ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 15 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
A fakaice yake kallonta don ganin yanayin da
ta shiga ta yi kamar za ta ce wani abu sai ta dake
kawai ta ce, “Mr. Ba wai kin ka nake ba, ka
fuskanci dalilin da na fada maka a baya.
Ai na gamsu tuntuni shi yasa nima na fadi
haka ganin tuni M.J ya gama yin tasiri a zuciyarki
ba kya ganin kowa sai shi.
Wannan karon kasa boye damuwarta ta yi ta ce,
Please Mr. Sameer ba na son ka sake yi min
maganar M.J bana son jin ko kadan.”
“Kan wanne dalili?
Ba sai ka ji dalili ba, kamar yadda na ce ka
manta please ka manta ba na son kowa yana kawo
min batun sa ko saka shi cikin al’amarin na ina son
1n manta da shi saboda na samu nutsuwa.
Babu damuwa zan yi duk abin da ki ka ce
mutukar hakan zai saki farin ciki, a yanzu a shirye
nake da na baki dukkan wata gudunmawa da za ta
saki fari ciki. Ni Sameer a shirye nake ki ba ni
kambun zama babban abokinki amininki domin
zama muna tattauna matsalarki. Na hakura da
kalmar soyayya a gare ki na dangana da cewa ke ba
Kaddarata ba ce sai dai ina son ki taya ni da samun
mace kamar ki.”
Tsananin tausayinsa ne ya kamata don ta hangi
tarin so da kaunarta a idanunsa, haka ta dinga jin
tana yaba jaruimtarsa.
“Mr. Sameer kar ka damu koma me ka ke nema
a gurina za ka samu, amma ina so ka ba ni lokaci
kadan ba da jimawa ba.
Tana fadn haka daidai lokacin da Alh. Lukman
ya fito daga gidansa domin daf da kofar get dinsa
suke tsaya suna ganinsa suka nutsu suka gaida shi, Www.bankinhausanovels.com.ng
Amsawa kawa1 ya yi ya wuce abin sai ganin haka
suma suka yi kokarin barin wurin. Sai da ya kai
bakin get din su Hajiya Babba sannan ya dawo ya
nufi gida, zuciyarsa cike da farin cikin maganar da
suka yi da ita nan ya dinga hangowa cewa zai yi
nasara da abin da yake nema a gurin Haana.
Yau a kalla fiye da wata guda da faruwar haka
Mr. Sameer da Miss Haana sun yi wata shakuwa
sosai ba tare da kowa ya sani ba, domin sam bai
fiye zuwa gidan ba a waya suke maganarsu ko
wane dare suna raba shi a waya. Haana ce ta zabi
hakan don gusar da damuwar da Malam M.J ya yi
mata tana yin hakan ne don ta kori damuwar da ya
jefa ta, amma sai dai duk da haka ta ji ta kasa
mantawa da shi duk da kuwa har yanzu tana jin ta
tsane sh.Hakan ba karamin kwantar wa da Mr. Sameer
zuciya yake ba. Sun shaku sun kuma gama
amincewa da kowa na san dauwansa sai dai har
yanzu Haana din ba ta ba shi damar ya bayyanawa
kowa ta amince da shi domin maganar gaskiya ta ji
Zuciyarta ta soma gamsuwa da da shi saboda yana
mutukar kokarin mantar da ita tunanin M.J har ta
Soma jin za ta iya tsayar da shi wanda zai zamo
mata makwafinsa.
Yau ma kamar kullum kwance take kan
gadonta suna yin wayarsu kamar yadda suka saba.
Rauda ce ta yi sallama ta shigo cikin dakin fuskarta Www.bankinhausanovels.com.ng
sake ganin yadda ta ga Haana na yin wayarta cikin
nishadi da walwala haka ta ji ita ma ranta ya yi
mata dadi, don daga ganinta ta san da wani
masoyinta take waya ko dai M.J din ne ko kuma
wani saboda tana da yakinin yanzu babu wata
soyayya tsakaninta da Mr. Sameer din don haka ta
zo don ta fada mata abin da ke damunta game da
shi, ko za ta 1ya taimaka mata ta samu saukin abin
a ranta.
Sallama ta yi da shi ta ce za ta kira anjima.
Yadda ta ga Haana na nishadin wayar ta ce, “Sister
da ban katse ku ba saboda na fuskanci kina jin
dadin wayar nan wai wa aka samo mana ne na
fuskanci kamar kin samu wani tun kwanaki nake
damun ki fada min wane ki ke cewa idan kin gama
nazari za ki fada mana, ko dai Malam M.j ne ya
dawo rayuwarki?
Nan da nan ta sauya fuska ta ce, “Plcase Rauda
mu bar wannan maganar na shafe babin Malam M.J tuntuni.
Zaro 1danunta ta yi waje ta ce, “Sıster da wuri
haka kamar cin wutar gobara.
To Rauda me zai rage da kansa ya fada min ya
tsayar da matar auransa to zan tsaya ne ina ta
yaudarar kaina kin ga idan an yi haka babu wanda
na zalunta sai kaina yana can cikin farin cikinsa ni
kuma na zauna ina bakanta zuciyata. Ta girgiza kanta ta ce.Ina ba zan iya ba maganar Ya Abba da Mr.Samcer ta yi mini tasirI da suke cewa na tsaya na fuskanci rcality kuma na gani don ga shi
shawararsu ta yi min amfani, saidai manta abin da kake so lokaci daya ba abu ne mai sauki ba, tunda naji daga gare shi ai dole na tsaya na yi fada da
zuciyata ko ya ki ka gani?Gaskiya ne Sister ba ni ganin laifin haka ko Www.bankinhausanovels.com.ng
nima nan da tawa matsalar na zo mikI, amma ina
son jin waye wannan da ya hambare gwamnatin
Malam M.J ne haka da har ya yi saurin tasiri a
zuciyarki haka please tell me na ji. Ta fada tana
mai kara nanukar inda take zaune kan gadonta
cikin murmushi.
Murmushi ta yi ta dan ja da baya kadan ta
jinginar da bayanta a kan gadon ta ce, “Rauda na
kamu da so lokaci guda son da ban san zan iya y1
masa ba, amma takarawar korar damuwar da nake
ciki yasa har ya samu wannan damar da tasirin
cikin zuciyata, ina son shi zan kuma iya auransa
saboda na fuskanta zai iya ba ni dukkan farin cikin
da nake son samu a rayuwata so da kula duk zan
samu a gurinSa.
Rauda ba kowa ba ne sai MR. SAMEER. Mr.
Samcer na yi mamakin yadda ya yi wa zuciyata
tasiri da har na ji zan aure shi ya damu na ba shi
dama na fada a gida naki na kuma hana ya fadawa
kowa. Hakan nasa na ce yau ya samu ya Abba ya
fada masa ya fadawa su Abba saboda ni ba zan iya
fada masaba saboda ni ina jin kunyarsa, shi yayana
ne shi kuma abokine dan uwansa. Shin Rauda ya
ki ka ga zabin nawa ya yi?
Tsananin tashin hankali, rudani da BUGUN
ZUCIYA su ne suka hadu suka ruda zuciyar Rauda
kai ba ita kadai ba har Ya Abba da yake tsaye
bakin kofar dakin tun hango zuwan Rauda ya nufo
dakin don ya ji yadda za ta fadi sakon da ya turo
ta.Haka Rauda ta ji jiri da wani irin nauyi da ta Ji
zuciyarta na yi mata duk inda ta yi kokarin danne
damuwarta ta kasa, tana dago idonta ta hangi Ya
Abba cikin nasa tashin hankalin, girgiza mata kai
ya yi alamar kada ta ce komai.
Shin kanta za ta tausayawa ko Yayanta da suke
Ciki daya? Juyowa Haana ta yi ta ce, “Sister ban ji
kin ce komai ba?'” Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna hada ido Rauda ta yi duk yadda za ta yi
sai da ta yi kokarin kirkiro murmushin yake ta ce,
Wonderful Sister zabin ki ya yi kyau kun kuma
dace
Tana fadin haka ta ji wani irin hawayen bakin
ciki ya zo mata ta yi sauri ta kau da kanta daidai
lokacin da wayarta ta hau ringing da sauri ta maida
hankalinta ga wayar tana
duba sunan ta ga sunan
Ya Abba.Ba ta juya ba ta dauki wyaar ta kara a kunnenta
ta ce, Haana Baba ke kira na zan dawo.
Kije ina jiranki ki dawo ki ba ni shawarwari.
Sam Haana ba ta fuskanci irin yanayin tashin
hankalin da Rauda dinta take ciki ba. A bangaren
Rauda kuwa godewa Allah ta yi da Ya Abba ya
kira ta da babu yadda za ta yi ta iya boye tashin
hankalinta har sai ta gane idan kuma ta gane akwai
matsala. Tana fitowa daga dakin sai Ya Abba ya yi
sauri ya janyo hannunta ganin yadda ta shiga
rudani sai yaji tsananin tausayin yar uwarsa ya
girgiza mata kai kawai sai kuka.
Rauda ki yi shiru kada ki bari wani ya gane
halin da ki ke ciki.
Daga masa kai ta yi tana zubar da hawaye ya yi
sauri ya rike hannunta suka faki idon mutane sai
suka yi dakinsa da ke can wani korido.
Kuka ta yi mai tsuma rai ya kasa ce mata
komai, domin shi kansa yana bukatar wanda zai
rarrashe shi, domin ya samu saukin KUNAR
ZUCIN da yake fama da shi. Tashin hankali goma
da ashirin tabbas da ya sani wannan ranar za ta zo
da musu cikin wannan tashin hankalin shi da
kanwarsa ciki daya da bai aika ta taje ta jiyo musu
wannan tashin hankalin ba ya y1 haka ne don kawai
Ya fitar da kanwarsa daga dakon son da take yi na
Sameer ganin kamar babu wata soyayya tsakaninsu ya aikaa ta ta bugo masa cikinta don ya samu Www.bankinhausanovels.com.ng
damar bayyana mata haln da yake ciki game
da ita. Tuni Rauda ta yi kokarin ta fada mata ya
hana ta saboda kanta ta gan0 cewa shi din sonta
yake amma ya kasa yadda zai yi ya fada mata.
Baya manta wata rana da ta Zo ta same sh1 a
dakinsa yasa hotonta a gaba yana kallon bai fi wata da dawowa ba, ya yi nisa cikin kallon hoton nata
har ta yi sallanma ta shigo bai san ta shigo ba, da
sauri ta lallaba ta je ta ga wane hoto yake gani da
ya shagaltar da shi haka da bai iya amsa sallamar taba.
Tsananin mamaki ta shiga cikin zuciyarta ta ce
To fa su haka tasu kaddarar take ita tana son
Sameer bai san tana yi ba, haka shi kuma yana son
Haana ba ta san yana yi ba, lallai suna cikin jarraba da kuma rubutun kaddara.
Bai yi aune ba ya ganta gabansa da sauri ya
shiga kokarin boye hoton nata cikin yanayin
damuwa da tausayawa ta ce, “Ya Abba ai na gani
hoton Haana ne, Ya Abba son ta ka ke yi ne?
Wa ya fada miki sonta nake y1 maza bace min
daga nan da wannan zancen shirmen naki. Ya
fada yana mai tsare gida.
Yi hakuri ya Abba kada ka boye min komai Ya
nima ina cikin irin wannan matsalar ko ba ka fada
min ba na jima da fuskantar cewa kana son Sister
sbaoda irin salon kauna da kulawar da ka ke ba mu
duk daban ne, kuma yau ga shi na ga hakan a
kwayar idanunka. Nan ta dage a kan sai ta fada
mata ya hana ta ya ce dole sai ta fusaknci hakan da
kanta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Babu yadda ta iya tunda ita ce karama dole sai
abin da ya ce da ita za ta yi. Ita ma a nan ta fada
masa ita ma halin da take ciki shi ma dagewa ya yi
Ya tursasa ta a kan cewa kowane hali za ta shiga
kada ta bari ta bayyanawa Sameer cewa tana son
shi a matsayinta na diya amce, idan ya fito ya ce
baya son ta ya dizgata ya kuma daina ganin
mutuncinta na diya mace idan kuma ta yi hakan
darajarta za ta zube.
Haka suka wanzu kullum yana ba ta baki da
kwantar mata da rai har kawo ya zuwa yanzu da
suke cikin wannan irin hali.
Dafa kafadarta ya yi ta dago idanunta da suka
Tine cikin hawaye suna hada 1do Wasu hawayen
suka wanke mata fuska.
Ya ce. Rauda share hawayenki ban son ganin
ki cikin wannan halin na kasa gane komai na kasa
cewa kala a kai anya kuwa ba alhakin Haaya ba ne
ya kama ni yadda na taho na baro ta shi ne abin
yake tabani da ke na yi wa kanwar wani haka nima
ga shi nan an y1 wa tawa.
Da sauri ta tambaye shi, Ya Abba wace ce
kuma Haaya a ina take?
Take ya ba ta labarinta da duk yadda suka yi
rayuwa da rabuwarsu ba tare da ya yi salalma da itaba, ita ma da ta ji nata labarin ta tausayawa Haava din.
Nan ya ce, “Rauda ina son baki farin ciki sai
dai ban san yadda zan yi ba, na san farin cikin ki ki
samu Sameer a matsayin mijin aure, idan na baki
Sameer ko na yi miki kokarin samun shi a
matsayin mijin aure zan jefa rayuwar Haana cikin
tashin hankali ta rasa M.J ta hakura yanzu ta kamu
da son Sameer idan na ce ta hakura da shi ban yi
mata adalci ba, domin na raba ta da wanda take so
na ce ta bar miki.
Come on, Ya Abba ka dawo tunanin ka kai ba
kai ne za ka iya ba ni Sameer ba, ka tuna. Kai
yayanmu ne wannan furucin da ka ke yi kana yinsa
ne kawai, Abba ne ko Baba za su iya fada mana.
Please ka dawo cikin tunanin ka kar ka damu zan
iya jure kowa ne kalubalen rayuwa ni kai na ina
Son ganin yar uwata ta samu abin da take so a
shirye nake na sadaukar da farin cikina ga ‘yar
uwata. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kamar yadda kullum ka ke ba ni kwarin gwiwa
a kan na jure zan cigaba da jurewa, sai dai kai ban
sani ba ko za ka iya jure rashin Haana, na san irin
tarin son da ka ke mata tunda har ka rufe ido ka
barar da irin wannan mahaukacin son da Haaya
take maka.
Ya Abba ban san ya zan iya cewa ka yi hakuri
da Haana ba idan na ce ka hakura da ita sai na ga
kamar ban yi maka adalci ba, amma ni insha
Allahu zan yi kokarin cire son Sameer a raina
tunda ban da kai babu wanda na fito na fadawa.
Saboda bana son na saka maka damuwa biyu
ga taka ga tawa. Ni dai na hakura da shi tunda na
fuskanci Haana tana son shi ni kuma ba zan ta6a
son abin da take so ba. Ya Abba zan koma gida
bana son cikin gida a fuskanci muna cikin matsala
ni da kai.
Ba ta jira cewarsa ba ta juya ta fice bai ce da ita
Kala ba, har ta fice. Tausayinta ne mai tsanani ya
ratsa zuciyarsa nan ya shiga cikin wata sabuwar
damuwa.
Cikin nasara ta zo ta fice ba tare da kowa ya ga
fitowarta ba. Fitowa ta yi tana sharar hawaye kanta
A kasa daf da za ta shiga get din gidansu ta ji an
kira sunanta. Da sauri ta juyo don ta shaida muryar
Mr. Saneer ta gani. Nan ta yi wani mugun dakiya
ta yi saurin korar damuwar da ke fuskarta ta kirkiro
murmushi ta ce,Ya Sameer ya gida?
Bai amsa mata ba ya shiga kura mata idanu
ganin irin kallon da yake mata yasa ta yi kasa da
idanunta don ba za ta iya jurewa ba.
Rauda me yasa ki kuka?
Ni ba kuka na yi ba.
To me nake gani a idanun ki?
Idona ke min ciwo.
“Ban yarda ba.”
Me yasa ba za ka yarda ba?
Saboda ba gaskiya ki ka fada min ba.'”
Ya a kai ka san ba gaskiya na fada maka ba
tare ka ke da ni ko yaya?
Rauda nine na saki kuka a kaina ki ka yi
kuka,
Dam! Ta ji gaban ta ya fadi ta yis saurin cire
kanta ta dube shi ta y1 ta kasa cewa komai zuwa
can ta ce, “A kan me zan yi kuka domin ka?”
Kwarai kuwa domn n1 wannan hawayen ke
fita saboda ki na sona.
Kallonsa ta yi Cikin jajayen idanunta da suka
rune da hawaye ta ce,Son ka fa ka ce waya fada
maka haka? Eh to ina Son ka a matsayin ka dan
uwana na jini mana.
Ba gaskiya ba ne bayan wannan son akwai
wani a Cikin zuCiyarki,.
“Please Ya Sameer ka bar ni na tafi abu na
bana son jin wadannan furucin na fitowa a bakin ka please na roke ka.
Dole ki ji, idan ba kya sona to ki kalli kwayar
idanuna ki ce min Sameer bana son ka hakan ne
kawai zai sa na yarda. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya Sameer a 1na kaji wannan maganar da ka
ke tuhumata da ita, ban taba son ka da wata siga ba
sai ta dangantaka, idan kana wannan tunanin ma ka
bari Look! Rauda kada ki boye min komai na
san
halin da ki ke ciki kuma insha Allah zan nemo
mafita.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG