ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 4 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE
Mun tsaya
Ita kuwa Rauda abin da ta fuskanta shi ne, tsabar kishi ne ya fito Karara a tare da shi, to amma kuma ganin itama bai barta ba sai take tunanin kishin dai kawai ya fi nunawa a kansu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Take kuma wata zuciyar ta fada mata cewa kishin Haana ya ke yi, kawai dai ya yi miki haka ne don kar ki fahimci ya fi baiwa Haana kulawa ne.
Dole ta hadiye wani abu da ta ji ya taso mata a can Kasan zuciyarta. A Bangaren Haana kuma, ta Kudire a ranta, daga wannan rana babu abin da zai sa ta sake zuwa wajen nan balle kuma ta dauko wa
kanta damuwa irin wannan, duk kuwa son da ta ke . yiwa wasan. ‘ Haka kawai sai ta ji ta tsani wajen, ba ma ta sha’awarsa ko kadan yanzu. Duk yadda ta yi ta Boyewa Sameer damuwarta, sai da ya gane ta, don sau biyu yana neman da su je wajen, sai kawai ta ce masa kanta ne ya ke ciwo, haka zai ja su Rauda su tafi, har sai da aka gama wasan suka yi nasara a Karshen wasa. Ganin Sameer ya fiskanci sabon sauyi wajen ‘ Haana, don ko ya shigo gidan ba ya ganin walwalarta. Haka ya dinga jin yana zargin kansa. Sai kawai shima ya dauke Kafa daga gidan. Da ya shigo sun gaisa da su Granny sai kawai ya wuce abinsa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai kawai ya wuce gidan su Rauda’su sha hirarsu. A nan ne ya ke. tambayar Rauda da kuma yi mata Korafin ya ga canji a fuskar Haana ko ta fada mata wani abu game da shi.
Nan ta ce masa “Babu abin da ta fada min, sai dai ka bani zuwa gobe zan gano bakin zaren. A washe gari ne Rauda ta yi sallama ta shiga dakin Haana wacce ta ke kwance tana latsa wayarta. Ta na ganinta kuwa ta yi sauri miKewa zaune ta na fara’a ta ce,
“Rauda ke ce da wuri haka?, kin ganni nan tun dazu muke chart da Yaya Abba, sai wani ja min rai ya ke bayan kuma yadda mu ka yi da shi da na gama Exam zai dawo”’
Murmushi kawai ta yi sannan ta ce
“Jiya kuwa da daddare suke waya da Mami na karba nake tambayarsa yaushe zai dawo, sai kawai ce min ya yi, kawai mu zauna cikin shiri, za mu iya ganinsa ko da yaushe cikin kwanakin nan, bai dai fada min ranar ba nima”.“Ni ma haka ya fada min”. Haana ta mayar mata da amsar haka.Haana wajenki fa na zo’.
“Wajena kuma?, to ai ga waje nan zauna’. Ta fada tana yi mata murmushi. Kun yi sallama da Yaya Abba ne?”. Mun yi mana, ai ya ma sauka daga online din”“Ok ya yi kyau. Dama tambayarki zan yi, wai don Allah mai ya hadaki da Yaya Sameer ne, na ga kuna taKun saka da shi?” Turo baki ta yi gaba sannan ta yi magana “Oh shi ne_ya aiko ki kenan ko?”, . “Eh kusan hakan zan ce”, Kawai sai ta yi tsaki sannan ta ce “Rauda kada ki bata min rai kema don Allah, please ki barni bana son ina daukar damuwa bayan wacce nake da ita. Mutumin nan ya bani ciwon kai tun rannan”.
Murmushi Rauda kawai ta yi. “Sister ban sanki da daukar zafi haka ba, yaushe har ku ka yi sabon da shi da har haka za ta soma shiga tsakaninku?. Gaskiya dai ni ban ji dadi ba, kawai ki manta komai ku dawo kamar da”, Www.bankinhausanovels.com.ng
“Rauda ke kanki kin san babu wani da namiji da yake gabana bayan Malam M.J, to kuma akan me zai saka ni a gaba yana ta yi min fada don wasu mutane sun tsayar da ni. Ya ji me na fada musu ne da zai ta yi min magana haka, ni ai ba budurwarsa ba ce balle matarsa da zai ta yi min fada haka har da kuma tsawa, bayan bana son fada da tsawa”’.
“Kar fa ki manta, ke Kanwarsa ce, dole idan ya ga abin da ki ka yi ba dai-dai ba ya yi miki fada”. Cewar Rauda.
“Ok, kin goyi bayansa kenan, me na yi wanda bai dace ba, nice na je na janyo su ko kuma su ne suka kawo kansu inda na ke da za ki ce haka?”.
“Mayar da wukar Hajiya, na ga kin dau zafi da yawa wanda ni kuma ba hakan nake so ba. Dama
na zo ne don na baki hakuri ki sakko daga kan fishin da ki ka yi ku dawo kamar da, ba wai na zo ne don na Kara sanya miki wani fishin ba”.
“Babu komai na fahimta. Amma ni dai ki fada masa kada ya Kara yi min tsawa, don na fahimci yanzu ke din ‘yar koransa ce, ya barni na ji da abin da yake damuna na rashin jin duriyar ABIN ALFAHARINA”
“To Allah ya baki Malam M.J a matsayin mijinki”
Cikin murna ta rungumeta tana dariya sannan ta ce “Ameen sister dina, ta dalilin wannan fatan naki,.na janye duk wani fishi da haushin da nake ji na Mr.Sameer yanzu na daina shi”
“Ko ke fa, ai dama ban sanki da haka ba”.
Dariya ta yi ta ce. “Bari ki gani na kira shi a gabanki ki ji yadda za mu Kare da shi. Ai ni matuKar za’a danganta ni da Malam M.J za ai ta ganin farin cikina, don ni kadai nasan irin so da Kaunar da nake yi masa. Bari ki ji’ Www.bankinhausanovels.com.ng
Bugu daya daga na biyun ya dauka. Sallama ya fara yi cikin sanyin murya. Ita ma cikin shaKiyanci da dariya ta ce masa. ) “Oh hello Mr.Sameer ciwo ka fara don na daina kula ka?, har kuma da turo min ‘yar koranka da sassafe ta katse min Barci na. to dole kuwa ku fanshi Barci na da ku ka katse min”
Tana jinsa ya yi wata ajiyar zuciya har sai da ta ji ta dan shiga rudani kadan. Kawai dai ta share
“Haba Raihanatu, babu sallama ba gaisuwa sai kawai ki sabi zance. To idan ma na kwana da ciwon ai girmanki ne, sannan ki fadi ko nawane a fanshi barcin na ki ai za’a iya.
‘Da fatan dai kin tashi lafiya?. Jin muryarki ya sanya na ji wani kuzari a tare da ni, ina fatan dai ba za’a Kara horani da fishin nan ba”
Har cikin ranta ba ta so wannan sabon salon da ya zo mata da shi ba. Cikin sauri ta ce da shi
“To ina neman afuwa Mr.Sameer, babu komai kuma ya wuce. Sai anjima, ka huta lafiya”
Ta na fadar hakan ta yi sauri ta katse wayar. Cikin hikima ta kashe wayar gaba daya don kar ma ya kirata, kada kuma Rauda ta fahimci wani abu ya fada mata. Nan Rauda ta kalleta tace
“Haba ko ke fa, kinga ai haka ya fi, babu wani abu da zai ajiye a ransa yanzu’’.
“Humm! Rauda idan ma ya ajiye wani abu a ransa shi ya jiyo, ya ga kuma zai iya ne”.To ni dai mu bar maganar nan haka, kar kuma na wargaza abin da na shirya”’. “Da dai ya fi miki, Ni din abin da nake daga gareki, ki cigaba da sanya ni a cikin addu’arki Allah ya dawo min da Malam M.J cikin rayuwata. Ba na jin idan na rasa shi a rayuwata akwai kuma. wani da namiji da zan iya mallakawa zuciyata kamar yadda na mallaka masa tawa”’
“Zan yi miki insha Allah ‘yar uwa. Sai dai ni ma ina da wata shawarar da zan baki, ina son ki dinga sassautawa zuciyarki, kada ki Kwallafawa ranki abin da zai zo ya cutar da ke..saboda ba komai mutum yake nema kuma ya samu ba, amma har cikin zuciyata ina mai yi miki fatan samun abin da ki ke so.
Sannan kuma ki dinga neman zabin Allah, tunda har ku ka:‘rabu da Malam M.J bai furta miki cewa ya na sonki ba. Amma ranar da muka hadu da shi a Country mall a haduwarku da shi na fahimci cewa shima yana cikin so da Kaunarki, saboda ko
mai a aikace sonki ya bayyana a tare da shi, furta miki ne kawai bai yi ba har kuma ya zo ya tafi ba tare da kun yi sallama ba, Amma jikina ya na bani cewa da yardar Allah zai dawo cikin rayuwarki’,
“Ameen Rauda. Kema Allah ya baki abin da ki ke so a rayuwarki kamar yadda kema ki ke min‘fata’. Da wannan su ka rufe hirar ta su ta fito ta wuce gida abinta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Daga wanka ta fito, sai kawai taga alamar saKo ya shigo cikin wayarta. Ba ta bi takan wayar ba, Allah-Allah ta Ke ta gama ta dai ta zo ta duba, can kuma Sai ta yi tsaki saboda tasan dai ba zai wuce kamfanin mtn ba.ma da suka saba turo sako na babu gaira ba dalili. Wannan da ta tuna ya saka ta ma fasa zuwa ta dauki wayar. Tana gama abin da za ta yi Sai kawai ta wuce wajen Granny abinta. Haka kawai sai ta ji zaman falon ya soma isarta, duk da kuwa kallo suke ana kuma hira. Sai ta ji kawai gara ta je ta dauki wayarta kawai ta hau Social Network ko ta samu ta ji-dan sanyi cikin ranta. .
Ta na shiga dakin ta dauki wayar, sai kawai ta ga sakon da ya shigo mata ba na Mtn ba ne, sako ne daga wata baKuwar lamba (Number), kuma daga gani ba ta nan bace. Cikindoki ta shiga . ‘ dubawa. .
SALAM.
Rathanatu nasan na barki cikin tunani da Zulumi tare da Jiran tsammani wanda ko kadan ban — SO haka ba, sai dai ina mai baki hakuri
Rashin nutsuwar da na samu kaina a ciki ya Sanya na manta da kaina da ma komai. Saboda a duniyar nan ba ni da wani abu da nake so da Kauna kamar Mahaifiyata. Amma a yanzu kam
Alhamdulillah ta na samun sauKi, saboda mun samu nasara an dorata akan magaini jikin ya na yin kyau.
Na yi kewarki sosai da sosai, komai naki idan na tuna ya kan sanya ni nishadi balle yadda mu ka yi ‘yar tsama da ke. a duk lokacin da na tuna hakan, ko ina cikin damuwa ne sai na yi murmushi ina kuma addu’ar fatan Alkhatri a duk cikin rayuwarki,
Sai dai kuma na ji haushi sosai da na tafi ba tare da na taimaka miki ba wajen cimma burinki, wato hadaki da Zuri’arku da ku ka rasa. Amma insha Allah, Allah zai kawo miki wanda zai taimaka miki don ki samu cimma burinki
Daga Malain M.J. –
Shin wai murna ma za ta yi ko kuma kuka, dariya za ta yi ko kuma yake?. Ta karanta sakon ya fi sau shurin masaKi, amma ta kasa tsayar da abin da zuciyarta ta zaba mata. Kawai sai ta saki dariya ta sumbaci wayar ta ta, lokaci guda kuma ta ji hawaye ya wanke ma ta fuskarta.
Ta ke kuma zuciyarta ta umarce ta da ta kira lambar ta sa shi ne Kawai za ta iya jin sauKin abin da ya ke yi mata yawo a zuciyarta.
Ta na kiran wayer sai aka sanar da ita cewa a kashe ta ke. sai kawai ta runtse idanuwant, sai kawai ta kwanta ta yi shame-shame akan gadon. Ta jima a haka ba ta san abin da za ta yi ba. Ga kuma wani ciwo da ta ke ji a cikin zuciyarta.
Dora hannu ta yi akan Kirjinta saboda wani irin bugu da take ji a cikin zuciyarta. Jin dumin hawaye a fuskarta ya tabbatar mata da yanzu ne za ta iya yin wani abu, don ko ba komai ta dan samu afuwar zafin da ta ke ji a Kirjinta da kuma radadin da ta ke ji cikin zuciyarta na yi mata. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ya salam! Me ke faruwa da ni ne, me . wadannan kalaman na Malam M.J suke nufi, ba dai ya na nufin ya yi nisa da rayuwata ba ne, ya na’ nufin ba zai kuma dawowa cikin duniyata ba, ko kuma ya na nufin shikenan mun rabu ba za mu sake ganin juna ba?.
Idan kuwa haka ne, ina zai kai zuciyata da ta gama makancewa a so da Kaunarsa. Wato kenan ni kadai nake kida na kuma nake rawa ta. Yanzu shikenan ba zan sake ganin Malam M.J ba har abada, ashe ba sona ya ke ba ni kadai nake son shi?.
Ta ke kuwa zuciyarta ta ba ta amsa da cewa. “Wa ya fada miki ba ya sonki?, tunda ga shi ma har ya ce ya na kewarki, sannan kuma ya na yawan tunano abubuwan da ya gudana a rayuwar da ku ka yi da shi a makaranta”’
Kamar dai ta na kokawa da abin da zuciyarta ta fada mata, amma nan ta ke ta yi watsi da abin da zuciyarta ta zo mata da shi, cikin kuka ta furta.
“Ba ya sona, don bai fada min wani abu ba da Zai nu na min cewa ya na sona ba, tunda gata shi har addu’a ya ke yi min Allah ya kawo min wani cikin
rayuwata da zai taimaka min. wato kenan shi ya tafi har abada ba zai dawo min ba.
Wayarta ta dauka da sauri ta kira’ Zahra, ta ce don Allah ta daure ta zo tana cikin wata damuwa. Sannan ta kira Rauda.
Ba’a jima ba sai ga Zahra nan cike da fargabar me ke faruwa. A dakinta ta same su ita da Rauda. Ko gaisawa ba su yi ba ta hau tambayar me yake damunta?.
Rauda ce ta ba ta labarin abin da yake faruwa, sannan ta miKa mata wayar ta karanta saKon wayar. Shiru ta yi na dan wani lokaci, kafin ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce .
“Haana shawata daya zan ba ki, ita ce addu’a. dukkan wata musiba ta na bayan addu’a, ita kadai za mu yi Saboda sanin kan ki ne babu wadda za ta auri mijin wa ta, sai dai idan Allah ya Kaddara mijin naku daya
Daga ni har ke babu wanda ya san cikakken tarihinsa, ba mu san wane shi ba, shin me ya zo da shi, shin da aurensa ma ko ba shi da shi. Duk fa ba mu san wannan ba.
Nasan dai da ciwo ka rasa abin da ka ke so kuma yake sonka. Saboda ina da tabbacin shi ma Malam M.J ya na sonki kamar yadda ki ke son shi. Matsalar miskilancinsa da kuma jin kansa ne ya sanya har ku ka kai wannan lokacin bai bayyana miki ba, amma duk wani abu da ya ke bayyana so kun tattare daga ke har shi babu kuma wanda bai nunawa
Kin fahimci abin da yake cikin saKonsa da ya rubuto miki?. Ya yi kewarki sosai da sosai, har kuma ya na fadin babu abin da ya ke tunawa sai ‘yar tsamar da ku ke yi da shi, kuma duk lokacin da ya tuna sai ya yi murmushi ko ya na cikin wane irin hali ne. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kin ga kenan ya na yawan tunaki kamar yadda kema ki ke yi, wanda hakan ya samu ta sanadin tsamar da ku ke yi har ta kai ku da sonjuna. Ko – a nan muka tsaya, mun san cewa shima ya na sonki. Yadda kuma ba ki daina tunaninsa ba haka shima bai daina tuna ki ba”.
Cikin damuwa ta ce. “Zahra ba na son na yaudari kaina, ai kin ji abin da ya ce?. Allah ya kawo min wani cikin rayuwata da zai taimaka min”, Www.bankinhausanovels.com.ng
Dariya Zahra ta yi ta ce “Ai taimako ya ce zai yi, ba wai zai so ki ba ya ke nufi. Addu’a kadai za mu yi, don ba mu san abin da Allah ya shirya nan gaba ba”.
Rauda ta ce “Haka ne Zahra. duk na fada mata wannan. Shi ma wata Kila ya na can ya ma fi ta shiga damuwa, amma ga ta ita za ta janyowa kanta damuwa. Idan da bakya cikin ransa da ba abin da zai sa ya tuno ki har ya turo miki da saKo ya nuna miki cewa kina ransa”. Haka suka dage sai da suka kwantar mata da hankali kan abin da ya faru da ita. Dole ta saki ranta ba don ta so ba.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG