ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 12 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Why!! Why!!! Haana me yasa za ki kirkiri matsala
ki dorawa kan ki bayan kuma ba ki da mafita a kan
ta bayan hakuri? Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana da na san dawowa ta Niger1a ba za ta
saki faran ciki ba ya mantar da ke dukkan wata
damuwarki wallahi da ban dawo ba, ko kadan bana
Son ganin damuwarkI bare tashin hankali, amma
rana daidai ne da ba zan dinga ganin damuwar nan
a fuskarki ba.Kin san na fara tsanar M.J domin duk
shi ne ya janyO wannan damuwar 1dan har ba za ki
dinga yi min magana ba zan yi fushi da ke zan
kuma daina nuna damuwa ta a kan dukkan wani
al,amarin ki.
Da sauri ta goge hawayen da ke zuba a fuskarta
ta ce.Ya Abba don Allah ka yi hakuri na yi maka
alkawarin daina shiga damuwa zan yi dukkan abin
da ka ke so, amma ina son ka taya ni da addu’a

abin da zai zamo mini alheri. Sannan ina son ka ba
ni labarin yadda kuke da Haaya ko zan ji dalilin da
yasa ba ka son ta.
Bai tsaya bata lokaci ba ya ba ta duk labarin
Yadda suka rayu da ita a can makaranta sai dai bai
gaya mata dalilinta ne yasa bai amince da ita ba, ya
boye mata abubuwa da dama. Daga karshe ya fada
mata akwai wadda yake son aura lokaci yake jira ta
ba shi ya tura iyayensa ga magabanta don ai
maganar aure.
Ta yi murna sOsai lokacin da taji yace yana da
wadda yake son zai aura lokaci kawai yake jira ya
tura iyayensu, babu irin nacin da ba ta yi ba a kan
ya fada mata a inda take, amma yaki sai cewa ya
yi ta yi hakuri karatu take ba ta nan da zarar ta
dawo ita ce mutum ta farko da za ta fara sanin


kowacece. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta shiga murna da tsalle ganin yadda take cikin
farin ciki shi ma sai ya ji shi tsundum a ciki take ta
ce, Allah Sarki Haaya na so da ita za a yi ban san
ta ba, amma na tausaya mata yadda ta kamu da son
ya Abbanmu ita ma Allah ya ba ta wanda za ta yi
farin ciki da shi, dama haka rayuwa take ba lallai
ne ka samu abin da ka ke so ba.
Murmushi ya yi ya ce, “Mu je falo gurinmsu
Granny, amma fa bana son ki fadawa kowa labarin
da na ba ki na Haaya ki ajiye shi a matsayin sirri ni
da ke.”
Murmushi ta yi ta ce, Kar ka damu Ya Abba
na babu mai ji anan muka yi mun kuma yi haka
mun binne.
Tare suka fito suka iske su Granny a falon,
ganin su tare cikin nishadi ta shiga yi musu addu’a
Allah yasa burinta ya cika a kan su kai da ganinsu
ka san akwai soyayya a tsakaninsu.
Yau kwana biyu kenan da sanin Sameer
cewa Rauda shi take so duk wata hanya da ya san
zai bi don su daina haduwa ya nemeta ya rasa dole
yau kwana biyu ya dauke kafa da zuwa gurin
Haana sai dai da kanta ta nemi jin ba asin rashin
Zuwansa kwana biyu ya fada mata yana cikin wata
damuwa dakuwa wani uzuri da ya hana shi zuwa,
amma ta jira shi zai zo gobe za su tattauna
matsalar.
Dole ya ware yau don ita ce ranar da zai shirya
duk abin da ke ransa ya kuma fito fili ya fada mata
ya gaji da jan ran da take masa don yana jin tsoron
Muhammad kada ya yi masa kwambale don ya
fuskanta shi take so haka shi ma yana sonta kuma
ya hana kansa zuwa ne don kada su Hadu da Rauda
kuma ya hana kansa zuwa ne don kada su Hadu da
Rauda saboda boye so ya fara jin haushinta saboda
ita mai kirkin ce.
Kamar yadda ya yi zargin haka ne kuwa ya
kasance yana shigowa gidan ya hange su a can
garden gidan tsaki ya saki to amma babu yadda zai
yi don idan bai je ba duk shirinsa na yau zai
wargaje. Cikin karfin hali ya karasa gurinsu ya yi
sallama. Www.bankinhausanovels.com.ng
Rauda tana ganin shi sai da ta yi wata ajiyar
zuciya a boye shi kadai ne ya lura, don ya tabbatar
da abin da ya sani amma sai ya yi wani irin
basarwa kamar bai san da komai ba hasalima sai ya
shiga tsokanarta yana cewa.
Wato Rauda ba a damu da ni ba kwana biyu,
Haana ce kadai ta biyo ni ta waya ta ji abin da ya
hana ni bullowa.
Lah! Ya Sameer ka yi hakuri ka tambayi
Sister yanzu haka kiranka ma muke yi.
Har cikin ransa yaji dan haushi ya ce, Uwar
naci plcase ki rabu da ni ‘yar uwarki nake so ba ke
ba. Amma a bayyane sai ya ce, Ayya na yarda to
sannu da kokari.
Ya maida kaillonsa gurin Haana ya ce,Yes
Miss Haana ban aron wayarki na bar tawa cikin mota
na duba ban ganta ba, bari na je na kira na gani.
OK, zan bayar, amma da sharadi ba a min
bincike cikin waya, idan ka yarda zan bayar.
Why not, me ye a cikin kwarmin ido ban da kwantsa.
Eh, na ji a yi maza aje a dawo min da ita
saboda ina expecting call mai muhimmanci.
Kya ji da shi. Ya wani warce wayar yana
dariya.Oh! Mr. Sameer haka za ka ce da ka samu na
ara maka tomorrow is another day.
Rauda ta zuba musu ido gani yadda suke
wannan wasan na su wanda kullum cikin haka suke
sai ta gane so ne ko shakuwa tabbas ta ajiye a ranta
cewa Haana ba wani son Sameer take ba, abota ce
da kuma kasancewa su na abokan wasa shi ne
kawai yake nunawa yana sonta.
Haana ta juyo tana kallon Rauda da ta tafi
tunani ta ce, ‘Oh! Hello, what is wrong with his
girl. Rauda lafiyar ki kuwa?
Da sauri ta dawo daga dan gajeran tunanin da
ta tafi ta yi murmushi ta ce, Kalau nake darama
dinku da Ya Sameer ne take burge ni.
Hmmm! Rauda da sani na nake yı wa Sameer
haka tuni na gama ta gane nufinsa a kai na idan da
na bar shi da tuni ya gama gabatar min da
Soyayyarsa gare ni. Ba wai kin sa nake ba sam har
yanzu babu wani da namiji a zuciyata, sama da
Malam M.J. Rauda kin fi kowa sanin haka sai dai
ki fadawa wani. Ina nan ina jiran daowarsa
rayuwata sai dai ba zan taba nunawa kowa cewa
shi nake jira ba musamman Ya Abba, don ya ce
idan ban fitar da shi a raina ba to za mu bata ni
kuwa da na bata da shi gwara na yi ta boye masa
halin da nake ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kuwa Mr. Sameer ina sane za mu yi ta
playing game da shi da haka har ya hakura da ni,
duk da na san shi ma is a nice person, duk macen
da ta same shi za ta more yana da kirki.
Cikin zuciyar Rauda ta fada farin ciki haka ta ji
ta kara
kaunar yar uwarta tunda ta gama gano
gaskiyar ba son Sameer din ta take ba, sai dai ba za
Ta fito fili ta fada mata cewa ita shi take so ba, ba
don komai ba, don kawai ba za ta iya ba saboda
kunyarsu ta Fulanin asali,
Suna hango shi ya dawo suka sauya magana,
Yana karasowa ya ce jikina ya ba ni kun yi magana
ta tunda gaba dayanku ga alamu nan a fuskokin ku.
Rauda ta
yi sauri za ta yi magana Haana tasa
hannu ta rufe mata baki ta ce, Bar ni da shi, mun
yi din nima jikina ya ba ni ka yi min bincike a
waya ka ga lambobin samari na lallai duk lokacin
da na fara zaman office kai zan fara kai wa
takardar sammace a kotu saboda ka amsa laifin
binciken da ka yi min a waya.
Dariya suka yi shi da Rauda ya ce,Samarin ki
din wa ai ni duk ba sa gabana bare har na binciko Su.
Ka hutar da shari’a to a miko min wayata. Ta
mika masa hannu ya saka mata.
Rauda ta yi dariya sosai ta ce, Kai ku kuwa
Idan mutum yana tare da ku sai cikinsa ya yi Ciwo
ni dai bari na je gida na dawo.
Rauda ba za ki gane Mr. Sameer ba shi da
magana da yawa idan ke ma ba kya practice masa
yanzu zai yi winning din ki
OK, nima ba wani dadewa zan yi ba zan
shigo.
Har cikin ransa ya yi farin ciki da tafiyar Rauda
don haka yau dukkan damarsa zai gama amfani da
Ita a nan.
Bayan Rauda ta bar gurn kenan ta ce, “Mr kai
nake sauraro na son nima na shiga ciki ka san
Abba yana daf da zuwa kar ya zo ya gan ni ba na
karatu na tsaya hira.
Murmushi ya yi ya ce, “AI ni kuma zan fi kowa
son ganin Abba ya gamu tare saboda zai fi kowa
sanin dalilinna don na gaji da jan ran da ki ke mn
please Haana ki tsaida hankalin ki.
Na san kin gane manufata da kuma dangantakar
da take gare ni, amma duk sai ki dinga mayar da ita
wasa, yanzu lokaci ya yi da za ki fuskanci me nake
nufi duk da kuwa kin sani ki ke kaucewa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana ina son ki ba ni dama na fadawa su
Abban gurin mu inaso su zo nemar min auran
ki da gaske nake ke nake son aura ki cire duk
wasan da ke ranki ki fuskance ni, ni fa auran ki zan
yi don kaf zuri’a dinmu babu wacce nake jin zan
Iya zaman aure da ita idan ba ke ba, ki kuma duba
yadda ta dalilinmu aka samu zurı’ a dinmu ta gyaru
kin ga kowa zai yi farin ciki ki kuma duba yadda ta
dalilinmu aka samu zuri’a dinmu ta gyaru kin ga
kowa zai yi farin ciki da jin cewa munyi aure.
Haana ina miki irin son da babu bakin da zai
Iya furtawa ko fasalta yawan irin son da nake miki,
amma kisani ba zan miki dole ba idan ba kya sona
Kuma bazan taba daina son ki ba har zuwa karshen
rayuwata. Ya ki ka ga ni za ki iya zama da ni a
matsayin abokin rayuwarki ko a’ a’? Ba na tunanin
idan na rasa ki zan yi aure har karshen rayuwata.
Shiru ta yi ta rasa ya za ta yi da Sameer, domin
ko kadan ba ta zaci cewa da wannan batun ya zo ba
da ba ta bari Rauda ta tafi ta bar ta ba. To amma
tunda har shi ma bai boye mata abin da yake ransa
ba ita ma ba za ta cuci kanta ta boye tata damuwar
ba Na ji abin da ka ce, amma maganar gaskiya
ina mai ba ka hakuri tuni muka yi wa junanmu
alkawarin aure da Malam M.J ka yi hakuri Allah
ya ba ka wacce ta fi ni gaskiya zan fi son
dangantakarmu ta abokai ta ci gaba a haka ka cire
batun aure a tsakaninmu. Na fito na fada maka
gaskiya ne don babu boye-boye a tsakaninmu da
fatan za ka fahimci magana ta.
Idan kuma ta yi maka zafi don Allah ka yi
hakuri ni ma ban so na bata maka rai ba. Tana
gama faidn haka ta mike ta ce, “Ni zan koma ciki.
“Babu laifi za ki iya tafiya.”
Ka yi hakuri da fatan ba fushi ka yiba.
Haka na ce miki za ki iya tafiya tunda dama
bada ni ku ka zo ba.”
Jin furucinsa ta san cikin fushi ya yi magana ba
ta kara cewa da shi komai ba ta juya ta tafi duk ta
dinga jin ta wani irin cikin ranta.Sati guda suka diba babu wata jituwa a
Isakannsu babu wanda yake neman wani haka
Sameer ya dauke kafarsa daga zuwa gidansu, Yana
shiga idan ya fuskanta ba ta cikin gidan ko da ya
Abba ya fuskanCi akwai yar wata rashin jituwa a
tsakaninsu sai ya ji farin CIki ya kama shi haka ya
shiga jan Haana da yawan shige mata duk inda za
shi ita ce take zama abokiyar rakiyarsa.
Ranar wata Laraba sun fito kenan za su fita da
yamma wannan karon tare da Rauda suka fito shi
kuma ya fito cikin shirinsa zai tafi Polo Club
Sanye yake cikin wasu kananan kaya blue jeans da
black shirt sanye yake cikin wasu manyan haruffa
da aka ce YOU ARE MY LOVE. Shigen nasa ya yi
kyau sai ta ga ya yi mata yanayi da Malam M.J
dinta ko dan ta don kwana biyu ba ta gan shi ba ne
ya yi mata wani fresh da shi. Ita dai tana mamakin
lokuta da dama da Mr. Sameer dinta yake satar
kama da Malam M.J ta jima tana ganin haka amma
sai tana karya ta kanta tana sawa a ranta Cewa
kewarsa ne yasa yake mata kama da shi.
Haka taji yau tana son masa magana don
kawai fushin da yake da ita, don ko ba komai ta san
ta yi kewarsa. Ta rabu da jin hayaniyarsa da ‘yar
tsamarsu da suka yi Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka ta dinga ji wani irin kewarsa ta ji tana son
yi masa magana. Yana ganin motarsu ya fasa shiga
Tashi motar ya tsaya don ya hango su. Ya Abba ne
Ke jan motar yana ganinsa don ya cusa masa haushi
ya wani nufo shi ya tsaya a gabansa don ya nuna
masa tare yake da mutuniyarsa.
Suna hada idanu da ita ya yi saurin kauda kai
Ya wani basar ya dan daure fuska. Sai kuma ya
watsar ya ce Abba ya gida ya jin dadi. Bayan ya
mika masa hannu suka gaisa.
Murmushi ya Abba yayi ya ce, Sai godiyar
Allah.
Ya cire kai ya kai kallonsa ga Rauda ya ce,
Rauda ya gida ya su Mama Me, kwana biyu ban
zo mun gaisa ba ki gaida ta ki ce zan shigo ina
busy ne.
Cikin jin dadi ta ce, “Za ta ji.
Har cikin ran Haana ba taji dadin yadda Mr.
Sameer ya nuna kamar bai ganta ba, to amma tunda
ta gane na ta laifin ne tana kuma Son su dawo
kamar yadda suke a da can. Da har za ta yi magana
sai taji ya ce,Abba zan wuce kada na makara
muna da training ne yau bari na wuce.
Oh! Mr. Sameer har ta kai a gan ni aki yi min
magana, ba fada me ya kawo gaba.
Raihanatu ki na lafiya.
Yadda ya kira sunanta cikakke sai da ta ji
gabanta ya fadi gaba daya sai ta ga yadda ya yi
acting kamar Malam M.J don shi ne kadai yake
kiranta da wannan sunan yadda ya tsare gida da
wani shan kamshi sai ta ga kamar shi din ne.
*Abba ni na wuce Rauda kada ki manta fa.
Bai jira cewar su ba ya kama hanya abinsa.
Ganin haka nan da nan fuskar Haana ta sauya har
Cikin ranta ba ta ji dadi ba yadda Mr. Sameer ya yi
mata ba ya wulakanta ta ta s0 ta ji haushi SOsai, amma
ganin yadda wani yanayi da wani daya
tafi ya bar ta sai ta ga kamar Malam M.J ne
Sarai Ya Abba ya fuskanci ba ta ji dadin abin
da ya yi mata ba, amma shi cikin ransa ya ji dadin
haka, don ya yi hakan ne don daya daga cikinsu ya
Ji haushi, sai ya ga kamar damuwar tata ta fi ta
Sameer. Nan da nan ji ya yi damuwa tana ziyartar
zuciyarsa don kO kadan bai san ganın Haana dinsa
cikin damuwa ko da kuwa wacce iri ce. Tabbas da
ya san za ta shiga wannan damuwar da bai yarda
sun tsaya ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya Abba ya yi saurin taka motarsa don su yi
sauri barin gurin. Shiru motar ta yi babu wanda ya
ce kanzal can dai Rauda ta ce,Sister wai mai ya
faru da ku ke da Ya Sameer.
Me ki ka gani kin san halinsa ba sai na fada
miki ba.
“Gaskiya ne.
Yana jin su bai ce musu komai ba don bai son
su sak0 masa maganar Sameer don ya ji ya bata
masa rai domin shi ne ya janyo damuwar da ya
gani a kan fuskar Haana dinsa nan ya ji yana son
korar damuwar da take son zama a cikin ranta.
Da sauri ya ce, Haana wai ina batun malamin
ki ne kwana biyu na ji kin daina min maganarsa kin
yarda da magana ta ko? Ya fadi hakan ne don ya
San maganarsa ce kawai zai ga farn ciki a kan
fuskarta ya kori kuncin da KUNAR ZUCIN da
yake hangowa a kan fuskarta ba wai don baya

< p>

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *