ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 



Mun tsaya 

Babbar damuwarsa shi ne yadda ya kasa gano
kan Miss Haana dinsa, sam ta ki ta ba shi time ko
bare har su yi magana.
Zuciyarsa tafi saka masa ccwa Ya Abba ne ya
Zuga ta karfi da yaji ya nunawa duniya cewa ya bar
masa amma yabi ta karkashin kasa yana yaki da
shi cikin ruwan sanyi yadda babu wanda zai gane
me yake faruwa.
Nasa tunanin kenan don haka ya yankewa ransa
yau zai nemi Ya Abba ya fada masa magana mai

zafi don ya ji irin abin da yake ji shi ma cikin
ransa.
Fadeelah kuwa murnarta na son komawa cıkı,
domin tun zuwan su Ya Muhammad tunda suka
hadu ranar da suka zo har kawo yau da suka kwana
biyu ba ta sake ganin fuskarsa ba duk ta tashi
hankalina Ya Abdul ne kadai ke kwantar mata da
hankali.
Cikin damuwa ta ce, “Ya Abdul don Allah wai
me yake faruwa Ya Muhammad yake boye min ka
san har yanzu ya ki bari mu hadu ko wani laifi na
yi masa ne?
Fadeelah ban san dalili ba me ye naki na daga
hankalinki bayan kun san ba zai bar garin nan
yanzuba na sani idan ba ku hadu ba yanzu na san
dole wata rana ku hadu ba na ji an ce shi zai aure ki
ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushi ne ya bayyana a fuskar ta ce, “Haka
ne Ya Abdul ashe kun ji to bari na koma anjima
zan dawo zan je na hada masa dishes irin wanda
yake so a gidan Hajiya Babba I know zai yi farin
ciki.”


Gaskiya ne da kuwa kin kyauta, kin san halin
angon naki ba dama gurin daukar dishes.
Dariya suka yi gaba daya ta ce, “Kai Ya Abdul
ai ba shi kadai ba ma har da kai bari na wuce ka
gaida min shi sai na dawo.”
Da hanzari ta fice tana bada baya yana fitowa
daga inda ya labe tsaki ya yi ya ce, ‘Kai yarinyar
nan tana son wahatar da kanta, ba ta san ba ta cikin
Tsarina  za tayi ta damuna daga bakina ba za ta ji
Nace da ila komai ba game da abin da ake so Sallamar da Mommy ta yi ita ce ta dakatar da
shi da cigaba da maganar suka yi saurin amsawa ta
samu guri ta zauna tace
“Mahammadu ya ku ka yi da kanwar taka da
fatan dai ba ka nuna mata halin naka ba, ban son
wata fitana ta biyo baya fa na ga tana farin ciki da
wannan hadin kaima kamata ya yi ka saki ranka.
“Mommy don Allah mu bar wannan batun ke
ma dai kin san abin da ke raina maganar Fadeela
mu ajiye ta tunda na ce bana yi ai ba a nemi
amincewa ta ba aka hada auran tunda na nuna bana
so to a bar ni mana.
“Mahammadu ban san kara jin wannan
maganar ta sake fitowa daga bakin ka kai ka ke iko
da mu ko mu muke iko da kai, tunda Mama Bara
tana son wannan auran bana jin akwai wanda zai
iya hanawa a yi shi, sai Allah ka fi kowa sanin halinta
babu wanda ya isa ya kawo mata wargi ko mu da
muke iyayenku ba mu isa tsallake maganarta ba,
bare ku da take iko da ku donhaka ba na son jin
wata magana makamanciyar wannan ta fito daga
bakin ka ka dai ji na fada maka.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Mommy me yasa za a yi min haka na sha
fadawa Fadeelah ta yi hakuri da ni ina da wadda
nake so me yasa da äka hada auranmu ba ta yi wa
Mama Bara bayani ba, ai ta san na sha fada mata
hakan.Mommy ba ni da matar da nake son aura a
duniyar nan da ta wuce Raihanatu, ita kadai nake
so, kuma da yardar Allah sai na aure ta duk abin
nan da nake fadi da tashi duk a kanta na yi shi ne
kuma su Daddy za su yi min haka.”
“Mahammad ka nutsu ba na son ka zo mana da
wata matsala da ban Raihanatun da ka ke magana a
kanta ba ka samu labarin cewa dan uwanka Sameer
shi ne wanda zai aure ta, tunda ka ga haka ta faru
ina mai tabbatar maka haka Allah ya tsara muku,kuma dukkan bawa babu wanda za iya tsallake
Kaddararsa ka ji na fada maka.
Ba zan so a ce daga zuwanka ka kawo mana
fitina da tashin hankali ba muna zaune lafiya cikin
zuri’a kowa yana farin ciki da wannan hadin kai
kuma ka zo mana da sabuwar damuwa.
“Mommy ki duba wannan abin ki gani fa
kamar ni aka fi kwara.”
“Muhammad za ka bar maganar nan ko kuwa?
Ta fada cikin dakewa.
Shiru ya yi bai sake cewa komai ba, don bai san
su soma jayayya da mahaifiyarsa.
“Fadeelah kuma ban yarda ka nuna mata ba ka
amince da maganar auranku ba.”
Tana gama fadin haka ta mike ta yi ciki.
Tattaro iska ya yi daga bakinsa mai zafí ya busar
waje, sannan ya rike goshinsa ya ce, ‘Ya Salam!”
Abdul ne ya dafa kafadarsa ya ce, “Barrister
Take it easy komai zai daidaita.
“Abdul this is somcthing huge ya ka ke so na yi
da raina? Www.bankinhausanovels.com.ng
Allah zai kawo yadda za a yi Yaya
Muhammad addu’a za mu yi ta yi.
T saye yake a bakin get din gidansu, nan ya
hango motar Ya Abba yana shirin fita ya gode
Allah dama gurin shi zai je sai kuma ga shi ya fito.
Matsowa ya yi don ya gan shi yana karasowa
gurinsa ya parker ya dan sauke glass din motar ya
Ce, Haji Sameer ya garin ne? Bayan ya yi masa
sallama.
Fuskarsa daure ya amsa ya ce, Sai godiya
dama gurinka za ni sai kuma ga ka idan ba za ka
damu ba sai mu yi magana ba wata mai tsayı bace
Cikin sakin fuska ya ce, “No problem bari na yi
gefe sai ka shigo. mu yi maganar idan ba za ta wuce
minti sha biyar ba.
Ya kara daure fuska ba na Jin sai na shiga kana
Ciki ma yanzu za mu gama ba za Ta kai mu wannan
mintinan da ka diba mana ba.
Murmushi Ya Abba ya yi don ya fara fuskantar
inda ya dosa tunda duk cikin fushi yake amsa masa
maganar tasa.
TO inaJinka.
Abu ne na ga ya canza shin ta wannan salon
yaudarar ka filo min da shi ka je ka zuge Miss
Haana ta yi min bore don kai ka same ta matsayin
mata ko to bari na fada maka duk makirCin da za
ka shiryo min ba ka isa ka raba ni da Miss Haana
ba ita ce burina kuma abokiyar rayuwata.
Dama na Jima ina mamakin cewa wai kai ne da
kanka ka ce ka bar min ita na aura, ka hakura, ashe
munafunci ne ka san ta inda Za ka bullo min me
yasa ba za ka baza kwanji ba mu shiga filin nema
ni da kai a ga wanda zai yi nasara’?
Abba ka ba ni kunya, tunda ka zama mai fuska
biyu kuma ba ka isa na bar maka ita ba, duk yadda
za a yi sai na aure ta.
Shi ke nan iya abın da za ka fada ko da saura
Ina son zan wuce?”
Ya Abba ya fada cikin kwanciyar hankali, ba
tareda nuna damuwar kalaman da ya jefe shi da su
ba, duk da kuwa ya ji ciwonsu.
Ran Mr. Sameer ya sake baci fiye da yadda na
da yake, ya ce, ‘Me zan sake fada ai na gaya maka
nedon ka sani ba ka isa ka raba ni da ita ba, ka je
ka sake tunani.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Murmushin yake ya yi wannan karon ya ce,
‘Sameer kai ya kamata ka je ka yi tunani da
zuciyarka, kan furuc
in da ka yi min A TUNANINA
tuni muka wuce wannan gurin ba ni da lokacin da
Zan iya tsayawa ina wannan batun da kai duk mu
biyun we are maturcd enough bana jin za mu dinga
abu kamar wasu yara kanana. Please think twice ni
na wuce.” Ya ci taya ya bade shi da kura.
Ran Mr Samcer idan ya kai dubu babu wanda
bai baci ba, ya bi motar da kallo cikin kunar rai, a
bayyane ya ce za ka san da wa ka ke magana mu
zuba da kai. Ya koma cikin gida abinsa.
Kamar kullum yau ma haka ya fito yana
hangen ta ta saman benen gidansu tunda suka dawo
kullum sai ya zo saman bene ya ga wucewarta
makaranta, sannan hankalinsa ya kwanta. Malam
M.J kenan da mutuniyarsa Haana.
Yau kwanansu hudu kenan da dawowa duk
gidan babu wanda bai je ya gaida iyayensa ba maza
da mata gida biyu ne bai yarda ya je ba gidansu
Rauda da Haana sai da ya tabbatar da duk sun tafi
makaranta, sannan ya je domin ba zata yake so ya
yi musu yadda za su yi mutukar mamakin ganinsa.
Tsananin son Haana kullum daduwa yake a
ransa bare ma da ya ji an ce an hada auransa da
Fadeelah sai ya ji kamar ma lokacin ya fara son
Haana din.
Daf da za ta wuce ta gaban gidan ta ji gabanta
ya fadi ba don komai ba sai don mutumin da take
hangowa kullum a barandar kullum idan za ta wuce
daf da ta zo za ta tsaya sai ya koma cikin falon yau
dai kin wucewa ta yi sai da ta dan tsaya a hankali
ta ga ana taba labule nan ta gano yana nan gurin
kare mata kallo yake son yi.
Wannan tunanin da ta yi kawai sai ta yanke
zuciyarta kawai ta yi gaba koma wane shi ya jiyo,
tana tuki zuciyarta na tuno mata abin haka ta ji tana
Son ganin wanene wannan mai mata leken?
Take zuciyarta tave Ke Haana kina da kirkı
kuwa ke mai son dangi ga yan uwanki da suka z0
ba ki je kin gansu ba Kin kyauta kuwa?
A bayyane tace Gaskiya ban kyauta ba, amma
guduun haduwa da haaya ne yasa ban je ba,
saboda ban san wacce amsa zan bata ba.
Wayarta ce ta shiga kara da sauri ta duba daidai
lokacin da ta fito daga estate din su ta hau babban
titi, sunan Fadeelah ta gani radau kan scrcen.
Sai da ta hau kan titi din sannan ta daga wayar
ta ce, “Hello “yar uwa wato an guje ni daga zuwan
Ya Muhaminad ko flash ba a yi min ba bare a tuna
da ni ana can ana ta soyewa.
Tsaki ta yi ta ce, “Kai Haana wace soyayya ban
da bakin ciki da wulakancin da na soma sha a
gurinsa ko kin san guduna yake kamar wata
dodanniya wallahi tun zuwansu sau daya na sa shi
a idona yana jin na shigo gidan zai tashi ya je ya
buya. Www.bankinhausanovels.com.ng
“What? Haka dama halinsa yake, amma ki ke
Son shi?”
“Ba za ki gane ba ne ‘yar uwa, Allah ya dasa
min tsananin son Ya Muhanmad ba na ganin ko
Wane da namiji a gabana idan bashi ba please
Haana time din ki ya yi na taimakona da za ki yi ki
Taya ni jawo ra ayinsa.
Tayi kwata ta ce, “Hala shi mutumne mai jin
kai da nuna isa?
*Ni ba zan gane hakan ba, ko me ya yi min ba
na ganin laifinsa, na san dai yana ji da ajinsa wanda
yana daya daga cikin halayensa da nake so.
“Ki bari na dawo daga makaranta ba wani
dadewa zan yi ba, ina tuki ne ko me yake ji da shi
zan sauke masa shi, kar ki damu na yi miki wannan
alkawarin Ya Muhammad ba ka isa ka yi wa
Fadeelah na haka ba, ka jira zuwana kai da kanka
za ka ba ta hakuri.
Murna ta kama Fadeelah ta ce, ‘Yar uwa da na
yi farin ciki mai tarin yawa kuwa idan haka ta
faru.
Don’t worry Fadeelah ina tare da ke
kodayaushe ina dawowa zan kira ki sai mu karasa
maganar.”
Nan suka yi sallama suka kashe wayar cikin
ranta ta ce Wai zuri’a dinmu me yasa muke da
maza masu jin kai ne da nuna gadara, idan ka cire
Ya Abba kowa sai na gan shi ko na ji labarinsa mai
zafi ne
Fadeelah nima ina cikin matsala da damuwa
fiye da ta ki, amma zan ajiye damuwata da matsala
ta na zo na taya ki samunnaki farin cikin tunda tun
farko na yi miki alkawarin hakan.
Matsalolina sun fara sani ina mantawa da
kaina, Ya Abba, Mr. Samcer, Rauda da Haaya
mutum hudun nan su ne matsala ta ban kuma san
yadda zan yi na warware ta ba, amma duk da haka
zan gwada ajiyewa na karbi taki matsalar na ga KO
zan iya nuki abin da ki ke s0 don kada na barki ke
ma ki shiga irin tawa matsala.
Sallama ya yi dakin kaninsa Abdul yana
kwance yana danne-danne wayarsa, bayan ya
amsa ya tashi ya ce, Barrister ta wuce ne?
Murmushi ya yi ya ce, Eh, ta wuce na ganta
kuma na ji dadi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Barrister wai me ka ke jira ne da ba za ka
bayyana ta ganka ba har yanzu ban da ni da
Mommy babu wanda ya san wannan boyayyiyar
dangantakar taku gwara ka je ta ganka ta yi mai
yiwuwa ba mamakI ma ta manta da kai tunda ba ta
yi tunanin za ka dawo ba, duba da ka ce tunda ka
tura text babu ko reply.
“Abdul, Raihanatu ba za ta taba mantawa dani
ba na gama gano ta, ta kamu da sona sOsai, irin son
da wuya ka manta da mutum a rayuwarka
matsayinta na mace ne yasa ta kasa furta min har
na tafi na bar ta, amma na gama gano komai a
kwayar idanunta da duk wanı move na ta.
I know Raihanah tana sona kamar yadda nake
jin sonta kullum na karuwa a zuciyata na gama
yanke wa zan tunkare ta ta gane cewa wane ne ni a
tare da ita ina ganin wasan buya din nan da na tara
ba zai kai ni ga samun abin da nake so ba.
Amma kafin nan zan fara ganin Sameer mu yi
magana a kan ya janye maganar aurenta ya bar min
Ita domin an halacci Raihanah ne domin ni kadai a
CIkin rayuwarta ba zan iya zuba ido na ga wanı ya
shiga rayuwarta ba ba ni ba.”
“Please Ya Muhammad ka dauki abin nan da
sauki kada ka zafafa kana ganin abin nan mai
yiwuwa ne kuwa?”
“Insha Allahuu babu abin da zai hana shi
yiwuwa.
To Allah ya bada nasara.
“Ameen Bros.” Gaba dayansu suka yi dariya.
Kwance yake a dakinsa wando ne three quarter
da riga armless ya yo kasa da kafafiunsa jikinsa na
kan gadon. Mr. Sameer kenan yana tunanin
damuwa da Ya Abba ya sa shi.
Knocking aka yi wa dakinnasa ya bada damar a
shigo. Turo kofa aka yi hade da yin sallama da
sauri ya mike daga kwanciyar da yake ya amsa
sallamar tare da mamakin ganin wanda ya shigo
dakin nasa. Ba kowa ba ne illa Malam M.J.
Ya dan razana da ganinsa amma da yake
wayayye ne sai ya yi saurin dakewa ya ce, ‘A’ah
mutanen turai sai yau kenan aka tuno da ni ga guri
Zauna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya nuna masa kujera da nuna cewa ya zauna,
mika masa hannu ya yi suka yi musabaha.
Murmushi Muhammad ya yi ya ce, “To ai tunda
ba ka neme mu ba mu sai mu zo inda ka ke tunda
hakan ba laifi ba ne.
“A yi min UZURI abubuwa ne suka yi min
yawa.
“An yi maka. Ya fada lokacin da yake Kokarin
Zama Kan kujera.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *