ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE



                Www.bankinhausanovels.com.ng 


Damuwa ce ta Cika masa zuciyarsa fal. Tabbas
ya na Cikin tsaka mai wuya, ta ya zai iya janye
wannan al amarin, ya ma zal 1ya cire Haana daga
ransa, ga tausayin Rauda ma da yake kwana ya
Tashi da shi. Dama ya zo ne ya fadawa iyayensa
cewa duk su biyun zai hada ya aura. Ya fara kawo
maganar Haana ne don ya ji yadda za su karbi abin,
sai kuma ga shi natan ma ba su karba ba, balle
kuma a je ga batun na Rauda.
Ya ma rasa yadda zai yi da damuwarsa. Sai
kawai ya dauki wayarsa ya kira Rauda, Wajen sau
uku ya na kiran wayar amma ba’a daga ba, sai a na
hudun daf da za ta tsinke ta daga.

Ya Abba ne zaune gaban Granny don amsa
kiran da ta yi masa, su biyu ne kawai a dakin daga
shi sai ita. Granny ta dube shi ta ce.
Mustapha karami dama na kira ka ne don mu
YI wata magana, to amma ina son na ji ra ayinka
akan haka.
To Granny ai ke nake saurare. Ya fada ya na
mai kara sanya nutsuwa hade da murmushi a
fuskarsa.
Mustapha shin ka na da wata wacce ka ke so a
Zuciyarka, ko kuma ka bamu damar mu nema maka
wacce za ka aura?.
Dam! Ya ji gabansa ya fadi. Ko kadan bai
kawo wannan maganar ce makasudin kiran nasa
ba. Shiru dai kawai ya yi na wani lokaci bai ce da
ita komai ba.
Ka yi shiru ba ka ce komai ba, amma bari na
bayyana maka komai. NI da Abbanku mun yanke
hada aurenku kai da kanwarka Raihanatu, ganin
shakuwarku da son da ku ke wa junanku ya sa
muka yanke hakan. Ko da yake tun tana karama na
fadawa Abbanku cewa idan har muna raye ina so
ya hada aurenku. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wannan shawarar muka yanke, amma ya ka
gani?


Granny a wajena ba matsala, sai dai ita Haana
din tunda muke da ita ba ta taba yi min kallon
wanda ba ciki daya muka fito ba. Duk irin kulawa
da kaunar da nake bata amma ba ta lura da hakan
ba, Granny Haana ita ce wacce nake So ba tun yau
ba, ita ce zabina kamar yadda take zabin ku, Sai
dai illar daya shi ne, bana jin sOn da ta ke min irin
na aure ne, sai dai na fi ganinsa a matsayin na ‘yan
uwantaka, don da kunne na na J1 suna hira da
Rauda cewa Sameer ta ke so, shi kuma ta ke son
aura.ina ganin mu barta kawar don ba na so a yi
mata dole a kaina, ina son ganinta cikin farin ciki,
kuma ba na so ko alama ta san da wannan maganar.
Da babu Sameer cikin rayuwarta zan so a fada
mata, to amma tunda na ji shi ta ke so to ku bar
maganar ba na so a yi mata dole a kaina
Cikin damuwa Granny ta ce. “Sam ni ban yarda
ban kuma amince da wannan maganar taka ba.
Burina ne wannan ace yau na bude ido naga na
hada wannan auren. Me ya sa za ka yi min haka,
kasan kana. sonta amma baka fada min ba har aka
bari haka ta faru?.
Ka kwantar da hankalinka, insha Allah ba ka da
wata mata sai Raihanatu, babu wanda ya fika shan
Wuya a kanta, kai ka yi dawainiyarta tun tana
karama, kun shaku babu kuma da wanda ta saba
sama da kai. Ina mai tabbatar maka da cewa
Raihanatu za ta yi farin ciki da kai a matsayin miji.
NI Ina ganin ba ka nuna mata kana sonta ba shi
yasa hakan ta taru.
Mun gama magana da Abbanku har yakai
maganar wajen yan uwansa don a soke dokar da
Suka likawa kansu ta hana aure tsakanin ZURI’A
DAYA
Girgiza kai ya yi sannan ya Ce. Granny me
yasa za ku yi haka, me yasa za ku yiwa yar uwata
auren dole?. Plcase idan har don ni z ku y1 haka, to na roke ku da ku bari.  gara ni na yi ta zama cikin kunci, ko kadan
bana son abin da zai tayar mata da hankali.
Ni naga irin damuwar da ta shiga lokacin da ta
rasa Malaminta na makaranta wanda ta ke SO, haka
muka sanya ta hakura. Yanzu kuma ta fara Son
Sameer nan ma kuma ace ba za ta aure shi ba.
Tabbas idan akai mata haka za ta shiga damuwa ko a
yanzu ma ina hango damuwar da za ta shiga
idan ta ji wannan maganar. Www.bankinhausanovels.com.ng
Granny idan har an yarda da abin da zan ce,
abar magana ta, na hakura da ita Allah zai bani
wata
Granny ta katse shi da cewa. Wa ya fada maka
Raihanatu za ta shiga damuwa?, ba wata damuwa
da za ta shiga baya ga ma ta yi farin ciki, za ta yi
murna SOsai ace abokin shawararta ya zamo
mijinta
Murmushi ya y1 da bai kai zucI ba ya ce.
Granny da hakan za ta kasance dana so, sai dai
tunda ta ce tana son Sameer abar maganar ta wuce,
kar ma a bari tasan wainan maganar
Me ya sanya za ka yi haka Mustapha?
Saboda Haana ta samu abin da take so zan iya
sadaukar da duk farin cikina akan farin cikinta,
Duk rintsin da zan shiga, ganinta cikin farin ciki
shi ne nawa farin cikin. Allah Granny ki fahimce ni
ta yadda za ki fahimtar da Abba.
Inason Haana so na hakika,
sadaukarwar da zan yi mata ita ce za ta nuna son
nake mata na hakika ne
Na fahimta, dama nima tuni na fahimci son da
ka ke mata, na kuma yi maka shiru ne har sai ka zo
ka yi min maganar da kanka, to amma sanin zurfin
Cikin ka da na jima da sani ya sanya kawai na kira
Abbanku na kuma tunatar da shi. Sai shima ya ke
fada min ai ya na sane ba wai mantawa ya yi ba.
To Granny ki yi hakuri ki fahimtar da shi
nawa dalılin, nasan zai yi min uziri
Sun jima sosai suna mahawara akan maganar,
har sai da Granny ta hakura akan dole ba wai don
ta so ba, saboda kawai damuwa da kuma rokonta
da ya ke. Daga nan ya fice ya barta cikin alhini tare
da tsananin tausaya masa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya na fitowa kai tsaye gidansu ya nufa. Ya na
shiga bai wuce ko ina ba sai dakin Rauda. Ya na
ganinta yasan akwai damuwa a fuskarta don
fuskarta kamar ta yi kuka. Ta na ganinsa ta yi
saurin kirkiro murmushi, amma kai da gani kasan
an yi shi ne ba wai cikin son rai da walwala ba.
Ya Abba sannu da zuwa
Yawwa Raudana, ba dai damuwar ba ce haryau?
Ba ita ba ce Ta fada ta na mai kara
murmushin fuskarta
To zan so hakan kuwa. Sai dai kuma nazo
wajenkI ne don na kara miki wata damuwar, da
fatan za ki yi hakuri da ni ki kuma yarda da abin da
zan fada. Nasan dai babu dadi, tunda nasan Irin
halin da ki ke ciki nima kuma shi nake ciki.
Murmushin dai ta sake yi, amma wannan karon
mai dauke da damuwa a fuskarta, ta na yinsa ne
kawai don ta nunawa Yayam nata cewa ba ta da
damuwa, sannan ta ce.
Ya Abba nasan ba za ka taba sanyalti Cikin
damuwa ba, sai dai ka korar min ita. A shirye nake
na yi duk abin da za ka sanya ni matukar dai kai za
ka yi farin ciki da shi.
Nan ya kwashe duk yadda suka yi da Granny
ya fada mata. 1ta ma ta tausaya masa. A haka ya
dora da fadin.
Please Raudana, ina son don Allah duk da
nasan abin ba sauki ki Cire son Sameer a zuciyarki,
ka
da ki yarda da abin da ki ka fada min ya ce miki
rannan daure ki barwa Haana shi tunda ita ya
furta ya na so. na roke ki ko da wasa kar ki taba
nuna yadda za ta gane kina son Sameer.
Ina so ki bar mata shi, 1dan har ki ka yi min
haka, zan san cewa da gaske kina sOn Haana za
kunma ki bata duk abin da take so
Hawaye ne ya zubo mata, nan ta fara magana
da Haba Ya Abba, idan wannan ne abn da ka ke
SO na yI maka alkawari, ai tuni ni na yiwa kaina
kan cewar ba zan taba bari ta san na taba son
Sameer ba. Kamar yadda ka sadaukar da naka farin
cikin, ni ma na sadaukar da nawan, farin cikin ga
Haana ya fi mana komai, tabbas da ita ce cikin
halin da muke ciki iyakar itama abin da za ta yi
mana kenan.
Tunda kuwa muna da yakinin hakan ai mu ma
ya zame mana dole mu yi mata haka tunda ba
faduwa muka yi ba
Rauda na gode sOsai, Allah ya baki abin da ki
ke so duniya da lahira, ya kaw0 miki wanda ya fi
Sameer komai a rayuWarki.
Dariya ta yi mai hade da hawaye. Da sauri ya
matso kusa da ita ya sanya hannu ya na share mata
hawayen.
Me ya faru da Raudana ta ke kuka haka, me ya
sameki Rauda ki ke kuka, Ya Abba me aka yi mata
har ya sanyata kuha haka? Www.bankinhausanovels.com.ng
Gaba daya suka juyo Cikin kaduwa. Haana
suka gani a bayansu Cikin damuwa. Da sauri ta
matso gaban Rauda cikin damuwa ta ce.
Ya Abba ba ka fada min abin da ya sanyata
kuka ba. Shiru suka yi duk su biyun. Godiyar su
ga Allah da bai sa ta ji abin da suka tattauna ba. Saiya rasa ma mai zai ce da ita. Can dai ya daure ya
Ce.
Kwantar da hankalinki Haana, ba komai ya ke
damun Rauda ba sai ciwon kai, shi ne fa wai ta ke
kuka ni na shigo 1na rarrashinta
Cire kai ta yi ta dube shi, kamar ba ta yarda da
abin da ya fada mata ba, amma tunawar da ta yi
cewa Ya Abba ba zai taba fada mata abin da yake
ba haka ba, sai ta cira kai ta ce.
Ya Abba damuwar da na gani a fuskar ku ta yi
yawa, sai jikina ya bani cewa akwai wani abu da ku
ke boye min
Har Rauda za ta yi magana, ya yi saurin dakatar
da ita ya ce. Haana mai ya kawo zargi a
Junanmu?, ke da Rauda abu daya ne a wajena,
yadda zan bata kulawa haka kema zan baki, ba ku
da bambanci a wajena, zan iya zama na yi sirr1 da
ke ba ta ma sani ba. Don haka mene ne ma na kawo
haka a tare da ke.
Matsayinmu daya duka mu ukun, ciki daya ne
kawai ba mu fito tare da ke ba. Idan kina min hak
za ki sanya ni cikin damuwa na fara wani zargi a
Zuciyata.
Da sauri ta tare shi da cewa. “Sorry Ya Abba,
ba haka nake nufí ba. Don Allah ka yi hakuri idan
na bata maka rai
Murmushi ya yi ganin yadda lokacin guda ta
nuna nadamarta akan abin da ta yi masa yä ce. To
na hakura, sai dai idan ki ka sake yi min haka zan
yi fishi da ke fiye da wanda na yi yanzu
Insha Allah ma ba zan sake ba. To ka yi
murmushi mana
Ba shi ba har Rauda sai da ta yi dariya. Ganin
ya kori damuwar da ke fuskarta sai ya ce. “To ni
zan tafi.
Ta juyo ta ce. “Ya Abba ba za ka tafi ba sai ka
yi mana shari’a da Rauda don kararta na kawo
maka. Yau kwana uku kenan ban sake ganinta ba,
ta ma kashe wayarta, 1dan na kira bana samunta, na
kuma ba da sako idan ta daWO ta zo 1na nemanta,
amma ba ta zO ba, ban san me na yi mata ba ta
kaura ce min haka.
Sannan ta shirya ta tafi Hotoro gidan Maman
Nawal ba tare da na sani ba, da na ji ta dawo ne shi
ne na shigo na ji laifin me na yi mata haka”.
Sai kawai ya yi murmushin yake ya ce. “Rauda
sam ba ki kyauta ba, maza ki bata hakuri, kice
kuma ba za ki sake ba
Ita ma Www.bankinhausanovels.com.ng
murmushin ta yi mai cike da danne
damuwar da ta ke ciki ta kama kunnenta sannan ta
ce. Ki yi hakuri sister, na yi miki laifi amma ba
zan sake ba nan gaba.
Da sauri Haana ta z0 ta cire hannunta daga
kama kunnen da ta yi ta ce. “Is ok, Ya Abba hakuri
naso ka sanya ta bani ba, dalilin kawai da ya sa ta
yi min hakan kawai nake s0 naji
Yanzu dai Haana kin ga ba ta jin dadi, idan
mu ka takura ta da magana ciwon ba sauka zai yi
ba, kuka fa sosai na samu ta na yi.
Nan da nan Haana sai ta rude. “Oh sister ki yi
hakuri ban san ciwon ya na damunki haka ba,
yanzu kin sha magani, Ya Abba mai ya sa ba ka
bata magani ba kaima ka tsaya kana ta yi mata
magana?. Rauda bai baki magani ba ko?”
Murmushi Rauda ta sake yi ta ce. “Sister ki
nutsu, ya bani magani na sha, na ga kamar kin rude
da yawa
Dole na rude da yawa Raudana, ba n1 da wata
yar uwa a duniya kamar ki, idan ina rashin lafiya
kema haka ki ke rudewa, kuma wannan rudewar
ma ban san na yi ba tunda kclema lokacin da ki ke
hakan ki ke yi. Ba na son na ganki CIkin damuwa
kO wan1 CIwo, please Rauuda ki yi sauri ki warke
Insha Allah zan warke Haana, tunda ga ki
kusa da ni har ma na ji na fara samun sauki.
Rauda ta fada ta na mai sanya murmushi kan
fuskarta.
Serious?. Haana ta fada cikin zaro manyan
Idanuwanta.
Eh mana. Rauda ta mayar mata cikin fadada
murmushin fuskarta. Gaba daya suka sanya dariya.
Ya Abba ne ya ce
To ni bari na wuce tunda na ga mai Ciwon ta
fara jin sauki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan Haana ta ce. “Kai Ya Abba, ya za ka tafi,
ai da ka tsaya mun yi hirar da kai don sai ta fi dadi
ma
Kar ki damu, ina da aiki ne, ba don haka ba sai
na zauna mu yi ta hira har sai kun ce da ni ya 1sa
haka na tashi na kara gaba
Sai ta yi dariya ta ce. “Shikenan Ya Abba sai ka
dawo Ta mai daga masa hannu alamar
bye bye. Sauri ya yi ya bar dakin. Don shi kadai ya
san abin da yake ji a zuciyarsa. Haka ya dinga jin
wata irin damuwa tare da wani irin shauki na so da
kaunarta da ya Ji suna ratsa masa zuciya. Ya dinga

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *