suka yi da Haana tana Kare masa kallo. Da sauri ta dan saki murmushin yake ganin sun hada idanu tana satar kallonsa . Nan ya cire kai ya maida dubansa ga Granny ya ce.
“Hajiya yanzu zan baki amsar wadannan tarin ° tambayoyin naki. Amma da farko zan so ku zauna a nan”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya nuna musu guri suka zauna kan tarin fararen kujerun robar da yake zaune kan daya.
“Hajiya ina jin dadin ya nayin yau, shi yasa ma ku ka sameni a wajen_nan, ba don haka ba ban ma fiya fitowa ba”. Sai ya tsagaita da maganar
Haana ta cigaba da satar kallonsa. Kyakkyawa ne shi, fuskarsa ko kadan babu tarin Kasumba., Sai dai ya na dauke da gashin baki baki sidik kamar gashin sumar kansa wanda ya kwanta sosai. Hakan ya Kara fito da kyawunsa. Sai dai kuma ta kasa gane da wa mutumin nan yake mata kama. Ganin zai sake kamata tana satar kallonsa sai ta yi sauri ta dauke idanunta daga kansa. Nan ya dora maganarsa.
“Zan iya cewa ina zaune ne a gidan nan ba da
izinin kowa ba sai da izinin mai gidan wato Alh
Mustapha Nasir Dan fillo, shi ne ya bani izinin zama a ciki tare da tarin sharadai gareni
Sannan kuma na zo ne daga garin Lagos inda nake aiki, amma iyayena suna zaune a garin Kaduna. Na zo kuma nan ne da Kudurina.
Sai tambayarki ta farko da na mayar da ita Karshe. Ni sunana Sameer Aminu Naseer. Da fatan yanzu Hajiya Granny ta waye ni?”. Ya Karasa da fadin hakan cikin murmushi.
Da sauri Granny ta ce “Samecr mai gidana dan wajen Zainab din Aminu?”.
Cikin murmushi ya mike da sauri ya dawo gabanta. Ai kuwa cikin murna Granny ta daga hannuwanta sama tana godiya ga Allah da ya nuna mata wannan rana.
Tana Addu’a hawaye na zuba a fuskarta. Da sauri Sameer ya Karaso ta rungume shi. Tana kuka tana fadin “Allah nagode maka da na fara ganin ZURY’A ta tun kafin Kasa ta rufe min idanu.
Sameer kai ne ka zama haka?, tun da na yi tozali da kai na gano fuskarka, amma don na Kara tabbatarwa da zargina sai na bari na fara jin komai daga gareka”.
Nan kuka kuma ya ci Karfinta don dadi. Da sauri ya saka hannayensa ya fara share mata hawayen, sannan ya dora da cewa
“A’a Granny, ki bar kuka, ai murna ya kamata ki yi da Allah ya nuna mana wannan ranar, Ina son . ki taimaka min Granny mu yaki wannan baKar
gabar da take cikin ZURI’A DAYA, wadda ta rabe ta zama gida daban-daban. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ina son ki taimaka min da gudummawa, don wannan shi ne dalilin zuwana, wato na shirya ZURI’A ta ta dawo kamar yadda take, mu dawo tsintsiya madaurinmu daya. Granny wannan shi ne burina, shi ne kuma dalilin da ya sa na zo garin nan”,
“Allah ya yi maka Albarka”. Sannan ta kai duba ga RaiHaanat ta ce. “RaiHaanatu wannan dan uwanki ne na jini, tunaninmu da burinmu duk iri daya ne, sai ku gaisa da shi”. Ta fada cike da munrna fal a fuskarta.
Murmushi ta yi, wanda ita ma idanunta cike suke fal da hawayen murna. Sannan ta ce. “Yaya Sameer barka da zuwa garemu, kullum addu’ar mu kenan, wato yadda za mu bi mu shirya komai, to amma dole sai da taimakon namiji da zai shige mana gaba,.sai kuma ga shi Allah ya kawo mana kai cikin rayuwar mu. Munji dadi sosai”.
“My Goodness Granny, Haana Baby ce ta girma haka?. Ya salam! Wallahi ganin fuskarta sai da na tuno Yaya Aziza, duk wanda ya san Yaya Aziza idan ya ga Haana a yanzu, zai rantse ita ce. Duk da muna yara amma har yanzu ina kallon fuskarta, bayan nan kuma ga hotunan mu nan muna childhood, ban manta da kamarta ba.
Ubangiji ka yi musu rahama ita da Yaya Hameed, ka kyautata makwancinsu da su da gaba
dayan al’umar Annabi (s.a.w)”. “Amin”, suka fada a tare.
Sannan ya dawo da kalonsa ga Haana yace“Zan fi so ki kiranin da Mr Sameer”’. “Au, ba ka son Yaya din kenan?”“Ina da hujja”“To shikenan yadda ka so haka zan ce Mr Sameer”.
Dariya suka yi gaba dayansu. Tsakanin Granny da Haana an rasa wanene ya fi farin ciki, ganin wani daga cikin Zuri’ar su ya zo gare su. Bayan sun taKaita murnar ta su da farin cikin ganin Sameer, sai Granny ta dora. “Da fatan dai kowa ya na cikin Koshin lafiya ‘yan uwan naka kowa da kowa tun bayan rasuwar kawun naku?”’Kowa da kowa lafiya Kalau, sai dai an dan samu rasuwar yara da aka haifa, amma iyayenmu kowa ya na nan. Sai dai wasu bama zaune waje daya, don an Kara samun wasu daga cikinmu sun Kara watsewa, amma dai wadannan ma su sauki ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan rabuwar ta mu da ku, shi ne babban ° gibi a cikin Zuri’ar mu. MatuKar aka yaki shaidan aka samu aka shirya, to komai zai dawo dai-dai insha Allah”.
Haana ta ce “Yaya Sameer Allah zai taimaka mana ta hanyoyi da dama, tunda har ya hada zuciyoyinmu damin son yin sulhu. Ina mai tabbatar maka zai bamu nasara ya datar da mu. Ba ni da
wani buri a rayuwata da ya wuce na bude idanuna ‘ na naga Estate din nan a cike fal da ZURI’A DAYA kamar yadda ta ke tun farko cike fal, kullum burina kenan”.
Murmushi ya yi sannan ya ce. “Haana lokacin hakan ya yi insha Allah, tunda har Allah ya sa na samu nasara zuwa nan, to insha Allah komai zai zo Karshe. Granny an bata muku sosai da sosai, kuma wanda ya bada damar hakan shi ne Mahaifina Alh Aminu, don ya bi son zuciyarsa, ya kuma yi nadama sosai, domin da kansa ya zayya na min komai, ya kuma fada min tarin laifukan da ya yiwa Abba Mustapha, giyar kudi da kuma kaidin abin duniya sun sa ya manta zumuncin Allah; hakan yasa ya rudu da yin hakan. °
Yanzu kuma ga shi ya yi nadama, sai dai bai san yadda zai yi ya wanke kansa ba domin tarin laifukansa, haka ni kaina na yi matuKar bakin cikin abin da ya yi. Lokacin da‘ ina yaro duk ban san hakan ba da tasu ta hado su da Daddy (Alh Ja’afar), don sun jima ba sa shiri.
Duk abin da ya ba shi, sai da ya saka ya dawo masa da kayansa. Ganin yadda arziKinsa shima ya bunKasa, hakan sai ya sa suka bata kowa ya janye ‘yan uwansa jikinsa, sai zumuncin ya dawo kowa da wanda suke ciki daya suke yi.
Bakar gaba ta cigaba da dorewa a haka. Daga baya dai aka sassauta, ‘don mu yara-munki yarda abin ya shafi zumuncin mu, don iyayenmu mata babu wacce ta goyi bayan hakan. Www.bankinhausanovels.com.ng
* Ga dai mu nan da yawan gaske amma an kasa samun wani da zai yi maganin hakan, saboda kawai son ‘ya’ya da dukiya. Tunda dai kowa ya na jin cewa shi mai kudi ne, babu ruwansa da rayuwar gidan wani
Haka dai muke zumuncinmu babu ruwanmu da rayuwar iyayenmu. Daga Karshe dai aka yi maganin matsalar wasu daga ciki. Amma dai. Daddy shi da Zuri’arsa ya kwashe su tuni suna Kasar waje suna rayuwarsu, babu kuma ruwansa da kowa. Da farko sun so su samu matsala shi da ‘yan uwansa, wato su Uncle Lukman kan zaman Hajiya babba, ya ce da ita zai tafi, nan kuwa suka Ki, itama kuma ta ce a nan za ta zauna da sauran yaranta babu inda za ta je.
Haka ya yi fushi ya tafi, sai dai ya na dan zuwa, amma shi kadai ba tare da iyalansa ba. Duk cikinsu kowa ya yi nadamar abin da aka yi muku, amma kowa ya na jin nauyin yadda za su zo su fuskance ki a yi gyaran, duba da tsawon shekarun da aka diba ba’a waiwaye ku ba, hatta shi kansa Alh Ja’afar ya yi nadama, sai dai tsaurin rai da kuma jin kansa ne ya sa ba zai iya zuwa ya bada hakuri komai ya wuce ba.
A TUNANI NA, mutum daya ne zai ba mu matsala wajen dai-daito, duba da ya nayin zafin zuciyar da yake da ita wato Daddy, sai naga ashe shima Abba Mustapha haka yake da nashi zafin.
A tsohon tunani na Abba Mustapha shi ne ya fi kowa saukin kai, amma da nazo wajensa na fada
masa batun Zuri’arsa, sai ya hauni da fada har ma . ya yi KoKarin Hanani zaman cikin gidan nan”
Granny ta ce “Kun yi maganar kenan, ya kuma gane ka?” Girgiza kai ya yi sannan ya ce. .
“Bai gane ni ba, don banzo masa da sigar da zai gane ba, amma dai ya na cikin kokwanto. Don haka ne ma ya gindaya min sharuda
A take Granny da Haana suka yi masa tambayar “To da wace siga ka zo masa?”. Murmushi ya yi sannan ya amsa da Zan fada muku yanzu kuwa. Alh Ammar shi ne mutumin da na biyo ta hannunsa, Abokin
‘ Abbanmu ne, don tare suka yi karatu kuma har yau suna zumunci, shi kuma — kasuwanci = suke gudanarwa da shi.
Akwai wani zuwa da ya yi Kaduna yake min maganar a matsayina na mai hankali, wace guddumawa zan baiwa Zuri’ata don ganin na yi hanyar da zumuncin mu zai dawo?.
Tun daga wannan maganar na ji ya zama dole na yiwa Zuri’ata wani abu da zai janyo haduwar mu waje guda. Da dabara da kuma wayo suka yi nasara har Abba Mustapha ya amince ya bani wajen zama cikin gidan Nan Www.bankinhausanovels.com.ng
Don ce masa ya yi Ni din dan wata ‘yar uwarsa ne da muke zama a Canada, na zo ne wasan kwallon Doki wato Polo Club. Wata rana da muka zauna da Abba Mustapha muna hira, sai nace masa.
“Ina sha’awar zama cikin Estate din nan, ka siyar min ko kuma ka bani haya”. Shi ne.yake ce min
“Babu daya da zan iya yi maka a cikin wanda ka nema, sai dai aron da na baka yanzu, da zarar kuma ka gama abin da ya kawo ka ka tashi ka tafi don akwai masu shi”.
A take na tambaycshi -cewar. “Su waye ma su shi, ko za ka iya hadani da su idan za su siyar min?”’. Nan take ya bani amsa da cewar
“Ba ma za su siyar maka ba, don Zuri’a ta ne su, kuma sun bar nan ne babu ranar dawowa”
“Me ya sa ba za su dawo ba, tunda ba za su dawo ba me zai Hana ka siyar ko kuma ka bayar da hayar? Ga gidaje ma su kyau da tsarin gaske, bai kamata a barsu haka ba, ina ganin babu tsari’”’Tsarin kenan”’. Ya bani amsa a taKaice cikin gajiyawa da zancen.
“Alhaji ka yi haKuri, naga fuskar’ka ta canza daga ‘yi maka wannan zancen”. Sai kawai ya yi murmushi sannan yace Babu komai Malam Sameer”’.
Haka dai ban daddara ba na sake kawo masa maganar Zuri’a dinsu a wani zama da muka sake
yi. Na dameshi da son jin tarihin Zuri’arsu. nan ya samu ya fada min amma a takaice, sannan yace min ya yafe su gaba daya kuma baya son kowa ya yi masa maganarsu, sannan kuma ya roKecni da kada na sake yi masa maganarsu tunda na ji abin da nake son ji.
Ban daddara ba, daf da zaiyi wannan tafiyar na sake zuwar masa da wata maganar
“Don Allah ina son ka daure ka fada min a inda sauran Zuri’arka suke, don na samu ko shirya su ne na yi, ba don komai ba sai don KARAMCIN da ya nuna min na bani wajen zama a wajen da Zuri’arsa suka rayu”
Cikin bacin rai ya ce. “Bana buKatar hakan, idan ka kuma shiga hurumin da ba naka ba, lallai za ka bar min gidana, don na fuskanci kana son yi min shishshigi cikin Rayuwata, ka tsaya a iya matsayinka na bako a nan, don ban yardar maka Kulla wata dangantaka da gidana ba balle kuma har kasan iyalaina. °
Matukar idan ka fiya damuna zan kore ka daga cikin Estate din nan. Idan za ka tsaya a matsayinka ka yi rayuwarka a cikin gidan nan kai kadai to zan iya baka damar zama a gidan nan iya son ranka, amma ban yarda ka shiga cikin hurumin da ba naka ba.
Don idan har kana yi min maganar Zuri’ata to za ka tashi ka bar nan gidan babu ruwana. Wai kai shin ma waye kai da za ka ce sai ka shiga maganar Zuri’ata?”’,
Ya na gama fadar haka ya~ fice. Ba mu sake haduwa ba sai labarin baya Kasar kawai na ji a wajen Alh. Sai dai ya fada masa maganar cewa ya fara zargin wani abu a kaina. don haka Alh ya ja min kunne na yi a hankalin kar ya
gano mu ba mu yi nasara ba kuma komai ya warware.,. To kunji wannan shi ne dalilin zuwana nan, da kuma yadda na samu na zo gidan nan. Domin ba don mutunci da Kimar da Alh ya ke da ita ba, da ban samu nazo gidan nan ba.
Hakika iyayenmu sun yi matuKar fusata Abba Mustapha, ta yadda ma baya sha’awar duk wani abu da ya shefe su a matsayin su na ‘yan uwa jini daya. Gaskiya ba a yi masa adalci ba, kuma duk matakin da ya dauka banga laifinsa ba, don an bi son zuciya kuma an manta da zumuncin Allah.
Granny yanzu komai ya na hannunki, dole ne mu san abin yi kafin ya dawo. Don nasan matukKar ya gane Zuri’a daya muke, ba zai yarda na cigaba da zama ba yadda ya tsani Mahaifina, nasan kuma dole tsanarsa nima ta shafeni. Www.bankinhausanovels.com.ng
Don a cikin ma su yi masa laifi daga Daddy sai Abbana, saboda a cikin labarin da ya bani a taKaice yayi min bayanin irin juya masa baya da suka yi. Kuma na ga tarin tsana da Kiyayyarsu a cikin idanunsa. . °
Granny ki daure ki bani dama na gyra zumuncin mu, ina son mu dawo ZURI?A DAYA kamar yadda muke tun tasowar mu”
Cikin Kwalla Granny ta riko hannun Sameer – sannan ta ce, “Maigidana Allah ya na tare da mu, tunda ya san Kudirinmu na Alkhairi ne. ina son ka saki ranka ka dawo cikin mu, ka bar komai a hannuna. don mu ma nan burinmu kenan ni da
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG