ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 10 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
nan ban ganki ba? Kuma ba ki yi min magana ba
Murmushi ta yi cikin sanyin jiki ta ce. Ai
tunda ka zo kuna magana da Haana na ganka, ni
kuma bana son katse mutum idan ya na magana
saboda ba dadi.
Ban yarda da ke ba na fusanci wani sabon
sauyi dake ko dai ba kya jin dadi kwana biyu ne sai
boye kan ki ki ke yi ba kya shiga jama’a.”
“Kar ku da mu zan sauya na dawo muku yarda
nake da, idan hakan ya yi muku.
Da kuwa kin kyauta. Cewar Sameer.
Ran Abba ne ya fara baci kawai sai ya fara
bawa motarsa wuta ya ce, Sameer mu za mu wuce
sai mun dawo.
Allah ya kiyaye, Miss Haana mai zai taho
miki da shi tsara ba don na ga kamar kin fi kowa
dokin wannan tafiyar? Ya fadi hakan da biyu ne
ganin yadda Ya Abba yake yi abin cikin kaguwa,
Duk abin da Mr. Sameer yake so ya fada da
bakinsa mu ji.
Gaskiya ne ba wani abu nake so ba illa kawai
Miss Haana ta kular min da kan ta.
Harararsa ta yi ta murguda masa baki, shi kuma
ya shiga dariya. Kai tsaye Ya Abba ya taka motarsa
cikin karfi suka bar gurin
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ko kadan Mr. Sameer bai yi mamakin hakan
ba, domin dama ya yi hakan ne da biyu don ya ga
wane irin action Ya Abba dn zai yi kuma ya gani.
Tabbas yau ya tabbatar da zarginsa Abba yana
nuna kishinsa a kan Haana wato gaskiyar zarginsa
ya fito, tunda kuwa ya nuna masa haka zai fito
masa ta wata hanya da zai daure shi da jijiyar
jikinsa.
Murmushin mugunta ya yi ya ce, Abba mu je
Zuwa za mu yi playing wannan game din da kai
tunda na gano inda ka dosa da ni har a ga wanda
zai yi winning da kuma loser.Ya yi das! Da
yatsunsa ya juya ya nufi cikin gidansu.
Yana kawo kai cikin dakinsa ya ji wayarsa na
ringing da sauri ya zo Zai dauka ya ji ta katse, nan
T GOmbe ya ga 2mss Call. Yana kokarin neman layin
wayarsa ta kara shigowa, daga wayar ya yi sallama
Ya dan saurara don daukar mai muryar saboda
number ce babu suna.
Sallama Hajji Sameer kana tare ne da dan
uwanka Barristcr Muhammad Jafar.
Murmushi ya yi ya ce, “Allah ya taimaki
Barrister ai na dauki muryar long time ka boye na
nemi wayarka na rasa har na zo na hakura da
nemanka. Ya fadi hakan bayan ya amsa masa
sallamarsa da farko.
Allah Sarki na ajiye wayar ne kan wani
Important issues yasa na canZa layin aiki muke mai
matukar wuya har yanzu ba mu kai ga gama case
din ba.
Gaskiya ne to Allah ya yi jagora.Cewar Mr.
Sameer. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ameen da dan uwana dama na bugo ne na yi
maka godiya, domin namijin kokarin da ka yi na
daidaituwar zura din aikin ka ya yi kyau na yaba
da kwazon ka, ka yi min komai saboda na cika
burin Raihanatu na s0 na ina nan na ga irin farin
Cikin da zan gani a kan fuskarta, na san za ta yi
matukar farin ciki idan ta san cewa Malam M.J
dinta ne ya turo ka Cikin rayuwarta da har ka yi
yadda ka yi ka sada ta da zuri’a dinta.
Sameer na gode sOsai ka yi hakuri da rashin
jina da ka yi don haka ka jira ni yanzu zan cika
maka ragowar kudin Contract din dana ba ka na
yaba gwazon ka zan kara maka wani kaso mai
tsoka a kan na baya, dOmin wani aikin da za ka yi min yanzu.
Cikin mamaki Sameer ya ce, “Barrister kana So
ka ce min dama kaine Malam M.J din da nake jin
labarin ka a gurin ta?
Murmushi ya yi ya ce, “Am so sorry, Sameer
da ban fayyace maka komar ba na game da rayuwar
da na yi da Raihana. Raihana wani tsiro ne da
Allah ya dasa min shi Cikin zuCiyata na girma da
shi na taso da shi na shigo rayuwar Raihana ne don
na bi ta hanyarta na shiryar da zuria din mu.
Bayan dan zaman da muka yi da ita na gama sanin
dukkan burinta da mafarkin ta.
Sai dai mun gina dangantakarmu cikin tsama da
nuna kOwa yana jin haushin kOwa wanda hakan ya
kara makantar da ni cikin sonta da kaunarta, amma
ban bari ta gano ina son ta ba sai dai ni na gano
tana sona.
Ana cikin haka ne na samu labarin ciwon
Mommy ya tashi dole na hakura na zo na same
ka muka yi tsada na ba ka dukkan logic da wani
dukkan conncction da zai kaika ga samu damar
zuwa cikin estate din ga shi kuma mun yi nasara
komai ya zo mana cikin sauki duk yadda muke
zammani sai abin ya zo mana cikin sauki. To mun
gode Allah. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai contract na gaba shi ne ka kular min da
rayuwar Raihana ba na so ka bari wani ya nuna
yana s0nta, domin ina son zan aure ta ta dalilin
Aureb mu zai sa a dawo da auren zuri’a kamar
yadda aka daina a can baya don haka ina son ka
fada min nawa zan ba ka wannan contract din na
biyu da za ka yi min kar ka ji komkai kamar yadda
ka fadi wancan da bakin ka wannan ma haka nake
so ka fada min.”
Cikin tsawa Sameer ya ce, Ya ishe ka haka
Muhammad ka tsaya iya matsayin ka kada ka wuce
gona da iri mana ka kuma san me ka ke fada min
don na fuskanci har yanzu ba ka san me ka ke yi
ba.Na raina wayonka da wayewarka da ka ke
tunanin kana da shi, me ka dauki kanka? Me kuma
ka dauke ni ko kana tunanin bukatar da ka zo min
da ita da farko na karba ne kamar yadda ka zata
zuri’a dinka, zuria dina ne ban fi ka ba, ba ka fi ni
ba. Ko kana tunanin kai kadai ne mai burin Son
ganin kiyayya da gabar da ake cikin ZURI’A
DAYA ta zo karshe to ka sa a ranka yadda ka ke
tunanin haka dubun ka tuni suka yi tunanin haka.
Na gode Allah da yasa ban karbi ko sisi din ka
ba da ban san wane rin rainin hankali za ka yi min
ba. Muhammad babu abin da na nema na rasa a
rayuwata, kuma kai ma ka sani duk abin da ka ke
takama da shi nima ina da shi tarin dukiya gurin
mahaifii, ilimi. da addini da wayewa sanin ya
rayuwa take duk na sani babu wani bude idanu da
za ka nuna min na karfi.
Contract din kane don kawai na yi wasa da
talent din ka ne, kana ganin kamar ina kwadayin
dukiyar da mahaifinka yake takama da ita.
To ka yi kuskure ka rike duk abin ka na yi wa
kaina da kuma zuri’a ta aiki tunda har na daidaita
zuri’a ta. Duk tunanin ka da hangen ka ka yi
tunanin da basirarka na shigo estate din nan idan
kana tunanin haka ka daina da basirar ka na hada
nayi amfani da tawa don gudun abin da zai je ya
dawo. Abokin Abbana na nema ya shige min gaba
da karyar da na shirya ne ya fadawa Abba
Mustapha da hakan na yi na sara har na samu
matsugunni a estate din nan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Don haka ba na bukatar wata contract daga
gurin ka kagan tunda na hada kan zuri’a ta na kuma
gamu da muradin raina wato Miss Haana ba ni da
wani buri a duniya da ya wuce na ganta a dakina
matsayin matata uwarya yana, kuma abokiyar
rayuwata.
Karya ka ke Sameer ba ka isa ba ka yi falling
din haka na saka maka ido ba ban turo ka cikin
rayuwar Raihana ba don ka yi soyayya da ita ba na
turo ka ne don ka zama tsanin da za ta taka ta kai
ga ganin hada zuri’a dinta.
Look! Muhammad ba ni da lokacin jin
wannan shirmen batun da ka ke fada min, saboda
kai ba ka isa ka hana ni son Haana ba kai a su wa
zan kuma yi duk yadda zan yi sai na mallaki Haana
al any COst just wait and watch
Yana gama fadin haka ya kashe wayar gaba
daya don kada ma ya sake kiransa, bare har ya bata
masa rai.
Ran M.J idan ya kai dubu to cikinsa babu
wanda bai baci ba, shi Sameer zai yi wa haka ya ce
zai yi wasa da rayuwarsa. Wasa da rayuwarsa mana
saboda duk wanda yake son raba shi da Raihana
din sa to kamar yana son raba shi da rayuwarsa ne.
Zai yi duk yadda zai yi sai ya ga yadda bai bari
ya same ta ba ya san Raihana dinsa tana son shi,
babu abin da za ta yi da Sameer.
A bangaren Sameer kuwa wata bakuwar
damuwa ce da kunci suka ziyarci zuciyarsa. Jin
cewa Barrister shi ne Malam M.J din da Miss
Haana dinsa take ba shi labarinsa wanda saboda shi
ne taki bari ta ba shi damar yin soyayya da ita
wanda shi kuma ya hakikance ala dole sai ta so shi
duk da ta gano manufarsa haka take. Www.bankinhausanovels.com.ng
A bayyana ya ce, “M.J karya ka ke ba za ka
taba samun Miss Haana din ba har karshen
rayuwarka zan yi duk yadda zan yi sai na jefa mata
tsanakar ka da haushin ka a rayuwarta. Yadda ka yi
bankwana da ita to haka za ka dawo ka same ta a
cikin dakina kai da ita sai dai hange daga nesa ba
zan taba barin bayan gaisuwa wani abu ya shiga
tsakanin ku ba.
A TUNANINA da Abba ne zai kawo min
matsala ashe ban sani ba kana can a gefe guda da
niyar ka sai na gama shirya rayuwata da ita ka zo
ka rusa min ita to karya ka ke Muhammad ba ka isa
ka shig0 rayuwarmu da Haana ka rusa mana ita ba,
dole ka hakura da ita ka bar min. Ni Sameer Aminu
babu wanda ya isa ya raba mu sai dai ta Allah ta
kasance a kanmu so da kaunarta yanzu na fara.
Ranar shi ma haka ya wuni cikin kunci da
KUNAR ZUCI, domn a ranar komai ya tuna kona
masa rai yake haka ya wanzu a ranar yana neman
mafita yadda zai bullowa al’ amarin don ya kudura
a ransa sai ya cirewa Haana son M.J a ranta saboda
sai ya bi hanyar da zai yi ya dasa mata tsananin
kiyayyarsa a zuciyarta yadda idan ma wani ya zo
mata da labarinsa sai ta tsani mai fada bare ma shi
da za a ambata mata shi
Da wannan tunanin ya wanzu har sa da ya
samu mafita sannan ya nutsu haka ya dinga jin
kishin da yakeyi a kan Abba yana sauka yana
komawa kan M.J ya dinga jin sam baya son wani
ya sake hada su da zai iya canza shi a matsayin dan
uwansa da ya yi. Bayan ya gama tsara yadda zai
bullowa Haana take ya ji ransa ya yi masa dadi.
Bayan sallar Magariba ya shigo gidan su Haana
sanye yake cikin jallabiya mai gajeren hannu duk a
falo ya same su suna ta hira sai dai bai ga Haana a
Cikinsu ba, ya kuma rasa yadda zai yi ya tambaya
tana ina, domin Granny da Ammi duk suna gurin.
Kawai sai ya ce, Ammi ni fa yau girkin ki na
zo ci ba abin da nake so ba Umma ta girka, shi ne
na zo ko zan samu tuwan samo din nan naki mai
dadi da miyar agushi ba na jin zan iya Cin wani abu
idan ba shi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ammi ta yi murmushi ta ce, “Ka tara ka samu
Sameer ina da miyar a firji bari na dora maka
tuwon da kaina yanZun nan tunda ba wani bata
lokaci zai yi ba.”
Tana gama fadin haka sai ta fara shirin mikewa
da sauri ya ce, “A a, a’ a Ammi in dai babu kada ki
wahalar da kanki bari kawai na fita resturant na je
na yi Order din wani abu na ci.
A kan me duk fadin gidan nan ka rasa abin da
za ka ci sai ka fita gidan abinci ka zauna a nan na je
na hada maka mnti nawa ne na gama’?
Shi ke nan Ammi na yarda zan ci naki, amma
ina kawata take ta zo ta yi min ko na hutar da ke
tunda miyar takI Ce, ita kuma ta yi min tuwon.
Yana rufe bakinsa sai ganin su ya yi ita da Ya
Abba sun sauko daga sama daga sai ga Abba
Mustapha na biye da su yadda ya ga nishadi a
fuskarsu ita da su
Ammi ta ce, To ga ta nan ma.
Granny ta ce Yauwa masha Allah gwara da
hakan ta faru yanzu Mustapha zo ka zauna korafi
zan yi yanzun nan tun da duk ga ku nan.
Cikin murmushi ya ce, To Umma korafin me
kuma bari na zo na ji?
Abba da Sameer sai kallon-kallo suke kowa da
Irin yadda yake ji Cikin zuciyarsa, amma duk sai
suka dake kowa ya bar abin da yake ji cikin ransa.
Sameer da sauri ya mike daga zaman da yake
kan kujera ya gaida Abba ya amsa cikin nishadi
bayan ya kira shi da Dantawaye, sunan da yake
kiransa da shi jifa-jifa idan ya so nishadi tun bayan
shiryawar da aka yi shi kuma duk lokacin daya
kira shi da wannan suinan sai yana sosa keya.
Fakar ido ya yi ya yi waving din Haana hade da
murmushi a fuskarsa. Harararsa tayi ta murguda
masa baki tare da fari da ido duk cikin wasa.
Murmushi ya yi ya girgiza kansa duk sun yi abin
nan cikin yan dakiku kadan. Duk abin da suke
Abba na kula da su sai kawai ya rasa wa zai ji
haushi cikinsu.
Abba ya ce, “Gani Umma me ye korafin naki?
Eh mana, a kan yaranku nan mana Samari iya
samari amma kun saka musu idanu babu wanda za
ku yi wa magana ya fitar da matar aure sai dai
yawo zuwa gidan abinci suna cika cikinsu ko ba
komai dai ai mu ma muna Son ganin yaran Www.bankinhausanovels.com.ng
Jikokinmu a gabanmu don ga shi nan Sameer wai
tuwo ya zo nema gidan nan idan da yana da
matarsa ba yana zaune zai fada mata abin da yake
SO ta yi masa ba shi ne ya zo zai tashi yata muna
hirarmu mai dadi wai ta yi masa tuwo.
Gaba dayansu babu wanda bai yi dariya ba sai
Abba domin mutukar Sameer yana guri duk abin
da ake yi na dariya bai fiye yi ba, musamman idan
Haana tana gurin.
Sauya fuska ta yi mur ta ce, Au! Baku bawa
zance na muhimmanci ba kenan tunda
dariya. Allah ni fa da gaske nake bai kamata mu
saka yaran nan duk a gaban mu haka ba duk sun isa
aure mazansu da matan me muke jira da su ko ba a
SO mu ga
ya’yan jikoki sai kasa ta rufe
Idanunmu?
Abba ya dawo daf da ita ya ce, “Umma insha
Allahu sai kin goya, ko a jiya sai da muka yi
maganar auran Mustapha Karami ni da Alh. Aliyu
sai dai ba mu samu matsaya ba, tunda ba mu Ji ta
bakinsa ba koma dai me ye duk cikin karshen
shekarar nan za mu ba su dama kowa ya fito mana
da wacce yake so sai mu je mu sami yayensu a yi
maganar auran nasu,
Yauwa ko da na ji mana, kai. Ta nuna ya
Abba da kai Sameer kun dai ji ko sai ku maida
hankali ban da ruwan ido.
Murmushi Mr. Sameer ya yi ya ce, Hajiya
Granny ai ni ba ni da matsala tunda ina da ke, ke ce
uwar gida sai kuma amarya da zan sake sai ki yi
hakuri, ki ajiye kishi; domin duk rana daya za a
kawo min ku. Www.bankinhausanovels.com.ng
Aa ni kam ka yi min tsufa ina ni ina kai ai ni
din nan da ka gan ni sai yaro dan sha bakwai ba
tsoho ba wanda ya kusan hararar arba in.
Dariya aka saka yi wannan karon sai da Ya
Abba ya dan dara, nan suka sake Granny a gaba
saida Abba ya tsawatar musu. Haka ya ja Ya Abba
suka fice don rakiyar da zai yi masa har cikin ransa
bai so zai tafi ya bar Sameer da Haana tare ba da da
yadda zai ya fasa wannan rakiya da ya yi ta amma
babu dama yana ji Sameer na fada mata abin da ya
kawo shi gidan ba ta yi musu ba ta nufi kicin. Take
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG